ciwo ba, ba zata
ji yanda take dukan kirjinta da wani yanayi da yake barazana da numfashin ta ba.
"Magana zamuyi Abdulkadir..."
Ita kanta saida taji sunan ya dira cikin kunnuwanta da wata murya da tasa jikinta bari, balle
Abdulkadir da yake jin kafafuwan shi na rawa, yaune karo na farko a tsayin rayuwar shi data
furta sunan shi kai tsaye haka.
"Waheedah..."
Ya kira da bayanannen mamaki a fuskar shi da muryar shi.
"Idan ba zaka zauna ba shikenan"
Cewar Waheedah cikin sanyin muryarta din nan, da yau yake taba shi a wajajen da baisan
akwai su a jikin shi ba.
"Waheedah..."
Ya sake kira yana jiran hakan yai tasiri a kanta kamar ko da yaushe. Sai dai cikin idanuwanta
yake ganin katangar daya kasa ko motsi balle yayi wani abu akanta tana ginuwa a tsakanin su,
kai yake girgiza mata a hankali, kamar hakan kadai ya isa ya hana abinda yake faruwa ya faru.
"Aurenka zaka saukake mun!"
Maganar ta jima tana mishi yawo kafin ta samu wajen zama tana sa shi kokawa da shaqar
numfashin da yakeyi ta hanci, bude baki yayi yana soma shaqar iskar ta bakin shi ko zata
wadace shi, yakai mintina biyu a haka kafin yaja wani irin numfashi, budaddiyar muryar shi na
sake budewa da wani yanayi yace
"Karki sake mun irin wasan nan, bana so, karki sake"
Wata dariya tayi da sautin ta yai mata wani iri har a cikin kunnuwanta, kafin wasu hawaye masu
dumi da bata da iko dasu suka zubo mata
"Ba wasa nake ba, Sadauki ba wasa nake ba"
Lumshe idanuwan shi yayi yana bude su, Sadaukin da ta kira shi na rage bugun da zuciyar shi
take yi, yana kuma bashi karfin raba jikin shi da bangon wajen yana karasawa inda take yaja
kujerar ya zauna gab da gadon nata, hucin numfashin shi da taji kan fuskarta na sata runtse
idanuwan ta, wani irin abu na tsirga mata har kasan zuciyarta, sanannen yanayin da takan ji duk
idan yai kusa da ita haka take jira ya dirar mata, amman shiru, babu ko alamar shi, hakan yasa
ta bude idanuwan nata tana jan jikinta ta mike zaune, bayanta ta jigina da gadon da take kai
tana kallon shi.
A duk jikin ta take jin lokacin da take jira yayi, lokacin da batasan ta dibarma zama dashi ba sai
yanzun take ji har a kasusuwanta ya cika
"Ka saukakemun auren ka"
Ta sake maimaitawa, wannan karin shi yai wata yar dariya yana kallon ta kamar ta samu tabin
hankali
"Doctor din nan yace babu wata matsala, haka yace baki samu wata matsala ba..."
Abdulkadir yake fadi, maganganun Waheedah din na tabbatar mishi ta samu matsala a
kwakwalwar ta, da hankalinta ba zata furta mishi wannan kalaman ba, bazai kusa da ita haka ta
sake maimaita kalaman ya saukake mata auren shi ba.
"Ki kwanta ki huta sosai kina jina?"
Yai maganar yana daga mata girar shi, cikin yanayin da take jira hannunta da taji ya motsa ya
sauka akan fuskar shi, sai taji shi akan tata fuskar tana shafa kuncin ta, cikin yanayin daya
sashi saurin fadin
"Waheedah..."
Wasu hawayen taji da suka fi na dazun dumi sun sake zubo mata.
"A gaban yarana, Sadauki a gaban yarana..."
Take fadi tana jin wani daci na taso mata daga kirjinta, kalmar hakuri na daya daga cikin
kalaman da baya amfani dasu, shisa yanzun da yake neman ta inda zai fara furtawa ya kasa,
indai abinda take son ji kenan zai kokarin furta mata ko zata dawo cikin hayyacinta.
