Share this page
iya nisa dani ba... Nasani" Yake fadi yana karasawa ya bude kofar, Nuriyya yagani, a karo na farko da yaji baiso ta kasance a bakin kofar ba. Rigarshi ce a jikinta sai wandon da ko cinyoyinta bai rufe ba. Ta kama gashinta da yake a kwance ta kulle shi a tsakiyar kan nata. Kwalliya ce a fuskarta sosai, da alama tayi wanka bayan fitar shi. Sosai yake kallonta yana neman samun nutsuwa koya take daga hakan. "Naji motar ka..." Nuriyya ta fadi, tana jin zuciyarta tayo tsalle zuwa wuyanta da yanayin dake fuskar shi, zatai karya idan tace bataji tsoro ba daya bude kofar, saboda taga wani abu kamar disappointment shimfide kan fuskar shi, kamar ba ita ya tsammaci gani a tsaye a gaban shi ba, sosai hakan ya tsoratata. Ganin ya kankance idanuwan shi yana kallonta har lokacin yasata fadin "Ya jikin Waheedah din?" Tanajin dacin dora sunan nata kan harshenta, wani irin tuquqin kishi na danne kirjinta da yanda zai kasance sunan Waheedah zatai amfani dashi yau dan tai nasara kanshi "Da sauqi" Ya furta can kasan makoshi, kai tadan jinjina tana shagwabe mishi fuska "Abinci fa?" Saida ta kira abinci tukunna yaji cikin shi ya murda mishi da yunwar da yakeji, numfashi ya sauke, duk ranar baici komai ba, Waheedah ko damuwa da cikin shi batayi ba. Yanda baya jure yunwa idan yana tare da ita har mamaki yake bashi. "Ki dafa koma menene" Yai maganar yana shirin rufe kofar a fuskarta, kallon shi Nuriyya takeyi tanajin cikinta ya murda mata da yunwar da takeji itama. Ba zatace ga rana daya datai wani girki kwakkwara ba tunda tazo gidan. Da tace mishi 'Abinci fa?' Batana nufin me zata dafa bane, tana nufin me zasuci ya fita ya siyo musu dan ita yunwa takeji ta fitar hankali, biscuit ne kawai a cikinta duk yinin ranar. Saurin dafe kofar tayi "Masoyi..." Ta fadi tana tattaro duk wata kissa da zata iya ta nade muryarta da ita. Numfashi Abdulkadir ya sauke, bacin ran da yakeji a kusa yake. Da Waheedah ce data gane gab yake da fashewa, ko bata bashi space din da yake bukata ba zata kama hannun shi ta zaunar dashi, zata dora kanta a kafadarshi su zauna shiru har sai yadan nutsu. Amman da alama Nuriyya bata karanci ranshi a bace yake ba. "Naga yamma tayi, na dauka ma ka siyo mana..." Tai maganar tana kallen shi fuskarta a shagwabe. Numfashi ya sake saukewa yana dorawa da "Idan ba zaki dafa ba ki barshi..." Da mamaki a fuskarta take kallon Abdulkadir, bai taba mata magana cikin yanayin dayai mata ba yanzun "Masoyi..." Ta kira "Kinjini ai" Ya fadi yana rufe kofar a fuskarta ya koma kan gadon ya kwanta. Wani bacin ran na sake danne shi. Dan yasan ba laifinta bane ba, ba ita ta bata mishi rai ba, bai kuma kamata ace ya sauke akanta ba. Yagani a fuskarta yanda hakan ya tabata, ba Waheedah bace ba, ita kadai ce a duniyar shi yake saukewa bacin ranshi ko da ba tada alaqa da hakan, saboda tabarshi, saboda ta nuna mishi bakomai dan yayi hakan, ta fahimta yana son saukewa a wani waje, dan ya zabeta bai dameta ba. Karamin tsaki yaja. Ko kadan bayason yawan tunane-tunane, Waheedah tasan hakan ta zabi ta sakashi cikin tunani. Nuriyya ta kai mintina biyar a tsaye a bakin kofar, ranta idan yayi dubu a bace kowanne yake. A rayuwarta batason wulakanci koya yake, idan akai matashi takanji kamar an mata hakanne dan a nuna mata ita din bakomai bace, amman tunda can idan wulakancin ya kasance daga bangaren shine takanji kamar zata hadiye zuciya ta mutu. Yanzun ma haka takeji, kirjinta har