Share this page
ta girgiza mishi kai, tana kallo ya sake kankance mata idanuwan shi kafin yace "Karya ne..." Yana sakata yin karamin murmushi "Ki ban ruwa in sha Waheedah..." Abdulkadir ya fadi yana kara gyara zaman shi akan kujerar, mikewa Waheedah tayi tana zuwa kitchen ta dibo ruwan ta kawo mishi, karba yayi yana shanyewa tas ya mika mata kofin data mayar kitchen, ta kai mintina uku a ciki tsaye batare datasan tunanin me takeyi ba. Kafin ta fito tana komawa kan kujerar ta zauna, wannan karin tana kwantar da kanta a jikin hannun kujerar, agogon dake daure a hannun shi ya duba yana mamakin gudun da lokaci yayi dan har tara da rabi ta gota. "Kinci abinci?" Ya tsinci kanshi da tambayarta, dan yanda ta langabar dakai a jikin hannun kujerar yasa shi tunanin ko yunwa take ji, shi kanshi baici abincin ba. A hankali Waheeda ta daga mishi kai, gyara zaman shi ya kara yi kan hannun kujerar. Lumshe idanuwanta Waheedah tayi, batasan iya lokacin da suka dauka a haka ba, balle tasan bacci ya dauketa, cikin bacci taji muryar Abdulkadir din na fadin "Ya jikin nata yanzun?" A hankali ta bude idanuwanta tana kallon Mami, da sauri ta mike tana murza fuskarta "Mami... Ina Amatullah din" Kallon ta Mami tayi "Suna asibitin ita da Hajja, bacci takeyi, da sauqi ma sosai, zasu dawo da safe in shaa Allah..." Numfashi Waheedah ta sauke, Abdulkadir da yake tsaye ya kalli Mami yana fadin "Me yasa baku tafi da ita ba?" Ware idanuwa Mami tayi tana kallon Abdulkadir din "Asibitin sai munyi gayya Abdulkadir?" Dakuna fuska yayi "Da kun tafi da ita ai, ta zauna tanata kuka a waje" Kallon ta Mami tayi, tana sakata sadda kanta kasa, sai yanzun take jin kunya ta lullubeta "Harabar motoci Mami, ga sauro a wajen...nikam da kun tafi da ita" Ya sake maimaitawa, yana kokarin tausasa harshen shi saboda Mami ce, dan murmushi Mami tayi, tasan halin yaron sarai, ta kuma san kokari yake kar maganar da yake tayi kamar yana mata fada ne. "Ai mun dawo yanzun" Mami ta fasi da murmushi a fuskarta. Kai Abdulkadir ya jinjina mata "Sai da safen ku. Allah ya kara sauqi" Yai maganar yana ficewa daga dakin kafin yace komai, kamar hakan Waheedah take jira ta karaso tana kwantar da kanta a jikin Mami data tureta tana fadin "Ke yanzun meye na kuka? Ke da zakiyi mata addu'a? Ke komai na kuka ne?" Dariya Waheedah din tayi tana jin hankalinta ya kwanta, bin Mamin tayi suna hira, kafin tai mata sallama ta wuce dakin su. Sai taji dakin yai mata shiru, musamman data kwanta, da yanzun Amatullah din tana mata tsegumin juye-jujen da take inta yi bacci, dan da yawan lokutta tana cikin bacci zataji Amatullah ta dala mata duka, ta kwashe kafafuwanta data jibga mata ta warbar gefe tana fadin "Adda Wahee ki kasheni saiki huta" Dariya tayi ita kadai, mikewa tayi ta kashe wutar dakin, tana daukar yar karamar fitila mai batir ta maqala a cikin hular dake saman kanta, tukunna ta kwanta tana janyo littafin ta dan taci gaba da karantawa. Idanuwanta da taji har zafi suke mata yasata lanqwasa shafin data tsaya din, tayi addu'ar bacci tana rufe idanuwanta, soyayyar Asma'u