dai..."
Kai Waheedah ta girgiza mata
"A'a ki tafi, ba tafiya zakiyi ba?"
Dan murmushi Nuriyya ta dora kan fuskarta
"Dallah ai kece kike son batamun rai. Ban labari yaushe Hamma din yazo?"
Wannan karin wani tsadadden murmushine ya bayyana kan fuskar Waheedah
"Allah Nuriyya ina son shi fa..."
Wani zafi Nuriyya taji kirjinta ya dauka, ta fada mata kwanaki, bata kulata bane, saboda tayi
kamar sai lokacin tasan tana son Abdulkadir, batasan meyasa take maimaita mata ba yanzun
'In shaa Allah ba zaki taba samun shi ba'
Nuriyya ta fadi a cikin ranta, a fili kuma tabe baki tayi tace
"Kina da hankali kuwa?"
Narai-narai Waheedah tayi da idanuwa, ita kanta tasan batada hankali, ta kuma san ta
rungumowa kanta dala ba gammo
"Bansan yazan ba Nuriyya. Nasan banda hankali, shisama ban taba tunanin samun shi ba,
kawai dai nasan ina son shi"
Ta karasa maganar muryarta cike da rauni
"Yafi miki alkhairi..."
Nuriyya ta fadi a taqaice tana dorawa da
"Bari inje gida... Zan dawo anjima"
Dan batasan Abdulkadir ya dawoba da ba zata shigo gidan haka ba, sauri zatayi taje gida tai
wanka ta tsara kwalliya tukunna ta dawo, batasan me yasa ba, haka kawai taji bataso yaganta
batare da tayi kwalliya ba. Kai kawai Waheedah ta iya daga mata dan batajin zata iya wata
magana, tunanin Abdulkadir ya cika zuciyarta fal.
*
Yassar na kula da yanayin Abdulkadir din tun jiya da yaje dauko shi, dayake sunyi waya a bakin
gate ya same shi tsaye da jakar shi, batare da yace ma Yassar din komai ba ya zagaya ya shiga
mota. Hannu ya saka ya kunna radio din motar cikin nuna ma Yassar din alamar bayason yin
magana. Haka daren jiya duk wanda yazo dan su gaisa da masifa Abdulkadir din yake amsa su,
kamar sannu da zuwan nasu na kara mishi bacin ran da Yassar ya kula yazo dashi. To yau ma
da alama da yanayin ya tashi, shisa tun asuba bai koma dakin nashi ba, duk da zai karya idan
yace abin bai dame shi ba.
Maballan kayansu da tela bai saka musu ba Yassar din yake sassaka musu a jikin riguna, daga
shi sai Aminu a falon, dan duk yawanci sun faffara shiga wanka. Abdulkadir ne ya fito daga shi
sai singlet da gajeran wando
"Ina kwana Hamma..."
Aminu ya gaishe dashi sanin halin shi, shiru Abdulkadir din yayi, hakan yasa Aminu sake gaishe
dashi dan a zaton shi ko baiji bane, daquna fuska Abdulkadir yayi
"Karka dameni Aminu, meyasa zaka fara gaisheni tunda sassafe"
Numfashi Aminu ya sauke yana jinjina kanshi kawai, da idanuwa Yassar yai mishi alama da
yabar falon, bai musu ba ya miqe ya nufi dakinsu, saida ya shiga ya turo kofar tukunna Yassar
da bai dago daga maballin da yake sakawa ba yace
"Me yake damunka?"
Zagayawa Abdulkadir yayi ya zauna inda Aminu ya tashi, bayason yin magana, bayaso ai mishi
magana, komai baya mishi dadi
"Da kai nake, me yake damunka?"
Yassar ya sake tambaya wannan karin yana sauke idanuwanshi kan fuskar Abdulkadir da babu
alamar walwala a tare da ita
"Karka dameni Hamma, dan Allah. Gidane ban niyyar zuwa ba"
Rigar dake hannun shi Yassar ya ajiye yana mayar da hankalin shi kan Abdulkadir din
"Ubanwa yace ka daga waya ka kirani inzo in daukeka to? Idan kasan bakai niyyar zuwa ba
saikai zamanka...meyasa zaka zo kana ma mutane bakin rai, ubanka akai maka?"