"Ka saukakemun auren ka, dan Allah ka saukakemun auren ka"
Take fadi tana kamo hannun shi, da sauri ya rike hannun nata yana dumtse wa, yanajin siraran
yatsunta da suke barazanar ballewa kowanne lokaci cikin nashi, suna saka shi sassauta rikon
dayai mata
"Bakisan me kike fadamun ba ko? Baki san kalaman da suke fitowa daga bakin ki ba"
Abdulkadir yake maganar yana yawata idanuwan shi kan fuskarta, yana so tagan shi, yana so
taga shine Abdulkadir. Kamar tasan hakan yake nufi ta furta
"Nagan ka...ka yarda dani naganka, na kuma san me nake fadi. Ka saukakemun auren ka nace,
kuma wallahi da gaske nake... Dan Allah sadauki"
Waheedah ta karasa maganar wani irin kuka na kwace mata, ji take in ta kara kwana daya da
igiyar auren shi a kanta hauka zatayi.
"Kaji dan Allah..."
Hannun ta ya saki yana jan kujerar shi baya, kai yake girgiza mata, baisan akwai wani waje mai
laushi daya rage a zuciyar shi ba sai yanzun da Waheedah tasa kalaman ta dai-dai wajen tana
dannawa. Yana alaqanta wannan hargitsin da yake ji da yanda ya jima baiji tashin hankali ba. A
gaban shi abokan aikin shi babu adadi suka tarwatse, wasu daga sassan jikin su na dukan jikin
shi harda fuskar shi, a gaban shi harsashin bindiga yasha fasa kan abokan aikin shi, mutanen
daya yarda dasu da rayuwar shi, mutanen daya kwashi shekaru yana kwana waje daya dasu a
karkashin kasa ko a samanta. Bayajin akwai sauran tashin hankalin dazai gani ya taba shi,
asalima ya dauka ya jima da katange zuciyarshi da faruwar hakan.
Sai yanzun da Waheedah take karyata shi, take nuna mishi raunin katangun daya gina.
"Dan Allah Waheedah...kinji... Dan Allah ki daina mun wasan nan"
Da mamaki take kallon shi, take hango raunin da bai taba bari tagani ba, da sati daya daya
wuce ne taji taushi irin wannan a muryar shi, ta hango rauni haka a cikin idanuwan shi, da tana
da tabbacin zuciyarta ta gama narke mata da soyayyarshi da ta jima tana dawainiya da ita, da
yanzun tana jikin shi ta rike shi cike da tsoron kar tabar kofar da wani abu zai sake shiga
tsakanin su fiye da yanda ya riga da ya faru, amman yau babu abinda hakan ya kara banda sa
zuciyarta yin wani taurin fiye da yanda takejin ta a kirjin ta.
Ganin da gaske bai dauka cikin hankalinta take magana ba yasa ta fadin
"Mami..."
Cikin wani sabon hargitsin Abdulkadir yake kallon Waheedah da take hawaye kamar an bude
wani abu.
"Mami!"
Ta sake fadi da karfin da yasa Mami turo kofar babu shiri, ganin kukan da Waheedah take yasa
Mami fadin
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un....Waheedah? Me yake faruwa haka?"
Salatin da Mami tayi yasa Anty biyo bayanta tana ma su Salim alamar dasu tsaya nan inda
suke karsu biyo su, ita ta karasa da sauri gefen Waheedah din ta zauna tana rikota jikinta. Kuka
Waheedah take kamar numfashin ta zai dauke, kallon ta Abdulkadir dake zaune yake yana jin
shi kamar a mafarki, yana jin shi shirun da yaji lokacin da bomb ya fara tashi da abokan aikin
shi a karo na farko a gaban shi, shiru ne da bai taba fatan ya sake jin irin shi ba, bai dauka
akwai abinda ya isa ya sake saka shi jin irin shi din bane bama, sai yanzun.
"An...Anty..."
Waheedah take fadi tana jin numfashin ta na mata wani sama-sama.
"Waheedah dan Allah ki daina kukan nan... Kinji...duk gamu nan, ko ma menene, muna nan tare
dake, kina jina?"
Kai Waheedah take girgiza ma Anty tana ci gaba da wani irin kuka da yasa jikin Mami yin sanyi,
dan ita kam tana tsaye ta rasa abinda ya kamata tayi
"Anty kuce ya saukake mun, dan Allah kuce Sadauki ya sakeni!"
Ba Abdulkadir din ba, har su Mami saida suka girgiza da kalaman da Waheedah din ta furta
"Kunji, kuce karya fita daga dakin nan bai rabani da auren shi ba..."