da Jikamshi na mata tsaye, soyayyar tasu na sata tunani kala-kala, kafin bacci yayi awon gaba da ita cike da mafarkin su. * Bangarensu ya nufa ya shiga kitchen tunda girkin Hajja ne ranar, tuwon shinkafa ne tayi da miyar taushe data sha albasa mai lawashi sai kamshi take. Yanajin dadin girkin Anty da Mami, amman abincin Hajja daban yake jin shi, a wajen shi duk wani abinci da zaici bayan na Hajja zai biyo, baisan ko kaunar da ke tsakanin su bace ta rufe mishi ido. Anan kitchen din ya tsaya yana dora abincin kan kantar kitchen din, hannun shi ya dauraye jikin famfon dake gurbin wanke-wanke. A tsayen yaci abincin. 'Kaga zaka tafi wani gari da babu idanuwan mu akan ka, dan Allah ka rike addininka, karkai wasa da sallah, in har kana yinta cikin lokaci, kana kokarin yinta yanda ya kamata zata kare maka aikata abubuwan dabai kamata ba. Kuma ka rage zafin zuciya, dan Allah Abdulkadir ka dinga sakama ranka salama' Nasihar da Abba yai mishi ta dawo mishi, kai yadan jinjina yana karasa cinye abincin ya wanke hannun shi ya fice daga dakin. Bangaren su ya koma, babu kowa a falon sai Yassar daya kalle shi cike da mamaki "Daga ina kake haka kaikuma?" Saida ya zauna tukunna ya daquna ma Yassar din fuska "Hamma kana tsareni da tambaya kamar yaro" Dariya Yassar yayi "Nakai shekarun dazan fita in dawo sanda naga dama" Dare yayi, dan sha daya harda rabi, gashi bayajin yana da karfin biyewa rashin kunyar Abdulkadir din da zuwa yanzun inda sabo ya kamata ace ya saba, in wani yaiwa a waje su Hajja yake jama zagi, mutane naganin bai samu wadatacciyar tarbiya ba. Abin nama Yassar takaici, mutane nabashi mamaki, yanda sukan dora laifin yara akan iyayensu batare da kwakwwarar shaidar cewa laifin na iyayen bane na ci mishi rai. A ganin shi burin kowanne iyaye dansu ya zamo nagartacce, ya zamo abinda zasuyi alfahari dashi. Baice wasu lokuttan ba'a samun baraka daga bangaren iyayen ba, baice ba'a samun sakacin iyaye a kan tarbiyar yaransu ba, amman hakan baya nufin duk wani abu da yaro zaiyi saiya zamana laifin iyayen shine, kowanne dan Adam yana da zabi a rayuwa, cikin zabin harda fatali da tarbiyar da iyaye kan dora yaransu akai, a bangaren Abdulkadir din kusan zaice hakane, tun yana da karancin shekaru yake da wata irin zuciya, da ko laifi yayi in zaka kasheshi da duka bazai ko motsa ba ballantana yai tunanin gudu, ko wani yazo ya da nufin janye shi zai nuna bayaso. Yana tuna lokuttan da Hajja ke dukan shi akan abubuwa da dama, kafin Abba yace tana binshi da addu'ar shiriya tunda dukan baya aiki, ga bakin shi bazai shiru ba, inka fadi daya saiya fadi goma, musamman in yana ganin akan gaskiyar shine, komin girmanka baka wuce Abdulkadir ya datsa maka maganar duk da tazo kan shi ba. Kallon shi Yassar yayi yana fadin "Dan Allah ka kula da kanka, banda fada da mutane, banda rashin kunya..." Murmushi Abdulkadir din yayi yana sa Yassar tashi daga kishingidar da yayi a jikin kujerar yana gyara zaman shi sosai "Nasan fada dai sai kayi, dan Allah banda fadan da babu dalili" Kankance mishi idanuwa Abdulkadir yayi "Nasiha kake