Share this page
kwanta kan kafet din. Sai yanzun takejin dama ta kira Yassar jiya ya dauki Fajr, dan ko wanka ba zata iya mishi ba, ballantana abinda zata bashi yaci. Wajen shidda na safe ko motsin kirki bata iyayi, ga wani irin zazzabi mai zafin gaske daya lullubeta. A haka AbdulKadir ya shigo ya sameta, dan shi ya dauka bacci takeyi da yaita sallama yaji shiru. "Waheedah..." Ya kira yanajin gabanshi yayi wata irin faduwa, da sauri ya karasa yana tsugunnawa ya dagota, jikinta da yaji kamar garwashin wuta yasa shi fadin "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..." Yana dorawa da "Baki da lafiya? Tun yaushe Wahee? Me yasa baki fadamun ba?" Dakyar ta iya bude idanuwanta ta kalle shi, da gaske kara mata ciwo yakeyi, daga muryarshi har tabatan da yakeyi. Tana ji ya zameta daga jikin shi yaje ya tashi Fajr daya shagwabe fuskarshi cike da bacci zaiyi kuka, ganin AbdulKadir din yasa yaron wartsakewa dukkan shi "Paapi" Ya fadi yana riko AbdulKadir din daya kamashi ya sauko dashi daga kan gadon "Fajr tashi, Omman ka zamu kai asibiti" AbdulKadir ya karasa maganar yana yin bandaki da Fajr, fuska ya wanke mishi yaga abin bazaiyi ba. Da kanshi yai ma yaron wanka ya goge mishi jiki da towel, kaya yazo ya dauko mishi yanajin dadin yanda komai yake a shirye, baisha wata wahala ba. Yana gama saka ma Fajr kaya da yake ta mishi surutun da hankalin shi baya kai, yaga Waheedah taja jiki dakyar ta mike. Muryarta na rawa tace mishi "Nikam kabarni da zuwa asibitin nan" Ko inda take AbdulKadir bai kalla ba, Fajr ya zaunar kusa da ita, ya koma ya dauko wayarshi dake cikin jaka. Yassar ya kira, sai da ta kusa yankewa tukunna ya daga batare da yace komai ba, jin hakan yasa AbdulKadir fadin "Hamma banzo da mota ba, Waheedah bata da lafiya kuma..." Da sauri Yassar din yace "Subhanallahi, ina zuwa yanzun" Ya kashe kiran daga can bangaren shi, yana saka AbdulKadir din bata rai, bayaso a kashe mishi waya a kunne, ko kadan abin na bata mishi rai, ya kuma rasa dalili. Wayar ya ajiye kan gado yana karasa ya kama hannuwan Waheedah duka biyun, batayi mishi musu ba. Kasa yai da muryarshi sosai saboda Fajr dake zaune a wajen "In tayaki kiyi wanka?" Kai ta girgiza mishi "Zan iyayi... Ka rakani bandakin kawai" Taimaka mata yayi har cikin bandakin, duk da hankalin shi bai kwanta daya barta ita kadai din ba, fitowa yayi yai tsaye bakin kofar bandakin, duk bayan wasu daqiqa saiya kira sunanta duk da yasan babu kyau tayi magana a bandakin. Badon Fajr ba shikam shiga zaiyi, karta fadi a ciki ya shiga uku. Saida yaga ta fito tukunna hankalin shi yadan kwanta, kama hannunta yayi yana janta zuwa gefen gado ta zauna. Da kan shi ya dauko mata doguwar riga da inners ya ajiye mata akan gado gefenta "Sannu, Bari in hadama Fajr Tea" Kai Waheedah ta daga mishi, ya kama hannun Fajr din suna wucewa kitchen. Flask ya fara jijjigawa yaji akwai ruwan zafi a ciki, ya samu kofi ya zuba madara da milo ya hada mishi rabi, ya saka sikari yana juyawa. Hannun yaron ya sake kamawa har falo ya zaunar dashi kan kafet yana ajiye mishi kofin shayin, Fajr na kama kofin yaga yana