Wannan karin Anty nata idanuwan cike yake da hawaye, fuskar Waheedah din ta dago tana
kallon ta
"Waheedah kinsan me kike fada?"
Anty ta tambaya cike da tashin hankali, tasan auren Waheedah da Abdulkadir wani irin aurene
da yake cike da hargitsi, ta hango mutuwar shi a watannin kusan takwas da suka wuce, amman
bai mutu ba, batasan dalilin da yasa sai yanzun ba. Duk da zatai karya idan tace a watannin
baya bataso mutuwar auren ba, ko dan kwanciyar hankalin Waheedah din, amman yanzun da
take ganin abin na shirin faruwa a gaban idanuwanta, tashin hankalin da take ciki bazai misaltu
ba.
Mikewa Abdulkadir yayi
"Ina zaka je? Ka dawo fa, karka fita baka rabani da auren ka ba... Ka dawo"
Waheedah take fadi tana kai hannu ta fisge karin ruwan dake jikin dayan hannun nata. Mami
kallon ta take tana da tabbacin ba a cikin hayyacinta take ba. Hannu Abdulkadir yadan daga
yana kasa magana, kafin dakyar yace
"Iskar dake dakin tamun kadan... Zan fita in shaqi iska ne"
Yai maganar muryar shi can kasan makoshin shi.
"Ka saukake mun saika fita kasha iskar..."
Waheedah ta fadi tana sa hannu ta share hawayen dake fuskar ta, tana tsayar da idanuwan ta
akan fuskar shi da wani irin yanayi da yasa bugun zuciyar shi karuwa. Juyawa yayi
"Sadauki... Sadauki!!"
Baiko juya ba, tafiya yaci gaba dayi yana ganin kofar dakin ta mishi nisa, kafin ya samu ya fice,
ko kofar bai ja musu ba, Anty ta rike Waheedah gam, dan shirin sauke take daga kan gadon tabi
Abdulkadir
"Anty ki sakeni, kuna kallo fa ya fita, Mami ki bishi ki karbomun takardata, idan bazai rubuta ba
ya fada miki da bakin shi ki dawo ki fadamun..."
Kallon ta Mami takeyi
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
Ta furta a hankali tana ci gaba da maimaitawa, dan batasan wani abu daya kamata ta fadi ba.
Wannan tashin hankalin da yake faruwa a gaban idanuwanta yafi karfinta.
"Anty dan Allah ku kira shi, kinji... Ku kiraa sh..."
Bata karasa maganar ba, ta sulale jikin Anty data saki wani irin sakati a firgice, cikin tashin
hankali ta ke girgiza Waheedah
"Haj Sakina ba kallona zakiyi ba,ku kira likita mana..."
Da sauri Mami ta fita tana ma su Aminu magana dasu kira likitan, kafin kace meye saiga likitan
da gudu, wani ma yana biyo bayan shi, dayan ne yace ma su Anty su fita daga dakin, ya rakasu
har bakin kofa yaja kofar.
"Me yake faruwa wai? Anty me yake faruwa?"
Zainab ta tambaya cike da damuwa.
"Meya sameta? Naga Hamma ya fita a hargitse shima... Dan Allah kuyi mana magana"
Cewar Nabila muryarta na karyewa. Hamma da ta fadi yasa Anty kallon su Aminu da fadin
"Ku bishi dan Allah, kar yace zaiyi tuqi a yanayin da yake ciki..."
Tsayawa sukai suna kallon ta cike da rashin fahimta, tsaki ta saki tana kama hanya cikin sauri ta
fita daga wajen, sai dai bata ga Abdulkadir din ba, ko alamun shi bata gani ba, har wajen
asibitin ta duba amman bata ganshi ba, wajen da taga an ajiye motoci ta nufa tana duddubawa,
duk da batajin tasan wacce irin mota Abdulkadir din yake da ita, kawai dai ta duba ne ko Allah
zaisa tagan shi. Dan dafe kai Anty tayi tana fadin
"Oh Allah na..."
Kasan zuciyarta take addu'ar Allah ya kaishi gida lafiya idan can din ya nufa, kafin ta juya tana
nufar hanyar da zata mayar da ita cikin asibitin Aminu Kano din, a duk jikinta take jin wannan
abin bana lafiya bane...!
