Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ©️ © 📖✏ FIKRA WRITER'S ASSOCIATION Facebook: Lubna Sufyan IG: Lubna Sufyan Email: Calmlubna@gmail.com *ABDDULKADIR* *LubnaSufyan* *SHIMFIDA* Alhaji Ahmad Bugaje shine yaro na farko a wajen Alhaji Auwal Bugaje da Hajiya Sa'adatu da suke kira da Daada. Asalinsu yan garin Bugaje ne da yake karamar hukumar Katsina, tsatson su Fulani ne, duk da ba sai an fada maka hakan ba. Yanayin jikin su da hasken fatarsu ma kawai idan ka kalla ya wadatar. Cirani ya kawo kakanninsu garin Kano, da niyyar siye da siyarwa, kafin daga baya su fada harkar canji, harkar da ta zame musu kamar gado a cikin zuri'ar su, dan kuwa itace silar arziqin su. Shi kanshi Alhaji Auwal itace sana'ar shi, kafin rasuwar shi kuwa, Allah ya azurta shi da samun yara takwas da tilon matar shi Hajiya Sa'adatu. Ahmad, Sani, Hamisu, Talatu, Sadiya, Maryama, Ali, sai Hafsatu. Sun sami wadattaccen ilimin addini dana boko, wanda a cikinsu daga Sani sai Ali ne suke aikin gwamnati, dukkan su sana'ar canji sukeyi, ko bayan da sukai aure suka hayayyafa. Bayan rasuwar Alhaji Auwalu, an raba musu gado a bisa tsari na addini. Ya kuma bar musu tarin dukiya mai yawa, dan a lokacin da wahalar gaske ka kira Bugaje ba'a samu wanda yasan shi ko ya taba jin sunan shi ba, saboda ana damawa dashi a cikin attajiran dake garin Kano. Ita kanta Hajiya Sa'adatu bata rasu ba sai bayan ta aurar da yaran ta mata gabaki dayan su. Gidan shi da yake nan Gadon Kaya, a garin Kano, Alhaji Ahmad ne ya gaje shi. Gidane babba, musamman daya kara gyara shi, manyan bangarori ne guda hudu a cikin gidan, sai wani bangare daya shima da yake daban. Ko harabar gidan kanta abin kallo ce. Ya kuma ji dadin kasancewar gidan mallakin shi, dan duk a cikin yaran Alhaji Auwalu shi kadaine ya auri mata har hudu, dukkan su tazarar shekara bibbiyu a tsakanin su, gashi yayi auren wuri saboda tashen kudi da yakeji a lokacin. 1. Matar shi ta farko, uwargidan shi Hajiya Hasiya da duka yaran suke kira Hajja tana da yara takwas tare dashi: Muhsin Yazid Khadija Mubarak AbdulKadir Zahra Nazir Zainab Halayyen Hajiya Hasiya sun hada da son girma tamkar ita ta yanke wa kasa cibiya, yawan fada, daukar zuga da son yaranta da kuma matsananciyar rowa. 2. Hajiya Saratu itace matar shi ta biyu, sannan duka yaran gidan suna kiranta da Mama. Tana da yara biyar da Alhaji Auwal dukkan su maza. Ahmad (Babangida) Yasir da Yazid (Yan biyu) Salim Khalid Halayen Hajiya Saratu, tana da fuska biyu, a gabanka baka da mai kaunarka kamarta, a bayan idonka kuwa baka da makiya kamarta, tana da gulma da hadin husuma, ga jarabtar cin bashi da Allah ya dora mata. 3. Hajiya Sakina, itace matar shi ta uku da yaran suke kira Mami, wadda kuma ita kadai ce ya aura a bazawara, dan shekararta daya da wata uku, Allah yaima mijinta rasuwa bayan yar gajeruwar rashin lafiya dayai fama da ita, ya kuma rasu a lokacin yabarta da cikin wata shidda, ta haifi yarinyar ta mace, bayan ta yayeta ne suka hadu da Alhaji Ahmad Bugaje. Bai aureta ba sai da yai