Share this page
zaki barni ba" Murmushin karfin hali tayi badan zuciyarta ta nutsu ba, amman shi dinma bata ganin nutsuwa a tattare dashi, bata so ya koma wajen aiki a haka. "Ka taba ganin mata tabar mijinta? Ina zanje nikam...ina tare da kai daga yanzun har sauran kwanakin da Allah ya aramun" Numfashi AbdulKadir ya sauke yana barin kalamanta na samun wajen zama a kasan zuciyarshi. Yakai mintina biyu tukunna ya saki fuskarta yana mikewa, bandaki ya shiga ya watsa ruwa, amman ko kadan baiji wani sauki ba, hankalin shi yakeji yaki kwanciya, ga wani bangare na zuciyarshi da yake azalzalar shi ya fadama Waheedah din kawai ya huta, amman ya kasa samun karfin gwiwar fada mata, baisan ta inda zai fara ba. Kwanciya sukayi, Waheedah na jikin shi, ko kadan bacci ya kaurace ma idanuwan shi, ya rasa abinda yake mishi dadi a duniya, karfe hudu ya mike ya karayin wanka, shiya hada kayanshi, ya rasa karfin zuciyar tashin Waheedah din, kai kawon da yakeyi da motsin shi da yai yawa shiya tasheta. Fuskarta kawai ta wanke tayi brush ta wuce kitchen tana fara fere dankalin turawa, iya wanda AbdulKadir din zaici ta soya. Kafin biyar harta gama komai yaci, tana kula da yanda yake komai da wani irin sanyi da yake taba mata zuciya. Kafin asuba yake fita daman, Yassar ne yake zuwa yana sauke shi tasha. Amman yau kwata-kwatsa AbdulKadir din bai tsammaci zai zo ba, har saida yaji karar shigowar mota tukunna. Jakarshi ya rataya Waheedah na rakashi har bakin kofa, ta kasa sabawa har yanzun, duk randa zai tafi sai tayi kuka. Yanzun ma idanuwan ta cike suke da hawaye, muryarta na rawa tace "Allah ya tsare mun kai a duk inda zaka shiga. Ka kula da kanka dan Allah..." Kai AbdulKadir din ya daga mata yana rungumeta a jikin shi, saman kanta ya sumbata da gefen fuskarta, tukunna ya dago ta daga jikin shi "Zanyi kokari in dawo wata na gaba in shaa Allah. Ki kulamun da kanku..." Sake rungumeshi tayi tanajin kamar karya tafi. Dakyar ta iya raba jikinta da nashi, tana sa hannunta ta share kwallar data tarar mata. Shi kanshi yanajin barin nata, da son samun shine duk inda zaije da ita zai tafi. Amman ya fahimce ta data fada mishi Fajr na bukatar samun ilimin addini mai inganci, zaman Lagos ba nata bane da yara, tafiso ta natsu waje daya. Shisa ma ya dawo da ita Kanon, tunda shima wani lokaci aiki na dauke shi watanni, duk inda yakaita in hakan ya faru ita kadai zata zauna. Gara a gida inda yasan tana zagaye da yan uwa. Sai da ya sake sumbatarta tukunna ya fice daga gidan yanajin yau ba wani bangaren shi ya bari ba, harda wani irin nauyi mai girman gaske da rashin gaya mata maganar auren shi, tunda ta tashi yake motsa bakin shi, kalamai ne sukaqi fitowa. Abba ya kamata ya tambaya ta inda zai fara tunda shi yayi hakan har sau uku. Zaifi kowa sanin kalaman daya dace yayi amfani dasu, amman Abba fushi yake mishi, tunda bai kirashi yau ya mishi Allah ya tsare ba. Wajen motar Yassar din ya karasa ya bude ya shiga yana fadin "Hamma ina kwana..." Inda yake Yassar bai kalla ba yaja motar yana fita daga gidan. Numfashi AbdulKadir ya sauke "Kai ma fushin kakeyi kenan har yau... Ni banyi fushi na Hamma kaine kakeyi... Ok" AbdulKadir ya karasa maganar yana sauke wani numfashin "Da Kawu Ali mukaje jiya... An daura auren tun jiya... Ban fadama Waheedah ba, Hamma na kasa fada mata, tunanin bai zo mun ba sam sai bayan an daura auren. Ya kamata in fada mata..." Katse shi Yassar yayi da cewa "Wallahi, Wallahi idan