dokin, tukun suka saki rigunan su ƴan lufudi kuma suka matso hannuwan su riƙe da bulalai suna masu buɗa hanya.
Yayin da ta fannin Babban yaya shima ya haye saman nasa dokin tini suna masu yin gaba, kasancewar sai bayan sun huce tukun Sarki zai huce, sai dai kuma har lokacin bai fasa faman wurga idanuwan sa cikin mutane ba dan ya hango ƙanin nasa, amma sai dai har suka ƙarasa filin hawa aka fara wasa da dokuna baiga ko Al'amin ba balle har yasa ran zaiga Asad, hakan yasa ya ƙudurta aransa da zarar sun gama hawan nan zai huce wurin Gimbiya Fulani Mamyn su, domin su tattauna da ita akan shawarar da ya yanke akan Yarima Asad, danko ba ƙaramun ciwo sukeji ba acikin ransu na hallayar sa shi da mahaifiyar su.
Ba'a tashi gama hawa ba sai gabannin magariba, tukun jama'a sukai ta watsewa kowa na komawa inda ya futo.
Afannin Babban yaya shima yana sauka daga kan doki ya huce masallacin su na nan cikin Masarautar.
Ko da aka idar da Sallah bai tsaya ko ina ba ya huce sashin mamyn su kai tsaye, domin yaje su tattauna akan yarce zasu ɓullowa Asad kamar yacce suke kanyi kullum.
*JAHAR KAGUL, CIKIN MASARAUTAR FULDE.*
Cikin tsantsar firgici da ruɗu Gimbiya Haddiyal ta ɗago kanta tana mai watsa manya manyan idanuwan ta da suka sake yowa waje akan fuskar Dadden tata.
Tukun daga bisani ta fara ɗaga laɓɓanta tana mai girgiza kai, wasu irin hawaye na ɓallewa daga cikin idanuwan ta, yayin da ita kuma mahaifiyar tata ta janye idanuwan ta daga kan ta tana mai mayar dasu wurin Innahuro da take manne ajikin ta, ta fara shafa gashin kanta.
Zumbur Gimbiya Haddiyal ta miƙe tsaye yarce kasan wacce aka tsikara, jikin ta na tsantsar rawa, banda ai'kin girgiza kai da ɗaga laɓɓa babu abun da take iyayi, sai idanuwa data kefa mahaifiyar tata dasu, tukun daga bisani ta juya da matuƙar sauri yarce kasan zata kifa aƙasa tana mai dosar hanyar ɗakin ta.
Uhm! Mahaifiyar tata ta sauke ɗan gajeran numfashi tana mai bin bayan Gimbiya Haddiyal da idanuwa, tukun daga bisani ta taɓe baki tana mai girgiza kai, kana ta janye idanuwan ta daga kan hanyar tana mai ɗaukar inibin dake cike acikin ƙwarya wanda Innahuro keci ta fara ci itama.
Cilla ƙafafuwan ta kawai take aduk inda ya samu ba tare da tana lura ba, sabo da tsantsar tashin hankalin da take ciki, ahaka har Allah yakai ta cikin ɗakin ta lafiya.
Kai tsaye ta doshi gaban tanƙashe-shen mudubin da yake manne ajikin bango ɗakin, tana ƙarasawa gaban sa taja ta tsaya tana mai ɗora hannuwan ta akan sa ta dafa sa.
Kallon kanta ta farayi acikin madubin tana cigaba da girgiza kai, kana har lokacin kuma hawaye basu bar tseren gudu ba daga cikin idanuwan ta, tukun daga bisani ta buɗe baki cikin kaushi tana mai faɗin. "Shin me Baffah ke nufi ne da zuwan Jauro (Yarima) Masarautar Yamma? Shin ina zan kai shi Gaɗaɗo am kuma? Inyi ya ya da soyayyar sa dake cunkushe aƙasan zuciya da ruhina?
Inaaa hakan bazai taɓa yuwuwa ba wallahi, babu wani ɗa namijin da yakai in kulasa balle har ya zamto miji gareni bayan Giɗaɗo am!