*
#Abdulkadir
#FWA
#AnaTare[7/27, 1:13 PM] +234 816 124 4732: ©️
📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
02
A nutse yake tuqin shi, dan ba ranar bane karo na farko daya taka mota cikin rashin kwanciyar
hankali, yana dai kula da yanda ake kauce mishi saboda katon tambarin bajon sojoji da yake
manne jikin gefen motar, sai kuma sticker dinsu a gaban motar, ko babu kayan da suke jikin shi,
kallo daya zakai ma motar kasan cewa ta soja ce. A haka harya kara gidan shi da yake Rijiyar
Zaki, kasancewar shi muqamin shi First lieutenant, akwai sojoji guda biyu masu tsaron shi a
gida. Daya daga cikin sune ma ya bude mishi gate, bai damu da ya tsaya ya gyara parking din
ba, kawai kashe ta yai ana harabar gidan yana fitowa, mukullin ma a jiki yabar shi bai cire ba.
Cikin gidan ya karasa, har saida ya wuce tsakiyar falon da takalman shi, kaman daga sama yaji
muryarta na fadin
'Babu sallama Sadauki? Takalmi har tsakiyar daki, ina sallah a wajen fa'
Bai kokarin cire takalman nashi ba, sallamar dai ya tsinci kan shi dayi. Jin shiru babu wanda ya
amsa yasa shi takawa cikin gidan yana karasawa bangaren Nuriyya, hadi da sake yin wata
sallamar, yasan tana can tana bacci, idan akace batai sallar Azahar ba bazai musu ba, ranar
girkinta ma tana bacci, balle yau da tasan ba itace dashi ba. Karasawa yayi bangaren dakin
baccin ta yana kwankwasawa, tukunna ya tura ya shiga, tana zaune kan gado, kunnenta liqe da
earpiece, ta tusa system a gaba, da alama kallo takeyi.
Jin shigar shi yasa ta zare earpiece din guda daya tana kallon shi a kasalance da idanuwanta
da suka fi komai a tattare da ita jan hankalin shi. Miqa tayi hadi dayin hamma tukunna tace
"Masoyi..."
Kamar yanda take kiran shi ko a gaban waye. Ganin yayi tsaye yasa ta mika hannunta tana
mishi alama daya karasa, tana sakeyin wata hammar
"Bacci nake ji Allah, jikina namun ciwo"
Tsintar kan shi yayi da tambayar
"Me kikayi?"
Daquna mishi fuska tayi
"Kallo nayi... Me Waheedah ta dafa dan Allah?"
Zuciyar shi yaji tayi wata irin dokawa da sunan Waheedah din da Nuriyya ta kira. Bai iya amsa
ta ba ya wuce kan shi tsaye yana nufar bandaki. Da ido Nuriyya ta bishi tukunna ta tabe baki
tana mayar da earpiece din data cire daga kunnen ta daya taci gaba da kallon da shigowar shi
ta katse mata. Rigar jikin shi ya fara cirewa yana mamakin yanda akai Nuriyya bata kula da jinin
da yake jikin kayan shi ba, bata ma kula da damuwar da take shimfide a fuskar shi ba. Kan
washing machine din da yake cikin bandakin ya ajiye kayan daya cire.
Ruwa ya bude ma kanshi yana yin tsaye, sanyin ruwan na nutsar da wani abu a tattare dashi,
idanuwan shi ya kankance saboda bayason rufe su gabaki daya, baisan meya faru ba, baisan
ya akai ba, yana da wata irin zuciya ta fitar hankali da bata da alaka da aikin shi, tun kafin
shigar shi aikin soja yake da wannan zuciyar da har Abban shi yakan mishi addu'ar samun
saukin ta a can baya, bayason rufe idanuwan shi ballantana yaga me zuciya ta saka shi aikata
ma Waheedah yau a karo na farko tun auren su. Bazai bata lokacin shi tunanin abinda ya
rigada ya wuce ba, wannan ba halayyar shi bace sam, yau bazai zama na farko ba, idan abu ya
wuce mishi ya riga ya wuce tunda ba zai iya komawa ya sake ba, gaba kawai zai duba ya
kiyaye. Da wannan tunanin a ranshi ya karasa wankan ya fito.
