Share this page
Abdulkadir yayi "Nifa bazan sha wani magani ba" Yazid Waheedah ta kalla da yake tsaye yana kallon su, shima Panadol din yake bukata, ji yake kamar yai ihu ko zata ga yana bukata fiye da AbdulKadir din ta bashi "Hamma kai mishi magana. Kan shi yana ciwo wai bazai sha magani ba" Kallonta Abdulkadir yayi yana tunanin idan Zainab ce da yanzun ya kwada mata marin da bakinta bazai sake gigin kai karar shi ba, amman Waheedah ce, batayi hakan dan ta raina shi ba, yana ganin damuwa tattare da muryarta. "Ki kyale shi tunda bazai sha ba" Yazid ya fadi, yana kuma jin tun maganar ta fito daga zuciyar shi dake wani irin ciwo. "Hamma..." Waheedah ta kira cikin sanyin muryarta da yasaka Yazid din juyawa yana dana sanin fitowar da yayi. Bazai yiwu yanajin azababben kishin Abdulkadir ba, AbdulKadir ne, kanin shi, dan uwan shi ciki daya. Amman zuciyarshi batasan wannan ba, kishi yakeji har idanuwan shi na lumshewa "Me yake faruwa ne?" Yassar daya karaso wajen ya tambaya "Bakomai..." Abdulkadir ya fadi a lokacin da Waheedah tace "Kanshi ne yake ciwo kuma wai bazai sha magani ba, har na ballo kuma" Kallonta Abdulkadir yayi ciwon kan da yake ji na karuwa "Bazan sha ba, ni babu maganin dazan sha. Nace ki ballo mun?" Yake fadi cike da masifar shi "Karbi maganin nan kafin inci ubanka, tunda ta ballo sai kasha wallahi. Kaji na rantse" Hannu Abdulkadir ya mikama Waheedah da take murmushi tana sakashi kankance ido cikin son watsa mata harara. "Mincika..." Yassar ya fadi yana kwashewa da dariya hadi da dorawa da "Anya ba'aima Hajja musayarka a asibiti ba? Abdulkadir wanne irin idone wannan?" Maganin Abdulkadir ya saka a bakin shi ya bude robar ruwan ya hadiye tukunna ya watsama Waheedah da Yassar din harara, yana saka Yassar sake kwashewa da dariya, mukullin motar shi ya saka a jiki ya bude. Bayan motar Abdulkadir ya bude ya shiga, yana dakuna fuska, tsakanin shi da Allah fushi yake an sakashi shan magani. Yazid ma bayan ya bude ya shiga ta bangaren shi. Hakan yasa Waheedah bude gaban motar zata shiga, hango Nuriyya tayi ta shigo gidan, dan tare da ita sukan tafi tunda Babansu bazai taba jerawa ya tafi idi da ita ba. Irin atamfar jikin Waheedah ce ta saka itama, dan tare Abba yai musu da duka sauran matan gidan. Hijab ce dako gwiwarta bata kai ba, daga inda Waheedah take tana hango kwalliyar da take fuskar Nuriyya, musamman jambakinta. Tana kuma hango yanda kugunta ya fito cikin skirt din da take sanye dashi, dan ita riga da skirt tayi. Kai kawai Waheedah ta girgiza dan in tai mata magana kan cewa hijab din tayi karama fada zasuyi da safen nan. Daman sunyi wani kan Anas. Karasowa Nuriyyar tayi "Wallahi na dauka kun tafi, inata sauri" Kai Waheedah ta girgiza mata "Yanzun dai zamu tafi. Na dauka ba zakije ba" Hararata Nuriyya tayi, tana ganin ta mata wani irin kyau naban mamaki. Dariya Waheedah tayi ta bude gaban motar ta shiga. Zagayo Nuriyya tayi ta bude bayan motar ta bangaren Abdulkadir da tunda yaji muryarta ya runtsa idanuwan shi yana budesu da wani irin bugawa da zuciyarshi tayi. Har addu'a yayi karya ganta harya tafi, yanzun ma kokarin kin juyawa yake yaji ta bude kofar, baisan lokacin daya juya ba, yana nasarar sauke idanuwan shi cikin nata. Janbakin ta na saka wani abu cikin kanshi yamutsawa. Tsarin kwalliyar da take fuskarta na samun wajen zama cikin kanshi. Kallon shi Nuriyya tayi, bugun zuciyarta nayin dai-dai da nashi. Yayi mata wani irin kyau cikin farin yadin shi, ga