Ni Gimbiya Haddiya an halicceni ne domin Giɗaɗo am kaɗai kamar yacce aka hallice sa domin ni, dan haka babu tayarce za'ai in bari wani mahaluƙi ya zamto shamaki atsakanin mu, Wallahi! Wallahi Jauro'n Yamma kayi kaɗan na zamto taka, domin ko fatar ka bazata taɓa jure zafin bulalar shaɗin aure na ba, darajarkar bata kai ka mallaki ko takalmin ƙafata ba balle har na zamto mallakin ka, zanyi amfani da ƙarfin ikona wurin ganin na lalata gaba ɗaya shirin ku akaina."
Ta ƙarasa maganar da ƙaraji tana mai kaiwa bango duka, tukun ta juya tana mai yin taku biyu daga inda take, kana ta sake ja ta tsaya cak awuri ɗaya, tukun ta sake ɗaga laɓɓa cikin kaushi tana mai faɗin.
"Kai da kanka zaka koma kace musu banyi ba Jauron Yamma, domin ko bazan taɓa yimaka ba kamar yacce ba ayini dan nayiwa wani ba bayan Giɗaɗo am."
Ta ƙarasa maganar tana mai fara ɗaga ƙafafuwan ta ta doshi bakin gadon ta.
Zama tayi akai tana mai buga uban tagumi da hannu bibbiyu, tare da kafe bangon dake kallon ta da idanuwa.
*JAHAR WASAI*
Anan cikin Masarautar wasai kuwa baki ɗauke da sallama Babban yaya ya tura kansa cikin bedroom ɗin Mamy'n tasu, kasancewar bai sameta afallo ba shiyasa yayo nan ciki.
Zaune ya hangeta akan darduma tafukan hannayen ta ɗage asama tana addu'a, da alamun yanzu ta idar da sallah itama.
Wucewa yayi can ciki yana mai ƙarasawa bakin gado ya zauna tare da ɗaga tafukana hannayen sa shima suka ƙarasa addu'ar tare.
Ɗago kai tayi tana mai kai idanuwan ta inda yake.
Dasauri ya sakko ƙasa yana mai ƙarasowa kusa da ita ya zauna, tare da tanƙwashe ƙafafuwan sa akan haɗɗaɗen kafet ɗin da yake shimfiɗe aƙasan ɗakin, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin tsantsar ladabi da biyayya yana mai faɗin. "Barka da hutawa, tare da fatan kina yini lafiya Mamy na."
Murmushin ta wanda ya zamto kalar nasa dana Asad kamar yacce kamannin su suka zamto ɗaya sak ta sakar masa tana mai kallon sa, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Alhamdulillah, fatan kuma duka kuna lafiya."
"Kowa lafiya ƙalau wallahi mamy na." Ya faɗa yana mai sakar mata murmushi, yayin da ita kuma ta sake gyara zama tana mai ƙara fuskantar sa, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Ya kuma taro ya tashi."
"Alhmdulillah Mamy." Ya faɗa shima yana mai sake fuskantar ta.
Gyaran murya tayi, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "To ni dai nasihar da zan maka amatsayina na mahaifiyar ka kan wannan jagorancin da aka baka itace.
Atakaice shidai shugabanci ba wani abu bane face wani babban nauyi da Allah yake ɗorawa mutum, dan haka nake shawartar ka da ka zamto adalin shugaba wanda al'umnar sa zasuyi alfahari da shi, kayi koyi da shugabanci irin wanda fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi Wassallam yay. Domin ko ita shugaba garkuwace da ake yaƙi abayan ta, ake kariya da ita, dan haka idan shugaba yayi umarni da tsoron Allah yayi adailci to yana da lada, in kuwa ya ai'kata saɓanin haka to wannan laifi yana kansa. Bukharine ya rawaito.
Hakanan kuma wajibi ne shugaba ya zama mai adalci tsakanin sa da talakawan sa, sabo da adalci shine tushen rayuwa, kuma sai da adalci ne al'amura ke dai-daita duniya da lahira.
Sannan kuma Sheikhul Islam Ibni taimiyya yana cewa. Al'amuran mutane na duniya suna dai-daita ne da adalci da yake haɗe da nau'ika na zalunci, fiye da yadda al'amura zasu miƙe da zalunci acikin haƙƙoƙi, ko da kuwa basuyi tarayya azunubi ba, dan haka akace Allah yana tsayar da daular mai adalci koda kuwa musulma ce, hakanan akace duniya tana dawwama da adalci da kafirci, amma bata dawwama da zalunci da musulunci."
