Share this page
shi "Ina wuni" Ya furta a hankali, duk cikin matan Abba yafi ganin girmanta, ita kadaice bata taba shiga harkar shi ba, asalima banda gaisuwa babu abinda yake hadasu, yanzun ma wucewa tayi hidimar gabanta, shi kuma ya taka yana karasawa har kitchen din, inda yaga Waheedah a tsaye, juyowa tayi tana kallon shi, kafin a dan daburce tace "Hamma..." Ludayin da yake hannunta ya karba, jajayen kayane a jikinta daya kara fito da farin ta yana saka shi daquna fuska 'In shaa Allah babu abinda zai hadani hanya da farar mace' Ya fadi a kasan ranshi, plate ya dauko batare daya kulata ba, yana kallo ta matsa tana hade bayanta da kantar kitchen din, abincin da yake tunanin zai iya cinyewa ya zuba "Ina miya?" Ya tambaya yana kin kallonta dan farinta na shigar mishi ido, da hannu ta nuna mishi tana sake matsawa dan zuciyarta dokawa take sosai, da tunanin shi manne ta yini, har fita tayi harabar gidan ko zata ganshi batare da tasan dalilin hakan ba, ta gaji da leqe-leqenta ta dawo cikin gida, ko sallar isha'i sai yanzun ne tayi alwalarta, a falo ta zauna tana jiran ko zata ga ya shigo dibar abinci, sai yanzun da yake tana da rabon tagan shi din. Cokali yasa hannu ya dauka hadi da wani plate din daya dora kan abincin ya rufe yana ficewa batare daya sake kallon inda take ba. Bangaren su ya koma, abincin ya fara ajiyewa tukunna yaje ya dauko ruwa ya dawo ya zauna. Daga shi sai Yasir da Yassar, Ahmad da suke kira da Babangida, sai Mubarak a falon. Film din da lokacin ake rubuta sunaye alamun farawa ya tsayar da idanuwan shi akai. 'Paheli' Ya karanta sunan film din da tun daga kidan daman yagane indiya ne. Abinci yake ci yana nutsar da hankalin shi kan film din, dan sosai yake jin dadin shi, kafin yaji an harbar mishi baya da kafa, ya kuma san Yassar ne "Sojan gobe ne yake kallon soyayya haka?" Yassar yai maganar yana dariya "Babu abinda zai hana insa a rufemun kai ko kwana biyune, saboda babu wanda ya rainani a gidan nan kamar ka" Dariya Yassar ya sake yi "Lallai ma yaron nan. Ka zama sojan tukunna" Juyawa Abdulkadir yayi yana kankance mishi idanuwa "Na kusan applying NDA ai, in shaa Allah. Kuma wayaki soyayya?" Wannan karin Babangida ne yace "Tambaye su dai, kaman suma ba kallon suke ba" Murmushin gefen fuska Abdulkadir yayi "Allah Hamma bazan auri matar da bana so ba, ina da buri mai yawa kan matata" Dariya sukayi gabaki daya "Hmm, tadai shiga uku da masifarka, aikai mai zama dakai tana da aiki wallahi" Mubarak ya fadi "Shisa nace zan auri wadda nake so..." Murmushi Yasir yayi mai sauti "Yaron da ko tafasa baiyi ba yana maganar soyayya da mata. Allah ya shirya" Daquna fuska Abdulkadir yayi "A'a Hamma...a'a wallahi, naji kamar kana so kace mun yaro" Ware idanuwa Yasir din yayi, bai gama mamakin Abdulkadir ba yaji ya dora da "Kaima yanzun kake level 2, bawai ka girmeni bane can da yawa" Yassar ne ya kara kai mishi duka da kafa, wannan karin yana kaucewa dan yagan shi "Me nayi? Karya na fada? Nidai Hamma Yasir karka fara gwada kirana yaro wallahi, ko mu kadaine balle a gaban yara" Abdulkadir ya karasa fadi yana kumbura