wani irin kamshi da yake, yau kam sosai take jin kasancewarta sallah. Murmushi tayi tana zama cikin motar ta rufe murfin tukunna tace "Ina kwananku" Yassar ne ya amsa yana dorawa da "Nuriyya anyi sallah lafiya?" Amsa shi tayi, turarenta na cika hancin Abdulkadir din, yana saka shi sauke numfashi a wahalce da yanayin da yakeji. Dan matsawa ya sakeyi jin yanda tayi kusa dashi da yawa, amman hakan bai rage mishi komai ba, saima hannunta daya kalla da take gyara hijabinta dashi, itama kunshine, ja da baqin lalle daya saka shi runtse idanuwan shi yana kirga daya zuwa hamsin, har yaji Yassar ya tayar da motar ya juyata suna ficewa daga gidan. Idanuwan shi ya bude yana gyara zaman hannun shi daya dauke babu shiri jin ya taba na Nuriyya, ta gefen idanuwan shi yaga ta kalle shi da idanuwanta da taja da eyeliner suna kara fitowa. Wani abu Abdulkadir yake ji tun daga dan yatsan kafarshi zuwa tsakiyar kanshi da kusancin da Nuriyya tayi dashi. Ita kam yau ranta kal ta zauna kusa da Abdulkadir, ta kuma lura da a takure yake, zataji dadi idan ya zamana itace tai affecting dinshi haka, yana nufin koyayane ya damu da zamanta. Inda idanuwan shi suke kallo take nema kafin ta kula da hannunta ne, dayan hannu ta zaro tana ci gaba da wasa da yatsunta. Abdulkadir na kula da yanda har cikin tafukan hannuwanta itama kunshine, sai dai nata da ratsin baqi, na Waheedah kuma gabaki daya jan lalle ne. Dakyar ya raba idanuwan shi da hannayenta. Dan yana gab da rike su, ita kanta ji yake kamar yasa dan yatsa ya dangwali jambakin da yake lebenta yaji yana da maiqo ko idanuwan shine kawai suke gane mishi har kyalli yake. Da gaske zuciyar shi raini take neman ja mishi, yana da wannan tabbacin yanzun. 'Kar muyi haka dake, dan Allah, terma four na shiga. Ba yanzun zan settling ba, saina gama NDA na fito, an posting dina wajen da zanyi aiki na nutsu tukunna' Abdulkadir yake magana da zuciyar shi yana rokonta data saurare shi, bashida wajen soyayya yanzun. Baya komai a rayuwarshi babu tsari. Wannan ne karo na farko da hakan ya kwace mishi akan Nuriyya, shisa yake jin komai ya cunkushe mishi, komai baya mishi dadi dan baisan yanda zai da ita ba. Ya rasa yanda zai da ita. Kokawa yake da kan shi da zuciyarshi akanta, yanzun kasancewarta kusa dashi yasa shi jin komai ya kara kwacewa daga hannun shi. Motar yaji Yassar ya tsayar alamar sun karaso. Kokarin bude kofar Nuriyya take amman ta kasa "Hamma na kasa, kofar taki budewa" Nuriyya ta fadi tana kallon shi cike da wani irin rauni da yake ji har bayan zuciyarshi. Baisan lokacin dayakai hannu ya bude mata kofar ba. "Nagode..." Ta fadi tana ficewa, idanuwan shi ya runtsa ya bude su, yana dan dafe kanshi da yake kara sarawa "Yazan yi ne wai?" Yai tambayar yana dukan jikin motar kamar ita tai mishi laifi...! *#TeamAbdulKadir* *#FWA* *#AnaTare*[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: ©️ 📖✏ FIKRA WRITER'S ASSOCIATION Facebook: Lubna Sufyan IG: SufyanLubna Email: Calmlubna@gmail.com Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43 *ABDDULKADIR* *LubnaSufyan* 13 "Mutumin da kike so na tare da uniform din nan, ban san waye ni batare dasu ba, ban taba son kaina babu su ba, bana tunanin zaki iya" Kai ta girgiza mishi, hawaye ne cike da idanuwanta amman sunki zuba, in haka masu ciwon zuciya suke ji zasu kasance cikin addu'arta a ko da yaushe, saboda ciwo ne mai matukar radadi. "Ba soyayyar nake tsoro ba Sadauki, ba mika maka dukkan zuciyata bane yake mun