tiriri ya kalli AbdulKadir din "Bamai zafi Omma take bani ba" Kofin AbdulKadir ya dauka ya kurbi shayin, babu wani zafin da bazai iya sha ba "Wanne irin shayine bamai zafi ba Fajr?" Shagwabe fuska Fajr yayi "Na Omma..." Kai AbdulKadir ya jinjina yana ajiye kofin "Bata da lafiya, sai kasha nawa yau" Turo baki Fajr yayi "Baka bani biscuit ba" Runtsa idanuwa AbdulKadir din yayi, wajen matar shi yake son zuwa ya dubata, yaron yana da rikici, duk karancin shekarun shi baya hana AbdulKadir din zane shi. Kitchen ya koma ya dudduba, baiga inda Waheedah ta ajiye biscuit ba idan akwai kenan. Ya dawo yana fadin "Ni banga biscuit ba" Narai-narai Fajr yayi da idanuwa "Kasan Allah idan kaimun rigima zaneka zanyi Fajr. Ka zauna kasha Tea din ka kana jina..." Ya karasa yana juyawa ya koma wajen Waheedah, harta saka kaya, da alama tadanji kwarin jikinta da tayi wanka. Kusa da ita ya zauna yana taba wuyanta, da zazzabi har lokacin "Shine jiya baki fadamun baki da lafiya ba?" Idanuwanta ta ware mishi "Zazzabi ne kawai, zai tafi" Kai AbdulKadir ya girgiza "Banaso... Karki karamun wannan, idan baki da lafiya ki fadamun ni dai" Kai Waheedah ta jinjina mishi, ba zata iya doguwar magana ba, kirjinta yayi nauyi, mararta na ciwo har lokacin. Kiran Yassar yagani, hakan yasa bai daga ba ya mike yana ficewa daga dakin da falon gabaki daya. Fajr na ajiye kofin shayin ya bishi da gudu ko takaa babu a kafarshi, yana kara gudun shi ganin Yassar ne, cike da farin ciki yake fadin "Uncle..." Daga shi sama Yassar din yayi yana dariya "Fajr..." Ya kira yana rike shi a jikin shi sosai "Zan bika ni" Kai Yassar ya jinjina "Tare zamu tafi aikam" Tukunna ya kalli AbdulKadir da yake mishi murmushi, hade fuska Yassar yayi kamar bashi ya gama dariya ba "Ya mai jiki?" Ya tambaya, kai AbdulKadir ya jinjina "Yanzun kai ma Fajr dariya kana magana muryarka lafiya kalau..." Mukullin dake hannun shi Yassar ya mikama AbdulKadir din yana juyawa tare da Fajr din tunda yana da kaya a gidan. Kyaleshi AbdulKadir yayi ya koma cikin gida suna fitowa tare da Waheedah, da kanshi ya bude mata mota ta shiga ta zauna, ya rufe tukunna ya zagaya ta dayan bangaren, ya tayar da motar, yana ja suka fita daga gidan zuwa wani asibitin kudi na masu ciki da bashi da nisa sosai da gidan. * Har azahar suna asibitin, dan ruwa suka saka mata leda biyu. Har Hajja ya kira bata daga wayar ba. Sosai ran shi yaji bai mishi dadi ba, daman ya fada mata ne, sai a turo wani cikin yan gidan da zai tayasu aiki, Waheedah din ta huta. Amman zaiyi komai da zai iya, kuma yaga Waheedah din da sauki, duk da ance ta samu wadataccen hutu, kafin a sallamesu su tafi gida. Magunguna kala biyu ne kawai aka basu, duk zuwan da yake asibitin tare da ita, wannan ne karo na hudu magani sai dai yaga guda daya ko biyu, sam basa tila magunguna. "Nikam kamar in dinga zuwa asibitin nan in bani da lafiya, sam basa bada magunguna masu yawa" Ya fadi yana kwance takalman kafar shi, sai da Waheedah ta cire hijabinta tukunna ta kalli AbdulKadir din "Asibitin masu cikin Sadauki?" Dakuna mata fuska yayi "Me yasa sai masu cikine kawai