Share this page
gaza a rikon wannan amanar. Ban taba saka maka baki akan Nuriyya ba, yaune na farko saboda yau dinne nake ganin zakayi kuskure mai girma, in kuma ina da wani muhimmanci a wajenka zaka hakura kabarta tunda ba tada inda yafi nan din, babu kuma wanda ya wuce kaddara dagani har kai" Jim Baba yayi yana tattauna maganganun Mama din, zuciyar shi na tafasa sosai, amman yasan gaskiya ce ta fada mishi. Babu inda Nuriyya take dashi da zataje, bakuma zai kyauta ma mahafiyarta ba, dan sunyi zaman da baya manta ta a duk daga hannuwan shi da zaiyi dan gabatar da addu'a. Wucewa yayi dakin batare da yace komai ba sai addu'ar neman shiriya da yake ma Nuriyyar a ran shi. Numfashi Mama ta sauke tana daga labulen tare da fadin "Inya huce kije ki same shi ki bashi hakuri, sai a kira AbdulKadir din aji idan abinda zai gyaru ne" Hawayen fuskarta Nuriyya ta share tana girgizawa Mama kai. "Saki uku ne" Labulen Mama ta saki tana girgiza kanta kawai. Addu'a ce kawai abinda ya rage tsakaninta da Nuriyya, alwalar isha'i ta daura ta shige daki kawai. Nuriyya kuwa kwanciya tayi, batafi mintina goma ba aka kawo wuta. Cajin wayarta ta saka ta fito tsakar gida ta wanke fuskarta ta koma tayi sallar isha'i. Sai take jin tadan samu natsuwa yanzun da tasan babu inda zataje. Baba bazai koreta ba, zata samu tasan yanda zatayi ta kwaso kayanta ta siyar dasu, dan batason shigowa da komai gidan sai kudinta da kayan sawa. Lambar wayar telanta ta laluba tai mishi magana ta whatapp dan akwai kayanta wajen kala biyar da zai kai mata gida washegari, tayi mishi kwatancen nan gidan tace ya kawo mata, su zata samu tadanyi amfani dasu kafin taje ta kwashe kayanta ta siyar ta siyi wasu na kece raini. Ta kuma yanke hukuncin Asma ce kadai zata san aurenta ya mutu, itama dan ta tayata siyar da kayan kitchen dinne, sauran saita samu mijin da zasu girgiza da jin shi tukunna zata sanar dasu dan suzo biki. Biki zatayi na alfarma ba irin na AbdulKadir da akai tayi mata tsegumin ko yar walima batayi ba. Da wannan tunanin na sabuwar rayuwar da zatayi bacci mai karfi yai awan gaba da ita. * Yana shiga gida ya hango Yassar tsaye da waya a hannun shi yana dannawa, parking yayi ya fito daga motar "Kai nake shirin kira, Waheedah tace mun ka fita tun dazun baka dawo ba...kar in sake ina maka magana kana kama hanya ka wuce, dan ubanka kasan yanda ka dagamun hankali? Yanzun ma machine na hau nazo" Juya mishi idanuwa AbdulKadir yayi "Na sha ruwa lafiya... Kai fa?" Ya fadi yana saka Yassar din watsa mishi wani kallo "Bana son iskancin banza... Me ya faru?" Numfashi AbdulKadir yaja yana fitarwa, hadi da jingina bayan shi da motar shi, sosai yake jin kunyar Yassar din, muryar shi can kasan makoshi yace "Dan Allah Hamma kayi hakuri, tun dazun naso inje amman kunyarka nakeji shisa na kasa zuwa.... Wallahi kunyarka nakeji har yanzun... Dan Allah kayi hakuri" Kai Yassar yake girgiza mishi tunda ya fara magana, in duka kudin AbdulKadir ya kashe zai hakura da sake motar, idan fiye da hakan yake bukata zai siyar da motar ya bashi duka kudin, yafi karfin wani dukiya a wajen shi, ballantana dubu arba'in da biyu, shi ya biyo bayan shine saboda yaga yanayin bacin ran daya shiga "Dan Allah ka daina wannan maganar AbdulKadir, kasan kafi karfin wannan kudin a wajena" Kai AbdulKadir ya jinjina "Nasani,amman ajiya kabani saboda baka son taba kudin" AbdulKadir ya karasa yana kallon Yassar din "Nikam kabar maganar kudin nan, kayi