Share this page
ya dawowa dai-dai. "A. Bugaje" Ahmad yace kamar yanda kowa yake kiranshi a NDA din. "Baka gyara wayar nan ba ashe?" Screen dinshi ya fashe, a kwana biyu yana dan samu ya amsa kira idan ya shigo, saita kara faduwa, yaje ya gyara dinne baije ba. Yassar ma a wayar Ahmad din yake kira su gaisa. "Zan gyara" Ya fadi a takaici yana karasawa kan gadon ya kwanta. System dinshi ya janyo da take ajiye kan tebir din da yake dakin, budewa yayi, hannuwan Waheedah da kunshinta na cika screen din. Har yau baiga kunshin da yai mishi kyau kamarshi ba "Hannuwan nan namun kyau wallahi, ina ma in gano yarinyar da take da shi" Ahmad ya fadi yana miqa kanshi dan yaga hango sosai. AbdulKadir yakai hannu ya latse system din yana kasheta gabaki daya. "Au dan bakin ciki kar ingani?" Yai maganar yana dariya. Har duba system din yayi baiga hoton ba, ya rasa kalar boyan da Abdulkadir yai ma hoton, idan zai mutu yana tambaya ko yasan mai hannun ne, ko yana da alaqa da ita kamar yanda yai zato da farko bazai kulashi ba ballantana ya samu amsa. Kamar yanda yanzun ma bai kulashi ba. A gidansu Abdulkadir banda Yassar baisan kowa ba, sai Hajja dan sukan gaisa idan ta kira Abdulkadir din koshi ya kira, sai Zahra da itama suna waya, itace ma daya tambayi AbdulKadir din ko kanwarshi ce ya samu amsar "Ban damu da ka kusa zama cikakken soja ba, zan karyaka Ahmad, da gaske zan karyaka..." Yayi dariya sosai, kuma hakan ya tabbatar mishi da cewa kanwar Abdulkadir din ce. Akwai yarinyar da yake yawo da hotonta a wallet din shi. Wasu lokuttan kuma yakan cire hoton ya saka a aljihun shi, duk idan aka bata mishi rai Ahmad na kula yakan saka hannun shi a aljihun shi, kamar hoton nada wani sihiri da zai hutar da fushin shi. Duk yanda yake so ya tambayeshi alaqar shi da yarinyar hoton saiya kasa, saboda a bayyane yake. Tana da muhimmanci na gaske a rayuwar shi. Bai dai taba nuna alamar yana da budurwa ko yana son wata ba. Idan har hirarsu ta tsawaita to ta dangancin aikin da suke gab da fuskanta ne na kare kasarsu. Sai dai watanni kusan bakwai da suka wuce, yakanga Abdulkadir din manne da wayarshi duk dare, ba daddanawa yake ba, da alama dai yana karanta wani abinne, yakan kuma ga yana murmushi shi kadai inya zauna da wayar a hannun shi. Gashi ya bude whatsapp din da babu yanda baiyi dashi ya bude ba, yaki. In kuma ya dauki wayar Abdulkadir din dan yai kira ko wani abu, banda yan gidansu da zaiga Hamma wanne, ko Adda wance, sai su Zahra, baya ganin kiranshi da kowa sai lambar daya sakama 'Wahee'. Yakan kuma ga saqoninta na shigowa wasu lokuttan. Baida tabbas, amman yana alaqanta hotonta ne Abdulkadir yake yawo dashi. Juya mishi baya Abdulkadir yayi, yana jan pillow ya dora hannuwan shi akai, dan baya sakawa a kanshi, koya kwanta yasa pillow daya fara bacci yake zarowa ya dora hannunshi akai. Gashi har yanzun kwanciyar jarirai yake, jikin shi a dunqule haka yake bacci. Idanuwan shi ya lumshe, hoton Nuriyya na mishi yawo kamar koda yaushe, tun yana kokarin danne shi harya haqura yabarshi. Ya daina kokawa da zuciyarshi akanta, zuwa yanzun ya fahimci zuciyar shi