fuska "Me zai faru in nace maka yaron?" Yasir ya tambaya "Nidai ai kashedi nayi" Ganin abin zai zama fada yasa Yassar cewa "Ya isa haka... Abdulkadir tashi daga falon nan" Kallon Yassar yake kamar ya mishi magana da wani yare daban dana Hausa "Yes ka tashi naje, ka jini kuma" Wata dariya mai sauti Abdulkadir yayi "Bazan tashi bafa, dan kallo nake, sai dai shi ya tashi" Ya karasa maganar yana nuna Yasir da dan yatsa, murmushi kawai Yasir yayi "Ka kyale shi kawai Yassar" "In bai kyaleni ba ya zaiyi dani daman?" Dafe kai Yassar yayi yana sauke numfashi, su Babangida da Mubarak daman basu sake saka musu baki ba, asalima kallon su suka ci gaba dayi, dan babu wanda ya shirya rashin kunyar Abdulkadir din, ganin kowa yai shiru yasa Abdulkadir mayar da hankalin shi kan film din, duk da zuciyar shi da yakeji ta kawo wuya. A hankali yake jin soyayyar da ake gudanarwa a film din na nutsar mishi da wani abu a kasan zuciyar shi, kamar yanda ya fada ne yana da buri mai yawa akan matar shi, kuma auren soyayya zaiyi, bazai auri yarinyar da bayaji har kasan ranshi ba, dan da kadan soyayyar da yake ma kakin sojoji zata dara tata. * Kamar yanda Waheedah tace Nuriyya zatai mata kitso, hakan ya faru ranar juma'a, tana dawowa daga makaranta, kaya kawai ta sake ta fadama Mami zata shiga gidan su Nuriyya, Amatullah ma anan tabarta zatayi wanke-wanke ta shirya itama su fita kitson dasu Zahra. A dakin su Nuriyyan suka zauna dan yin kitson "Karkimun manya fa" Waheedah ta fadi, tana saka Nuriyya kwashewa da wata irin dariya "Dame za'ayi kananun kitson to?" Duka Waheedah takai mata "Bana son iskanci, ai kinga dai gashina ya fara dawowa Allah" Dariya Nuriyya ta sake kwashewa da ita, tana kallom gaban kan Waheedah din da duk ya giwgwiye, daman bawai tana da gashin kirkin bane, taje wata yar ajinsu ta fada mata tayi retouching da Petals yana saka bakin gashi, dan farin Waheedah yasa gashin ta jane, Petals din baisaka mata bakin gashi ba saima gaban daya kara kwashewa kamar an aske "To zaki sake gwada Petals dinne?" Nuriyya ta tambaya har lokacin tana dariya, ita kanta Waheedah murmushi take "Allah zai kama mun ke, dan gashin nan da kike mun wulakanci sai kin tashi da safe ya kwakushe" Duka Nuriyya takai mata, duk da ba za'a sakata a layin masu dogon gashi ba, Allah ya bata yalwarshi babu laifi, tana kuma bala'ij ji da gashin har ranta. "Aniyarki ta biki" Wannan karin Waheedah ce tayi dariya, hira suke sosai ana kitson, a haka har aka gama "Ki tambaya Mami muje rijiyar lemo gobe in Allah ya kaimu" Nuriyya ta fadi, gidan Antynta take son zuwa, kuma Naira Hamsin gareta, batajin zata isheta, in suka tafi da Waheedah din tasan zata biya kudin motar. In ta tambayeta ma ba zata hana ta ba, tambayar ce ba zata iya ba, wani abu na mata zafi a kasan zuciyarta da tunanin hakan. Kai Waheedah ta girgiza mata "Da wahala Mami ta barni wallahi" Dan duk yanda Mami ta yarda da kawancen su da Nuriyya, tasan bata son yawon da babu dalili, duk da in ana biki ko suna a bangaren su Nuriyyan takan barta taje wasu lokuttan, amman yanzun tasan babu wani dalili, fada ma