ba.
Shima idanuwan shi ya kankance akanta da dakyar take ganin kwayar cikin su, fuskarshi a
kumbure take har idanuwan da alamar rashin wadataccen bacci.
"Ina zaki je?"
Ya maimaita tambayar yana kallonta, tsaye yake ya hango hijabinta da yake share harabar
gidan, blue ne mai hasken da yai mishi kyau sosai. Badan baya ganin masu saka hijab ba,
amman kowa zai gani da hijab itace mace ta farko da take zuwa mishi a rai, kuma bai taba
ganin wanda hijab yake ma kyau kamarta ba, zai rantse yanayin tafiyarta a cikin hijabanta
daban yake. Kamar hijab din na bata wani asirtaccen confidence da idanuwa basa iya gani, sai
yaga kamar ba Waheedah mai sanyin halin nan ba, kwarjininta daban yake mishi in tana cikin
hijabanta.
Idanuwanta take raba mishi, wannan karin cike da wani yanayi da ya saka jikinshi daukar dumi,
kalar hijabin ta kara mata farin da yasa shi furta
"Wanne irin mai kike shafawa?"
Da mamaki bayyane a fuskarta tace
"Vaseline..."
Kankance mata idanuwa ya karayi
"Yana kara haske?"
Dariya tayi tana girgiza mishi kai
"Hamma Vaseline fa"
Kafadunshi yadan daga mata, bazai sani ba, tunda haske take kara mishi a duk ganin dazai
mata.
"Ina zaki je?"
Ya sake tambaya a karo na uku. Da murmushi a fuskarta har lokacin tace
"Makaranta..."
Ta dauka wani abu zai canza tsakaninsu da maganar auren, amman bataji komai ba ita kam,
banda soyayyar shi da duk lokacin da zata dauka babu wani waje a jikinta daya rage wanda
baya dokawa da soyayyarshi, sai ta sake jinshi a wani wajen da batasan yana motsi ba. Babu
abinda ya canza, shidinne dai, Hammanta, Sadaukinta, ko babu maganar auren batajin akwai
inda zatakai soyayyar shi.
"Da sassafen nan? Waye zai kaiki?"
AbdulKadir ya fadi yana katse mata tunanin da takeyi
"Ina da class, nama makara, napep zan hau..."
Kai ya fara girgiza mata yana sata dorawa da
"Ina zuwa Hamma, ba kullum ake kaini ba"
Kan AbdulKadir yake girgizawa har lokacin, yaushe Waheedah din tai girman da zataje
makaranta, ta tafi ita kadai bai zauna mishi ba sam
"Na iya zuwa Allah"
Ta fadi ganin shakkun dake cikin idanuwan shi
"Ki jirani ina zuwa..."
Cewar AbdulKadir din yana juyawa da sauri. Binshi tayi da kallo harya shige bangarensu,
idanuwanta akan kofar tana jiran fitowarshi da dukkan zuciyarta. Baifi mintina biyar ba taga ya
fito yana takowa zuwa inda take, tari tadanyi da yanda zuciyarta ta matse cikin kirjinta kamar
akanta yake tafiyar.
"Muje..."
Yai maganar yana yin gaba, tabishi a baya har wajen motar Yassar, mukullin yasa yana bude
kofar, ita kuma ta zagaya, saida ya zaro wayarshi daga aljihun bayan wandon tukunna ya shiga
ya zauna, hannu ya mika ya bude ma Waheedah dayar kofar ta shigo itama. Wayarshi ya dora
kan cinyarta kamar babu inda zai iya ajiyewa a cikin motar gabaki daya. Daukar wayar tayi ta
rike a hannunta, tanajin shi ya tayar da motar yana jansu suka fice daga gidan.
"BUK, old site..."
Tace mishi
"Nace miki bansani ba?"
Kai ta girgiza mishi
"Me yasa kike fadamun to?"
