bayan shi, tana kallo ya tura kofar yana shiga da
cikin gidan da sallama.
Amsa shi Waheedah tayi tana mikewa, ta sake kaya zuwa wata atamfa da tafi dazun yin kyau,
ga wani irin kwarjini da yaga ta mishi, gidan gabaki daya sai kamshin turarukanta yakeyi da yai
mishi dadi.
"Sannu da zuwa..."
Ta fadi, tana ware idanuwanta ganin Nuriyya, harara ta watsa mata
"Sannu Nuriyya"
Ta fadi, dan rabon da ta sakata a idanuwanta harta manta, duk da suna chatting kuma suyi
waya. Amman batace mata ta dawo ba, tunda ko shekaranjiya ta kirata sun gaisa. Ita kuwa
Nuriyya wani irin ras kirjinta ya doka jin kalaman Waheedah din, da kuma harar datai mata.
Maganar tata nasa AbdulKadir yaji nashi kirjin ya doka, cikin wani irin tashin hankali ya taka
yana kama hannun Waheedah ya soma janta, juyawa tayi tace ma Nuriyya
"Ina zuwa..."
Kafin ta mayar da hankalinta kan AbdulKadir din cike da mamaki. Har bedroom dinsu, sannan
ya saki hannunta tana kallon zufar da goshin shi yakeyi.
"Waheedah..."
Ya kira yana jin sauran kalaman sun makale mishi, kallon shi takeyi da irin zufar da yakeyi, kafin
wani abu ya sara mata a tsakiyar kai. Lokacin da tayi ma Nuriyya magana taga ta matsa tana
boyewa bayan AbdulKadir din har jikinta na taba nashi, batasan me yasa sai yanzun
kwakwalwarta ta zabi tayi processing wannan yanayin ba. Numfashi take ja a hankali tana fitar
dashi, a nutse takeyin hakan tana son iskar ta isa inda ya kamata. Kafin ta iya kallon
AbdulKadir, muryarta na dukan dodon kunnenta da fadin
"Nuriyya..."
Tayi shiru tana sake jan wani numfashin ta tabbatar da kirjinta ba zai bude zuciyarta ta fito ba,
tukunna taci gaba
"Nuriyya ka aura?!"
Kasa magana yayi, zufa yakeji tana tsatsafo mishi a duk wata kafa da zai iyaji, abin har mamaki
yake bashi, tunda zazzabine ruf yaji ya rufe shi duk da zufar da yakeyi.
"Ma shaa Allah"
Waheedah ta fadi tana sake kallon shi da fadin
"Kabarta ita kadai"
Ya bude bakin shi yafi sau biyar yana mayarwa ya rufe kafin ya iya furta
"Waheedah..."
Dariya tayi da tasa shi sake kallonta
"Sadauki... Kaje..."
Badan yana son ya tafin ba, sai dan yana so ya fita daga dakin ko zai ji iska na ratsa shi. Fita
yayi yana samun Nuriyya a tsaye bakin kofa kamar mai jiran kyat ta bude tayi ta kanta. Da
gasken a tsorace take, dan tana da tabbacin AbdulKadir din ya janye Waheedah ne dan karta
far mata.
"Muje.."
Ya fadi lokacin daya karasa yana kama akwatinta ya dauki sauran ledojin da baisan ya sake su
ba, suka wuce har bangaren da zata iya kira nata yanzun. A falo ya ajiye akwatin ya nufi
bedroom din tabi bayan shi, ledar ya ajiye yana shiga bandaki ya dauro alwala, itama yace taje
tayi. Sallah yaja su sukayi ta godiya ga Allah, kafin AbdulKadir din ya mike ya dauko ledojin
yana cire na Waheedah ya fice daga dakin ya nufi bagarenta, kwankwasawa yayi yana turawa.
A tsaye ya sameta tana dauko kayan bacci
"Sadauki..."