Yassar yake fadi dan shima ranshi ya fara baci, hakan Abdulkadir ya kula dashi yasa shi fara
shirin mikewa dan yabar wajen
"Wallahi idan ka tashi ranka saiya baci, ka zauna ban gama maganar da nake ba..."
Komawa Abdulkadir yayi ya zauna, karshen abinda zaiso a yanayin da yake ciki shine bacin ran
Yassar din, yana da zuciya yasani, abinda yake bata mishi rai a kusa yake, amman yana sauka
da wuri, wasu lokuttan idan yai duka ko yai fada shikenan. Amman na Yassar daban ne, yakan
jima ranshi bai baci ba, amman idan ya baci duka gidan sai hankalin kowa ya tashi
"Meke damunka? Bazan sake maimaitawa ba"
Numfashi Abdulkadir ya sauke yana rasa amsar dazai ba Yassar din, bashida wata kwakkwarar
amsa, me zaice mishi? Ranshi a bace yake saboda zuciyarshi nason ja mishi abinda su
dukansu bazai musu dadi ba? Ko kuma fada mishi zaiyi yanda yake ta kokarin ciro Nuriyya
daga duk inda take a cikin jikinshi kafin ta zame mishi matsala amman ya kasa? Wanne daga
ciki zai fada mishi da bazai mishi kallon marar hankali ba, ko zai fada mishi yanda Waheedah ta
saka shi zuwa gida bai niyya ba, yanda alkawarin dayai mata yai mishi tsaye a wuya saida ya
janyoshi garin kano. Amsar da tafi mishi sauki yaba ma Yassar din
"Bansani ba, komai bayamun dadi"
Numfashi Yassar ya sauke, yanayin da Abdulkadir din yai maganar na saka bacin ran da yake ji
soma dishewa.
"Kayita istigfar, tana yaye damuwa"
Kai Abdulkadir ya jinjina mishi yana mikewa tsaye
"Bari inyi wanka... Kayana fa? An dinkamun?"
Dan kallon shi Yassar yayi
"Da bikin su Hamma ai masifa kaimun, na maka dinkin da bai maka ba...."
Daquna fuska Abdulkadir yayi
"Da wanne kayan zanje sallar idi?"
Dan daga mishi kafadu Yassar yayi
"Bakazo da kaya ba?"
Idanuwa ya kankance ma Yassar
"Gajerun wanduna ne fa..."
Maballan shi Yassar yaci gaba da sakawa, ganin AbdulKadir din na tsaye har lokacin yasa shi
fadin
"Kamun tsaye a kai"
Da mamaki Abdulkadir yace
"Hamma da gaske baka dinka mun ba?"
Wani kallo Yassar ya watsa mishi daya tabbatar mishi da gaske yai maganar. Kuma da gangan
yaki dinka ma Abdulkadir din kaya, saboda rashin kunyar dayai mishi wancen karin, har cayai
shi bazai saka wasu manyan kaya ba. Ya fadama kanshi bazai sake dagama Abdulkadir din
hannu ba, tunda ba yaro bane yanzun, amman hakan baya nufin bazai nuna mishi kuskuren shi
ba. Yana jin Abdulkadir din ya wuce, danko dagowa baiyi ba, ya saka daya daga cikin nashi
kayan, idan zasuyi mishi kenan, dan yaga ya kara budewa...!
*#TeamAbdulkadir*
*#TeamYazid*
*#FWA*
*#AnaTare*
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: ©️
📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
12
Da kayan shi rungume a kirji ya shiga dakin hadi dayin sallama, bai samu kowa a falon ba sai
Yassar daya amsa mishi sallamar yana kuma binshi da kallo yana fadin
"Meye a jikin kayan daka rungumosu kamar sabon jariri?"