kaci gaba da magana zan saukeka ka nemi abinda zai kaika tasha ko ka taka da kafa bai dameni ba. Allah kadai yasan yanda nakai zuciyata nesa na fito... Kayi abinda kake so, wannan matsalarka ce, tun jiya ka rigada ka nuna mun banda matsala da aurenka. Kabar shi a haka kawai, bana son jin duk wani abu daya shafi tsakanin ka da Nuriyya, yanzun, anjima, gobe, kai har iya zaman rayuwar aurenku idan kana son zaman lafiya dani ba zaka kawomun zancen ta ba" Muryar Yassar din ta tabbatar ma da AbdulKadir yana nufin dukkan kalaman daya fada, daga zuciyarshi yai maganar. A karo na farko da yaji bayason kure hakurin Yassar din. Shiru yayi, yana kara jin komai ya hade mishi waje daya. Wayarshi ya laluba yana ganin text din Nuriyya. Mayar da ita yayi ya ajiye, itama baisan me zaice mata din ba, baisan me zaicewa kowa ba. A bakin tashar unguwa uku Yassar ya sauke AbdulKadir din yana fadin "Allah ya tsare..." Yaja motar shi ya wuce, da gaske fushi Yassar yake mishi, dan yakan samu waje yai parking, baya tafiya sai yaga AbdulKadir din ya shiga mota suna shirin tashi tukunna. Wani irin numfashi AbdulKadir yaja yana fitar dashi a wahalce, zai karya idan yace ranshi bai sosu ba, amman Waheedah ta danne duk wani abu da yakeji yau. Zai bi takan sauran al'amura idan ya samu hanyar fada mata ya kara aure. * Inda Baba ya fita yabarta, nan ya dawo ya sameta, badan bataso ta tashin ba, sai dan tanajin tsoron tashi ta farka daga mafarkin da takeyi na cewar AbdulKadir yazo neman aurenta wajen Baba. Magana ce da takejin ta kamar almara. Sallamar da Baba yayi yana kiran Mama ya katse mata tunanin da takeyi, duk da hakan baisa ta daina jinta kamar a mafarki ba. Mama ta fito tana kallon Baba da farin cikin dake fuskar shi. "Auren Nuriyya aka daura yanzun a masallaci" Cike da mamaki Mama take kallon Baba, tasan kullum zancen shi baya wuce na Nuriyyar duk sanda zasu kebe, amman bai mata zancen ya samo mata miji ko kuma akwai wanda ya same shi da maganar aurenta ba. "Ban fahimta ba, aure fa kace Baban Nuriyya..." Kai Baba ya jinjina mata "Fitar da nayi dazun da maganar suka zo, to a shirye suke ashe" Har lokacin da mamaki a fuskar Mama tace "Duk da a shirye suke, kuma ba auren farko bane abin da mamaki, badan baya faruwa ba har a auren budurwar, amman gaggawa na daga shaidan fa, wanene yaron? A musulunce ya kamata ayi bincike kafin a daura" Murmushi Baba yayi "Nasani, nima nayi tunanin, amman ganin dan gidan Alhaji Ahmad ne shisa ma banki ba" Da wani sabon mamakin karara a fuskar Mama take kallon Baba "Dan gidan Alhaji Ahmad kuma? Wanne daga ciki?" Gyaran murya Baba yayi tukunna yace "AbdulKadir" Wannan karin da tashin hankali bayananne Mama take kallon shi, cike da yanayin da yasa yaji gabanshi ya fadi "Lafiya kuwa? Me ya faru?" Kai Mama take girgizawa "AbdulKadir naji kace, AbdulKadir dan gidan Alhaji Ahmad" Da sauri Baba yake jinjina mata kai. "Eh shi nace" Bango Mama ta laluba tana samun kujera ta katako ta zauna akai tana wani irin mayar da numfashi hadi da fadin "Nuriyya me kikayi? Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..." Sosai Baba yake kallon Mama "Kimun bayani yanda zan gane... Me yake faruwa wai" Kai Mama ta daga tana kallon Baba da idanuwan da suke cike da hawaye, ko da fada mishi tayi ba lallai bane ya fahimta, abune da 'ya mace kawai zata fahimci ciwon shi, dan ita zuciyarta wani irin zugi take mata, batajin zata dauki abinda akai ma Waheedah din, batasan hawayen ta sun zubo ba sai da taji su kan kuncinta, muryarta na sarqewa tace "AbdulKadir dinne baka sani ba? Baban Nuriyya AbdulKadir dinne baka gane ba kafin ka biyewa son zuciyar 'yarka ka wakilci daurin auren nan ko me?" Kafafuwan shi Baba yaji sunyi sanyi, tsugunnawa yayi, yasan matarshi farin sani, a tsayin zamansu, abinda zai sakata zubar kwalla babba ne. "Maryama na kasa fahimtar ki, kimun magana yanda zan gane, kaina ya daure" Wani irin kallo Mama take mishi da duk ya kara dagula mishi lissafi "Kasan yana da aure ko?" Kai Baba ya jinjina yana kallonta cikin kaguwa da jin sauran zancen "Kana so kace mun baka san wacece matar shi ba" Kai Baba yake girgiza mata, zai iya tuna lokacin da akai auren AbdulKadir din, su uku ne ko fiye da haka aka daurama aure ranar in zai tuna, dan a makare yaje, ko cikin masallacin bai samu shiga ba saboda cikowar mutane, ya tsayane har Alhaji Ahmad ya fito yai mishi Allah yasa alkhairi ya wuce. Wani irin daci Mama takeji har kasan zuciyarta, bata shiga harkar Nuriyya ne saboda batason rainin yarinyar, shisa a lokutta da dama take binta da ido, tasan tana da halaye marassa kyau, amman bata taba zaton ko zata nunawa kowa zai fada kan Waheedah ba. "Amman kasan Waheedah ai" Kan dai Baba ya sake daga mata "Ya zakice nasan Waheedah... Waheedah fa" Baba ya maimaita, yarinyar da aminiyar 'yar shi ce, kaunar dake tsakaninta da Nuriyyar ta kara karfin zumunci shi da Alhaji Ahmad din har yake samun alkhairai da dama daga shi har 'yar tashi. Hankali da nutsuwar yarinyar yasa duk shekarun shi yana ganin girmanta ba kadan ba. Kuma ko da Nuriyya tayi aure duk idan Waheedah tazo gida saita biyo ta gaishe dasu ko baya nan, yakan dawo ya samu sakon abin alkhairin da ta kawo musu. "Hmm..." Mama ta fadi zuciyarta kamar zata baro kirjinta, sai da ta hadiye wani abu dayai mata tsaye a makoshi tukunna tace "Mijinta ne ka aura ma 'yarka" Cikin tashin hankali Baba yake kallon Mama, yana son tace mishi abinda yaji ba gaskiya bane ba. Yasan Nuriyya daya daga cikin yaran Alhaji Ahmad ta aura, amman harga Allah bazai ce wanne bane a cikinsu, kuma bai taba kawo ma ranshi AbdulKadir din bane ba, tunda da kan shi yazo neman auren Nuriyyar, kuma itama Nuriyyar tasani, ko a mugun mafarki kuma bai hango cewar zasu hadu su biyun suyi wannan cin amanar da addini bai haramta ba, amman kunya da kara ta haramtashi ta kowacce fuska. "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un" Baba yake fadi yana maimaitawa, idan hankalin shi yayi dubu gabaki daya yagama tashi. Ya rasa abinda zaice, mikewa Mama tayi tana kara share kwalla kafin tace "Bansan abinda kikayi ba Nuriyya, bansan da idon da zaki kalli Waheedah a matsayin kishiya bayan duk halarcin da taimiki da zumuncin dake tsakanin ku ba, wallahi bansani ba. Nikam nasan bazan iya kallon idanuwan yarinyar nan ba.... Duk da ina son tasan bada sa hannuna kikai mata wannan cin amanar ba" Mama ta karashe maganar tana barin wajen, Baba kuwa har lokacin ya kasa magana, hannu yasa cikin aljihunshi ya zaro sadakin Nuriyya da tunda aka fara maganar kanta yake a kasa, hawaye kawai suke zubar mata badan zata iya cewa ga asalin dalilin zubar tasu ba. Duk da ta daina jin duk wata magana da ta biyo bayan an daura aurenta da AbdulKadir, sai yanzun da tabi kudin da Baba ya ajiye mata da kallo. "Wallahi da nasan mijin Waheedah ne sai dai ku nemi wanda zai daura muku auren nan Nuriyya... Bansan me kikayi ba, daga ke har shi, ban kuma