Share this page
mishi a plate, ta samu dan kwano data fito dashi ta zuba farfesun naman da dumamawa tayi da safen, dan tun jiya da rana tayi ta saka a fridge. Bata san yanda AbdulKadir yake so ta fara cewa Yassar karya tafi da Fajr ba. Wannan aikin sai shi, dan akwai dawowar da yayi yaje har gaban Hajja ya dauko yaran shi. Wani abin idan yayi sai dai ita taji kunya, shikam ko a jikin shi. Hira suke danyi sama-sama harya gama cin abincin ya miqe, tayata kwashe kwanonin yayi ya wanko hannun shi a kitchen din, ya fito yana fadin "Zanje mu gaisa da Hajja... Sai in biya in dauko Fajr...ko zaki rakani?" Kai Waheedah ta girgiza mishi "Aiki zanyi wallahi, dan Allah karkai mun rigima Sadauki, kaga kifi na gyara, aiki zanyi... Kaje ka dawo" Waheedah ta karasa tana shagwabe mishi fuska, dan ya fara kankance mata idanuwanshi cike da rigima, zai iya cewa ta ajiye kifin suje su dawo. "Shikenan tunda ba zaki rakani ba" Langabe kai tayi "Ba kin rakaka nayi ba, aiki zanyi. Anjima kadan zaka fara kira mun yunwa" Murmushi yayi, dakinta ta wuce tana dauko wallet din shi da wayar shi da suke ajiye kan gadon ta, bude wallet din tayi taga da kudi a ciki, ta fito tana kawo mishi. Numfashi ya sauke, zai iya rantsewa daya gan shi a kusa da ita yake manta yanda zaiyi abubuwa da yawa. Da bata dauko mishi ba, ya manta wallet din da wayar basa jikin shi. Har bakin kofa ta raka shi, tukunna ta dawo ta shiga kitchen. * Da Mami kawai ya gaisa, dan bai samu Hajja ba, yarinyar kanwarta ta haihu, tunda safe ta tafi Aminu Kano. Tunanin ya kira wayarta bai zo mishi ba, da bai sha wahala ya fito ba, yayi kwanciyar shi yai bacci. Inya tashi sai yazo ya dauki Fajr din. Fitowa yayi daga gida, yana sakko kafarshi bakin kofa yana cin karo da ita, wani irin tsalle zuciyar shi tayi daga kirjin shi, kafin ta koma mazauninta tana ci gaba da wani irin dokawa da yakeji har cikin kunnuwan shi. A duk tsayin shekarun nan, bai taba barin kan shi yayi tunaninta ba, saboda yasan matsayin hakan a addinin shi, ya kuma san darajar kan shi, fadin garin Kano zai musu kadan da duk namijin da yasan yana mishi tunanin Waheedah. Kuma ko ba komai, shi mutum ne da baya tunani akan abinda ya wuce. Nuriyya na daya daga cikin su, ganin karshe da yai mata yana NDA ne, kuma daga lokacin sai labarin aurenta ya samu. Bai sake sakata a idanuwan shi ba, tunaninta kuma bai sake fado mishi ba. Sai yanzun, duk shekarun nan kusan, basu nuna a jikinta ba, tana nan yanda yasan ta, sai dai wata irin wayewa da ta shigeta, da sauri ya sauke idanuwan shi yana neman yafiyar Allah a cikin zuciyar shi na tsayawa da kare mata kallo da yayi. "Hamma.... Ina kwana" Ta fadi, muryarta na sauka kunnuwan shi da wani irin yanayi da bai taba tunani ba. Idanuwan shi har lokacin suna kasa ya amsa ta "Lafiya..." A taqaice, kamar yanda yakanyi tun da can, ita kanta Nuriyya batayi tunanin ganin shi ba, watan aurenta shidda kenan da mutuwa, taje gidan Waheedah sosai a tsakanin, dan tunda ta gama iddarta take yawo sosai da sosai. Ba zatai karya ba, ganin kwanciyar hankalin da Waheedah take ciki a duk lokacin da takan je gidanta yana tsaya mata a rai, shi yasa ma ta kusan wata daya yanzun bata taka gidan ba. Yanda Waheedah ta samu duk wani abu da take mafarkin samu na tsaya mata. Miji mai kudi, ga gidanta da ita kanta dinta, ga yaronta da takeji kamar ta sace saboda yanda yake mata kyau. Duk