mata alkawarin rike mata yarinyarta, kasancewar mijinta Mahmud maraya kuma tilon namiji a wajen iyayen shi, dan haka sauran yan uwan nashi duk matane, babu wanda yai yunkurin karbar yarinyar da tasaka ma suna Wahidah, dan shine zabin mahaifinta a cewar shi indai ya samu ya mace. Bayan Wahidah ta haifi yara uku da shi Sa'adatu (Amatullah) Aminu Habib Halayen Hajiya Sakina, macece mai yawan hakuri da kau da kai, tana da sanyin hali da ko surutu bai dameta ba. 4. Hajiya Halima da yaran duka suke kira Anty. Mata ta hudu kuma amarya a gidan Alhaji Ahmad, yar tsohon Wazirin Kano da Allah yaima rasuwa ce ya aura. Dan a cikin matan shi ita kadai ce take aikin gwamnati, da aikin ta ya aure ta. Allah ya azurta su da yara shidda, saboda tafi sauran matan shi haihuwa gab da gab, kusan abinda akan kira da kwanika. Nusaiba Nabila Kabiru Adnan Barakah Kasancewar Hajiya Halima jinin sarauta yasa tana da izza, ko kadan bata shiga harkar kowa, kuma bata daukar raini ko ya yake, zaka iya cewa tana da fada inhar ka shiga gonarta. Sannan tana da matukar kirki da kyauta irin ta saraki. * Duk da karayar arziqin data samu Alhaji Ahmad Bugaje, sanadin yan damfara daya hadu dasu a wajen harkar shi ta canji yana cikin rufin asiri. Duk da abubuwa sun canza mishi sosai da sosai, amman yan uwan shi basu bari ya wulakanta ba, da yake suna da zumunci na gaske. Kuma yana gidan shi na nan gadon kaya har lokacin. Sannan har gobe indai zakace Yan gidan Bugaje saika samu wanda ya san wani daga cikin yan gidan, saboda yawan da suke dashi da kuma kasancewar akwai sauran masu arziqi cikin su har zuwa wannan lokacin. *** Tafiyar nan zata banbanta da kowacce iri, a karo na farko da SOYAYYA zatai mana jagora a kacokan din tafiyar. Duk da bazai zama dalilin da tafiyar zata kasance babu tangarda ba, banyi alkawari Happily ever after ba, ban yarda akwai shi ba. Sai dai nayi alkawari tafiyar zata kasance irin wadda baku taba cin karo da ita ba. Badan alkalamina yafi na kowa ba, sai dan alkalamina daban yake da na kowa. Ku biyo Yan gidan Bugaje a tasu tafiyar da take cike da tsantsar soyayya da cin Amana. *#Abdulkadir* *#FWA* *#AnaTare* *#LubnaSufyan*📖✏ FIKRA WRITER'S ASSOCIATION Facebook: Lubna Sufyan IG: SufyanLubna Email: Calmlubna@gmail.com *ABDDULKADIR* *LubnaSufyan* 01 DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI * Tsaye yake jikin bangon wajen, lokaci zuwa lokaci yakan saka hannun shi cikin sumar kan shi, bazai iya tuna ranar karshe da wani abu ya daga mishi hankali haka ba, yanayin yake ji ya zame mishi bako. Kayan da yake jikin shi yabi da kallo, gajeran wando ne na kakin sojoji da ko gwiwar shi bai taba ba, sai rigar wandon mai yankakken hannu, wuyan shi da alamar sarqar da baka ganin kota mecece, sai shi da take wuyan shi, wani dan dogon karfe ne maqale a jiki da yake dauke da sunan shi da kuma lambar aikin shi, dan lokutta da dama idan mutuwa ta gifta, sarqar ce kawai shaidar gane waye da waye ta runtsa da shi. Duk da kalar kakin bai hana shi ganin jinin daya bata kayan ba, jinin