zafi yake mata. Batasan me akai mishi a waje ya bato mishi rai ba, dan ita tasan batai mishi komai ba. Yunwar da takeji na karasa bacin ran ya hade mata, wucewa tayi ta koma bangarenta tana nufar kitchen. Fridge ta bude tana rasa abinda zata dafa, akwai kaza a ciki danya. Abdulkadir na kokari sosai wajen kula dasu tasani, kajine da yawa a nata fridge din, Waheedah kanzo har bangarenta ta kawo mata, bata cika amfani dasu bane shisa suka taru, randa taji kwadayi ya kamatane take daukowa ta soya. Yanzun ma kulli daya ta fito da ita duk tayi kankara, ta rufe fridge din tana sakata cikin abin wanke-wanke ta bude fanfo. Tukunya ta fito da ita tana ajiye, kazar da take a yayyanke ta kwashe ta zuba cikin tukunyar, ruwa ta zuba a ciki ta dora kan gas tana kunnawa. Wajen fridge din ta karasa tana dubawa taga ko tana da cefane. Gani tayi babu, tunda ba girkin takeyi ba, bata kula ba. Fita tayi zuwa bangaren Waheedah ta shiga kitchen din nata tana bude fridge, akwai kayan miya a cikin robobi a ajiye wajen roba biyar. Na farkon ta fara dauka ta wuce ta koma, diba tayi ta zuba cikin kazar, sosai take ganin ya mata yawa, dan robar nada girma,a fridge dinta ta saka dan ba mayarwa zatai ba, koda zata sake amfani dashi. Maggi tazo ta bare ta watsa, taliya zatayi jalof. Tana gama zuba maggin taji kiran sallar la'asar. Daki ta koma tayi alwala, zani kawai ta daura saman kayan jikinta ta saka hijab ta gabatar da sallar. Ko dardumar bata linke ba ta cire hijab din da zanin tana watsa su kan gado ta koma kitchen din, yunwa takeji ta fitar hankali, budewa tayi taga ya tafaso, amman wani karni ya daki hancinta dan kazar ko wankuwa batai ba, kuma kayan miyar babu albasar kirki a markaden su. Dauka tayi ko dan bata karasa dahuwa bane ba, ludayi tasa taji ko kazar tadan yi laushi, rufewa tayi ta tsaya kamar minti biyar a kitchen din, har lokacin ranta a bace yake, tukunna ta bude daya daga cikin locker din dakin ta dauko taliya guda daya. Kakkaryawa tayi ya zuba cikin tukunyar tana jujjuyawa tukunna ta koma falo ta zauna. Gara ko kallo ne tayi ta rage zafi. Tana kunnawa ta dauki remote suna dauke wutar su, wani dogon tsaki taja "Tsinannu..." Ta furta a fili tana mikewa. Kitchen din ta koma taga tsaliyar harta fara laushi dan kanana ce, da tana gidan su takan jima bataci taliyar turawa ba, filawa Babansu yakan siyo a kado musu taliyar Hausa, ita ko lokacin sai tayi sati biyu bata dora tukunya ba, tun Mama na mata fada harta gaji ta hakura, idan ta matsa mata abincin ba za'a ga dai-dai ba, garama idan da mai da yaji ne, ko wake da shinkafa ce wani lokacin waken a tsai-tsaye za'aci shi. Bai gama dahuwa ba, shisa ta daina sakata, tunda ba wadatar abincin suke dashi ba da za'a dinga barnar shi. Taga alamar taliyar ta kusan dahuwa, amman sosai ruwan yayi yawa. Abin kama tukunya da bangaren Waheedah ta dauko shi bata mayar mata ba ta saka tana dauke tukunyar daga kan gas din, rage ruwan tayi cikin abin wanke-wanke tukunna ta sake mayar da tukunyar kan gas. Tunawa tayi bata zuba mai ba, shisa taga taliyar ta mata wani iri, dubawa tayi ta dauko man a cikin roba, da yake na 'ya'yan itatuwa ne suke amfani dashi. Tana ma da man gyada da Waheedah ta bata yakai kwalba biyu, a cewarta kanwar babanta ce ta kawo mata da tazo gidan. A ludayi ta tara man tana zuba ludayi biyu ta cakuda, gani tayi kamar bazai wadata ba, ta kara ludayi daya tukunna ta rufe tana mayarwa. Jujjuya taliyar ta sakeyi, ta