na doka mata. Zai wani abu akai, saiya fita daga NDA ya dan samu nutsuwa, yanzun koma menene yake ji dole ya jirashi ya nutsuwa tukunna. Lokaci irin wannan hirar Waheedah yakan karanta, har tai mishi saida safe, yakan koma baya yaita sake karantawa har saiya fara jin bacci. Amman kwana biyu hakan baya samuwa saboda bai gyaro wayarba. Yana kewar hirarrakinta, dan takan hana mishi tunanin Nuriyya irin haka, takan debe mishi kewar gida da gujema ganin Nuriyya ya hanashi zuwa. Sosai surutun ta yake mishi dadi 'Hamma kasan me ya faru yau' Yakan karanta sakkoninta da sanyin muryarta, har yanayin idanuwanta yakan gani, kamar tana cikin dakin tare dashi. Idan an bata mishi rai yakan lumshe idanuwan shi yaji muryarta cikin kanshi 'Banda saurin fushi Hamma, dan Allah banda saurin fushi kaji' Takan fada mishi haka a sakkoninta, tana saka murmushi kwace mishi. Inba ita ba, babu wanda ya isa yana bashi umarni haka, ko abinci takan mishi magana yaci, karya zauna da yunwa, wata rana sunanta kawai zai rubuta, zata ce mishi ya ajiye wayar ya kwanta. Yanda take karantarshi har mamaki yake bashi, tashi yayi ya dauko wallet dinshi ya ajiyeta gefen kanshi yana gyara kwanciyarshi. Hotonta yai amfani dashi ya danne na Nuriyya da zai sakashi tunanin abubuwan da zasu addabeshi. Baccin ya fara jin yana fisgarshi 'Hamma kayi addu'a' Yaji muryar Waheedah na fadi cikin kanshi, batare daya bude idanuwanshi ba yayi addu'a, ko tofawa baiyi ba, bacci ya dauke shi. * Washegari da yake ya fada asabar, Ahmad ya dame shi, suka shiga kasuwar wayoyi ya gyara screen din wayarshi tukunna suka dawo. Suna dawowa charge ya saka wayar dan yaga yayi kasa sosai. Yai sallar azahar yazo ya zauna ya fara cin abinci, wayar ya ciro daga chargy ya bude data dinshi yana ci gaba dacin abincin, text dinshi ya shiga ganin wajen sakonnin ashirin, ya kuma san Waheedah ce. Dubawa yayi duka na jin ko yana lafiyane. Zuciyar shi na daukar wani irin dumi da sakonninta ne kadai kan haifar. Tana bashi kulawar da yake so, kulawar da babu wanda yake bashi ita sai Hajja, itama bakowanne lokaci ba. Whatsapp din ya shiga, sakkoninta ne da yawa, zaice ita kadai take turo mishi sakkoni haka, su Nawaf gaisuwace, sai kuma zagi idan ya karanta bai amsa ba. Yassar ma hakan ne, yafi jin dadin nata fiye da nakowa, ita kadaice bata taba magana akan halayyarshi ba, asalima tana saka shi jin babu wani abu marar kyau a abinda yakeyi din. Bata damu dako ya amsata ko bai amsata ba, idan tazo takan sake mishi magana ta kuma bashi labari, Waheedah daban take da kowa na rayuwar shi. Daga farko ya fara karanta sakon, da gaisuwa ce, hirar makaranta. Sai kuma ta fara bashi labarin suna hidimar biki. Karanta sakkonin yake yana cin abinci, kafin yaji shinkafar ta bimishi ta hanyar da bai kamata ba, tari ya kuwa sarqe shi, ruwa ya dauka babu shiri yana kwankwada, amman tarin bai daina ba, ga kirjinshi da yakeji kamar an fara hada wuta a ciki, idanuwan shi harsun kawo ruwan wahalar shaqewar da yayi, hakan yasa shi kankance su yana sake duba sakon Waheedah 'Nikam nagaji sosai Hamma, daman haka hidimar bikin kawa yake? Allah