mun?" Duka Yassar yakai mishi da yasa shi ture Yassar din yana fadin "Cin zali babu kyau" Hadi da mikewa dan kan shi yakeji ya mishi nauyi "Idan nabar gidan saika nemi wanda zakaci zali" Ya karasa maganar yana wucewa hadi da turo kofar dakin shi, murmushi Yassar din yayi yana komawa kan kujerar ya kwanta yana sauke numfashi. Addu'ar Allah ya tsare da ta neman saukin zafin rai yake nemawa Abdulkadir din, da damuwar yanda kanin nashi zai rayuwa shi kadai a wani gari batare da kulawar wani nashi a kusa ba...!!! *#TeamAbdulKadir* *#TeamWaheedah* *#FWA* *#AnaTare*[© 📖✏ FIKRA WRITER'S ASSOCIATION Facebook: Lubna Sufyan IG: SufyanLubna Email: Calmlubna@gmail.com *ABDDULKADIR* *LubnaSufyan* 07 Zaune take gaban mudubi badan zatai kwalliya ba, tunda ta fito daga wanka ta sakama jikinta riga da wando na Pakistan, ta dauko hula ta ajiye kan mudubin, anan ta shafa mai ta zauna batare da tasan asalin abinda take tunani ba. A hankali ta dauki farar hular ta saka a saman kanta, tana gyara zamanta, hasken hular na saka nata hasken kara fitowa. A hankali cikin sanyin yanayinta tayi baya da kujerar da take sama tana mikewa tsaye. Madai-daicin tsayin da take dashi bai hana sirantakarta fitowa ba, duk da girman kayan jikinta. Falo ta fito tana ganin Mami a tsaye hannunta riqe da hijab "Ke ba dake za'aje kun shin ba?" Mami ta bukata, tana kallon Waheedah data girgiza mata kai, girman yarinyar na bata mamaki, yanda shekaru suke gudu na tsoratar da ita, yanzun Waheedah din tace a aji shidda sakandire, Waheedar tace take shirin zana jarabawar gama aji shidda, ko Amatullah ta gitta sai taita kallon su, tana mamakin lokacin da rayuwa ta kawota inda take, da gaske haihuwa kyauta ce mai girma, kyauta ce da take ma fatan duk wani wanda Allah bai nufa da samu ba ya samu ko zaiji abinda ake ji. "Jikina yamun nauyi Mami, suje abinsu, nace Amatu zata sakamun jan lalle idan zamu kwanta..." Waheedah tai maganar tana katse wa Mami tunanin da take. "Allah ya kaimu... Zamu fita kasuwa da Haj. Halima" Kai Waheedah ta jinjina tana fadin "Saikun dawo..." Tsaye tayi har saida taga Mami ta fita daga dakin tukunna, daga nan cikin dakin tana jiyo hayaniyar mutane da yake nuna alamun bikin da zasu sha a cikin gidan, tun da satin ya kama ake hidima, babu kuma ranar da kanta baya mata ciwo, dan bawai tana son hayaniya bane, amman biki yara uku ita kanta tasan saidai suyi hakuri, Muhsin, Khadija da Babangida, da shi Babangida ma za'a daga, dan ginin shi ko rabi baikai ba, sai Kawu Hamisu ya bashi gida mai daki biyu ya zauna har Allah ya hore mishi ya kammala nashi. Ita duk ba wannan bane a ranta, Abdulkadir ne manne da zuciyarta, zata iya cewa tun tafiyar shi da rana daya bai taba barin tunaninta ba. Lokutta da dama tana tashi daga bacci takanji kirjinta yai mata nauyi da tunanin halin da yake ciki, shekara daya akace zaiyi yazo gida, amman yanzun shekaru biyu kenan. Watannin baya kasa hakuri tayi, batasan lokacin da tambayar ko yana lafiya ta subuce mata a gaban Abba ba, shine ma yace mata yaje ya duba shi sau daya. Yana lafiya, tukunna