Murmushin shi Yazid ya kara fadadawa, Waheedah ta goge mishi kayan, akwai kalar kamshin
da ya kula tana yi duk idan ta gifta shi a cikin gida, idan zata fitane kawai bayajin yana kamshin,
sosai kuma yake jinjina ma kokarinta na wajen ganin ta gujema abubuwan da addini ya haramta
mata da mata kan dauka kananun zunubi a zamanin da ake ciki. Haka kawai yau da ita ya tashi
manne a ranshi fiye da kowanne lokaci, shisa yakai mata kayan yace ta danne mishi ta kuma
shafa mishi turare. Tunda ya amso yake jin kayan har kasan zuciyar shi.
"Hamma..."
Yassar ya fadi ganin yanda murmushin Yazid din yake kara fadada da duk dakika.
"Karka dameni Yassar"
Yar dariya Yassar yayi, harda shi cikin yan gidan wajen yima Yazid surutun kin nemo matar
aure, amman yanayin da yake nunawa yanzun kamar na sabon kamu a soyayya
"Anya Hamma? Baka kamu ba kuwa?"
Dakuwa Yazid din yai mishi, yana tsintar kanshi da jin wata irin kunyar kanin nashi da ta bashi
mamaki. Sosai Yassar yake dariya yanzun kam
"Yaa Rabb... Hamma da gaske soyayya kake? Wace mai sa"ar ce?"
Ya karasa tambayar da farin ciki nannade a muryarshi, a kasan ranshi harya fara addu'a da
fatan ta gari ce, akance ba'a shaidar mutum, amman zai tashi tsaye yai shaidar dan uwan shi,
duk a cikin gidan Yazid ne kawai zai bada shaida akan shi batare da wani shakku ba, ya yarda
da nagartar shi dari bisa dari. Yana da tabbacin matar da duk zata kasance karkashin kulawar
shi ba zata taba samun dalilin yin koke ba. Yazid mutum ne mai hakuri da kauda kai akan
al'amuran duniya.
"Wacece Hamma? Kaji? Dan Allah wacece?"
Yassar ya sake jero mishi tambayoyin yana saka shi sauke numfashi mai nauyi. Bai taba
fadama kowa sirrin da yake zuciyarshi ba, har ita Waheedah din da sirrin ya shafa, amman yau
yana jin ya fada ma wani, yana kuma jin son raba sirrin da wani, watakila ya samu karfin gwiwar
fadama Waheedah din itama. Ya kuma san Yassar na da sirri ba kadan ba, idan bashi yace ya
fadama wasu ba, maganar ba zata taba wuce tsakaninsu ba. Cikin sanyin murya Yazid yace
"Bata sani ba har yanzun ai"
Dan ware idanuwa Yassar yayi
"Jiran me kake to? Meyasa baka fada mata ba?"
Kafadun shi duka biyun Yazid yadan daga cikin yanayin dake fassara shima baisan dalili ba
"Ina ganin kamar tayi yarinta ne, hakan nake fadama kaina saboda banason tabbatar da na
rasa karfin gwiwa ne"
Fuskar Yassar dauke da murmushin fahimta yace
"Ba'a yarinta da sanin 'So' Hamma, saboda abune mai wahalar sha'ani..."
Kai Yazid ya iya jinjina ma Yassar din, yanajin jikin shi yayi wani irin sanyi, da gaskene ya
kamata Waheedah tasan yanda yagama tsara musu sauran rayuwar shi idan yana da rabon
gani, bai taba hango komai na rayuwar aure da wata idan ba ita ba. Ko a titi yaga budurwa da
saurayi, ita ce take fado mishi a rai. Idan kallo yake yaga wani abu daya burgeshi, da ita yake
hasaso aiwatar dashi. Yana mata kyauta lokaci zuwa lokaci, amman yana jin tamkar ya janyo
ranar dazai kashe mata duka kudin da suke cikin aljihun shi, ranar da zai siyo duk rigar daya
gani yake tunanin zatai mata kyau ya kawo ta saka mishi yagani.
Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, fuskarta na mishi yawo a cikin kwanyar shi, wucewa
yayi da niyyar shiga daki ya sake kaya, Yassar dakatar dashi da fadin
"Ka fadamun sunanta idan ban santa ba"
Saida ya murza hannun kofar dakinsu tukunna yace
"Waheedah... Waheedah ce Yassar"
Wani dum Yassar yaji cikin kanshi, kafin hanjin cikin shi su hautsina suna saka shi mikewa babu
shiri ya rufa ma Yazid din baya. Yanda ya tura dakin na saka Yazid din tsorata, wani irin yanayi
yake gani a fuskar Yassar daya saka zuciyarshi soma dokawa yana fadin
"Yassar?"
Cike da shakku da alamar tambaya, kai Yassar yake girgiza ma Yazid din yana son ya tabbatar
mishi ba Waheedah bace yake so, yana son ya gaya mishi bai hada soyayya da Abdulkadir ba,
kallon Yazid din yake da idanuwan shi yana rokon shi da cewar zuciyar shi batai mishi haka ba.
"Yassar..."
Yazid ya sake kira wannan karin muryar shi na rawa cike da tsoro, ko kadan bayason abinda
tunanin shi yake shirin hasaso mishi, hannu yadan daga ma Yassar din yana saukewa,
kafafuwan shi har rawa yake jin sunayi dan shi mutum ne mai raunanniyar zuciya. Gadon da
yake dakin ya laluba ya zauna a gefe, yanajin yanda zuciyarshi ke dokawa har cikin kunnnuwan
shi. Yanayin shi kawai da Yassar yake gani na kara tabbatar mishi da yanda ya dade da
soyayyar Waheedah adane a cikin kirjin shi batare da kowa yasani ba. Wani abu Yassar din yaji
yana danne shi, yanda akai bai kula ba na bashi mamaki, dan shi mutum ne mai kula da
al'amuran yan uwan shi. Cikin wani yanayi yace
"Hamma..."
Yana tsintar bakin shi da yi mishi nauyi wajen karasa maganar da yake sonyi. Halin da Yazid din
zai shiga yake tunani. Amman ko jiya da yana neman canji, bayan Abdulkadir din yazo ya dauki
wallet din shi ya bude hoton Waheedah na jiki a manne, ya kuma ga ya sake wallet din, amman
hoton na manne. Yasan kanin shi, yasan kanin shi fiye da kowa a gidan. Idan har ya cire hoton
Waheedah daga dayar wallet din ya mayar a sabuwa tana da muhimmanci a wajen shi, idan har
zai ajiye hoton daga farko to yana da tabbacin wani abu na faruwa a tsakaninsu. Idan har zai
iya bazai bari su hada yarinya daya da Yazid ba, yana numfashi bazai taba bari wannan rikicin
ya faru ba.
"Dan Allah Yassar kace wani abu, a tsorace nake wallah"
Yazid din yace yana sa wani abu tsagewa biyu a kirjin Yassar din, da yake tsaye yana tattaro
duk wani karfin halin dazai iya
"Ba Waheedah ba Hamma, kowacce yarinya banda ita"
Kai Yazid din yake girgiza mishi yana jin iskar dake dakin na fara yi mishi kadan, cikin sabon
tashin hankali yace
"Yassar..."
Da sauri Yassar din ya girgiza mishi kai, ganin yanayin da yake fuskar shi, ya tabbatar Yazid na
tunanin shine yake son Waheedah
"Bani bane, Hamma bani bane ba"
Kan shi Yazid yadan dafe da ya fara ciwo, yanajin alamar zazzabi nason rufe shi
"Abdulkadir ne, ba zance soyayya suke ba kai tsaye, amman hoton tane a jikin wallet din shi
shekara daya kenan..."
