Share this page
amman har ranta take jin shi, duk karfin hali irin nata hawaye takeji cike taf da idanuwanta, yanzun tagane kishi ne yake cin 'yar tata "Kuma Nuriyya ta aure shi, ni bazan taba mata haka ba, bai haramta ba, amman bazan auri mijinta ba...me yasa zata auri nawa? Mijina Mami, Sadauki ta gani duk fadin Kano...." Waheedah take fadi batare data sani ba, dan yanda take maganar tana wani irin kuka kasan ba a cikin hayyacinta take ba, sosai take kuka tana sambatun da ba zatace ga daga inda suke fitowa ba, riketa kawai Mami tayi tana jijjigata kamar karamar yarinya. A jikin Mamin tayi kuka har bacci ya dauketa, banda ajiyar zuciya babu abinda take saukewa, a hankali Mami ta zame Waheedah kan kujerar tana dauke mata Ikram. Bacci tayi har azahar, lokacin da ta tashi wani irin zazzabi ya rufe ta ruf, dakyar taja jiki ta wuce dakin Mami tayi alwala, sai da taba Ikram tasha dan duk hakurin yarinyar harta fara kuka, tukunna ta samu tayi sallah. Duk yanda Mami ta lallabata kasa cin abinci tayi, shayi ta hada ta samu tasha rabin kofi, da idanuwa Mami take binta duk inda tayi, har saida ta gama jijjiga Ikram tayi bacci, Mami ta karbeta ta saka zani ta goyata. Waheedah din na zaune kan kujera, tanajin kamar ta shige ciki dan gujema magana da Mami din. Cikin sanyin murya Mami tace "Na dauki ido na saka miki ne tun farko saboda nayi tunanin in har kina da matsala ina da kusancin da zaki sameni da ita. Bazance miki hakuri ba abu bane me kyau, duk da akan ce idan yayi yawa yana zama cuta. Babu inda hakuri yake yawa, a zamantakewa ta yau da kullum, ko a zamantakewa ta aure, musamman ma ta aure..." Gyara zama Waheedah tayi, tanajin yanda hawaye suka cika mata idanuwa, magana Mami ta cigaba dayi "Ba hakuri bane yake yawa ya zama cuta, rashin yafiya ne, akwai banbanci tsakanin ai maka abu ka hakura bakace komai ba, da ai maka abu ka hakura ka yafe. Yafiyar itace take saka duk yawan lokuttan da kai hakuri kake samun riba, idan har zaka hakura ba zakayi magana ba kabar abin a ranka bashida wani amfani, gara ka fito da shi kawai..." Mami ta karasa maganar tana sake sauke muryarta da fadin "AbdulKadir halin shine ya fito fili, shisa babu wanda ya tambayeshi me ya faru, babu ma wanda yai tunanin yaji nashi uzurin, kowa laifi ya dauka ya dora mishi. A karo na farko koya dace ko bai dace ba Waheedah, ko da za'a ce nayi son kai zan fadi raina ya sosu da auren Nuriyya da AbdulKadir yayi, bai taka addini ba, amman banji dadi ba ko kadan, saboda halin da zaki shiga nayi tunani" Wannan karin Waheedah bata koyi kokarin share hawayen dake zubar mata ba, yanda muryar Mami take a karye kawai na kara taba zuciyarta, ita kanta Mamin kokarin tarbe hawayen da suke ta mata barazana take, yanayin Waheedah din na gwada karfin zuciyar ta fiye da yanda ta zata. "Mutuwar aure tafi yin shi wahala, duk yanda ake ganin da kalamai kawai za'a yita. Ban taba ganin inda uwa taso mutuwar auren yarta ba Waheedah, ko ya kaddara ta rubuto hakan, ni shawara kawai zan baki a wannan matakin, bazanyi kokarin haramta miki abinda addini ya halarta miki ba, abu daya zance miki, kiyi magana da AbdulKadir..." Kai Waheedah take girgiza ma Mami wasu sabbin hawayen na zubar mata, har ranta tagaji da auren shi, tanajin idan ta koma komai zai iya faruwa, ciki harda tarwatsewar zuciyarta, ba zata iya daukar wani ciwon bayan wanda taita dauka ba "Wallahi Mami nagaji, nagaji har raina..." Waheedah ta fadi cikin