Ya sake maganar yana dan kallonta kafin ya mayar da hankalin shi kan tuqin da yakeyi. Har
malamansu gabaki daya yasani, bazai ce ga course din da take dashi ba a ranar, amman idan
ya duba wayarshi zai iya fada mata, a cikin labaranta gabaki daya yasan hakan, me yasa take
tunanin bai rike ba? Dan bai amsa ba baya nufin bai karanta ba, baya nufin hankalin shi baya
kai. Shiru tayi bata amsa shi ba, tunda tasan halin shi.
"Bakici abinci ba...bakici komai ba kika fito"
Yai maganar kamar tunanin ya fado mishi. Girkin Mama ne har ranar, da yunwa ya tashi ya
kuma je bangarenta bata gama ba, lokacin daya shiga ma ake fere doya. Ko da yayi maganar
da alamar tambaya ne, Waheedah batajin zata amsa shi, bazai sauke mata fadanshi da sassafe
ba.
"Kinsan yanda abincin safe yake da muhimmanci?"
Murmushi taji ya kwace mata, ba abincin safe bane kadai yake da muhimmanci a wajen
AbdulKadir, duka abinci nada muhimmanci dan baya wasa da cikinshi ko kadan. Wani shago ya
hango hakan yasa shi tsayawa, batare dayace mata komai ba ya fice daga motar. Wayarshi
dake hannunta ta latsa dan taga ko karfe nawa, zuciyarta nayo tsalle zuwa makoshinta ganin
hoton dake kan wayar. Hannuwanta ne babu tantama, da kunshinta da bata manta ranar daya
dauka ba.
"Hamma..."
Ta fadi da wani irin yanayi a muryarta tana shafa screen din wayar. Dai-dai lokacin da
AbdulKadir ya bude motar ya shigo yana dora mata leda akan jikinta da kashedin
"Karki sake fitowa bakici wani abu ba"
Bata abinci takeyi ba, kallon shi take tanajin wani irin yanayi da bazai fassaru ba, har suka
karasa makarantar babu wanda ya sake cewa wani abu. Har department dinsu ya kaita yana
zaune cikin motar saida yaga ta shiga aji tukunna ya sauke numfashin da baisan yana rike
dashi ba, kafin yai wata irin hamma, ba wani bacci ya samu ba jiya, yana kwance yana tunanin
yanda akai rayuwa ta kawo shi inda yake yanzun. Sai dai zuwa safiyar yau komai ya mishi
dai-dai. Tana son shi, zai aureta, ya rigada ya gama duk wani tunani da zaiyi akan hakan.
Yanzun yaga garin da aka kaishi ne abinda yake ranshi, sai yai magana da Hajja dan yaji ko
nawa ne zai tara. Juya motar yayi yana nufar gida.
*
Sallar azahar ya dawo, yana kwance a daki yaji an turo kofar kamar za'a karyata
"AbdulKadir me kayi?"
Yaji muryar Yassar din ranshi da alamun a bace yake. Sai dai a iya tunanin AbdulKadir din
baisan ya mishi wani abu da zai bata mishi rai ba. A nutse ya tashi daga kwanciyar shi ya zauna
yana dakuna ma Yassar din fuskarshi cike da rashin fahimta.
"Kajini ai, me kayi?"
Yassar ya sake fadi yanajin yanda yake gab da kwashe AbdulKadir din da mari. Aiki ya fita, yau
da wuri yake tashi, yana dawowa yakejin ana maganar auren AbdulKadir din da Waheedah
cikin wata shidda tare za'a hada da nasu Yazid. Maganar yake ji kamar wasa, saida ya tambayi
Mama tace mishi da gaske ne, Abba da kanshi ya fada musu. Yasan halin AbdulKadir zai iya
cewa fiye da kowa a gidan, yasan yanda yake son kanshi fiye da tunani, amman bai dauka
yakai haka ba. Bai dauka yakai yai amfani da soyayyar da Waheedah din take mishi ta wannan
fannin ba.
"Kaimun magana yanda zan gane Hamma..."
AbdulKadir ya fadi a kasalance, bacci yakeji, kuma da niyyar yin baccin ya kwanta
"Waheedah... Me kayi AbdulKadir..."