Baibi takan Nuriyya ba, kamar yanda bata bi ta kan shi ba, da towel din daure a jikin shi ya fito
daga bangaren ta yana nufar bangaren Waheedah, dan nan yake da tabbacin zai sami kayan
shi a nutse, dakin baccinsu ya shiga, kamshin ta na cika mishi hanci, tana son amfani da
turarukan larabawa, sai dai bazaice ga wannne da wanne takan hada kamshin su ya bada kalar
da yake bayarwa ba. Kan gadon ta ya hango kayan shi data fito mishi dasu, ya karasa ya
dauka, riga ce fara qal, sai wando iya gwiwa baki mai wasu igiyoyi. Sai da ya fara saka singlet
din da take ta zabga kamshi tukunna ya saka sauran kayan yana daukar towel din ya koma
bangaren Nuriyya dashi.
Idan yace ga asalin abinda yakeji karya yake, kan shi dai yayi mishi wani irin nauyi.
'Ka saukakemun auren ka'
Maganar Waheedah ta dawo mishi tana saka shi kai hannu dai-dai kirjin shi inda yake jin wani
abu na mishi kaikayi ya murza. Bandaki ya koma ya mayar da towel din ya rataye, tukunna ya
karasa kan gadon yana kwanciya gefen Nuriyya da ko inda yake bata kalla ba. Hannun shi ya
mika yana zare earpiece din kunnenta, ya sake miqawa ya zare dayan, juyowa tayi fuskarta
babu walwala
"Kallo fa nake..."
Idanuwan shi ya kankance mata, yana sa ta fadin
"Dan Allah mana Masoyi, kuma wallahi yunwa nakeji, nace me matarka ta dafa muku kayi
banza dani"
Runtsa idanuwan shi Abdulkadir yayi, duk idan yana tare da ita yakan sha wahala, komai saiya
fito fili yayi magana tukunna zata gane, ba surutu yake so ba.
"Bata da lafiya... Tana asibiti"
Sai yanzun tagane dalilin dayasa ya shigo mata, inda Waheedah din nan bata tunanin jarabar
nacin ta zai sa tabari Abdulkadir ya shigo bangarenta haka kawai batare da wani dalili ba. Tabe
baki tadan yi
"Allah ya bada lafiya..."
Ta fadi da wani yanayi a muryar ta da tasa Abdulkadir mikewa
"Me kikayi yanzun?"
Ya bukata muryar shi can kasan makoshi, ware mishi idanuwa Nuriyya tayi
"Me nayi nikuma?"
Hannun ta ya damqo yana janta kamar bata da wani nauyi zuwa gab dashi
"Abinda kikayi da bakin ki yanzun nake nufi"
Wani irin yawu Nuriyya ta hadiya, tasan halin shi, tun kafin dan zaman nan na auratayya ya
hadasu, tunda kusan fiye da rabin rayuwarta a gidan su tayi ta, ta kuma san raini na daya daga
cikin abinda baya dauka ko daga wajen yayyen shi, iyaye ne kawai Abdulkadir yake dagama
kafa, sai dai ita din takan mishi abubuwa da yawa sai dai ya kalleta ya wuce, sosai ta shagwabe
mishi fuska tana matsawa hadi da shigewa jikin shi.
"Yunwa nake ji Masoyi...dan Allah karkai mun fada... Ni banyi komai ba, addu'a nai mata"
Yanda ta narke mishi yasa shi sauke numfashi, a hankali ya janye ta daga jikin nashi, yana dafe
kan shi da hannu.
'Karka fita baka saukemun auren ka ba'
Maganganun Waheedah ne suke ta dawo mishi. Tsintar kan shi yayi da saukowa daga kan
gadon, asibitin yake son komawa ya tabbatar da bata samu matsala a kwakwalwar ta ba,
bayajin zai samu wata nutsuwa in bai tabbatar ba
"Ina zaka je?"
Nuriyya ta bukata
"Zan koma asibitin ne"
Ya amsa ta, yana jiran yaji ko zata ce mishi su tafi tare ta duba jikin Waheedah din. Baisan wani
abu taji ya taso mata tun daga kirjinta har cikin wuyanta yana mata tsaye ba. Bata son nuna
mishi kishin da taji, dan haka tace
"Zaka dawo da wuri? Kayo mun take away dan Allah..."
Kallon ta Abdulkadir yakeyi
"Me yake damun ki Nuriyya?"
Itama kallon shi takeyi
"Bangane me yake damuna ba, kar ince ka taho mun da take away idan zaka dawo da wuri?
Jikina yamun nauyi bazan iya girki bane shisa, kuma laifinka ne daka qi dauko mun yar aiki..."