zuru-zuru, duk azumin ne?" Kai AbdulKadir ya girgiza ma Yassar din "Banajin dadi Hamma, kirjina ciwo yake mun" Cike da damuwa Yassar yace "Ko zamu koma asibitin ne? Kaga shisa suka so ka kwana rannan dan suga yanayin jikin, kuma baka shan magungunan ko?" Numfashi AbdulKadir ya sake saukewa, kafin ya sauke muryar shi yana fadin "Na saki Nuriyya... Saki uku" Cike da rashin fahimta Yassar yake kallon shi dan kamar daga sama haka yaji maganar "Bangane ka saketa saki uku ba, baka da hankali ne kai? Ina tunanin ka ya tafi? Rashin hankalin naka har yakai haka" Kai AbdulKadir yake girgiza mishi "Baka san me tayi mun ba Hamma, baka tambayi me tayi mun ba, kar kaimun fada bakaji duka abinda ya faru ba" Sosai Yassar yake kallon AbdulKadir din, sam baiji dadin jin maganar ba, badan yana son Nuriyya ba, sai dan saki abune mai girman gaske "Koma me tayi maka, shisa addini ya bada maslaha akan ka fita kabar mata gidan idan kaga zata tunzuraka, karka yanke hukunci sai ka samu nutsuwa ka sauka daga fushin daka dauka. Macece ita, ba ko yaushe take da hankali ba, komai ya fito daga bakinta fada maka zatayi" Shiru AbdulKadir yayi, dan maganganun Yassar din ciwon da yakeji suke kara mishi, cikin taushin murya Yassar yaci gaba da fadin "Nikam sam banji dadi ba, kuma baka kyauta mun ba Wallahi, na dauka munyi magana ta fahimta akan wannan zuciyar taka da rashin neman shawara" Wani abu AbdulKadir ya hadiye da yai mishi tsaye a wuya "Kayi hakuri" Ya fadi yana sa Yassar din kallon shi, yanayin AbdulKadir din na karya mishi zuciya, da kaga alamun shi kasan yana cikin jimamin rabuwa da Nuriyya din, amman kaddarar suce tazo da haka. Da yawan lokutta mutane biyu kan hadu dan su koyar da juna wani darasi kafin kaddara ta raba hanyar su, hakan ne abinda ya faru da zaman AbdulKadir din da Nuriyya "Allah yasa hakan shine mafi alkhairi" Cewar Yassar yana dorawa da "Karka saka damuwa sosai a ranka, babu wanda yake wuce kaddarar shi, yin aure da mutuwar shi lokaci gare su, Allah bai nufi zamanku zai tsawaita ba" Kai AbdulKadir din ya jinjina "Hakane Hamma... Nagode" Sallama Yassar din yai mishi, babu yanda baiyi da ya sauke shi gida ba, amman yaki, cayai yaje ya kwanta ya huta, yana bukatar ya samu wadataccen hutu. Bai wani ja maganar ba, dan kan shi ciwo yake sosai, har bakin kofa dai ya raka Yassar din tukunna ya dawo yana shiga gida da sallama. Baiga Waheedah a falo ba, hakan yasa shi ya wuce cikin daki ya sameta a kwance. Kan gadon ya karasa ya dauki Imaan dake bacci yana sauketa kasa kan nata gadon, ya matsa sosai ya rungume Waheedah ta baya yana sauke wani irin numfashi da baisan yana rike da shi ba. Hannunta ta dora kan nashi dake cikinta, tana lumshe idanuwanta, tana jin yanda zuciyarta ke bude mata duk wata kofa da ta taba son shi hadi da dokawa da karfin gaske, tana jin yanayin kaunar shi da kusancin shi da ita hakane kawai yake haifar da ita, tana jin yanda tayi kewar yanayin sosai. "Sadauki" Ta furta cikin yanayin daya manta rabon da yaji ta fadi, da sauri ya kamata yana juyo da ita, sosai yaji dadin hasken da yake gauraye da dakin, idanuwanta yake kallo yana ganin soyayyar shi a ciki, yana ganin yanayin daya manta rabon daya ganshi a tare da ita. Wata ajiyar zuciya ya sauke yanajin ciwon da yake ji ya rage mishi, rungumeta yayi sosai a jikin shi "Nagode..." Ya fadi batare da yasan dalilin yin godiyar ba, kawai ya tsinci kan shi da son yi mata godiyar ne. Dumin jikin shine