Share this page
k'asa a hankali tana mai masa wani irin wai-waye da shi, a haka har ta kai ga zuwa kan cikin sa. Cikin tsantsar k'warewa a salon iskanci ta cigaba da yin k'asa da hannun ta har ta k'arasar da shi zuwa kan mararsa dai-dai wurin robar wandon dake jikin sa, kana daga bisani kuma ta fara k'ok'arin tura hannun ta ciki. A kuma dai-dai locin Yarima Asad yaji abun da take shirin yi masa, hakan ne yasa yayi saurin janyewa daga jikin ta yana mai hurgar da ita a k'asa. Tukun ya fara aika mata da ruwan masifar sa cikin tsantsar zafin rai, domin kuwa babu abun da ya tsana sama da yaga yarinya na shirin haike masa, to fa daga wannan ranar ko wacece ke yake rabuwa dake, dan ko acewar sa wai har yau baiga macen da takai matsayin da zaiyi irin wannan mu'amalar da ita ba. Yayinda su kuma su Al'amin da suke yi yake musu kallon shasha-shu marasa aji, inda su kuma suke ce masa daga su har shi d'in basu da bam-banci ko a wurin Allah, tun da dai duk kalar abu d'aya suke ji idan sunyi, dan haka idan zai warema ya cire girman kai ya mori rayuwar sa yayi, idan kuma bazai ba to karya k'ara sanya musu ido, domin kuwa sunfi k'arfin su tsaya a iyakar jagwal-gwalo. Gaba d'aya sun manta da kalar girman zunubin da suke aikatawa. Wata irin mahaukaciyar dariya Billy ta kwashe da ita daga wurin da take, tana mai kallon baturiyar nan da take aikin rusar kuka zaune a k'asa. Tukun daga bisani kuma ta fara d'aga k'afafuwan ta cikin tsantsar farin ciki, tana mai dosar wurin da baturiyar nan take. Tsaye tayi a kanta tana mai aika mata da wani irin matsiyacin kallo, kafin daga bisani kuma ta buga wata irin k'wafa da matuk'ar k'arfi, tana mai juyawa ta tafi, zuciyar ta cike da k'udirin tunkarar Yarima Asad a gobe da nata salon ba gudu baja da baya, babu kuma sauran wani b'oye-b'oye. Yayin da ita kuma wannan baturiyar ta bita da kallo tana mai mamakin abun da yasa tazo gaban ta tsaya, kana kuma tayi mata tsaki da zata tafi, sai dai kuma damuwar da take ciki a yanzu ta rabuwa da Asad tafi bak'in ciki akan abun da Billy tayi mata, shi yasa ma bata bita taji dalilin ta nayin hakan ba, sabo da ba itace a gaban ta ba yanzu. A b'angaren Yarima Asad kuwa cikin tsantsar zafin rai da tafasar zuciya ya murd'a handle d'in k'ofar d'akin yana mai tura kansa ciki, tukun ya mayar da ita ya rufe gam. 'Dan madaidacin falo ne mai matsakacin girma da ya gaji da had'uwa. Duk da dai ba cike yake da kayan tarkace a cikin sa ba. Wasu irin itallian chair's ne masu azabar kyau zagaye a cikin d'akin. Sai wani d'an farin mini freg da yake kafe a wuri d'aya, yayin da k'asan d'akin kuma ya kasance shimfid'e da wani irin lallausan capet kalar yadin kujerun, daga saman capet d'in kuma wani glass center table ne a jiye a wurin. Tun daga bakin k'ofar ya fara cire guntayen kayan jikin sa yana mai fatali da su akan hanya, a haka har ya k'arasa cikin bathroom d'in da ya gaji da had'uwa, a lokacin kawai d'an guntun farin short-nika ne ya rage a jikin sa. Direct ya huce wurin da shower take yana mai zuwa ya kunna ta, tukun daga bisani ya matsa k'ark'ashin ta yana mai lumshe