zasu je? Basa bada magani da yawa" Kai Waheedah ta girgiza "Dan na masu cikine shisa basa bayarwa da yawa, bakowanne magani ake sha ba in ana da ciki" Kai ya jinjina mata yana fahimta, ita kuwa hannunta take murzawa inda akai mata karin ruwa tanajin yana mata ciwo. Har lokacin ba zatace ga asalin yanda takeji ba, kallon AbdulKadir din kawai takeyi duk inda yayi, kamar tana jira yace mata maganar da sukai daren jiya wasa ne, sai dai tasan akwai maganganun da badon ba'a wasa dasu ba, AbdulKadir dinne dai bazai taba mata wasa dasu ba. Idanuwanta ta lumshe taji yace "Me zaki ci?" Budesu tayi a kanshi a hankali "Taliyar Hausa nake so, zan dafa idan na tashi. Kai me zakaci?" Dan shiya kamata ta tambaya ma, daya kwaso tafiya, ko hutawa baiyi ba "Nima ina ci, a ina kika ajiye in dafa mana?" Tun kafin ya karasa take girgiza mishi kai, ita zata shaida dahuwar taliyar shi, narkewa ne kawai batayi ba, amman harshi kan shi bai iya yaci ba, daga ta tafi kitso, tayi miyarta take ce mishi taliya zata dafa, data dawo tunda babu wahala shine ya dafa, ta nadi uban ruwan da ta tabbatar bai tafasa ba ya zuba taliyar 'Kinga dana dauko daya sai inji kamar ta dahu, amman naga batai fari ba kamar yanda kike dafawa' AbdulKadir din ya fadi lokacin da ta shiga kitchen din ta samu taliyar kan wuta. Idan ya dafa taliyar hausa tabbas kunu zata koma. "Nagode. Allah ya bada ladan niyya Sadauki. Zan dafa.. Kaje ka watsa ruwa ka kwanta. Baka huta ba" Kai ya girgiza mata "Zanyi wanka, nikam banajin bacci. Ke da baki da lafiya, ya za'ayi ki iya dafa taliya...naga yanda kikeyi. Zan dafa nikam... Bari in fito wanka" Ya karasa maganar yana shigewa daki, bai jima ba ya fito, ya saka riga mai yankakken hannu da gajeran wando. Rigima ce cike da idanuwan shi, barnar taliyar da take bala'in ji da ita zai mata "Akwai sauran doya, a dafa doya kawai" Murmushi AbdulKadir yayi "Baki yarda dani ba ko? To wallahi saina dafa..." Ya fadi yana shiga kitchen din ya dauko tukunya. Mikewa Waheedah tayi tana bin bayan shi "Sadauki dan Allah nidai kabar shi, zan iya. Kaga zazzabin ma ya sauka tun dazun" Da gasken take tun kafin a cire ruwan farko da ta samu bacci zazzabin ya dauka, ciwon marar ma yai mata sauki. Kirjinta ne dai takejin kamar zai bude da wani irin ciwo. "Gara ki dauko mun taliya kije ki zauna. Kuma ba wasa nake ba" Taliyar ta dauko mishi, ta ajiye taja kujerar rubber da take ajiye a kitchen din in zata yanka wani abu tana jin qwiyar tsayuwa ta zauna. "Ruwan sai ya tafasa" Tace ma AbdulKadir din ganin duk mintina biyu saiya bude tukunya. Da taimakon ta ya dafa musu taliyar, tana da soyayyen manja da zafi baisa ya kwanta mata ba. A asibitin sukai sallah daman. Dan haka Waheedah taje ta kara watsa ruwa itama ta sake rigar jikinta da takejin tana mata warin asibiti har lokacin tukunna ta fito sukaci abinci. Yinin ranar babu inda ya fita sai masallaci, duk da tana iya kokarinta na ganin jikinsu bai hadu da juna ba, ko hannunta bataso ya rike sai taji ya kara mata ciwon da take ji a kirjinta. Abin har tsoro ya fara bata. Bai mata zancen auren ba, ita kuma tama kanta