Dan dafe kai AbdulKadir yayi yana fadin
"Oh... Aurenta zanyi..."
Numfashi Yassar yaja ta baki yana fitar dashi ta hancin shi
"Baka son ta AbdulKadir, me kayi haka?"
Kafadu AbdulKadir din yadan daga mishi
"Tana sona..."
Wata dariya Yassar yayi batare da yasani bama
"Wai ma meya faru ka sameni kanata hure-huren hanci kamar dragon... Ba jiya kake mun
maganar yanda take sona ba?"
Kai Yassar ya dafe yana sauke numfashi, sosai yakejin yanda ya kusa kwada ma AbdulKadir
mari
"Da nace tana sonka bance kaje kace zaka aureta baka shirya ba"
Gyara zaman shi AbdulKadir din yayi
"Eh haka Abba yace ba'a aure babu shiri, shisa ba za'ayi nan da sati biyu ba, tare da nasu
Hamma Mubarak za'a hada, wai za'ayi su lefe... Zanje inma Hajja maganar ma... Zan tara kudin
in shaa Allah, albashina da dan yawa... Zai isa idan na tara..."
Ciwon kai Yassar yaji ya saukar mishi, abinda yake nufi daban, abinda AbdulKadir yake fahimta
daban, ba shiri na hidimar aure yake mishi magana ba, shiri na zaman aure da yake bukatar
fiye da soyayya.
"AbdulKadir... Baka son ta"
Dakuna fuska AbdulKadir yayi
"Tana sona Hamma.. Me yasa bazai ishe mu ba?"
Ya karasa maganar yanajin ranshi ya soma baci, baiga dalilin da zaisa Yassar ya dinga
maimaita mishi magana daya kamar itace abu mai muhimmanci a maganar auren, ya tambayi
Waheedah tace tana son shi da aure, shima kuma a shirye yake yai zaman aure da ita, bai
kuma san meye yafi wannan muhimmanci ba.
"Bacci nake ji... Dan Allah kabarni nikam. Na rigada nagama magana da Abba, auren nan zai
faru... Maganganun duk da muke din nan basu da wani muhimmanci tunda ba zasu canza
komai ba"
AbdulKadir yai maganar yana komawa ya kwanta hadi dajan mayafi ya rufe jikin shi. Kai Yassar
yake girgiza mishi yana dana sanin furta mishi cewar Waheedah nasan shi, har ga Allah bai
taba tunanin ba soyayya suke ba, da yasani da bazai taba tayar ma fa AbdulKadir da maganar
ba, amman lokaci ya kure. Kamar yanda AbdulKadir din ya fadane, maganganun shi ba zasu
canza komai ba.
"Dan Allah karka cutar da ita, karkai amfani da soyayyar da take maka ka cutar da ita
AbdulKadir, marainiyace, karka cutar da ita..."
Yassar yai maganar da wani irin yanayi a muryarshi, a kasan zuciyarshi yana addu'ar kar
AbdulKadir din ya taba dana sanin auren Waheedah din, dan yanajin ya yanke hukuncin
aurenta cikin gaggawa, ko da ya shirya zaman aure da ita, yayi gaggawa yagane hakan a jiya
kawai. A wani bangaren yana fatan akwai wani bangare a kirjin AbdulKadir din da yake dokama
Waheedah batare daya sani ba.
"Ka jamun kofar inka fita"
AbdulKadir ya amsa kamar baiji maganganun da Yassar din yayi ba.
"Allah ya tabbatar da alkhairi..."
Cewar Yassar yana ficewa yajama AbdulKadir din kofa, idanuwan shi ya lumshe, dan bashi
Yassar zai saka tunani ba, bacci mai karfi ya dauke shi.