zatai mata. Hannu ta saka cikin aljihun wandon Pakistan din da take sanye dashi ta zaro Naira dari, kudin makarantar da aka bata ne ranar, babu abinda ta siya dashi. "Ki dai siya ma su Nana ko Guava ce" Karba Nuriyya tayi cikin ranta tana fadin 'Ashe su Nana' A fili kuma batace komai ba, dan bakinta yakan yi nauyi da taima Waheedah godiya a irin yanayin nan, ita ma Waheedah bata taba damuwa ba, dan a ganinta sun zama yan uwan ita da Nuriyya, babu wannan a tsakanin su, mikewa Waheedah tayi tana kakkabe jikinta, hadi da durqusawa ta dauki hijab dinta "Ki gaishe da Antyn dan Allah. Bari inje nasan su Amatullah basu dawo ba, in kamawa Mami girki" Kai Nuriyya ta jinjina, tana jin son cin komeye zasu girka din, dan ta tabbatar zaiji nama. Mami bata kwauron nama a abincin ta "Inkin dawo ki biyo, dambun shinkafa Mami zatai mana, in kuma baki biyo ba naba Aminu ya kawo miki" Dacin da takan ji wasu lokuttan Nuriyya taji ya mata sallama a cikin makoshin ta, zatayi komai dan suyi musayar matsayi da Waheedah, da duk rana take sa tana kara jin yanayin. "Wai aita magana kiyi shiru ki kyale mutane" Numfashi Nuriyya ta sauke "Ba kunne yake ji ba? Ai ina jinki ko?" Kai kawai Waheedah ta jinjina tana saka Hijab dinta "Allah dai ya shirya halinki" Ta juya ta fice daga gidan, wanka Nuriyya ta shiga, da yake ba nawa gareta ba, nan da nan ta shirya, taci uwar kwalliya, wata doguwar riga da Abban su Waheedah din ya siyo musu lokacin dayaje Umrah ta saka tana nade kanta da mayafins rigar daya bala'in karbarta. Sallama tayi da Mama tana ficewa daga gidan, a kofar gidan su Waheedah taci karo da Abdulkadir dan nan ne hanyar da zata bi ta nufi titi, haka kawai zuciyarta tai wata irin dokawa, ba tun yanzun yake mata kyau ba, yakan yi mata kama da mazan da takan karanta a litattafan Hausa. "Ina wuni Hamma?" Ta furta a hankali, a karo na farko da Abdulkadir zaice ya tsaya ya kare mata kallo, baisan tana da kyau har haka ba, ga yanayin jambakin ta ya zauna a fuskarta, raini ne bayaso ko a wajen yan gidansu, shisa duk wasu tarkacen kawayen su Zahra baya damuwa da su, in sun gaishe shi ya amsa, in basu gaishe shi ba shikenan, sam bayason raini da rashin kunyar kananun yara. "Lafiya..." Ya amsa tukunna ta wuce, cikin gida ya koma, yana kudurta a ranshi kudin kayan kwalliya daban zai ware ma matar shi, dan ko wajen aiki ya koma yana son tuno fuskarta da kwalliyarta da yasan zasu rage mishi kewar ta da zaiyi. Burin shi akan matar shi mai girma ne, shi kanshi yasani, duk da burin shi na saka uniform ya girme shi nesa ba kusa ba, amman ya matsa mishi ya samu wajen zama daram a zuciyar shi. *#TeamAbdulKadir* *#TeamWaheedah* *#FWA* *#AnaTare* [7/27, 1:13 PM] +234 816 124 4732: ©️ 📖✏ FIKRA WRITER'S ASSOCIATION Facebook: Lubna Sufyan IG: SufyanLubna Email: Calmlubna@gmail.com *ABDDULKADIR* *LubnaSufyan* 06 Akan ce kwanaki na gudu, bai taba yarda da hakan ba sai bayan sunan shi ya fita cikin jerin mutanen da suka samu gurbi a makarantar horar da sojoji ta NDA da take cikin garin Kaduna, bayan surutun da ake tayi ja cewar makarantar nada wahalar samu, sai kana