alkawarin in bai tayar mata da maganar ba, ba zatace mishi komai ba. Inya tayar mata dinma maganar data fada mishi jiya ita zata maimaita mishi, bata da wasu kalaman banda wannan. Sai da daddare ya samu ya turama Nuriyya text 'Ya kika wuni? Zan zo sai gobe in shaa Allah. Waheedah bata jin dadi. Zan kiraki goben, ki kula da kanki' Bai jira amsarta ba yasa chargy ya kwanta gefen Waheedah da duk idanuwanta data rufe bai hana shi kakume mata ba. Ta godema Allah da bai jima ba bacci ya dauke shi, amman koya ta motsa sai taji ya sake riketa kamar zai shige jikinta. Ta jima sosai saboda yanda kusancin da yayi da ita yake kara ma kirjinta ciwo, kafin barawon bacci ya saceta. ** Washegari da karfinta ta tashi, babu abinda takejin yana mata ciwo banda zuciyarta. Doya ta dafa, Anty ta aiko mata da wani yaji mai dadi, lallaba shi takeyi karya kare, tata doyar ta diba dan da mai da yaji takejin ci. AbdulKadir ta soya mishi tashi. Tana gamawa ya fito shikuma suka ci karo a bakin kofar kitchen din "Ni ban isa ba ko Waheedah? Bazan ce karkiyi abu kijini ba" Kai ta girgiza mishi "Yayi kyau, yanzun kuma karya nayi. Me nace miki dana dawo masallaci? Ko shara karkiyi... Amman ban isa ba shisa kika fito" Numfashi Waheedah ta sauke, tasan zaiyi fada daman, amman ta kasa komawa bacci, aikin da ga fito tanayi yana rage mata tunani tunda babu wuta balle ko kallo tayi, ko da wutar ma batajin yin wani kallo ita. "Kayi hakuri, ba wani aiki nayi ba, doya kawai na dafa na soya" Yanda tai maganar yasa shi jin wani iri, karasawa yayi yana kama hannunta "Dan kinga bana iya miki fada shisa kika daina jin maganata" Murmushin karfin hali tayi tana ware mishi idanuwa "Dan Allah karki karayin komai, ki huta, inkin ji sauki sai kiyi" Kai ta daga mishi. Ya sumbaci gefen fuskarta, ya dago hannunta yana shafa inda yai ja da alamar hudar zaman allurar karin ruwan da akai mata. "Sannu..." Ya furta cike da kulawar da ta ragema kusancin da yayi da ita kara mata ciwon da takeji. "Zaka karya yanzun?" Kai ya daga mata, ta dora da "Ina da zobo a fridge, ko zaka sha Tea?" Da sauri ya girgiza mata kai "Yaushe kikayi zobo?" Hannunta ta zame daga cikin nashi tana bude fridge din ta dauko roba daya "Tun shekaranjiya, da yawa nayi, Fajr duk yamun barnar shi" Tare suka fita da kayyakin, AbdulKadir a kular ma yaci tashi doyar. Itama tayi mamakin wadda taci dan lokacin da suka zauna ko yunwar bataji. AbdulKadir din ya kwashe kayan tana zaune. Tanajin shi yana ta kwaramniya da kwanoni. Sai daya fito taga hannuwan shi duk ruwa "Me kayi?" Ta tambaya "Wanke-wanke... Har gogewa nayi" Murmushi tayi mishi da yake ganin kamar bai kai idanuwanta ba. "Sannu da aiki..." Amsawa yayi da "Yawwa" Yana dan nazarin yanayinta kafin ya wuce dakin. Wayar shi ya dauka ya kira Yassar, yau dinma sai da yayi tunanin ba zai dauka ba tukunna ya daga. "Ina jin ka" Numfashi AbdulKadir ya sauke "Gaba babu kyau Hamma...Kuma yanzun mun girma mu ba yara bane, bai kamata muna irin wannan..." Bai karasa ba saboda Yassar din ya kashe mishi waya a kunne, lumshe idanuwa AbdulKadir yayi yana budesu hadi da furzar