AbdulKadir, dan wallahi na kasa wrapping din kaina akan maganar nan"
Kallon shi AbdulKadir yayi
"Yaushe Abba ya zama abokin wasana? Meye wahala a fahimtar maganganun da nayi? Auren
da zan kara ne yake maka wahalar fahimta?"
Numfashi Yassar yake ja yana fitarwa a hankali, da alama idan bai kai zuciyarshi nesa ba, mota
zai koma yajata ya take AbdulKadir din duk su huta.
"Bansan me kake so ince maka ba Hamma... Bansan me yasa kazo kana kallona kamar akwai
haramci a cikin abinda nake so inyi ba"
AbdulKadir yake fadi ranshi inyai dubu kowanne a bace yake, tun a hanya yake jin maganganun
daya fadama Abba suna dawo mishi, abin na mishi kamar mafarki, yana kasa yarda da abinda
yake shirin faruwa din. Amman zuwan Yassar ya kara tabbatar mishi da cewa auren zaiyi babu
fashi. Dan baiga dalilin da zaisa Yassar ya dinga mishi kallon da yake mishi ba. Kai Yassar yake
girgizawa, muryarshi a gajiye yace
"Bani da matsala da auren ka, wadda zaka aura din ce damuwata, me yasa sai ita? Kawarta ce
AbdulKadir..."
Kankance mishi idanuwa AbdulKadir yayi
"Sai me ya faru dan kawarta ce? Haramun ne in auri kawar ta?"
Dafe kai Yassar yayi da yakejin wani irin ciwon kai ya dirar mishi. Ga zuciyar shi dake zafi, in
har yanajin haka da abinda AbdulKadir yake shirinyi, baisan ya Waheedah zataji ba
"Ka daina yin kaman mai asthma Hamma, bazai sa in fasa auren nan ba. Bansan me yasa
Abba zai fada maka ba, tunda ai zan gaya maka da kaina daman"
Da hannuwa biyu wannan karin Yassar ya tallafe fuskar shi. Da ance mishi akwai ranar da zata
zo da zaiji bayason ganin AbdulKadir zai karyata, amman abinda yake ji yanzun, maganganun
AbdulKadir din ko kadan bayason gani. Dashi ake jinjina maganar matan da suke cakawa
mazajen su wuka duk idan hakan ya faru, AbdulKadir yasa shi fahimtar kadan daga cikin dalilin
da maza suke ba matansu har shaidan yai galaba akan su, su hau dokin zuciya su aikata
abinda zaisa ka su dana sani daga doron duniyar har lahira.
Idan akwai mazaje dari irin AbdulKadir, yana da tabbas lahirar mata da yawa zata raunana,
zasu zama barazana da kwanciyar kabarin mata da dama. Fuskar shi Yassar ya bude yana jan
wani irin numfashi ya fitar dashi rai a bace
"Babban kuskuren rayuwar Waheedah shine amince ma auren ka"
Wannan karin AbdulKadir ne yaja wani irin numfashi, kai yake girgizawa
"Baka fadamun maganar nan ba Hamma, ka janye kalamanka..."
Mukullin shi Yassar yake lalubawa cikin aljihu, ya kuwa yi nasarar ciro shi yasa a jikin murfin
mota ya bude. AbdulKadir ya mayar da murfin yana rufewa, ya kuma rike hannun kofar gam.
Muryarshi can kasan makoshi yake cewa
"Hamma ka janye kalaman ka, dan Allah ka janye ko zasu rage mun zafin da sukeyi..."
Tsaki Yassar yaja
"Ka matsamun daga jikin mota kafin in kwada maka mari AbdulKadir.... Wallahi yanda nake ji
komai zai iya faruwa..."
Kallon shi AbdulKadir din yakeyi, a tsayin rayuwar shi yaune rana ta farko da Yassar ya fada
mishi maganganun da yakejin ciwon su har cikin kasusuwan shi, akan maganar abinda addini
ya halarta mishi ta kowacce fuska. Yasha ganin ya ta mutu, kanwarta ta auri mijin, baisan me
yasa nashi zai banbanta ba.