san dalilinku nayin abinda kukayi ba. Amman in kunyi da son zuciya amana ba zata taba barinku ba..." Baba ya fadi yana tashi shima. Dakin shi ya wuce yana jinjina al'amarin da kuma daukar da Waheedah zatayi musu ta mutanen da basu san darajar zaman tare da girman alkhairi ba, kuma bazai ga laifinta ba. Da gaske ne gaggawa a komai daga shaidan take, yanda ya kaqu ya rabu da Nuriyya yasa shi amincewa auren batare da tunanin komai ba. A karo na farko da yabi son zuciyarshi gashi tun ba'a je ko ina ba ya fara dana sani. Nuriyya kuwa kudin ta dauka tana komawa daki ta kwanta, har lokacin bata daina jinta kamar a mafarki ba. Wayarta ta dauko, duk da tana shakkar ta kira AbdulKadir din, text ta tura mishi 'Nagode Masoyi, duk da na kasa yarda na zaka matarka, wallahi ina jina kamar a mafarki' Sai da taga sakon ya shiga tukunna ta sauke wayar kan kirjinta tana jin wani irin nishadi da bata tabaji ba a rayuwarta yana lullubeta, kafin bacci ya kwasheta cike da mafarkin rayuwar da zatayi a matsayin matar AbdulKadir. * Komai bai sake hade mishi waje daya ba sai bayan komawar shi Lagos. Duk wani wanda yake sama dashi a gidansu saida ya kira yai mishi tas kan maganar auren, gabaki daya babu wanda ko Allah yasa alkhairi yai mishi, ya manta rabon da yayi kwanaki da bacin rai haka. Har kannen nashi ma Zahra sai da tayi mishi text 'Hamma baka kyauta mana ba, zaka zageni nasani, amman bai dameni ba wallahi. Abinda kayi baka kyauta ba' Ya kuwa kira din ya sauke mata masifa kamar zai cinyeta, kukan ta daya ishe shine yasa shi kashe wayar shi, daman wanda zai huce akan shi yake nema. Gabaki daya ya rasa yanda zaiyi ko inda zai saka ranshi yaji sanyi, ga Waheedah duk waya ko video call din da zasuyi sai yaga ta kara mishi wani irin kwarjini da ko maganar kirki sai yayi da gaske yake iya hadata balle har yai mata zancen auren. Nuriyya ma kullum suna waya a gajarce, a satika biyun da yayi a Lagos doguwar waya daya sukayi, shima bayan ya kira Anty Talatu da tunda yake a rayuwarshi bai taba tunanin akwai ranar da zai bukaci wani abu daga wajenta ba. Amman babu yanda zaiyi, babu wanda zai tambaya tunda duka yan gidansu basa magana dashi dan ya kara aure, itace ta fara zuwa kan shi. Ko ita din ma mamakine bayyane a muryarta da ta daga wayar, suka gaisa tana dorawa da "Lafiya dai ko AbdulKadir? Kowa lafiyar shi kalau?" Kai ya daga kamar tana ganin shi "Lafiya kalau Anty, zan tambayeki ne daman" Yanajin sauke numfashin da tayi kafin ya dora da "Idan ka auri bazawara zakayi akwatuna duka ko?" Dariya Anty tayi daga dayan bangaren "In kana da halin hakan, ai kyautatawa ce, amman bakowa yakeyi ba gaskiya. Zaka iya magana da ita kaji, wasu sunfi son a basu kudin ma akan a sai musu kayan, kai ma kuma zaifi maka sauqi" Jinjina kai AbdulKadir yayi, dan bai fahimci maganar Kawu Ali kan lefen ba, ita kuma Nuriyya batayi mishi zancen ba. Shisa ya kira Antyn dan yaji in sai yayine sai yasan yanda zaiyi "Kaman nawa zai isa" Ya tambaya "Gaskiya bazance ba, daga dubu dari in kana da hali har dari biyu ma, ko kasa da hakan. Iya aljihunka iya abinda zaka yi" Shiru AbdulKadir yayi "Idan nace banda dubu dari biyu nayi karya, amman akwai hidindimu a gabana nikam, matata nada ciki" Yar dariya Anty tayi "Bakayi tunanin akwai wata hidima a gabanka ba kake shirin kara aure, na dauka halin naku na mazane ya motsa ai, aljihunka kaji a cike da kudin da bakasan yanda zakayi dashi ba sai karin aure..." Dan murmushi