taji kamar ya wuce misali, hakan yasa ta taba wuyan shi, tana sauko da hannunta ta saka cikin rigar shi tana taba jikin shi sosai "Zazzabi kakeyi" Ta furta tana dago kanta daga jikin shi tana kallon idanuwan shi da yake kara kankance mata "Tashi ka sha magani" Dakuna fuska yayi yana girgiza mata kai "Ba zazzabi nakeyi ba, banajin dadine kawai" Dan daga mishi girarta tayi duka biyun, duk da sanin dalilin rashin jin dadin nashi na saka wani irin kishi naban mamaki tsirga mata "Shine zazzabin ai, kaci abinci?" Kai ya sake girgiza mata "Banajin yunwa, na sha shayi a wajen Hajja" Wannan karin zame jikinta Waheedah tayi daga nashi "Kaje gidan shine baka taho da Fajr ba Sadauki?" Hararta yayi "Nine bani da kunya ai, kije ki dauko shi da kanki" Murmushi tayi kawai tana sauka daga kan gadon "Karki wahalar da kanki, ni babu maganin da zan sha" AbdulKadir ya fadi, komawa kan gadon tayi tahau tana saka hannunta cikin aljihun shi ta dauki mukullin motar shi, Hajja tace mata yana asibiti rannan, ta tabbatar an bashi magunguna, suna mota dan inya shigo dasu gida zata sa yasha. Aikam magungunan ta dauko a mota tana dawowa dasu dakin ta ajiye kan gado "Bafa zan sha magani ba saboda lafiyata kalau" Har lokacin batayi mishi magana ba, fitowa da magungunan tayi kala hudu, akwai paracetamol a ciki, shi kadai ta ballo guda biyu tana sakawa a hannunta ta mika mishi, akwai ruwa a roba kusa da ita data shigo dashi ta dauko ruwan, kunshin hannunta yake kallo, shiyasa shi karbar maganin yana hadawa da hannunta ya rike "Ka sha dan Allah, shi kadai ne ai" Dauke idanuwan shi yayi daga hannunta yana sauke su cikin nata "Bazan sha ba gobe" Yai maganar cike da tabbaci, kai kawai Waheedah ta daga mishi, tana kallon shi ya shanye maganin yana hade fuska kamar zai amai, sosai ya dakuna fuskar shi yana turo mata labban shi, murmushi kawai tayi, fushi yake dole saboda tasa shi yasha magani. Ko Fajr inta bashi magani da kuka da komai yake sha, ko AbdulKadir din yana nan baya tayata, ca zai mata magani bashida dadi. Tsaf halayen shi yaron ya kwashe. Bata matsa mishi yaci abinci ba, dan tasan in har da kanshi zaice mata bayajin yunwar to bazai iya cin abincin bane ba. Ita ta kashe musu fitilar dakin tukunna tahau gadon, duk da tana rike a jikin shi, ko kadan ya nemi bacci ya rasa, ita kanta ba baccin takeyi ba, rashin baccin shi ya hanata yin nashi, suna kwance har karfe uku kafin su tashi su karasa raya daren ta hanyar gabatar da sallolin nafila. BAYAN WATA SHIDDA Ba zatace ga lokacin da ta taba jin dadin rayuwarta irin watanni ukun nan ba, tana gama iddarta ta fara shiga gari yanda take so, satinta daya bayan rabuwarsu da AbdulKadir ta samu ta fita da rana ita da Asma sukaje gidan suka kwashe kayan kitchen dinta, bata samu AbdulKadir a gidan ba, sai Waheedah da sallamar su kawai ta amsa. Harda kayan abincin da suke kitchen din kaf ta kwashe tana tafiya dasu gida. Haka tace ma Mama cikin kudin kayan kitchen dinta ne data siyar. Da su ta siyi atamfofi da leshi, ta rage sauran da a kayan kwalam da maqulashe ta karar dasu. Kwalliya takeyi ta kece raini, samari ne suke mata layi kala-kala suna mata hadarin kudi, sai yanzun tasan rabuwa da AbdulKadir din alkhairinta ne, sakayau take jinta, a watanta na biyu bayan tagama idda ne ta hadu da Saminu. Matashin saurayin da bazai shige shekara talatin da biyu ba, daga yanayin shi tasan bai taba aure ba kafin ya tabbatar mata da hakan, da wuri ta sanar