taji tadan samu nutsuwa ta wasu fannonin. Kan kujera ta zauna, niyyar kwanciya take, tunanin Suratul-Kahf da bata karanta ba na sauko mata, kasancewar ranar juma'a. Ta rigada ta saba data idar da sallar asuba take karantawa, yau din bata samu wannan lokacin ba, saboda ta taya Mami gyaran gidan da aka bata, dan duk wanda ya kwana, ana sallah suke ficewa su koma sashin Hajja. Tunanin taje ta dauko Qur'an din takeyi, Aminu ya shigo da sallamar data amsa mishi cikin sanyin murya "Commander an diro..." Ya fadi yana dariya, hadi da wucewa kitchen, muryar shi Waheedah take ji ta dira kunnuwanta da wani irin yanayi, kafin ma'anar kalaman nashi su zauna mata, zuciyarta taji ta fara tsalle-tsalle da take tunanin kashedi ne, dan yanda ta fara doka mata, in bata miqe ba, tanajin tsaf zata fito daga kirjinta tayi kafafuwan kanta ta fice daga dakin dan neman duk inda Aminu yace Abdulkadir din yake. Mikewa Waheedah tayi tana saka hannu ta dafe kirjinta, inda take jin zuciyarta na kara gudu da duk daqiqa. A bakin kofa ta zira takalman bandaki da batasan ya akai suka zo wajen ba. Manya-manya ne, karamar kafarta na yawo a ciki, amman bata ma kula ba. Tafiya kawai take kamar wadda aka sakawa batira, kafafuwanta take takawa tana nufar bangarensu, badan sun taba doguwar maganar da tsayinta ya wuce mintina biyar ba, amman tanajin wata irin sanayya da tai mishi da take tunanin sai dai su goga da Hajja in akazo maganar sanin halayen shi. Abdulkadir din data sani bazai shiga cikin gida ba, idan wani ne daban ya shekara biyu baya gida, yana zuwa bangarensu zai wuce yaga mahaifiyar shi, banda Abdulkadir, zai iya jira, daya shiga hayaniyar da take bangaren Hajja gara ya jira. Tana da tabbacin yana bangaren su. Nan kuwa kafafuwanta suke daukarta, bayan shi ta fara hangowa, zata rantse da Allah ba girma kawai ya kara ba, harda tsayi, jakace rataye kan kafadar shi, rigar jikinshi ta kamashi kamar zata bude, damtsen hannun shi tabi da kallo daya kusa yar siririyar cinyarta. Sosai take takawa, bugun zuciyarta na karuwa, wani irin dumi taje ji jikinta ya dauka kamar zazzabi na shirin kamata. Tsaye tayi a bayan shi tana kasa motsa labbanta, hannunta daya na kan kirjinta kamar maison kare zuciyarta da take tunanin zata iya fitowa kowanne lokaci. Hannun shi Abdulkadir yakai yana sake kwankwasa kofar, yana jiyo kidan da suka kunna har nan inda yake tsaye. Tsaki yaja yana addu'ar wanda zaizo ya bude kofar ya kasance kasa yake dashi, yanda zai zabga mishi marin tsayuwar da yasha a bakin kofa, in ba wulakanci ba, ya zasu kunna kida su kuma kulle kofa daga ciki. Yana shigowa gidan ya fara dana sanin zuwa. Baisan meye a maganganun Yassar da sukanyi tasiri akan shi haka ba, amman saiya sauke mishi sakashi zuwan da yayi. Bayason hayaniya irin haka, saboda yasan dole sai wani ya bata mishi rai, ga hannun shi yana saurin tashi, yanzun abin harya fi nada. Yana sane yaqi zuwa hutun sallar da sukan zo na kwana biyu ko uku in yayi tsayi. Bawai dan baiyi kewar gida ba, sosai yake jin kewarsu, musamman Hajja da Zahra, babu wanda yagani tunda