Share this page
abu, daya jasu sallar suka idar, yana kallonta taja jiki takoma kan gado, ko hijab bata cire ba. Yanzun ma hannun shi da yake kan kafadarta take turewa tana shagwabe mishi fuska "Me zanyi?" Ta tambaya muryarta cike da bacci, har lokacin idanuwanta a rufe suke, murmushi yayi har hakoranshi suka fito. Gyara zaman shi yayi gefenta yana saka hannuwan shi duka biyun ya dagota hadi da girgizata "Ki tashi Waheedah.... Hamma zai kasheni inya dawo bamu shirya ba, idan mukaje gida sai kiyi baccin..." A hankali take bude idanuwan ta, tanajin kanta kamar an dora buhun siminti, duk wata gaba da take jikinta ciwo take mata, bata taba gajiya irin wadda tai daga satin bikin zuwa wayewar garin ranar ba. Kallon fuskar AbdulKadir da yake mata dariya tayi, tana tunanin inda take kafin komai ya dawo mata. "Hamma..." Ta kira tanajin kunyar duniya ta tattaru ta rufe ta. Dariya yayi "Ki tashi ki watsa ruwa mu tafi..." Kai ta daga mishi tana bin hannuwan shi da suke rike da ita da kallo, hakan yasa AbdulKadir sakinta, ta dayan bangaren ta ja jikinta ta sauka, kanta a kasa ta wuce shi zuwa bandakin tana rufo kofar, wani numfashi da batasan tana rike dashi ba ta sauke. Ruwa ta watsa tana mayar da gabaki daya kayan da ta shiga dasu, tukunna ta fito. AbdulKadir na zaune inda tabarshi yana danna wayar shi, sai lokacin ta tuno da tata wayar tana gida cikin jaka. Hakan kuma na tuna mata da su Anty Talatu da suka bari da yanda zata fara hada ido dasu yanzun. "Hamma..." Ta kira cikin tashin hankali, dago da idanuwan shi yayi yana kankance su akanta "Ina zamuje?" Ta bukata, da mamaki yake kallonta "Gida..." Ya amsa a taqaice, kai ta girgiza mishi, tana sashi daga mata gira cikin alamar tambaya "Su Anty na nan, ban san me zance musu ba..." Bude baki yai da niyyar amsata, kwankwasa kofar da akayi ya hanashi. "Wallahi badan Waheedah ba da tuni mun tafi...yanzun ma bazan sake magana ba..." Yassar ya fadi daga wajen dakin, da alamun ranshi a bace yake, mikewa yayi yana daukar hijab din Waheedah ya karasa inda take tsaye, juya hijab din yayi zuwa dai-dai tukunna ya juyo da wajen kan yana saka mata, damtsen hannunta daya ya rike yana jinshi kamar kara a cikin hannun shi, gyara mata zaman hijab din yayi sosai, ya juya ya koma ya dauko dankwalin kayan nata, hannunta ya sake kamowa ya saka a ciki, kallon shi kawai takeyi "Sadauki su Anty na nan.... Dan Allah... Bansan me zance musu ba" Waheedah take fadi muryarta a karye, ko inda take AbdulKadir bai kalla ba, wayarshi da wallet ya dauka ya saka a aljihu, yazo ta gabanta ya wuce, saida ya zira takalman shi tukunna ya dauko mata nata yana ajiyewa a gabanta. "Hamma..." Idanuwanshi ya kankance mata "Ki zabi abinda zaki cemun guda daya..." Da sauri ta amsa shi "Sadauki..." Kai ya jinjina mata yana dorawa da "Kisa takalmanki, idan Hamma yaimun fada raina zai baci, naki zai baci kema saboda na shirya tun dazun ke kike batamun lokaci" Takalman ta saka, idanuwanta na cika da hawayen da batasan dalilinsu ba. Gaba AbdulKadir yayi tana bin bayanshi suka fita daga dakin, tsaye tayi ya kulle kofar, kanta