Share this page
yin saba tun da ake Haihuwa a cikin gidan, domin kuwa hatta da shi Mai Martaba sai da yayi wasa da doki irin wasan da bai taɓayin kamar sa ba, wato wasa na ban mamaki, wanda yayi matuƙar ƙayatar da al'ummar wurin, yayin da zuciyoyin magauta kuma suka cika dam da baƙin ciki tamkar sayi bindiga, donin kuwa a cewar su wannan wasa da dokin kawai da sarki yayi shi yake nuni da ada duk ba haihuwa ake masa ba sai a yanzu ne akai masa, sannan kuma Gimbiya Huwaila da Gimbiya Amina matan sa suka sa aransu cewar duka bai ɗauki Ƴaƴan wurin su ba amatsayin Ƴaƴa, tunda a lokacin su su duk bai nuna irin wannan farin cikin ba, hakan yasa suka ƙudiri aniyar ganin bayan Baban Yaya da kuma Ɗan jariri Asad mai farin jinin jama'a. "UNGUWAR ƊAN TANKI.* Tunda su Aishatu suka dawo gida har kawo yau bata dawo hayyacin ta ba, domin kuwa ataƙaice ma har a gadon asibiti sai da aka kwantar da ita, sabo da jinin ta da yayi bala'in hawa. Sosai hankalin duka jama'ar gidan dama duk dangin su yayi matuƙar tashi, a lokacin da labarin abun da ya faru ya riske su. Kaka tayi kuka, tayi kuka kamar ranta zai futa da jin wannan baƙin labarin, tayi tsinuwa bila adadin ga mutanen Baƙar Masarauta, sannan kuma tayi nadamar sanya Ishaƙ ya bar Aishatu da tayi yafi a ƙirga, yayin da ta fannin Mahaifin Ishaƙ shima yaji ina ma ace ya hanasu tafiyar tare, sai dai kuma babu wani bawa da ya isa ya canza abun da Allah ya tsaro. Lokacin da labarin ya riski dangin Aishatu na Jahar Ruman, suma hankulan su ba ƙaramun tashi yayi ba, hakan yasa tun a washegarin ranar suka haɗo kayan su da komai da komai nasu suka sake baro Ƙasar Malin cikin ɗacin rai, suna masu dawowa Ƙasar Hausa, Jahar wasai cikin rugar su da suka bari kafun su koma can. Sosai Aisahtu ta fige ta rame, ta lalace dukan ta, domin kuwa har yau bata dena kuka ba da surutai kala-kala, musamman ma idan akace dare yayi, sannan kuma kullum idan ta kwanta bacci sai tayi mafarkin yaron nata a hannun wata mata tana kula da shi. Ganin da su Ishaƙ sukayi Aishatu taƙi kwantar da hankalin tane ya sa suka fara nemar mata addu'oin dan gana suna bata tana sha, sannan kuma suka sanar a massallatan Unguwar su cewar a taya su da addu'a, kana suma kullum suke kan yin ta, domin kuwa tamkar mahaukaci haka Aishatu take komawa idan tana surutai. Yayin da su Ahmad da sauran ƙannen sa suke sata a gaba suyita aikin kuka, ataƙaice dai gaba ɗaya gidan sun koma abun tausayi. *BAYAN SUƊEWAR SHEKARA HUƊU* *ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.* Sosai Bir yayi matuƙar girma tare da wayo da kyawu, domin kuwa idan mutum ya gansa muddin ba sanin shekarun sa yayi ba, sai yayi tinanin yakai irin shekara bakwai ɗin nan, sabo da girman jikin sa, har yanzu kuma yana a wurin Iyar Bayi ne, ita take kula da shi take masa komai, domin shi duk a tinanin sa ma itace Uwar sa, hakan yasa yake kiran ta da Iya ta, yayin da itama a koda yaushe take jin sonsa na ƙara ƙaruwa a cikin zuciyar ta fiye dana baya. Zuwa yanzu shima har ya fara yin wasu abubuwan irin na bayi, waƴan da suka haɗa da ɗibar ruwa da kuma ɗaukar icci na Yanzu haka zaune suke a ƙasan inuwar wata bishiya suna wasa shi da abokan sa guda biyu. Sanye suke d.............