daddaga ludayin a hannunta ta dan-dana. Gishiri ta dauko ta zazzaga dan taji kamar bai mata ba, hannunta ya kubce kuwa, cikin hanzari tai kokarin saka ludayi ta kwashe amman duk ya narke dan abincin nata tafasa, tsaki ta sake ja, komai baya tafar mata dai-dai. Dabara ce tazo mata, ta dinga kwaso romon da ludayi tana zubawa cikin wajen wanke-wanke tukunna tadan dibi ruwa ta kara ciki, gani tayi cefanen naso yai mata kadan, ta zaro taliya daya ta saka a bakinta, duk da hakan gishirin nason mata yawa, kuma bataji cefane kamar yanda ta Waheedah kanyi ba. Robar ta dauko ta kara dibar wani ta zuba ta cakuda, sai taga tadan mata kyau a ido. Kamshine kawai baya tashi. Faranti ta dauka tana zuba musu ita dashi a hade, kusan duka naman ta kwashe ta saka musu a ciki. Dauka tayi zuwa falon ta ajiye ta koma ta dauko cokulla masu yatsu ta saka a ciki, tukunna ta taka zuwa bangaren Waheedah da batasan me yake acan din ba tunda bata nan, a falo ta same shi zaune. "Ka taso muci abinci" Ta fadi tana kallon shi harya mike ya taka ya wuce ta batare dayace komai ba. Yunwa ke cin shi sosai da sosai. Bayanshi Nuriyya tabi har falonta. Kan kafet suka zauna, cokali AbdulKadir ya saka cikin abincin yana jujjuyashi, yanayin taliyar bai mishi ba sam, yakanci kome Waheedah ta dafa ta bashi, bai saba fada mata ga abinda yake son yaci ba, idan unguwa taje ma saita gama mishi girki take fita indai yana nan. Zubawar kan zame mishi aiki, da lokacin cin abincin yayi zata kirashi a waya taji ko yaci. Lokutta da dama zai saka mata rigima saita baro duk inda take ta dawo sunci tare, ko yace shi baisan yanda zai zuba ya isheshi ba, haka zata fada mishi ludayin dazai amfani dashi, ko guda nawa zai zuba, miya tasa ya samo wajen zubawa ya zuba tace ya dinga diba yana sakawa a abincin inya rage saura ya saka mata a fridge. Sai dai Waheedah ce, tasan abinda yake son ci, tasan abinda bayaso, taliya na daya daga cikin abincin da bawai ya dameshi bane, gara da miya, amman jalof haka tsuranta bata dameshi ba. Idan Waheedah tayi tana hada mishi salad sai yaci, idan yace ta dafa taliya, takance mishi tana son ya dinga cin komai saboda inya koma wajen aiki bata kusa. Sosai yake cakuda taliyar yana tunanin sakata a bakin shi, naman ma ko kadan bai mishi ba, idan a wajene babu yanda zaiyi saiyaci, amman cikin gidanshi bai saba da abinci irin hakan ba. Bayason yin wani dogon nazari ya nannado taliyar yana sakata a bakin shi. Nuriyya yake kallo da take cin abincin hankalinta a kwance, kamar yana mata dadi, abinda baisani ba, bawai abincin ya mata dadi bane, ita kanta taji yanda gishiri yadanyi yawa. Sai dai yunwa takeji ta fitar hankali, inda baya nan ma zataje ta hada shayi. Amman batason nuna mishi yanda abincin bai mata ba. Dakyar Abdulkadir ya hadiye taliyar dake bakinshi yana dubawa danya dauki ruwa, bata kawo mishi ba "Baki bani ruwa ba..." Ya furta, sai lokacin ta dago tana kallon shi, mikewa tayi ta dauko mishi ruwa a fridge tazo tana kawo mishi. Ganin ya kalleta yasa ta komawa ta dauko kofi tazo ta ajiye, budewa ruwan tayi tana zuba mishi, dauka yayi yasha, ruwan ya kulle mishi ciki lokacin daya dira cikin hanjin shi, ko kadan bazai iya cin taliyar nan ba, ganin ya bai dauki cokalin ba yasa Nuriyya fadin "Har kayi me?" Daquna mata fuska yayi "Bana son taliya Nuriyya..." Da rashin fahimta take kallon shi "Idan Waheedah ta dafa kana ci" Kai ya jinjina mata da taji kamar ya watsa mata garwashin