kuka, kai Mami ta jinjina mata "Bance wani abu ba nima, kiyi magana da shi, magana ta fahimta, lokutta da dama aure kan samu tangarda ne saboda rashin tattauna matsala har a samu maslaha, kowa naganin laifin dan uwan shine, babu kuma wanda yake kokarin sauke girman kai ya saurari dayan har a gano bakin zaren, ki fada mishi matsalar ki, ki saurari uzurin shi" Shiru Waheedah tayi tana share kwalla "Kina jina?" Mami ta fadi, kai kawai Waheedah ta iya daga mata, tana sake shigewa cikin kujera. Numfashi Mami ta sauke, komai baya mata dadi sam, kitchen ta wuce badan tana da wani abu mai muhimmanci da zatayi a ciki ba, sai dan inta ci gaba da kallon Waheedah din hawayen da take ta boyewa ne zasu zubo. Duk wannan kishin da yake nuqurqusarta, da gajiyar da take fadin tayi, zaka fahimci yanda rabuwa da AbdulKadir shine karshen abinda take son yi...! #TeamAbdulKadir #TeamWaheedah #LubnaSufyan [7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan IG: SufyanLubna Email: Calmlubna@gmail.com Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43 *ABDDULKADIR* *LubnaSufyan* 28 Cikin baccin da baisan lokacin daya dauke shi ba yaji wayar shi na ruri, idanuwan shi a rufe ya lalubota, har kiran ya yanke, numfashi ya sauke yana dora wayar a kirjin shi hadi da gyara kwanciya. Wani rurin yaji wayar ta sake dauka, dakyar ya bude idanuwan shi yana ganin Nuriyya ce, dagawa yayi ya kara a kunne batare da yace komai ba "Masoyi..." Ta kira ta dayan bangaren, shirun AbdulKadir ya sakeyi, sosai ta bata mishi rai, Waheedah ce a tunanin shi da komai shisa baiyi lokacinta ba har yanzun "Hello..." Ta sake fadi, muryar shi can kasan makoshi cike da bacci yace "Ina jin ki" Ya lumshe idanuwan shi da suke mishi yaji saboda bacci "Naga baka dawo ba har yanzun... Dan Allah kayi hakuri..." Ta karasa maganar muryar ta na karyewa "Ina gida ni tun dazun" Cewar AbdulKadir din yana ganin rashin hankalin Nuriyya da zatayi tunanin dan ta bata mishi rai zai tafi wani wajen, a lokaci daya kuma yana ganin yanda har yanzun bata san wa take aure ba, jin tayi shiru yasa shi fadin "Kiyi bacci, sai da safe" Kafin tace wani abu ya kashe wayar shi. Bai taba zaton akwai ranar da matar shi zata bata mishi rai harya raba shimfida da ita ba, duk fadan da zaiyi da Waheedah in dai suna gida daya a jikin shi take bacci, ko baya mata magana kuwa. Numfashi yaja yana sauke shi, kirjin shi zafi yake sosai, tunanin Waheedah din yanzun ya kara taso mishi da wata irin kewarta. Wayar shi ya duba yana ganin karfe sha daya na dare, karamin tsaki yaja, dare ma baiyi ba sosai, ga baccin gabaki daya yabar idanuwan shi. Lambar Waheedah ya kira a kashe "Dan Allah ki kunna wayarki, ba sai kin daga ba Wahee, ko ringing din naji a kunne na zan dan samu nutsuwa" AbdulKadir ya fadi yana sake gwada kiran wayar, a kashen dai ya sake ji, tashi zaune yayi ya jingina bayan shi da jikin gadon. Dayan pillow din ya dauka yana dora shi kan cinyar shi. Bude wajen text yayi yana rasa abinda zaice mata, ko da can kalaman shi taqaitattu ne, balle yanzun kuma. Fasa tura mata yayi yana scrolling can sama, tsofin sakunanta ya dinga karantawa, duk yawan da suke dashi sai yaga sun kare mishi da wuri, WhatsApp ya koma yana jin dadin yanda baya goge chat, dan lokutta da dama ita take goge mishi in ta dauki wayar, sai tace yana cika waje. Danma ya hanata goge mishi nasu, tunda idan yana wajen da babu network su din yake karantawa suna rage mishi