Ta faɗa idanuwan ta akan sa, yayin da shi kuma babban yaya ya durƙusar da kansa ƙasa yana mai sauraran ta jikin sa na tsantsar ƙara yin sanyi, kana kuma yana godiya ga Allah da ya azurtasa da uwa tagari acikin zuciyar sa.
Zama ta sake gyarawa tana mai ƙara fuskantar sa, tukun ta ƙara gyara zaman hijab ɗin dake sanye ajikin ta, sannan ta ɗora da cewa. "Manzon Allah Sallalahu Alaihi Wassallam yana cewa. Babu wani zunubi daya fi sanya azaba da wuri fiye da zalunci da yanke zumunci. Azzalumi ana bugeshi aduniya koda kuwa an masa gafara da rahama alahira, sabo da adalci tsarine acikin komai da komai, idan aka tsayar da al'amarin duniya akan adalci sai komai ya tsaya, koda kuwa ma'abocin duniyar nan bashi da rabo alahira, idan kuwa ba atsayar da al'amuran duniya akan adalci ba, to lamarin bazai tsaya ba, koda kuwa ma'abocin sa yana da imani da zai ishesa alahira. (Duba maj'mu'ul fatawa 28/146).
Hakanan shugaba ya zama ƙarfi wajen zartar da abun da yake gaskiya ne acikin talakawan sa, ya nisanci zalunci, da ƙarya, da cin amana, da ha'inci da sauran munanan halaye. Wannan sune kaɗan daga cikin haƙƙoƙin talakawa akan shuwagabannin su, dan haka wajibi ne akan shuwagabanni su kiyaye waƴan nan haƙƙoƙin, sabo da al'amuran talakawan su amana ce awuyan su, kuma Allah zai tambaye su abun da ya basu kiwo daga bayin sa."
Ta ƙarashe maganar tana mai sa hannu ta zame hijab ɗin dake sanye ajikin ta, tukun ta miƙe daga kan prayer mat ɗin da take kai tana mai komawa bakin gado ta zauna.
"Nagode sosai Mamy na, Allah ya saka da alkhairi, rabbi yayi mana jagora cikin duka harkokin mu albarkacin fiyayyen halitta."
Babban yaya ya faɗa yana mai miƙewa ya koma kan wata mayyar royal chair da take kafe daga jikin bango.
"Amin ya rabbi." Mahaifiyar tasa ta faɗa tana kallon sa, tukun daga biani ta ɗora da faɗin. "Ina ƙanin naka yake ne, rabon da muhaɗu tun safe yau, ɗazu kuma Baby take cemun yace mata ta kirani tazo bata saman ba?"
"Uhm! Mamy ai Asad ɗin naki ne sai dai addu'a kawai, amma yaron nan kullum girma yake ƙarawa amaimakon yayi hankali sai dai wani sabon salon shirmen da yake ƙara futowa da shi, dama yanzu haka ma akan batun sa nazo wurin ki." Babban Yaya ya faɗa yana mai kallon mahaifiyar tasa.
Yayin da ita kuma ta girgiza kai tana mai lumshe idanuwan ta ba tare da tace komai ba, sai dai kuma kallo ɗaya kawai zaka mata kasan akwai damuwa aƙasan ranta, sabo da yarce yanayin fuskar ta ya nuna, tukun daga bisani ta buɗe idanuwan nata akan fuskar Ciroma tana mai faɗin. "To yanzu kai me kazo da shi akan batun kenan?"
Wai Mamy ace Asad ko bakin fada bai jeba balle harya hau doki ayi hawa da shi, kai ataƙaice ma duka baya cikin gidan nan ya fuce ya tafi yawon sa. "Cewar Babban Yaya" ransa duk ba daɗi.
Murmushi mahaifiyar tasu ta saki, wanda kana ganin sa basai anfaɗa maka ba zaka san na yaƙe ne, tukun daga bisani ta buɗe baki idanuwan ta akan Ciroma tana mai faɗin.