dashi cewar ita aurenta biyu, nuna mata yayi duk wannan ba matsala bane ba. Dogone sosai mai kirar karfi, kusan da kadan zaifi AbdulKadir, sai dai nesa ba kusa ba, ba zaka hada kyawun Saminu da AbdulKadir ba. Saminu ya tsere mishi tun daga hasken fata da dogon hanci, wayewa kawai AbdulKadir zai nuna mishi. Da alamu Saminu baiyi karatun boko ba, dan turancin shi irin wanda akan tsinta a hanya ne. Yace mata dai shi dan kasuwa ne. Yana siyar da atamfofi da leshi da suke kawowa daga Legas zuwa nan garin Kano. Rashin wayewar shi bai dami Nuriyya ba, saboda yana sakar mata kudi kamar baisan ciwon su ba, ga siyayya yana mata kaca-kaca. Mafarkinta ne yake shirin cika, dan a sati Saminu na iya zuwa da mota kala biyu, watan su daya cif da haduwa ta nuna tana so ya fito, yace mata babu wata matsalar komai. Wannan karin Baba da kanshi ya fadama Wakilan Saminu cewar Nuriyya ta taba aure har sau biyu. Sukace duk Saminu ya sanar dasu. Ko sadaki dubu hamsin suka bayar. Kallo daya zakaiwa Nuriyya kaga tsantsar farin cikin dake fuskarta, ga sabuwar waya kirar infinix dal a kwali Saminu ya kawo mata. Yar walima tayi a gidansu Asma ta tara kawayenta aka ralle, tunda dubu dari Saminu ya bata dan yin hakan. Da kan shi yai mata maganar tarewa ta nuna mishi ita bata da wani kayan daki ba kuma tada kudin yi. Zuwa yayi da mota ya dauke su ita da Asma sukaje wani tsantsareren gida dakuna shidda, da komai da komai a ciki, yace ta duba idan yai mata. Ranar da suka dawo har Mama sai da ta kula da rawae kafar da Nuriyyar takeyi "Ki dai bi komai a hankali Nuriyya..." Cewar Mama, farin cikin da Nuriyya take ciki yasa ta fadin "In shaa Allah. Nagode" Ta wuce daki. A kwana biyun sosai ta matsama Saminu kan maganar tarewa, yace karta damu zaizo har gida ya dauketa ranar wata alhamis da tayi juyin waina gardamammiya da rayuwarta. Har gida Saminu ya shiga suka gaisa da su Mama, yayi musu siyayya sosai ta kayan ciye-ciye, ya kuma kara yi musu godiya tukunna ya fita waje yana jiran Nuriyya. Ta dauki jakarta da mayafinta a kafada Mama ta shigo dakin "Nuriyya kinga kin samu mijin da alamu suka nuna yana sonki, dan Allah kibi rayuwar nan a hankali, kiyi hakuri da duk yanda zata zo miki..." Kai Nuriyya take jinjina ma duk wata nasiha da Mama tayi mata badan ta jita ba, dan hankalinta nakan alkawurran da Saminu yayi mata, na cewar hajjin shekarar da ita za'ayi ta. A satin zasuje suyi hoto, a fara maganar biyan kudi. Tun a mota take fadin "Kasan a jirgi kawai nake hango ni" Dan ta gama fada ma su Asma da duk wasu kawayenta maganar zuwan su Hajji, group dinsu ma yanzun Hajiya Nuri suke kiranta, sunan da yake kara sawa kanta ya kumbura. Tunda suka hau titin unguwar su take kula da cikin kurna yake nausawa maimakon Rijiyar zaki inda gidan daya kaisu ita da Asma yake. Ganin suna barin cikin kurna suna nufar dan dinshe, unguwar da tafi tsana duk a cikin karamar hukumar dala yasata fadin "Naga munayin dan dinshe" Kai Saminu ya jinjina mata, dan shi din bamai yawan magana bane ta kula "Zan amshi sakone" Ya amsa ta a takaice, numfashi ta sauke mai nauyin gaske tana sake gyara zama cikin motar. Haka har suka karasa cikin dan dinshe, kusan karshen unguwar dan gidan da yayi parking ne karshe a unguwar sai wani gidan bulo daga gefe, unguwar shiru kamar anyi sata. Taso ta zauna a cikin motar yace mata ta fito su shiga tare, batason duk wani abu da zai bata mishi rai a daren su na farko yau, shisa ta fito, tadai