Ta fadi, ya karasa
"Apple na siyo miki"
Hannu ta mika ta karbi ledar
"Aikam ka kyauta, dan banajin cin komai"
Space din dake tsakanin su AbdulKadir ya hade yana zagaya hannuwan shi ya rungumeta a
jikin shi. Zuwa yanzun ya kasa gane ko da gaske lafiyarta kalau ba, yasan Waheedahr shi
daban take da duk wasu mata daya taba cin karo dasu. A kaf duniyar shi kuma Hajja ce kawai
macen da Waheedah bataiwa nisa ba, duk da haka yanajin kamar ya kamata ta nuna mishi
ranta ya baci, ko yaga kishi a idanuwanta, amman ya kasa ganin komai, yana kuma jin kamar
tana boye mishi asalin abinda takeji ne.
Sosai ya riketa a jikin shi
"Allah ya bani ikon yi muku adalci"
Ya furta a hankali yana lumshe idanuwan shi, badan zuciyar shi bata dokawa Nuriyya ba, sai
dan yanajin inda Waheedah take babu wanda ya taba hangowa balle harya zauna. Ita din
daban ce a rayuwar shi. Hannuwanta Waheedah ta zagaya ta bayanshi tana sake shigewa jikin
shi, ta lumshe idanuwanta da yanda takejin zuciyarta kamar da bulallukan tsokoki aka jerata,
yanzun kuma rugujewa take ta ko ina, kurar ce take saka jikinta daukar wani irin dumi. A hankali
ta zame jikinta daga nashi tana sauke idanuwanta cikin nashi, rankwafowa yayi ya sumbace ta.
"Sai da safe"
Ya fadi yana juyawa, bata iya ce mishi komai ba, harya fice daga dakin yana komawa ya samu
Nuriyya da tunda ya fita takejin kamar ta bi bayan shi ya dawo saboda wani irin azababben kishi
daya turnuqeta, gani tayi ya dade, zuciyarta har tafasa takeyi, kwana daya take dashi, yace
mata gobe zai wuce, Waheedah ba zata bar mata shi ya dawo ba, zuwa yanzun kishi ya maye
gurbin duk wani tsoro data shigo dashi gidan. Murmushi tayi tana ganin ya shigo, jikinta ya mutu
ganin bai mayar mata da murmushin ba.
Karasawa yayi ya zauna gefenta yana kallonta, fuskar shi babu alamar wasa yace
"Bana son tashin hankali, bana son rigima badan ban iya ba, bansan yanda zan daina ba idan
na fara. Nasan halin matata tun kafin in aureta, nasan abinda Waheedah zatayi da wanda ba
zatayi ba tun kafin insan zan aureta, bansan halinki ko daya ba na aureki, idan har naji rigima a
gidana daga wajenki hakan zai fara.
Ko baki girmama Waheedah ba idan baki shiga huruminta ba nasan ba zata taba biyema kome
zakiyi ba. Zaman lafiyarta na da muhimmanci a wajena, idan har zamana dake zaiyi nisa zaki
zauna da ita lafiya..."
Kai Nuriyya ta jinjina mishi a hankali, itama tasan halin Waheedah din, ba saiya jaddada mata
ba, wanda duk yake tare da Waheedah yasan halinta, kuma ita bata shigo gidan dan ta nemi
rigima da ita ba, duk da tanajin idan Waheedah tai mata ba zataki ramawa ba. Zadai tayi karya
in tace idanuwanta basa mata yaji da shirin taruwar hawayen bakin cikin maganganun shi. Wani
irin kishi takeji marar misaltuwa, zuciyarta na dan tsahirta mata da hannunta da AbdulKadir din
ya kama.