✍ *A PAGE ƊIN JIYA NAYI MANTUWA A WURIN FAƊIN SUNAN MATAR SARKIN WASAI TA BIYU MAI SUNA AMINA, YAYIN DA NI KUMA NA SANYA SUWAIBA, DAN HAKA AMINA SHINE SUNAN NATA, SUWAIBA KUMA SUNAN ƊAYA DAGA CIKIN ƳAƳAN HUWAILA NE BABBAR MATAR SARKI ABDALLAH.* *BAƘAR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 17* Sanye suke da ƴan guntayen baƙaƙen wandina na yadi iyakar guiwoyin su babu ko riguna a jikin su dukan su. Riƙe Bir yake da kwari da gwafa a hannun sa yana mai gyara danƙon jikin ta, kasancewar tana ɗaya daga cikin abubuwan da yake matuƙar so a rayuwar sa. Tun da ya taso yaga mayaƙan Baƙar Masarauta na amfani da ita, sai shima abar take matuƙar birge sa, hakan yasa ko da yasuhe da ya futo daga ɗakin su muddin suna nan yake hucewa wurin su yaje ya tsaya yay ta kallon su, wani lokacin ma har ya ɗauki abar ya fara shirin gwada harbawa shima, hakan da ɗaya daga cikin maharban nasu ya gani ne yasan ya sa haɗawa Bir wata ƴar ƙarama dai-dai da shi ya basa, a ranar kuwa ba ƙaramar murna da farin ciki yayi ba, sannan kuma wuni yay adaji yana harbin tsuntsaye, har sai da Iyar Bayi taje ta kamosa da kanta da taji shiru, domin ko ita ko kaɗan bata son harkar kwari da gwafar da Bir ɗin yake yi, sabo da tana tsoron kar wataran aga ya ƙware da harkar amayar da shi cikin Maharban Masarautar, sabo da idan hakan ta faru to rabin rayuwar sa zata ƙare ne a yawon dajika, sannan kuma koda wani faɗan ya taso to yana ɗaya daga cikin mutanen da za'a na turawa, hakan yasa take ƙin abar sosai, sai dai shi kuma Bir akullum ƙara ƙaunar kwari da gwafar sa yake. Tun yana ɗan ƙaramin sa yake da wata irin halayya ta taurin kai da kafiya, domin kuwa muddin baiyi niyyar yin abuba to ko ance yayi bazai taɓa yin sa ba, ko da za'a dake sa ne kuwa, haka kuma dan an dake san a banza, sabo da baya kuka kwakwata, sai dai mutum yayi ya gama, wannan dalilin ne yasa Iyar Bayi take kiran sa da suna JARUMI, saboda yadda yake da tsantsar jarumtar a ɗan ƙaramin sa. "Jarumi! Jarumi!!" Muryar Iyar Bayi dake tawowa wurin da suke ta daki dodon kunnen Bir da yake shirin harba tsinken gwafar sa jikin bishiya. Da sauri ya juya ɓarin da take yana mai kai dara-daran kyawawan idanuwan sa kan fuskar ta, tukun ya buɗe baki yana mai faɗin. "Me ayi ne Iya yanju ma?" "Wanka da cin abinci mana Jarumi, kaga su Mauzum tun ɗazu nayi musu wanka, gasu nan har sunzo kuna wasa tare, amma kai tun da kafuce tun safe kaƙi ka dawo kana nan kana shirme." Iya Bayi ta faɗa tana mai ƙarasawa kusa da Bir ta riƙo hannun sa. Yayin da shi kuma ya buɗe baki yana mai faɗin. "To a ƙoshi Iya ta, idan a gama halbo cuncuna zanjo kimun wanka, she ki shoya mana shi mucinye ko." Ya ƙarasa maganar yana mai sakar mata dariya, tayarce har sai da kyawawan jerarrun fararen haƙwaran da suke a bakin sa suka bayyana. "A'a Bir bani gwafar nan haka, in yaso bayan na maka wankan kaci abinci sai kadawo ka cigaba da harbo sun, domin kuwa idan ba haka ba nasanka sai ka kai har dare