a kasa yake, koda ya kama hannunta binshi kawai takeyi, inda duk ya cire kafarshi nan takw saka tata, daya tsaya bada mukulli ma a reception, tsayawa tayi batare data amsa gaisuwar da matar tayi mata ba, asalima ko dagowa batai ba balle taga kalarta, tana tunanin da idanuwan da zata kalli su Anty Talatu ne. Har bakin motar Yassar suka karasa, yana tsaye daga waje, addu'a Waheedah takeyi kar Yassar yai mata magana, shima ganin kanta a kasa yasa shi kin ce mara komai, Allah ya hadata da wani irin miji da sukai hannun riga shida kunya. Shi kanshi Yassar din tayata jin kunyar abinda AbdulKadir yakeyi. Wata irin harara Yassar ya watsa ma AbdulKadir yana f "Wallahi da ka kara minti biyar da saidai ku nemi abin hawa..." Dakuna fuska AbdulKadir yayi yana amsawa da "Na tashi lafiya Hamma, thank you, fatan kaima ka tashi lafiya?" Wata hararar Yassar ya watsa mishi dan yasan gatse yai mishi, zagayawa yayi ya bude motar ya shiga. Saida AbdulKadir ya bude ma Waheedah bayan motar ta shiga, ya mayar da murfin ya rufe sannan ya shiga gaban, Yassar yaja motar yana fita daga hotel din zuwa hanyar da yake tunanin zata mayar dashi barikin su AbdulKadir din, yana addu'a ya gane hanyar ba sai yayi magana da AbdulKadir ba. * Bayan AbdulKadir take bi har cikin gidan, kanta a kasa cike da wata irin kunya da bata taba tsintar kanta ciki ba. Jikinta taji ya soma bari jin AbdulKadir yayi Sallama, kuma Anty Talatu ta amsa mishi muryata dauke da wani irin yanayi "Anty. Sannunku da gida... Ya gajiya?" Kallon shi Anty Talatu takeyi, murmushin takaici mai sauti na kwace mata, ba tun yanzun tasan AbdulKadir bashida kunya ba, tun randa tazo gidan akace ya mayar da ita, tai mishi fada kan ya zagi wani saurayi daya kusan bigewa ya gaya mata maganganu, tace ya tsaya ya sauketa, ya kuma yi parking gefe yana jira ta fita. Amman jiya ne ta tabbatar da gaske bashida kunya. Yanzun ma yanda yake hada idanuwa da ita ya kara tabbatar mata da hakan "Waheedah ina son magana dake kafin mu wuce" Anty Talatu ta fadi, tana saka Waheedah dago da manyan idanuwanta tana kallonta cike da tsoro, tukunna ta kalli AbdulKadir da yake gefenta, dan daga mata kafadu yayi, yana kallon Anty Talatu data juya "Anty gaisheki fa nayi, baki amsani ba kika wuce" AbdulKadir yace cike da takaici, dan ba kullum yake bata gaisuwar shi ba, yau ma dan yana cikin nishadi ne shisa ya gaisheta, amman ta wuce bata amsa ba kamar ya mata wani abu. Ko juyowa batai ba, hakan yasa shi kankance idanuwan shi, yanajin yanda ranshi yake gab da baci. Cikin sanyin jiki Waheedah ta wuce ta bayan AbdulKadir zuwa dakin da Anty ta shiga. A tsaye ta sameta, daga bakin kofa ta tsaya tana jin idanuwanta sun fara tara hawaye, batason fada, ko kadan batason tayima kowa laifi a rayuwarta. Hankalinta gabaki daya a tashe yake. "Waheedah idan kika biyema soyayyar namiji zaki sha wahala wallahi, bance karki bi mijinki ba, amman ba'a kowanne yanayi ba, yanzun ke mutuncinki ne ace darenki na farko a gidan miji kin dauki kafa kin bishi hotel?" Kai Waheedah ta girgiza, hawayen da suke cike da idanuwanta suna