Wannan karin da duk hannayen shi Yazid ya dafe kan shi yana wani irin sauke numfashi kamar
wanda yasha gudu. Zazzabin da yake ji na saukar mishi gabaki daya. Dago fuskar shi yayi yana
saka hannu ya dauki hular shi dake ajiye akan gadon ya soma fifita dashi, dan sosai iskar dakin
ta mishi kadan har bayajin tana kai mishi inda ya kamata ballantana ya iya tunanin wani abu.
Shi kanshi Yassar din wani irin nauyi yake ji yana danne shi da bazai ce ga daga inda yake
tasowa ba, amman Yazid din ya kamata yasan abinda yasani shima.
"Koni ba kullum nake kallon fuskar Abdulkadir in fada mishi magana ba, badon ina tsoron shi
ba, sai dan ina gudun ya fada mun maganar da zan dake shi saina karya shi.
Ina kula dasu Hamma, cikin ido Waheedah take kallon shi tai mishi magana..."
Sosai Yazid yake fifita fuskar shi, muryar shi can kasan makoshi yace
"Kadan bani waje..."
Cike da wani irin yanayi Yassar yake kallon shi
"Hamma..."
Kai Yazid ya girgiza mishi, zuciyarshi yake ji ta kumbura ta cika kirjin shi taf, bayason ta
tarwatse a gaban Yassar, bayason ta tarwatse a gaban kowa
"Dan Allah Yassar... Bana son in breaking a gabanka... Abin zaimun yawa..."
Numfashi Yassar din ya sauke yana kallon Yazid sosai, cike da son tabbatar da koma meye zai
biyo baya, koya Yazid din zai karye, zai iya komawa dai-dai. Kamar Yazid yasan me Yassar din
yake tunani yadan tattaro sauran karfin da yake ji yana mishi murmushi hadi da jinjina mishi ka
cike da son tabbatar mishi cewar wannan abin bazai kashe shi ba, tukunna Yassar ya juya ya
fita daga dakin. Kofar na rufewa Yazid ya kwanta kan gadon yana dunkule jikin shi. Wani irin
ciwo yake ji da bai taba tunanin akwai kalar shi ba.
Numfashin shi har tsai-tsayawa yake da yanda kirjin shi yake zafi, yana jin yanda da duk dakika
wani abu a zuciyar shi yana karyewa hadi da faduwa a cikin kirjin shi da wani irin ciwo da
bashida kalaman dazai dora shi. Baisan tunanin me ya kamata yayi ba, asalima tunani daya
yake cike da kan shi da zuciyar shi dake karyewa.
'Bazai hada soyayya da kanin shi ba'
Ko rana aka saka mishi da Waheedah yagane Abdulkadir din najin ta a zuciyar shi fiye da
matsayin kanwa zai hakura yabar mishi, idan ma Allah bai nufa zai aureta ba, su biyun zasu
hakura ta samu wani. Amman soyayyarta zata kashe shi kafin ya hadata waje daya data kanin
shi. Yanzun yake kara godema Allah da bai furta mata ba, yana kuma tabbatar da wannan ne
dalilin daya rike shi harya kasa furta mata. Yafi minti goma a kwance yana son ciwon da yake ji
ya lafa mishi ya tashi ya saka kayan shi dan masallacin idi zasu tafi su duka gidan.
*
Tana fitowa wanka, mai ta shafa ta zura doguwar rigar sabuwar atamfarta, dankwalin ta daura
yanda zata iya dora hijab akai batare daya dameta ba. Fuskarta ta duba a mudubi, atamfar
yellow ce da ja, tayi matukar karbar hasken fatarta, maikon fuskarta taga kamar yai yawa. Farar
hodar da take shafawa ta dauka ta zazzaga a jikin soson hodar Amatullah dan ba zata tuna ko
tana da soson hoda ko bata dashi bama. Murzawa tayi a fuskarta ta ajiye tana sake dubawa.
Kayan kwalliyar da banda farar hodar da wasu cikin turarukan dukan su sauran na Amatullah ne
take dubawa.