idanuwan sa ruwan ya fara sauka atsakiyar kansa, ba tare da ya cire short-nikan da ya rage a jikin sa ba. Lokaci d'aya ya fara sauke wasu irin tagwayen ajiyar zuciya, sabo da sanyin ruwan da yake sauka akan sa yana harbawa har cikin k'wak'walwar sa, wanda hakan yasa yaji zuciyar sa ta farayin sanyi. Sai da ya d'auki tsayin mintina goma shabiyar ak'ar-k'ashin showar, kana daga bisani ya kauce daga wurin yana mai k'arasa cire sauran sitirar da tayi ragowa a jikin sa, ya koma cikin jakuzie'n da yake cike da ruwan kumfan da ya had'a yayi zaman sa a cikin sa. *K'ASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAK'AR MASARAUTA.* Suna k'arasawa gaban ruwan wannan badakaran ya kamo k'afafuwan Bir duka biyun da hannun sa, tukun ya d ago su sama yana mai mayar da kansa k'asa, sannan ya d'aga sa daga tsayen da yake yana mai danna kansa a cikin ruwan nan. Take kuwa Bir ya fara wani irn shure-shure, yana mai hahaura k'afafuwan sa da matuk'ar k'arfi, tare da motsa jikin sa, amma sai dai kuma ko alamun k'wacewa baiyi ba daga hannun dank'are-ren mutumin nan mai sufa da samudawa. Sai da suka d'auki kimanin minti goma, tukun wannan badakaran ya zaro Bir daga cikin ruwan, yana mai yadda shi a gefe. Yayin da idanuwan Bir kuma sukayi wani irin kakkafewa, ga cikin sa kuma da yayi matuk'ar girma, alamum ba k'aramun ruwa yasha ba kenan. Da sauri wani badakare yayi kansa gadan-gadan, a lokacin da wancan d'in yayi cilli da shi a gefe. Yana mai k'arasawa wurin da yake, kana ya d'aga damb'areriyar k'afar sa d'aya, yana mai taka cikin Bir da ita. Take kuwa yayi wata irin d'agowa sama, bakin sa na futar da uban ruwa da matuk'ar yawa. 'Daga k'afa badakaran nan ya sake yi da matuk'ar k'arfi, yana mai direta akan cikin Bir. Wata irin k'ara Bir ya saki k'asa-k'asa, bayan wani ruwan ya sake futa daga cikin bakin sa da matuk'ar yawa, yana mai bud'e idanuwan sa tare da kifewa rufda ciki a k'asa. Da sauri d'ayan badakaran ya sake matsawa wurin da yake yana mai d'aga k'afar sa d'aya yayi wani irin k'wallo da Bir. Ai kuwa yadda kasan iska ta d'aga leda haka Bir yayi gefe yana mai zuwa ya gwaru da wata bishiya, tukun ya fad'i a k'asa. Wani irin jini ne mai matuk'ar gudu ya b'alle daga cikin gashin Bir yana mai tsiyayowa akan fuskar sa. Yayin da shi kuma yake ta sakin nishi da k'yar, yana mai juya juyi a wurin da yake cikin tsantsar azabar da take ratsa jikin sa, ga kuma idanuwan sa da suka furfuto waje tsabar wahala. A tare gaba d'aya dakarun nan suka sake d'aga k'afafuwan su suna masu nufar inda yake. Suna k'arasawa wurin da yake gaba d'ayan su suka zare mahaukatan bulalan su suna masu fara dukan sa da su ta ko ina, yadda kasan sun samu jaki, kai ko jaki ma bai can-canci amasa irin dukan nan ba kasancewar sa abu mai rai, sai dai ace gini ko dutse. Sai da suka yi masa jina-jina, ta yadda har ya zamto sai da k'yar yake iya motsi a wurin da yake, tukun babban cikin su ya kalli k'aramin su yana mai fad'in. "Kayi maza kaje ka sanarwa da Gimbiya cewar anyi tamkar yadda tace, umarnin ta na gaba kawai muke jira." Ya k'arasa maganar yana mai sa