da bai kai hasken fatar Waheedah din ba, yaron yafi su dukan su kyau. Ko a wayar Waheedah ta so ganin AbdulKadir din, ta ga yanda ya koma. Haka kawai ta tsinci kanta da son sani, amman bata samu damar hakan ba, Waheedah kuma ko da wasa batai mata zancen shi ba, bata ga fuskar da zata sakko mata da zancen ba ita kuma. Dan sosai Waheedah ta canza, ba wai ita Nuriyyar ta canzawa ba, ita dince gabaki daya ta canza. Dan duk wani sirrin aurenta da taso ji ta kasa, tana mata kyauta kamar da, su sha labarin duniya dai, amman hirar halin da aurenta yake ciki, ko wani sirrinta sam bata ji ko daya ba. Abin kuma ya tsaya mata. AbdulKadir din take kallo, ya kara girma, dan sai ta ganta yar karama a gaban shi, ya aske gashin kan shi kasa sosai, sai ta ga idanuwan shi kamar sun kara kankancewa, akwai tabbai kanana a fuskar shi, sai wani babban tabo da alamun dinkine daga gefen habarshi zuwa wuyan shi, zuwa wani waje cikin rigar shi da take son ganin iya inda tabon ya tsaya. Shi kam bata ga alamar ya canza ba, dan yanda ya amsa mata gaisuwa, hakan yake amsa mata tunda can, a taqaice, cike da rashin kulawar da yake bata mata rai. Gani tayi yana shirin wucewa, da sauri ta tsinci kanta da fadin "Hamma..." Juyowa AbdulKadir yayi yana kokarin kar su hada idanuwa, zuciyarta taji tana dokawa "Aure na ya mutu, wata shidda da suka wuce, aurena ya mutu..." Ta karashe, tana kallon yanda a hankali ya sauke idanuwan shi cikin nata. Wannan karin kallonta yake, kallonta yakeyi da canjin da kalamanta suka haifar mishi, kallon ta yakeyi yanajin yanda babu shamakin igiyar auren da yake tunanin ta haramta mishi hakan. Ba zaice ga abinda ya faru ba, yanajin wani hijabi da yake tsakanin su ya yaye, yanajin abinda yake tunanin ya binne a NDA na warwarewa. "Me yasa?" Ya bukata, cike da rashin fahimta Nuriyya tace "Me yasa me?" Saida AbdulKadir ya hadiye wani abu daya tsaya mishi a wuya, tukunna ya amsa ta "Me yasa kika fadamun?" Wannan karin tata zuciyar taji ta doka, ita kanta ba zata ce ga asalin dalilin da yasa ta fada mishi ba, kawai taji tana so yasani ne, bada tunanin komai ba. "Ina so ka sani ne kawai" Kai ya girgiza mata, ya rabata ya wuce yana jin yanda take bin shi da idanuwa, yana kuma jin yanda da duk takun da zaiyi da canjin da kalamanta sukai mishi. Machine ya tare zuwa gidan Yassar din. Har cikin gida ya shiga, ya samu Yassar ya fita shi da Fajr din, hakan yasa shi juyawa, ko zama baiyi ba, duk yanda Hauwa ta tabbatar mishi da cewar ba nisa Yassar din yayi ba. Gida kawai yake son ya tafi, wajen Waheedah ko zai daina jin abin da yake ji. BAYAN KWANA BIYU Baccin da bata samu a kwanaki biyun da AbdulKadir yazo bane take ramawa, dan dakyar ta kai Fajr makaranta, bata tashi ba sai da azahar, masallaci ma suna raka'ar karshe, a daddafe tayo alwala ta gabatar da sallah, jin yanda jikinta yai nauyi har lokacin yasa ta sake watsa ruwa, atamfa ta saka, riga da zani tana daura dankwalin a kanta, ko mai bata shafa ba, tunda AbdulKadir din baya nan, bataga wahalar da kanta da zatayi ba. Falo ta fito ta kunna kayan kallon ta ganin da wuta. Tunanin AbdulKadir din zai iya kiranta kowanne lokaci yasa ta tashi ta dauko wayarta daga daki. Text ta tura mishi 'Ya hanya? Allah ya tsare ya saukeku lafiya' Ta ajiye wayar, duk da kallon da takeyi bai hanata tunanin wanke-wanken da yake jiranta a kitchen ba. Kwankwasa kofa taji anayi "Shigo..." Ta fadi, tana tuna cewar ta rufe kofar da mukulli, tashi tayi ta karasa ta bude, murmushi na kwace mata ganin Nuriyya. "Sannu da rashin kirki" Waheedah ta fadi tana mayar da kofar ta rufe, dariya Nuriyya tayi suna karasawa suka zauna. "Ina ta so inzo Allah.... Ban samu lokaci bane ba" Hararta Waheedah tayi "Haka zaki ce daman, kingama sai kimun kitso, kan ya isheni wallahi" Kai Nuriyya ta jinjina mata, suna gaisawa sosai, Nuriyyar ta dora da fadin "Fajr ana makaranta?" "Wallahi kam, tunda na kaishi na dawo na kwanta. Babu abinda nayi a gidan nan. Bari inyi wanke-wanke dai, me zakici? Akwai shayi, ko in tafasa mana taliya tunda ina da miya" Dan jim Nuriyya tayi kafin tace "Taliyar dai, bama yunwa nakeji ba, ki gama aikin ki a nutse..." Kitchen Waheedah ta wuce tana barin Nuriyya a falon. Kwanciya tayi ta dauki remote tana canza tashar zuwa Arewa24, wani film din Hausa sukeyi 'Bakin alkalami'. Shi ta nutsar da hankalinta tana kallo, kafin taji wayar Waheedah din na ihu kan kujerar, daga kitchen din Waheedah tace "Nuriyya dan Allah taimaka mun da wayata, Sadauki ne ina jin..." Mikewa Nuriyya tayi daga kujerar tana daukar wayar, aikam shi dinne, ga sunan nan a rubuce, haka kawai sai taji zuciyarta tana wata irin dokawa, lambar ta nutsar da hankalinta akai, komai na AbdulKadir daban ne, lambar kanta bamai wahala bace ba, hanyar kitchen din ta nufa da wayar, ta mikama Waheedah, da sauri ta dawo ta dauki tata wayar, gabanta ke wata irin faduwa lokacin da ta saka lambar AbdulKadir din a wayarta tana saving da 'Hamma AbdulKadir'. Ta mayar da wayar cikin jakarta ta ajiye. Ta koma ta kwanta, amman yanda gabanta yake faduwa yasa kwata-kwata ta daina fahimtar film din. Ko da Waheedah ta fito daga kitchen din ma sai take ganin kamar zata gane abinda tayi, har wata zufa takeji ta daban, duk da fankar dakin, dakyar ta iya yiwa Waheedah kitson, sukaci abinci, tana yin sallar la'asar tace wucewa zatayi. Tana kai Magriba ma wasu lokuttan, musamman in tazo Fajr na makaranta tunda wuni yake, hade makarantar tasu take da islamiyya. Sai tace sai ta gan shi zata wuce, amman yau din ba'a nutse take ba. Biscuit kala-kala da cake din da matar Yassar ta kawo mata lodi guda ta dibarwa Nuriyyan, ta bata dubu biyu, dan tasan zata kwana biyu bata dawo ba. Yanayin kaddarar Nuriyyan na tsaya mata a rai, duk da bata tambayeta me ya faru ba, tasan da laifin Nuriyyar a mutuwar aurenta, amman Waheedah na cikin mutanen da basa yanke ma kowa hukunci batare da sanin asalin abinda ya faru ba. Tana mata fatan alkhairi a ko da yaushe, dan har yanzun bata da wata kawar da tafita, sai dai yan uwanta. Sukan kwana biyu basu hadu ba yanzun kuma, Amatu ma aure ya watsa ta Gombe. Dukkan su aure yayi nisa dasu, sai wani abin ya faru akan hadu gabaki daya. Sai dai waya ko da yaushe da sukanyi. Anan falon tai zamanta, tana jiran lokacin dauko Fajr daga makaranta yayi taje ta taho dashi. Wani indiyan film ta nutsu tana kallo. LAGOS Wanka yayi, ya kwanta, daga shi sai singlet da gajeran wando, ya ja bargo ya rufe jikin shi, saboda ruwan da akeyi, garin yayi sanyi, kuma yana jin kwiyar tashi ya kashe fanka, lokaci irin wannan yakanyi kewar Waheedah kamar ba jiya suka rabu ba, da tana nan zata kashe mishi fanka, har bargon ma ita zata rufa mishi, ko bacci yake zata lullube shi, yanda ake take gane yanajin sanyi na bashi mamaki, amman