cika da mamaki ganin ya zaro mukulli a aljihun shi yana bude gidan, bin bayan shi tayi. Karamin gidane dan karami, da dakuna guda biyu, bandaki sai dan kitchen dako kofa babu, sai karamin risho a ciki da yar tukunya daya tabbatar mata da cewar kitchen ne. "Gidan fa babu kowa... Wanne irin sako zaka karba?" Nuriyya ta fadi tana kallon shi, ko kulata baiyi ba ya tura dakin da yake a share tas, da katifa matsakaiciya an gyarata itama, sai kamshin kafur yake da alamar yanayin damuna yasa aka saka saboda warin raba. Zuciyarta taji ta kasa natsuwa da ta shiga dakin "Ni dai ka dauki sakon da zaka dauka mu wuce" Wani irin kallo Saminu yai mata da yasa hantar cikinta kadawa "Babu sakon da zan dauka" Ya karasa maganar yana samun waje gefen katifar ya zauna. "Ki shigo malama kar sauro ya cika mana daki" Cike da rashin fahimta Nuriyya take kallon shi "Ki shigo sai in miki bayani" Zuwa lokacin kafafuwanta har rawa suke, shiga dakin tayi tana kasa zama, dan zuciyarta dokawa take tayi da wani irin karfi da yake saka jikinta bari "Wata hudu da suka wuce na shiga unguwarku wajen wani abokina muna zaune majalissa wajen mai rake kika zo kika wuce. Kina gifta mu naji kin kwantamun har kasan raina, lokacin na furta hakan. Ban bar majalissar ba saida naji kaf labarinki, aurenki da Anas da kuma mijin kawarki da kika aure. Cikin kasa da awanni biyu suka fadamun labarin da nasan kinfi karfina, saboda banida kudin da zaki gani ki saurareni" Saminu ya karasa maganar yana mata wani murmushi da yasa tajin kamar an watsa mata ruwan kankara "Sunana Saminu da gaske, kuma kamar yanda na fada miki dan asalin kauyen dan busai dake nan jahar Kano. Abinda baki sani ba shine ni bani da wasu kudi, mahaifinki yasan sana'ata ni direban babban mota ne, kudin duk da nayi miki hidima dasu, kudin da kikai tunanin ina dasu tsintar su nayi. Sai bayan na tsince sune tunanin inzo miki a matsayin attajirin me kudi yazo mun saboda kin manne mun a zuciya. Ko kadan bakiyi wahalar siyewa ba saboda abin duniya ne a gabanki, nan dinne gidan dana samu na gina a cikin sana'ar da nake... Kar kuma kiyi tunanin akwai wani tashin hankali da zakiyi da zaisa in sakeki saboda wallahi nasha banban da duk wasu maza da kika aura a baya, babu kalar tashancin da banci karo dashi ba, banje wajenki ba sai da nayi shirin zama dake a duk yanda kika so mu zauna" Mayafinta Nuriyya ta sauke daga kafada tana wulwula shi cikin son fifita fuskarta da iska ta daina kai mata, bata taba sanin menene tashin hankali ba sai yau. Tunda Saminu ya fara magana take jin wasu notika na kwancewa a jikinta, cigaba yai da fadin "Duk motocin da kikaga ina zuwa wajenki dasu cikin ragowar kudin da suka ragemun nake arowa, gidan dana kaiku na ubangidan wani abokin wasana ne da yake gadi na roke shi alfarma naje daku kika gani, naso inji babu dadi na yaudararki da nayi, sai naga mu dukan mu badan Allah muka gina dangantakar ba, ni dan son mallakarki, ke kuma dan son abinda nake dashi, zaki iya taimaka mun mu gyara zaman mu daga yau mu nemi yafiyar Allah" Wannan karin dariya Nuriyya tayi da bata da alaka da nishadi, tana son wani yazo ya tasheta daga wannan mugun mafarki, dan a mugun mafarkine kawai zata auri direba, direban ma na babbar mota. "Da gaske ina kasuwanci, tunda idan nakai timatiri legas ina dauko gawayi in dawo dashi nan in siyar" Da kuka dariyar ta kwace mata, kafin tasa hannu tana goge hawayen ta ajiye mayafinta a kasa ta kalli Saminu