zubawa a cikin ruwan ɗaya bayan ɗaya har tasa duka, yayin da kalar ruwan kuma duka ta sauya lokaci guda, tana mai komawa ruwan ɗorawa.
Miƙewa tsaye tayi bayan ta ɗauki wasu layoyi masu matuƙar yawa ta riƙe su a hannun ta, sannan ta juya ɓarin da mazan nan suke riƙe da abubuwan nan da ta ɗauko su yanzu, tana mai faɗin.
"Kuyi maza ku gyara mun turamen nan yanzu, ya zamto sun zagaye wannan kaskon ruwan."
Tayi maganar cikin harshen fulatanci, tukun ta juya ɓarin da Hadimar Gimbiya Kaɓel take tana mai sa hannu ta ɗauki jinjirar nan tsirara, ba tare da ta haɗa da showel ɗin ba.
Yayin da su kuma Hadiman nan maza suka yiwa turamen kamar yacce tace suyi musu.
Layoyin da suke riƙe a hannun ta ta ɗaurawa yarinyar a kan ƙaurin ta duka biyu, kana ta kama damtsen hannuwan ta suma ta sanya musu wasu layoyin, sannan ta durƙusa ƙasa tana mai matsawa gaban kaskon nan, tukun ta rumtse idanuwan ta da ƙarfi tana mai fara yin wasu irin surutai.
Take a wurin wani kalar hayaƙi ya fara futa daga cikin ruwan, yana mai wani irin juyawa, tukun ita kuma ta tsunduma ƴar jinjirar nan acikin ruwan tana mai sanya tafin hannunta ɗaya, ta fara ɗebo sa tana zubasa ajikin ƴar tun daga kan gashin kanta.
Tsanyarewa da kuka jinjirar tayi da matuƙar ƙarfi, yayin da su kuma waƴan nan makaɗan suka fara buga kayan kiɗan su suna masu fara ɗirkar rawa, tare da zagaye turamun nan suna ɗaga hannuwan su sama cikin tsantsar farin ciki.
Ita kuwa kaka har yanzu idanuwan ta a rumtse suke tana aikin sakin wasu irin surutai daga cikin bakin ta, kana kuma tana cigaba da ɗebo ruwan tana zuba sa a jikin jinjirar.
Bata ita ta dena surutan ba har sai da taji ruwan nan ya dena juyawar da yake yi tas, sannan kuma ya dena futar da hayaƙin da yake futarwa, tukun ta buɗe idanuwan ta tana mai kaisu zuwa cikin ruwan.
Wani irin murmushi ne ya suɓuce mata, sabo da yarce taga ruwan ya koma fari kar, yacce take son yayin dama, domin kuwa komawar tasa farin shine yake nufin ai'kin yayi, wato an bawa yarinyar tsafin kenan itama.
Miƙewa tsaye tayi tana mai cilla ƴar jinjirar dake aikin tsala kuka sama, tukun tayi sauri ta caɓe ta, haka tai-tayi mata har kimanin sau ukku, sannan a ƙarshe ta zurata a cikin ɗaya daga cikin turaman nan bayan ta caɓe ta.
Tukun ta juya tana mai zuwa wurin da ta ajiye sandar nan da ta futo da ita.
Ɗaukar ta tayi a hannun ta tana mai riƙeta gagam, sannan ta buɗe baki cikin harshen fulatanci da ƙarfi bayan ta kalli jama'ar dake wurin, tana mai faɗin.
"To Jama'a ku shaida, ni Gimbiya Unau, matar Tsohon Lamiɗon Masarautar Fulɗe, nayi kyautar sandar tsafi na ta gado wacce nima na gaje ta a wurin Kakata ga kyakkyawar jika ta da aka haifomun ita yau halak malak, domin ta zamto mata kariya a rayuwar ta."
Ta ƙarasa maganar da sakin murmushi, tana mai matsawa gaban turaman nan.
Yayin da su kuma makaɗan nan suka canza salon kiɗi bayan jama'ar hurin sun saki ihu da tafi, a lokacin da Kaka ta gama bayanin ta.
Sosai wurin ya sake turnuƙewa da rawa da ihu, sabo da kiɗan da ke tashi mai tsantsar daɗi.