Kai Abdulkadir yake girgizawa
"She was your BestFriend (Aminiyarki ce a baya)..."
Ya furta a hankali, yana mamakin Nuriyya din, yanda yake kallon ta yasa ta cire earpiece din
daga kunnuwanta tana ture system din, saukowa tayi daga kan gadon tana takawa ta karasa
inda take, ba zaka kirata gajerar mace ba, amman tsayin Abdulkadir na kwatance ne, ga girman
da yake dashi kasancewar baya wasa da motsa jiki, sai ta ganta yar karama a gaban shi,
matsawa tayi tana riko hannun shi, hadi da daga kanta tana sauke idanuwan ta cikin nashi.
"Masoyi yau kam laifina kake ta gani, bansan me nai maka ba"
Ta karasa maganar tana tattaro hawaye dakyar ta cika idanuwan ta dashi
"Karki mun kuka Nuriyya... Karki mun kuka"
Dayan hannunta ta saka tana share kwallar data taru a gefen idanuwan ta
"Bansan me nayi maka ba..."
Yanda tai maganar cike da rauni ya taba shi, numfashi ya sauke, baisan me yake damun shi ba
yau. Ganin ya fara saukowa a fuskar shi kawai yasa Nuriyya dora kanta a kirjin shi tana sakin
wani guntun murmushin da take da tabbacin baya gani, batasan meya faru ba yau, idan zatai
fada dashi Waheedah ba zata zama sanadin hakan ba, yaune karo na farko daya jefeta da
kalmar alaqar dake tsakaninta da Waheedah a baya, ba zata bari hakan ya faru ba, tana sane
sarai saboda ba tace zataje duba Waheedah din bane.
"Kome nayi kaina a kasa Masoyi...kar a sauke sojan a kaina yau... Umm?"
Tai maganar tana kara narkewa a jikin shi, dagota yayi yana sumbatar gefen fuskarta batare da
yace komai ba ya juya yana ficewa daga dakin, bin bayan shi tayi tana leqawa ta tabbatar da
yayi nisa tukunna ta dawo dakin tana turawa hadi da fadin
"Ni na dora mata ciwon... Yanzun haka karya take... Bansan yaushe Waheedah ta koyi
munafunci da bakin hali ba..."
Da kan gadon zata koma taci gaba da kallon da take, sai kuma ta fasa saboda cikin ta dayai
wata irin murdawa da yunwa. Babu shiri ta koma tana ficewa daga dakin, kitchen din ta ta nufa,
a dispenser ta dibi ruwan zafi ta hada shayi, kwalin biscuit ta dauka tana wucewa ta koma daki,
ta kasa daina zagin Waheedah a cikin zuciyar ta, yau da safe Abdulkadir din ya koma bangaren
ta, shisa ta zauna tana kallon film din ta a system dan kartai tunanin yanda Waheedah take
manne dashi kamar mayya, yanzun ma ba zata bari tunanin Waheedah ya bata mata rai ba,
hakan take maimaitawa kanta harta samu wajen zama tana gyara system din ta dauki earpiece
din ta mayar a kunnuwanta ta kunna film din, tukunna ta dauki kofin shayin data ajiye tana janyo
biscuit din gabanta.
**
A hanyar shi na zuwa asibitin yaga Apple, dan harya wuce yayi parking yana fita daga motar ya
taka da kafar shi zuwa wajen masu Apple din, hannu ya saka a aljihunshi duk da yasan bai
zuba kudi ba, amman Waheedah ta dauko mishi wandon, yana da tabbacin duk wani abu dazai
bukata tasa a ciki, akwai kudin kuwa, biya yayi ya karbi ledar yana komawa mota. Zai iya
rantsewa da Allah duk idan ya dawo gida ya ganta, yakan manta yanda yake iya yin komai
batare da ita a kusa dashi ba. Dayan aljihun yakai hannu ya laluba yaji I.D cards din shi na ciki
yana kuma da tabbacin har da ATMs din shi duk suna ciki.
Sai da ya sauke wani numfashi da baisan yana rike dashi ba tukunna yaja motar yana nufar
asibitin. Parking din motar shi yayi a inda akeyi yana takawa zuwa cikin asibitin, hannun shi rike
da ledar Apple din daya siya, indan tashi ba za'a ci Apple ba, dan yana cikin kayan marmarin da
baya kan shi sam-sam. Zama da Waheedah ya sashi koyan ci, duk da haka badan yana jin
dadin shi ba, duk idan ta yayyanka yanda takan yi ta miqo mishi bayaqin dauka, ko idan tana ci,
data gutsura take miqa mishi shima ya gutsura saita sake karba, ko ruwa zata sha saita bashi
shima. Baya tunanin Waheedah na iya cin wani abin yana zaune ko yaci nashi bata bashi ba.