zubowa, ci gaba da magana Anty zatayi aka turo kofar. Idanuwan shi AbdulKadir ya sauke kan Anty, ranshi ya gama baci. "Ki fadamun Hadith daya ko aya data ce kar matata tabini hotel..." Ya karasa maganar yana cigaba da kallonta, shisa bayason mutane, saboda irin wannan ra'ayoyin nasu ya sha banban da nashi, idan kuma ana maganar ranshi zai iya baci, baisan matsalar hausawan mu da hotel ba, yawancin su suna tunanin babu wanda yake ziyartar wajen sai mazinata, basa tuna cewa akwai matafiya da halin kwana ya kama a hanya suka tsaya, akwai wanda aiki ko kasuwancin yan kwanaki yakai shi, bashida zabin daya wuce kama hotel din dan ya zame mishi masauki. Ranshi na kara baci da amfi ma duk macen da za'a gani a hotel kallon marar tarbiyya, musamman idan aka gansu tare da namijin da zai iya zamowa Yayanta ne tafiyar ta kamasu, dakunan da zasu kwana mabanbanta ne, ko kuma mijinta ne, kowa zaka gani a hotel yana da dalilin shi na zuwa wajen, ba kuma duka dalilan bane suke zama na banza. "Kar kaimun rashin kunya AbdulKadir..." Anty Talatu tayi maganar ranta a bace "Saboda na nemi ki bani hujja kan dalilin da yasa rashin mutuncine kwanan da mukai a hotel?" Mikewa Anty Talatu tayi daga zaman da take bakin gadon tana fadin "Allah ya shirya ya bada zaman lafiya" AbdulKadir din ya amsata da "Amin..." Yana matsa mata ta rabashi dan ta wuce, kafin ta fita ya dora da "Mungode Allah ya saka da alkhairi ya mayar daku gida lafiya" Bata amsa shiba ta fice daga dakin, ya mayar da kofar ya kulle a bayanta, yana mayar da hankalin shi kan Waheedah da take faman hawaye. Kuka baya damun shi sam, yasha zane Zahra ya zauna ya jirata ta gama kukan da zatayi suyi magana, kuka marar dalili ne bayaso, amman wannan da Waheedah takeyi har kasan zuciyarshi yake jinshi. "Banaso Waheedah, banason kuka marar dalili" Kallon shi tayi, wasu hawayen na kara zubo mata, tsoro takeji kar Anty Talatu ta fadama Mami ta mata wani abu, Mami zatai mata fada tasani "Karta fadama Mami" Dariya AbdulKadir yayi yana girgiza mata kai "Baki da hankali ke kam..." Ya karasa maganar yana kama hannun kofar "Bari inyi sallama dasu Hamma..." Kai ta daga mishi tana sa hannu ta goge fuskarta, yana fita ta karasa gefen gadon ta zauna. Har lokacin hankalinta yaki kwanciya, ko kadan batason tashin hankali. ** PRESENT DAY Kwankwasa kofar da taji anyi ya katse mata tunanin da take, sallama Hauwa tayi da Waheedah ta amsa mata cikin sanyin murya, turo kofar tayi tana fadin "Na dauka kinyi bacci, Yassar nason magana dake daman" Kai Waheedah ta girgiza mata, tana dafa gado ta mike, juyawa Hauwa tayi, tabi bayanta, a bakin kofar ta samu Yassar din a tsaye "Waheedah yanzun Anty ta kirani, tace za'a mayar dake asibiti ashe..." Numfashi Waheedah ta sauke "Dan Allah Hamma kubarni da asibitin nan, hutawa suke so inyi kuma zan huta..." Kallonta Yassar yake, a yanayin da yake ganinta bayaso ya takura mata, amman kuma lafiyarta nada muhimmanci "Da gaske zan huta... Allah kuwa, idan naji banajin dadi sosai saimu koma" Tayi maganar cikin son tabbatar mishi, a hankali ya jinjina mata kai "Dan Allah