Waheedah ce, takan gane yana bukatar abubuwa da yawa a lokutta dashi kan shi bai gane yana bukatar ba. Hoton shi ya dauka yana rufe da bargon ya tura mata a whatsapp, yana shiga tana hawa ta bude, itama nata ta turo mishi da Fajr dake bacci a kusa da ita, tana rubuto "Muna ta kewarka" Daga kasan hoton, hira sukeyi sosai, dan in yana hira da ita baya ma fita daga kan chat din ballantana ya duba ko wani ya mishi magana, Waheedah ma ta koya mishi chatting, kuma da ita kadai yakanyi hira mai tsayi. Sai kannen shi in sun gaishe dashi yakan amsa, suma ba kullum ba. Message na iya kwana biyu bai ko bude ba. Badan yagaji da hira da Waheedah din ba, tunda kullum bata rasa labarin da zata bashi, yace mata ta kwanta, dan yasan zata tashi da sassafe ta shirya Fajr makaranta. Sai da yaga ta sauka, tukunna, bai kai da kashe data din shi ba kiranta ya shigo. Da murmushi ya daga ya kara wayar a kunnen shi "Bakya jin magana ko? Bance ki ajiye wayar ki kwanta ba" Yanajin dariyarta ta dayan bangaren "Zan ji muryarka ne fa, yanzun zan kwanta" Har lokacin da murmushi a fuskar shi "Ke kadai nake sawa abu, sai kinga dama Waheedah, in fada miki magana kiyi kamar bakijini ba..." Dariyar ta sakeyi "Yanzun zan kwanta Allah. Sai da safe. Allah ya tsare mana kai" Amsawa yayi da "Amin. Ki kula da ku" Tukunna ya kashe wayar, ya sauketa daga kunnen shi, yana duba lokaci, karfe sha daya har da rabi, saqo yagani a saman na Waheedah da shine karshe. 'Hamma...' Dubawa yayi da mamakin ko waye, ba zai wuce Zahra ba, dan itace sarkin sake lamba, kullum cikin yarda waya take. Budewa yayi yana ganin tana online, da sauri ya amsa 'Na'am..." Fara typing yayi da shirin tambayarta ko lafiya? In yaji lafiya ne sai ya sauke mata fada da tambayar abinda takeyi online da daren nan. Hannuwan shi yaji sun daina rubutun a yake ganin sakon da ya shigo 'Nuriyya ce' Daquna fuska yayi, sannan ya kankance idanuwan shi, badan baigane ta ba, sai dan mamakin dalilin da yasa take mishi magana da tsakiyar dare haka. Tun randa yaganta tana manne da ranshi kamar yanda takanyi tun lokacin da take budurwa, lokacin farko da zuciyar shi ta fara doka mata, ba bakon yanayi bane a wajen shi, shisa bai dame shi ba balle ya hana shi hidindimun shi. 'Ok.' Ya rubuta mata, yaja data din shi ya kashe, ya ajiye wayar a gefe ya gyara kwanciyar shi, addu'ar bacci yayi ya lumshe idanuwan shi, Nuriyya manne da zuciyar shi, ba sai me zaice mata ba shisa ya kashe data din shi, baima san ko yana so yai hira da ita din ba. In ya riga ya gama waya da Waheedah baya son jin muryar kowa kuma, ko yin magana da wani. Dan ko Yassar ya kira shi yakan daga da fadin 'Nafa yiwa Matata sallama Hamma, kana kirana kuma, na gama jin muryarta yanzun ina jin taka' Yassar yakan amsa shi da 'Wallahi da bani da aure, kai zaka sa dole in fara nema, sai kace kai kadai ne me mata a duniya' Dariya kawai AbdulKadir zaiyi, amman har ranshi bayaso kowa yai mishi magana in yayi sallama da Waheedah. Baiqi ta zamo farko da karshen wadda zai wa magana a duk ranakun shi ba. Da wannan tunanin a ran shi bacci mai nutsuwa ya dauke shi. * Wayarta take kallo, ta tsammaci ya tambayeta inda ta samu lambar shi, tun jiya ta kasa samun sukuni, so takeyi ta kirashi, amman ta kasa samun karfin gwiwar yin hakan. Har ranta tana shakkar shi, kwarjinin da yake mata da, ganin shi da tayi ya ninku. Batasan me