nafi Nuriyya gajiya' Kasa yayi babu shiri yana isa sakonta na karshe 'Hamma har an daura auren Nuriyya fa' Karanta sakon yake yana son fahimtar asalin ma'anar shi, kafin yaji numfashin shi na barazanar daukewa. Kanshi yake girgizawa yana sake danna wayar ko zaiga wani sabon sakon Waheedah din da zai karyata na karshe. "No... No... Wasa ne wannan" Ya furta yana jin zuciyarshi kamar tana rabewa biyu, kullum Waheedah na mishi hira, me yasa bata taba ce mishi Nuriyya zatayi aure ba, sai yanzun ne zata fada mishi an daura mata aure. "Haka nace ki jirani, in nutsuwa waje daya Nuriyya. Nace ki jirani" Yake fadi kamar wanda ya samu tabin kwakwalwa, ji yake gabaki daya duniyar ta hade mishi waje daya. Wayar ya cilla kan gado yana ture abincin, mikewa yayi ya fice daga dakin kwanan nasu. Wajen motsa jiki ya nufa, yana addu'ar kar wani ya tare mishi hanya, dan ko gani bayayi sosai, wani abu yake son duka, idan ba punching bag ba, to fuskar duk wanda tsautsayi ta gifto dashi. Allah ya taimake shi harya karasa wajen motsa jikin baici karo da kowa ba, bai kuma kula ko ana kaucewa bane idan an hangoshi "A. Bugaje..." Ahmad dake wajen ya kira ganin yanayin Abdulkadir din "Ka matsamun Ahmad..." Abdulkadir ya fadi yana karasawa ya dauki abin nade hannu ya fara nannadawa a hannun shi. Ahmad na karasawa wajen shi "Me ya faru? Lafiya? Kaimun magana dan Allah..." Dayan hannun Abdulkadir yake nadewa 'Hamma har an daura auren Nuriyya fa' Shine maganar dake mishi yawo a ko ina na jikin shi tana kara saka kirjinshi wani irin radadi, yasan bacin rai, yasan fushi, yasan abubuwa da dama. Amman yanayin da yakeji yanzun daban ne a rayuwarshi, yanayine da baya fatan ya sake jin shi har abada, dan haka bazai bari ya dame shi ba, zai daki wani abu har saiya daina jin kirjinshi na mishi kamar zai bude. "A. Bugaje..." Ahmad ya kira cike da damuwa a muryarshi, Allah ne shaida yana jin Abdulkadir din kamar dan uwanshi. Bai kuma taba ganin yanayin da yake gani a fuskarshi ba, bai kula shi ba, punching bag din ya soma duka kamar zai jijjigota, da dukkan karfin shi yake dukanta, amman ji yake kamar yanayin da yakeji na karuwa da duk dukan, kamar da tunanin Nuriyya a matsayin matar wani zuciyarshi na kara budewa. Saida yaji numfashin shi na barazanar daukewa tukunna ya daina dukan yana dora hannuwan shi gwiwoyin shi hadi da wani irin sauke numfashi, tukunna ya dago ya hada wata irin zufa. Kankance idanuwan shi yayi yana kallon Ahmad, muryarshi can kasan makoshi yace "Tayi aure. Ahmad tayi aure..." Kai Ahmad ya jinjina mishi yana fahimtar dalilin da yasa Abdulkadir din shiga yanayi, bai magana na ba, dan yaune karo na farko da Abdulkadir din yake fada mishi wani abu mai girma haka "Ta jirani fa in nutsu ne... Shine tayi aure. Ni nace banyi tunanin aurenta bane? Me yasa zatayi aure?" Ya karasa yana sauke numfashi, hannu Ahmad yakai ya taba kafadar shi cikin son nuna mishi yana tare dashi, ya fahimta. Abdulkadir din ya kauce yana fadin "Don't... Kabarni" Ya juya yana ficewa daga wajen motsa jikin, dan iskar da take wajen ta mishi kadan, kanshi kamar zai bude saboda