koya kikeji kiyi magana mu koma, nasan ba shiri kuke da AbdulKadir a yanzun ba, amman zai kasheni idan wani abu ya sameki karkashin kulawata" Murmushin karfin hali tayi tana rasa abinda zatace mishi. "Allah ya sauqaqa" Yassar yai maganar cikin sanyin murya, saida ta amsa shi da "Amin..." Tukunna ta juya ta shiga dakin tana turo kofar, data bude da sauri tana fadin "Hamma wayata... Tana can, sai kayan su Ikram..." Kai Yassar ya jinjina mata, ta sake mayar da kofar ta rufe. Shikam hanyar da zata fita dashi daga gidan ya nufa yana ce ma Hauwa "Bari in dawo ba dadewa zanyi ba..." Cike da damuwa take kallon shi "Bakaci abinci ba har yanzun..." Murmushi yai mata "Zanci da na dawo... Kici ke dai..." Kai ta girgiza mishi "Nidai zan jiraka... Karka dade kaji?" Numfashi ya sauke yana jinjina mata kai ya wuce, har wajen motar shi ya karasa ya shiga yana nufar gidan AbdulKadir. * A harabar gidan yayi parking din motar shi, batare daya fito daga ciki ba ya kira wayar AbdulKadir din ya fada mishi yana cikin gidan. Ko mintina biyar ba aiba saiga AbdulKadir din ya fito. Da murmushi a fuskar shi yake takawa zuwa wajen motar dan a zaton shi Waheedah Yassar ya dawo mishi da ita, yasani daman, a jikin shi yakeji Waheedah ba zata iya kwana wani waje yana gari ba, bata taba ba, ba kuma zata fara ba yau. Yana karasawa wajen motar ya kama murfin bayan yana kikiniyar budewa, kasancewar gilasan baqaqe ne baka ganin waye a ciki daga waje. Qasa da gilashin gefen shi Yassar yayi, ya ziro kai yana fadin "Ka maida hankali ka karyamun murfin mota AbdulKadir..." Sakin kofar yayi yana matsowa saitin Yassar din "Tana ina?" Cike da rashin fahimta Yassar yace "Ita wa?" Dakuna mishi fuska AbdulKadir yayi, yanayin da yasa Yassar din jan karamin tsaki "Malam ka wuce ka dauko mun kayanta dana yara, sai wayarta tace tana nan in hado mata dasu" Lokaci daya murnar da AbdulKadir din yakeyi ta bace, wani tuquqin bacin rai na maye gurbinta, ga yunwar dake cinshi na kara taimakawa wajen rura mishi bacin ran. "Kace mata tazo ta diba da kanta" Bude motar Yassar yayi ya fito, shima nashi ran yake ji a bace "Kalleni..." Ya fadi yana dorawa da "Ka kalleni dan ubanka. Nayi maka kama da abokin wasan ka? Ko na maka kama da dan aike... Karka kara batamun rai fiye da yanda yake a bace..." Juyawa AbdulKadir yayi yana nufar hanyar gidan, Yassar bazai kara bata mishi rai ba, Waheedah ta gama hada mishi zafi. Bin bayan shi Yassar din yayi yana tsayawa cikin falon, dai-dai fitowar Nuriyya da wandone a jikinta ko cinyoyinta bai rufe ba tana fadin "Masoyi..." Da sauri tayi baya babu shiri ganin Yassar din, AbdulKadir ko inda take ma bai kalla ba ya wuce hanyar da zata kaishi dakin baccin Waheedah din. Batama yi tunanin sako abaya ta dawo ta gaishe da Yassar din ba, tasan ya tsaneta kamar sauran yan uwan AbdulKadir din, gara kannen shi suna gaishe da ita ciki-ciki. Amman ko wacce irin gaisuwa taima Yassar din yakan amsata ne da 'Sannunki' Ya mayar da girar kasa da ta sama ya hade. Yanzun dinma ganinta ya kara bata mishi rai, ko lokacin da take kawance da Waheedah batai