kewarta. Lokacin da yabi duk wani text dinsu ya gama karantawa karfe biyu saura. Duniyar yakeji ta mishi wani irin fadi, ga kadaici naban mamaki daya lullubeshi, da yanajin nutsuwa sallah zaiyi har gari ya waye, amman bashida wannan nutsuwar. Saukowa yayi daga kan gadon yana fita daga dakin zuwa bangaren Nuriyya. Bacci ya samu tanayi hankalinta a kwance, shi yace tayi bacci da kan shi, baisan me yasa baccin ya bata mishi rai ba 'Kin batamun rai, bana tare dake shine kikayi bacci kika barni' AbdulKadir ya fadi a ran shi yana girgiza kai, bandaki ya wuce ya watsa ruwa. A rayuwar shi baya hada wani da wani, hakan na cikin abinda bayaso sam, ko fada Hajja take mishi ran shi yana baci yaji tana kwatanta shi da wani. A wajen shi Allah ya halicci mutane daban-daban mabanbanta halaye da ra'ayoyi, har kamanni ma, wanda Allah ya halitta yan biyu sukazo da kamanni daya, suka kwanta a ciki daya ma saika sami halayensu daban. Sai gashi yanzun daya fito ya tsinci kan shi da hada halin Nuriyya da na Waheedah a waje daya yana aunawa, Waheedah ba zata taba bacci tabarshi ba, ko da shi ya bata mata rai, a yanda zata dinga kallon shi da idanuwanta kawai zaka gane babu nutsuwa a tattare da ita. 'Na baka hakuri fa Sadauki, kai mun magana dan Allah, wallahi a takure nake jina, ni banason yin fada da kai' Kalamanta suka dawo mishi 'Hamma har yanzu fushi kake mun? Babba da hakuri aka san shi' Takance, duk idan tayi amfani da Hamma to ya kwana yana mata fushi, ko tana son tambayar shi unguwa, zatace shifa Yayanta ne. Murmushi yaji ya kwace mishi, kafin kirjin shi ya sake amsawa kamar zai bude, har zazzabin rashinta a kusa dashi yake ji. Sai da ya sake komawa bangarenta ya sakko gajeran wando da singlet tukunna ya dawo dakin Nuriyya din, baccin da take zai hana mata, tunda shi ya kasa, kuma bayajin tunanin Waheedah zai barshi ya samu. * Da safe dakyar Nuriyya ta tashi sallar asuba, tana ta turo baki saboda baccin dake idanuwanta, bata kwanta da wuri ba, idan tace dan bai dawo bane karya take, kallo takeyi a system dinta suka dauke wuta, bata tuna dashi ba sai da chargyn system din ya kare, kudine ta riga ta kashe, fada ne zaiyi ya gama. Ita ko kadan batama hango zai mata fada akan dubu arba'in ba, yanda take ganin kudin shi, yafi karfin dubu arba'in, idan nashi ran ya baci itama natan a bace yake. Data kirama yace tayi bacci tana kashe wayar guntun tsaki taja ta ajiye ta kwanta, daman ko baice ba baccinta zatayi. Dan tunda harya dawo daga ko ina Major ya kaishi bai mata fada ba wani abu ya nutsu a ranta. Batajin akwai wani babban abu da zatayi mishi kuma da zai kai wannan, iya kacin shi fada, duk da fadan na tsaya mata a rai, in yayi yagama shikenan. Ta kula bashida riko, da wahala ya kwana yana fushi kan abu daya. Tana idar da sallah ta janyo wayarta, chajin taga saura goma, dan ta manta ta saka sanda aka kawo wuta. Haka kawai tunanin azumi da saura kwana biyu ya diro mata, wayar AbdulKadir din da take kan drawer din gado ta janyo, ta saka sunan Waheedah a cike taga bai bude ba. Tasan dai duk password din shi baya wuce sunanta, dan waccen wayar daya sake haka password din yake, har wani daci-daci take ji duk idan ta dauki wayar shi, shisa yanzun taji zuciyarta tayi wani tsalle da tunanin ko sunanta ya saka, jikinta har bari yake lokacin da ta saka sunanta, sai taga wayar bata bude ba, kamar daga sama taji sallamar shi yana dorawa da "Me kike mun da waya?" A dan tsorace ta