hidima.
Duk da matsala dayace take fama da ita yanzun, itace rashin haihuwa, banda wannan rayuwa
take data sa tagane farin ciki bako yaushe yake zuwa da kudi ba, farin ciki kanzo idan ka samu
wadatar zuciya da iya inda Allah ya zaunar dakai. Tayi nasarar ganin Anas sau daya tun bayan
rabuwar su, ta kuma roki daya yafe mata, duk da har yanzun takanyi juyi da amsar daya bata
'Na jima da yafe miki Nuriyya saboda bana son wani abu ya sake hadani dake, ciki kuwa harda
tsayuwa gaban Ubangiji a filin tashin kiyama, wallahi na jima da yafe miki karki damu'
Sosai takanyi tunani akan kalar rayuwar da tayi a baya, da mutane biyun da suka nuna mata
kauna fiye da kowa a rayuwarta da yanda tayi amfani da wannan kaunar ta cutar dasu
"Nuriyya"
Waheedah ta fadi tana katse mata tunanin da takeyi
"Ki yafemun dan Allah, na cutar dake da yawa, wanda kika sani da wanda baki sani ba, ki
yafemun Waheedah..."
Numfashi Waheedah ta sauke
"Babu komai, Allah ya yafe mana"
Wannan karin ajiyar zuciya Nuriyya ta sauke tana dorawa da
"Ki rokar mun AbdulKadir da ya yafemun shima"
Kai Waheedah ta daga mata tana hango motar AbdulKadir din
"Sai anjima..."
Tace ma Nuriyyar tana kama hannun Ikram din
"Ina Fajr?"
Nuriyya ta tsinci kanta da tambaya tana saka Waheedah juyowa ta kalleta cikin idanuwanta
"Na yafe miki Nuriyya, tun kafin ki tambaya, amman hakan baya nufin ina son sake kasancewa
dake a rayuwata, babu wani abu da zai sake hadani kawance dake"
Kai Nuriyya ta jinjina ma Waheedah din, bata koji zafin maganganunta ba, ko itace a matsayinta
abinda zatayi kenan.
"Nagode..."
Nuriyya ta fadi da wani irin yanayi a fuskarta
"Ina miki fatan alkhairi a duk inda rayuwa zata kaiki"
Waheedah ta fadi tana jan Ikram suka tsallaka inda AbdulKadir yayi parking din motar, Nuriyya
kuma ta shiga gida. Bayan motar ta budema Ikram ta sakata a ciki, tukunna ta bude gaban ta
shiga
"Kinsan sarai gobe zan tafi, shine zaki zo ki barni ni kadai"
Murmushi kawai tayi
"Nuriyya nagani yanzun ta shiga gida, tace ince ka yafe mata"
Shiru AbdulKadir din yayi badan baiji me tace ba, sai dan a shekaru uku yaune rana ta farko da
maganar Nuriyya ta gifta a tsakanin su. Motar shi ya tayar yana wucewa dasu gida, bashida
abin cewa yanzun ma, shisa ya zabi yin shiru, wanda duk zaiji labarin shi da Nuriyya zai san
kaddarar zaman aure ce kawai ta gifta a tsakanin su, yanzun ta zama bayan shi, bayan da baya
dubawa idan harya wuce, ya gama yafe mata duk wani kuskure da tayi mishi a dan gajeran
zaman da sukayi. Shima fatan shi idan ya kuskure mata ya zamana ta yafe mishi.
Dan da Abbba ya kira shi yai sake mishi nasiha kan abinda ya faru din daya kira mishi ko da
gaba zai tunanin kara aure saida hanjin cikin shi ya murda, yana addu'ar Allah yasa kaddarar
shi ta zama da mata biyu ta kare daga kan Nuriyya, Waheedah ta ishe shi rayuwar duniya yana
kuma fatan ta zama matar farko da zai nema idan ya tsallake duk wani mataki yayi nasarar
shiga aljanna.
Suna karasawa gida an kawo wuta, Ikram nata tsalle ganin tv a kunne da tashar cartoon
network da suka saka shun the sheep. Nan falon suka barta suna shigewa dakin su. Waheedah
na cire hijabin dake jikinta, AbdulKadir ya taka ya hade space din dake tsakanin su, sai nishi
take kamar tayi wani aikin karfin.
Hannun shi daya ya dora kan cikinta kamar abinda yake ciki hakan yake jira yayi motsin da taji
har bayanta ya amsa tana runtsa idanuwanta ta bude su akan AbdulKadir da yake mata dariya
"Ke kam kamar ba matar soja ba"
Harar shi tayi
"Da zan iya dana cire cikin nan ka dauke shi kona kwana biyune"
Tsinin cikin bazai barshi ya rungumeta yanda yake so ba, hakan yasaka shi sakin hannunta ya
zagaya yana rungumeta ta baya hadi da rada mata maganganun da sirrine a tsakanin su,
hannu tasa tana dan ture shi hadi dayin dariya kafin ta dora hannunta saman nashi da ya ke
kan cikinta tana lumshe idanuwan shi. ABDULKADIR din ta, sojan ta, Sadaukin ta. Bata same
shi da sauki ba, kaddarar zaman su bata kawosu inda suke da sauki ba, bata da wani tabbaci
akan yanda rayuwa zata kare musu, amman tana da yakinin indai suna tare da juna koya
rayuwa zata hankade su koda sun fadi dayansu zai daga daya...!
DUKKAN GODIYA TA TABBATA GA ALLAH.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 37 Chapter of 37