a wurin nan ba tare da ka gama ba." Iyar Bayi ta faɗa tana mai ƙwace kwari da gwafar da suke riƙe a hannun sa, sabo da sanin da tayi muddin ba amsar sun tayi ba to bazai taɓa binta ba. Diddira ƙafafuwan sa ya farayi a wurin yana shirin sakin kuka, sabo da ƙwace masa da tayi. Hakan da Iya ta gani ne yasan ya ta buɗe baki tana mai faɗin. "Haba dai Jarumi da kuka, ka taimaka kar kabani kunya mana, kasa yau mutane suyi mana dariya." Ta ƙarasa maganar tana mai jan hannun sa sukayi gaba. Ba dan Bir yaso tafiya ba yabi Iyar Bayi suka tafi, yayin da suma abokansa su Mauzum suka biyo su a baya. *ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.* A yanzu haka shekarun Babban Yaya goma shahuɗu a duniya, sosai ya ƙara girma tare da nutsuwa da kuma hankali, wanda hakan kuma ba ƙaramun ƙona zuciyar magautan su yake ba, domin kuwa babu kalar asirin da basuyi masa ba amma duk a banza har yau yaƙi cin sa, sai dai kuma suma ɗin har kawo yau basu haƙura sun dena ba, kamar yacce har yau Fulani bata sare ba wurin yiwa Ƴaƴan nata addu'a, sannan kuma suma ta koya musu sukeyi da kansu. Tunda Fulani ta haifi Asad har yau bata sake haihuwa ba, sosai yaron yayi girma bana wasa ba, domin kuwa babu wanda zai gansa yace bai kai shekara bakwai ba a duniya muddin ba sanin sa mutum yayi ba, yayin da kyawunsa kuma a kullum yake ƙara futowa. Gaba ɗaya halayyar sa ba iri ɗaya bace da ta Babban Yaya, dan kuwa shi akwai shi da san yawo, tare da maitar Doki, wanda har hakan da mai Martaba ya gani yasa ya siya masa dawakai har guda ukku ƙanana ƙosassu ana kula masa da su, sannan kuma ake ɗora sa akan su aduk lokacin da za'ayi hawa, ko kuma ranar juma'a, kai wani lokacin ma haka nan kawai ake ɗora sa saman dawakan ayi ta zageye da shi acikin gari, shi kuma yay ta aikin dariya yana jin daɗi, kasancewar sa yaro mai yawan fa'arh da dariya. Yayin da shi kuma Babban Yaya bai damu da shiga mutane ba, asalima ya fison ya gansa a kusa da mahaifiyar su Fulani ako da yaushe, sannan kuma ko kaɗan basa da maitar dokin da Asad yake da ita, dan shi a yanzu haka ma duka dokunan sa guda biyu ne, saɓanin Asad da yake da guda ukku. Sosai sukayi wata irin mahaukaciyar shaƙuwa tsakanin sa da ƙanin nasa, kamannin su ɗaya sak, sai dan hasken fata da Asad yafi Babban Yaya da shi. Ko kaɗan Fulani bata son yawan yawon da Asad yake yi, asonta tafi son ace kullum yana gaban ta tana masa addu'oi kamar yacce suke tare da Babban yaya, sabo da tsaro badan tsoro ba, domin kuwa babu wata hallaya ɗaya ta mutan gidan nasu da bata santa ba, yayin da shi kuma yaran kwata-kwata baya son zama a cikin gida, asalima kullum a Fada yake yini kusa da Mai Martaba suna hira, sabo da ko kaya yanzu haka kullum iri ɗaya suke sawa da shi da Mai Martaba, hatta da alkyabba kuwa, wanda hakan kuwa ba ƙaramar shaƙuwa ce ta ƙara shiga tsakanin sa da Mai Martaba ba, tayarce har yake jin sa fiye da duka sauran yaran sa a zuciyar sa, sannan kuma yake gaza ɓoye soyayyar sa a gaban kowa, wannan dalilin ne yasan ya Fulani bata fiye samun damar yi masa addu'oi ba, kamar yadda take yiwa sauran