"Me yasa zaka fadamun haka? Hamma me yasa? Saboda nace zan auri Nuriyya? Dan zanyi
abinda Allah bai haramtamun ba...ya tana mutuwa, mijin ko bai nuna yana son kanwar ba a
bashi, me yasa nawa zaiyi maka zafi haka?"
Ture shi Yassar yayi yana fadin
"Mahaukaci ne kai wai? Dan ubanka allurar sojojin kai ka miqa musu suka caka maka ita?
Addini bai haramta maka auren Nuriyya ba, amman al'ada ta haramta maka shi, kunya ta
haramta maka, ko mutuwa Waheedah tayi ka nuna kana son auren ta, akwai mutane da yawa
da zasu ga rashin kyautawar haka... Ka matsamun AbdulKadir, ka matsamun in
wuce...mahaukacin banza marar tunani"
Yassar ya karashe yana kara sa hannu ya ture AbdulKadir din, ya bude motar shi ya tayar.
AbdulKadir nabin shi da kallo harya fice daga gidan. Bai ce mishi komai ba, saboda yaga alama
Yassar din marin shi zaiyi idan ya sake magana, a karo na farko kuma da yasan inya mare shi
ramawa zaiyi, dan shima ran nashi ya gama baci. Yafi mintina goma a tsaye a wajen, kafin ya
iya wucewa ya shiga gida. Kai tsaye daki ya shiga yana wucewa bandaki ya sakarwa kanshi
ruwan sanyi ko zai samu sauqin abinda yakeji.
Daga shi sai towel ya fito, ya samu gajeran wando ya saka, Waheedah har tayi bacci ya hau
kan gadon yana matsawa gab da ita. A hankali yake girgizata
"Wahee.... Waheedah..."
Bude idanuwanta tayi cike da bacci tana jin fitilar dakin dake kunne ta shigar mata idanuwa
yana sa ta mayar dasu ta rufe babu shiri.
"Ki tashi Waheedah.... Kinji... Kimun hira"
AbdulKadir ya karashe yana kara girgiza ta, bude idanuwan ta tayi tana kallon fuskar shi
"Banajin dadi Sadauki... Dan Allah kabarni inyi bacci"
Kai ya girgiza mata, ita batajin dadine, shi zuciyar shi zafi take mishi kamar kirjin shi zai bude,
hannunta ya kamo ya dora kan kirjin shi inda yakeji yana mishi ciwo na gaske
"Wahee raina a bace yake, zuciyata zafi take mun wallahi, Hamma ya batamun rai"
Yanda ya karashe maganar yasa ta mikewa, sosai take kallon shi, idanuwan shi harsun canza
launi saboda bacin rai, tashi zaune tayi tana jingina bayanta da gadon, zazzabine ruf a jikinta,
tashin da AbdulKadir din yai mata yasa har amai takeji. Ganin ta tashi yasa shi barin pillown shi
yana komawa kan cinyoyinta ya kwanta, ya kama hannunta ya dora kan fuskar shi yana neman
sauqi koya yake.
"Kayi hakuri dan Allah... Kome zai fada maka nasan baya nufin kalaman, bacin rai ne kawai...
Daya huce shikenan, kayi hakuri"
Ta fadi a tausashe, kara naniqe mata yayi, ba zata iya hana shi ba, duk da zazzabin da take ji,
yanayin shi ya gama raunana tata zuciyar, indai zata sama mishi sauki koya yake zata kokarta.
Biye mishi tayi, bata samu yayi bacci ba sai wajen karfe biyun dare. A daddafe ta shiga bandaki
tana dubawa ko da ruwan zafi dan basu bar wutar ta zauna ba. Dakyar ta iya watsa ruwa, ga
wata yunwa da take wujijjigata, kitchen ta wuce ta duba sauran abincin da yake tukunya, ba
zata iya cin shi da sanyi ba, dan haka ta dora tayi warming.