wuta, tabbatar mata yake tata ce bazai ci ba, amman yanacin ta Waheedah, magana zatayi ya dora da "Ba irin wannan bace" Cokalinta ta ajiye itama, tana danne kishi da tuquqin bakin cikin daya taso mata tayi mishi wani murmushi "Kaci naman to" Baiyi musu ba, cokalinshi ya dauka yana kokarin sabulo tsokar naman, amman yaji abu ya gagara, idan abincin Waheedah ne yana saka cokali a jikin naman yake raboshi da kashin shi saboda ya dahu. Ajiye cokalin yayi yasa yatsun shi ya tsamo cinyar yana kaiwa bakin shi ya kafa hakori a ciki, qiri-qiri yaji naman, kona waje yafi shi dahuwa, gutsura yayi yana taunawa, ruwan naman na sauka bakin shi da wani dandano marar dadi, gashi ko maggin kirki bai kamashi ba. Ajiye na hannun shi yayi yana dakuna fuska "Wanne irin nama ne wannan? Bai dahu ba..." Abdulkadir ya fadi yana ciro na kora wanda ya gutsura da ruwa "Bangane bai dahu ba..." Nuriyya tai maganar a kufule, kankance idanuwan shi yayi yana kallon ta "Kici a bakinki..." Naman ta sa hannu ta dauka ta gutsura, ita kanta taji bai dahu ba, ajiyewa tayi kunya na kamata, tasan bata iya girke-girken nan ba, girman kanta kuma bazai taba barinta tace Waheedah ta koya mata ba, shisa take ta damun shi daya dauko mata 'yar aiki, kuma ko da ta iya ma, Allah ya dora mata ganda, ba zata iya girke-girken da Waheedah ke yini tana yi ba. Duk ranar girkinta takanja jiki, kota jashi tace suje bangaren Waheedah din su tayata hira, dan suci abinci acan din. Farko-farko ta dauka Waheedah din kan basu saboda Abdulkadir din ne kawai. Saida taga ko baya nan taje bata hanata, wani lokacin takan aika Fajr ya kirata tazo ta dibi abinci. Yanda Abdulkadir din bai taba kula tana gujema girki ba har mamaki yake bata. Addu'a take Waheedah karta jima a asibitin, dan taga alamar zasu samu matsala da Abdulkadir kan abinci. Mikewa yayi da alama ranshi a bace yake, yana sawa ta mike itama "Dan Allah Masoyi kayi hakuri, cikin sauri nayi girkinne dan naga yamma tayi..." Baice mata komai ba ya rabata ya wuce, ranshi a bace yake, kuma yunwa yakeji, idan yai magana baida tabbacin abinda zai fito daga bakin shi, addu'a yake kartai kokarin binshi dan baisan me zai faru ba...! *#TeamAbdulKadir* *#TeamWaheedah* *#TeamYassar* *#AnaTare* [7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan IG: SufyanLubna Email: Calmlubna@gmail.com Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43 *ABDDULKADIR* *LubnaSufyan* 15 Tunda suka shiga gidan Yassar ta gaisa da matar shi Hawwa da yar kanin Abba ce ya aura, ta samu kujera a falon ta zauna. Batasan me Yassar din yace mata ba, taga dai tazo tace mata ta tashi taje ta huta, daya daga cikin bedrooms din dakin ta rakata. Fajr kin binta yayi saboda yana kallon cartoon, da yake Yassar din ma yakan je ya dauko shi yai hutun karshen mako a gidanshi wasu lokuttan, yaron ya saba dasu. Tana shiga ta kwantar da Ikram, bandaki ta shiga ta daura alwala dan ko sallar azahar batayi ba. Ta fito ta gabatar da sallah, zaune tayi akan kafet din tana dora kanta a jikin gadon, kanta a cunkushe take jin shi, ta rasa abinda yake mata dadi a gabaki daya duniyar. Tunani ne ya dauketa yana watsata shekaru Shida da wasu yan watanni da suka wuce, kafin rayuwa ta kawota inda take. * Tun bayan bikin Nuriyya, sai ya zamana babu abinda Waheedah ta saka a gaba banda karatunta, takanyi kwana biyu bata leqa gidan Nuriyyar ba, duk da ba wani nisan kirki ne a tsakanin su ba, ita tana cikin Naira da kwabo, su