da hanya. Zai karya idan yace Abba baisan mutane ba, ko cikin kawunnan shi baza'a rasa wanda yasan wani da zai taimaka mishi wajen samun makarantar ba, baidai nemi taimakon su bane kawai. Kuma da yake yana da rabo sai gashi Allah ya bashi. Ranar wani sama-sama yake jin shi, sosai ya yarda ranaku na gudu. Duka yaushe ya fara sakandire, gashi harya kammala yana shirin jefa takun farko a hanyar shi ta cikar burin shi. Ji yake kamar ya janyo lokacin tafiyar, yan gidan kansu sun fahimci nishadin da yake ciki, dan tunda suke basu taba ganin ya wuni da murmushi a fuskar shi ba, ko gaishe shi kayi ranar da murmushi yake amsawa. Idan ka tona ran kowa a gidan qal yake, musamman yaran da duk ya kasance akwai tazarar koda satika ce tsakanin shi da Abdulkadir, har tambaya sukayi akace musu akan shekara daya ma ba'azo gida ba, dan sai hutun sallah da ba koyaushe yake kaiwa sati biyu ba ballantana ma ya shige hakan. Ran su qal suke jinshi, zasu sakata su wala a gidan batare da tunanin Abdulkadir din ba. Yanzun ma abinci suke ci a dakin Anty. Waheedah ta kalli Zahra tace "Wai da gaske daga shekara sai shekara Hamma Abdulkadir zai dinga zuwa gida?" Kai Zahra ta daga mata tana hadiye abincin data cika bakinta dashi. "Haka naji Hajja da Hamma Yazid na maganar..." Kai Waheedah ta jinjina tanajin wani abu yai mata tsaye a wuya batare da sanin dalili ba "Kinsan duk yanda nake murnar tafiyar nan...Zanyi kewar shi fa" Ta karasa maganar tana dan yin jim "Babu wanda yake shan dukan Hamma Abdulkadir irinki duk gidan nan...kewar me zakiyi tashi? Jibgar da kike sha?" Nabila tai maganar tana cakuda abincin ta, dariya Zahra tayi, dan batasan ya zatai ma Nabila bayani ta fahimce ta ba, da gaske ne babu wanda yake shan dukan Abdulkadir din duk gidan kamar ita, sai dai ko shigowa yayi bai ganta ba sai ya tambaya tana ina, idan abu ya shigo dashi ko bata nan sai yasa an ajiye mata, tana kula da ko aiki yake so ai mishi ita kadai yafi matsawa, da wahala rana ta fito ta koma bai taba lafiyarta ba, duk da hakan tana jin Yayan nata har kasan ranta. Abincin suka ci gaba daci suna hira abinsu, Anty ta fito daga dakin baccin ta tana ganin yanda suka mayar mata da falo "Lallai yaran nan, falo nane haka? Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..." Ta karasa ganin shinkafar dake dankare kan kafet dinta "Wallahi tas zaku sharemun daki...ko kwayar shinkafa banason gani" Turo baki Nabila tayi dan Allah ya dora mata son jiki naban mamaki "Anty su Hamma ne fa..." Hararta Anty tayi "Banga su Hamma ba, kuna gani..." Waheedah kam murmushi tayi hadi da fadin "Za'a share Anty... Damun gama. Har wanke-wanke ma duk zamuyi" Tanajin zungurin da Zahra tai mata "Naganki dan ubanki, wato tace wanke-wanke shine kike zungurinta ko?" Cewar Antyn tana dorawa da "Maquyatan banza da wofi, sai kace ba mata ba" Ta juya ta koma dakinta, harara Nabila da Zahra suka zabga mata, Nabila na fadin "Adda Wahee ke zakiyi wanke-wanken?" Kai Waheedah ta daga musu tana ajiye cokalinta cikin abincin dan ta riga ta koshi tuntuni, hanyar kitchen din ta nufa tana ganin jibgin kwanonin