Ta dauko plate kenan ta fara zubawa taji takun AbdulKadir din, kafin ta juya ya rungumeta ta
baya, muryarshi cike da bacci yace
"Shine kike barni ko?"
Numfashi ta sauke
"Yunwa nakeji...ka koma ka kwanta, da naci abinci zan dawo..."
Tanajin shi yana girgiza mata kai, ko daya farka baiji ta a kusa dashi ba ranshine yaji yana shirin
kara baci. Ya duba bandaki bai ganta ba, shisa ya fito nemanta.
"Sadauki dan Allah... Karka karyani"
Magana yai mata data tsaya iya kunnenta, ta ture shi tana dariya. Abincin ta zuba, falo ta koma
yabita ya zauna a gefenta. Wani lokaci har bataso a bato mishi rai, in kuwa ya faru gara ta
tambayeshi ya sauke mata fadan shi da ya shiga yanayin nan da ko bandaki ta shiga tabar shi
saiya bita. A kanta abin yake karewa, yanzun din kuma yaki fahimtar ba ita kadai bace itama, ko
karfin kirki bata dashi. Yabarta taci abincin a nutse yaki, sai murza ido yake yana hamma, gashi
rabin jikin shi a kanta yake. Samu tayi tagama suka wuce suke kwanta.
*
Tunda ya dawo sallar asuba yaga sakon Hajja
'Ka zo ina neman ka'
Wayar ya kashe gabaki daya. Zai je inya tashi, saiya gama baccin safen shi amman. Waheedah
kuwa dankalin Hausa taji tana marmari, tana dashi dan haka ta fere bayan ta idar da sallah, ta
yayyanka ta zuba a karamar roba ta saka ruwa. AbdulKadir na dawowa Masallaci yaga tana
karatun Qur'ani ya samu waje ya zauna a gefen gado, tana idarwa ta ajiye ta cire hijab din ta
wuce kitchen yabi bayanta.
"Yanzun Waheedah sai kin soya dankalin zamu kwanta? Bacci fa nake ji"
AbdulKadir da yake tsaye yace ma Waheedah da take share wajen da ta bata. Indai bacci ne ta
fishi bukata, tunda bai bari ta samu na kirki ba, yama fita samun baccin, batace mishi komai ba.
"Ke kadai nake ma magana kijini kuma kiyi shiru"
Abin kwashe shara ta saka cikin dustbin, ta wanke hannunta tukunna ta kalle shi da fadin
"Yi hakuri... Muje"
Kankance mata idanuwanshi yayi da suke cike da rikicin da bata da karfin biye mishi. Kwanciyar
sukai, sanda ta tashi karfe goma, ruwa ta watsa ta saka doguwar riga ta material da farar hula
tukunna ta wuce kitchen tana dora mai dan ta fara soya dankalin. Idan AbdulKadir ya tashi zai
fara mata maganar abinci ne tasani, kuma tashin zaiyi, dan daya laluba yaji bata kusa dashi
tashi zaiyi.
Tana sauke kaskon farko AbdulKadir din na fitowa daga shi sai towel
"Baki dauko mun kayan da zan saka ba"
Ya fadi, in tace yaje ya dauko da kan shi dogon surutu zasuyi, kuma karshe ita zata dauko
mishi, sauran dankalin ta juye ta wuce daki ta dauko mishi farar riga marar nauyi da wani three
quarter mai igigoyi daga kasan, sai singlet da boxers, turare ta fesa mishi a jiki tana ajiye mishi
kan gadon. Murmushi yayi mata yana sa hannu ya taba fuskarta
"Ya kuka tashi? Ya jikin ki?"
Murmushi Waheedah tayi
"Baka tambayi jikina ba sai da kagama sani aiki ko?"
Yar dariya yayi, ta gaishe shi da asuba, ya tabata yaji babu zazzabin, bai dai tambaya bane sai
yanzun. Ganin yayi shiru yasa ta fadin
"Mun tashi lafiya. Kasa kaya, kar dankalina ya kone..."