daga kai tana sauke idanuwanta cikin nashi daya kankance mata "Bakomai, zan duba abune, nama kasa budewa kuma" Gira daya AbdulKadir ya daga mata dan baiga abinda ta ajiye a wayar shi da zata duba ba, hakan ta kula dashi yasa ta dora da fadin "Hotuna zan kalla fa, wayata babu chaji, ban saka ba na manta" Karasawa AbdulKadir yayi yana hawa gadon "Ko gaisheni bakiyi ba kike son cinyemun chajin waya" Murmushi Nuriyya tayi mishi tana matsawa sosai ta kama hannun shi "Ina kwana" Kankance mata idanuwa AbdulKadir yayi "Waheena" Ya fadi yana zare hannun shi daga cikin nata yaja kafafuwan shi ya hau dasu kan gadon, cike da rashin fahimta "Password din" Ya fadi yana kwanciya ya lumshe idanuwan shi, Nuriyya tabi shi da kallo yanda yake shirin komawa bacci kamar bai fada mata abinda taji dacin shi ya taso daga kasan zuciyarta zuwa makoshinta ba. Har wani hucin bacin rai takeji kamar kububuwa, AbdulKadir kuwa baccin shi ya koma, yana barin Nuriyya nan zaune ranta in yai dubu a bace yake. Dan kamar ba zata bude wayar ba, kafin ta yanke hukuncin Waheedah ba zata hanata latsa wayar AbdulKadir din ba, tunda yanda takejin mijinta ne itama haka takeji. Kuma tana so ta shiga messages din shi harna whatsapp taga ko yaushe Waheedah zata dawo. Wani malolon takaici ya sake taso mata, ganin saita kara saka wani password din tukunna zata iya gani, gashi lambobine wannan karin, hakura tayi tana shiga wajen kira taga ko yayi magana da Waheedah. 'Matar Sadauki' Sunan farko data fara cin karo dashi a jerin wajen kiran wayar AbdulKadir yaso wanke mata bacin ran da takeji, kafin ta kula da kiran fita yayi ba shigowa ba, tana kuma ganin 'Nuri' Daga kasa, wannan karin wani irin tsakine ya kwace mata, fita tayi tana kara kula da wallpaper din AbdulKadir din, hoton Fajr ne daya sata jin son samun nata yaron taso mata yana zuwa mata wuya, ba sosai takanyi tunanin samun ciki ba, amman duk idan taga giccin Fajr tanajin kamar ace yaron nata ne. Kulle wayar tayi zata ajiye taga hoton dake fitowa idan an kulle waya kunshine, daga yatsun ta gane hannun Waheedah ne. A gefen AbdulKadir ta ajiye wayar tana addu'ar ya mirgino ya dora mata nauyi screen din ya samu matsala ko zai rage mata takaicin da take ciki. Mikewa tayi ta cire hijabinta, kan gadon tahau daga can karshe ta kwanta, banda tafasa babu abinda ranta yake, kafin ta matso tana kwanciya jikin AbdulKadir din da Waheedah takeyi kamar nata ne ita kadai, sai dai duk yanda bacci bai wadaceta ba, ta kasa samun shi, data rufe ido hoton hannun Waheedah ke mata yawo da sunanta da take da tabbacin ita tayi saving din lamba dinta a haka a wayar AbdulKadir din, saboda rashin aji, ita ba zatai haka ba da ta dauki wayar AbdulKadir din tana sake nata sunan zuwa 'Matar Masoyi' Da tunani barkatai a ranta, dukkan su suna hadewa sukai mata wani irin zafi lokaci yake ta tafiya, wutar da aka kawo yasata sakkowa daga kan gadon. Chaji ta fara sakawa tukunna ta shiga wanka ta fito, gaban mudubi ta zauna ta tsara kwalliya sosai a fuskarta, bum short ta saka da wata karamar riga, tana samun hula ta saka a kanta. Tayi kyau das da ita, yunwa ta fara addabarta, kitchen ta wuce ta dafa ruwan zafi a kettle tana hada shayi mai kaurin gaske ta duba biscuit ta dauko, shima ya kusan kare mata, gashi babu wasu kudi a hannunta, zatai ma AbdulKadir maganar kudi idan an kwana biyu, tasan bazai hanata ba. A kitchen din ta tsaya ta fara shan shayin dan yunwa take ji sosai. Takun