k'afa ya shuri Bir da ita. Yayin da shi kuma wannan badakaran da ya aika ya juya da matuk'ar sauri yana mai nufar hanyar da zata sadasa da wurin da Gimbiya Tasmir take. A b'angaren Gimbiya Tasmir kuwa cikin tsantsar zafin rai da k'unar, zuciya ta cigaba da tafiya da matuk'ar sauri tana mai dosar hanyar da zara sadata da b'angaren su. Sosai takejin zuciyar ta na wani rin k'una da tafar fasa idan ta tuna yadda Bir yayi mata k'uri da ido, har da su busa mata iskar bakin sa akan fuska. Wata irin tafar-fasa take jin zuciyar ta nayi mata tsabar b'acin rai, lokaci d'aya taji bata da wanda ta tsana sama da shi. Babu abun da ke k'ara k'ona mata rai sai yadda zuciyar ta ta dinga wani irin bugu a gaban sa, babban abun takaicin kuma shine tana barin wurin da yake d'i taji ta dawo gudu dai-dai, hakan ne yasa taji aranta tana mai son sanin dalilin da yasanya taji haka dan ta tsaya a gaban sa, tana son sanin me ya taka, wana kalar sihiri gare sa da har kallon sa ya sanya ta fad'uwar gaba. Har ta kusa k'arasawa b'angare nasu taja ta tsaya a wuri d'aya, ba tare da ta cigaba da tafiyar ba, tana mai rumtse idanuwan ta da matuk'ar k'arfi, sabo da tinanin da ya fad'o mata aranta, na sanin muddin ta shiga cikin gidan nasu a wannan yanayin na b'acin ran da take dole ne tasan sai wani daga cikin a halin ta ya tambaye ta dalili, wanda idan hakan ta faru take ganin bata da amsar da zata bayar, domin kuwa ba zata tab'a iya bud'e baki tace wani k'ask'antaccen Bawa ne ya b'ata mata rai, sabo da hakan zai zamto babban abun kunya mai muni ne gare ta, wato a matsayin ta na d'iyar Sarki Barbaru yar lelen sa, kuma ace Bawa ya b'ata mata rai, harya sanya bak'in ciki a ckin ranta ta yadda har ya bayyana akan fuskar ta kowa ya gani. Da matukar sauri ta juya baya zuciyar ta na cigaba da tafar-fasa, sabo da wannan tinanin da ya fad'o ranta, domin kuwa data fad'awa wani abun da ya faru da ita cikin 'yan gidan su, tana jin gwanda ta kwana ba a cikin sa ba. Hakan ne yasa ta d'auki hanyar wani lambu da yake acan bayan b'angaren su, wanda nan d'in ma dama yana d'aya daga cikin wuraren da take zama domin hutawa a lokuta da dama, kasancewar ba k'aramun dad'in wurin take ji ba. Kan wata had'ad'd'iyar kujerar gini ta zauna akai, tana mai d'ora k'afa daya akan d'aya, tare da lumshe kyawawan idanuwan ta. Zaman ta baifi da minti Ashirin ba a wurin wannan badakaran da aka aiko sa wurin ta ya k'araso wurin, kasancewar nan d'in ne wurin da ya fara yowa d'in dama, sabo da sanin da yayi na zai iya cin karo da ita a wurin, tunda wurin zaman ta ne dama. Tun daga nesa da ya hange ta zaune akan kujera ya juya baya da sauri, tukun ya fara tawowa da baya da baya yana mai yowa wurin da take, yana mai k'arasowa kusa da ita ya juya kansa sunkuye a k'asa yana mai fad'uwa k'asa wanwar yayi ribda ciki, kana daga bisani kuma ya tashi yana mai cake guiwoyin sa a k'asa, sannan ya bud'e baki cikin k'ank'antar da murya yana mai fad'in. "Anyi duk abun da kikace ayi ranki ya dad'e, yanzu kawai umarnin ki na gaba muke jira." Ya fad'a yana mai yin shiru tare da k'ara sunkuyar da