*
Ba zatace ga yanda satika biyu suka wuce mata ba, tasan dai a cikinsu abubuwa da dama sun
faru, harda maganar da Mami tai mata kan auren AbdulKadir din itama kamar Abba tana son
karin tabbaci ne. Data samu din kuma addu'a tai musu
"Allah yasa alkhairin juna ne ku, Allah yasa muku albarka a tafiyar dake gabanku Waheedah,
Allah ya yafe ma mahaifinka ta kyautata makwancin shi"
Ko ita kadai ta zauna addu'ar Mami kan sanyaya wajejen da batasan suna mata zafi ba. Tun
yan gidan na mamakin maganar auren suma har sun daina, dan Zahra ma saida tace mata
"Lallai ma, ki rasa wa zaki aura a duniyar nan sai Hamma AbdulKadir? Ya gama zaneki ya
lallabo kuma zaki aure shi...Tafdin..."
Dariya kawai takanyi, Mubarak ma da yakai ta makaranta a cikin satikan saida yai zancen
"Zuciyarki bata kyauta miki ba Waheedah... Ta rasa wa zata janyo muku sai masifaffen nan. A
kafa aka dauramun AbdulKadir saina tsinke nayi takaina..."
Shima dariyar tai mishi a kunyace. Ba zasu taba fahimtar yanda take son AbdulKadir din ba, ita
kanta ba zatacr ga yawan soyayyar da take mishi ba, halayenshi kaf babu wanda ya taba
damunta balle ya daga mata hankali, fadanshi kan tsaya mata a rai duk idan yai matashi wasu
lokuttan, tana kuma tsoron fadan nashi, sai dai bai taba zama dalilin da zai hanata tunkararshi
da kowacce irin magana ba, kuma bai taba sa taji soyayyarshi ta yi ko alamar dishewa ba. Tana
son shi da duk wani abu da yake tattare dashi.
Kwata-kwata tun satin farko take neman wayar Nuriyya bata samu ba, sau biyu ta biya ta
makarantarsu bata samunta, sai a sati na biyune ta sameta a waya ashe batajin dadine, har
gida taje ta dubata take kuma fada mata sa ranarta da AbdulKadir, tayi mamakin da
'Allah yasa alkhairi'
Kawai Nuriyya ta furta, saidai Waheedah tai mata uzurin cewar dan batada lafiya ne, tadai
gyara mata gidan da yai kamar yayi wata baiga tsintsiya ba, ga tarin wanke wanke, kusan duk
wani abu da yake kitchen din bashida kyau. Ko ina ta gyara mata tsaf, har girki tai mata tukunna
sukai sallama tabar gidan. A satin kuma saida ta koma dubata har sau biyu, zancen bikinta dai
bai sake hadasu ba, zatai karya wannan karin in tace ranta bai mata wani iri ba. Ta dai sake
mata uzuri da rashin jin dadin auren Anas da takeyi har lokacin, hankalinta baiyi kwanciyar da
zatai rawar kafa kan nata auren ba.
Ranar lahadi ce, ba makaranta ke akwai ba, takanje islamiyya a ranakun hutun karshen mako,
amman ranar AbdulKadir zai wuce, an tura shi Minna. Yace mata ba dawowa zaiba sai bikinsu,
bazai tafi bata ganshi ba, text dinshi tagani a wayarta
'Ina wajen motar Hamma Yassar'
Mikewa tayi zuciyarta na dokawa kamar zata fito waje. Hijab dinta ta dauka ta saka, tukunna ta
dauki ledar dake ajiye kan gadon, addu'a take kartaci karo da Mami a falon dan batasan kalar
kunyar da zataji ba. Ita da AbdulKadir din ba wani lokaci suke samu su kadai ba tun bayan
maganar, yanzun takan samu ya amsata dai-dai a WhatsApp, wani lokacin kuma yana kira, duk
da hirar ita zatai mishi, ko in tana mishi a WhatsApp zai kirata yace bacci yake ji ta karasa mishi
labarin zai gani da safe.
Wasu lokuttan kuma in tana makaranta yace karta taho ta jira shi zaije ya daukota. Banda
wannan babu abinda zatace ya canja, in sun hadu zata gaishe shi kamar da, zai satai mishi abu
kamar yanda yakan satai mishi a baya. Allah ya amshi addu'arta bata samu Mami a falon ba,
kamar marar gaskiya haka ta fice da saurinta. Wajen harabar motocin ta same shi ya jingina
bayanshi da motar, jikinshi sanye da rigar saqi ta sanyi marar nauyi, dogon hannune amman
yaja hannuwan rigar sosai, sun tattare daga wajen damtsen shi.