bacin ran da yakeji a cike dashi. Har wani ja-ja yake gani yana gilmawa ta cikin idanuwan shi. Tayi aure bata jira shi ba, shine tunanin da yake cike dashi, yana jin wani yanayi na maye gurbin koma meye yake ji akan Nuriyya...! #TeamAbdulKadir #TeamYassarDinAntyFati #TeamWaheedah #FWA [7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan IG: SufyanLubna Email: Calmlubna@gmail.com Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43 *ABDDULKADIR* *LubnaSufyan* 14 "Sadauki dan Allah... Ka saukake mun auren nan" Muryar Waheedah ta daki kunnuwan shi tana dawo dashi daga dogon tunanin daya tafi, runtsa idanuwan shi yayi yana sake budesu akanta. Dubawa yake ko zaiga alamar wasa a tata fuskar, ko zaiga hijabin da ta saka tsakanin su ta yaye. Kan hannun kujerar dake kusa dashi ya zauna yana maida numfashi, sosai ya girgiza, bazai tuna ranar karshe da wani abu ya girgiza shi haka ba. Kallon Waheedah ya sake yi da yaji kamar kafafuwan shi na rawa saboda tashin hankali. Hannu yaga tasa tana share kwallar da ta tsiyayo kan kuncinta. Kirjin shi yaji yana zafi, gani yake yau din gabaki daya duk wani abu da tasan bayaso takeyi, kamar kuma tana yi dinne dan ta bata mishi rai. "Wahee..." Ya kira muryarshi can kasan makoshi, bata dago ba, taji shi, ta saurara ne ko tsikar jikinta zata tashi kamar ko da yaushe, tsayin shekaru baisa ta daina jin yanayin soyayyar shi ta daban da take taso mata duk idan ya kira sunanta. Wannan karin babu abinda taji banda gajiya da komai, duniyar take ji ta hade da ita a waje daya, kamar tana cikin dakin da babu ko da window ballantana kofa, ji take fitarta daga dakin zata zo da saukake mata auren shi da zaiyi. "Wahee magana nake miki" Abdulkadir ya fadi, yana kokarin danne bacin ran da yake ciki, yanayin da yazo mishi a wahalce, saboda Waheedah ce, bai taba boye wani yanayi nashi ba a tare dashi. Bai taba tsoron bude mata komai nashi ba, tare da ita bai taba jin akwai wannan bukatar ba, idan ranshi a bace yake yana nuna mata saboda tasan yanda zatayi dashi, idan farin ciki yake takan gani. A gabanta yake dariya sosai dan yasan bazata taba raina shi ba, a yar karamar duniyar shi daga ita sai Yassar yake tsokana sosai. Ita fiye da kowa, ko Yassar kanyi shakkar mishi wani wasan, amman cikin ido Waheedah kan kalle shi ta tsokane shi. Ganin tayi shiru har lokacin yasa shi saukowa daga kan kujerar yana tsugunnawa kusa da ita. Hannuwanta ya kamo duka yana rikewa cikin nashi. Kusancin shi bai taba kinyin tasiri akanta ba, yasani, lokutta da dama ko damun shi tayi da surutunta, matsawa zai ya rike hannunta bakinta zai shiru. Idan wani abu yai mata daya riketa a jikin shi yaji ta zagaya hannuwanta a bayanshi yasan ta karbi hakurin shi batare daya furta ba. Yanzun ma hakan yake so yayi amfani dashi kafin komai ya karasa kubce mishi. Ita kanta Waheedah mamaki takeyi, dan tasan abinda yake kokarin yi din, lokuttan duk da yayi tasani, amman hakan bai taba hanashi tasiri akanta ba, wannan karin zuciyarta ta gama bushewa. Hawayen da ke shirin zubo mata taji sun tsaye cik, kamar tabatan da yayi ya kara busar mata da