kansa a k'asa. Yayin da ita kuma Gimbiya Tasmir take ta aikin karkad'a k'afarta ba tare da ta bud'e idanuwan ta ba har lokacin. Kana daga bisani bayan shafewar mintina bakwai da gama maganar tasa, ta d'aga masa tafin hannu ba tare da tace komai ba. Hakan da ya ganine ya sanya sa mik'ewa tsaye da sauri, tukun ya bud'e baki yana mai fad'in. "An gama ranki ya dad'e, na barki lafiya." Kana ya juya cikin sauri, yana mai dosar hanyar da ya biyo yazo wurin, domin kuwa tana nufin asake sane da da'ga hannun da tayi, sabo da tinanin da tayi na karta koma wurin kallon fuskar sa ya sanya ranta ya sake b'aci, duk da yadda tayi niyyar zuwa ta gansa bayan an gama masa hukunci a d'azu, shiyasa kawai ta bada izinin asake sa, domin kuwa tariga da ta sani tunda har suka ce an gama, to tasan anyi fiye da yadda take zato ma, wannan dalilin ne ya sanya ta bada izinin a sake san, sabo da tariga da tasan ko yanzu ya gane bam-bancin dake a tsakanin su. Cikin 'yan k'alilan lokaci wannan badakaran ya k'arasa wurin da 'yan uwan sa tare da Bir suke. Tukun ya bud'e baki yana mai fad'in. "Tace asake sa kawai." Hakan da Babban cikin nasu yaji ne ya sanya sa sake d'aga gundumemiyar k'afar sa d'aya, yana mai k'ara yin k'wallo da Bir, tukun suka juya suna masu yin tafiyar su. Yayin da shi kuma Bir ya sake yin sama tukun ya fad'o k'asa, sannan ya fara shirin tashi daga kwancen da yake, cikin tsantsar azabar da yake jin tana ratsa ko ina na ilahirin jikin sa, dan kuwa hatta da idanuwan sa sai da k'yar yake iya bud'e su, ga kuma jini da yake ta zuba a jikin sa. Jin da yayi ya kasa tashi zaune ne ya sanya sa fara jan ciki a wurin da yake, yana mai nufar hanyar da zata sada sa da b'angaren su na bayi, cikin tsantsar azabar da ke cigaba da ratsa jikin sa, amma a hakan fuskar Gimbiya Tasmir kawai yake hange acikin idanuwan sa, tare da d'an k'aramin bakin ta, da kuma dogon hancin ta, yana mai jin ina ma zai sake arba da ita yanzu a gaban sa, domin kuwa ko kad'an baiji ya gaji da ganin kyakkyawar fuskar ta ba, wacce ada bai tab'a tinanin haka take da kyau ba, sai yau da suka yi kusanci da ita dab da dab. Cikin tsantsar tashin hankali su Mauzum sukayo wurin da yake suna masu sakin Ihu tare da kiran sunan Iya, sabo da hango sa da sukayi daga can nesa yana tawowa da jan ciki, ga kuma jini dake bin jikin sa, dama kuma tini tun d'azu an kawo musu labarin ya had'u da Gimbiya bai gudu ba, har hankalin iyar bayi ya tashi. Cikin tsantsar rud'u Iyar Bayi ta futa daga cikin d'an-d'akin ta tana mai gyara d'aurin d'an guntun k'yallen da yake a k'ugun ta. Tukun tayi wurin da ta hangi Bir su Mauzu na shirin d'aukar sa, hankalin ta a tsantsar tashe. Yayin da su kuma su mauzum sukayo wurin da take hannun su d'auke da Bir, gaba d'ayan su suma a rud'e. A k'ark'ashin inuwar Bishiyar darbejiyar da take a gaban d'akin Iyar Bayi suka a jiye Bir. Yayin da Iyar Bayi kuma tayi saurin matsawa kusa da shi jikin ta na tsantsar karkarawa, tukun ta d'ago kansa da tafukan hannayen ta tana mai d'ora sa akan cinyar ta. Kana ta shafa lallausar sumar da take kwance a kansa, tana mai fad'in. "J...............