kuma su Waheedah din a kofar ruwa, ko da kafa zata gangara. Amman suna yawan waya, kusan kullum zasuyi chatting, wani lokacin kuma inta riga Nuriyya tashi daga makaranta takan biya ta FCE dinsu sai su gaisa. A yanayinta take fuskantar yanda har lokacin taqi kwantar da hankalinta da auren Anas din. Sai dai fadan da Waheedah take mata yasa ta daina gaya mata komai, inta tambaya ma sai dai Nuriyyan tayi murmushi tace mata lafiya kalau, duk da tasan karya take, bata takurata, kullum Nuriyyar na cikin addu'o'inta akan ta samu kwanciyar hankalin da kowacce mata take samu a dakin aurenta, tare da mata addu'ar nutsar da hankalinta da auren Anas din. A bangaren samarin da suke kawoma Waheedah tayin soyayya ma babu abinda ya canza, dan bata fasa gaya musu cewar an mata miji ba, kamar yanda bata fasa bama AbdulKadir labarin yanda ranarta ta kasance a kullum ba. Duk da yanzun saqqonin nata na zuwa, suna kuma nuna alamar an karanta. Amman tun kafin bikin Nuriyya rabon da ta samu amsar shi. Batasan ya akai ba, amman a shirunshi take karantar akwai abinda yake damun shi, tana kuma jin hakan har kasan zuciyarta, kuma koma menene yake damun shi din, tare suke cikin damuwar, dan itama nata hankalin ba'a kwance yake ba. Daina kirga kwanakin zuwan shi tayi, zasu fi mata sauri idan bata kirga ba, sosai ma tayi mamakin kanta da bata taba tambayarshi yaushe zaizo ba. Tana alaqanta rashin yin hakan da yanda jikinta yake bata ba lafiyar shi ba. Haka rayuwa taci gaba da tafiyar mata har bayan shekara daya, shekarar da tayi dai-dai da lokacin fitar AbdulKadir daga NDA. Lokacin da har a fuskar Mami takan karanci damuwar da ta kasa furta mata akan rashin wani da za'a nuna ace yau yazo zance wajenta. Musamman da aka sa bikin Zahra, dan wannan karin yara uku Hajja zata aurar, Zahra, Mubarak da kuma Yazid da sai yanzun da alama surutun kowa ya ishe shi ya fito da matar aure, duk da sukan jima basu sakashi a idanuwansu ba, da alama yabar Kano din kenan kuma sai dai ziyara. Duk da gidan nasu Allah yai musu fahimta kan cewa shi aure lokaci yake dashi. Duk yanda kaso ka kawar da yaro, idan lokacin shi baiyi ba dole zaka hakura, shisa sam Abba baya jira, wanda duk Allah ya fitowa da miji aurar dashi yakeyi, ko Nusaiba akwai wanda ya fito cikin yan uwa da nufin aurenta, takiya da cewar ita karatu take so tayi, tunda ko sakandire bata kammala ba, babu yanda basuyi akan a tsayar da magana ba, Abba ne yaki, cewar shi su dai jira in zasu iya, yarinyar ta kara mallakar hankalin da zata yarda da auren dan su, karya yanke hukunci da zai zamana kowa baiji dadinshi a gaba ba. Ita kanta Waheedah zuwa lokacin tana so ace ta fara kula wasu, tasha fadama kanta daga yau duk wanda yazo mata da tayin soyayya zata amsa shi, amman saita tsinci kanta da kasa yin hakan. Ko wani ta tsaya dashi takanji kamar tana cin amanar AbdulKadir ne, tanajin rashin hankalin dake cikin hakan, tunda bai furta mata kalmar so ba, asalima bai san tana haukanta ba, amman haka take ji. Zuwa yanzun azumi ta fara da tsayuwar dare akan neman zabin Allah, sai take jin da duk rana kamar ana kara rura mata wutar son AbdulKadir dinne a zuciyarta. Yau ma a gajiye ta dawo daga makaranta, dan bata dawo ba sai yammaci liqis, har a kasusuwan jikinta take jin gajiya. Da sallama ta shiga dakin tana zare takalmanta a kofa. "Mami..." Ta kira tana cilla jakar hannunta kan kujera, da hijabin ta nufi hanyar kitchen inda ta samu Mami tana tace