wahala, rashin tabbacin ka a rayuwa ta ne, bazan damu da raba soyayyarka da Uniform dinka ba, shi din da yafi ni muhimmanci ne matsalar" Ta karasa maganar tana jin dacin son kan da take son yi a harshen ta, zabi take bashi, ita da take bakuwa a rayuwar shi ko Uniform dinshi daya girma da soyayyar shi? Tana jin idanuwan shi na yawo a fuskarta cike da son ta dago nata su sauka cikin su, amman taki yarda hakan ya faru. "Waheeda..." Ya kira sunanta, yana jan haruffan cikin sigar da shi kadai yake iya hakan. "Karki ce mun in zaba... Ba zaki so amsar ba" Runtsa idanuwanta tayi tana bude su da wani irin ciwo. Me yasa yaki ganin abubuwan data sadaukar saboda soyayyar shi. "Duk abinda kike tunanin kin sadaukar saboda soyayyata bai kai uniform dina muhimmanci ba...karki so kanki da yawa haka" ** "Adda! Addaa!!" Idanuwanta da take ji sun mata nauyi ta bude, tana jin Amatullah ta kwashe da dariyar da ta sata jan karamin tsaki, dan mafarki take, kamar yanda a kwanakin nan mafarkan AbdulKadir din suke addabarta. A cikin daya daga mafarkan ta kira shi da Sadauki, tun bayan tashin ta tsinci kanta da kiran shi Sadaukin dan sunan ya dace dashi ta kowanne fanni. Batasan murmushi ya kwace mata ba saida taji Amatullah ta sake kwashewa da dariya "Addaaaaa!" Hararta Waheedah tayi da yasa Amatullah din sake yin dariya "Jiba inda kike bacci fa, cikin kaya" Miqa Waheedah tayi hadi da yin hamma tana miqa hannu ta dauki wayarta qirar Nokia Symbian E5 dake ajiye a gefe ta danna dan ta duba lokacin, karfe biyu harda kwata. Gabaki daya jikinta a gajiye take jinshi. "Anata nemanki fa..." Kai Waheedah ta dagama Amatullah din, tana kallo ta fice daga dakin. Zaune tayi a wajen tana tunanin ta inda zata fara miqewa, gajiyar da take ji har cikin tsoka da kasusuwan jikinta. Idanuwa ta lumshe, fuskar Abdulkadir na mata yawo, wata irin kewar shi take ji taban mamaki, zata alaqanta hakan da jimawa da tayi bata ganshi ba, tun hutun da yazo na sallah, shima ranar idi ne, tun da suka dawo daga masallacin idi bata sake sakashi a idanuwanta ba harya tafi. Satin da zata fara zuwa makaranta, Babban Yaya ya basu wayoyi, taga cikin mazan gidan ma kusan duk ya ba 'yan matasan. Matanne yace sai sun gama aji shidda. Sosai taji dadin kyautar wayar har ranta. Yassar ya saka mata manhajar kafofin sada zumunta, ciki harda Whatsapp, har kati Yassar din ya saka mata. Lambar Abdulkadir ce ta farko da tazo sakawa taga Yassar duk ya saka mata lambobin su. Sunan kawai ta sake zuwa Sadauki. Shi kuma ta fara dubawa a whatsapp, sai lambar ta nuna bayayi. Sosai zuciyarta taji tai mata nauyi, lambar Yazid ta nema taga Yassar ya saka mata, shi kuwa yana Whatsapp. Sallama tayi mishi tana fada mishi itace. Shima tayi kewar shi ba kadan ba. Zata iya cewa shima tun bayan Sallah da canjin wajen aiki ya dauke shi zuwa Abuja. Sai kwanaki da akace mata ya shigo, ita kuma taje gidan kanwar mahaifinta, kuma ba sosai take kwana ba, ranar dai rabon ba zata hadu dashi bane yasa ta kwana din, taji takaicin abin. Ta kuma yi mamakin da Yazid baije can din ya sameta sun gaisa ba, Yazid din data sani zai nemeta, bazai zo Kano bayan watanni masu yawa ya koma basu gaisa ba. Sai dai Zahra tace mata da Asuba ya wuce, a cewar shi ayyuka sun mishi yawa. Abdulkadir din kuwa text tai mishi tana fada mishi itace, tukunna ta sake tura mishi wani tana tambayar lafiyar shi. Kasa hakura tayi duk da bai amsa mata sauran sakkonin ba, ta tura mishi wani tana cewa bata ganshi a Whatsapp ba, ya bude. Bata samu amsa ba sai bayan kwana wajen biyar tsakani, a kwanaki duk lokacin data samu tana duba wayar taga ko ya amsata bata gani bane. Sosai zuciyarta ta matse lokacin da take dubawa. Ba wata doguwar amsa bace. 