*
Waheedah kuwa AbdulKadir na fita daga dakin ledar apple din ta bude ta dauki guda daya tana
shiga bandaki ta wanko ta dawo kan gado ta zauna. Cinye shi tayi batare data gane dandanon
shi ko dalilin da yasa takeci ba, kafin taja kafafuwanta zuwa kan gadon ta kwanta akan bayanta,
jin kirjinta na shirin budewa yasa ta juya tana kwanciya kan gefen hannunta na dama. Wani abu
takeji yana zubar mata, da sauri tasa hannu ta taba fuskarta, amman babu digon hawaye ko
daya, kuka take amman daga ciki.
Ranar ne ya zame musu MAFARIN komai daya kawo su inda suke yanzun, ranar ne kuma
Waheedah taji ta shiga wata duniya da tai nisa da zubar hawaye, duniyar data bata mukullin
waccen data bari tana budewa tana zuba duk wani bacin rai da zai sameta ta rufe har zuwa
yanzun...!
#LubnaSufyan
#TeamAbdulKadir
#TeamWaheedah
#AnaTare
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
25
PRESENT
A rayuwar shi bai taba sanin menene asalin ma'anar kalmar wulakanci ba sai da yaje NDA,
kamar yanda ba zaice ga tun lokacin da yake son saka uniform din sojoji ba. Sai dai shi mutum
ne da idan yasa abu a ranshi, wahala ko makamancin hakan baya hanashi cimma burin shi. Zai
iya rantsewa a yan shekararsu babu wanda ya sha wahalar da yasha a NDA, daga horo zuwa
jibga, akwai lokutta da dama a shekarar shi ta farko da baiyi tunanin zai gama NDA da ran shi
ba. Saboda bai iya tauna magana kafin ya fadeta ba, kuma bai iyayin shiru idan yana tunanin
akan gaskiyar shi yake. Abinda ya ja mishi tsana da kauna daga wajen manyan shi.
Zai iya cewa kwana biyar din da yayi bakomai bane akan irin wahalhalun da ya sha a baya.
Abinda ya bambanta da sauran loluttan shine, bashi yayi laifin da kan shi ba, kuma yanzun da
yake hanyar shi ta zuwa gida zai shiga gidan batare da yaga Waheedah ba, kuma yayi
kwanakin biyar da tunaninta cunkushe a kan shi, ranakun da sukayi mishi wani irin tsayi naban
mamaki. Sabon da yayi da rashin wanka na tsayin lokaci idan aiki ya kaisu wajajen da babu
nutsuwar yin hakan bai hanashi jin wari da karnin jinin da yake ba.
Ko sallama baiyi ba lokacin daya shiga gida, bangaren Nuriyya ya wuce, dan haka ko kadan
bata tsammaci shigowar shi ba. Ta dauka auren Anas shine babban tashin hankalin daya faru
da rayuwarta, sai kwanaki biyar da suka wuce da ta dawo gida tana rasa inda zata saka
rayuwar ta taji sanyi. Da zazzabi ta wuni, ta kuma tashi dashi ganin har an kwana daya
AbdulKadir din bai dawo ba, tayi tunanin zuwa gidansu ta sanar dasu halin da ake ciki, amman
ta rasa samun karfin gwiwar yin hakan. Wanda duk suke dan son ta a gidan su AbdulKadir din
sanadin Waheedah ne daman, tun bayan auren ta da AbdulKadir babu wanda ya sake ko kallon
inda take ballantana magana ta hadasu.
Ta gwada zuwa gidansu AbdulKadir din sau daya, tunda Hajja ta amsa mata gaisuwa bata sake
ce mata komai ba, ta muzanta fiye da tunani ranar, dan har kuka tayi bayan ta fito, bata kuma
sake marmarin komawa ba. Babban tashin hankalin da ta shiga shine tunanin abinda zai biyo
baya da fitowar AbdulKadir din, ta kira lambar Waheedah bata san adadi ba, amman a kashe,
dan tasan inta fada mata zata gayawa yan gidansu AbdulKadir din ayi wani abu a kai.
Hankalinta in yayi dubu a tashe yake da taga kwanaki na tafiya babu alamar AbdulKadir din.