take tsammanin zai faru ba. Amman tana son mishi magana din, sai yanzun da ta kasa bacci, da tunanin shi fal ranta tukunna ta yanke hukuncin ta duba shi a whatsapp. Hoton dake kan display picture din shi ya fara saka zuciyarta daukar wani irin zafi, hoton shine, sai hannun Waheedah da yake rike cikin nashi, yatsunsu lankwashe cikin na juna, AbdulKadir din ya dago hannuwan ya sumbata. Wani irin abu takeji, inda tana da karfin ikon sake hoton, ta cire hannun Waheedah ta saka nata a ciki, zatayi hakan, tun ranar farko da taje gidan Waheedah takejin son samun abinda duk take dashi. Dp din AbdulKadir ya saka shi cikin lissafin abinda take son samu iri daya da Waheedah. 'Ok' Din shi take ta kallo ta kasa yarda da cewar baima damu da ita din bace, balle harya tambayi inda ta samu lambarshi. "Zan sa ka damu dani Hamma AbdulKadir... Wallahi nafi karfin wulakancin ka..." Ta fadi a fili, kalaman na zauna mata, tanajin yanda take a shirye da tayi komai indai zata same shi, kwanciyar hankalin da Waheedah take ciki, shigar alfarmar da takeyi da komai nata, take son samun irin shi. Kwanciya tayi tana lumshe idanuwanta, muryar Anas na dawo mata 'Saki kike so ko Nuriyya? Tunda na aureki hankalina bai kwanta ba, ke kanki baki bari naki ya kwanta ba, balle kibari nawa ya kwanta, saboda kina hangen abin duniya. Ba baki na miki ba, amman wallahi ba zaki taba samun kwanciyar hankali ba, alhakina bazai barki samun wannan nutsuwar ba. Bawai zan sakeki dan kin isa bane, zan sakeki saboda ina bukatar samun kwanciyar hankali...' Tashi zaune tayi tana girgiza kanta cike da son batar da tunanin Anas daga ranta, karya yake yace alhakin shi zai kamata. Ta yarda farkon auren su ta bashi wahala, bala'in yau daban na gobe da ban, inda take so tafiya take ko ya barta ko bai barta ba, abinci kuwa sai dai inya dawo ya dafa, har gyaran gidan shi yakeyi. Amman ta karfi da yaji Anas ya karbi mutuncinta, a cewar shi abin nata bana kare bane ba. Daga lokacin kuma tashin hankalinta ya fara itama, dan Anas daina raga mata yayi, saiya daina kawo abinci, duk idan ta fita batare daya barta ba, saita kwana ta yini da bakar yunwa, komin zagin da zatai mishi. Hakkin shi inya tashi karba baya tausaya mata, karfi yake nuna mata. A haka ta samu shigar cikin farko, a shekarar auren su, lokacin ya fara nuna mata wani irin gata da soyayya, kome tace tana so sai yai mata, amman ba wannan bane a gabanta, da rana daya bata tabajin soyayyar Anas ba, kullum tsanar shi kuma gaba takeyi a zuciyarta. Kudin da ta dinga karba a wajen shi sanadin cikin, da su tayi amfani aka cire mata shi. Dan ba zata hada jini da Anas ba, balle yara su sakata zama dashi. Idan ance mata zata shekara hudu da Anas zata karyata, ko shekara bata hango ba, ciki biyar ta zubar a gidan shi, na karshen ne yagane, kuma shine yai sanadin sakin da yai mata. Har gida yazo ya samu Baba ya bashi hakuri, ya kuma yi mishi bayanin duk abinda ya faru. Taga tashin hankalin da bata taba tunani ba, dan Baba ca yai saita koma ko ya tsine mata, kafin yaji saki Uku Anas din yai mata. Ko kadan Baba baiji dadin zancen ba, hausawa kan ce ka haifi yaro baka haifi halin shi ba. Haka Nuriyya ta zame mishi. Badan yana duba abubuwa da yawa da korar Nuriyya daga gidan zai haifar mata da shi ba, da babu dalilin da zaisa taci gaba da zamar mishi a gida. Amman duniya ta nuna mishi ta zaba fiye da darajtasu