'Na bude' kawai ya tura mata a taqaice. Amman zuciyarta ta mata wani irin sanyi. Tun lokacin suke magana ta WhatsApp din, ko tace take mishi magana, dan tana iya tura mishi sakonni sama da ashirin bai amsata ba, lokutta da dama zata ga ya bude ya karanta. Amsawar ce takan mishi wahala. Bai dameta ba a lokacin, har zuwa yanzun kuma baya damunta. Saboda bashi yake son magana da ita ba, itace take son magana dashi. Indai yagani ya karanta, har kasan ranta ya wadace ta, duk rana zata bashi labarai kala-kala, abinda akai a makarantar su, me tayi a ranar, me ya faru da yan gida. Wani lokacin zai karanta ya turo mata Emoji din murmushi, randa ta wuni batai mishi magana ba zai sake turo mata da Emoji, idan yaga ta jima bata amsa shi ba zai kira sunanta. Zata rantse akwai yanayin yanda yake rubuta sunan da takan gane idan a gajiye yake ranar, idan ranshi a bace yake, ko idan yanajin fadan shi. Takan yi murmushi a dukkan yanayoyin tukunna ta bashi labari kamar ko da yaushe. Bata taba gwada kiran shi ba ko sau daya. Takan tura mishi voice notes a whatsapp, a kasan zuciyarta tana fatan shima zai fahimci tana kewar muryar shi ya tura mata. Hakan bai taba faruwa ba. Sai dai lokacin da tayi wani zazzabi mai zafi, ta kwana biyu bata ko samu karfin duba waya ba. Kuma randa ta duba din bata da katin da zata siya data ta duba whatsapp din. Har washegari, tana kwance a daki ya kirata, tana dagawa ta kara a kunne, kafin tace wani abu muryar shi ta daki kunnenta "Me ya sameki?" Lumshe idanuwanta tayi, muryar shi na nutsar da wani abu cikin kirjinta da batasan a tashe yake ba. Kafin ta amsa ya dora da "Meyasa ba zaki fadamun kina wani abu ba?" Murmushi tayi "Hamma..." Bai bari ta karasa din ba "Karki sake mun haka, bana so Waheedah" Numfashi ta sauke a kunnen shi "Bani da lafiya ne Hamma" Ya kai dakika talatin kafin ya sake magana cikin wata irin murya da ta dinga shigarta har kwanya. Duk da hirar batai tsayi ba tai mata dadi. Satin saida ya jera kullum saiya kirata yana jin ya jikinta. Da zata iya mishi karya zata ce bata warke ba dan yaci gaba da kira. Amman ba zata iya ba, daga lokacin kuma idan harya kirata to ta dawo makaranta a gajiya tana bashi labari tace kanta na ciwo, yana kira yace mata tasha magani ta kashe waya ta kwanta. Amman ba zai amsa maganar tata a whatsapp ba. Mutane da yawa zasuyi mamakin badaudaden halin shi, ita kam babu wani abu a tattare dashi da bai mata ba, ko yake bata mamaki. Numfashi ta sauke tana samu ta miqe dakyar, dan inta zauna tunane-tunane ba tashi zatayi ba. Kayan da tazo dauka ta saka cikin wata yar jakar biki da aka ba Mami wajen Walima, ta dauke. Ficewa tayi daga dakin, tana cin karo da Mami a falo "Badai tun shigowar da kikai ba?" Kai Waheedah ta langabar "Wallahi Mami jikina ciwo yake... A gajiye nake jina" Yar dariya Mami tayi "Ai dole, tunda kune kirjin biki" Dariyar itama Waheedah tayi, tana fadin "Kirjin biki kam nashan wahaka Mami" Ta karasa maganar tana ficewa daga dakin. Gidan su Nuriyya ta shiga da yake cike da mutane, tana samun Mama ta bata kayan da ta dauko. Tukunna ta sake komawa gidan nasu, wannan karin bangaren Anty. Tana shiga dakin da sallama. Idanuwanta na sauka kan Nuriyya da ake ma kunshi. "Wai