✍ *BAK'AR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 26* "Jarumi! Jarumi!! Jarumi!!!" Iya ta faɗa cikin tsantsar ruɗu, tana mai shafa lallausar sumar dake kansa tare da bin burɗikan bulalan da suke kwance a jikin sa da idanuwa. "Me yaja maka Jarumi na? Akan me zaka shiga harkar Gimbiya bayan kasan ita ɗin ba tsaran ka bace ba? Wayo ni, wayyo ni na shiga ukku na lalace." Iyar bayi ta sake faɗa a tsantsar ruɗe tana mai jijjiga Bir, gaba ɗaya hankalin ta idan yayi dubu sai da duka ya tashi, domin kuwa tana yiwa Bir wata irin soyayya, fiye da wacce ta kewa duka sauran yaran data raina, tana mai jin sa a cikin ranta tamkar ita ta tsugunna ta haife sa, ita kanta wasu lokutan har mamakin kalar soyayya da take yiwa Bir ɗin take, amma idan ta tuna da itace ta riƙe sa tun ranar da yazo duniya, ta kula da cinsa shan sa wankan sa da komai nasa, sai taga ai dole ne ta jisa a ranta. Shi yasa duk wata damuwarsa take zamtowa tata damuwar itama. Da matuƙar sauri ta jayue kan Bir daga cinyar ta tana mai a jesa a ƙasa, tukun ta miƙe cikin tsantsar ruɗu tana mai kama hanyar ɗakinta. Ko minti biyar ba tayi ba da shiga ɗakin sai gata nan ta futo hannun ta ɗauke da ƙwarya, tana mai sake yowa inda suke. Cikin ƙanƙanin lokaci ta zuba duka ƙullikan magun-gunan data ɗauko na ciwukan a cikin ruwan da yake a cikin ƙwaryar. Sannan ta fara ɗibar ruwan da hannun ta tana mai watsawa Bir shi a jiki. Yayin da gaba ɗaya wurin kuma ya kasance zagaye da ƴan uwan su Bayi suna ta kallon su. Shi kuwa Bir lumshe idanuwansa yayi, yana mai jin yadda ruwan ke ratsa duka ciwukan jikin sa. Amma ko kaɗan ba sune damuwar sa ba, asalima babu abun da yake gani a cikin idanuwansa face kyakkyawar fuskar Gimbiya Tasmir. Yayin da yake ganin ɗan ƙaramin bakin ta a cikin idanuwan sa a lokacin da take motsa sa tana tambayar sa waye shi. Lokaci ɗaya wani irin murmushi ya suɓuce masa ta gefen baki, sabo da tino yadda ranta yayi tsantsar ɓaci da yayi, domin kuwa ba ƙaramun kyau yaga ta sake yi masa ba a hakan. Ji yake inama ace yanzu ma idan yayi wurin zai sake ganin ta, tabbas da babu abun da zai hana sa sake tsayawa a wurin, domin ya ƙara arba da kyakkyawar hallitar ta. Sosai Iyar Bayi ta shafewa Bir duka jikin sa da maganin nan. Kana bayan ta gama ta ɗago kansa tana mai buɗe baki tace. "Shin ma mene ya kai ki shiga sabgar Gimbiya Jarumi na? Yanzu duba fa kaga irin illar data sanya aka yi maka." Ta ƙarasa maganar cikin sanyi, idanuwan ta a kan fuskar Bir da take ganin yana ta sakin murmushi lokaci bayan lokaci. A hankali Bir ya fara buɗe idanuwan sa har ya buɗe su duka akan fuskar Iyar Bayi. Tukun ya saki wani irin murmushin gefen baki yana kallon ta, kana ya buɗe baki cikin yin ƙasa da murya, ta yadda ita kaɗai zataji abun da zaice mata, yana mai faɗin. "Rabo ne Iya ta." "Rabo kuma Jarumi, wannan wana irin rabo ne haka mai tafe da tsantsar tsautsayi?" Iya ta faɗa tana mai kallon Bir, tare da mamakin jin furucin da ya futo daga cikin bakin sa. "Ba zaki taɓa fahimta ba a yanzu Iyata, amma tabbas akwai lokacin yana nan zuwa, wanda ba