da mijin aurenta, idanuwa su Baba ya dauka ya saka ma Nuriyya, yabarta da duniyar da yake da tabbaci zata gyara mata zama. Mama daman ba darajar kirki take dashi a idanuwan Nuriyyar ba tun da can, balle yanzun da take ganinta dai-dai da kowa. Ganin babu mai mata fada yasa take duk abinda taga dama. Kullum yawon gidajen kawayenta tun na FCE da yawancin su yan duniya ne na asali. Maza kuwa kala-kala take tarawa a kofar gidan su. Yanzun ne takejin lokaci yayi da zata tsayar da hankalinta kan kudirinta. Dan duk a cikin masu zuwa mata da maganar aure bayan ta kare iddarta, talakawa ne, masu kudin da maganar banza sukan zo mata. Ita kuwa duk fitsararta bata kai nan ba, aure take son yi, soyayya bata gabanta, inda zata huta tayi abinda take so ne muradinta. Ta kuma hango hakan akan AbdulKadir. Komawa tayi ta kwanta, ta dauki wayar, duk da zuciyarta da take dokawa bai hanata tura mishi text ba 'Naga ka sauka, har kayi bacci? Sai da safe Hamma. Allah ya tsare mana kai' Ta saka wayar a caji ko da zasu kawo wuta cikin dare tukunna ta kwanta. Juye-juye take, bacci ya kaurace mata, tunani ne a ranta kala-kala...! #TeamAbdulKadir #TeamWaheedah #LubnaSufyan [7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan IG: SufyanLubna Email: Calmlubna@gmail.com Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43 *ABDDULKADIR* *LubnaSufyan* 21 A watanni uku babu dabarar da take tunanin tana da ita da zatayi aiki akan AbdulKadir. Ga wata irin soyayyar shi da takeji kamar ana hura mata wuta. Inda ance ita Nuriyya zata ajiye yanda take ji da kanta ta dauki duniya ta fadama da namiji tana son shi zata karyata. Amman sai gata, ba sau daya ba, ba sau biyu ba, harta bace kirgan lokuttan da ta furta ma AbdulKadir din kalmar so. A rana tana iya tura mai sakonnin text fiye da goma, tana tambayar lafiyar shi, ko yaci abinci, da sauran duk wani abu da take tunanin inta tambaye shi zai amsata. Sai dai tun kafin ma tace mishi tana son shi din, tana iya tura mishi sakonni hamsin a whatsapp ya bude ya karanta yai banza ya kyaleta. Sakonnin ma da alama suna zuwa, amsa ce kawai bata samu, tana iya kiran shi sau goma a jere bai daga ba. Yanzun kuma ta tsagaita mishi da kiran wayar, tunda ya daga ya balbaleta da fadin 'Ko matata sau biyu take kirana. Karki sake mun kiran yara Nuriyya. Bakisan bana so a dameni ba ko? Me yasa zaki dameni? Ranki zai mugun baci kika sake mun kiran yara. Idan ina son magana dake, kiran farko zan daga, idan bana kusa na zo nagani zan kiraki...' Ko amsarta bai jira ba ya kashe wayar. Kwana tayi tana kuka daren ranar. Komai sai da taji baya mata dadi. Tayi dana sanin sanayyar dake tsakaninta da Waheedah, sanayyar da tasa take kishinta, take son mallakar duk wani abu da take dashi, sanayyar da ta jefata cikin son mallakar AbdulKadir har yake mata wannan wulakancin. A tsayin watannin kwata-kwata bata taka kafarta gidan Waheedah din ba, sai dai su gaisa a waya, ko ta whatsapp wasu lokuttan, haka tace mata tana gidan kawunta dake Bebeji, taje tadan huta. A watannin ko fita batayi, tana gida kullum, samarin ma sun fita daga ranta, tana dan daga kiransu ne wasu lokuttan saboda ta samu katin waya. Waheedah kuma kan turo mata na dubu daya da dari biyar duk wata, ta siyi data. Duk da tana jin lokaci zai zo da ba zata bukaci wannan taimakon daga wajen Waheedah din ba. Ta dai samu AbdulKadir din, satin