mishi ba sam, yanzun tsanar dayai mata ta kara linkuwa, yakan so ko yayane ya dinga mata fara'a saboda AbdulKadir din, amman ya kasa. Yakai mintina goma a tsaye a wajen kafin AbdulKadir din ya fito da wata yar jaka da kaya a ciki, kan kujera ya ajiye yana dora mishi wayar Waheedah da charger a kai ya juya batare da yace komai ba. Shima dauka yai ya fice daga gidan. Bangaren Nuriyya inda yabar tashi wayar ya nufa yana daukar ta ya rike tukunna ya samy waje ya zauna kan kujera, kirga mintunan da yake tunanin zasu kai Yassar din gida, gara yakai ma Waheedah wayar, saiya kirata ko zai samu ta fada mishi dalilin da yasa take son tarwatsa mishi zaman lafiya haka. Nuriyya ce ta fito daga bedroom dinta, dan taji motsin shi, tasan Yassar ya tafi. Kan kujerar ta karasa ta zauna tana jingina jikinta dashi, hannun shi ya zagaya yana rikota, sauqi yake nema koya yake, so yake ta dauke mishi hankali daga tunanin da yake dan bayaso. Gefen fuskarta ya sumbata, ta sake narke mishi "Jikina namun ciwo..." Muryar shi can kasan makoshi yace "Me kikayi?" Sake kwanciya tayi a jikinshi, hanyar da zata gujema yin girki take nema "Me zamu ci da dare? Ko musha Tea?" Tun kafin ta karasa kalmar Tea din yake girgiza mata kai, ana zaune lafiya bazai sha shayi ya kwanta ba, yunwar da yakeji ma tafi karfin shayi. "Wani abu dai banda shayi" Shagwabe fuska tayi tana sauke muryarta cike da kissa "Kamar me? Ka zabi wani abu mai sauqi" Dakuna fuska AbdulKadir yayi, yanayin na mishi baqunta, shifa sam bai saba fadar abinda zaici ba, dafawa Waheedah takeyi ta kawo mishi "Ki dafa komai ma, ni ban saba zabar abincin ba, kome kika bani zanci, amman banda shayi" Numfashi taja tana saukewa "Ko mu fita muci a waje?" Kallonta yayi yana kankance mata idanuwan shi "Saboda me?" Ya bukata yana jiran jin dalilin da zaisa su fita waje suci abinci. Haka kawai tunani ya watsa shi washegarin auren su da Waheedah. * "Me zakici in siyo mana?" Ya bukata bayan tafiyar su Anty, yana kallon yanda take dakuna mishi fuska tana tambayar shi "Muna da abinci a kitchen, me yasa zaka siyo?" Kafadu yadan daga mata "Sai an dafa..." Ya amsa a taqaice "Nasani, amman akwai" Kai ya girgiza "Amarya bata girki" Murmushi tai mishi tana mikewa ta nufi kitchen din, binta yayi. Tare sukaita bude-buden abubuwa a kitchen din harta gama dauko wanda take bukata, da wani gari daya gani kamar yaji, sai dai yafi yaji ja yaga ta jiqa a ruwa, sai tumatir na leda, macaroni tayi musu jalof da sauran kajin da aka kawo musu da su Anty basu cinye ba suka saka mata a fridge. Sosai yaci abincin dan ya mishi dadi. * "Masoyi..." Nuriyya ta fadi tana riko hannun shi, ganin yayi shiru kamar yana tunani "Ki soya mana ko dankali saiki mana sauce" Ya fadi da wani nisantaccen yanayi a muryarshi, ranta taji ya baci saboda zaman fere dankalin da zatayi "Banda dankali fa, sai dai in siyowa zakayi" Kai ya girgiza mata, bayajin fita sam "Ki duba kitchen din Wahee... Tana dashi" Mikewa tayi tana nufar bangaren Waheedah din da tunanin yaushe zata dawo gidan. Dan ita ba zata iya wannan bautar ba sam-sam, rabonta da wani