zuciya. Hannuwanta ta zame daga cikin nashi, tana yawata idanuwanta akan fuskar Abdulkadir din "Ka kwashi yaranka, ka bani takardata..." Tai maganar muryarta na mata baqunta cikin kunnuwanta, balle Abdulkadir da yake kallonta idanuwanshi na kankancewa da bacin rai. Kallon shi take, yanayin da take gani a fuskarshi a da zai tsoratata, sosai zuciyarta zata fara rawa da abinda zai faru, amman yau ko a jikinta take ji. Itama ranta a bacen yake, karo na farko da takejin son dora bukatarta sama da tashi. Wani murmushi yayi mai sauti yana mikewa, bin shi da kallo Waheedah tayi ganin ya soma tafiya, amman ba kofa ya nufa ba, hanyar da zata kaishi dakin Anty. Wani sabon zazzabi take ji yana lullubeta, da gaske Abdulkadir yakeyi yaranta zai dauka. Hawayen da suka bushe mata take jin sun fara farfadowa. Tana kallon shi harya bace mata, dakin Anty ya nufa kanshi tsaye. Ko kwankwasawa baiyi ba ya tura kofar yana samunta a tsaye. "Ikram zaki bani" Kallon shi Anty takeyi, tasan taurin kanshi tun yarinta, amman nayau da take gani daban ne, musamman Waheedah, bata taba ganin ran yarinyar a bace irin nayau ba, ko menene Abdulkadir din yai mata mai girma ne. Amman hakan baya nufin tana son ganin mutuwar auren nasu, kodan yara dake tsakani "Abdulkadir karkayi haka, karka yanke hukunci cikin fushi dan Allah. Ka duba yarinyar nan duka watanta nawa a duniyar? Idan zaka tafin ne ma, ka dauki Fajr shi. Kabarta ta huta idan an kwana biyu saika dawo kuyi magana, itama tahau dokin zuciya ne" Kankance idanuwan shi Abdulkadir yayi, yana wani irin sauke numfashin bacin rai, Waheedah ita taja mishi tonon sililin nan. Da ta saka kowa yazo yana tsoma mishi baki a cikin maganar iyalin shi "Kiban yarinyata Anty..." Abdulkadir din ya fadi yana kokarin danne sauran maganganun da suke kan harshen shi. Itama Antyn ranta take ji yana kara baci "Ba zakaji magana ba kenan ko? Ba zaka ji ba ko Abdulkadir..." Runtsa idanuwan shi yayi yana budesu "Idan da naso jin ra'ayinki kan abinda yake faruwa ina da bakin dazan bukaci hakan...kiban yarinyata" Hannu Anty ta saka tana kwance goyon Ikram din, mika mishi ita tayi tana furta "Allah ya shirya" Karbar yarinyar yayi da taketa bacci kamar komai bai faru ba, nutsuwar da take ciki na sakashi sauke numfashi, saida ya gyarata cikin hannun shi tukunna ya kalli Anty "Amin" Ya juya yana ficewa daga dakin, yanda ya doko kofar na saka Anty yin dana sanin marin da taki daukeshi dashi. Sai dai tasan Abdulkadir idan bai rama ba, sai ya gaya mata maganganun da zatayi satika tana juyi dan kunar rai. Wani abin da zai maka koda an samu igiya an kulle shi a baka kulki ka jibgeshi bazaka huce ba. Kan gado ta koma ta zauna, zuciyarta na tafasa. Shikam falon ya karasa yana kallon yanda Waheedah take kallon shi cikin sabon tashin hankali. Hakan ya mishi dadi, gara taga da gaske yaranshi zai dauke, saita tashi su koma gida gabaki daya. Idan rigima takeji zai bata dai-dai wadda zata isheta harda kari idan bukatar hakan ta taso. Waheedah batasan ta mike ba saida taga kallon da Abdulkadir din yake mata. Ta dauka zuciyarta ta bushe, ta dauka babu wani abu