Yaune ta yanke hukuncin ko me su Hajja zasuyi mata zataje ta same su, dan in su basu
kasheta ba, zullumi zai kasheta, ko abinci ta dan samu ta dafa, plate daya haka zata wuni tana
jagalar shi. Tayi zuru-zuru ta fita hayyacin ta, ko hankalinta a kwance yake sai tayi kwana biyu
bata share dakinta ba, shima idan AbdulKadir na gari ne sai tayi shara ta gyara gado. Daya tafi
kuma tana hada sati dakinta baiga tsintsiya ba, yanzun kuwa a kwanaki biyar din nan ko
wanke-wanke batayi ba, falon a hautsine yake da gwangwanin lemuka da robobin ruwa, dan
tunda ta zo gidan shi rabon ta da shan pure water, inya bata kudi ruwan roba take zuwa ta siyo.
Ita kanta rabonta da wanka tun jiya, duniyar take ji ta hade mata waje daya. Yanzun da
AbdulKadir din yake a gabanta, wata irin ajiyar zuciya take saukewa da bata san daga inda take
fitowa ba, ta dauka hawayenta sun gama karewa, sai yanzun da taji idanuwanta sun ciko taf da
hawaye. Bata taba tunanin bakin mutum zai iya kara baki ba sai yau, duk kumburin fuskar shi
bai hana idanuwan shi yin zuru-zuru suna kara shigewa ciki ba. Gashi yayi wani irin
dukun-dukun. Kallon ta kawai AbdulKadir yayi yana wucewa cikin dakin baccin su, kai tsaye
bandaki ya wuce yana cire kayan da yasan sun rigada sun tashi aiki.
Bandakin yake gani yayi mishi kaca-kaca, ga kayan wanki saman injin wanki harda jiqaqqu,
wanka yayi, ya saba jikin shi da sabulu yafi sau biyar amman duk da haka jin shi yake kamar
akwai sauran dauda a jikin shi. Towel ya dauka yana goge jikin shi ya daura shi a kugun shi ya
fito, idan yace ga asalin abinda yakeji karya yake, dan bayajin komai, zafin dukan da yake jikin
shi, ko bacin rai, shiru komai yake mishi. A karo na farko da ko ganin Nuriyya din bai saka shi jin
komai ba. Banda Waheedah babu abinda yake cikin kan shi. Takawa yayi yana fita daga dakin,
a tsaye bakin kofa yaga Nuriyya tana kallon shi
"Masoyi..."
Ta fadi muryarta na rawa, fuskarta da bayanannen tsoro. Idanuwan shi AbdulKadir ya kankance
a kanta yana kara saka tsoro cika zuciyarta
"Dan Allah... Dan Allah kayi hakuri... Kaji... Bazan sake ba.... Dan Allah karka sakeni, kai mun
komai karka sakeni, dan Allah..."
Numfashi nai nauyi AbdulKadir ya sauke, da gaske yake bayajin komai, ciki harda magana da
ita, wucewa yayi da nufin karasawa bangaren Waheedah ya dauki kayan da zai saka. Bin bayan
shi Nuriyya tayi tana kamo hannun shi, gabaki daya shirun shi ya kara rikitata
"Masoyi..."
Tsaye AbdulKadir yayi batare daya juyo ba, hannun shi yake kokarin zamewa daga cikin nata,
ta sake kamashi tana matsawa ta zagaya ta fuskance shi, wasu irin hawaye masu zafi na zubo
mata, tana saka shi tuna yanda ko kadan batasan shi ba, da ta kyale shi, ta nemi waje ta zauna,
da bata tsaya a gaban shi tana mishi kukan da baiga dalilin shi ba. Numfashin ya sake saukewa
"Kaji... Dan Allah kayi hakuri...dan Allah... Wallahi ba zan sake ba"
Nuriyya take fadi kuka mai karfi na kwace mata, hannun shi AbdulKadir ya zare daga cikin nata,
yana rabata ya wuce, jin takun tafiyarta yasa shi juyawa
"Bance kin mun wani abu ba, ban miki magana ba saboda bana son yin magana da kowa, ki
kyaleni Nuriyya, ki kyaleni kafin mu samu matsala..."