AbdulKadir yayi "Nasan ba zamu gama wayar nan lafiya ba Anty... Dole sai kin fadamun maganar da zanji daman ban kira ba" Dariya Anty tayi sosai "Allah ya shirya mana halinka AbdulKadir..." Sallama yai mata hadi da godiya kafin ya kashe wayar. Da gaske yake da yace mata hidima ce a gabanshi, akwai kudaden da yake ajiye da sai dolece take sakawa ya tabasu, yana ajiyewa ne saboda tsaron lalura. Dan sai da aka haifi Fajr tukunna yasan kula da yara ba abu bane me sauqi. Saima daya fara haqora, ga kyanda. Shisa baya wasa da ajiye kudi dan irin lalura haka. Yanzun kuma Waheedah nada wani cikin, yana son ta samu duk kulawar da take bukata, asibiti me kyau da baifi karfin shi ba. Sannan ga kayan babies da itama kayan da zai mata da sauran hidindimu. Amman auren ma shiya yanke hukuncin yin shi. Dole ne yayi abinda ya dace. Akan maganar kudin kayan ne sukai doguwar waya da Nuriyya. Ya karbi account number dinta ya tura mata, ta mishi maganar tarewa yace mata saiya koma nan da sati biyu sai suyi maganar. Badan bashida wajen da zai ajiyeta ba, sai dan har zuwa lokacin bai fadama Waheedah ba. Duk wayar da zasuyi sai yaji zuciyarshi ta doka, hankalin shi baya kwanciya sai yaji tana mishi hira, gani yake kamar wani daga cikin yan gidansu zai sameta ya fada mata. Duk da zaiso hakan, zasu hutar dashi, amman kuma dukkan zuciyarshi na fada mishi zai kyautu ya fada mata da kan shi. In da zai samu kwarin gwiwar yin hakan. Idan yace ga yanda watan ya wuce mishi da sauri haka yayi karya. Bai taba ganin gudun kwanaki ba sai da yagan shi yana hada abinda yake bukata a yar jakar shi da yammacin juma'a, dan ranar zaibi motar dare ya isa Kano da safiyar asabar. Yasan yau dinne ranar karshe da yake da ita da zai fadama Waheedah ya kara aure, idan bata sani yau ba sai yaje gida gobe tukunna, ba kuma yajin zai iya kallon idanuwanta ya fada mata. Bashi da wannan karfin halin, yanzun kuma yake sanin hakan. Gefen gadon dakin yake zaune, ya mika hannu ya dauko wayar shi. Lambar Waheedah ya lalubo, basu dade da gama magana ba, ita tasa shi ya tashi ya hada kayan shi, tace karya taho da yunwa, yaci wani abu. Amman abinci ne karshen abinda yake ranshi. Sake kira yayi, ta daga da fadin "Sadauki... Harka shirya kayan?" Kai ya daga mata batare da yace komai ba, dan a rayuwarshi ita kadaice take fahimtar shirun shi, da yayi magana da baiyi ba Waheedah takan fahimta, abin ya daina bashi mamaki. "Menene? Shirun nan naka yana mun yawa kwana biyu. Wani abu yana damunka amman kaqi fadamun ko?" Numfashi ya tsinci kanshi da saukewa da baisan yana rike dashi ba. Muryarshi na rawa yace "Magana nake so in fada miki, ba tun yau ba, tun ana gobe zan taho, bansan ta ina zan fara bane Wahee...a karo na farko da bansan yazan miki magana ba, ina nufin kece, komai fada miki nake batare da tunani ba, na kasa yanzun.... Ina so in fada miki har raina amman na kasa" Ya karashe yanajin wani irin tashin hankali da bai taba tunani ba "Nice kaman yanda kace... Akwai wani abu da zaka boyemun? Ka fadamun dan Allah... Menene?" Kai AbdulKadir yake girgizawa, yanayin muryarta ya kara sakawa yaji komai ya kwance mishi "Bansan ya zan fara ba" Shiru tadanyi na wasu dakika kafin tace "Sadauki kana tsoratani, cikine a jikina ko ka manta? Ka fadamun dan Allah" Wannan karin hannu yasa yana dafe kan shi, bugun zuciyarshi na karuwa, sauke wayar yayi daga kunnen shi yana kashewa. Kafin ya rasa kwarin gwiwar da yakeji ya bude shafin tura saqo ya fara rubutu 'Aure nayi ana gobe zan dawo Waheedah, bansan yazan fada miki ba' Ya tura yana jin kamar yabishi ya kamo, sai dai kamar auren shine, ya riga da ya faru, babu damar komawa baya ya canza komai, sakon ya riga ya shiga dan ya nuna mishi alama Waheedah ta samu, zufa yakeji a duk wata kafa ta jikin shi yana jiran ganin sakonta. Da hasken wayar ya dauke sai ya sake tabawa, bai san ya dauki mintina talatin yana jiran sakonta ba saida ya duba lokaci. 