iya ke kaɗai ba kowa ma zai fahimta." Ya ƙarasa maganar yana mai sake lumshe idanuwan sa, tare da gyara kwanciyar kansa akan cinyar Iyar Bayi. Yayin da ita kuma tayi sakato tana mai binsa da idanuwa, fargaba da tsoron abun da yake shirin aikatawa na cika zuciya da ruhinta, domin kuwa tasan halin ɗan nata, duk abun da yace zaiyi to fa zaiyi san da gaske bada wasa ba. "Koma dai mene ne Jarumi, na roƙeka daga yau akan karka ƙara cewa zaka tsaya akan hanyar Gimbiya tamkar yadda kayi yau, domin kuwa ban shirya yin kukan rashin ka ba anan kusa." Cewar Iyar bayi tana mai cigaba da shafa kansa. *ENGLAND* Cikin tsantsar farin ciki Billy ta koma mazaunin su. Ko da ta koma zaune ta samu Zee a gefen bed tana kwalliya, da alamar futa zatayi itama. Inda take bata kalla ba ballan tana har ta bata labarin abun da ya faru, domin kuwa tun da ta ga Zee bata bata karfin guiwa ba akan son da take yiwa Yarima Asad gaba ɗaya ta dena bata labarin sa, sannan kuma ta kudurta a ranta cewar sai ta bata mamaki, sai ta tabbatar mata da cewa ita Billy'n da ban take da sauran matan, haka kuma tun da ta zo duniya bata taɓa neman abu ta rasa -sa ba. Yayin da Zee kuma ta juyo ɓarin da Billy take fuskar ta ɗauke da far'a, tana mai faɗin. "To ya dai Beb, ina fatan dai yau an dace ko?" Ta ƙarasa maganar tana mai gumtse dariya a cikin bakin ta. Yayin da ita kuma Billy ta kalle ta tana mai faɗin. "Uhm!" Kawai. Kana tayi shiru tana mai ɗaukar wayar ta ta fara shafata. Miƙewa Zee tayi tana mai fucewa daga cikin room ɗin gumtse da dariya a cikin bakin ta, yayin da cikin zuciyar ta kuma takewa Billy kallon ƴar wahala. *WASHEGARI* Da mafarkin YarimaAsad Billy ta kwana, kamar yadda ta kwanta da tinanin sa a ranta. Hakan yasa yau tana ta shi da safe ta shirya shaf-shaf cikin shigar doguwar riga tare da ɗan ƙaramin mayafi akan ta, tana mai fucewa daga cikin room ɗin su ba tare da ta yiwa Zee ko sallama ba. Direct ta huce wani haɗaɗɗen wuri da akayi sa domin gyaran gashi, tun daga kan na maza har zuwa na maza. Sosai wuri yayi bala'in haɗuwa, domin kuwa gaba ɗayan sa anyi sa ne da glass. Ba tare da ɓata lokaci ba aka fara yi mata gyaran gashin tare da wankin ƙafafu, kasancewar wuri ne babba da yake cike da wadatattun ma'aikata, shi yasa ba afiya haɗa dogon layi ba ana jira kafin azo kan mutum. Cikin lokacin da bai zarce awa ɗaya ba aka gama yi mata gyaran gashin nata tare da wankin ƙafafuwan, tukun ta zauna wata baturiya ta fara tsantsara mata wasu irin ƴan mitsi-mistin kitso da gashin dokin da jelolin sa suke saukowa har zuwa gadon bayan ta. Sai da suka ɗauki kimanin awa huɗu suna abu ɗaya tukun aka gama, kuma wai a hakan ma sabo da an yiwa kan nata rubdugu ne, domin kuwa bayan waccan da ta fara yi mata har da wasu matan guda biyu ne suka ƙaru akan ta, wato dai mutum ukku ne suakyi mata kitson. Misalin ƙarfe ukkk na rana ta dawo mazaunin su. Zaune ta tadda Zee akan kujera tana cin abinci. Da sallama ɗauke abakin ta-ta shigo ɗakin. Kana ta huce zuwa kan dining table ɗin da ta hangi food flask ajiye a kansa, tana mai zuwa ta fara zuba abincin da yake ɗauke