AbdulKadir ya karashe maganar yana juyawa ya wuce, da idanuwa Nuriyya tabi shi, zatace
yana da wata irin kula da ko a tunaninta ba tayi zaton zata samu a gidan aure ba, abinda duk ta
nuna tana so yana kokarin yi mata, idan kudi ta tambayeshi yana bata, wani lokacin yana ce
mata bashi da kudin da zai bata ta kashe, akwai hidimar da zaiyi. Sai dai akwai bangaren shi da
takejin bata sani ba, sannan mutum ne shi mai wahalar sha'ani duk da ba sosai zaman su yake
tsayi ba, inya dawo kwana biyune, ita daya, Waheedah daya, amman zatai karya idan tace bata
takura da kwana dayan.
Bata cika tsawaita tunaninta akan abin bane kawai, amman AbdulKadir din da Waheedah kanyi
magana ko da yaushe daban yake da ita wanda take gani. AbdulKadir din Waheedah namiji ne
da ko a littafin hausa batajin akwai irin shi, dan mazan littafin hausa miskilai ne, AbdulKadir din
Waheedah ba haka yake ba, AbdulKadir din Waheedah kan mata abu batare da ta tambaye shi
ba, yana girmamata fiye da yanda take nunawa, dan Nuriyya da idanuwanta taga hakan.
AbdulKadir din Waheedah bashi da wani hali marar kyau, ita shine mutumin da take so,
mutumin da tayi tunanin ta aura.
Sai bayan auren da ta fara cin karo da kashedi a darenta na farko taji zuciyarta ta tsinke, sai
kuma lokutta da dama da zaiyi tunanin tayi mishi abu tayi kokarin bayani ya rufeta da wani irin
fada mai cin rai, kananun abubuwa masu tarin takaici da ba zaka gani daga nesa ba, ko kuma
take tunanin AbdulKadir din Waheedah ba zai tabayi ba, sannan yana surutai cikin baccin shi,
yana firgita sosai, ranar farko da hakan ta faru tsoron shi ta dingaji, musamman da tayi kokarin
taba shi bayan ya farka ya hankadeta yana mata wani irin kashedi da har yau bata sake kokarin
zuwa kusa dashi in yana surutan shi a bacci ba.
AbdulKadir na da matsalolin da take da tabbacin bata gama gani ba. Sai dai batasan ita kadai
yake nunawa ba, ko harda Waheedah. Falonta ta koma ta zauna tana jin wasu hawaye masu
dumi na zarya kan kuncinta. Ita dai yanzun koma me zaiyi indai bazai saketa ba da sauqi.
*
AbdulKadir yana sake kaya, dakin Nuriyya ya koma ya shiga bandaki yana daukar wandon
daya cire ya zaro wayarshi da wallet, wayar da take a kashe ya kunna yana fitowa. Sakonni ne
guda biyar suka shigo tana gama loading, budewa yayi, biyu daga MTN ne, daya bankin shine,
yasan albashi ne, biyu kuma Yassar ne, ya shiga na farkon
'Lafiyar ka kuwa? Wayarka a kashe. Duk da ba ina so ka zo ka dame ta bane, lafiyarka ko?'