da kallon da yake mishi yasa wani abu tsinkewa a cikin shi, baida kalmar dazai dora abinda yake ji, saboda jini baya daga mishi hankali, ko kafin aikin shi yana da wata irin dakakkiyar zuciya taban mamaki, yau shine yakejin alamun zufa a goshin shi da ganin jini a jikin rigar shi. "Paapi zan sha ruwa..." Muryar Fajr ta doki kunnuwan shi tana tuna mishi cewar bashi kadai bane a wajen. Dan juyawa yayi yana kallon su, Fajr da yake cikin shekarun shi na biyar yanzun, dan dai yana da girman jiki da tsayin da zaisa kai tunanin ya wuce shekara biyar din da baima karasa ba, yana zaune da kanwar shi da duka watan ta hudu a duniya, yanda ya riketa dam yana sa Abdulkadir leqa yarinyar yaga ko tana numfashi. "Wanne irin riqo kai ma Ikram haka?" Kallon shi Fajr yayi yana shagwabe mishi fuska, dan shi ya gaji da rikon yarinyar. "Ni ina so in sha ruwa. Paapi, Omma fa?" Hannu Abdulkadir ya mika yana karbar Ikram din daga hannun Fajr, bacci take hankalinta kwance, dan daquna fuska yayi yana son tuna ko ya taba jin kukan yarinyar tun dawowar shi, bata da rigima ko kadan. Idanuwan shi yake hangawa ko zai hango inda zai samo ma Fajr din ruwa batare daya bar wajen ba, bayason motsawa daga inda yake ko likitan zai fito da wani bayani. Kasan zuciyar shi yake ji wani abu tamkar bargo da yake ta haduwa yana kara kauri, yasan shi yake so ya lullube da rashin gaskiyar da yake yawata mishi a ko ina na jikin shi. "Fajr ina zan ga ruwa anan?" Ya fadi, yana gyarama Ikram kwanciya akan kafadar shi, yanda ta kwantar da kanta a jikin shi na nutsar da kadan daga cikin abinda yake ji. Daga idanuwa ya sake yi ya kuwa sauke su kan Mami da ta turo kofar glass din wajen tana takowa, yanzun yake dana sanin kiranta da yayi, amman lokacin daya kira din a rikice yake, baisan abinda ya kamata yayi ba, ita tace ya dauko Waheedah din ya kawota asibiti, daya tashi saiya kwaso harda su Fajr. Aminu ya hango ya rufo mata baya, sai kuma Salim da Zainab. Ya manta yanda yan gidan su suke, yanayin aikin shi ya manta yanda ko kurjewa kayi indai za'a kaika asibiti mota daya tayi kadan, dan kusan rabinsu sai sunje, in kuka jima baku dawo ba zakuga sauran rabin da aka bari a gida sun biyo bayan su, yana tunanin duk wani asibiti da suke da file a garin Kano sun san Yan gidan Bugaje da wannan al'adar tasu, ba'a ma hanasu shiga. Suna karasowa Zainab ta mika hannu tana karbar Ikram daga hannun shi, baiyi musu ba ya mika mata ita. "Ya jikin nata?" Mami ta tambaye shi, idanuwan shi ya sauke kasa yana tsintar kan shi da kasa hada idanuwa da ita. Sai dai kafin ya amsa Fajr ya riga shi da fadin "Mami Omma ta fadi, jini mai yawa a kanta..." Hannu Mami ta miqa ma yaron daya taso yana kama hannunta hadi da zagaya dayan hannun nashi jikin kafafuwan ta, daga idanuwan shi yayi yana saukewa cikin na Abdulkadir da yake tsaye, harshen shi yake ji ya mishi nauyi, dan ya kasa amsa ma Mami tambayar da tai mishi. Rashin gaskiya ne shimfide a fuskar shi. Da wani irin yanayi da yake ji ya mishi wani iri Fajr yake kallon shi, sosai yaron yake kallon shi yana kara shigewa jikin Mami, idanuwan shi na cikin na Abdulkadir yace "Paapi ne yai pushing (Turewa) dinta ta fadi... Mami Paapi ne..." Wani irin shiru ya biyo bayan maganar yaron, shiru ne da hayaniyar shi tafi ta surutu, dan ko wani yazo wucewa shirun da yake wajen zai iya taba shi, dakuna fuska Abdulkadir yayi yana son nemo kalmar abinda ya lullube shi. 