Kafin ya amsa ta juya da sauri ta fice daga dakin. Albasa ta yanka dan tana so, ta zuba a cikin
wancen data kwashe, na biyun bai karasa ba har AbdulKadir ya fito, falo ya wuce ya zauna
yana jiranta, tana gamawa ta hada mishi shayi ta zubo dankalin ta fito. Ci sukayi suna hira,
suna gamawa yace mata zaije gida. Rakashi tayi har kofa tukunna ta dawo ta hada
wanke-wanke tayi, ta goge kitchen din tukunna ta koma dakin su ta gyara gadon, batajin zata
iya share shi tunda ba dauda yayi ba, kuma batama jin dadin jikinta. Komawa tayi ta kwanta
tana tunanin abinda zasuci da rana.
*
Gida ya shiga, bai samu Hajja a falo ba, ya wuce dakinta yana kwankwasawa, ya tura bayan ta
amsa hadi dayin sallama. A zaune ya sameta kan gado ta mike kafafuwanta ta saka glass din
karatu da littafin 'Tarihin Annabi Kamalalle' a hannunta tana karantawa.
"Hajja..."
Ya fadi cikin sigar gaisuwa, littafin ta ajiye tana cire gilashinta shima ta ajiye shi a gefe. A nutse
take kallon AbdulKadir
"Menene matsalarka? AbdulKadir yau kam ka gayamun menene matsalar ka"
Da mamaki a fuskar shi yake kallon Hajja yana girgiza mata kai
"Bani da matsalar komai Hajja"
Numfashi ta sauke
"Kawai wulakanci ne kenan ko? So kake kaja mana abin magana shisa kake so ka auri
Nuriyya... Itama Nuriyyar dan ubanta idan tana da kunya ai ko mutuwa Waheedah tayi idan
kazo mata da wannan maganar za ta dubi amintakar dake tsakanin su taki amincewa. Amman
naga alama yanda kasa kafa ka shure duk wata kunya da ake halittar dan adam da ita haka
itama tayi fatali da tata"
Gefen Hajja AbdulKadir ya zauna yana fadin
"Hajja akan maganar ne kema kike so ki bata ranki? Me yasa bazan aureta ba bayan addini ya
halarta mun, me yasa kuke son haramtamun abinda Allah bai...."
Kara yaji cikin kunnen shi na haggu da ya katse mishi maganar da yake shirinyi, kafin daga
baya ya fuskanci abinda ya faru. Hannun shi yasa yana taba kuncin shi cike da tsantsar
mamaki.
"Hajja... Marina kikayi Hajja... Mari Hajja"
Kai ta jinjina mishi tana fadin
"Ina gab da kara maka wani in baka bacemun dagani ba wallahi. Tunda kai bakasan abinda ke
maka ciwo ba, abinda duk kaga dama shi kake son yi.... Aure ko? Auren cin amana, ayi lafiya
AbdulKadir, wallahi ba baki nai maka ba, alhakin Waheedah bazai barku ba"
Hajja ta karasa maganar tana kokarin tarbe hawayen da takejin sun cika idanuwanta dan
takaici, rokar mishi yafiyar Allah take da yanda ya bata mata rai kar wani abin ya same shi.
Mikewar yayi kuwa, baya niyyar bata hakuri koya ce mata ya fasa auren. Muryar shi can kasan
makoshi yace
"In kin huce kimun addu'a Hajja..."
Ya wuce yana fita daga dakin, yaja mata kofar a hankali, yanajin yanda ita kadaice zata mishi
abinda tai mishi din. Duk da ran shi yakai koluluwa a baci. Daga jiya zuwa yau, abinda Abba yai
mishi, Yassar, yanzun kuma ita. Kamar tunzura shi sukeyi da son yin auren, dan yanajin bashi
bane mutum na farko da addini ya halarta ma abu al'ada ta haramta mishi. Zai dai zama cikin
mutane kalilan da ba zasu taba barin al'ada tayi nasara akan su ba.