Fita yayi yana shiga dayan
'Ka kashe wayarka ne, kayi shiru dan in daga hankalina in goyi bayanka ko AbdulKadir? Yayi
maka kyau'
Murmushi yadan yi duk da nishadi na daya daga cikin karshen abinda yakeji. Wallet din shi ya
saka a aljihun shi. Ya samu waje gefen gadon yana zama, dan dayaga albashin shi bayaso su
kwana baiyi hidindumun da zaiyi dasu ba. Waheedah ya fara turama kudin nata hidimar na wata
kamar yanda ya saba, sannan ya tura ma Nuriyya ma, saiya tura wasu cikin account din shi na
ajiyar kudin tsaron lalura. Ya turana Abba da Hajja. Kati ya tura ma sauran yan gidan kamar
yanda ya saba duk watan duniya, ko yayane yakan tura musu. Wata natsuwa yaji ta daban
daya sauke wannan nauyin.
Wancen watan daya fita ya karo musu kayan abinci, dan shi yake siyan su shinkafa da su taliya,
sai mai. Kananun abubuwa ne yake basu kudin a hannunsu. Haka suke tsarin da Waheedah,
Nuriyya ma data shigo bai canza ba. Duk da ita tana tambayar shi kudi, Waheedah kuma bazai
tuna ranar karshe da ta tambayeshi kudi ba, inya dauka ya bata tana karba, in baibata ba bata
taba tambayarshi. Na Nuriyyar baya damun shi sam, yakan yi mamakin abinda takeyi da kudi
ne kawai wasu lokuttan.
Mikewa yayi ya saka wayar a aljihu, mukullin motar shi yagani ajiye akan drawer din kusa da
gadon ta, ya dauka ya fito, ko inda take bai kalla ba ya taka yana ficewa daga gidan. Motar ya
shiga ya tayar, kan shi tsaye gidan Yassar ya nufa, yana kallon yanda maigadin Yassar din ya
kara sauri wajen bude gate din ganin motar tashi. Saurayine matashi, daga yanayin shi
AbdulKadir din ya fuskanci yaron tsoron shi yakeji. Har cikin harabar gidan ya shiga da motar
yanayin parking, tukunna ya taka yana karasawa cikin gidan. Sallama yake tayi baiji alamar
akwai mutane ba.
Ranar aiki ce yasani, Yassar din zai yiwu yana wajen aiki, matar shi ma tana aiki a asibiti,
bangaren accounting tunda abinda ta karanta kenan. Sai dai yasan Waheedah na nan, dan
haka ya taka zuwa bangaren da ya sameta zuwan karshe da yayi. Kwankwasa dakin yayi
tukunna ya tura hadi dayin sallama, kamshi na dukan hancin shi, duk da bana turarukanta bane
ba, kamshin yai mishi dadi sosai. Wani irin tsalle zuciyar shi tayi naban mamaki ganin
Waheedah a zaune, doguwar rigace ta atamfa a jikinta wani irin dinki da bazaice ga yanda yake
ba, ta saka Ikram cikin jakar goyo ta goyata ta gaba tana tallabe da yarinyar da take bacci.
Kwalliya ce a fuskarta da ba koda yaushe takeyi ba, ta daura dankwalinta ya zauna das a
saman kanta kamar a jiki akayi. Tana zaune gefen gado ta dora kafa daya kan daya, da plate
din soyayyen dankali a gefenta da cokali mai yatsu a ciki, ta dora system din da yake zaton ta
Yassar ce akan wani dan tebir tana kallo. Kafafuwanta yake kallo da suka sha zanen flower tayi
wani irin ja mai duhu, kafin ya yawata da idanuwan shi yana tsayarwa kan hannunta daya dake
tallafe da Ikram da shima yasha kunshin.
Kai ta dago tana kallon AbdulKadir din, zuciyarta na wata irin dokawa da wani sabon tashin
hankalin da ta kwana biyar bataji shi ba, duk wani abu da su Yassar suka san zai dauke mata
hankali ya rage mata tunani shi sukeyi mata. Har system din Hauwa dake cike da fina-finai daga
American zuwa na indiya harda na korea da tafi so ta kawo mata, ta manta lokacin karshe data
huta haka. Ji takeyi kamar tayi wata takwas rabonta da samun bacci mai nutsuwa, wata takwas
rabon da ta zauna ta huta ma rayuwarta, rabon da tayi wani abu don kanta kawai.