Kallon shi tayi tana daukar hotunan shi cikin kanta dan ya mata kyau sosai da sosai.
"Tafiya zanyi Waheedah..."
Ya fadi lokacin da ta karasa ta tsaya a gefen shi, kai ta jinjina mishi, tana sane da tafiyar kamar
tare zasuyita, dan tanajin yanda zai tafi da fiye da zuciyarta, harda kadan daga cikin ruhinta.
Ledar dake hannunta ta mika mishi ya karba yana rikewa
"Ka kula da kanka Hamma... Banda kin shan magani dan Allah...in bakajin dadi kaje a duba ka
kaji?"
Ta karasa maganar tana kallon shi, tasan yana kula da kanshi takowanne fanni banda lafiyar
shi, saboda bayason magani, bata taba ganin mutumin da bayason magani irin shi ba.
"Kibarni ba yaro bane ni..."
Yai maganar yana tsareta da kananun idanuwan shi, ita kadai take tsira shi da maganganu
haka, take mishi kamar yaro batare data nuna alamar ta raina shi ba. Yanda take nuna tsoron
shi yakan ga hakan har cikin idanuwan ta, amman baya hanata fada mishi duk abinda tayi
niyya. Ledar dake hannun shi ya bude dan bazai iya jira saiya karasa daki ba, inya karasa
dinma jakarshi zai dauka Yassar yakai shi tasha.
"Ba anan zaka bude ba Hamma..."
Waheedah tai maganar da murmushi a fuskarta
"Saboda me?"
Ya tambaya yana saka hannun shi cikin ledar
"Saboda haka kowa yakeyi"
Agogo yaji cikin ledar ya dauko yana fitowa dashi hadi da fadin
"Ni ba kowa bane ba"
Ya karasa maganar yana mika mata agogon ta karba, hannun shi ya miqa mata, akwai wani
agogon a daure, na sojojine ma, kwance mishi agogon tayi ta daura mishi wanda ta siya din,
dubawa yayi yana jinjina kai, nashi agogon ta mika mishi tana jin zuciyarta ta matse waje daya.
"Ki ajiyemun, idan na dawo zan karba..."
Ya fadi, yanayinta yasa shi son yabar mata wani abu, agogon ne kawai abinda yake dashi a
yanzun. Koda bata bashi wani ba yai niyyar cirewa ya daura mata, ganin tayi tsaye tana kallon
agogon kamar ya bata wani bangare na zuciyarshi yasa shi karbar agogon daga hannunta,
dago idanuwanta tayi tana ware su kan fuskarta. Bai manta kashedin Yazid na cewar ba
muharramar shi bace, ya daina tabata, kawai yayi watsi da kashedin ne ya kamo hannunta
yana zagaya agogon a jiki hadi da daurawa. Dariya yayi har hakoran shi suka fito, ta jima
bataga hakoran shi haka ba inba magana yake ba.
"Wahee..."
Ya fadi yana sa tsikar jikinta miqewa
"Wanne irin hannune wannan?"
Yai maganar da dariya a muryarshi ganin agogon na yawo, kwancewa yayi yana saka shi cikin
tafin hannunta ta dumtse
"Ki kula da kanki Waheedah..."
Kai kawai ta iya jinjima mishi, kafafuwanta kamar an kwance abubuwan da suke daure dasu
saboda sanyin da taji sun mata. Numfashi AbdulKadir ya sauke har lokacin yana rike da
hannunta da yakejin shi dan karami a cikin nashi, tsintar kanshi yai da fadin
"Kice ma duk wanda zai kulaki a makaranta mijin da zaki aura soja ne. Ki fada musu Second
Lieutenant A. Bugaje ne, yana da kishi fiye da tunani"
Murmushi mai sauti taji ya kwace mata, duk da idanuwanta cike suke taf da hawaye, kewar shi
ta fara danneta tun yana tsaye a gabanta. Batasan hawayenta sun zubo ba saida taji yatsun
dayan hannunshi ya share kuncinta.