'Kunya' Wata murya ta furta can kasan kwakwalwar shi, sai dai shida kunya nada wata irin tazara da bazata misaltu ba, bata taba kamo shi ba ko acan ba, baisan ma ya akan jita ba, kai tsaye yake dukkan al'amuran shi, yau kam ba kamoshi kawai tayi ba, lullube shi tayi ruf, bargon rashin gaskiya mai kaurin gaske na bin bayanta, numfashin shi ma kamar a lissafe yake jin fitar shi. "Mami kinga abinda nake ce miki ko?" Aminu ya fadi yana korar shirun da yake kewaye da wajen. "Aminu..." Mami din ta kira cike da kashedi, akan ce yaro baya karya, musamman mai karancin shekaru kamar Fajr, sai dai yaran yanzun kuruciyar su cike take da abin mamaki, bakomai daya fito daga bakin su bane abin yarda, hakan shine take ta fadama kanta dan karta yarda da abinda Fajr din ya furta, duk da yanayin Abdulkadir din ya gasgata maganganun yaron nashi, amman batason ta yarda da hakan. Sam bata kula da girgiza mata kai da Aminu yake ba saida yace "Karki ce inyi shiru wannan karin ma, kina jin abinda Fajr ya fadi, Wallahi na jima da sanin Hamma Abdulkadir ne ajalin Adda Wahee..." Cikin tashin hankali Mami ta kalli Aminu din, yanayin kallon na sakashi kasa karasa maganar da yake, dauke idanuwan shi yayi daga kanta yana watsa ma Abdulkadir da yake tsaye wata irin harara, wani daci Aminu yake ji a kasa makoshin shi, ba tun yanzun Abdulkadir ya gama ficewa daga ranshi ba, Mami nace mishi Waheedah ta fadi ta fasa kai ya san Abdulkadir nada hannu dumu-dumu cikin faduwar tata, sai dai ko kadan bai hango sanadin zai zamana da hannun shi ba, ya dauka bacin ranshi ne ya sata faduwa tunda duk sun san tana da hawan jini. Da yana da iko kan igiyar auren Waheedah da Abdulkadir da tuni ya sa almakashi ya datse ta, datsar da babu hanyar da za'a abi a sake daurata har abada. "Hamma..." Zainab ta kira cike da wani yanayi dayasa Abdulkadir din sake kasa da kan shi, dan koya dago ma bashi da kalaman dazai musu amfani dashi, baisan me zaice musu ba, yawan magana ba dabi'ar shi bace ba tunda can, ko da yana da abin fadi kuwa, ballantana yanzun da babu abinda yake so kamar kasa wajen ta bude dai-dai inda yake tai kasa dashi. Kafin ta sake cewa wani abu likitan ya fito daga dakin da Waheedah take, wasu Nurses guda biyu na biyo bayan shi. Idanuwan shi ya sauke kan Abdulkadir, sai dai kafin yace ya bishi office kamar yanda Mami tasani ta riga shi magana da fadin "Ni mahaifiyar tace, wannan kannen tane, duk abinda zaka fada mishi zai mai-maita mana ne, gara ka fada anan din kawai..." Abdulkadir din dai likitan ya sake kallo, kai yadan jinjina mishi a hankali yana bashi izinin yin magana, numfashi ya sauke tukunna yace "Babu wata matsala