girki harta manta. Gashi ta kula da AbdulKadir din nada mugun cin abinci, kuma tana da tabbacin Waheedah ta lalata shi haka. Kwando ta samu ta kwashi dankalin da take tunanin zai ishe su ta koma nata bangaren. Ta wuce AbdulKadir zaune inda ta same shi, wayar Waheedah ya kira a kashe, hakan yasa shi ajiye tashi yana jin ranshi a jagule. "Masoyi ba zaka zo ka tayani ba? Da yawa fa dankalin..." Nuriyya ta fadi daga bakin kofar kitchen din kamar zata fashe da kuka, gashi bata iya saka peeler ba, dole sai dai da wuqa. "Ban iya ferewa ba nikam" Yai maganar da iya gaskiyar shi, yakan dami Waheedah da zai tayata aiki in tanayi, amman banda Maggi bata bashi komai, sau daya ta bashi yankan albasa, yajin daya cika mishi ido yasa har ya yanke hannu, bata kara ba, da yayi magana zatace ya rufa mata asiri, kafin azo a kamata taba soja aiki ya yanke hannu. Sai dai yakan miqo mata su cokali ko kwano. Jin Nuriyya bata kara mishi magana ba yasa shi zamewa ya kwanta kan kujerar, ya dora hannun shi saman goshin shi yana lumshe idanuwan shi. Baifi minti biyar ba ya bude idanuwan shi, sai dai me, yanda tunanin Waheedah ya addabeshi da ya rufe idanuwan hakan ma daya bude su. Tashi zaune yayi, tunani bakon abune a tare dashi, babu abinda ya isa ya saka shi tunani haka, Waheedah tasani, bazai iya kwana baisan matsayar matsalarsu ba. Wayar shi ya dauka ya wuce ya dauko mukullin mota tukunna ya dawo yana fadin "Nuriyya bari in dubo Waheedah, zanyi sallah a hanya..." Kai ta daga mishi daya saka shi dakuna mata fuska, babu shiri tace "Tam a dawo lafiya, kayi mata sannu" Nashi kan ya jinjina mata, ita bata isa tai mishi ba, tana kuma lura da Waheedah na amsa shi da kai baya ce mata komai, amman ranar farko data kwatanta magana yai mata, data gwada yi mishi shiru ma saida ya sauke mata masifarshi har kuka tayi ranar. Akwai abubuwa da yawa da take lura Waheedah kawai take yinsu yana dauka, hakan kuma na mata quna har kasan ranta. Tana jin takun tafiyar shi har ya bace mata. * Kamar yanda ya fada, a hanys ya tsaya yai sallar magriba, sannan ya karasa gidan Yassar. Ya gwada kiran wayar Waheedah bai samu ba, hakan yasa shi shiga gidan kanshi tsaye hadi dayin sallama. Hauwa ta amsa mishi suna gaisawa, AbdulKadir din ya dora da "Waheedah fa?" Dan jim tayi na minti daya, batasan me yake faruwa ba, ba kuma tason shiga koma menene, idan akwai abinda zama da Yassar ya koya mata bai wuce kin shiga abinda babu ruwanta a ciki ba. Dan haka ta nuna mishi hanyar dakin da Waheedah din take ciki, tana ci gaba da hidimar da takeyi ta fito musu da abincin dare. Sauri AbdulKadir yakeyi yana godema Allah da baiga Yassar ba, dan zai iya cewa bazai ga Waheedah din ba. Dakin ya tura ko sallama baiyi ba yana mayarwa ya rufe. Tsaye yaganta ta goya Ikram tana jijjigata, kallon mamaki take mishi, dan ta dauka ma Fajr ne ya shigo mata daki babu sallama haka, juyowa tayi tai mishi fada taga AbdulKadir a tsaye. Lumshe idanuwanta tayi ta bude su akan shi tana jiran soyayyar shi da takanji ta taso mata duk lokacin da zai bayyana a gabanta, amman shiru, babu abinda takeji