Sosai yake shiga cikin asibitin harya karasa bangaren da Waheedah din take, dan sun kama
dakin da ita kadai ce, kan shi tsaye ya nufi dakin da yake lamba ta sha biyu, kwankwasawa yayi
hadi da murza hannun kofar ya shiga batare daya jira an bashi izinin ba. Baiga kowa a dakin ba
sai Anty, da sallama ya karasa ta amsa shi a sanyaye. Ledar Apple din ya ajiye a gefe kan
abinda akan ajiye kayayyaki, tukunna ya kalli Anty da take zaune tana goye da Ikram yana fadin
"Ke kadai? Ya jikin nata?"
Cikin sanyin murya ta amsa shi da
"Sun koma gida, ba'a son hayaniya ne ko kadan, saboda jininta yayi wani irin hawa. Abdulkadir
me yake faruwa?"
Kujera ya janyo yana samun waje ya zauna, fuskar shi da bata cika fara'a ba ya sake hadewa
waje daya. Tambaya na daya daga cikin abubuwan da bayaso, musamman wadda ta shafi
matsalar iyalin shi.
"Tambayar ka nake, me yake faruwa?"
A daqile yace
"Tsakanin mune... Komai zaiyi dai-dai..."
Sakin baki Anty tayi, na dan lokaci ta manta waye Abdulkadir, yanzun yake tuna mata.
"Tsakanin kune take rokon mu da mu karbar mata takardar saki a hannun ka?"
Dago da kan shi yayi yana kallon Anty
"Kaman yanda nace, tsakanin mune. Anty karki wuce hurumin ki dan Allah"
Ya karasa yana mayar da kallon shi kan Waheedah da take bacci, hannun ta da yake daure da
ruwa ya kama yana gyara mata zaman shi, baibi takan Anty da take kallon shi ba, rashin kunya
ce Abdulkadir ya saba batun yanzun ba, batasan me yasa tai tunanin iyalin daya fara tarawa
zasu saka halayyar shi canzawa ba. Bata sake cewa komai ba, tasan halin rashin hakurin ta,
kaca-kaca zasuyi ita dashi a asibitin nan, dan bakinta bazai shiru ba, Abdulkadir kuma ba zaiqi
datsa mata duk maganar data fito daga bakin shi ba. Yanke hukuncin tashi ta koma wajen dakin
tayi, idan ya gama zaman shi ya fita ta dawo.
Yana jin bude kofar ta da rufewa, juya idanuwan shi yayi, yana kara matsawa kusa da
Waheedah sosai, sam bayason baqar tambaya, baiga meya shafi Antyn da matsalar gidan shi
ba, dayan hannun Waheedah ya kama yana zagayo dashi takan cikin ta hadi da riqewa.
"Wahee kinga me kika ja mana ko?"
Ya furta a hankali, yanzun yake kara samun tabbas akan ba cikin hayyacinta ta furta mishi
kalaman dazun ba. Numfashi ya sake saukewa, sosai ya ja kujerar yana kwantar da kan shi a
cikinta, kan kuncin shi haggu ya kwanta yanda zai iya kallon fuskarta, har lokacin dayan hannun
shi na cikin nata. Wani numfashin mai nauyi ya sake ja yana fitarwa hadi da lumshe idanuwan
shi. Babu tunanin komai cikin kan shi, kallon ta yake wata irin nutsuwa na saukar mishi, a hakan
bacci mai karfi ya dauke shi shima.
*
Kan ta takejin kamar an dora mata katon dutse, idanuwan ta dakyar ta iya daga su, nauyi taji
saman cikin ta, a zaton ta Fajr ne, dan haka yakanyi mata, komin baccin da takeyi zata jishi
yazo ya kwanta a jikin ta, bazai taba kwanciya kan katifa ba, ko ta sauke shi daya farka yake
sake koma kan jikin ta ya kwanta. Hannu takai tana dorawa kan cikin ta inda take jin nauyin,
zata rantse dumin shi ya banbanta dana sauran
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 37