"Kaima fa abun da ka riga kasani ne, babu tayarce za'ayi ZAKI yaje fada, tunda yasan irin mutanen da zai tarar aciki da kuma kalar shigar da kowa keyi wacce shi yake ganin ƙauyanci ce agaresa idan yayi ta, sannan kuma shi kansa wurin hawan kasan ba zaije saba duk yarce yake da maitar doki, ko da ko bai bar cikin gidan nan ba, tunda yasan ana kaɗa-kaɗe da bushe-bushen da bai son jin kalar su." Ta faɗa tana mai cigaba da sakin murmushin yaƙe, tukun daga bisani ta tsayar da murmushin da take yin tana mai ɗorawa da faɗin. "Akullm akuma kowane daren duniya sai na kai goshina ƙasa ina roƙon Allah ya canza masa dabi'un sa, ya dawo mutumin ƙwairai kamar kowa, amma shiru kake ji har yanzu." Ta ƙarasa maganar jikin ta na yin sanyi.
"Ki kwantar da hankalin ki Mamy na, akwai mafuta da nazo mana da ita, wacce sheikh Ahmad ya samar mun da ita, sannan kuma ina tinanin insha Allah idan har nayi aiki da ita komai zai zo ƙarshe bi'izinillah." Babban Yaya ya faɗa yana mai gyara zaman sa akan kujerar da yake kai.
Cikin sauri mahaifiyar tasa ta buɗe baki tana mai faɗin. "Shin wata kalar mafuta ce kenan?"
"Ashekaranjiya da muka zauna karatu da sheikh Ahmad, bayan mun gama sai nake kora masa bayanai akan hallayar yaron nan, to shine ya cemun tunda har ni kaɗai ne wanda yake ganin girma na, sannan kuma duk abun da nace yayi yake yi baya iya ƙetarewa, kana kuma akwai tsantsar shaƙuwa da ƙaunar juna tsakanin mu, to kamata yay ya zamto koda yaushe yana gefe na, ma'ana dai in janyo sa ajiki na ya zamto duk inda zani in dinga jansa yana rakani, haka kuma aduk lokacin da na kasance ina cikin gida to in zamto ina kusa da shi koda kuwa awurin cin abinci ne, hakan shine zai sa ya rage yin wasu abubuwan da yake yi, sannan kuma zan samu damar ɗora sa akan hanyar da nake son yabi cikin sauƙi.
To bayan na dawo gida da na zauna na sake nazari akan magan-ganun sa, sai naga tabbas hakan itace mafita, dan haka shiyasa tun jiya na yanke hukuncin cewar zan fara aikina na farko amatsayina na Ciroman gida tare da shi, wato jibi zan jasa mutafi JAHAR KAGUL, CIKIN MASARAUTAR FULƊE domin siyo shanun da za'ayi layya dasu acikin gida, kasancewar an aika musu da saƙon zuwan mu tun awancan satin daya huce." Babban yaya ya faɗa yana kallon mahaifiyar tasa.
"Masha Allah, tabbas hakan yayi sosai, sai dai kawai muyi fatan Allah ya shige mana gaba, dan nima na goyi bayan hakan ɗari bisa ɗari." Ta fada tana mai jin daɗi aranta, sai kace wacce take da tabbacin idan sukayi hakan zasuyi nasara.
*WASHE GARI.*
*JAHAR KAGUL MASARAUTAR FULƊE.*
Yau tun safe aketa shirya -shiryan tarbar Yariman Masarautar Yamma acikin masarautar fulɗe.
Yayin da ita uwar gayya wacce za'ayi zuwan domin ta ta kwana cikin tsantsar ƙunci da damuwa.
Zaune take agefen gado sanye da wasu haɗaɗɗun kayan fulani koraye irin na sarakai ajikin ta.
Yayin da gefe da gefen ta kuma wasu Ƴammatan bayi suka kasance zaune awurin suna masu aikin gyara mata mayawaicin baƙin gashin dake ɗauke akan ta.
Kallo ɗaya zaka mata kasan ko kaɗan bata farin ciki, sabo da yarce fuskar ta take amatuƙar ɗaure, babu alamun annuri tattare da ita, sai dai kuma duk da ɗaure fuskar da tai hakan bai hana tsantsar kyawun da Allah yayi ta da shi ba bayanna.