wanke-wanken da ko kadan basu daga mata hankali ba, indai aikine da zatayi da jikinta baya mata wahala, duk da Mami kance ta cika yin abu da sanyin jiki. Saida ta fara share kitchen din tukunna ta fara wanke-wanken, tafiyar Abdulkadir tayi mata tsaye a makoshinta. Shekara daya na mata wani irin nisa naban mamaki, a wani bangaren kuma tana mata saurin zuwa, duka yaushe yagama jarabawar aji shidda harta fito, ita kanta aji biyar take shirin shiga yanzun hakan. ** Ranar lahadin da saura kwana daya su koma makaranta, kuma yai dai-dai da litinin din da Abdulkadir din ma zai tafi Kaduna. Wani iri take jinta, dan haka tanayin wanka tagama abinda takeyi ta fito zata shiga gidan su Nuriyya ko hira suyi, ta fito harabar gidan taci karo da Abba. "Abbah..." Ta kira fuskarta dauke da fara'a cikin yanayin da ita kadai take kiran shi da hakan. Shima muryar shi dauke da fara'a yace "Waheedah..." Murmushinta ya kara fadada "Ina kwana..." Amsawa yayi yana dorawa da "Har za'aje islamiyya ne da wuri haka?" Kai Waheedah ta girgiza mishi, kafin ta amsa yace "Wajen Hassanarki zakije kenan" Dariya Waheedah tayi "Abba mana" Jinjina kai yayi yana saka hannu a aljihu "Aina sani....itama goben suke komawa makaranta ko?" Kai Waheedah ta dan daga mishi, dubu uku ya zaro daga aljihunshi yana mikama Waheedah din "Na manta ne wallahi, ki bata saita dinka sabon kayan makaranta itama, abin na raina tun randa na bayar da naku dinkin..." Da fara'a a fuskar Waheedah ta karbi kudin "Allah ya kara arziqi Abba... Angode sosai" Murmushi kawai Abba yayi, hankalin yarinyar yasa yake jinta kamar daga cikin shi ta fito, ko kadan bayaso taji maraicin rashin mahaifinta, alkawari ya daukarwa mahaifiyarta na cewa zai riqeta, ko da mahaifinta na raye, nauyin alkawarin daya dauka zai cigaba da danne shi. "A dawo lafiya. Allah ya tsare mana kai" Waheedah ta fadi, Abban ya amsata, tsaye tayi saida taga ya shiga mota ya juyata ya fice daga gidan tukunna ta karasa takawa tana isa kofar gidan ta fice tana shiga gidan su Nuriyya din. Bata ma sameta a gidan ba, Mama ta aiketa, kudin da Abban ya bata ta mikawa Mama tana mata bayani, sosai Mama ta nuna jin dadinta hadi dayin godiya mai yawa, tukunna Waheedah ta koma gida. Bangaren su ta nufa ta shiga dakinsu ta kwanta. Bata da abinda zatayi, gashi sunqi kawo wuta balle tayi kallo ta rage zafi Tunawa tayi da wani littafi da tafi wata shidda da karba wajen Nuriyya, amman bata karanta ba, dan har yanzun ita karance-karancen littafin Hausar nan basa kanta, saukowa tayi daga kan gado tana dauko tsohuwar jakar makarantarta, aikam tana saka hannu ta bincika ta janyo littafin, kan gado ta dora shi tana mayar da jakar tukunna ta koma tahau gadon ta kishingida tana daukar littafin. ABIN DA AKE GUDU na BATUL MAMMAN ta duba sunan littafin da marubuciyar, sosai takan ji Nuriyya na maganar marubuciyar da yanda tsarin rubutunta yake tafiya a nutse, dan takance bata da gwana a marubutan Hausa kamar matar. Shafin farko ta bude tana nutsawa cikin labarin ASMA'U. * Ko da suka dawo islamiyya so take kawai ta gama duk wata hidima da zatayi tai