Yana fita daga gidan, machine ya tare yahau zuwa zoo road, rabon shi da gidan kanin Abba,
Alhaji Ali da suke kira da Kawu Ali, harya manta. Amman shi kadai ne mutumin da yake da
yakinin zai tsaya mishi kan maganar, dan a gidan su Abba kaf shine yake dan boko na gaske,
kuma mutumin da ko a yaran shi zaka fuskanci wayewar da suke tafiyar da rayuwar su a kai.
Duk da a baya AbdulKadir din kanyi tir da kalar tarbiyar tasu, yau dai Kawu Ali zai mishi ranar
da bai zata ba.
Da yake ranar lahadi ce, babu aiki, ya kuwa yi nasarar samun Kawu Ali a gida. Fada mishi
abinda yake faruwa yayi, sosai Kawu Ali ya jinjina maganar
"Shima Alhaji yana da matsala wallahi, yanzun da kuzo kuna abinda bai kamata ba ai gara ayi
auren. Kayi hankali da kazo ka sameni da maganar, kaje abinka, zan kira shi muyi magana in
shaa Allah"
Dan jim AbdulKadir yayi kafin yace
"Gobe in shaa Allah zan wuce ne Kawu, nafi so a gama maganar kafin in tafi"
Kai Kawu Ali ya jinjina yana fadin
"Bari in kira shi yanzun inji idan bai fita ba, sai muje gidan"
Gyara zama AbdulKadir din yayi, yana sauraren Kawu Ali ya kira Abba, bayajin me Abban yake
cewa. Amman da alama baya gida, Kawu Ali na sauke wayar ya kalli AbdulKadir
"Sai da dare, ya fita. Amman karka damu in shaa Allah komai zaiyi dai-dai"
Godiya AbdulKadir yaima Kawu Ali tukunna ya wuce, gida ya nufa, a kitchen ya samu
Waheedah tana ta aikin da baisan na menene ba, falo ya koma ya kwanta kan doguwar kujera.
Babu abinda yake so sai yaga an daura auren ya gama da wannan matsalar, ganin tunani zai
mishi yawa inya kwanta yasa shi tashi yabi Waheedah kitchen din
"Me kike dafa mana?"
Kallon shi tayi tace
"Dambun shinkafa"
Murmushin da yai mata yasa taji gabaki daya wahalar dambun ta bace mata
"Ina son shi sosai"
"Nasani... Harda zobo na dafa mana, shi zan hada yanzun"
Murmushin AbdulKadir ya sake yi mata, a cikin gidan su ya baro marin da Hajja tai mishi, dan
bazai saka abin a ranshi ba. Abu daya da kowa bai sani ba shine yana da Waheedah, babu
wani abu da zai bata mishi rai fiye da rana daya. Zatayi wani abin da zaishi ranshi kal, kamar
yanzun din ma, gashi duk da hasken da yake ganin ta kara, ta mishi kyau cikin riga da skirt
dinta, dankwalin ta daura shi simple, da jan jambaki a labbanta da tunda ta kula yana so take
sakawa, dan ita kwalliya ba damunta tayi ba.
Ganin yana matsowa cikin kokarin hade space din sake tsakanin su yasa ta nuna shi da ludayin
hannun ta tana matsawa baya
"Sadauki aiki nake wallahi, dan Allah kaje kayi zamanka, zobo zan hada kaga.... Kaji"
Dariya AbdulKadir yayi yana ja ya tsaya, har saida ta karasa wajen kantar kitchen din, tukunna
ya taka yana taba fuskarta zuwa wuyanta
"Ni zanji ko da zazzabi a jikinki ne kawai..."
Murmushi tayi, tasan halin shi sarai. Shiya miko mata robar sukari ta hada zobon da zallar shine
yasha kayan kamshi, sai flavor din abarba da tadan diga na ruwa. Da dumin shi haka
AbdulKadir yace mata shi yana sha. Dole ta zuba mishi tukunna ya fitar mata daga kitchen din
yana komawa falo, taci gaba da aikinta.