Sanye ƙafafuwan ta suke cikin wani plat shoe mai tsanin taushi da kyawu, yayin da hannuwan ta kuma suke sanye da wasu azababbun jajayen awar-waraye na fulani amma sarakai, sai wuyan ta da yake damɓare da wata haɗaɗɗiyar sarƙar duwatsu ja zaune akan sa.
Gida ukku suka kasa gashin kan nata, tukun ko wacce ta kama kaso ɗaya na gefe da gefe suna masu kitse sa sukayi duk baya da su, sannan suka sake raba na tsakiyar gida biyu shima, kana ko wacce ta sake kama kaso ɗaya suna masu kitse sa shi kuma yayi duk gaba, tayarce jelolin suka biyo takan goshin ta, tukun suka sauka akan kafaɗun ta suna masu hucewa har kan cikin ta.
Ɗauke duk abubuwan da sukayi amfani dasu wurin yin kitson sukayi, tukun suka koma gefe guda suna masu tsayawa cirko -cirko tare da durƙusar da kawunan su ƙasa.
Sai da sukayi tsayuwar kimanin mintina goma ba tare da ta ɗaga kai takalli ɗaya daga cikin su ba, tukun daga bisani ta ɗaga laɓɓa tana mai faɗin. "Kuna iya zuwa ku shirya kafin su ƙaraso." Acan cikin.
Amma da yake hankulan su da nutsuwar su duka suna gare ta shiyasa tana faɗin haka suka ɗan durƙusa atare suna masu faɗin. "Mun barki lafiya Gimbiya." Sannan suka juya suna masu fucewa daga cikin ɗakin nata.
Acan ɓangaren Lamiɗo mahaifin Gimbiya Haddiyal kuwa, shi da kansa ya sanya aka gyara wurin da ɗiyar tasa tare da sirikin sa zasu zauna idan ya iso, sannan yasa aka kai shimfiɗa ta al'farma da suke da ita acikin masarautar aka shimfiɗa, kana ya cewa Mahafiyar Gimbiya Haddiyal ta tura ƴan matan da zasu je su shirya ta aje afara shirya ta, ba dan komai ba kuma yake haka sai dan kasancewar su Aminai da shi da Lamidon Yamma.
Misalin ƙarfe shaɗaya na safe dai dai wata baiwa dake sanye da kayan fulani ta shigo ɗakin Gimbiya Haddiyal bakin ta ɗauke da sallama.
Amsa mata sallamar tayi daga kan gadon da take zaune ba tare da ta ɗago ta kalle ta ba.
"Allah ya taimakeki yake Gimbiyar Masarautar Fulɗe, Ance in sanar dake Jauro'n Yamma ya ƙaraso."
Baiwar ta faɗa kanta duƙe aƙasa.
Yayin da ita kuma Gimbiya Haddiyal taji wata irin faɗuwar gaba ta ziyarce ta, tukun daga bisani ta lumshe dara-daran idanuwan ta ba tare da tace komai ba, kana ta buɗe su akan baiwar nan dake tsaye agaban ta tana mai kallon fuskar ta, kafin daga bisani kuma ta miƙe tsaye tana mai tsayawa akan ƙafafuwan ta.
Sosai tayi bala'in kyau cikin shigar dake sanye jikin ta.
Dasauri ƴammatan bayin da suke tsai-tsaiye agefen ta suka matso kusa da ita suna masu sa hannu suka ɗauki wata haɗaɗɗiyar jar alkyabba irin ta fulani mai adon duwatsu ajikin ta suna masu ɗora mata ita akan jikin ta, tukun suka koma daga bayan ta suna masu tsayawa, gaba ɗayan su suma sanye suke da kayan fulani na mata babu ko takalmi aƙafafuwan su. Yayin da ita kuma wannan ɗayar data kawo rahoto tai saurin juyawa tana mai fucewa daga cikin ɗakin.
Cikin takun ta na isa da izza ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar bakin ƙofar ta, tukun su kuma ƴammatan bayin nan suka rufa mata baya suna masu ɗora ƙafafuwan su aduk inda ta cire nata, ahaka har suka ƙarasa tanƙashe-shen falon nan.
Kishingiɗe ta hangi mahaifiyar ta aƙasa kan tum-tum ana ta aikin mammatsa mata ƙafafuwa.