yaran, sannan kuma shi kansa Asad ba damuwa yayi da addu'ar ba kamar yacce Babban yaya yake yin ta a lokacin da yana ƙarami kamar sa, asalima ko yi masa Fulani zatayi wataran sai ta riƙe sa, tukun take samu ta masa azkar ɗin, idan kuma ba haka ba tana cikin yi zai ruga ya barta a wurin ba tare da ta gama ba, hakan ko ba ƙaramun tsoratata yake ba, sai dai kuma ako da yaushe cikin kaiwa Allah kukan ta take yi. A yanzu haka Abokin Asad guda ɗaya ne, wato Al'amin ɗan gidan Galadima ƙanin Mai Martaba, da aka haife sa bayan haihuwar Asad da wata ukku. Sosai sukayi matuƙar shaƙuwa yaran, yadda kasan waƴan da aka haifa a tare, domin kuwa hatta da abinci tare suke ci ako da yaushe, haka kuma shima Al'amin a cikin Fada yake yini wurin su Mai Martaba, kamar yacce Asad yake yini anan ɗin. Ko hawa aka tashi yi, shiga iri ɗaya ake yi musu su biyun, sannan kuma kusan ajere ake riƙo dawakunan su suna asaman su. Haka mutane zasuyi ta ɗaga musu hannu ana kiran sunan su, barin ma Asad da yake da wani irin farin jinin al'umma tun yana ɗan ƙarami, domin kuwa aduk lokacin da aka futa da shi akan doki sai jama'a sun tsaya suna kallon sa, yayin da shi kuma zakaga yana ta ɗaga musu hannu sama yadda kasan Babban mutum. A ɓangaren magautan su kuwa har yau basu dakata da asirce- asicen da sukeyi ba akan yaran biyu domin ganin bayan su ta kowace hanya, wato Asad da Babban Ƴaƴa, barin ma Asad a yanzu, dan kuwa sunfi tsanar sa sama da Babban Yaya nesa ba kusa ba, sabo da yadda suka ga kaga Mai Martaba naji da shi fiye da Babban Yaya, hakan yasa mutane suka fara zargin tsaf yaron zai iya hawa kan karagar mulki muddin ya ɗore da san zaman Fada har girman sa, wannan dalilin ne yasan ya su suke jin tsanar sa fiye da yadda suke jin ta Babban yaya a zuciyar su, sannan kuma suka mayar da hankali wurin ganin sunga bayan sa ta kowace irin hanya ce, domin kuwa hakan ne kawai zai sama musu salama a rayuwar su. *UNGUWAR ƊAN TANKI.* Sosai su Ishaƙ su kaci wuya akan Aishatu, kafin daga baya kuma Allah ya sanya mata dangana ta sanadin addu'oin da aka dage ana tayi ba dare ba rana, masallatai da cikin gida akan ta, sai dai kuma gaba ɗaya ta canza, halayyar ta dawo sabuwa, domin tun lokacin da abun ya faru ta koma shiru shiru, gaba ɗaya magana ma sai dole ke sata take yi, ako da yaushe sai dai ta shige ƙuryar ɗaki ta zauna kan gado tai ta faman aikin tinani, wani lokacin ma harda kuka. Hakan da ta dawo ɗin kuwa ba ƙaramun sosa zuciyar Ishaƙ da mahaifan sa yake ba, sosai take matuƙar basu tausayi da yarce ta koma ɗin yanzu. Tun bayan haihuwar Ɗan da tayi a cikin jirgi ruwa bata sake yin wata haihuwar ba, yayin da Ahmad kuma yake da shekaru goma shahuɗu dai -dai a duniya yanzu. Sosai yaron yake da matuƙar hankali da nutsuwa, uwa uba kuma ga san addini da ƙoƙari, domin kuwa har ya sauke izu sittin na alƙur'ani akan sa, ga kuma litattafai da yayi matuƙar sani na addini. Afannin boko ma yanzu haka yana matakin ajiki ukku ne na ƙaramar makarantar secondry, wato Jss 3. Sosai halin da mahaifiyar tasa take ciki yake matuƙar damun sa, tayarce har wani lokacin