*
Kafin isha'i Kawu Ali ya kirashi da su hadu a gida. Dan haka yana fitowa daga masallaci yahau
machine ya wuce. Dakin Abba ya nufa, zuciyar shi a dake yake jinta. Dan ya gama yanke
hukuncin duk abinda zasu fada bazai canza ra'ayin shi ba. Da sallama ya shiga dakin Abban
yana samun shi zaune da Kawu Ali. Wani irin kallo Abba yabi shi dashi da yake jin yana neman
sanyaya mishi jiki.
Yana zama kuwa kamar jiran shi Abba yake
"Ni ban isa ba ko AbdulKadir? Ban isa da kai ba kake son nuna mun, kuma nagani. Allah yai
maka albarka ya kuma shiryeka.... Aure ayi lafiya amman wallahi babu hannuna a maganar"
Numfashi Kawu Ali ya sauke, ya bude baki zaiyi magana Abba ya katse shi da fadin
"Ku biyun tashi zakuyi kubani waje, kai boko ta hanaka ganin aibun abinda zaiyi, shikuma taurin
kai ko? Allah ya bada zaman lafiya, sai kuje kuyi duk abinda kuke so, bana son jin kowacce irin
magana indai kan auren nan ne..."
Ganin sun zauna yasa Abba mikewa ya shige bedroom din shi yana barinsu. AbdulKadir kan shi
a kasa yake, tunda yake da Abba bai taba ganin ranshi ya baci haka ba. Shi kan shi Kawun jikin
shi a sanyaye yake jin shi.
"Abbanka yace yarinyar nan makota take, kuma bazawara ce, abin bazaiyi wahala ba....da
Babanta yana nan ma sai mu fara magana"
Mikewa AbdulKadir yayi yanajin shi kamar yana yawo a gajimare, komai yake jin yai mishi wani
irin shiru.
"Sai mu duba mugani"
Ya fadi, muryar shi na dawowa kunnuwan shi da wani irin yanayi. Tare da Kawu suka fita har
kofar gidan su Nuriyya, sallama sukayi da Babanta, ya kuwa fito, yagane AbdulKadir din,
amman yayi mamakin ganin su a kofar gidan. Gaishe dashi AbdulKadir yayi yanajin Kawu Ali na
mishi bayanin komai. Sosai Baba ya nutsu yana sauraren su. Duk yanda yake son sakama
Nuriyya ido, zai karya idan yace matsalar yarinyar bata damun shi tana kuma bata mishi rai.
Alhaji Ahmad mutum ne da yake gani da matuqar mutunci, kuma yana taimaka mishi sosai da
sosai. Ba zaiso Nuriyya ta zama sanadin da wannan zumuncin da suka shafe shekaru suna
ginawa ya zube ba. A nutse yace ma kawu Ali
"Ku bani mintina biyar in dawo"
Cikin gida ya shiga ya sa aka kira mishi Nuriyyar, muryarshi babu alamun wasa yace
"AbdulKadir ne yaron Alhaji Ahmad da Kawun shi suka zo kan maganar auren ki"
Dagowa tayi ta kalli Baba tanajin ta kamar a mafarki, text din karshe da AbdulKadir yayi mata
shine
'Karki kirani, ki jirani zanma Abba magana'
Bata kirashi din ba kuwa, da zullumi ta kwana fal ranta, ko abinci sai dazun da magriba ta tura
shi badan tana gane kanshi ba, haka kawai zuciyarta rawa take mata. Gani take ko sama da
kasa zasu hade ba za'a bari AbdulKadir ya aureta ba, yanzun kuma da Baba yazo mata da
maganar sai take ganin kamar mafarki take.