Direct ta doshi inda take fuskar nan tata babu alamun annuri bare far'ah.
"Barka da wutawa Dadde am."
Ta faɗa tana mai durƙusawa aƙasa bayan sun gama gaisawa da matar dake yiwa mahaifiyar tata tausa kanta duƙe aƙasa.
"Yawwa Bello ta, fatan kin fito lafiya." Mahaifiyar tata ta faɗa tana mai kallon ta fuskarta ɗauke da murmushi, domin kuwa ba Lamiɗo kaɗai kesan haɗin nan da za'ayi ba hatta ita tana so, sabo da aganin ta hakan shine zai sanya ɗiyar tata ta haƙura da soyayyar aljanin dake zuwar mata amafarki acewar su.
Jijjiga kai kawai Gimbiya Haddiyal tayi ba tare da tace komai ba, tukun daga bisani ta miƙe tsaye daga durƙushen da take tana mai faɗin.
"To Dadde ni zan huce."
"Tom shikenan ki tabbatar kinyi abun da ya dace, kar ki kuskura wani labari mara daɗin ji yazo wurin mu bayan tafiyar sa."
Mahaifiyar tata ta faɗa tana kallon ta.
Jijjiga kai kawai tayi tana mai jin ranta na mata wani irin suya da raɗaɗi, tukun ta juya tana mai dosar hanyar da zata sadata da waje Ƴammatan bayin nan na biye da ita abaya.
Acan kuwa ɓangaren Jauron Yamma ƙarfe shaɗaya dai dai suka ƙaraso cikin masarautar Fulɗe, da shi da mutanen sa akan dawakan su da sukaji uban Ado.
Koda suka iso kai tsaye aka zarce dasu zuwa fada suka kaiwa Lamiɗo gaisuwa, tukun daga bisani ya bada umarnin ayiwa Yarima jagora zuwa wurin da zasu haɗu da Gimbiya Haddiyal, sa'annan ya tura jakadiyar sa kan taje ta sanya afaɗawa Gimbiya Haddiyal cewar Yarima ya ƙaraso.
Dogo ne sosai mai ƙirar ƙarafan mutane, sanye yake da kayan fulani na maza, amma irin nasu na sarauta waƴan da sukayi matuƙar amsar jikin sa.
Yana da kyawun sa dai dai misali shima, yana da hasken fata duk da dai bai kasance irin farin nan tas ba. Yayin da fuskar sa kuma ta kasance aɗaure babu alamun annuri tattare da ita.
Tafe suke shi asaman doki, su kuma jama'ar sa da kuma waƴan da aka sa sukai sa wurin da zasu gana da Gimbiya akan ƙafafuwan su.
Wani tafkeken lambu mai cike da korayen ganyayyaki tare da ni'imtacciyar iska da inuwa acikin sa suka shiga.
Direct suka doshi inda wata shimfiɗar fata mai matuƙar taushi da kyawu take, yayin da saman shimfiɗar kuma aka ajiye tum-tum tum-tum daga kowace kusurwa, sai daga kan shimfiɗar kuma gaba ɗaya jere take da kayan itatuwa acikin wasu ƴan kwandinan kaba masu tsananin kyau, waƴan da suka haɗa dangin su ayaba, lemo, inibi, tufa, kankana, da dai sauran su, sai akusa dasu kuma wani rantsetstsen kofin silba ne ruwan zuma da yayi matuƙar haɗuwa cike danƙam da madarar shanu mai matuƙar dumi, ga kuma ɗan ƙaramin kofi na tsiyaya akife akan plate ɗin silban da babban yake akai, sai abu na gaba kuma da ya kasance dammamar fura da nono ɗauke acikin wata haɗaɗɗiyar ƙwaryar da aka sanya ludayin duma acikin ta, sai kuma fai-fain kaba da aka rufe ƙwaryar da shi, sai abu na karshe kuma da ya kasance naman kaji da ƴan shila banƙararru acikin wata ƙatuwar roba mai tsaninin kyau da ake yi mata murfi da fai-fai itama.
Riƙe dokin nasa akayi tukun ya sauko akai.