Yayin da ita kuma kaka ta ƙarasa zuwa gaban turmin da jinjirar nan take a ciki, sannan ta ɗaga sandar ta tana mai riƙe ta da hannu biyu, tukun ta fara zagaye turaman tana mai yin wasu irin kalamai da ƙarfi, kana daga bisani ta tsaya a gaban wanda jinjirar nan take a ciki, tukun ta ɗan zura sandar cikin turmin tana mai durƙusawa ta kamo hannun jinjirar da yake a dunƙule ta warasa, tukun ta ɗora sandar akan tafin hannun yarinyar.
Take kuwa ta ɗan riƙe jikin sandar a ƙoƙarin ta na ta sake rumtse hannun ta.
Hakan ya sanya Kaka rangaɗa wata irin buɗa da matuƙar ƙarfi, tukun ta janye sandar daga cikin turmin tana mai faɗin.
"Haƙiƙa kyauta ta karɓu, ke kika zamto ƴar gata gare ni, domin kuwa ke kaɗai ce kika samu kyauta mai daraja irin ta sanda ta a wuri na."
Ta ƙarasa maganar tana mai a jiye sandar a ƙasa, sannan ta koma ta ɗauko jinjirar a cikin turmin, tukun ta miƙa ta zuwa hannun Hadimar Gimbiya Kaɓel.
Amsar ta tayi tana mai sanya ta cikin showel ɗin ta lulluɓe ta da shi, tukun ta juya ita da tawagar ta da suka biyo ta suna masu komawa wurin da suka futo.
Yayin da ita kuma Kaka ta fara ɗibar kayan tsafinta tana mai mayar da su cikin bukkar nan, su kuma waƴan nan turamen Hadiman nan suka sake ɗaukar su suna masu tafiya da su wurin da suka ɗauko su.
Sai da Kaka ta gama mayar da komai banda sandar nan, tukun ta mai da ƙofar bukkar ta rufe ta, sannan ta juya tana mai ɗaukar sandar ta doshi hanyar ɓangaren Gimbiya Kaɓel, domin taje ta damƙa mata sandar jinjirar tata.
*JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.*
Yau aka tashi da tsantsar farin ciki a ɓangaren Gimbiya Fulani, sabo da haihuwar Ƴa macen da tayi da asuba itama, bayan shafe shekara takwas da tayi rabon ta da haihuwa, wato tun bayan haihuwar Yarima Asad da yayi matuƙar girma da wayo yanzu kenan.
A lokacin da sautin kiɗin tambarin Ƴa mace ya daki kunnen magautan ta ba ƙaramun farin ciki sukayi ba, domin kuwa dukan su dama suna cikin tsantsar fargaba ne ako da yaushe, sabo da tsoron abun da kunnuwan su zasu juyo musu.
Yayin da ita kuma a ɓangaren ta sukayi matuƙar farin ciki da samuwar ƴar, wacce ta ɗebo kamannin mai martaba sak, yarce kasan kaki yayi ya tofar.
A ɓangaren Asad kuwa yafi kowa farin ciki da murnar haihuwar da Mamayn tasu tayi musu, badan komai ba kuwa sai dan sanin da yay na za'ayi hawan suna a ranar suna, gashi shi kuma dama ya kasance mayen doki, sabo da yaga yacce akayiyyi a lokacin da Gimbiya Huwaila ta sake haihuwar ƴa macen da bata so ba, sannan kuma da lokacin da Gimbiya Amina itama ta ƙara haifo ƴa mace, wannan dalilin yasa yake ta fatan asake yin wata haihuwar a gidan su, sabo da mai martaba yace masa ya bari sai an sake wata haihuwar, tukun sai ya fara yin kilisa, shima a lokacin ya ƙara girma, sabo da yarce yaso abar sa shi kaɗai akan dokin sa shekaru biyu baya da suka huce lokacin da Gimbiya Amina ta haihu, amma mai martba yaƙi, hakan ne yasa yayi matuƙar farin ciki da haihuwar da mamyn tasa tayi fiye da duk sauran yaran, domin kuwa yanzu shi da kansa yake hawa dokunan sa ba tare da wani ya riƙe sa ba.
A ɓangaren Babban Yaya sosai yayi ya zama saurayi, domin kuwa a yanzu yana da shekaru goma shatakwas ne a duniya dai -dai, a karatu kuma yana matakin ajin ƙarshe na secondry ne, kuma da zarar ya kammala za atura sa ƙasar turai jami'a, kamar yacce sauran yayyan sa mata da kuma ƴan gidan duka suke karatun su acan.