ya tafi daga Abba da sai Yassar. Dan shi kusan duk wata biyu sai yaje ya duba shi, kafin ya tafi kuma duk zuwan da zaiyi sau sunyi fada. Saida yaja dogon tsaki tukunna ya kara kwankwasa kofar da karfi wannan karin. Alama yaji ta cewar akwai mutum a bayan shi, kafin ya tsayar da hankalin shi waje daya, yanajin shiga da fitar numfashin Waheedah da takeyin shi a tsorace. Juyawa yayi gabaki daya, yana tsorata Waheedah da take tsaye, ta kuwa yi baya gabaki daya, cikin zafin nama ya riqo hannunta, saida yaga ta tsaya da kafafuwanta tana ware mishi idanuwanta da suke cike da tsoro tukunna ya saki hannunta, yana mamakin yarinyar daya bari ce a gaban shi, komai ya canza tattare da ita banda farinta, runtsa idanuwan shi yayi yana sake bude su akanta, tayi wani irin girma naban mamaki, farin da rashin kibar yana nan, sai dai za'a iya kiranta da budurwa, duk da a idanuwan shi tana nan a yar yarinyarta. Waheedah kuwa dayan hannunta ta saka tana kama wanda Abdulkadir ya saki, zuciyarta naci gaba da lugude a cikin kirjinta, numfashinta ma kokawa take dashi cikin yanayin da kusanci dashi haka kadai yake bayyanawa, sosai ya canza mata, kuma ba askin kanshi kadai bane yasa fuskar shi canza mata, dan ya aske shi qasa sosai, Abdulkadir da yake tara suma, fuskar shi tai mata fayau da askin da akan kira buzz a turance. Ga tabbai qananu a fuskar da batasan yanda akai yaji su ba. Tabon da yake gefen goshin shine kawai tsohon abu a fuskar shi, dan tasan dashi tun kafin ya tashi. Idanuwanta ta sauke zuwa wuyan shi, inda yake da wani dogon tabo daga gefen mummuqen shi zuwa wuyan, yana bace ma ganinta daga inda rigarshi ta lullube, wani abu na matsewa a zuciyarta, hannunta takejin yana mata kaikayi haka kawai, so take ta kaishi kan tabon da alamu suka nuna sabone sosai, ta kuma kirga duka qananun da take gani kan fuskarshi, yanda inya sake dawowa zata ga ko yaji wani sabon ciwon ko baiji ba. Kofar da Abdulkadir yaji an bude yasa shi dan juyawa, kafin ya sake juyowa yana mayar da hankalin shi kan Waheedah. Yana mamakin yanda ta tsaya tana kallon shi, kamar tana son bude har tsokar jikin shi taga ko yana boye wani abu cikin kasusuwan shi, yana kuma mamakin tsoron da yake cikin idanuwanta bai hanata kare mishi kallo haka kamar ta aike shi ba, batun yanzun yake kula da ita ba. Ko abu su Zahra suke son tambayar shi ita din suke sakawa, haka zata kalle shi cike da tsoron shi da baya hanata yi mishi tambayar, karfin halinta bazai gaji da bashi mamaki ba. Baisan dariya mai sauti ta kubce mishi ba, saida yaga yanda ta hadiye wani abu da yafi karfin yawu "Hamma..." Ta furta, muryarta can kasan makoshi, idanuwa Abdulkadir ya kafeta dasu, yana sata sake hadiye wani abu da take ji tokare da makoshin ta. Zata rantse tanajin zuciyarta ta yunkuro mata da tambayar da ta jima tana ma iska a dakin su, tunda shidin da take son tambaya baya nan. "Shekara daya akace Hamma.... Shekara daya akace zakayi kazo... Me yasa ka dade?" Wata gajerar dariyar Abdulkadir ya tsinci kanshi da sakeyi "Shine gaisuwar?" Ya bukata, muryar shi na nutsar da