"Kinga abinda kikai mana aurenki na farko, badan bana miki addu'a ba, amman wallahi ban
taba tunanin zaki sami namijin da yake da masuyi mishi fada bayan yayi bincike yaji abinda ya
fito dake daga gidan mijinki su barshi ya aure ki. Idan za'ayi magana ta gaskiya ni bazan bari
dana ya aureki ba. Zuwa nayi in tambayeki dan idan kika kaso wannan auren ki nemi inda zaki
wuce daga gidan mijin, wallahi Nuriyya ba zanyi kaffara ba, kika kaso auren nan ba zaki zauna
mun a gida ba"
Kai ta daga mishi, haka kawai idanuwanta na cika da hawaye. Juyawa Baba yayi ya koma kofar
gidan ya samu su AbdulKadir yana fadin
"Idan yanzun kun shirya ma ana iya daura aure tunda ba budurwa bace"
Ware idanuwa AbdulKadir yayi, yana da inda zai ajiye Nuriyya, yana da kudin Sadaki da zai
bayar, amman akwai su lefe da sauran kananun abubuwa, duk da an tayashi bikin Waheedah
bazai manta kalar kudaden daya tara ba.
"Baba akwai su lefe"
Dariya Kawu yayi yana cewa
"Kayya AbdulKadir... Ai ta taba wani auren, za'a iya daurawa yanzun, duk da gaggawa na daga
shaidan, amman auren za'a iya daurawa sai kuyi maganar lokacin tarewa da sauran abubuwa"
Kai AbdulKadir ya daga yana fadin
"Babu kudi a jikina, sai dai inje banki in dawo yanzun"
Jinshi yake kamar a mafarki, kai Kawu Ali ya girgiza mishi yana fadin akwai kudi a wajen shi.
Mota suka koma Kawu Ali ya kirgo dubu hamsin suka sake fita, masallaci sukaje akayiwa Liman
magana, da wasu manyan mutane da suke zaune a majalissa nan gefen masallacin. Cikin kasa
da mintina talatin aka daura auren aka gama komai. Kawu Ali da kanshi ya sauke AbdulKadir
har gida dan yace mishi bada mota yazo ba.
Ya shiga cikin gidan, ya dora hannun shi kan handle din kofa, amman ya kasa murzawa, komai
daya faru yakeji yana danne shi, kamar wani mafarkine yakeyi sai yanzun ya farka ya samu
mafarkin da gaske ne. Aure yayi, Nuriyya ya aura, ba wannan bane damuwar shi, bai fadama
Waheedah ba, bai kuma san ta inda zai fara fada mata ba...!!!
#TeamWaheedah
#TeamAbdulKadir
#LubnaSufyan
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
23
BABBAN ASIRIN DA MUKE FAMA DA SHI A AL'UMMAN CE SHINE SON ZUCIYA. LOKUTTA
DA DAMA MUKAN DORA ALHAKIN ABUBUWA MASU YAWA AKAN KALMAR ASIRI DAN
GUJEMA FUSKANTAR AINAHIN GASKIYA.
FOR ANTY FATINA (Batul Mamman) SonSo mai tarin yawa 💕
Yakanji mutane na fadin gwiwoyin su sunyi sanyi, akwai lokutta da yawa da zaice ya taba jin irin
yanayin, baisan asalin yanda yake ba sai yanzun da yake a bakin kofar gidan shi amman ya
kasa shiga.
"Oh Allah na"
Ya tsinci kan shi da fadi ganin da gaske shine a tsaye bakin kofar gidan shi ya kasa shiga.
Lumshe idanuwan shi yayi yana bude su hadi da sauke numfashi, duk wani sauran karfi da
yake jin ya rage mishi ya tattaro ya murda hannun kofar dashi. Kafafuwan shi da yakeji kamar
itace saboda nauyin da sukai mishi yaja yana shiga cikin gidan dayin sallamar da ta tsaya cikin
makoshin shi. Gyaran murya yayi yana sake yin sallama, amman duk da haka a hankali yaji
muryar shi ta fito.
Dakyar yaja kafafuwan shi zuwa bedroom din su, ko sallama sai bayan ya tura ya shiga yayi ta.
Amsawa Waheedah tayi, tana jera kaya a wardrobe din dakin da take cikin bango.