Taji dadi da AbdulKadir din bai dameta ba, shisa ta kashe wayarta ta ajiye. Bashi kadai ba, har
yan gidan su batason kowa yayi mata maganar, kuma kowa ya kyaleta. Yanzun ganin
AbdulKadir din na mata barazana da dan kwanciyar hankalin da ta samu, dan jiya da akazo
yiwa Hauwa kunshi itama yi mata akayi, jinta takeyi daban, kamar tabaro waccen Waheedahr a
gidan AbdulKadir, yanzun kuma watace daban da batasan akwaita bama.
"Wahee..."
AbdulKadir ya kira da wani irin sanyin murya mai tattare da mamakin ganin hankalinta a kwance
yake. Dan ganinta yasa komai dawo mishi, dukan da yasha a barikin sojoji da yake nan garin
Kano, yunwar da yake tattare da ita ta kwanaki na rashin samun wadataccen abinci, rashin
bacci, da duk wani rauni da baya iya nunawa a gaban kowa. Itama Waheedah kallon shi takeyi,
tana kallon kumburin dake kasan idanuwan shi da tasan rashin bacci ne, da kuma wasu
kumburin na alamun duka. A karo na farko a rayuwarta da taji halin da yake ciki bai dameta ba,
ballantana harta tambaye shi ya akai ya shiga ciki.
Dauke idanuwanta tayi daga kan shi tana mayar da hankalinta kan kallon da takeyi, tana kai
hannu ta dauki plate din dankalinta tana cigaba daci
"Waheedah..."
AbdulKadir din ya kira wannan karin cike da rashin yarda cewa ita din ce ta nuna mishi halin ko
in kula, ita din ce ya shigo waje ta kalle shi taci gaba da wata hidimar kamar baya nan. Takawa
yayi yana karasawa inda take ya zauna gefenta yana son ta sake ganin shi dinne
"Baki ganni bane?"
Ya tambaya yana kallon fuskarta da babu kowanne irin yanayi akai, dankalin data tauna ta
hadiye tana tsayar da film dinta dan batason komai ya wuce ta.
"Naganka... Menene? Takardata ka kawomun?"
Wata irin dariya mai sauti AbdulKadir yaji ta subuce mishi, tabbas Waheedah na da aljanu, yana
mamakin yanda akai basu taba tashi ba sai yanzun, film dinta ta dannama play tana mayar da
hankalinta a kai. Hannuwan shi AbdulKadir ya saka fuskar shi a ciki yana fitar da wani irin
numfashi, bashi da karfin yin ko hayaniyar kirki, duk wani kashi da yake jikin shi ciwo yake,
yasan yanda ake dukan ma'aikata in na horo ne, sun san inda suke duka da zai shigeka batare
daya ji maka ciwon da zai hanaka zuwa aiki washegari ba. Lokutta da dama ko fuskarka ba zata
gwada alamun dukan da kaci ba.
Suna dukan inda uniform zai kare shatikan ko ciwukan. Sauke hannayen shi yayi yana rutsa
idanuwan shi da yanda hakarkarin shi ya amsa, yasan ba karaya ko daya a jiki, amman wajen
ya tara jini saboda dukan da yasha, bashi bane na farko, Waheedah kan sa towel da ruwa mai
zafi ta gasa mishi ta bashi panadol ko da bayason sha.
"Kwanana biyar a barikin sojoji..."