zobo. Kanta ta dora a bayan Mami din tana fadin "Mami kashina kaman zai fito waje..." Dariya Mami tayi tana ture Waheedah din "Dagani nikam... Kashin ne kaman zai fito waje?" Kai Waheedah ta daga mata, cikinta take jin ya tattaru waje daya saboda yunwa. "Nagaji sosai, gashi yunwa nakeji" Robar sugar Mami ta dauko tana zubawa cikin bokitin zobon. "Kije kici abinci..." Dakuna fuska Waheedah tayi "Mami baki dafa mana komai ba?" Murmushi kawai Mami tayi, kamar Waheedah zatayi kuka ta baro kitchen din tana zira takalmanta ta fice daga gidan. Ta manta girkin Mama ne ranar da taci wani abu a makaranta, yunwar da takeji kuma ba zata barta ta tsaya koda indomie ta dafa ba. Zataje taga ko abinda Mama din ta dafa zai ciyu. Bangarenta ta wuce tana shiga da sallama, bata samu kowa a dakin ba, dan haka ta wuce kitchen din, kulolin da ake zuba abinci ta bude, tana cin karo da malmalolin tuwon shinkafa da suke kulle a fararen ledoji. Plate ta dauka, tasaka malmala daya a ciki, lumshe idanuwanta tayi tana addu'a a cikin zuciyarta miyar ta kasance ta taushe ce, ko ya aka watsal-tsala zata iya daurewa taci kodan yunwar da takeji. Zuciyarta taji tayi wani irin tsalle da yasata bude idanuwanta tana dafa dayan hannunta jikin kantar kitchen din, batasan me tagane nashi ba, takun tafiyar shi, kusan shi, ba zatace ga asalin abinda taji ba, amman ba saita juya ba, tasan shi dinne ya shigo kitchen din, AbdulKadir ne, sosai take jin shi gab da ita, jikinta yai mutuwar da ta kasa juyawa ne kawai, tana kallon shi ya mika hannu ya dauki plate ta saman kanta, ta gefe ya zira hannu yana dauko tuwon guda daya, ya saka a plate din yana karo wani guda dayan. Tunda la'asar ya dawo gidan, yana daki a kwance ne saboda bayason surutu, bayason magana da kowa. Ko passing out da akanyi shagali a gida, ayi su calender su menene ya fadama Yassar ya gayama su Hajja bayaso, suyi mishi addu'a kawai, kar wanda ya tara mishi mutane, in sunyi koda yazo zai juya. Sanin halin shi yasa basuyi komai din ba, duk da haka Hajja tasa ya daukar mata hoton shi guda daya, tayi babban agogo ta kafe a falonta. Tunda can bayason mutane, saboda suna bashi haushi, yanzun abinne ya karu, ko kadan bayason jin shi cikin mutane. Yana jiran list din sunaye ya fito zuwa inda za'a kaishi ya hada jakarshi yayi gaba. Tun da yazo yunwa ke cin shi, bai fadama kowa yana hanya ba, a cikin abokan shi wani zaizo Kaduna ya biyoshi. Dan haka bai samu kowa a gidan ba, yaran gidan wasu na boko, wasu na islamiyya, Hajja kuma ta fita, har kitchen ya shiga bai samu wani abinda zaici ba, Nazir kadai yagani yace mishi girkin Mama ne, hakan yasa yunwar tashi bacewa na wani lokaci, kafin yanzun ta sake taso mishi tana fito dashi babu shiri. Hijabin jikinta ya sanar dashi ita dince, bayajin akwai mai saka dogayen hijabai har suna share hanya a gidan nasu banda ita. Ba zaice ga asalin abinda tai mishi take bashi haushi ba, duk da haushin kowa da komai yake ji. Amman nata yai yawa, yanajin inda ta fada mishi Nuriyya ta fara kula wasu da yayi wani abu akai kafin lokaci ya kure mishi. Duk da tun daga ranar da aka daura mata aure, bai sake bari tunaninta ya dame shi ba, ya riga ya faru, babu abinda zai iya akai, amman ya tabashi ta fannin dashi kanshi bai taba tunani ba. Ganinta yanzun din yana saka wani abu matsewa a kirjin shi. Wajen tukunya yadan matsa yana budewa, wata irin miyar kuka tai mishi sallama, tunda yake bai taba ganin miyar kuka mai