*UNGUWAR ƊAN TANKI.*
Sai da Aishatu ta shekara bakwai da haihuwar da tayi a Baƙar Masarauta, tukun ta sake haihuwar wani Ɗa namijin, wanda yake da shekara ɗaya a duniya yanzu kenan, mai suna Salman.
Har kawo yau dai tana nan da halayyar ta ta rashin son yin magana da kuma zaman cikin ɗaki, sannan kuma bata bar tinane-tinanen nan da takeyi ba, kamar yacce a kullum daren duniya take mafarkin wannan yaron da koda yaushe yake ƙara girma.
Yayin da Ahmda kuma yake da shekara goma shatakwas yanzu a duniya.
A fannin karatun boka yana matakin ajin ƙarshe na secondy ne yanzu, yayin da fannin na addini kuma ya sake yin matuƙar zurfi, domin kuwa a yanzu haka har aji yake da shi a Islammiyar su, sannan kuma yake jan sallah a wani sabon masallacin kamsu salawat da aka buɗe anan cikin unguwar tasu aka basa limancin sa, kasancewar duk yafi sauran yaran harma da manyan ilimi a unguwar, hakan kuwa ba ƙaramun farin ciki ya sanya iyayen su ba.
*ƘASAR MALIN, YANKIN JAHAR KARFU CIKIN BAƘAR MASARAUTA.*
Cikin tsantsar farin ciki ta durƙusa ƙasa, tana mai sa hannu ta ɗauki kyakkyawa jinjirar dake ai'kin tsala kuka da matuƙar ƙarfi, ta ɗora ta akan showel ɗin da yake ninke a gaban ta, bayan ta yanke mata cibi, tukun ta ɗago tsaye tana mai rangaɗa w..............✍
_HAR YANZU LABARIN BAI FARA BA FA. DOGUWAR TAFIYA CE, MAI 'DAUKE DA ABUBUWA KALA-KALA ACIKINTA. AZABABBIYAR SOYAYYA, SADAUKARWA, TSANANIN BAN TAUSAYI, TARE DA MATUK'AR ZALINCI DUK SUKE ACIKIN LABARIN BAK'AR MASARAUTA. AYI COMMENT DA SHARHI HAKAN SHI ZAI SA MUJE HAR ZUWA WURIN DA NAKE FA'DA MUKU._
*BAƘAR MASARAUTA*
*NA*
UMAR FARUQ*D*
*PAGE 18*
Wata irin buɗa mai matuƙar sauti, yayin da ita kuma ɗaya ta juya a guje tana mai fucewa daga cikin ɗakin domin taje takai rahoto.
Cikin ƙanƙanin lokaci gaba ɗaya labarin haihuwar Ƴa macen da Gimbiya Salwa tayi ta zagaye duka cikin Baƙar Masarauta.
Lokacin da labarin ya isa kunnen Sarki Barbaru ba ƙaramun farin ciki yayi ba, domin kuwa tsabar murnar da yayi da jin labarin a take a wurin yayiwa Hadimar da ta kawo masa Albishir ɗin kyautar Raƙumi ɗaya.
Tukun ya miƙe daga kan kujerar sa cikin sauri yana mai kama hanyar waje.
Ko da ya ƙarasa cikin ɗakin zaune ya samu mahaifiyar sa riƙe da jinjirar a hannunta, tana shafeta da mai.
Da sauri ya ƙarasa zuwa inda suke yana mai zube guiwoyin sa a ƙasa, tukun ya buɗe baki cikin tsantsar farin ciki, idanuwan sa a kan fuskar kyakkyawan jinjirar da ya gani, yana mai faɗin. "Shin da gaske ne ba mafarki nake ba, wannan kyakkyawar jinjirar ta wace?" Ya faɗi maganar ta sigar tambaya, yana mai kai yatsun hannuwan sa zuwa kan ƙafar jaririyar ya riƙe.
"Tabbas kuwa ɗiyar kace a gaske kake ganin ta ba mafarki ba, haƙiƙa Ubangiji Gargabilu yay mun kyautar jika mace." Tsohuwar matar da take zaune tukuf riƙe da Ƴar ta faɗa tana mai kallon fuskar Sarki Barbaru ɗauke da murmushi a bakin ta.