a cikin su. Yayin da Zee kuma ta juyo gare ta tana mai faɗin. "Ke ko Billy wannan wane irin gyaran kai ne aka miki haka mai jan mugun lokaci." Ta ƙarasa maganar tana mai ture plate ɗin dake kan cinyar ta, tukun ta tashi tana mai dosar wurin da Billy take. Yayin da ita kuma Billy ta buɗe baki daga wurin da take tana mai faɗin. "Da yake ba iya gyaran kan kawai akayi ba, har kisto sai da aka yi." Ta ƙarasa maganar tana mai zame mayafin kanta kitson ya bayyana. "Kai masha Allah, kinga yadda kitson yayi bala'in haɗuwa kuwa Beb. Kai tukunna ma, wai meke faruwa ne haka da na ganki tun jiya kina ta wasu gyara-gyare?" Zee ta faɗa daga wurin da take tsaye idanuwan ta akan kitson Billy, da yayi matuƙar tafiya da ita. "Ba zaki gane bane Beb ko nace zan miki bayani I know, but just wait and see, ina mai tabbatar miki da sai na baki mamaki a yau -yau ɗin nan." Billy ta faɗa in serious toungue, tana mai sakarwa Zee murmushi. Yayin da Zee kuma ta jijjiga kai daga wurin da take tsaye, sabo da fahimtar inda kalaman Billy suka dosa da tayi. Kana daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Can't wait to see, but firstly ina miki fatan Al'khairi." Ta ƙarasa maganar tana mai komawa kan kujerar da ta tashi ta zauna, tare da mayar da idanuwan ta kan tv'n da take kallo. Misalin ƙarfe huɗu na yamma dai-dai Billy ta futo daga cikin bathroom. Ɗaure take da wani lallausan farin towel a jikin ta. Yayin da hannun ta kuma yake riƙe da wani ɗan ƙarami tana mai tsane ruwan jikin ta da shi. Direct ta huce gaban dressing mirrow ɗin da yake cike danƙam da kayan kwalliya kala-kala. Kujerar da take ƙarƙashin sa ta janyo tana mai zama akan ta, tukun tayi wurgi da ɗan ƙaramin towel ɗin da yake riƙe a hannun ta a ƙasa. Kana ta janyo mayukan da take shafawa tana mai fara matso su a cikin tafin hannun ta, tukun ta murza su, kana ta shafe sa akan lallausar fatar jikin ta da take ta faman glowing, alamun ba ƙaramun daɗi ake jiyar da ita ba. Cikin ƙan-ƙanin lokaci ta gama mutsika mayukan, tare da tura-rirrikan jikin da take amfani da su a jikin ta, kasancewar lokacin zaman Asad ya kusa, shi yasa take komai cikin sauri. Ba tayi wata kwalliya ba mai yawa akan fuskar ta, domin kuwa powder kawai ta shafa tare da lips bam akan laɓɓan ta, sai kwallin da ta sanya acikin idanuwan ta, sabo da jin labarin da tayi na cewar kwalliyar cika fuska bata birge Asad ko kaɗan a binciken da tayi akan sa. Mayar da duk abubuwan da tayi amfani da su tayi zuwa mazaunin su, tukun ta miƙe tsaye daga kan kujerar da take akai, tana mai juyawa ta doshi wurin da wadrobe ɗin su take. A gaban haɗaɗɗiyar wadrobe ɗin ta tsaya tana mai ɗora hannun akan murfin ta ta buɗe sa, sannan ta fara bin sababbin ƙananan kayan da suke saƙale a cikin ta da idanuwa. Ta ɗauki tsayin mintina huɗu tana kallon kayan, tukun daga bisani ta miƙa hannun ta zuwa ciki tana mai ɗorasa akan wata haɗɗaɗiyar baƙar riga mai tsananin kyau, da tsayin ta zai iya kai mata har guiwa idan tasa ta. Ɗauko ta tayi tana mai ajiye ta a gefen gado, tukun ta sake mayar da hannun ta ciki tana mai zaro

Chapter 27 of 76