har yanzun ba'a gama ba?" Waheedah ta fadi tana karasawa ta samu waje ta zauna. Nuriyyar bata amsata ba, ko dagowa batayi bama. Bata tsammaci amsa ba, ita kanta zuciyarta ta mata wani irin nauyi dan zata ce ita kadai tasan halin da aminiyarta take ciki. Dan a watannin nan biyu yanda take tashi ta gabatar da sallolin dare kan matsalar Nuriyya, ko ita da Nuriyyar bata tashi tayi addu'a kan matsalar irin haka. Watannin su shidda da fara zuwa makaranta dukkan su, sunyi jarabawar zango na farko a cikin biyun da yake a shekara daya. Dan Nuriyya ma ta riga Waheedah gama jarabawarta ta farko. Duk da lokacin wata irin wayewa taban mamaki ta shigi Nuriyyar. Wasu irin samari take tarawa da Waheedah bata san daga inda ta kwasosu ba. Ko wayar hannunta Nokia C2, daya daga cikin samarin da tayi ne ya kawo mata. A gida tayi karyar cewar Anas ne. Waheedah kawai tasan asalin gaskiya, har fada sukayi akan wayar. Dan Waheedah taga rashin kyautawar abinda Nuriyyar takeyi. Kowa yasanta da Anas, duk da tana tare dashi ne har lokacin saboda yana da yake wahala da ita. Tayi wasu samarin da suka fishi kudi, kyau, da komai, amman a cikinsu babu wanda yake dawainiyar da Anas din yake mata, shisa ta kasa rabuwa dashi. Duk da ya dameta da maganar aure, hakan yasa tayi kuskuren cewa ya gaida mahaifinta. Tasan Baba yasan da Anas, dan Mama kan nuna mishi inya siya mata kaya, koya kawo musu wani abin. Yakanyi hakan, idan lokacin doyane ko dankalin Hausa, da yawa yake siyowa ya kawo musu, haka kayan marmari. Baba ya fara mata fada kan tara samari, duk da tsoron shi da take kamar ranta, dan Baba baya wasa. Tsayayyen mutum ne, bai hanata cigaba da tara samarin ba, sai dai takance suzo da yamma idan Baba bayanan. Tashin hankalin duniyarta ya farane randa Baba yazo ya sameta da wani dan makarantar su, da sai yayi magana ne zaka san bahaushene, idan kaji sunan shi kasan musulmine saboda yanayin shigar shi da kuma askin da yake kanshi. Ranar dukanta ne kawai Baba baiyi ba saboda fada. A ranar ne kuma yace tai ma Anas magana idan da gaske yake ya turo. Tsaye duniyar tai mata waje daya, saboda ko kadan Anas baya cikin tsarin mazan da take son aure, a rikice da wuni ranar tana jiran Magriba tayi, Anas yazo ta bashi hakuri ta gaya mishi ba zata aure shiba, kafin ya jaza mata masifa. Magriba nayi kuwa sai gashi yazo, sai dai bata samu damar fada mishi ba, Baba ya fito ya same su yana gaya mata ta koma cikin gida. Da kanshi yaima Anas din magana. Abu kamar wasa washegari sai ga dangin Baban Anas din a gidansu aka tsayar da magana aka kuma saka biki wata uku kacal. Dan shi daman a shirye yake. Baba kuma yana dan tanadi, tunda yasan auren Nuriyyan zai iya zuwa kowanne lokaci, duk abinda ya samo yakan ba Mama ta ajiye, ita kuma adashi ta shiga irin na talakawa dan a taru a rufama kai asiri. Har da Abba aka karbi kayan sa ranar Nuriyyan aka kuma tsaida magana. Babu kalar tashin hankalin da bai faru a watannin ba, da kukan ta shabe-shabe, da duk yanda take tsoron Baba ta same shi tana tsugunnawa kan gwiwoyinta akan cewar ita bata son Anas. Baba yace ta makara, dan shi bazai zama karamin mutum ba, idan bata san shi meyasa tasa yaje ya gaishe shi. Me yasa ta dinga karbar mishi kaya? Tabbatar mata Baba yayi idan an fasa auren sai dai idan shine ya kwanta dama, ko Anas yazo gidan da kanshi yace ya fasa aurenta. Tun daga ranar tashin hankalinta ya fara, a watannin babu kalar wulakancin da batayiwa Anas, duk da har fada mata