"Ba'a san matar soja da rauni ba"
Ya fadi yana mata murmushi, zuciyarshi yake jin tayi wani shiru, hawayenta sun tsaya mishi a
makoshi, da gaske Yassar yake, tana son shi, a fuskarta yake karantar hakan, yana mamakin
yanda ya dauke shi tsayin lokaci baiga hakan ba. Har a kasusuwan shi yake jin aurenta ne zabi
mafi girma da ya tabayi a rayuwar shi.
"Matar Sadauki"
Tai maganar tana saka idanuwanta cikin nashi. Kai ya jinjina mata yana maimaita
"Matar Sadauki..."
Sunan na zauna mishi a duka jikin shi, wannan karin ita tai dariya. Zatai kewar shi tasani,
amman ya bata abinda zai riketa harya dawo.
"Allah ya tsare maka hanya ya sauke ka lafiya"
Amsawa yayi da
"Amin..."
Yana dumtsa hannunta dake cikin nashi kafin ya saki, muryarshi can kasan makoshi yace
"Zan kiraki..."
Kai ta daga mishi, tukunna ya juya, agogon shi dake hannunta ta dumtsa tana sauke numfashi
mai nauyin gaske, idanuwanta akan shi harya bace ma ganinta...!!!
*#TeamAbdulKadir*
*#TeamWaheedah*
*#BatulMamman*
*#AnaTare*[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
17
Tunda aka fara kamun hankalinta nakan wayarta da Amatullah ta baro mata a gida. Mutuwa
tayi, hakan ya sakata bata dan tasa mata a caji. Ba tunanin gidan da yake shakare da mutane
ko za'a sace mata waya takeyi ba. Amatullah ta tabbatar mata da ta rufe dakin da mukulli ta
kuma taho dashi. A'a, duk inda karfe bakwai tayi tasan AbdulKadir zai kirata, a watannin
shiddan nan da suka wuce mata kamar kiftawar idanuwa, karfe bakwai ya zama lokacin
wayarsu. Duk da tun jiya take baza idanuwa taga ta inda zai bullo, amman shiru, kuma ko da ya
kirata jiya saita tsinci kanta da jin nauyin tambayarshi yaushe zaizo din.
Gashi kamun babu maza, matane kawai, batai tunanin zai kaisu har lokacin ba, satin bikin ma
jinshi takeyi kamar a mafarki. Itace za'ai bikinta wai. Tunda satin bikin ya kama take baza ido
taga ta inda Nuriyya zata bullo, amman sai text tayi mata cewar an kwantar da ita asibiti saboda
haka ba zata samu damar zuwa ba. Ta kikkirata yafi a kirga tana mata ya jiki, sosai taso zuwa
har asibitin dan ta dubata amman bata samu dama ba. Ta dauka taji jiki lokacin bikin Nuriyya
din, sai yanzun ne tasan yanda ake jin jiki da nata bikin yazo, abinci ma duk yinin ranar bata
samu ta saka shi a cikinta ba. Har wani haske take gani yana gilmawa ta cikin idanuwanta duk
idan ta mike saboda yunwar da take ji.
Jiya da sukai waya da AbdulKadir yayi mata fadanshi kaman zai ari baki da tace mishi bataci
komai ba, kanta na mata ciwo. Yanzun ma tana jin alamar ciwon kai na barazar yi mata sallama,
cikinta da taji yayi karar yunwa ta dafe tana gyara zamanta kan kujerar da take zaune.
"Ni fa nagaji wallahi, bakiji yunwar da nakeji ba"
Cewar Zahra da take zaune kusa da ita, tayi matuqar kyau cikin alkyabbar da ta dora kan kayan
jikinta da iri dayace data Waheedah din
"Nifa duk yau babu abinda yaje cikina banda ruwan shayi da safe"
Juyowa Zahra tayi tana kallon Waheedah da tambayar
"Kina aikin me?"