sallar isha'i ta koma daki ta karasa jin yanda za'a kare da labarin ASMA'U, da ta dauka Nuriyya zuzuta marubuciyar kawai takeyi, sai yanzun da labarin ya tabata fiye da tunani. Ga tarin darussan da iya tsayin rayuwarta bata taba hango faruwar su ba, tashin hankali abune da sai dai taji labarin shi a waje ko a fina-finai, sai kuma yanzun da take karanta shi a littafin BATUL MAMMAN. Kayan makarantar su duk ta hada ta goge. Dauka tayi tana nufar daki, taga Amatullah a kwance a kasa kan kafet. Tunda zasu fita islamiyya take fadin cikinta na ciwo, har suka dawo, dan Waheedah ba zatace taga taci abinci ba "Ki tashi ki fadama Mami ko magani sai ta baki... Ya zaka zauna ciwo na cinka" Waheedah ta fadi tana ajiye uniform din a gefen gado, hadi da taba Amatullah din, zuciyarta tai wata irin dokawa ganin kamar bata motsi, tsugunnawa tayi tana kamota "Amatu... Amatullah..." Take fadi tana jijjigata, idanuwanta cike taf da hawaye, dakyar Amatullah ta daga idonta "Adda Wahee cikina, cikina ciwo yake..." Hannu Waheedah tasa tana share kwallar da take shirin zubo mata, muryarta a karye tace "Bari in kira Mami...sannu" Ta kara maganar tana zame Amatullah daga jikinta, ta fice daga dakin da sauri, koda taje wajen Mami dinma hannunta kawai ta kamo dan ta kasa magana, saboda kukan da take, dakin nasu Mami tabita hankali a tashe, a kafada ta sabe Amatullah din tana daukar hijab din Waheedah da tagani inda tai sallar Magrib tana nufar hanyar fita daga bangaren nasu, Waheedah na rufa mata baya. Bangaren Hajja ta nufa da Amatullah dan tasan Abban su bai isa dawowa ba. "Subhanallah, me ya faru haka?" Hajja ta tambaya, Mami na amsata da "Cikinta ne yake ciwo..." Hajja batace komai ba ta koma cikin dakin da hanzari, Hijab dinta ta dauko itama ta saka ta dauko mukullin motar ta tana fadin "Muje... Bari in dubo cikin yaran nan, ko wani yana nan. Tafiya asibiti da namiji nada dadi, kodan zirga-zirga..." Basu ma karasa bangaren nasu ba saiga Muhsin ya shigo gidan. Motar Hajja ta bude tana karbar Amatullah da take fitar da numfashin wahala ta sakata a bayan motar tana shiga. Ganin Waheedah dake kuka ta kama murfin motar yasa Mami fadin "Ina zaki ke kuma? Wuce ki koma gida..." Rau-rau ta sakeyi da ido, wani kallo Mami ta watsa mata dayasata sakin murfin motar, tana kallo suka rufe, gefe ta matsa, Muhsin din ya juya motar suka fice. Tsaye tayi a wajen tana share hawaye, hadi da sauke ajiyar zuciyar da take jin tana mata zafi. Ita kam da sun tafi da ita hankalinta zaifi kwanciya. A wajen ta zauna ko sauron dake gartsa mata cizo bataji, danma da haske, kasancewar an kunna musu gen. Bata san iya lokacin data dauka a wajen ba, ta hada kai da gwiwa, kuka kawai take sharba. Abdulkadir ne yazo wucewa, dan ranar ya wuni ne dasu Nawaf tunda washegari da sassafe zai wuce, ajiyar numfashin ta ya soma ji, kafin ya tsaya yana dakuna fuska, sosai ya saurara yaji daga inda kukan yake fitowa, dube-dube ya shiga yi, yana hangota rakube wajen ajiye motocin, daga hannuwanta yagane itace 'Me yarinyar nan take anan?' Ya tambayi kanshi yana karasawa wajen, ta hade