gudun zuciyarta. Ta dauka girman shi zaisa muryar shi ta canza ko ta kara budewa, tana nan yanda tasanta, shidinne kawai ya canza a bayyane. Dan murmushi taji ya kwace mata "Ina wuni..." Kai Abdulkadir ya girgiza kawai "Ki kawomun abinci" Ya fadi maimakon amsa gaisuwarta, ya juya yana sa hannu ya tura kofar, akan ce idan ka girma, rana da abubuwa nasa haskenka yadan dishe. Bayajin ko wahala zatasa Waheedah dishewa, da tunanin farinta da yakeji cikin idanuwan shi har lokacin ya shiga dakin yana fadin "Uban waye ya kunna kida ya kuma kulle kofa daga ciki?" Ya karasa maganar yana kare musu kallo, dakin kusan cike yake da mutane, bakin fuskar da bazai wuce dukan su ahalin Bugaje bane ba, dan ga kamannin nan yana gani, wasu kuma ya gane su. "Ubanka ne, nace ubanka ne ya kunna" Abdulkadir yaji muryar Yassar cikin kunnuwan shi, kafin yaji hannun Yassar din kan wuyan shi dayai ma wani irin riqo da yasa Abdulkadir din riqo hannun Yassar daya kasa banbarewa "Hamma zaka kasheni...me yasa kakemun hakane a gaban yara... Ka sakeni dan Allah" Abdulkadir yake fadi, yana raina karfin shi da yake tunanin ya karu saboda yanayin horon daya samu a makaranta. "Daga zuwan ka, shisa babu wanda yai kewar ka" Cewar Yassar daya saki wuyan Abdulkadir din yana tallabe mishi bayan kai "Dan banzan yaro kawai" Idanuwa Abdulkadir ya sauke kan Salim da yake kallon shi yana murmushi "Idan na karaso saina tabbatar labbanka sunyi kumburin da zaka kwana biyu bakai murmushi dasu ba" Mikewa Salim yayi yana wucewa dakinsu, ba akan shi Abdulkadir zai fara sauke kurar NDA daya kwaso ya shigo da ita ba. Dariya Yassar yakeyi, Abdulkadir din ya wuce bayan ya watsama duk wani da suka hada ido dashi a cikin dakin harara. Dakin shi ya wuce yana murda kofar yaga ta bude. Shiga yayi da takalman shi, dakin a share yake, sai dai akwai kaya kan gadon, juyowa Abdulkadir yayi da nufin zuro kai yaji wanda ya shigo mishi daki ya zuba mishi kaya akan gado. "Nine, ni nake kwana a dakin da aka fara hidimar biki..." Yassar ya fadi muryar shi dauke da gajiya da rikicin Abdulkadir da baya karewa. Yana yawan zuwa dubo shi a makarantane, tun ranar farko da yaje yaga halin da yake ciki, yasha wani irin duka ga zazzabin da yake da tabbacin dukanne yasa mishi shi, gashi ya rame sosai, daya dawo gida har kuka yaima Abba da fadin yaje ya dawo da Abdulkadir din, tunda zama sojan ba wahayin shi aka saukar mishi ba. Dan yana da tabbacin rashin kunya da bakin shi zaisa su mishi dukan da zai ajalin shi wata rana. Abba yace shi yaji zai iya, abar shi, kilan sanadin sojan yasashi fara ganin kan mutane da gashi. Amman hankalin Yassar din ba'a kwance yake ba, bazaiki ace kullum yaje ya duba halin da yake ciki ba, yaji dadi ma yanzun da wayar hannu ya yawaita, ko bakaje kaga mutum ba, zakaji muryar shi, amman zai karya idan yace baya addu'ar kar Abdulkadir yai abinda zasuyi mishi dukan mutuwa a NDA din nan, dan yaga alama abin babu sauqi. "Kaine mutum na farko da zan kulle ko kwana biyune Hamma, saboda kana mun abinda kake so a gaban yara" Abdulkadir ya fada babu alamar