In shaa Allah, munyi mata karamar tiyata saboda buguwar ta shiga sosai...badai yanzun zata tashi ba, amman zaku iya shiga ku ganta, banda yawan surutu dan Allah, kar a tasheta, tana bukatar hutun sosai ko dan jininta da ya hau fiye da na da..." Kai Mami ta jinjina tana mishi godiya tukunna ya wuce, hannun Fajr ta kama tana raba Abdulkadir ta shiga cikin dakin, daga inda take tsaye tana hango ramar da Waheedah tayi, tayi wata irin ramewa da duk da idanuwanta a rufe suke kana ganin ramin da yake kasan su, kanta nannade yake da bandeji, hannunta daure da karin ruwa. Wani irin abu Mami taji ya matse a cikin zuciyarta, a hankali ta taka tana jan kujera ta zauna, ta dora Fajr kan cinyarta. Hannu yaron yakai kan jikin Waheedah "Omma..." Ya fadi, Mami na kama hannun shi ta janye "Karka tashe ta Fajr, bacci take kaji..." "Ni zan sha ruwa..." Fajr ya fadi yana sa Mami din juyawa ta kalli Aminu da suma duk sun shigo dakin. Kafin tayi magana Salim yace "Bari in karbo... Ruwan kawai ake bukata? Ko zan taho da wani abin..." Waheedah ta kalla, tasan babu abinda Abdulkadir ya dauko, hakan yasa ta fadin "Ka fara kawo ruwan dai, sai kazo kuje gida kai da Zainab akwai yan abubuwan da zaku dauko mana..." Kai Salim ya jinjina mata yana juyawa ya fice daga dakin. A bakin kofa yaga Abdulkadir a tsaye, kallon shi kawai Salim yayi yana girgiza kan shi, tukunna ya wuce, kan kujerun da suke wajen Abdulkadir ya karasa yana zama, yau gabaki daya nasa shi jin abubuwan da yake tunanin yayi bankwana dasu shekaru da dama da suka wuce, yanzun kallon da Salim yai mishi yasa shi jin wani irin abu na lullube shi, so yake yaga halin da Waheedah take ciki, amman ya kasa shiga dakin, kunyar hada idanuwa da Mami yake ji, bazai iya shiga in tana nan ba. Kanshi ya saka cikin hannuwan shi yana dafewa. Tunanin barkatai na soma kawo mishi ziyara. * Salim na kawo ma Fajr ruwan suka juya su duka ukkun, harda Aminu, dan Fajr dinma manne musu yayi, dole ta karbi Ikram daga hannun Zainab, towel din da yarinyar take ciki tayi amfani dashi ta goyata. Tukunna ta danyi dabara ta zauna kan kujerar dakin, tunda ta rubber ce. Shisa tace har babbar darduma a dauko musu. Sosai ta nutsar da hankalin ta kan Waheedah, hannunta da ya kara zama siriri, daman abinka da ba qibar kirki ba, yanayin kaddarar yarinyar nasa idanuwan Mami din cika taf da hawaye. Tana da hakuri da kauda kai tasani, amman na Waheedah yayi yawa, ita ko baki ba zata iya budewa tace ana mata abu ba, in kuma ka tambaya murmushi kawai takanyi 'Mami rayuwar duka babu yawa, komai zai wuce kamar bai faru ba' Shine maganar ta a ko da yaushe idan kaso sanin halin da take ciki, da ba'a ganewa in baka kula da yanayin ramewar da take a tsaye, ko murmushin ta da baya kaiwa cikin idanuwan ta ba, to ita dai kam Mami zata iya cewa tun yawon arba'in din Ikram da tazo musu rabon da ta sakata a idanuwan ta, sai dai a waya, ta kuma hana su Aminu kawo mata zancen gidan Waheedah din, dan haka ko sun kula da wani abin in sunje ba zuwa suke suna fada mata ba. Batasan