'Dan Allah kice wani abu Waheedah, ki ce wani abu' Nan ma saida ya kara mintina goma yana zufar da duk iskar fankar dake dakin bata kai mishi kafin yaga wayar shi ta kawo haske. Jikin shi babu inda baya rawa ya daga yana dubawa. 'Ran daren da zaka tafi? Wata daya daya wuce kenan ko?' Da sauri ya fara bata amsa 'Da gaske Wahee, ki yarda dani tun ranar naso in fada miki, tun ranar' Wannan karin bata dauki lokaci ba ta turo mishi 'Karka damu. Allah yasa hakan ne mafi alkhairi, bari inyi alwala naji an fara kiran Magriba' Wata irin ajiyar zuciya AbdulKadir din ya sauke, kafin ya sake ganin text dinta 'Allah ya tsare ya kawo mana kai lafiya, ka daici abinci karka manta. Zan sa chargy an kawo wuta, saura 2%' Da murmushi a fuskarshi yace 'Nagode, Nagode sosai. In shaa Allah. Ki kulamun da ku. Zan kiraki dana shiga mota' Ya sa ran amsa koya take, dayaga bata turo komai ba ya mike yana hakura. Wanka ya shiga yayi ya fito ya sake kayan jikin shi tukunna ya fita masallaci. Saida ya biya ya siya abinci yaci, hankalin shi yakeji ya kwanta sosai. Yasan daman idan kowa bai fahimce shi ba, Waheedah zata fahimce shi, shisa take da matsayin da babu wanda yake dashi a rayuwar shi. Yana dawowa jakar shi ya dauka yayi addu'a a bakin kofa kafin ya fita ya kulle gidan yana takawa zuwa gate da zai samu yaje inda zai hau machine zuwa tasha...! #TeamWaheedah #TeamAbdulKadir #LubnaSufyan[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan IG: SufyanLubna Email: Calmlubna@gmail.com Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43 *ABDDULKADIR* *LubnaSufyan* 24 Wayar tasa a chargy kamar yanda ta fada mishi, sai dai ta kasa dagowa daga tsugunnan da tayi. Wayar take kallo tana gane asalin ma'anar 'Yawo kan gajimare'. Duk da ba zatace ga ranar da wuyanta ya gajiya da daukar nauyin kanta ba, yau kan jinshi take kamar baya jikin ta, gashi yana mata tamkar iska ta cika shi tana fita ta hancinta da kunnuwanta har ma da idanuwanta. Kafin kan nata yai wata irin sarawa cike da fahimtar ma'anar 'Aure nayi ana gobe zan dawo Waheedah, bansan ya zan fada miki ba' Da kuma abinda hakan yake nufi a rayuwarta, numfashinta takeji yana barazanar kin wuce kirjinta yakai inda zai ba zuciyarta damar cigaba da dokawa yanda ya kamata. Wani irin numfashi take ja a wahalce, a karo na farko a rayuwarta da tashin hankalin da takeji yafi karfin hawayenta. "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un" Ta samu furtawa tana zama sosai kafin taja kafafuwanta ta dora kanta a sama ko zataji saukin zafin da zuciyarta take mata, lokacin da ta fara laulayi jinta take a wata duniya ta daban, duniyar da wanda ya taba shiga halin da ta tsinci kanta ne kawai zai fahimta, bata san akwai duniyar da zata shiga tafi waccen wahalar sha'ani ba sai yanzun. Ciwo take ji daya wuce fatarta da jininta zuwa cikin kasusuwan jikinta. Idan tace ga asalin abinda ya fi mata ciwo karya take. Auren da yayi da batada darajar da zata sani kafin a daura shi, kallon idanuwanta