tafiyar AbdulKadir din taji, kafin ya rungumeta ta baya "Yunwa nakeji Nuriyya" Yatsine fuska tayi dan tasan baya ganinta, muryarta ciki-ciki tace "Me zan baka Masoyi? Nima yunwar ce ta tasheni... In hada maka shayi?" Sake matseta AbdulKadir yayi yana sauke numfashi "Shayi da me?" Ya tambaya "Da biscuit" Nuriyya ta amsa, tana sa AbdulKadir din sakinta ya kama hannunta yana juyo da ita, ta mishi wani irin kyau mai ban mamaki "Ni zaki ba shayi da biscuit Nuriyya? Na miki kama da Fajr" Shagwabe fuska tayi "Bansan me zan baka ba wallahi, me kake son ci?" Kafadu AbdulKadir yadan daga mata, shima baisani ba, Waheedah bata tambayar shi abinda zaici, bashi kawai takeyi "Ni dai bazan ci biscuit ba, bari inyi wanka. Kimun koma menene" Ya karasa maganar yana juyawa ya fice daga kitchen din, kamar hakan Nuriyya take jira tayi wani irin juyi tana buga kafarta a kasa, ko kadan wannan wahalar ce ba zata iya ba sam, a gidansu ma ba girki take ba, can da babu kudi, gidan Anas ma sai ranar da tayi ra'ayi tunda in bai bata kudi ba, inya ajiye dauka take, duk bala'in da zasuyi, ko kudin waye. Daya daina ajiyewa kayan abincin shi take diba ta siyar, akwai gidajen da ake abincin siyarwa kala-kala a unguwar, wani lokacin ma danyen take kai musu, sai a dinga aiko mata dafaffe har kudinta ya kare. Ranta a bala'in bace ta karasa shanye shayin nata, kitchen din Waheedah ta wuce tana dauko duka kwalin indomie din da ko rabi ba'ayi amfani dashi ba. Batasan abinda zata dafa mishi ba banda indomie din, in zaici yaci, in ba zaici ba kam batasan ya zatayi dashi ba ita. Wannan wahalar ko kadan jikinta ba zai dauka ba, tasan Waheedah zata dawo babu dadewa, tunda mayyar AbdulKadir din ce bata iya nisa dashi. Tana ta kwashema Waheedah albarka a ranta tana dora indomie din, ta duba, albasa ma bata da ita sai da ta sake komawa kitchen din Waheedah ta dauko ta dawo. Lokacin da AbdulKadir ya fito harta karasa ta kashe gas din, ta samu plate tana juye mishi ta saka cokali mai yan yatsu a ciki. Ta dauka zaiyi magana, baice komai ba ya saka cokalin ya fara ci, kitchen ta koma dan tayi wanke-wanke, a kasan ranta takejin yanda harta fara gajiya da zaman gidan. * Mami da kanta tace mata takoma gidan Yassar ta huta abinta, babu wanda zai dameta a can din, dan tunda yan gidan suka ga tana nan sai hirar ta dawo bangaren Mamin. Ita kanta Waheedah din tana bukatar shirun, tasan in tana nan gidan ba zata same shi ba, duk da sosai taji nauyin da kirjinta yayi ya mata sauki, musamman da aka hadu anata hira, sun rage mata kadaicin data jima tana fama dashi. Sun kuma rage mata zafin zuciyar da take tare dashi, sai gab da Magriba Yassar yazo ya dauketa daya dawo daga wajen aiki ya biyo. Fajr ma bata ganshi ba, bata kuma bi ta kanshi ba, tunda ba bakon waje yake ba, ballantana yana wajen Hajja inda babu wanda ya isa ko murya ya daga mishi ai bazai nemeta ba. Da suka koma tadan samu taci abinci dakinta ta koma, tana sallar isha'i ta haye gado taci gaba da kallon film din daya rage mata tunani ba kadan ba. Har saida taji dakyar take bude idanuwanta sannan ta hakura ta kwanta. Badan taji kiran sallah ba, kawai sabo da tashin asuba dinne yasa tun kafin lokacinta ya karasa harta tashi. Tana gabatar da sallah Ikram ta dauka tabata tasha sukayi kwanciyarsu suna komawa bacci. Sanda ta tashi goma tayi, wanka ta shiga, ta fito ta dauki Ikram dan tayi mata itama, da kuka aka gama wankan, daman in dai kana son