AbdulKadir ya tsinci kanshi da fadi da wani irin sanyin murya, Waheedah batama ji shi ba, dan
gabaki daya hankalinta ya tattaru kan kallon da takeyi, hannu AbdulKadir yakai yana rufe
system, hakan yasa ta kalle shi
"Bana so, banma ga dalilin da zaka shigomun daki ka nemi dagamun hankali ba"
Murmushi AbdulKadir yayi
"Ina da duk wani dalili da zan shigo dakin nan, hankalina ba'a kwance yake ba, banga dalilin da
zai sa naki ya kwanta ba Wahee, ke kika zabar mana wannan rayuwar...sannan ba dakinki bane
wannan... Dakinki yana gidana"
Da kalar rigimar dake cikin idanuwan shi take kallon shi tana jin dai-dai take da duk wani abu
daya shirya tarar ta dashi, gabaki daya yagama fita daga ranta, ko ganin shi batason yi, auren
shi takeji kamar wata igiya data shake mata wuya tana hana mata yin numfashi a walwale,
shisa take so ya datseta ya warware mata ko zata samu ta shaqi iska mai nutsuwa.
"Bani da daki a gidanka, bani da komai a gidan ka sai kayan da nake gab da zuwa in kwashe
dan takardata zaka bani tunda babu inda aka taba aure dole"
Mikewa AbdulKadir yayi, ya dauka bashida karfin yin hayaniya, amman tunda can Waheedah
tafi kowa damar bata mishi rai, bata amfani da wannan damar ne sai yanzun.
"Igiyar aurenki a hannuna take, yanzun kuma na fara rikon ta, kaya kuma Allah ya baki iko, kina
jina? Allah ya baki iko dake da duk wanda yake da tsautsayin shigomun gida da nufin tayaki
kwashe su... Aljanu ne kike dasu da bansani ba sai yanzun, to wallahi ko su ubansu yayi
karya....ke da kanki ma kinyi karya kisani yin abinda banyi niyya ba"
Kallon shi Waheedah takeyi itama tana tsintar kanta da mikewa tsaye
"Ana dole ne? Nagaji... Nagaji da aurenka"
Cikin hargowa yace
"Ni bangaji ba, gajiyarki bata da wani muhimmanci"
Dariya Waheedah tayi tana jin duk wani kwanciyar hankali data samu a kwanakin nan na bace
mata
"Abubuwa da yawa da suka shafeni basu da muhimmanci a wajenka daman, saboda haka
banyi mamaki ba"
Cike da rashin fahimta AbdulKadir yake kallon ta
"Bangane abubuwa da suka shafeki ba suda muhimmanci a wajena ba"
Gyarama Ikram zama ta sakeyi a jikinta tana kara tallabeta
"Kwakwalwa ce a kanka duk da bako yaushe kake amfani da ita ba, sai kayi tunani ai"
Kallon ta AbdulKadir yakeyi, ya dauka ya gama shan mamakinta tunda ta iya bude baki ta nemi
ya saketa, amman da duk wani gani da zai mata bayan haka da yanda take kara shayar dashi
mamaki
"Zagina zakiyi Waheedah?"
Kai ta girgiza mishi, zagi ba dabi'arta bane tunda can, ko Fajr ma zata kirga lokuttan da ta zage
shi balle shi AbdulKadir din
"Idan ba zagi ba, me maganganun ki suke nufi? Rashin kunya kike neman yimun da bansan
lokacin da kika koyeta ba"
Yake karasa maganar da wani irin bacin rai marar misaltuwa
"Nifa ban zageka ba, rashin kunya kuma in dai koya nayi bai kamata kayi mamaki ba tunda nayi
rayuwar aure da kai"
Da hannu yake nunata
"Gashi nan... Yanzun me kikayi.. Wani zagin ne wannan ai... Wallahi Waheedah ki kiyayeni, kina
gwada hakurina... Kuma tashi zakiyi mu koma gida"
AbdulKadir yayi maganar yana son ture alamun da yakeji kamar na tsoro na son taso mishi, ga
hankalin shi da yake a tashe kasan bacin ran da yake fama dashi, musamman da Waheedah
tayi mishi wani irin kallo tana komawa ta zauna tare da fadin
"Saika daukeni ka dora saman kai ka mayar dani ai"
Kai AbdulKadir yake jinjina mata, inda take ya karasa,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 37