tana fadin "Wallahi karyar iskanci kakeyi, ni zaka yaudara? Saminu ni zaka yaudara? Sakina zakayi yanzun nan dan bazan taba zama da kai ba. Kaga na maka kalar matar da zata zauna a wannan akurkin kajin?" Dariya Saminu yayi "Saki? Ai wallahi gara ki fara sakawa a zuciyarki mutuwa ce abinda zata gifta ta rabani da aurenki" Mayafinta Nuriyya ta tsugunna ta dauka tana jin yanda duniyar take jujjuya mata, shirin fita takeyi daga dakin, cikin zafin nama Saminu ya taso yana riko hannunta, juyowa tayi tana daga dayan da niyar sharara mishi marin da zaisa ya saketa a daren nan ta koma inda ta fito ya rike hannun yana hadawa da dayan yai mata rikon da takeji kamar zai karyata tukunna yasa dayan hannun nashi ya sharara mata wani irin mari da yasa ta jin wani gishiri-gishiri a cikin bakinta "Na gaya miki duk kalar zaman da kike so muyi dake shi zamuyi, idan mutunci kike so zamu lallaba rayuwar mu, idan rashin mutunci kike so zan zauna dake dashi" Kiciniyar kwacewa take tana auna mishi kalar zagin da in sun kwana a tafa yakanji karuwai nayiwa masu neman su. Shisa yasha alwashin kudin goron da akewa direbobi nabin mata bazai zamana cikin su ba, koba dan komai ba yana tsoron lahirar shi, duk tangaririya da wahalar rayuwar daya sha da saken daya samu sanadin mutuwar iyaye bai saka shi ya lalace ba. Iskanci zabine a kowanne yanayi duk da yakan zo da kaddara, amman akwai zabi a cikin al'amuran rayuwa. Wani marin ya sake dauketa dashi yana wurgi da ita kan katifar dakin ya fita yana kulle dakin daga waje, yanajin yanda take dukan kofar tana cigaba da auna mishi zagin dako a jikin shi. Mota yake ya fito da kayayyakin Nuriyyar da suke ciki ya shigo dasu tsakar gidan, sai da ya dawo kofar gidan ya tsaya abokin shi daya roka alfarma yazo ya dauki motar mutane ya mayar musu ya iso, yabashi mukullin tukunna ya koma gidan ya kulle. Ya shiga ciki ya bude dakin Nuriyyar da ta fito, ya nuna mata karfi yana daukarta ya mayar da ita cikin dakin, bala'i ne take gani irin wanda take jin labarin shi, dan Saminu bai jira ya saka abin duka ba, da hannun shi yaci gaba da mata wani irin duka da ko lokacin da AbdulKadir yake tashen zane su a islamiyya bai taba mata irin shi ba. Tun tana samun bakin zagin shi tana kai mishi yakushi har ta galabaita, nishin kuka ma bata iya fitarwa, a haka Saminu yabi ta yana raya daren. Zuwa safiya kallo daya zakai mata kasan tagama fita daga hayyacinta, a gida yai sallar asuba. Ko kazar daya siyo sai da safen yace mata tazo suci, kai kawai ta iya girgiza mishi dan dakyar ta iya samu tai wanka tayi sallah saboda ciwon da ko ina na jikinta yake mata, shine kawai abin daya tabbar mata da cewar ba mafarkin auren Saminu takeyi ba, da gaske ne auren shi tayi. "Kalar duk zaman da kika zabar mana shi zamuyi Nuriyya" Ya kara tabbatar mata lokacin daya fice daga dakin, kanta kawai ta hade da gwiwa wasu irin hawaye masu zafi na silalo mata, hausawa sunce babu inda son zuciya baya kai mutum, ko da wasa bata taba hango nata zai kawota cikin wannan bala'in ba, ko kadan idan sama da kasa zasu hade ba zatayi zaman aure da Saminu ba...! #TeamAbdulKadir #TeamWaheedah #LubnaSufyan [7/16, 9:57 PM] +234 802 111 7692: Facebook: Lubna Sufyan IG: SufyanLubna Email: Calmlubna@gmail.com Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43 YouTube: https://youtu.be/WwocHslDAYk *ABDDULKADIR* *LubnaSufyan* Epilogue Hannu hijab take gyarama Ikram, ta kasa rankwafawa saboda tsohon