Langabar dakai tayi, Zahra din naganin tayi mata wani irin kyau da kwalliyar da akai mata marar
hayaniya. Jambakin ya zauna kan labbanta kaman dasu aka halicce shi
"Babu wanda yabani abinci fa... Anty Hafsah ce ta tambaya ko naci, to tace bari ta kawomun
kuma ta shiga wata hidimar inajin ta manta..."
Tabe baki Zahra
"Zubawa nayi na shige daki na zauna naci abuna...ulcer ba zata kamani ranar bikina ba"
Dariya Waheedah tayi sosai tana sa Zahra din yin dariya itama. Haka sukaci gaba da hira da
take tsayawa iya kunnuwansu.
*
Tsaye yake bakin wajen, jikin shi sanye da shadda ruwan toka mai cizawa sai hula da tayi
matukar dacewa da shaddar jikin nashi. Ya kankance ma Anty Ramatu kanwar Hajja idanuwan
shi da suke cike da rikici
"Bansan sau nawa zan gaya maka babu maza ba AbdulKadir, duk da yawancin mutanen da
suke wajen yan uwane...me ma kazoyi wajen kamu?"
Ta sake mishi tambayar, dan itama wata makociyarsu da tazo matane zata tafi, ta rakota bakin
kofar wajen ta samu AbdulKadir din ya cakumo rigar daya daga cikin masu gadin wajen yana
shirin hadashi da bango saboda yace mishi maza basa shiga.
"Me zanyi a wajen kamu. Waheedah zaki kiramun ko ki matsa in shiga in kirata da kaina"
Kai Anty Ramatu ta girgiza mishi
"Muma yanzun zamu taho... Addu'a kawai za'ayi... Ka wuce gida gamu nan"
Kallon da AbdulKadir yake mata ya fara tabbatar mata da cewar babu inda zashi kafin ya bude
baki yana tabbatar mata ta hanyar fadin
"Ki kiramun Waheedah..."
Yanajin hakurin shi na gab da karewa, bayason fadin wata magana da zatace ya mata rashin
kunya. Tun karfe wajen biyar ya iso garin Kano, kiran wayarta yayi yajita a kashe. Duk da yana
hanya ma bai hanashi bude WhatsApp dinshi ko zaiga sakonta ba, amman shiru, yinin ranar ko
dan text bai samu ba. Kiris ya kira Yassar ya rokeshi yake ya duba mishi ko tana lafiya, ko
ciwon kan ne ya hanata bude wayar. Da damuwarta ya sauka garin Kano. Ake fada mishi suna
wajen kamu. Ya jira har lokacin daya saba kiranta dan yana da tabbacin ko da bai kirata ba ita
zata kirashi, amman wayarta a kashe.
Bayason ya zauna yana wani tunani, dan ba abokin yinshi bane, shisa yasa daya daga cikin
sababbin kayanshi da Yassar ya nuna mishi, yaso su fita amman yaki, baibi takanshi ba suka
wuce koma ina ne zasu din, dan shi bai tambaya ba, bayason hayaniyar. Waheedah yake jin
gani yaji dalilin da yasaka rufe waya bayan tasan zai kirata. Amman Anty Ramatu nason bata
mishi rai. Bada ita yakejin yin fada ba, da Waheedah ne. Yana kallonta ta jinjina mishi kai
"To kayi hakuri dan Allah ka jira, ayi addu'ar inajin ma an fara saimu fito gabaki daya..."
Ganin har lokacin idanuwan shi na kafe a kanta yasa ta kara fadin
"Kaji... Yanzun zamu fito"
Kai ya jinjina ma Anty Ramatun a hankali yana juyawa ya koma jikin wata mota ya tsaya saitin
kofar wajen. Dan shi a motar Yassar yazo tunda bashida tashi har lokacin. Kuma baiyi parking
dinta a kurkusa ba, kasancewar akwai motoci da yawa a wajen. Baifi mintina goma a wajen ba
ya fara ganin mutane na firfitowa, hakan yasaka shi raba bayanshi da jikin motar da yake jingine
yana tsayawa tare da duba Waheedah da idanuwanshi a cikin taron mutanen. Anty Ramatu ya
hango rike da hannunta, duk da baya ganin fuskarta da take sadde a kasa, ga hular alkyabbar
jikinta ta kara boye mishi fuskarta.