da wani numfashi ran shi a bace, wayar Yassar din ya sake kira, wannan karin yana dagawa yace "Wai meye?" Numfashin AbdulKadir ya sake fitarwa, zai dauki girman yau, girman da Yassar din ya kasa dauka "Motar ka daman, in ba zaka bukata ba, zanyi abu da ita" Dan shiru Yassar yayi "Me yasa baka zo da taka ba? Wanne abu zakayi?" A ranshi AbdulKadir yayi niyya tun jiya, daya koma akwai abokan aikin shi da zasu taho Kano su biyu satin sama, zai basu motar su taho mishi da ita, yabarta a gida tunda sai yazo yake gane yafi bukatarta anan din fiye da can Lagos. Tunda inba wani dalili ba sunfi fita da motar aiki. "Da gaske kana son sanin abinda zanyi da ita?" Murya a dakile Yassar yace "Inka gama ka dawomun da motata gaskiya" Yana kashe wayar. A karo na biyu a rana daya daya kashema AbdulKadir din waya a kunne, inda wani ne a gidan ba Yassar ba, kome zaiyi da motar ya hakura, amman shi kan shi Yassar din yasan ba zaiyi zuciya ba. Shi kadai AbdulKadir yake tambaya abu, ya zageshi, kuma ya bashi abin ya karba. Shakuwar dake tsakanin su ta daban ce, Yasir ne suka kwanta a ciki daya a lokaci daya, amman zai iya rantsewa babu shaquwa mai karfi irin wannan a tsakanin su. Dan zai iya kwana biyu ma basu gaisa da Yasir din ba, musamman yanzun da shi yana Katsina, tunda aiki ya mayar dashi can ya samu yar Katsina ya aura. Falo AbdulKadir ya dawo yana samun Waheedah a zaune inda yabarta. Zama yayi ya zame jikin shi ya kwanta yana dora kan shi a cinyarta. Jin yana gyara kwanciya yasa ta fadin "Karka danne mun hancin yaro Sadauki" Dariya AbdulKadir yayi "Yarinya dai" Shiru tayi ta kyale shi, cikin Fajr ma haka sukai ta wannan gardamar, sai ta haifi namiji. Kuma shi yace bayason sani a asibiti, wannan dinma yace mata ko an tambayesu zasuce basa son sani, sai ta haihu tukunna. "Ina so in fita, amman banaso in barki ke kadai" Hannunta ta dora kan fuskar shi, tana jin maganar shi can nesa, da wani yanayi a fuskar ta tace "Ka fita abinka, naji sauki ai. Ka tahomun da kwakwa inka ganta" Kai AbdulKadir ya jinjina mata "Bacci zanyi yanzun. Sai azahar tukunna, kwakwa kawai?" Ya karasa maganar yana juya kwanciyar shi, ta daga mishi kai. Baice komai ba ya lumshe idanuwan shi. Kanta Waheedah ta jingina jikin kujerar dake bayanta. Tunani take, amman ba zatace ga ko na menene ba, kawai tasan ta lula tsakiyar wata duniya da bata ganin falonta balle tayi tunanin karshenta. * Jikin shi ya mishi nauyi saboda baccin da yayi, dan sai da Waheedah ta tashe shi da aka kira sallah. Hamma kawai yake a mota, harya karasa kofar gidansu Nuriyya yayi parking, gida yake son shiga, amman bayaso su bata mishi rai, kan shi a cunkushe yake jin shi, bayason hada abubuwa da yawa waje daya, tunanin zai iya damun shi. A cikin motar yai zaman shi yana kiran wayar Nuriyya ya fada mata yana kofar gidan. A cikin motar ta same shi, tana zama da wani irin bugun zuciya naban mamaki. Turarenta daya cika motar na mishi daban "Ina wuni" Ta gaishe dashi cike da kunyar da batasan tana da ita ba. "Lafiya kalau. Ya kike?" Kanta a kasa tana wasa da yatsunta da suka sha kunshin jan lallen