dazai sake taba ta, saida taga yarinyarta a hannun shi tukunna takejin yanda yake son rabata da sauran nutsuwar da ta rage mata, muryarta a karye ta soma magana "Me kake so dani? Sadauki me kake so dani haka? Meye ban baka ba? Lokacin da sukazo saura suka samu daga zuciyata, saboda kaso mafi girma na tare dakai..." Shiru tayi tana mayar da numfashin daya taso mata mai hade da kukan da yasa ta kasa karasa maganar data fara "Ki biyoni mu tafi gida, koma menene zamu gyara shi mu biyu..." Abdulkadir ya fadi yana rokonta da duka zuciyarshi da ta amince, saidai a fuskarta yake ganin hijabin da baisan daga inda ta samota ta saka a tsakaninsu ba, hannu tasa ta share hawayenta tana girgiza mishi kai, yanayin daya kara mishi zafin da kirjin shi yakeyi. Kai ya jinjina yana fadin "Kiyi abinda kike so Waheedah..." Ganin ya juya yana shirin barin dakin ya sata furta "Takardata Sadauki..." AbdulKadir bai nuna alamun yajita ba ya fice daga dakin. Aurenta a hannun shi yake, yara nashi ne, zai dauka duk sanda yaga dama. Ya dauka idan yayi amfani dasu zata hakura ta dawo hayyacinta daga rashin hankalin da take ciki. Hakan bai faru ba, zai dauki yaran yanzun, zai tafi dasu. Zai kuma ga wanda ya isa yasa shi sakinta, tonon asirine ta gama yi mishi, abinda bai taba tunanin zata tabayi ba, sosai ta girgiza shi, dan harya shiga bangaren Mami yana mamakinta, yana kuma duba cikin kanshi ko zai tuna asalin laifin dayai mata banda na ranar amman ya rasa. Bai samu Mami a falon ba, Aminu ne zaune da Fajr da hankalin shi gabaki daya akan tom and jerry din da yake kallo a babbar talabijin din dakin. Batare da yayi magana ba ya karasa yana saka hannun shi daya ya dago da Fajr din da a shagwabe yace "Paapi..." Gyara mishi tsayuwa Abdulkadir din yayi yana fadin "Wuce mu tafi..." Da rashin fahimta yaron yake kallon shi da idanuwan shi irin na Waheedah din "Omma fa?" Saida Abdulkadir ya sauke numfashi tukunna yace "Banda ita..." Maqale kafada Fajr yayi, yana shagwabe fuskarshi sosai "Zan zaneka Fajr... Ka wuce nace" Wucewar Fajr yayi dan duk karancin shekarun shi yasan cewa Abdulkadir din zane shi zaiyi kamar yanda ya fadi, kukan shi ma bai bari ya fito ba, dan yana bala'in tsoron duka, ko tsintsiyar kwakwa yaga Waheedah ta fito da ita ta ajiye waje daya zai nutsu. Abdulkadir kuwa ya taba saka charge ya zane shi, sosai yake tsoron yin wani abu a gaban shi. Sai lokacin Aminu yace "Tunda ba zashi ba ka kyaleshi" Kallon shi Abdulkadir yayi yana kafe shi da idanuwa, bai manta maganganun daya fada mishi a asibiti ba dazun, kawai ya kyalene baice komai ba saboda a lokacin yana cikin jin kunyar Mami "Ka mantani ko? Aminu ka manta wanene ni" Kai Aminu ya sauke kasa yana jin zuciyarshi na dokawa cike da tsoro. Bai manta ko waye Abdulkadir ba, haushin shi da yakeji dinma a yanzun ya nemeshi ya rasa "Zan dakeka, zan fasa maka bakin da saikayi sati magana da kowa na maka wahala balle kayi tunanin mun rashin kunya..." Abdulkadir ya karasa yana directing bacin ran nashi kan Aminu. Sosai yake jiran yaron yai motsin da bai mishi ba, ya ajiye Ikram kan kujera ya dake shi kamar