wasa a muryarshi, hannu yaga Yassar ya kawo, da sauri ya rufe kofar yana dariyar daya manta rabon da yayi irin ta. Kan gadon ya karasa yana kwanciya, kafafuwan shi a kasa, duk da ba takalman bane suka hana shi dora kafafuwan kan gadon, ra'ayin kwanciyar a haka kawai yake ji. Iskar gida kanta daban take data NDA, gyara kanshi ya sakeyi, farar rigar Yassar dake gefe nasa Waheedah fado mishi, badan kalar nata farin iri dayane da rigar ba, ko kusa basuda alaqa, kawai ya tsinceta a ranshi ne, yafi alaqanta hakan da jiran da yake ta kawo mishi abinci, dan yunwa yake ji ta fitar hankali. ** Kitchen ta koma, tana jinta kamar akan iska take tafiya, tanajin yanda zuciyarta ta lullube mata wani nishadi da idan tabari ya fito fili tsalle-tsalle zata fara kamar karamar yarinya, ba tana cikin kunci bane a shekaru biyun nan, sosai take zagaye da yan uwanta da suke sakata farin ciki, amman nishadin da take ji yanzun ganin Abdulkadir dinne kawai yake bayyana shi. A litattafan Hausar data karanta taga soyayya kala daban-daban, shisa ta sakama kusancin da takeji da Abdulkadir ayar tambaya, dan har yanzun batajin yana da suna a zuciyarta. Dan abinda takeji akan shi yasha banban da duk wata soyayya da take gani a litattafai. Abinda takeji akan Abdulkadir batasan tun yaushe ya fara ba, kawai bude idanuwa tayi a kusa dashi taji zuciyarta na wata irin dokawa, idan sone ya kamata ta fara tunanin koshi yanajin kalar kusancin da takeji akan shi, amman har kasan zuciyarta bata damu dako yanaji ko bayaji ba, asalima tanajin yanda nata ya ishesu su biyun. Kuma tana jin tsoron shi kamar yanda su Zahra suke jin tsoron shi. sai dai akwai wani karfi da yake tasowa daga zuciyarta koda yaushe yana danne tsoron in tana son magana dashi. Da murmushin daya kasa barin fuskarta take zuba mishi shinkafa da miyar da Mami ta girka, ta kuma san saboda Amatullah ta dafa, dan ba zataci abincin da batasan waya dafa ba, haka zata wuni tana shan shayi, kyankyamin da yarinyar take dashi har mamaki yake bama Waheedah. Salak ta zuba mishi a gefe da su tumatiri da ta yayyanka harda kokomba. Batasan waye da waye baici abinci ba, amman naman dake miyar kusan fiye da rabi ta zuba ma Abdulkadir din. "Tunda shi baqone..." Ta furta ma kanta, Allah kadai yasan kalar abincin da suke ci acan, gara yau yasan yazo gida. Babban faranti ta samu ta dora karamin a ciki tana rufewa, tukunna tasa cokali a gefe. Ruwa ta daukar mishi da kofi duk tasa cikin farantin tukunna ta dauka tana ficewa zuwa bangaren su Abdulkadir din, saida ta kwankwasa suka ce ta shiga tukunna ta cire takalmanta a wajen ta shiga. "Ina Hamma Abdulkadir?" Tai tambayar tana kallon Naziru daya nuna mata dakin Abdulkadir din da dan yatsan shi, yana mayar da hankalin shi kan kallon da yake, dan shi kadai ta samu a falon ma, da alama kowa ya fice hidimar gaban shi. Abinda bata sani ba shine Abdulkadir ya fito ya zare wayoyin speakers din da suka kunna kidan dashi, da yaji bai hana kidan yi ba, yaje ya raba extension din da kayayyakin suke jone da socket din dakin gabaki daya yana zubarwa a