jin kukanta to wanka ko yunwa, kafin wani lokaci harta shirya kanta cikin riga da zani na atamfa da dinkin ya zauna mata sosai, kwalliya tayi tana saka jambaki a labbanta, Ikram ta shirya tsaf tana kallon yanda kamanninta da AbdulKadir suke kara fitowa "Ikram ki rufamun asiri mana, dan Allah banda idanuwan" Waheedah ta fadi tana gyarama Ikram din riga da ta dauka wasa take mata ta dashe mata baki tana dariya, itama dariyar ta tsinci kanta dayi "Dariya kike ko? Da gaske banda idanuwan..." Waheedah take fadi tana jijjiga Ikram dake dariya sosai "Kuma karkiyi irin rigimar shi, macece ke wahala zaki sha" AbdulKadir da tun daga bakin kofa yakejin dariyar su, hakan yasa shi murza hannun kofar yana shigowa ya tsaya yana kare musu kallo da murmushin daya manta rabon da yayi shi a fuskar shi yace "Ki daina hure ma yarinyata kunne...Fajr da ya biyo rigimarki me nace?" Juyawa Waheedah tayi fuskarta dauke da mamakin ganin AbdulKadir din, duk da ya saba shigowa waje bataji shi ba sai dai ta ganshi, kare mishi kallo tayi ya saka gajeran wando iya gwiwarshi na sojoji sai farar riga a jikin shi, kamshin turarukanta yakeyi. Fuskar shi har lokacin da kumburi, kare mishi kallo tayi kafin ta dauke idanuwanta daga kan shi tana janye Ikram ta matsar da ita tsakiyar gadon ita tana zama a bakin gadon, ta dora hannuwan ta daga gefe da gefe. A hankali AbdulKadir yake takawa zuwa inda take, tsintar kan shi yayi da tsugunnawa saboda Waheedah ta sunkuyar da kanta. Hannun shi yakai yana dago da habarta, agogon dake daure da hannun shi tabi da kallo, shine kyauta ta farko data shiga tsakaninta da shi, duk tarin agogunan shi, wannan din shi yafi daurawa fiye da ko yaushe, lokutta da yawa wanka da alwala duk dashi yakeyi, fatar duk ta koke, in tai mishi magana sai yace agogon na da muhimmanci a wajen shi, har wani ta siya mishi, amman dai yafi son wannan din. Bama aiki yake ba, batasan me yasa yake yawo da shi ba. AbdulKadir idanuwanta yake son gani, so yake yaga ko da giccin tarin soyayyar da take mishi ne. "Wahee..." Ya kira yana wani irin sauke murya cikin yanayin da baisan zuciyar shi zata taba iya jin shi ba balle ta fito dashi, idanuwan nata kuwa ta saka cikin na shi, maganganun Mami na dawo mata suna saka wani abu da batasan yana kulle a kirjinta ba budewa. Komai takeji yana dawo mata kamar a lokacin yake faruwa, tana jin wasu irin hawaye da suke fitowa daga wani waje a zuciyarta daya jima yana ciwo kafin su fara zuba kamar an bude su, dumin su ya fara ji a jikin hannun shi da yake kan habarta kafin ta sake sunkuyar da kanta. Da sauri AbdulKadir ya tashi ya zauna gefenta yana kama hannunta ya juyo da ita ta fuskance shi "Waheedah..." Ya kira yanajin yanda kukanta ya karasa birkita mishi tunani, wani irin dana sani yana saukar mishi kamar ruwan sama, ba ita ba, yanajin zai jima a rayuwar shi bai dagawa wani hannu ba a yanayin da yakejin shi. Hannu yasa yana kamo fuskarta ta ture shi tana saka nata hannun ta goge hawayen da sunqi daina zubowa, hannu AbdulKadir ya sake kaiwa, kafin ya taba fuskarta ta sake ture shi "Ka kyaleni....kabar ni" Ta fadi cike da kashedin da AbdulKadir bai taba tunanin tana da zuciyar fito da shi ba, dan sanyin halinta yayi yawa, wani kuka na sake kwace mata. Gyara zaman shi yayi yana kokarin saka hannuwan shi duka biyun wannan karin, ture su ta sakeyi da dukkan karfinta tana mikewa, wani irin kallo take mishi da yasa shi jin kamar an watsa mishi ruwan