kanta da gwiwa da alama kuka takeyi. "Waheedah..." Ya kira, muryarshi na dukan dodon kunnenta da wani irin yanayi da yasata dagowa, fuskarta ta karayin ja, idanuwanta duk sun kumbura saboda kukan da takeyi, saiya tsinci kanshi da kasa yi mata fada. Muryarshi dauke da wani yanayi yace "Menene? Waya dake ki?" Kai Waheedah ta girgiza mishi, wani rauni takejin yana kara danneta da ganin shi, hawayen ta na kara zubowa. "Me kike anan to? Meya faru? Mutuwa akai?" Abdulkadir ya tambaya, wannan karin da damuwa a muryarshi. Kan dai ta sake girgiza mishi "Kimun magana Waheedah, kina son batamun raine kome?" Ya karasa maganar a fadace, dakyar, muryarta can kasan makoshi tace "Amatu...Amatullah ce bata da lafiya" Numfashi ya sauke "Shine kikazo nan kina kuka...ina Amatu din yanzun?" Hannu tasa ta goge hawayen dake shimfide kan fuskarta tana jan hanci "Sunje asibiti..." Ta amsa muryarta na sake karyewa "Me yasa basu tafi dake ba? Mtswww" Abdulkadir ya karasa maganar da jan karamin tsaki. Kukan da take yana mishi wani iri "Tashi daga nan" Ya umarta, idanuwanta cike da hawaye take kallon shi "Zan jira su dawone Hamma..." Wani irin kallo yai mata yana fadin "Zaki tashi ko saina watsa miki mari? Cikin sauron zaki zauna da yake baki da hankali ko?" Mikewa Waheedah tayi babu shiri, tana ganinta yar mitsitsiya a gaban shi, duk da halin damuwar da take ciki bai hanata jin yanda zuciyarta take dokawa ba. "Ki koma cikin gida. Idan naganki a wajen nan saina zaneki..." Wasu sabbin hawayen taji sun zubo mata, duk da basu hanata kin bin umarnin shi ba, tsaye yayi a wajen yana kallonta harta sha kwana, dan dafe kanshi yayi, yana jin ranshi na baci babu dalili, bangaren su ya nufa, ko sallama baiyi ba ya wuce su Yassar da suke cikin abinci "Ko shi da wa kuma?" Yazid ya tambaya, Yasir ya amsa shi da "Indai bakin ran Abdulkadir ya motsa ko babu dalili yin shi yake..." Dariya sukayi, sai gashi ya fito, karamin tsaki yaja, dan baiga abinda zai basu dariya ba, ranshi yana baci suna dariya "Ku komai na dariya ne" Ya fadi yana kara jan tsaki "Kai da uban wa?" Yassar ya tambaya, bai samu amsa ba, Abdulkadir din yazo ya wuce yana yin ciki da kafafuwan Yazid da yace "Ikon Allah...bani na kar zomon ba" Shima bai samu amsa ba, Abdulkadir din ya fice daga dakin, yana doko musu kofar kamar zai karyata. Haka kawai ya tsinci kanshi da nufar bangaren su Waheedah dan bai yarda cewar ta koma ba, hangota yayi tsaye bakin kofa tana kai hannu tana goge fuskarta "Yarinyar nan bata da hankali" Ya furta a hankali, kukan da takeyi ma zai saka mata wani ciwon kan, ga sauro daya gama moreta a wajen da ta zauna. Da alama bata ganshi ba, dan saida ya kure mata tukunna ta ruga da gudu tana shirin komawa cikin dakin, Abdulkadir ya damqo hannunta "Hamma dan Allah..." Waheedah ta fadi idanuwanta kamar zasu fado, ga wani lugude da zuciyarta take mata "Me nace?" Kai ta girgiza mishi, hawaye na silalowa daga idanuwanta "Me nace miki?" Ya tambaya a tsawace "Kar in fito... Haka kace kar in fito..." Idanuwa Abdulkadir ya tsura mata, baiyi niyyar dukanta ba, haka kawai yaji yana son