ganga. Zuciyarshi zatai mishi sanyi ko yaya ne idan ya zane wani, tunda bazai iya zane Waheedah da ta bata mishi ran ba. Amman Aminu ko dago dakai baiyi ba ballantana yai kokarin cewa wani abu. Kai Abdulkadir din ya jinjina ya juya ya kama hannun Fajr yana janshi suka nufi hanyar da zata kaisu harabar gidan inda motarshi take a ajiye. * Yassar ya hango ya bude motar shi ya fito, cikin shigar manya kaya da hula da suka kara mishi wani irin kwarjini. Tsaye Abdulkadir din yayi batare daya san dalili ba, yana nan har Yassar din ya karaso ya same shi "Ina kuma zakaje da yara?" Yassar ya bukata, yana kai hannu ya dafa kan Fajr daya fada jikin shi yana fadin "Uncle..." Yana gidan shi a kwance yaga wayar Hajja. Saida zuciyar shi ta doka, dan yasan ba lafiya ba, indai Hajja zata daga waya ta kirashi sai da wani babban dalili. Baiyi mamakin jin dalilin Abdulkadir bane ba. "Bakaimun sallama ba Hamma..." Abdulkadir ya fadi yana kankance idanuwan shi, dan yaga yanayin Yassar din shima yasan abinda yake faruwa. Wani irin kallo Yassar ya watsa mishi "Yaran ka dauko? Ka sake tan?" Kai Abdulkadir ya girgiza mishi, hannu Yassar ya mika yana karbar Fajr da Abdulkadir din ya kasa hanashi "Nasan baka da hankali ko kadan, amman banyi tunanin yakai haka ba. Gidan ubanka zakaje da jaririya? Ko Nuriyyar ce zata shayar maka da ita?" Sosai Abdulkadir ya dakuna fuskarshi "Karkai mun fada Hamma, idan zaka dauki sides saika tsaya kaji nawa bangaren tukunna" Tsaki Yassar yaja, da yace bazai sake shiga matsalar Abdulkadir din ba, yanzun ma dan Hajja ta kirashi shisa ya dauko kafarshi yazo. Hannun Fajr ya kama yana shirin raba Abdulkadir din da nufin wucewa "Hamma ina zakaje mun da yara?" Kallon shi Yassar yayi "Idan ka biyoni saina watsa maka mari, mahaukacin banza..." Murya can kasa Abdulkadir yace "Yarana, a gaban yarana Hamma..." Tsakin Yassar ya sake ja yana wucewa abin shi, yanajin Abdulkadir din na biye dashi. Baiko juya ba harya karasa bangaren Anty, tunda Hajja tace mishi suna can data kira. Waheedah ya samu ta hada kanta da kujera, yanayin ta nasa wani abu tsaya mishi a rai, dagowa tayi fuskarta harta tara jini saboda kuka. Sosai Yassar yaji kirjinshi yayi nauyi. Karasawa yayi ya zauna kan kujerar yana mika mata Ikram. Da sauri ta karbi yarinyar tana riketa a jikinta, duminta na saukar mata da wata irin nutsuwa taban mamaki "Nagode Hamma..." Ta fadi cikin wata irin murya da tasa Yassar sake kallon Abdulkadir din yana watsa mishi wani kallo. Kankance mishi idanuwa Abdulkadir din yayi, ya dauka Yassar na bayanshi, kamar ko yaushe akan abubuwa da dama. Tun a watanni baya yagane cewa shima bayan Waheedah yake, bashida matsala dan Yassar yaso Waheedah, ko bakomai kanwarshi ce, amman shima kaninshi ne, kuma yana da kishin da bayaso a fifita soyayyarshi akan ta kowa. Ko Hajja bayason yaga tana nuna ma su Yazid soyayya fiye da wadda take nuna mishi. "Kiyi hakuri Waheedah..." Kai Waheedah ta girgiza ma Yassar da takejin maganar shi kamar ya watsa mata ruwan zafi. Shima kan yake girgiza mata yana saurin dorawa da "Ba ina nufin kiyi hakuri da koma menene