yake zama yay kuka shi kaɗai. A kullum rana ta Allah idan ya same ta zaune a ɗaki tayi tagumi, sai ya zauna gaban ta yay mata nasihohi, sannan kuma ya zauna yay ta kawo mata labarai dan ya ɗauke mata kewa, haka itama kaka take zuwa su haɗu su duka biyu, wani lokacin ma har da sauran Ƴaƴan ta mata ƙannen Ahmad, su sata a gaba suna bada labarai ana shan dariya, to anan ne itama zakaji ta tsoma bakin ta ana hirar da ita, wani lokacin ma har tayi dariyar itama. A kullum rana ta Allah idan ta kwanta bacci sai tayi mafarkin yaron nan da take yi, sai dai kuma yanzu ba'a jariri take ganin sa ba, tana ganin sa ne a ɗan matashin yaro, haka zai ta miƙo mata hannu yana son ta kama sa, amma sai kuma gaba ɗaya taji ta kasa ɗaga ƙafafuwan ta zuwa wurin da yake, gaba ɗaya sai ƙasa ta riƙe su, yayin da shi kuma idan ya tawo domin yazo gare ta, sai wasu irin mutane masu wata kalar siffa mara kyan gani suzo su janye sa suyi gaba da shi, haka zatai ta ɗaga masa hannu shima yana ɗaga mata suna kuka, amma mutanen nan su janye sa suyi gaba da shi, tukun sai ta farka daga baccin ta cikin tsantsar tsoro da firgici. _BAYAN SHUƊEWAR SHEKARA HUƊU._ *ƘASAR HAUSA, JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULƊE.* Tun bayan haihuwar Buba Gimbiya Kaɓel bata sake haihuwa ba tsawon shekaru takwas kenan, sai yanzu da take ɗauke da tsohon ciki haihuwa yau ko gobe, domin kuwa har ya shiga watan haihuwar sa cikin. Yayin da ita kuma Gimbiya Mairamu matar Lamaiɗo ta biyu ta sake haihuwar ƴaƴa maza har guda biyu a bayan haihuwar hairisu, tayarce Ƴaƴan Lamiɗo suka zamto har su bakwai, amma sai dai cikin su duka babu Ƴa mace gaba ɗayan su maza ne, hakan ne yasa dukan su suke fatan Allah yasa wannan karan Gimbita Kaɓel ta haifo musu ɗiya mace. Sosai suka shiryawa haihuwar, kuma suke zumuɗin ta yadda kasan ba'a taɓa haihuwa ba gidan. *ƘASAR MALIN, YANKIN JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.* Tun bayan haihuwar Yarima Sairan da Gimbiya Haiwa Babar matar Sarki Barbaru tayi har kawo yau tsawon shekaru goma shabiyar bata sake wata haihuwar ba. Yayin da ita kuma Gimbiya Salwa Amarya ta haifi Ɗa namiji mai suna Saufan shekaru tara baya da suka huce kenan, tun daga lokacin kuma bata sake haihuwa ba sai yanzu da take ɗauke da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe, sosai suke fatan Allah yasa wannan karan ta haifo musu ƴa mace dukan su, domin kuwa ba ƙaramun san Ƴaƴa mata suke ba, hatta da shi Sarki Barbaru. Acan ɓangaren Bayi kuwa yanzu Bir yana da shekaru takwas dai dai aduniya, yayin da wayon sa da girman sa da kuma taurin kansa duk suka zarce shekarun nasa, domin kuwa tun a yanzu bako wane aiki bane ake sa sa yayi sa kai tsaye, sannan kuma muddin akace yaran Bayi sunyi laifi to zaka same sa yana ɗaya daga cikin ƴan laifin, domin kuwa ko kaɗan basa da tsoro, sannan kuma ko wane irin duka za'a masa baya taɓa yin kuka. A yanzu ya fahimci ba Iyar Bayi bace ta haife sa, sabo da yadda wasu daga cikin ƴan uwansa bayi suke goranta masa cewar shi da ma tsunto sa akayi bashi da Iyaye, idan sukayi faɗa, hakan kuwa ba