Rasa wani abu da zata dauka tayi amfani dashi tai. Ko a gida zata zauna bata tunanin zatayi
wata kwalliya fiye da wadda take fuskarta, ballantana fita zasuyi, su dukan su suke zuwa
masallacin idi a gabatar da sunnar da take cikin zuwa sallar idi. Fuskar mace kan shiga cikin
al'aura, wato abinda ya kamata ya zama a rufe duk lokacin da ta tsara mata kwalliya, sharadin
saka niqab ya fada akanta koda batada kyawun dazai karya alwalar maza. Tana yawan tunasar
da Amatullah da Nuriyya, amman biris suke da ita, wasu lokuttan ma Nuriyya kan ce mata ita ta
cika tsawwala lamurran addini.
Sai dai tasan zunuban da yawancin mutane kan dauka kanana, sune suke taruwa a hankali har
suyi girman da mutum bazai iya dauka ba. kwalli ta hango ta dauka ta sakama idonta, tana
ganin yanda fuskarta ta sake fitowa. Da gaskiyar Mami, kwalli na mata kyau. Mikewa tayi ta
dauki turare ta tuna fita zatayi, ta mayar ta ajiye. Hijab dinta da take a linke ta dauka ta warware
tana sakawa a jikinta. Doguwa ce har kasa, sai dai babu hannu a jiki, tana kuma sane ta dauko
dan kunshin da yake hannuwanta.
Kafafunta ma safa ta saka musu, batai kunshi dan mazan da ba muharramanta ba, tayine dan
kwalliya. Dogayen takalmanta da suke ajiye ta saka. Amatullah kan mata tsiya cewar tana saka
dogayen takalma ne dan bata da nauyin da zata dinga gurdewa. Dariya kawai Waheedah kan
yi, ta riga ta sabane da dogayen takalman tun yarinta, gashi kuma hijabanta wani lokaci suna
dan jan kasa, idan ta saka dogayen takalman sai taga sunfi kyau. Bata ga Mami a gidan ba, har
dakinta ta leqa bayan ta fito, tana da tabbacin suna bangaren Hajja danyin hidimar bikin sallar
da suke haduwa su duka hudun suyi.
Dan haka ta fice daga gidan itama, yau dai ta shirya da wuri, badan gugar da taima Yazid bama
da tuni ta jima da shiryawa. Babu mai mata mita ta cika sanyin jiki. Takawa tayi har inda ake
ajiye motocin gidan tana samun guda daya ta tsaya a jikinta, saitin da zata iya hango bangaren
su Abdulkadir, dan shi take so tagani tunda ta tashi. Tafi minti biyar a tsaye kafin ta hango shi ya
fito, jikin shi sanye da farin yadi da hula rike a hannun shi cikin yanayin da yasa bugun zuciyarta
karuwa. Dago kai taga yayi yana tsayar dashi akanta. Bata hango idanuwan shi daga inda take,
murmushi ya kwace mata.
Sosai take murmushi da yanda mazaunin idon AbdulKadir din kawai take iya hangowa daga
inda yake. Hakan yasata sauke kallonta daga kan shi, zata rantse idanuwanta kawai ta sauke
tana kallon takalmanta, ta sake dago su taga Abdulkadir din tsaye a gabanta yana kankance
mata idanuwan shi, zuciyarta taji cikin makoshinta inda tai tsaye tana ci gaba da dokawa.
"Murmushin me kike?"