yai miki ba..." Da mamaki Abdulkadir yake kallon Yassar "Hamma?" Ya kira, ko kallon shi Yassar baiba, asalima maganar da yakeyi yaci gaba "Idan nan din zasu dameki ki tashi mu tafi gidana..." Wani murmushi mai sauti Abdulkadir yayi da bashida alaqa da nishadi "Kana magana kamar izinin fitarta yana hannun ka" Zama Waheedah ta gyara tana daga Ikram ta mike, towel dinta ta zame ta sakata a bayanta. Goya yarinyar tayi a bayanta. Kamar yanda Yassar din ya fadi, tana bukatar hutu, bataso kowa ya dameta ko yayi kokarin bata hakuri, tana kuma da tabbacin Yassar bazai bar kowa yazo ya dameta ba. Zata jira takardarta a gidan shi. In yaso daga baya ta dawo gida. Dan daman batayi niyyar zama bangarensu ba, balle Mami ta tambayeta meya faru. Batasan ta inda zata fara ba, ya saukake mata shine abinda tafi bukata. "Ina zakije?" Abdulkadir ya bukata yana kallon ta cike da sabon mamaki "Ka aikomun takarda ta gidan Hamma, ko kabama Abba, duk wanda yafi maka sauki dai" Tai maganar tana kallon Yassar da fadin "Hamma muje..." Ta kama hannun Fajr, bai cika yawan magana ba, amman bai taba tunanin zai rasa abin cewa gabaki daya ba sai yanzun, dan ba kalaman shi bane kadai suka kubce mishi, harda abinda ya kamata yai tunanin da ya wuce tsananin mamaki. "Waheedah tsinuwar mala'iku da duk takun da zakiyi batare da izinina ba..." Ya tsinci kanshi da furtawa ganin ta saka kafarta daya wajen dakin. Juyowa tayi da wani irin yanayi a fuskarta "Tunda safiyar yau nake zubar da hawaye, kuma kaine sila, tsinuwar zatai balance Sadauki... Ina jiran takardata" Ta karasa tana ficewa daga dakin. Wani murmushi Yassar yayi, tunda ya san yarinyar bai tana tunanin tana da kwarin gwiwar karbarma kanta 'yanci ba sai yau. Lokutta da dama yakanji kamar harda laifin shi a abinda take fuskata na zama da Abdulkadir, yakanji a kaso dari ma aurenta da Abdulkadir yana da hannu cikin kashi tamanin harda doriya. Musamman watannin baya haka yakejin duk laifin shine, amman yanzun ta fara rage mishi nauyi. Duk da can kasan zuciyarshi bazaiso mutuwar aurenta ba, amman hakan bazai hanashi goyon bayan gaskiya ba. Wannan karin son Abdulkadir baizai rufe mishi idanuwa ba. Batare dayace komai ba yabi bayanta. ** Bazai ce ga yanda yakai gida ba, nutsuwar shi bata taba kwacewa akan tuqi ba sai wannan karin. Bangaren Waheedah ya wuce yana shiga har dakin baccin su, wannan karin takalman shi ya cire bayan ya zauna kan gadon tukunna ya kwanta. Pillow dinta ya dauka yana rikewa a jikin shi, kamshin turarukan ta ya shaka yana lumshe idanuwan shi. Yakanyi kewarta duk idan yazo ya koma wajen aikin shi. Bai taba tunanin zai kewarta yana gida ba, amman ya fara, cikin kasa da awa biyu komai ya birkice musu. 'Sadauki zaka karyani...' Yaji muryarta cikin kanshi data saka shi bude kananun idanuwan shi, kafin ya sake mayarwa ya rufe su yana kara matse pillow din a jikin shi, sanyin shi na sake tunasar dashi cewa ba ita bace ba "Ba zakimun haka ba, Waheedah ba zakimun haka ba..." Ya furta a hankali yanajin an kwankwasa kofar dakin, wata irin dirowa yayi daga kan gadon "Nasani, nasan ba zaki

Chapter 14 of 37