yayi zata cigaba da karatunta, shi zaiyi kokari ya biya mata komai, duk dan hankalinta ya kwanta. Amman kamar duk wani abu dazai dan kyautata mata yana kara tunzurata ne. Haka zasu zauna ita da Waheedah susha kuka. Ita kanta Waheedah din saida tai zuru-zuru a yan lokuttan. Tayi-tayi da Nuriyya ta kwantar da hankalinta, taci gaba da addu'a, batasan abinda Allah ya boye a auren ba, amman taqi. Kullum Anas cikin kiran Waheedah yake ya kawo mata karar Nuriyyan, amman ko maganar takan kasa yima Nuriyya saboda halin da take ciki. Abin harya fara bama Waheedah tsoro dan wayar karshe kan karar Waheedah da Anas ya kawo mata, maganganun shi sun tsaya mata 'Nima akwai zuciya a kirjina Waheedah, nima na iya fushi. Wulakancin da Nuriyya taimun jiya yasa naji kamar in samu Baba a fasa auren nan. Sai dai kinsan me? Wallahi bata isa ba, bata isa ta mayar dani dan iska ba, har gardama nayi da Mamana akanta da tace mun ita auren bai kwanta mata ba. Ta hakura saboda na nuna mata bazan iya barin Nuriyya ba. Zaman wulakancin take so muyi aiko? Ki fada mata a shirye nake da ita, wanda duk ya gaji saiya sauko ayi zaman lafiya. Amman ko zata mutu sai an daura auren nan' Sosai maganganun shi suke ma Waheedah yawo, bata gani ba, amman takan karanta wulakancin da namiji a litattafan Hausa, takan kuma ganina fina-finai. Shisa take gujema wulakanta mutane ko yaya suke kuwa. Musulunci ma yai hani da hakan, duk mazan dakan bita a makaranta takan fada musu an mata miji, dan bata son fara abinda ba zata iya karasawa ba. Tana jin yanda bata da wani wajen saka kowa a zuciyarta, Abdulkadir ya cike ko ina "Ina son shi Nuriyya, ina son Hamma, wani irin so da bana tunanin inda zai kaini, saboda bansan ko zuciyar shi zata dokamun yanda tawa take doka mishi ba, amman ina son shi, ban damu ko zai soni ba shima..." Dariya Nuriyyar tai mata lokacin tana tambayarta ko a film din Hausa taji kalaman, to a watannin nan ma sam bata ma Nuriyya zancen Abdulkadir din. Dan hankalinsu ba'a kwance yake ba. Tunda satin bikin ya kama, Nuriyyar ma tayi wani irin sanyi naban mamaki, ko magana batayi sosai. Kamu kadai zasuyi washegarin ranar juma'a, ran asabar a daura aure hadi da yinin biki, kawayensu na islamiyya duk sunzo, harda kawayen Nuriyya na FCE dinsu duk sunzo suma yin lallen da Anty ce ta dauki nauyin shi. Abba kam Allah kadai yasan me yayi musu, dan data shiga gidan Mama na mata godiya sosai. Mami ta siyi kayan kitchen masu yawan gaske, tunda aka saka ranar take siya tana ajiyewa a hankali a hankali. Duk da a yanayin da auren yazo ma Nuriyya bai hana Waheedah jin dadin yanda danginta suka hidimtawa Nuriyyar ba. Kusan duka hidimar bikin Waheedah ce tsaye akai. Daga kan dinkunan da Nuriyya zata saka, itace mai zirga-zirga wajen tela, haka sauran hidindimun da za'ayi. Tunda satin ya kama kuma rabon da suyi magana da Abdulkadir. Har wayar shi ta kira a karo na farko, tajita a kashe. Duk sakkonin data tura mishi a whatsapp basu je ba. Tana fada mishi hidimar bikin da sukeyi. Yanzun ma Whatsapp din ta sake budewa tana bashi labarin zirga-zirgar da tayi, da kunshin da za'ayi musu, da yanda take tunanin zaman kunshin. Saida ta ajiye wayar tukunna take tunanin saida satin bikin ya kama tukunna take fada mishi. Yazid ne ta fadama da suka gaisa kamar yanda sukanyi lokaci zuwa lokaci. Sai taga kamar Abdulkadir din. A kasan zuciyarta take addu'ar Allah yasa lafiyar shi, shirun nashi ya fara mata yawa, inda tana ganin sakkoninta