"Godiya ta tabbata ga Ubangiji Gargabilu, haƙiƙa kagamamun komai da kabani kyautar ƴa mace." Sarki Barbaru ya faɗa yana mai miƙa hannu ya ɗauki Ƴar.
Zaman sa ya gyara a wurin da yake, yana mai tanƙwashe ƙafafuwan sa, sabo da yaji daɗin riƙon ƴar da kyau, tukun daga bisani ya miƙa hannun sa zuwa inda yaga wata ƴar roba mai matuƙar kyau da take a gaban Mahaifiyar tasa, yana mai janyo ta gaban sa, tukun ya buɗe murfin ta.
Baƙin fenti ne tare da soso mai yankan Tambarin Masarautar tasu a cikin sa.
Hannu ya sanya yana mai zaro soson daga ciki, bayan ya dangwalo fentin, sannan ya ɗago sa yana mai kai sa kan fuskar yarinyar ya manna mata shi a kan goshi, kana ya sake manna mata akan kumatunan ta duka, har lokacin fuskar sa ɗauke da tsantsar murmushi.
Kyakkyawa ce a jin farko jinjirar, gata da wani irin yalwataccen gashi da yake sunƙum tun da ga kan ta har zuwa kan fatar jikin ta.
Sosai take da girma yacce kasan wacce tayi irin sati ukkun nan a duniya. Banda wawurar yatsu tana kaiwa baki tare da wuwwurga manya-manyan fararen idanuwan ta masu ɗauke da baƙar ƙwaya huluk a cikin su babu abun da take yi.
Ɗago ta Sarki Barbaru yayi, bayan ya gama manna mata tambarin masarautar a jikin ta yana mai riƙe ta a hannun sa, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin farin ciki, idanuwan sa ƙur a kan jinjirar, yana mai faɗin.
"Shekarau da dama ina zaman jiran zuwan ki, idanuwan sun daɗe suna tsumayen ganin ki, kunnuwa sun jima suna son jin sautin muryar ki, yayin da hannuwa kuma suka ɗau tsawon shekaru suna nararin jinki akan su, amma Ubangiji Gargabilu bai yaddar ba sai yanzu, dan haka na miki alƙawarin zamtowa Uban da babu kamar sa a duk faɗin duniya a gareki, Uban da ko a lokacin baya ba ayi kamar sa ba.
Zan baki gata irin gatan da babu ɗiyar data taɓa samun kalar sa a duniya, zan hanaki kuka, sannan kuma na sanyaki dariya ɗiya ta, zan baki kariya irin kariyar da ba'a taɓa baiwa wata ƴa kamar taba a gidan duniya, sannan kuma zaki zamto Jaruma irin Jarumar da babu kamar ta a faɗin duniya, zaki zamto jaruma wacce tarihin ta zaiyi shuwura ya zagaye duk duniya, Jarumar da tarihin ta bazai taɓa gushewa ba, wannan alƙawari ne na ɗaukar miki yake Ƴata."
Ya ƙarasa maganar yana mai rungume ta a ƙirjin sa, tukun daga bisani ya janye ta yana mai miƙa ta zuwa hannun mahaifiyar sa, sannan ya miƙe yana mai juyawa ya fuce daga cikin ɗakin.
*BAYAN SATI ƊAYA.*
Yau ta kasance ranar sunan jinjirar da aka haifa, hakan ne yasa tun daren jiya ake ta shirye-shirye a cikin Baƙar Masarauta, tare da girkuna kala-kala.
Duk inda ka gifta banda Bayi Mazan su da Matan su babu abun da ake gani.
Yayin da filin da za'ayi bikin suna kuma ake ta aikin shirya sa, wani irin kiɗa mai matuƙar sauti da daɗi na tashi daga cikin sa.
Zagaye yake da randina manya manya da suke ci da huta ta ko ina, yayinda daga can jikin bango kuma aka a jiye wasu irin kujeru masu tsananin kyau da suka ji uban ado a jikin su, daga can tsakiyar filin kuwa nan ma ɗin wani ƙatoton kaskon hutar ne a ajiye.