Ya tambaya yana tsare ta da idanuwa, dan shi baiga abin nishadi a safiyar ranar ba, kan shi
ciwo yake. Gashi komai baya mishi dadi, kai ta girgiza mishi tana saka shi fadin
"Taqabbal Allaahu minna wa minkum"
Ya dora da
"Ba'aimun dinkin sallah ba"
Cikin yanayin da ya saka wani murmushin kwace mata, dan yanda yai maganar kamar karamin
yaron da akaima gagarumin laifi ya sakata jin tamkar tana kan lilo. Komai nashi ya mata, komai
a tattare dashi. Amsa gaisuwar sallar da yai mata tayi a hankali har lokacin tana murmushi
"Ba abin murmushi bane ba, kayan Hamma Yassar na saka, basumin dinkin sallah ba, kowa an
mishi banda ni"
Abdulkadir din ya fadi yana rasa dalilin da yasa yake gaya mata. Kawai ya tsinci kanshi da son
gaya mata ba'ai mishi dinkin sallar ba, yana kuma jin son gaya mata duniyar ma bata mishi
dadi, baisan ta inda zai fara ba. Idan tana kusa dashi yakan tsinci kanshi dayin abubuwan da
baisan dalilinsu ba. Abu daya yake gani a fuskarta, zai iya yin komai a gabanta, ba zata taba
raina shi ba, bai taba ganin hakan a fuskar kowa ba sai tata, ko Yassar bakomai yake iyayi a
gaban shi ba, a hakan ma ya raina shi dan yana ganin ya bashi wasu yan shekaru, shisa yake
kokarin ganin ya kama girmanshi a gaban Yassar din.
Dayan hannun shi ya dago ya bude mata shi, links ne a cikin tafin hannun nashi. Hakan yasata
tattaro hijab din jikinta ta fito da hannayenta da Abdulkadir din yabi da kallo, zuciyarshi na fada
mishi bai taba ganin hannuwa masu kyau irinsu ba. Links din ta saka hannu ta dauka,
Abdulkadir na rike hannun nata
"Kunshi kikayi"
Maganar ta fito daga kasan makoshin shi lokacin da ya dago dayan hannun shi yana kamo
dayan hannun nata dashi hadi da duba kunshin nata da yakejin na kwance wasu kusoshi cikin
kanshi. Wani irin yanayi yake ji da bazai fadu ba. Motsi yaji a bayan shi, amman bai juya ba,
asalima bayason ya dauke idanuwan shi daga hannuwan Waheedah din, a karo na farko da ko
kadan tunanin hasken fatarta baizo mishi ba, baya ganin komai sai jan lallen dayai wata irin
fitowa a hannunta.
Tun daga nesa Yazid ya hango su, yana jin zuciyar shi kamar zata fito waje, dan zazzabi ne a
jikin shi ruf, dakyar ya iya fitowar ma, baisan kafafuwan shi sun motsa ba lokacin dayaga
Abdulkadir din ya rike hannun Waheedah sai da yagan shi tsaye a bayan shi, amman daga
Waheedah din har Abdulkadir sunyi kamar basu san yana wajen ba. Musamman Waheedah da
yake ganin tsayuwar duniyarta akan Abdulkadir din ta cikin idanuwanta, tana saka shi tuna duka
lokuttan da yake ganin hakan a idanuwanta idan Abdulkadir na wajen, yana sakashi tunanin
kalar sakarcin shi wajen kasa fahimtar abinda yake faruwa a tsakaninta da AbdulKadir din, dan
yana tunanin tayi yarinta ta fahimci wani So ballantana harta fada cikin shi.
"Waheedah..."
Yazid din ya kira yana saka zame hannuwanta daga cikin na Abdulkadir tadan kalli bayan shi
inda Yazid yake tsaye
"Hamma..."
Ta fadi tana saka Abdulkadir din juyawa ya kalli Yazid din shima
"Taqabbal Allaahu minna wa minkum"
Abdulkadir ya fadi yana mikama Yazid din hannu, karba yayi ya amsa yana kuma yi musu
murnar sallah a bisa tsarin addinin musulunci tukunna ya zagaya ta bayan motar ya tsaya, dan
kirjinshi yake ji kamar zai bude. Juyawa Abdulkadir yayi yana mikama Waheedah hannuwan
shi. Dai-dai lokacin da Yazid din ya juyo yana kallon su, links din Waheedah ta daura mishi,
idanuwan shi nakan hannayenta da yake jin kamar ya yanke ya koma Kaduna dasu, ya manna
a jikin bangon dakin shi, duk lokacin dayai ra'ayi ya juya ya kalla. Hakan dayai tunani ya saka
shi laluba aljihun shi ya zaro wayarshi daga ciki.