sun tafi ya karanta, tasan yana lafiya, amsata ne kawai baiyi ba. Kunshin akai mata itama, suna dan hira da kawayen Nuriyya, dan ita ta lafe a gefe daya tana kallon kunshin dake hannunta, tana jin kamar bata cikin gangar jikinta, kamar ruhinta ya fita daga jikin ya koma gefe yana kallon abinda yake faruwa da ita, abin yana mata kamar mugun mafarkin da zata iya farkawa daga shi kowanne lokaci. Bata hango ma kanta auren Anas ba kona minti daya, inda tasan hakan zai faru da ta jima da sallamar shi ta hakura da kwadayin hidimar da yake mata. Tasan Baba fiye da kowa, idan ba mutuwa tayi ba baza'a fasa auren ba. Amman tana jin da gaske mutuwar zatayi idan aka daura auren. Ba zata iya zama da Anas ba, bata hango rayuwar aure dashi ba, ko bikinta ba haka ta hasasoshi ba. Saboda ta hango auren hamshaqin maikudi, biki irin na alfarma, gida tanqameme da iyayenta ba zasuyi tunanin kayan daki ba. Duk da taji Baba na fadawa Mama cewar Abban su Waheedah ya siyi kayan daki, katifa kawai zasu siya. Tana kuma da tabbacin masu kyaune, za'a saka mata kayanta a gidan da bai cancanta ba. Gyara zama Nuriyya ta sake yi, sosai takejin abin kamar a mafarki. Waheedah da take ta hira da kawayenta suna dariya take kallo, tana jin wani nauyi a kirjinta. Yanda kawayenta na FCE da basu taba ganin Waheedah ba suke zancenta yai mata zafi, yanda take shiga zuciyar duk wanda yaganta lokaci daya na tsayama Nuriyya a makoshi. Yanzun yanda take dariya na kara hada mata zafi, babu abinda take tunani sai kanta, da za'a daureta a auren Anas cikin kwanaki biyu, Waheedah zata ci gaba da hidimarta babu nauyin auren kowanne talaka akanta. Zata iya samun maikudi ta aura, karshen abinda take si ya faru kenan. Zata karasa mutuwa idan Waheedah ta samu Abdulkadir, shisa take addu'ar karya taba kallon Waheedah din da wannan niyyar. Bazai taba yiwuwa a liqa mata auren Anas, Waheedah kuma ta samu Abdulkadir ba. Sai dai ko bata same shiba, tasan zata samu wani wanda yafi Anas din kudi, zata samu abinda ita bata samu ba kamar koda yaushe. Hakan kadai idan tayi tunani tanajin kamar zatayi hauka. Ko kadan rayuwa batai mata adalci, Waheedah ta zama kamar kaddara ta shigo da su rayuwar junan su dan ta nuna ma Nuriyya abinda duk take son zama amman yai mata nisa. Idanuwanta ta lumshe, alkawari taima kanta ta gama zubda hawaye akan abinda yake faruwa, tunda Anas yace yaji yagani, zata ga ko zai iya jure zaman aure da ita. Dan ta gama shirya mishi wulakancin da zaisaka shi dana sanin aurenta. * NDA KADUNA Wanka ya fito, daga shi sai gajeran wando, da towel rataye a wuyan shi. Ahmad da shi kadaine abokin shi a zaman shi makarantar horar da sojojin tunda yazo ta shekaru hudu da wani abu, har yana shirin fita kuma, dan watannin daya rage musu bashida yawa. Suna shekararsu ta karshe kenan. Babu ruwan shi da kowa, in baka shiga lamarin shiba, sai abinda bazai iya kaucewa bane kawai zai hadaku. Ko wajen motsa jiki, ko training, ko a aji, wani abu dai daya zama mishi dole, saboda akwai masu saurin daukar zafi irin shi. Saidai bakowa yake jurewa hukuncin manyansu idan fada ya kaure ba. Tun suna mamakin taurin zuciya irin na Abdulkadir harsun bari, shisa zuwa yanzun babu mai shiga sabgarshi sai ta kama, a yan Terma five kenan, balle kuma wanda suke kasan shi, har basaso wani abu ya hadasu da Abdulkadir din. Zai dakeka kamar ya samu ganga, musamman idan ya tashi yana jin bacin rai, in ya samu wani ya huce a kan shi yakanji

Chapter 13 of 37