Yana ganin yanayin tafiyarta, har suka karaso inda yake din
"Gata nan mintina biyar, kuyi maganar da zakuyi tafiya zamuyi"
Dakuna ma Anty Ramatu fuska yayi
"Zan taho da ita gida. Nazo da mota"
Kai ta girgiza ma AbdulKadir din, bada ita za'ayi wannan rashin hankalin ba
"Kuyi maganar ku, ko kabari muje gida sai kayi maganar a nutse. Amman yanda mukazo tare
haka zamu koma tare da ita"
Ta karasa maganar tana sauke numfashi. Cikin bacin rai yake kallon Anty Ramatu
"Meyasa ba zamu tafi gida tare da ita ba?"
Kallon shi take itama
"Haka kawai..."
Kai AbdulKadir ya jinjina, koda zaiji maganar da aka fada mishi yana son ayita da hujjar da zata
gamsar dashi, kaf gidansu Yassar ne kawai yakan sakashi yin abu wasu lokuttan batare da ya
bashi kwakwaran dalili ba kuma yayi. Amman ko Abba yana fada mishi dalili, da Anty Ramatu
tabashi wani dalili mai karfi zai iya juyawa ya tafi in yaso saisu hadu a gida. Amman haka kawai
ba zata fara gaya mishi abinda zaiyi ba. Hannun shi ya mika da nufin kamo na Waheedah
yajata subar wajen, Anty Ramatu ta tare da fadin
"Ai ba'a daura ba tukunna, Malam AbdulKadir..."
Bude baki yayi zai gaya mata maganar da take yawo cikin kanshi Anty Talatu ta karaso wajen
tana riganshi da fadin
"Hajiya Ramatu ke aketa nema. Ashe kina nan... AbdulKadir..."
Anty Talatu ta karasa maganar tana maida hankalinta kan AbdulKadir da har lokacin Anty
Ramatu yake kallo
"Ai kamun namu babu maza..."
Kallonta Anty Ramatu tayi
"Na fada mishi fa, wai yanzun tare yake so su koma gida da Waheedah.... Nace yaje zamu taho
gidan..."
Murmushi Anty Talatu tayi, dan ita tasan halin shi sarai, Anty Ramatun ma da alamu ba sosai
suke haduwa da AbdulKadir din ba
"Ki fada mata da Waheedah zan koma gida... Banaso inyi magana tace na mata rashin kunya"
AbdulKadir ya fadi yana kallon Anty Talatu. Kai kawai ta jinjina mishi tana fadin
"Allah ya tsare...muma gidan mukayo"
Ta karasa maganar tana janyo hannun Anty Ramatu da take kallon AbdulKadir daya kankance
mata idanuwanshi cike da rashin kunya.
"Hannunta fa zai rike Hajiya Talatu. Kina ganin babu wata matsala su tafi gida su kadai... Yaron
yanzun basuda kunya wallahi"
Wannan karin dariya Anty Talatu tayi
"AbdulKadir ne Hajiya Ramatu... Babu abinda zai faru... Idan basu tafi taren bane matsala..."
Kai kawai Anty Ramatu ta jinjina, amman duk da haka bataso tafiyar AbdulKadir da Waheedah
din ba, musamman data juya taga ya rike hannun Waheedah din tana bin bayanshi. Wannan
tabe-taben rashin kunyar ko kadan ba sonshi takeyi ba. Idan yai hakuri gobe dai-dai lokacin ta
rigada ta zama mallakin shi duk rikon dazai mata ladan hakan zai samu ba yanzun da babu
komai cikin hakan sai tarin zunubi ba.
*
Bai tsaya da ita ko ina ba sai gaban motar, har lokacin baiga fuskarta ba, kanta a kasa yake,
banda dokawa babu abinda zuciyarta take
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 37