ƙaramun sosa masa rai yake ba, sannan kuma aduk ranar da aka faɗa masa haka to yaran da ya faɗa ɗin ya shiga ukku a wurin sa, domin kuwa baƙaramun duka yake masa ba, sannan kuma haka zaizo ya tasa Iyar Bayi a gaba yana ce mata ta faɗa masa ina babar sa take, su waye suka haifosa, sannan kuma a'ina ta tsinto sa, sai dai kuma koda wasa Iyar Bayi bata taɓa gigin basa amsa ɗaya ba daga cikin amsoshin tambayoyin nasa, asalima idan ya fara yimata tambayar tashi take tana barin wurin, domin kuwa kotace zata lallashe sa ba lallasuwa yake ba, gashi ita kuma tana matuƙar tsoron faɗa masa, sabo da gudun abun da zai faru da ita daga baya, domin kuwa ba ƙaramun gargaɗi Sarki Barbaru yayi mata ba da kansa, akan cewar kar a taɓa barin yaron yasan tarihinsa ko da wasa, saboda kar ko wataran yay gigin cewa zai bar su, muddin kuwa ta bari hakan ya faru, to tasani abakin rayuwar ta. Wannan dalilin shike sanya Iyar Bayi tana tashi tabar wurin Bir aduk lokacin da yazo mata da batun, sannan kuma magan-ganun nasa suke matuƙar firgita ta. Afannin harba kwari da gwafar sa ma kullum abu gaba yake ƙarawa, domin kuwa ba ƙaramun jin daɗin harkar yake ba, sannan kuma baiƙi ba ya yini adaji yana harbe-harbe ba tare da damuwar komai ba aransa. _BAYAN KWAN BIYU_ Yau Gimbiya Salwa ta tashi da masifaffen ciwon naƙuda mai matuƙar tsanani, tun cikin daren jiya take abu ɗaya, amma har kawo yanzu misalin ƙarfe shaɗaya na rana shiru kakeji bata haihu ba. Durƙushe take a cikin ɗakin ta daga gefen gado tana mai faman cize leɓen ta, yayin da gumi kuma ke yanko mata ta ko ina a jikin ta. Agefen ta kuwa wasu dattijan matane tsaye akan ta, ɗaya na aikin yi mata firfita da furta kalmar sannu gare ta, yayin da ɗaya kuma take dafe da bayan ta tana mai faman faɗin. "Yi nishi sosai Gimbiya kin kusa da yardar Ubangiji Gargabilu, yi nishi da ƙarfi kin kusa sannu kinji." Ta faɗa tana mai shafa mata bayan ta, yayin da ita kuma take ta ƙoƙarin yin nishin tana girgiza kanta. Wani irin nishi tayi mai matuƙar ƙarfi, tukun daga bisani kuma sai ga kukan jariri nan ya cika ɗakin da matuƙar sauti ba ƙaƙƙautawa. "Godiya muke abun bauta Gargabilu." Matan nan biyu suka faɗa cikin tsantsar farin ciki, ɗaya daga cikin su na durƙusawa wurin ƴa macen da idanuwan ta suka gane mata kwance tana cilla ƴan ƙafafuwanta sama tare da sakin kuka... *ƘASAR HAUSA, JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULƊE.* Yau jama'ar cikin Masarautar Fulɗe suka tashi da tsantsar farin ciki, ta sanadin haihuwar da Gimbiya Kaɓel tayi da asuba, kuma abun farincikin shine 'Ya Macen da suke fata a wannan karan ita Allah ya basu. Zo kuga kuwa farin ciki da murna wurin jama'ar gidan tun daga kan Lamiɗo har zuwa kan Bayi da hadiman gidan mazan su da matan su. Kakar su mahaifiyar Lamiɗo kuwa labarin haihuwar na isa kunnen ta ta taso ta tawo daga ɓangaren ta zuwa ɓangaren Gimbiya Kaɓle cikin matuƙar farin ciki. Sosai tayi matuƙar ruɗewa alokacin da idanuwan ta suka yi mata arba da kyakkyawar Ƴar da aka haifo ƙatotuwa da ita fara tas, cikin kayan fulani na jarirai da aka shirya ta. Cikin