Waheedah na kallon shi, zuciyarta kamar zata fito waje. Tana kuma kallon shi yana danna
wayar, kafin ya kamo hannunta yana mikar dashi, ya kuma kamo dayan ya dora a kan dayan
cikin yanayin yanda yake son yagan su, ita kam a gabanshi takan koma kamar yar tsana mai
batir da remote, remote din kuma yana hannun Abdulkadir, yanda duk yake so tayi hakan yake
juyata. Idanuwanta tsaye yake kan fuskar shi, tana jin yanda yake rike da yan yatsunta, kafin ya
saki yana duba wayarshi hadi da dan daga mata kai cikin yanayin da yasata sauke hannuwanta
tana murza su cikin hijab, har lokacin tana jin nashi hannuwan manne a jiki.
Kanshi Abdulkadir yadan dafe daga gefe yana runtsa idanuwa, tukunna ya bude su akan
Waheedah yana fadin
"Kaina na ciwo..."
Bata ce mishi komai ba yaga ta juya da sauri, yana bin takalman kafarta da kallo, ko tunanin ta
fadi cikin dogayen takalman nan batayi. Yana kuma kula da yanda kusan duka takalmanta
dogayene. Bayan shi ya jingina da motar yana duba hoton hannuwanta a cikin wayar tashi,
blackberry badai camera ba, sosai hoton ya dauku, shiya mayar kan wallpaper din shi daman
hoton wani lallen ne, wannan dai yafi mishi kyau. Baisan lokacin da yasa hannu ya shafi screen
din wayar ba, yana karama Yazid zazzabin da yake ji. Dan yana kallon duk abinda yake faruwa,
bai daisan haka zai mishi zafi na gaske ba.
"Abdulkadir..."
Ya kira a hankali yana saka Abdulkadir din juyawa ta bangaren da yake ya kalle shi
"Karka sake rike Waheedah, akwai haramci a hakan, kasani ba saina fada maka ba, ba
muharramarka bace ba"
Dakuna fuska Abdulkadir din yayi
"Kunshi tayi Hamma..."
Ya fadi kamar hakan zai zama dalilin da zaisa ya rike hannuwanta
"Na dai fada maka, ranka zai mugun baci idan na sake gani"
Yazid ya fadi cikin yanayin da AbdulKadir din bai taba gani a tare dashi ba. Hakan yasaka shi
daga kai a hankali kawai tukunna ya juya yana hada bayanshi da motar wajen. Ranshi bai baci
ba yau, bashida wannan wajen, kunshin Waheedah ya dauke mishi wannan yau kam, bashida
lokacin fada da Yazid din, duk da ya tsoma mishi baki cikin lamurran da baiga ta inda ya shafe
shi ba. Waheedah ce ta dawo da robar ruwa a hannunta, dayan hannun a dumtse, tana sake
goge mishi komai da yake cikin kan shi. Robar ruwan ta mika mishi, ya karba, idanuwan shi
kafe kan hannuwanta, dan yaji suna danna mishi tunanin Nuriyya inda yake son boye shi dan
karya sake dawo mishi.
Dayan hannun Waheedah ta ware mishi yana ganin Panadol guda biyu, kai yake girgiza mata, a
duniya babu abinda ya tsana irin magani, ko rashin lafiya yake bayasha. Yassar ya taba tura
mishi cikin ayaba yana ce mishi ko itace yaci zaiji karfin jikin shi, kawai yana gutsura ya tauna
magani a ciki, kuma ya tsare shi da saiya hadiye, har amai yayi.
"Bazan sha wani panadol ba"
Ya fadi yana kankance mata idanuwa. Kallon shi Waheedah takeyi
"Kanka na ciwo fa Hamma..."
Dakuna mata fuska
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 37