bayan an daura din dayi mata murmushi kamar babu wani abu mai muhimmanci da yake tunanin ya kamata ya sanar da ita, ko kuma zabar ya fada mata abinda ya canza rayuwarta da ta tashi ta sakon waya. "Banda daraja har haka a idanuwanka Sadauki? Ban nuna maka farin cikin ka na da muhimmanci a wajena bane da zai isa in baka goyon baya akan kowanne irin al'amari ba?" Waheedah take maganar kamar zararriya, dan batasan a fili takeyin ta ba, ta dai san daga wani bangare na zuciyarta mai ciwon gaske maganganun suke fitowa. Bata san iya lokacin da ta dauka a zaune tana kallon bango batare da tasan asalin abinda take tunani ba, banda wani irin ciwo da bata tunanin akwai abinda yake da maganin shi batajin komai. Kamar a wata duniya da ta jima da bari take jin wayarta na ruri, dakyar ta iya raba idanuwanta daga bangon da take kallo tana sauke su akan wayar 'Sadauki' Ta gani rubuce a jiki "Me kake so dani Sadauki?" Ta tambaya tana kallon wayar harta yanke, wani sabon kiran ya sake shigowa. Hannu ta mika ta zare wayar daga chargy tana dannawa ta amsa kiran hadi da karawa a kunnenta da wani irin sanyin murya tace "Hello..." Tana mike kafafuwanta da sukai mata sanyi, ga abinda ke cikinta da taji ya dunqule waje daya kamar yana tayata daukar ciwon da takeji, hakan nasata fahimtar wani irin ciwon mara da batasan tun yaushe ya fara mata ba. "Kin fara bacci ne?" Kai ta girgiza mishi a hankali, a karo na farko da taji muryarshi na kara mata ciwo, taji da magana dashi gara mata kallon bangon da takeyi, shi baya kara mata ciwo, amman muryar AbdulKadir din kamar gishiri a sababbin ciwukan da yaji mata takejinta. "Na sa chargy ne" Dan jim yayi ta dayan bangaren kafin yace "Inata kira tun dazun babu network" Sama-sama take jinta, komai na mata wani iri "Har kun taho?" Ta tsinci kanta da tambaya "Tun dazun, amman cunkoso har yanzun muna cikin Lagos" Kai ta jinjina mishi "Allah ya tsare maka hanya ya kawo ka lafiya" Amsawa yayi da "Amin..." Yana dorawa da "Ki kula da kanku" Ita ta jinjina kan tana kasa cewa komai ta sauke wayar daga kunnenta, chargyn ta mayar, dakyar ta iya mikewa, wani irin jiri daya dibeta yasa ta koma tana kiran sunan Allah duk wanda ya zo bakinta. Numfashi take fitarwa a wahalshe, ciwo take ji da bazai misaltu ba, tafi awa daya a zaune kafin ta iya mikewa, Fajr ma bata iya ta matsar dashi gefe ba, ita taja jiki kan katifar ta kwanta gefen shi. Ko sallar isha'i batayi ba, amman ciwon da takeji ba zata iya zuwa bandaki har ta iyayin alwala ba. Daga kwancen ma jiri take ji. Bata san dare yayi ba sai lokacin da ta samu ta sauko daga gadon ta dauki wayar ta taga karfe daya. Ajiyewa tayi har lokacin jiri takeji. Ga ciwon marar da takeji ya tsanantar mata, ga wasu ciwukan daban da ba zatace ga daga inda suke fitowa ba, amman mararta da zuciyarta su tafi ji. Bango ta dinga bi har takai bandaki, dakyar ta iya daura alwala ta fito. Daga zaune tayi sallah dan ba zata iya tsayuwar ba, azkar ta gabatar na bayan sallah, tana kwanciya anan kan kafet din dan ko addu'a bata iyayi ba. Sunayen Allah duk wanda yazo bakinta fadin shi takeyi ko zata samu saukin azabar da takeji. Akan kunnenta akai kiran sallah na farko, har aka sakeyin wani aka shiga masallaci tukunna ta iya raba jikinta da kafet din. Alwala ta sake zuwa tayi dan batajin ta cikin yanayin da zata tabbatar tana da alwalar. Ta shiga wata duniya mai wahalar misaltawa. Sallah ta dawo tayi, tana sake komawa ta

Chapter 24 of 37