Kana wanda ya riƙe dokin yaja sa suna masu juyawa tare da sauran ƴan rakiyar duka suka bar wurin, yayin da shi kuma Yariman Yamma ya saɓule takaman fatar dake sanye aƙafafuwan sa, tukun ya hau kan shimfiɗar nan yana mai kishingiɗa akan tum-tum, kana ya ƙure hanyar da yake tsammanin tana nan zata ɓullo da idanuwa.
Zaman sa baifi da minti goma ba Gimbiya Haddiyal da tawagar ta suka ɓullo wurin.
Tunda suka bullo ya kafe ta da idanuwa daga nesa yana kallon ta bako ƙiftawa, wani irin kallo yake aika mata dashi tun daga nesa, wanda duk wanda ya gansa basai an faɗa masa ba zai san yayi nisa cikin kogin ƙaunar ta.
Cak ta tsaya a'inda take daga ɗan nesa da shi ba tare da ta cigaba da takowa ba.
Tsaye suma ƴammatan bayin nan sukayi abayan ta cak, tukun daga bisani ta ɗaga musu hannu ta sama ta baya ba tare da ta juya ta kalle su ba.
"Afuto lafiya Gimbiya." Suka faɗa suna masu juyawa suka doshi hanyar da suka biyo.
Ba ita ta cigaba da tafiya ba har sai da ta tabbatar da tabar jin motsin su tas, alamun sun bar cikin wurin, tukun ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar kan shimfiɗar da Yariman Yamma yake kishingiɗe akai, idanuwan ta kafe ƙur akan fuskar sa kamar yacce shima ya kafe ta da nasa, sai dai ita kuma ba irin kallon da yake mata ba take masa, tana masa kallo ne na tsantsar -tsanar sa da take ji aranta tare da ƙin sa, ahaka har ta ƙarasa bakin shimfiɗar da yake kai.
Lumshe idanuwan sa yayi yana mai sake gyara kishingiɗar sa yayi balance ransa face, domin kuwa sai yanzu data matso wurin sa ya ƙara tabbatarwa da kansa lallai ba ƙaramun dace yayi ba, muddin ya mallaki wannan babbar kadarar aduniya amatsayin abokiyar rayuwar sa. Tukun daga bisani ya sake wara idanuwan sa akan fuskar ta da take cunkushe tsaye agaban sa, kana ya buɗe baki cikin yin ƙasa da murya yana mai faɗin.
"Barka da isowa Gimbiyar Jauron Yamma, Sarauniya kuma ga tsuntsaye da shanu na Masarautar Fulɗe."
Ya faɗa fuskar sa ɗauke da annuri.
Yayin da ita kuma taji saukar furucin sa na Gimbiyar Jauron Yamma da wani irin azabar raɗaɗi acikin ranta, tayarce har sai da ta rumtse idanuwan ta da ƙarfi tare da taune lower lips ɗin ta.
Tukun daga bisani ta warasu akan fuskar sa kamar yacce shima yake kallon ta gaba ɗaya har sun fara canza launi suna yin ja.
Sannan ta tuɓe takalman da suke sanye aƙafar ta tana mai dosar kan shimfiɗar da yake kishingiɗe akai, zuciyar ta na tsantsar turiri.
Tsaye tayi agaban sa tana mai aika masa da wani irin matsiyacin kallo, tukun daga bisani ta ɗaga laɓɓan ta cikin kaushi, tana mai faɗin. "Shin wa...............✍
*HAK'IK'A INA GAB DA DAKATAWA GABA D'AYA MUDDIN BAZAKU DINGA YIN COMMENT BA.*
🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎
👑👑
🦋
🦅🕊🦆
🐍🎠🐄🏹
_*NA*_
UMAR FARUQ*D*
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
*PAGE 07*
"Shin waya sanar da kai wannan tatsuniyar da har kake shelantawa duniya cewar ni ɗin takace?" Ta faɗa cikin kaushi tana mai kafesa da dara-daran idanuwan ta, tukun daga bisani ta ɗora da faɗin. "To idan ma mafarki kake ina son kayi gaggawar farkwa, domin kuwa ni ɗin nan daka gani an hallice ni ne domin mutum ɗaya, haka kuma na daɗe da zamtowa mallakin sa, dan haka ina mai shawartar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 76