muninta ba, yana ganin ruwan daban, kukar daban, man da yake a sama kamar daga baya akai tunanin zubashi yana gefe shima. "Mama!" Ya kira yana saka Waheedah sake lumshe idanuwanta da yanda muryarshi ta sauka cikin kunnuwanta tana saka tsikar jikinta tashi. Sai lokacin ta samu karfin juyowa tana sauke idanuwanta akan shi, rigar sojoji ce a jikinshi mai dogon hannu, sai gajeran wando, ya kara mata wani irin girma naban mamaki, sai taganta yar kararrama a gaban shi. Wani yawu ta hadiye ko zuciyarta zata rage gudun da take a kirjinta "Mamaa!!" Ya sake kira a karo na biyu, dai-dai lokacin da Mama ta karaso kitchen din a rikice, dan ko bataji muryarshi ba tasan babu wanda zai mata wannan kiran saishi, bata dai tsammace shi a lokacin bane saboda tasan baya garin "Wacce irin miya ce wannan?" Ya bukata yana tsareta da idanuwa, Kallon shi Mama tayi girman shi na bata mamaki, kaf gidan batajin akwai mai tsayin shi. "AbdulKadir... Saukar yaushe?" Ta tambaya maimakon amsar tambayar dayai mata "Wacce irin miya ce wannan?" Ya sake maimaitawa yana yin kamar baiji maganar datai mishi ba, hadi da dorawa da "Ya mutum zai saka wannan miyar a bakin shi? Meyasa za'ai mana tuwon shinkafa da wannan miyar? Me yasa kike mana girki kamar Abba baya bada kudin da za'ai mana me dadi?" Numfashi Waheedah ta sauke ganin yanayin dake fuskar Mama yasata fadin "Hamma..." Sai lokacin ya juya yana sauke mata kananun idanuwan shi da suke cike da rikici, kai tadan girgiza mishi alamar yabari, kome yake shirin sake fada karya fada, yai shiru kawai. Wani irin tsaki yaja yana ajiye plate din ya fice daga kitchen din, itama Waheedah nata plate din ta ajiye tana rufa mishi baya, Mama tabisu da kallo kawai, dan AbdulKadir ya dade da daina bata mamaki. "Hamma..." Waheedah ta kira tana mayar da numfashi saboda gudu-gudun da tayi wajen binshi, juyowa yayi gabaki daya yana sata runtsa idanuwanta tukunna ta bude su "Meye?" Ya bukata yana tsareta da idanuwan shi da suke birkita mata lissafi, akwai kwarjini na musamman dashi kadaine yake mata "Me zaka ci?" Ta bukata, kai AbdulKadir ya girgiza mata, yana sake juyawa. Yanajin idanuwanta nabin shi harya sha kwana. Numfashi ta sauke tana kai hannu a kirjinta inda zuciyarta take doka mata, takai mintina biyu a wajen tukunna ta wuce tana komawa bangarensu, sam ta manta da wata yunwa da takeji, tana shiga ta wuce daki, tana samun Amatullah ta fito daga bandaki da alamar alwalar magriba tayi dan ana gab da kira, hijab ta cire itama tana shiga bandakin ta gabatar da alwala. * Sanda ya dawo daga sallar isha'i ya samu abinci a dakinshi an ajiye. Tunanin farko da yazo mishi shine Waheedah ce, zama yayi yana daukar plate din ya bude, dankaline da kwai, sai karamin flask din da yasan shayine a ciki, budewa yayi yana zubawa, kamshin shayin yasa shi sanin ba Waheedah bace ba, Hajja ce, ita kadai take saka Na'a'na'a a shayinta. Haka kawai a kasan zuciyarshi sai yaji yaso ace ya fito daga hannun Waheedah ne, daya girgiza mata kai bayana nufin bazaici komai bane ba, yana nufin baisan me zaici ba, amman bata kawo mishi komai ba. A cup ya zuba shayin ya soma hadawa da soyayyen dankalin da kwai yana ci, lokacin yaji an turo dakin da sallamar da kafin ya amsa Yassar ya dora da "Ba zaka iya cemun zaka zo ba?" Kafadu yadan daga ma Yassar din bayan ya amsa sallamar da yayi, gefen shi Yassar ya zauna yana daukar cokalin dake cikin plate din ya cako dankalin yasa

Chapter 15 of 37