ganin ta tsorata haka. "Wallahi Hamma kafata daya na cikin daki... Dayace kawai a waje... Wallahi" Waheedah ta fadi, baisan dariya ta kubce mishi ba saida yaji sautinta cikin kunnen shi. Zahra na da wauta, bayajin kuma a cikin gidan akwai wanda yakai Nabila rawar kai, amman Waheedah cikin sanyi take nata rashin hankalin, dariya yake daya kwana biyu baiyi ba, ita kanta Waheedah din kallon shi take da mamaki, bawai baya dariya bane, amman dariya irin haka da sauti ba zata tuna ranar karshe da taga hakan ya faru dashi ba. Dayan hannunta tasa tana share hawayenta, dan karamin murmushi na kwace mata. Hannunta Abdulkadir yaja zuwa cikin dakin, ya zaunar da ita kan kujera, da murmushi a fuskarshi ya nufi kitchen din, ruwa ya dibo a cup yazo ya kawo mata, karba tayi tana mamakin yanda batasan tana jin kishi haka ba, ta kusan shanye ruwan, ta ajiye kofin hadi da sauke numfashi, mikewa tayi "Ina zakije?" Abdulkadir da yake tsaye ta tambaya, muryarta a dishe tace "Fuskata zan wanke" Kai ya daga mata, ta zagaya ta bayan kujerar ta wuce, dan gani take inta wuce ta gaban shi zaiji yanda zuciyarta take dokawa. Kofin ruwan ya dauke yana mayarwa kitchen ya fito ya koma kan hannun kujerar dake kusa da kofa ya zauna. Fitowa Waheedah tayi, yabi fuskarta da ta kara mishi ja saboda kukan da tayi, yana tunanin kartai ciwon ido da yanda yaga idanuwan sun kumbura. Wajen data tashi ta koma tana zama, wasa take da hannuwanta, ko zuciyarta zata rage gudun da take, lokaci zuwa lokaci takan dan dago ta saci kallon Abdulkadir din da yake zaune, kananun idanuwan shi na kafe a kanta, duk da alamun shi sun nuna yayi nisa a duniyar tunani. Hakan ne a bangaren Abdulkadir din, in da zaka tabashi ka tambayeshi tunanin da yakeyi baisani ba, balle kuma azo dalilin daya sashi yake zaune a wajen, kukan da yaga tanayine ya dame shi, shisa ya dawo kota sake fitowa, yanzun din ma yana zaune ne karya tafi ta sake fita, yana kuma so yaga dawowar su Mami din ya duba jikin Amatullah, dalilan duka sun zauna mishi, dan baya tunanin akwai wani dalili baya hakan, numfashi yaja a hankali yana fitarwa, yana jinjina ikon Allah akan Waheedah din, yanda ta kubcewa fitowa a zabaya abin al'ajabine, hannuwanta da take wasa dasu ya tsayar da idanuwan shi akai, har faratan yatsunta farare ne. 'Wannan wanne irin haske ne?' Ya tambayi kan shi yana sake sauke numfashin dayasa Waheedah kallon shi, duk cikin yayyen nasu shine basa hira dashi, bakama ga wannan fuskar ba, inba gaisuwa ba, saidai in shi da kanshi ya tambayeka abu zaka amsa, amman hira kam bayayi dasu, wani irin gudu taji zuciyarta ta kara, sautin na bugawa har cikin kunnuwanta, da labbanta da ta dagasu dakyar tana fadin "Gobe In Allah ya kaimu zaka tafi ko?" Da mamaki Abdulkadir din ya kalleta, yana dan daquna fuskar shi hadi da jinjina mata kai, wani abu Waheedah ta hadiye da takejin shi tsaye a makoshinta, batasan ya akai take son tambayar shi ba "Hamma sai kayi shekara baka dawo ba ko?" Kai ya sake jinjina mata, kamar bazaiyi magana ba kafin yace "Menene? Ba murna kuke zan tafi ba" Wannan karin ita

Chapter 6 of 37