kankara "Ka kyaleni, kaje ka taba fuskar Nuriyya" Da mamaki AbdulKadir yake kallonta, kafin shima ya mike yana son hade space din dake tsakanin su, baisan abinda ya kamata yace mata ba, kuma lallashinta yake sonyi, taki bari ya tabata, gabaki daya komai ya cunkushe mishi "Dan Allah kiyi hakuri Waheedah..." Ya fadi yanajin shima gab yake da nemo kuka duk inda yake, kilan in ya taga hawaye a fuskar shi sai tagane abinda nata hawayen yake mishi, takawa ya sakeyi, ta dago hannuwanta tana kokarin ture shi, kama hannuwan nata yayi yana sa karfi ya rike su "Karyewa kike son yi shisa zaki tureni ko?" Kiciniyar kwacewa takeyi zuciyarta na wata irin tafarfasa "Nace kiyi hakuri...Dan Allah kiyi hakuri, ba zan kara ba wallahi" AbdulKadir ya karasa maganar muryar shi na karyewa, har lokacin yana rike da hannuwan Waheedah da take kallon shi kamar tana shirin rufe shi da duka, ga hawayen da bayaso sunki daina zubar mata "I'm sorry" Ya fadi da harshen turanci yana dorawa da fadi cikin harshen larabci "Ana Asif..." Sosai yake kallonta, tunda yake baisan yanda hakuri yake fitowa daga zuciya ba sai yanzun da yake a gabanta, hannunta daya ya dago ya dora shi a kan kirjin shi inda zuciyar shi ke dokawa kamar zata fito waje saboda tashin hankali "Su kadai ne yarukan da nake ganewa, idan akwai wani kalar hakurin ki fadamun....nace bazan kara ba, idan akwai abinda nayi miki banda mari ki fadamun duk sai in hada in baki hakuri" AbdulKadir yake fadi yanajin a wannan gabar kome take so shidin zaiyi indai zata hakura ba zata kara furta mishi kalmar ya saukake mata auren shi ba, hannuwanta take kiciniyar kwacewa, sakar mata yayi, yana kallo tasa ka bayan hannu ta goge fuskarta da har ta kara ja saboda kukan da takeyi "Kinga fuskar ki harta kumbura, kiyi hakuri kar kanki yayi ciwo Wahee..." Kallon shi take, tanajin wani tuquqin kishi naban mamaki yana taso mata "Bakayi tunanin kaina zai ciwo ba ka kara aure ban sani ba?" Maganar ta dirar mishi cikin kunnuwa tana daukar wasu dakika kafin ta karasa cikin kan shi tana rarrabuwa zuwa inda zai fahimta "Da kayi auren ka ban sani ba kamar na isa in hanaka, sai ka zabi ka dauki wata daya kafin ka gayamun ta text...Text" Waheedah ta maimaita maganar cikin gunjin kukan da yaji ya samu wajen zama a zuciyar shi yana daskarar dashi tsaye a wajen, wannan karin ita ta taka tana hade space din dake tsakanin su, cikin fuska take kallon shi "Bakayi tunanin abinda zanji ba ko Sadauki? Banda darajar da zan san ka yanke hukuncin da ba rayuwarka kawai zai canja ba harda tawa.... Bai isheka ba sai da ka sake nuna mun duk abinda zanji a kai ba matsalarka bane, ka fadamun ka kara aure ta text!" Wannan karin da hargowa ta karasa maganar tana ture AbdulKadir din duk da ko motsi ya kasayi, tsaye yake kamar bishiyar da ta samu dashe mai kyau, kalamanta yake ji na saukar mishi da wani irin yanayi da bashida kalaman dora su, kuka Waheedah takeyi mai sauti, zuciyarta na ciwo kamar zata rabu da kirjinta, numfashi take ja tana fitar dashi a wahalce, sai dai kalaman takeji na tunkudedeniya da juna wajen fito mata, tagaji da rike su, tagaji da rike komai "Da ka fadamun ta text, ko kadan hankalin ka bai baka ka fadamun kawata ka aura ba ko? Saboda kai ne, AbdulKadir da babu wanda ya isa, darajar kowa a kasan taka take shisa baka fadamun ba sai da ka dauko ta ka kawomun ita cikin gida na....Kawata Sadauki... Kawata ka aura, idan kaso ka kasheni

Chapter 29 of 37