daya gabata, har gayawa kanta tayi ta hakura dashi, tagaji da wulakancin da take kwasa, amman da safe saita tsinci kanta da tura mishi sako ta gaishe dashi. Yau ma kamar ko da yaushe, yana online wajen karfe goma da rabi, dan ya saka hoton Fajr a status din shi, har ta bude ma tayi mishi magana 'Fajr fa yafi ku kyau' Ko budewa baiyi ba. Wani radadi kirjinta yake dan tasan da Waheedah yake chatting, zuwa yanzun wani irin kishi take da ita naban mamaki. Batasan me AbdulKadir yagani a jikin Waheedah ba, akan ce kana kiba inka haihu, amman tana nan yanda take, kamar sillen kara, in zasu jera ita da Waheedah, babu abinda Waheedah take dashi da za nuna mata. Tana da kyau tasani, daga na fuska harna jiki, batasan abinda Waheedah din take dashi har haka ba. Ko me tayiwa AbdulKadir din harya aureta. "Yanzun haka mayyar ita tace tana son shi" Ta fadi a fili, zuciyarta kuma na saka mata, indai wannan hanyar Waheedah tabi, to itama gata akai, amman babu alamar nasara. Saqe-saqe take a zuciyarta. Kafin taji wayarta da ta saka a silent tana zuuuu alamar kira ya shigo. Karamin tsaki taja, dan batasan kowanne maye bane cikin dare, tana dubawa jikinta taji har kyarma yake, ga zuciyarta na wani irin dokawa, ganin sunan AbdulKadir din da tayi editing zuwa 'Masoyi 💕' Na fitowa kiri-kiri, tunda tace tana son shi ta sake sunan, haka kuma takan kira shi dashi a duk sakonninta, bai taba kiranta ba, ita dinma inta kira shi ba dagawa yake ba. Jikinta rawa yake sosai lokacin da ta kara wayar a kunnenta "Masoyi..." Ta tsinci kanta da fadi, muryarta a karye, tanajin shige da ficen numfashin shi ta cikin wayar, yafi mintina biyu baice komai ba, badan numfashin shi da takeji da shuu kamar alamun yana cikin mota ba, zata iya rantsewa ya kashe wayar. Kafin yace "Sai da safe..." Yana kashewa din batare da ta samu damar amsa shi ba, murmushi tayi tana sauke wayar ta rungume a kirjinta, wani irin nishadi takeji yana ratsata ta ko ina. Ko ba komai yau ya kirata da kanshi, hakan kawai nasara ne. Da tunanin shi fal ranta bacci ya kwasheta. * Bata gane cikin Fajr kamar sadakar shi aka bata ba sai yanzun da take dauke da cikinta na biyu, da tun a satika kadan da shigarshi ya soma wasan kura da rayuwarta. Daga zazzabi zuwa amai tun kafin asubahi. Duk wani labari da taji masu ciki na bayarwa lokacin da take da cikin Fajr ne ya hadu waje daya yake wujijjigata. Bata son jin kamshin duk wani abinci mai miya. Nabila ta kira ta kwashe mata duk wani kayan miya da yake cikin gidan ta tafi dashi. Abinci sai dai ta saka mai da yaji, man ma na ja, idan tasha bakin ruwa sai tayi kamar zata amayar da kayan cikinta. Citta ta gyara ta dandaqa da kanumfari ta saka a fridge, duk in zata sha ruwa sai ta dan tsiyaya a ciki dan ya canza launi. Bata taba ganin tashin hankalin irin na watanni ukun nan ba, ga cikin harya fito mata, kamar mai yan biyu. Hankalin AbdulKadir yaki kwanciya, duk yanda take tabbatar mishi da lafiyarta kalau, laulayine kawai, kuma ance zai mata sauqi in cikin yadan kara girma. Amman duk wani dan lokaci da zai samu cikin kiranta yake. Har dariya takan mishi idan yana mata wasu tambayoyin "Kanki na ciwo? Kina jin zazzabi, bani lamba daga 1 zuwa 10 ya kikeji?" Wani lokacin har da fushin shi inta ce mishi ita lafiyar ta kalau, ya sha kiran Hajja inyaji muryarta can kasa yasa tazo, kunya yakan bata kamar ta nutse

Chapter 21 of 37