Yayinda acan kan wani dakali kuma da yake a gaban filin aka saƙale wasu irin danƙara-danƙara Shanu har kimanin guda goma shabiyu, sai daga gefen sa kuma manya-manyan tukwane ne ɗore akan duwar-watsu suna ci da huta, har kimanin guda takwas, da alamun dai girki akeyi ne a wurin, duba da yarce matan hurin suke ta faman ƙara iza wutar, ga kuma kayan ayukka irin su robobi da fanteku da suke a jiye a gaban su da matuƙar yawa.
Misalin ƙarfe goma na safe dai dai salon kiɗan da ake bugawa a wurin ya canza, tukun daga bisani sai ga tawagar Bayi nan Mazan su da Matan su sun fara shigowa cikin filin da rawa, sai dai kuma a wannan karan babu wani abu da yake ɗauke a hannuwan su, kasancewar ba bikin godiya bane ake yi, sai ma tsantsar murmushi da annashuwa ne da suke a kwance a kan fuskokin su.
Shigowar su duka baifi da muntina biyar ba, sai ga tawagar su Sarki Barbaru nan sun tawo Dakaru na take musu baya.
Sarki Barbaru ne atsakiya kamar yacce suka saba tawowa idan suna taro, sai dai wannan karan kuma hannun sa ɗauke yake da Ƴar jaririyar da aka haifa.
Yayin da gafe da gafen sa kuma matan sa biyu Gimbiya Haiwa da kuma Gimbiya Salwa mai jego suka kasance, gaba ɗayan su suma sunci uban ado mai matuƙar ɗaukar hankali da tsada a jikin su, a gefen su kuma yaran su ne maza suke biye da su, yayin da bayan yaran kuma da gefe da gefen su kuma duk dakaru ne, hannuwan su riƙe da bulalai tare da makamai soke a jikin su.
Sanye sarki Barbaru yake da wasu irin kaya masu matuƙar kyau da tsada a jikin sa, yayin da jinjirar dake riƙe a hannun sa kuma aka sanya mata wata doguwar riga mai tsananin kywu da tayi mata dai dai a jikin ta, sai wasu ƴan takalma masu tsananin kyau da suke sanye a ƙafar ta.
Kai tsaye suka doshi gaban kaskon hutar da yake a tsakiyar fili dukan su.
Zagaye kaskon sukayi a dai dai lokacin da suka ƙarasa gaban sa, tukun Sarki Barbaru ya yaye showel ɗin da yake ƙudun-dune jikin jinjirar yana mai cillasa cikin hutar kaskon nan, sannan ya ɗaga ta sama yana mai tsayar da ita asaitin kaskon hutar nan, tukun ya buɗe baki cikin sauti yana mai faɗin. "Gargabilu! Garbailu!! Gargabilu!!!" Da tsantsar ƙarfi.
Take kuwa jama'ar dake wurin suma suka ɗaga murya da matuƙar ƙarfi suna masu faɗin hakan, yayin da ita kuma jinjirar na ta tsanyare da kuka.
Ƙara gyara riƙon Ƴar Sarki Barbaru yayi a hannun sa, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin.
"Jama'a ina son ku shaida, ni Sarki Barbaru na sanyawa Ƴata mafi soyuwa a raina suna TASMIR, a yau bayan shafewar kwana bakwai da zuwan ta duniya.
Na raɗa mata suna Tasmir akan darajar shanu ɗai-ɗai ɗai-ɗai har kimanin guda Goma shabiyu mafiya girma daga cikin shanun da nake da su, sannan kuma nayi Al'ƙwarin bata kariya a yanzu, irin kariyar da babu wata ɗiya mace a duniya da take da kamar ta."
"Huuuuuuuuuuu!!!"
Ɗakacin Jama'ar dake cikin filin suka sanya ihu da matuƙar ƙarfi, tukun daga bisani Boka mai wutar kasko ya taso daga kan shimfiɗar da yake zaune yana mai yowa wurin da su Sarki Barbaru suke.
Hannu ya miƙa yana mai amasar ƴar a hannun Sarki Barbaru a lokacin da yazo, bayan ya gama shirya kayan tsafin sa duka, sannan ya fara saɓulewa jinjirar kayan da suke sanye a jikin ta a bainar jama'a, har ya cire mata su tas, tukun ya rumtse idanuwan sa yana mai kai ta gaban kaskon wuta ya fara sakin wasu irin surutai da matuƙar ƙarfi.