banda son kara yin nisa dashi. "Waheedah..." Ya kira muryar shi na fitowa a karye da ganin nisan da tayi mishi cikin idanuwanta duk da tana tsaye a gaban shi "Ba zan iya bacci bansan me kike so dani ba..." Murmushi tayi, kallon ta yake, da gaske murmushi tayi, shi kam ko kadan baiga abin nishadi a yanayin da suke ciki ba "Da wanne yare kake so in fada maka? Na maka da Hausa, in maka da turanci ko da larabci? Su kadai nasan kana fahimta... Sakina nake so kayi Sadauki, ka fadamun idan akwai abu mai wahala cikin gane hakan" Tabbas ranar tazo mishi da abubuwa naban mamaki, Waheedah yake kallo yana son ganin ko da gaske matar shi ce a gabanshi, da gaske Waheedahr shi ce da ko murya bata taba daga mishi ba, balle ta tsaya idanuwanta cikin nashi tana gaya mishi magana irin hakan. Ji yake kamar an watsa mishi ruwan sanyi an kunna mishi AC. Jikin shi ba la'asar kawai yai ba, isha'i yayi makararriya. "Waheedah?" Ya iya furtawa yana kallonta, ganin taki sauke idanuwanta, kuma bata da alamar amsa shi yasaka shi fadin "Nine fa, Waheedah ni ne?" Kai ta jinjina "Naganka ai... Kaga na nuna alamar bakai bane?" Wannan karin dariyar takaici mai sauti ta kubce mishi "Yaushe kika koyi rashin kunya?" Maganar da yai zaton cikin kanshi yayi ta fito fili, sautin muryar shi na dukan kunnen shi da wani yanayi. Kafadu tadan daga mishi "Zama da madaukin kanwa..." Waheedah ta fadi tana zama gefen gadon "Me kike nufi?" Cewar AbdulKadir cikin bacin rai, kallon shi tayi wannan karin tana ganin yanda yake gab da birkice mata. "Karka tasar mun da yarinya, Sadauki bazan iya hayaniya ba, dan Allah inba takarda zaka bani ba ka fita...sanda ka shirya bani kasan inda nake" Kai kawai ya iya jinjinawa, yana juyawa ya bude kofar ya fice daga dakin, a falo ya samu Yassar da alama lokacin ya shigo "AbdulKadir..." Ya kira cike da mamaki, ko inda yake AbdulKadir bai kalla ba, hanyar da zata fitar dashi daga dakin kawai yake nema, saboda yanajin yanda wani agogo yake harbawa cikin kanshi yana mishi kashedin saura kiris ya cika, bayaso lokacin da koma meye ya dibar mishi ya cika a cikin mutane, kar a samu matsala. Rabon da ranshi ya baci irin haka harya manta, dan har wani duhu-duhu yake gani. Ganin hakan yasa Yassar kara kiran shi "AbdulKadir..." Gani yai ya fice daga dakin, babu shiri Yassar yabi bayanshi, ko takalma bai tsaya ya saka ba. Kafadar shi ya dafa yana juyo dashi "Magana nake maka" Ya fadi yana yawata idanuwan shi kan fuskar AbdulKadir din, bakuma yason abinda yake gani shimfide akai. "A haka zaka shiga mota kai tuqi? Saboda baka da hankali" Numfashi AbdulKadir ya sauke yana jan hancin shi da yake ji kamar yaji-yaji a ciki, muryar shi can kasan makoshi yace "Me yasa igiyar aure ta shiga tsakanina da Waheedah? Hamma me yasa?" Runtsa idanuwa Yassar yayi, cikin alamar rarrashi ya ce "AbdulKadir..." Kai AbdulKadir din ya girgiza mishi yana jin kaman zai kama da wuta da yanda jikin shi ya dauki dumi saboda bacin rai. "Na mareta da safe, bansan ya akai ba Hamma, wallahi ban sani ba, amman cikin idona ta kalla tai mun rashin kunya... Yanzun ta