cikin dake jikinta. AbdulKadir sai kiranta yake, yace shi bazai shiga cikin gida ba, saida ta fito harabar gidan ma tagan ko motar bai shigo da ita ba, kofar gidan ta fito ita da Ikram tana tsammanin ganin motar shi. Amman ko alamarta babu, dan baima karaso ba duk yabi ya daga mata hankali kamar wani wajen tazo ba gida ba. A shekaru uku zatace babu abinda ya canza musu banda samuwar karin cikin da yake jikinta, rayuwa suke a nutse da ba zatace a kullum cike take da farin ciki ba, suna samun matsalolin da basu fi karfin yin sulhu tsakanin su ita da AbdulKadir ba. Sai dai zuwa yanzun ta fahimci rayuwar haka take tafiya a ko ina, ta koyar da ita babu wani abu waishi dawamammen farin ciki, sai dai akwai farin cikin da kake samu ko yayane a cikin kowacce rana tunda zaka tashi da tarin dalilan da zaka godema Allah domin su. "Waheedah..." Taji muryar Nuriyya ta dirar mata cikin kunnuwa, daga ranar da ta kwashe kayanta rabon da ta sakata a idanuwanta, duk da lokutta da dama takanyi tunanin kotana wacce duniyar, juyawa tayi tana kallon Nuriyyar da rayuwa tasa tayi wani irin sanyi. Da hijab doguwa a jikinta, duk. Da ba wata shigar azo a gani bace a jikinta, ba'a wulakance take ba, dan har kasan ran Waheedah din taji dadin ganinta a nutse. Haka zuciyarta take, wanda suke nufinta da sharri ma da fatan alkhairi take binsu, dan a wajenta duka duniyar bata da wani yawa. Mu duka kuma yan cirani ne da muke haduwa da mutane mabanbanta a hanyar mu, burin kowa shine samun ribar da zai alfahari da ita idan lokacin shi ya cika. Shisa bataga dalilin da zaisa bata lokacinta akan abubuwan da ba zasu amfaneta ba. Sosai Nuriyya taji dadin ganin Waheedah din, tun tana ganin auren Saminu kamar abu na wasa, kamar abinda ba zata tana yarda dashi ba, tun tana mishi rashin mutunci yana jibgarta harta fara saduda da lamurran duniya, dan taje gida Abba ya rantse wannan karin idan harta kaso auren Saminu ba zata zauna mishi a gida ba, Mama kuma tace ba zata bashi hakuri ba. Haka ta hakura ta koma, kullum rana sai Mama ta kirata a waya tayi mata nasihar da saida ya dauketa shekaru biyu bata jita ba, shima shekarun satar fita tayi batare da ta fadama Saminu ba, akai mummunan hatsari a gaban idanuwanta mota ta take mace da goyonta ko numfasawa basuyi ba. Motar kuma ta kama da wuta haka direban ya fito yana ihu yanaci da wuta mutane na kokarin kawo mishi dauki, bata tunanin ta taba tsorota kamar yanda ta tsorata a wannan yanayin dan a gigice ta karasa gidansu da kafafuwanta kamar zararriya, tana shiga gida jikin Mama ta fada tana wani irin kuka mai tsuma zuciya, gabaki daya duniyar bakomai bace ba, kana aikin banza kake cinye kwanakinka, sosai hatsarin ya tuna mata da kwanciyar kabarin da take jiranta, tarin tashin hankalin da yake cikin kwananta na farko ita kadai batare da taimakon kowa ba. Ranar a gida ta kwana, duk da washegari Saminu zai dawo daga Legas. Samun shi tayi ta bashi hakuri kan irin zaman da suke, sosai kuma suka fahimci juna suka kuma nemi juna gafara. Data nutsu saita sami farin ciki a zama da direban data raina, direban da take ganin tafi karfin tayi rayuwar aure dashi a duniyar da bakomai bace, data nemi tana son ta gwada neman aiki da takardun NCE dinta bai musa mata ba, ca yayi ma akwai wani ubangidan shi zai mishi magana yaji. Cikin ikon Allah aka samo mata aikin koyarwa a wata primary ta mata da ke nan dan dinshen. Dai-dai karfin shi Saminu yake mata

Chapter 36 of 37