kasa ya juya ya koma daki baice ma kowa komai ba. Yassar ne yace su hakura kawai su kyale shi, shisa kowa ya fice daga dakin, shi kanshi Nazir din sai gaban tv din ya koma sosai dan ya rage maganar tayi kasa yanda kunnuwan shine kawai zasuji. Wucewa Waheedah tayi, tana kwankwasa dakin "Shigo..." Abdulkadir din ya fadi, a hankali ta tura kofar tana shiga hadi dayin sallama, tashi zaune Abdulkadir yayi yana kasa hakuri data ajiye mishi farantin, yasa hannu ya karba, a kan cinyar shi ya dora yana budewa hadi da saka cokali a ciki ya fara cakuda gefe, tukunna ya diba yana zubawa a bakin shi. Yanda ya sauke numfashi nasa Waheedah jin da tana da iko kullum saita aika mishi abinci Kaduna. Tasan ya kamata ta tafi, amman kafafuwanta kamar an dasasu a wajen, bayanta ma ta jingina da bangon dakin tana kallon yanda yake cin abincin da sauri-sauri. Abinci ya mishi dadi sosai, bai damu da tsayuwar da Waheedah din tayi ba, ko kofar dakin data bar mishi a hangame. Haka kawai yaji ya kasa ce mata tsayuwar me take mishi a dakin har lokacin. Batasan meyasa takejin son mishi magana haka ba, jikinta har dumi yake dauka da yanayin son mishi maganar "Dame kaji ciwo Hamma?" Ta tambaya, yanda yadan tsaya, kafin yakai cokalin abincin bakin shi yana juyowa ya sauke mata kananun idanuwan shi yasa zuciyarta dokawa cike da tsoron shi da bai hanata sake fadin "Yaushe zaka tafi?" Abincin Abdulkadir yake taunawa a nutse, inda wani ne ba ita ba, zaiji kamar ya raina shi da yawa da har zai tsaye yana jero mishi tambayoyi, amman a muryarta yake jin yanda tsakaninta da Allah tayi tambayar, babu raini kowani abu, kawai tana son sani din, amman daga haka raini yake farawa, shiru yayi ya kyaleta yana cigaba da cin abincin shi "Sune basa barin ku zuwa? Ko kaine kawai kaqi zuwa? Hamma kaga wani tabon fa har a gefen kuncinka... Dame kaji ciwuka haka dan Allah?" Waheedah taci gaba da jero mishi tambayoyin da take jin suna fito mata a sauqaqe, kamar sun shekaru masu yawa a tare dashi, kamar tayi sabon da zatayi labari dashi mai tsayi batare da fargabar komai ba haka take jinta, duk da a kasan zuciyarta wani abu yake fada mata ba amsa zata samu ba, itama ba tana tambayar shin bane dan ya amsata, tana tambayar ne kawai saboda tana son magana dashi ko da bazai amsa ba, indai yana jinta ya isheta. "Ko kun fara fita aikin soja ne?" Ta bukata, tana ware idanuwanta, zuciyarta cike da wani sabon tsoro da tunanin abinda hakan yake nufi "Hamma kun fara zuwa yaqi ko? Inalillahi wa ina ilaihi raji'un...oh Allah na... Ko harbine tabon wuyanka? Oh Allah na" Cokalin Abdulkadir ya ajiye cikin abincin shi yana fadin "Fitar mun daga daki Waheedah..." A daburce tace "Na'am..." Dan tunaninta yayi nisa cikin kalar tashin hankalin da take gani a fina-finan sojojin da take cikin kallo yanzun duk idan ta samu lokaci. Yazid kanbar mata laptop dinshi inya samo, saita kalla a ciki. "Ki fitar mun daga daki kafin in watsa miki mari" Abdulkadir ya fadi can kasan makoshi, saboda dariya na gab da kwace mishi, yana kallon tsoron da ya cika idanuwanta

Chapter 7 of 37