Ya jima yana surutan yadda kasan bazai dena ba, tukun daga bisani ya tsaya da surutan da yake yin yana mai buɗe idanuwan sa, sannan ya sake miƙa hannun sa ya ɗauko wani ruwan tsumin magani da yake a cikin kofi, yana mai wanke ƴar tas da shi, tukun ya sake miƙewa tsaye yana mai ɗaga ƴar sama a hannun sa, kana ya buɗe bakin sa bayan yakai ƙwayar idanuwan sa kan jama'a yana mai faɗin.
"Haƙiƙa kariya ta tabbata a jikin Gimbiya Tasmir irin kariyar da babu mai kamar ta, kamar yacce ubanta ya buƙaci ta samu, sannan kuma Jarumta da ƙarfin zuciya zasu dawamma a gare ta ta sanadin irin ai'kin da aka yi mata."
Ya faɗa yana mai miƙawa Sarki Barbaru ita, yayin da su kuma jama'ar dake wurin suka sake buɗe baki suna masu faɗin.
"Gargabilu! Gargabilu!! Gargabilu!!!"
Da tsananin k'arfi suna masu ɗaga hannuwansu sama.
Amsar ƴar sarki Barbaru yayi, tukun ya juya yana mai kaita kan shimfiɗar fatar da take shimfiɗe a gaban su ya kwantar da ita, tukun ya miƙe tsaye yana mai kai hannun sa zuwa kan ƙugun sa, bayan ya shigar da shi cikin al'kyabbar dake sanye a jikin sa, ya zaro wata irin Takobi mai matuƙar tsawo da ƙyalli.
Juyawa yayi gaban mutane yana mai kallon su, bayan ya ɗaga Takobin tasa sama, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin muryar sa mai futar da amon sauti yana mai faɗin.
"Ni Sarki Barbaru, a yau nayi kyautar Takobin tsafi na tare da macijiya ta wacce Kaka na ya bani su zuwa ga ƴata abar ƙaunata Tasmir, domin su zame mata kariya a rayuwar ta."
Ya ƙarasa maganar cikin ƙaraji, yana mai juyawa ya kalli inda ƴar tasa take, tukun daga bisani ya rumtse idanuwan sa da matuƙar ƙarfi, bayan ya ɗaga Takobin tasa ya nuna gefen wurun da jinjirar take a kwance da ita, sannan ya buɗe baki cikin muryar sa mai matuƙar amo yana mai faɗin.
"Rai Rai Rai Rai Buuuu Hoooo Reeeeee!" Da tsananin ƙarfi, take kuwa a wurin Takobin nan tayi wani irin kawo farin haske a jikin ta yana walwali.
Buɗe idanuwan sa yayi a kan Takobin yana mai girgiza kai, tukun daga bisani ya sake buɗe baki yana mai kallon gefen wurin da Jinjirar take a kwanc,e tare da faɗin. "Shairamaaa!" Da tsananin ƙarfi.
Take kuwa wata irin danƙare-riyar macijiya ta bayyana tana mai karkaɗa harshe ta, idanuwan ta ƙur a kan fuskar Sarki Barbaru.
Yayin da shima ɗin yake kallon ta da nasa idanuwan ba ƙiftawa, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin muryar mai amo yana faɗin.
"Shairama ga Ƴata nan Mace ɗaya ƙwal a duniya, ina son daga yau ki koma gare ta, sannan kuma ki zamto mata kariya a bokiyar shawara agare ta kamar yacce kika zamto agare ni, ki kasance mai bayyana a duk lokacin da ta buƙace ki, sannan kuma ki share mata hawayen ta a duk lokacin da takawo miki kukan ta, kamar yacce kikai mun, domin kuwa wannan jinjirar da kike gani a gefen ki itace farin ciki na, ina sonta tamkar yacce nake son rayuwa ta, ina sonta irin soyayyar da nake yiwa abun Bauta Gargabilu, wannan dalilin shine ya sanya na bar mata ke ni kuna na haƙura, domin kuwa ni na sani zata fini buƙatar ki, dan haka gata nan kusa dake daga yau itace shugabar ki ba ni ba."
Ya faɗa yana mai matsawa kusa da wurin da jinjirar take kwance ya cake Takobin a gefen ta.