tsantsar farin ciki ta miƙa hannu tana mai amsar ta ahannun Hadimar Gimbiya Kaɓel, bakin ta na furta kalmar. "Tubarakallah Masha Allah." Tukun daga bisani ta fara rawa a cikin ɗakin ɗauke da ƴar ahannun ta, kana ta ɗora da faɗin. "Amma akan me za'a sanya mata kaya bayan ba a riga an bata kariya ba, dan haka amshe ta nan ayi maza-maza a cire mata kayan nan afuto mun da ita zuwa ɓangarena, ni kuma yanzu zanje na fara haɗa kayan tsafi, domin kuwa ku da kanku kun sani a ranar da yaro yazo duniya muke bashi makari acikin gidan nan." Ta ƙarasa maganar tana mai miƙawa Hadimar nan ƴar. Tukun ita kuma ta juya cikin sauri tana mai gyara ɗaurin zanin da yake a haɓar ta, tare da kama hanyar waje. Yayin da ita kuma wannan Hadimar ta fara cirewa kyakkyawar jinjirar kayan da suke sanye a jikin ta, tukun daga bisani ta miƙe tsaye hannun ta ɗauke da ƴar ba kaya a jikin ta, sai ɗan showel ɗin da ta naɗe ta a cikin sa tana mai kama hanyar waje. Yayin da suma sauran matan da suke a cikin ɗakin duk suka miƙe suka bi bayan ta, sabo da suyi kallon shagalin da za'ayi a ɓangaren tsohuwar mahaifiyar Lamiɗo. Tafkeken wuri ne mai matuƙar kyau da girma. Zagaye yake da ɗakuna irin na fulani a cikin sa. Gaban wata bukka Kaka ta ƙarasa tana mai sa hannu ta buɗe murfin karar da yake a jikinta, tukun ta danna kanta zuwa cikin bukkar. Wasu irin kayan karikitai ta ta futo da su riƙe a hannun ta cikin wani baƙin kasko, tana mai zuwa ta ajiye su a bakin ƙofar bukkar, tukun ta koma ciki-cikin sauri, kana daga bisani sai gata nan ta sake dawowa hannun ta riƙe da wani kaskon, wanda yake ɗauke da ruwa a cikin sa, sannan ta sake juyawa still tana mai komawa cikin bukkar. Bata jima a ciki ba ta k'ara futowa ɗauke da wata Sanda irin ta Fulani a hannunta, tana mai zuwa ta a jiye ta kusa da waƴan can kayan. Tukun ta juya bayan ta tana mai kai idanuwan ta zuwa inda wasu maza suke, da alamun dai Hadimai ne su ɗin, duba da irin suturar dake sanye a jikin su da ta zamto kalar ta Hadiman. Daga nan wurin da take ta buɗe murya cikin ƙarfi tana mai faɗin. "Kai kuyi maza maza kuje gaban rafin gabas, zakuga turamen tsafi na tarihi gaban bishiyar ɗorawa ku ɗauko mun su." Da tom suka amsa mata su duka huɗun, suna masu juyawa cikin sauri suka tafi. Dawowar su daga wurin da ta aike sun tayi dai-dai da lokacin da Hadimar Gimbiya kaɓel tare da tawagar ta suka ɓullo wurin, hannun ta riƙe da jaririyar. Yayin da su kuma Hadiman nan maza suka tawo ɗauke suke da wasu irin manya-manyan turame masu matuƙar girma akafaɗun su. Ƙarasowa wurin da Kaka take sukayi suna masu a jiye su a gaban ta, wurin da kayan nan suke. Yayin da ita kuma ta duƙusa ƙasa da sauri tana mai fara futo da abubuwan da suke a cikin kaskon nan. Wasu irin ƙullikan tsummokarai ta zaro masu matuƙar yawa, tukun ta fara kwance su da ɗai-ɗai da ɗai-ɗai, kana ta ɗibu wasu iccina daga cikin ƙulli ɗaya tana mai zuba su acikin ruwan nan da ya kasance shi ba na zafi ba, sannan kuma shi bamai sanyi ƙarara ba, tukun ta sake ɗibar wani ta zuba sa shima a cikin ruwan. Haka ta dinga ɗibar su tana

Chapter 18 of 76