iya lokacin da ta dauka a zaune a wajen ba, sai da taji sallamar su Zainab din, amsawa tayi a hankali, yawan su na bata mamaki, kusan su duka gidan suka dawo, kasa-kasa suke magana, tarkacen da taga sun kwaso zaka rantse watanni zasuyi a asibitin, da alama abincin ranar da duk basuci bane ba zasuci shi yanzun a asibitin. Kujera Zainab ta mikoma Anty, dan a wajenta ma sukaje suka amshi abinci suke fada mata Waheedah na asibiti, ta biyosu suka taho tare. "Haj. Halima wai dagoki sukayi kenan" Mami ta fadi, Anty na zama da fadin "Ai baki kyauta mun ba, ko ba zaki shigo ki fadamun Waheedah na asibiti ba ai saiki aikomun ko? Ke ce zaki kwana da ita?" Murmushi kawai Mami tadan yi, daman tayi niyyar Zainab ta kwana ne, ita da dare saita tusa su Aminu a gaba, kirkin Anty bazai gaji da bata mamaki ba. "Ya jikin nata?" Anty ta tambaya "Gata nan dai bata tashi ba har yanzun..." Mami ta fadi, su Nabila da suka fara fada da Salim Anty ta kalla "Zanci ubanku wallahi, ku kamar kaji bakwa zama waje daya?" Harara Salim yake watsa ma Nabila "Anty hannuna ya fara taba plate din..." "Ni na riga gani, Anty kice yabarmun suci dashi da Aminu..." Nabila ta fadi a tabare, Salim na samun damar fisge plate din. "Kuci tare ke da shi..." Shagwabe fuska Nabila tayi, idanuwanta na cika da hawaye "Ni bazan ci dashi ba" Numfashi Anty ta sauke "Na sake magana akan ku saikun koma gida, tunda ba yara bane ku, da ina sanyin surutu dana taho da Albarkah..." Sanin halinta yasa suka nutsu, tare suka zuba abincin, tana kallo suna kaiwa cokulan juna karo, dauke idanuwanta tayi daga kansu, dan sun saba, kullum cikin fada suke, ko makaranta zasu je haka suke kamar kaji, kuma ta rasa kalar fadan nasu, randa ya jibgeta kuma tana kuka haka zata bishi su tafi tare. Indai kace zaka shiga rigimar su kaine zaka sha kunya. "Ikram ce kika goya haka?" Anty ta tambaya tana daga hijab din Mami, taga yarinyar ta farka tana ta kalle-kalle. "Idon ta biyu ma..." Cewar Anty "Ikon Allah..." Mami ta fadi tana mikewa ta kwance goyon tana sauko Ikram "Ke baiwar Allah babu magana..." Inji Mami tana gyarama Ikram din zama, da alamu hakurin mahaifiyarta ta biyo, sam yarinyar bata da rigima, ruwa ta karba ta zuba a murfin tana ba Ikram din "In kuma basa ba yar su ruwa fa?" Anty ta bukata "Nidai ai na bata, wannan shirmen nasu na zamani ba dani za'ayi shi ba, cikin su babu wanda ba'a bama ruwa ba, meya same su?" Dariya Anty tayi "Ni kaina bazan iya ba wallahi, gani nake daukar alhaki ne..." Hira suke a hankali a hankali, Anty ita tasa Mami dan tsakurar abinci, dan damuwa ce fal ranta. "Ba za'a zuba a mika ma Abdulkadir ba kuwa? Yana wajen nan" Mami ta fadi tana sa Anty kallon ta "Ni rabani da wannan dan Allah, ya koma gida yaci wajen dayar matar shi, ban zubo abincina da shi ba nikam" Shiru Mami tayi, sai dai duk yanda taso ta nuna halin ko in kula da Abdulkadir din sai ta kasa, Ikram ta mikama Anty tana mikewa ta taka zuwa kofa tasa hannu ta bude dakin tana leqa kai, yana zaune kuwa ya hade kanshi cikin hannayen