Yayin da ita kuma Macijiyar nan tayi wata irin juyawa, tukun ta fara tafiya tana mai zuwa ta fara hawa kan jinjirar ta dinga kanan-naɗe ta, sai da ta gama kanan-naɗe ta tas, tukun ta zaro harshen ta tana mai lasar fuskar jinjirar da shi, sannan daga bisani ta fara barin jinkin jinirar tana mai yin wurin da Takobin nan take a cake.
Kanan-naɗe Takobin tayi tas, tukun daga bisani kuma ta ɓace ɓat yarce ƙasan ba a taɓa yin ɗuriyar taba a wurin.
Take a wurin kuwa ɗaukacin jama'ar dake wurin harda su Sarki Barbaru da iyalan sa suka sanya ihu, suna masu faɗin.
"Gargabilu! Gargabilu!! Gargabilu!!!"
Yayinda shi kuma sarki Barbaru ya ƙarasa wurin da huƙar nan take a cake yana mai funcike ta daga cikin ƙasa, sannan yasa hannu ya ɗauki jinjirar tasa, tukun ya juya yana mai kaita wurin Mahaifiyar sa da take tsaye duk a kusa da su.
Amsar ta tayi tana mai sanya mata wasu sababbin kayan da wata Hadima ta miƙo mata su yanzu, ba wayan da aka cire mata ba, tukun ta mayarwa Sarki Barbaru ita.
Gaba ɗayan su ɗaga ƙafafuwan su suka farayi suna masu dosar wurin da kujerun nan suke a ajiye.
Yayin da makaɗa kuma suka cigaba da sakin kiɗi da matuƙar ƙarfi, maraya na ai'kin ɗirkar rawa.
Su kuwa Bayi mata Iyaye hucewa sukayi zuwa wurin da tukwanen nan suke, suna masu buɗe su suka fara ɗibar abinci suna zubawa a manya-manyan farantai, yayin da su kuma Ƴammatan Bayi ke ai'kin ɗaukar abincin suna kaiwa mutane su.
A ɓangaren Bayi Maza manya kuwa, su hurin da shanun nan suke a saƙale suka huce suna masu ciro su, aka zuba musu kayan haɗi akan su, kana aka kwarara musu mai mai matuƙar yawa, tukun suka matsa da su jikin huta suna masu fara babbake su.
Haka dai akai ta shagali a ranar, ana yankan nama anaci tare da kaɗaɗe, maraya na ai'kin dillaƙar rawa kowa cikin tsantsar farin ciki.
*ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.*
Ko ina ka kalla cikin Masarautar jama'a ne suke giftawa ta ko ina, kowa da kalar shigar dake sanye a jikin sa, kasancewar yau ne sunan jinjirar da Gimbiya Fulani ta haifa.
Tun safiya a kayi raɗin suna yarinya taci suna Bilkisu, wato sunan mahaifiya Gimbiya Fulani, hakan yasa Gimbiya Fulani tayi mata laƙabi da BABY.
Sosai a keta shagali tun safe, har zuwa yanzu da a kayi sallah la'asar ana shirin yin hawan suna, kamar yacce aka saba ako wace haihuwa da akeyi a cikin Masarautar.
Yau Yarima Asad jin ta yake tamkar sallah a wurin sa, koma ace fiye da sallah, kasancewar yau ɗin itace rana ta farko da zai fara yin hawa akan doki ba tare da wani ya riƙe masa dokin sa ba, daga shi har Al'amin.
Ana idar Sallahr la'asar a cikin masallacin Masarauta Yarima Asad da al'amin suka futo cikin sauri.
Sanye suke da wasu azababbar shadda ɗin kin doguwar riga tare da wando a jikin su, da sukayi matuƙar yi musu kyau iri ɗaya a jikin su.
Cikin sauri suka kama hanyar part ɗin mai Martaba, kasancewar anan kayan su da zasu sanya yanzun suke, domin kuwa gaba ɗaya yau ɗin kaya iri ɗaya suka sanya da su da Mai Martaba, duk da dama shi Asad kusan kullum hakan ne yanzu, dan kuwa rabon da Mai Martaba yayi ɗinki shi kaɗai ba tare da an masa ba tun kafun a yaye sa.
Suna shiga cikin part ɗin suka ci karo da Jakadiya zaune a kan kujera daga bakin ƙofar ɗakin Mai Martaba, yayin da hannuwan ta kuma suke riƙe da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 76