"Takalma Sadauki... Saboda kai bana sallah a tsakar daki saina saka darduma, ko ina
shigarmun kake da takalma..."
Nan inda yake ya tsaya ya kwance igiyar takalman da suke kafarshi yana zame su tukunna ya
karasa cikin dakin ya zauna kan gado.
"Sannu da aiki..."
Ya furta da wani irin sanyin murya da yasata barin abinda takeyi ta juyo tana kallon shi.
"Sadauki?"
Waheedah ta kira cike da alamun tambaya, dan yanayin shi gabaki daya ya bata tsoro, ganin
bai dago ba, asalima sake sukunyar da kan shi yayi, yasa ta rufe wardrobe din tana karasawa
ta zauna kusa dashi. Kafadar shi ta dafa tana fadin
"Lafiya? Me ya faru? Menene? Wani bashida lafiya a gida?"
Kai AbdulKadir yake girgizawa da duk tambayarta, amman ya kasa dagowa ya sauke idanuwan
shi cikin nata. A karo na farko da yake tir da gaggawa kan al'amura batare da tunani ba.
Saboda bai taba tunanin zaiji abinda yakeji din ba yanzun, ya rasa karfin gwiwar fuskantar
Waheedah ya fada mata yayi aure, an daura mishi aure, matsalar shi ba gaya mata da wa aka
daura mishi auren bace a yanzun, ta inda ma zai fara mata maganar auren.
Kan shi ya dora a kafadarta yana sauke wani irin numfashi
"Waheedah...."
Ya fadi cikin wani irin yanayi, hannunta ya kamo ya rike yana rasa kalaman da zaiyi amfani
dasu. Da Hajja bata mishi fushi sai ya kirata tazo ta taimaka mishi ta fadama Waheedah din, ko
Yassar ma, wani dai ya fara fada mata dan shikam har wani zazzabin tashin hankali yakeji ya
fara rufar mishi.
"Kana bani tsoro Sadauki... Na kasa yarda komai lafiya"
Waheedah tace tana dumtsa hannun shi da yake cikin nata. Idanuwan shi ya lumshe da
maganganunta yanajin komai yai mishi tsaye cik. Waheedah ce, Waheedahr shi. Ta ina zai fara
fada mata ya kara aure batare da saninta ba, sai yanzun tunanin ita ya kamata ta fara sani kafin
kowa yazo mishi. Dagowa yayi daga jikinta ya ja Kafafuwan shi kan gadon yana lankwashe su.
Numfashi ta sauke, tunda ya shigo gidan sai yanzun ya hada idanuwa da ita, duk da akwai wani
abu da take gani tattare da yanayin fuskar shi da yasa zuciyarta yin rawa.
Fuskarta ya tallafa cikin hannuwan shi yana fadin
"Karki barni Waheedah, ki tabbatar mun da ba zaki barni ba"
Nata hannuwan ta dora kan nashi dake fuskarta
"Dan Allah ka gayamun me yake faruwa"
Ta karasa maganar idanuwanta na cikowa da hawaye dan gabaki daya ya tsoratata
"Wani waje mai hatsari zasu sake turamun kai ko? Ka fadamun dan Allah..."
Cewar Waheedah muryarta na karyewa. Wannan na cikin bangaren da tafi tsana a aikin shi, in
duk aka turasu wajen da ake hatsaniya, tare da kwanciyar hankalinta yake tafiya, wayar duk da
zataji sai gabanta yai wata irin faduwa, idan tayi sati daya bataji shi ba, ko baccin kirki batayi.
Tana da tabbacin matan sojoji tare suke raba duk wani tashin hankali dake cikin aikin mazajen
su. Mata da yawa nason auren sojoji, ita AbdulKadir take so, in da tana da yanda zatayi da
baizo mata a soja ba. Tashin hankalin dake cikin aikin shi yana da yawa.
Kai ya girgiza mata, muryarshi can kasan makoshi yace
"Babu inda aka turani, kawai ina son jin ba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 37