shi. "Abdulkadir..." Ta kira a hankali tana kallon yanda ya dago kai, idanuwan shi sun sauya launi. Yanayin kaddarar su na mata nauyi "Ba zaka shigo kaganta ba?" Abinda yake son yi kenan, amman ya kasa, yanzun dinma kunyar Mami tasa shi sadda kanshi kasa yana kasa cewa komai. "Ka shigo ka ganta..." Mami ta umarta, sai da taga ya mike tsaye tukunna ta dawo da kanta cikin dakin, a hankali ya tako yana shigowa, daga bangon kusa da kofar ya tsaya yana jingina bayan shi a jiki, inda Mami take zaune ta koma tana zama, idanuwan shi ya tsayar kan Waheedah da nata suke a rufe da alamun bacci, duk da haka yana jin gabaki daya idanuwan su na yawo a jikin shi, ya zabi yaki kallon sune kawai dan bayason yaga kallon tuhumar da suke mishi. Zuciyar shi yaji tayi tsalle tana shirin dawowa cikin makoshin shi, kafin ta koma mazauninta tana ci gaba da wata irin dokawa da yake ji ba cikin kunnuwan shi kawai ba, har a ko ina na jikin shi, bai tsammaci Waheedah zata bude idanuwan ta data sauke cikin nashi ba. "Waheedah... Alhamdulillah..." Yaji muryar Anty ta fadi, yana kuma jin motsin kannen shi da suke mikewa suna tahowa sukai ma gadon Waheedah din rumfa, yadai daina gane me suke ta fada, saboda har lokacin idanuwan Waheedah na cikin nashi, kallon shi take da wani irin yanayi da yasa zuciyar shi rawa. Yasha ganin yanayi da dama cikin idanuwanta, kaunar shi na daya daga cikin yanayoyin da suka rinjayi sauran, suka rinjayi lokuttan da ko a kasan bata mata ran da yakan gani akwai kaunar shi. Wannan yanayin bakone, kuma bazai ma kan shi karya ba, ya soma ganin alamun shi wajen kwana hudu da suka wuce. Sai dai duk idan yaga giccin yanayin yakan ga alamun kaunar shi da yake son rinjayar ko meye din yake gani. Yau kam kallon ta yake, duba idanuwanta yakeyi sosai yana neman alamar kaunar shi a cikin su ya rasa, a hankali yake girgiza mata kai, akwai inda ta boye soyayyar shi, ba zatai mishi haka ba, Waheedah ce yasani, kaunar shi bangare ce na rayuwarta da bata boye mishi, ba zata fara ba yau, bakin ta yaga ya fara motsawa kafin yaji dirar muryarta cikin kunnuwan shi da fadin "Mami dan Allah ku ban waje inyi magana dashi..." Bazai ce ga asalin abinda yake ji ba, amman yasan bayason subar dakin, bayason fuskantar ta, a karo na farko da yake son gujema fuskantar wani abu, bai taba hango zuwan ranar nan ko a mafarkin shi ba. "Ko ruwa ki sha..." Anty ta fadi, yana kallo Waheedah ta girgiza mata kai, har lokacin shi take kallo da yanayin nan cikin idanuwan ta. "Ina son magana da shi dan Allah..." Ta sake furtawa, yana kallon daga Mami har Anty suna mikewa, su Salim suka fara wucewa suna fita daga dakin. Anty ce karshe, bata fita ba sai da ta dan tsaya tana mai wani irin kallo kamar tana son yawo da idanuwanta cikin zuciyar shi ne taga abinda yake boyewa kowa, tukunna ta fice tana turo musu kofar. "Ka zo ka zauna..." Waheedah ta fadi, daga inda yake taga ya girgiza mata kai. Zuciyarta take jin ta daskare a kirjinta, ta dunqule waje daya kamar dutse, ta dauka datai hakan ba zatai mata

Chapter 1 of 37