kara... Bansan meya faru ba, bansan me nai mata haka ba....amman a karo na farko inajin igiyar auren da ta hadamu batai mun adalci ba. Da ta bani damar da zan daketa yanda raina yake so da ta dawo hayyacin ta ta fadamun me nai mata sai in san yanda zanyi in gyara..." Dafe kai Yassar yayi, baisan abinda ya kamata yayi ba, a yini daya yana ganin AbdulKadir din na shirin susucewa, baisan me zai faru in aka dauki kwanaki a haka ba, tsintar kanshi yayi da musu addu'ar samun maslaha su duka biyun, dan sun saka shi a tsakiya ta yanda bazai iya zaben bangare ba. Motar shi AbdulKadir ya bude tukunna ya sake juyowa "Ka fada mata, wallahi bata isa ba...wallahi bata isa ta birkitamun lissafi ina zaune lafiya ba...idan rigima take so Hamma ka fada mata AbdulKadir ne...taga wajen kwanana shisa ta rainani haka..." Da idanuwa yake bin AbdulKadir din da kallo, murmushin da baisan ta inda ya taho ba yana shirin kwace mishi. AbdulKadir na kiran Waheedah bata isa ta birkita mishi tunani ba, amman hauka yake tuburan, tsaye yayi saida yaga yanda AbdulKadir din ya birka mota kamar zai takashi tukunna ya matsa da sauri. Numfashi Yassar ya sauke, yana hango AbdulKadir din ya ziro kai ta window din motar ya kalli maigadin da bai bude mishi kofa da wuri ba, da sauri Yassar ya taka ya karasa kafin ya jibgi yaron mutane a banza. "Dan kanwar uwarka bakaji karar mota bane halan?" AbdulKadir din ya tambaya yana kallon yaron da yake a tsorace, da hannu Yassar yai mishi alamar ya matsa, da kanshi ya bude ma AbdulKadir din mota yana fadin "Allah ya tsare Samarin Hajja..." Tsaki AbdulKadir yaja "Idan na zageka a fili yanzun zakace na maka rashin kunya" Wata irin dariya ta kubce ma Yassar din, har AbdulKadir din ya figi mota, Yassar na tsaye ya rike gate din yana kwasar dariya, dakyar ya samu ya shiga cikin gida, har lokacin da murmushi a fuskar shi, a rayuwar shi bai taba hango abinda zai saka AbdulKadir susucewa a yini daya haka ba, har Waheedah din da kanta kuwa...! #AnaTare #TeamAbdulKadir #TeamWaheedahFacebook: Lubna Sufyan IG: SufyanLubna Email: Calmlubna@gmail.com Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43 *ABDDULKADIR* *LubnaSufyan* 19 TAQABALALLAHU MINNA WA MINKUM Tana kitchen din har aka kira sallar Magriba, bata mike ba saida ta karasa yanka dankalin tukunna, wanke shi tayi ta tace a kwando, tana ganin kamar yankan yayi girma, amman ta riga ta gaji, ko bata gaji bama ba zata sake tsayawa yankawa ba, ranta a bace take jin shi. Gas ta kunna ta dora kasko ta zuba mai a ciki, tunanin ta barbadama dankalin gishiri bai zo mata ba, man ma ko dumi baiyi ba, balle yayi zafi, ta dibi rabin dankalin ta zuba a ciki tukunna ta fice daga kitchen din. Dakinta ta wuce tana shigewa bandaki ta dauro alwala ta fito, sallah ta gabatar a nutse, bata tsaya addu'a ba ta tashi ta nufi kitchen din dan ganin halin da dankalin ta yake ciki. Danqare ta same shi, kasancewar man da yasha yayi luntsum, haka ta cigaba da cakuda shi, duk ya kakkarye ya dame cikin man, yana kara jagula mata lissafi gabaki daya. Batajin a cikin abubuwan da

Chapter 19 of 37