da rashin aikinyi yasa ta daura shi shekaranjiya. Ta mishi maganar tarewa ne saboda zaman gidan ya isheta, kwata-kwata Mama bata hira da ita, gaisuwa ce kawai take hadasu, ko dariya take inta hangota zata daina, Baba ma inta gaishe shi dakyar yake amsawa. Gashi babu damar ta fita daga gidan ballantana ta sha iska. Yanzun ma maganar take sakeyi mishi, amman kunya ta hanata. "Alhamdulillah" Ta amsa, AbdulKadir din na tsintar kanshi da kamo hannunta yana wasa da yatsunta da suka sha kunshin da yai mishi kyau sosai. Sai yake ganin hannun ya mishi daban, ko a mafarki bai hango rike hannun wata macen da zata kira kanta da matar shi banda Waheedah ba. Komai bako yakejin ya dawo mishi, duk da hannun Nuriyya din a cikin nashi yasa wani abu tsirga mishi cikin kai yana yamutsa mishi tunani. "Kin shirya ne?" Da sauri ta dago kanta tana sauke idanuwanta cikin nashi tana kasa yarda da cewar shi din mijinta ne. "Eh na shirya, amman ban fadama su Mama ba tukunna" Kai AbdulKadir ya jinjina mata "Ki fada musu to, saiki kirani inji yaushe... Gobe in shaa Allah zan wuce" Shagwabe fuska Nuriyya tayi "Gobe? Da wuri haka Masoyi? Jiya banganka ba" Kallonta yake, sunan da take kiran nashi dashi na mishi banbarakwai a lokaci daya kuma yana saka mishi wani irin nishadi. Murmushi yayi da yasa gwiwoyin Nuriyya yin sanyi. Tasha ganin murmushin a fuskar shi, amman yaune karo na farko da yayi shi domin ita, wani shauqin kaunar shi taji yana fisgarta. "In dauko wasu kayan ka tafar mun dasu?" Nuriyya ta bukata da sauri tana dora dayan hannun nata saman nashi, tanajin dadin yanda take da damar yin hakan yanzun. Kai AbdulKadir ya daga mata, ya fada mata inda zata zauna akwai komai, kitchen ne kawai ba kaya. Ta siyi kayan kitchen sosai, kusan abinda tayi da kudin da ya bata kenan, daman akwai sauran kudin kayan dakinta wancen da ta siyar bayan ta fito daga gidan Anas. Da su da sadakinta ta hada ta siyi fridge. Yana gidan Asma'u kawarta, dan duk kayyakin ma ita ta dinga turama kudin tunda sana'arta kenan, siyar da kayan kitchen din. Ta kuma kawo mata komai da ta siya, fridge dinne da babu inda zata ajiye. Hannun AbdulKadir ta saki tana fita daga motar cike da zumudin kayanta zasu isa gidan AbdulKadir din, itama kuma zata bi bayansu babu jimawa. Ganin ta fara fitowa da kaya yasa AbdulKadir fitowa daga motar ta bude mata boot, yana taimaka mata ta zuba wanda zasu shiga, wasu kuma a bayan motar. Tukunna sukai sallama, yana wucewa gida. Da niyyar inta kirashi ba ranar zata tare ba, saiya tura mata kudin abinci, daman wancen watan bayan tafiyar shi saida ya tura mata kudin abinci tunda tana karkashin kulawar shi, yasan hakan hakkinta ne. A hanya yai la'asar tukunna ya wuce gida. A mota yabar kayan. Yana fara shiga gidan da sallama, a falo ya samu Waheedah, ta mishi wani irin kyau cikin jan lace din daya karbi fatarta, ga jambakin da yake so manne da labbanta tana saka komai kwance mishi. "Wahee" Ya tsinci kan shi da fadi maimakon amsa sannu da zuwan da tai mishi. Karasawa yayi ya zauna gefenta kan kujerar yana fuskantarta. "Ya jikin ki" Idanuwa ta ware mishi "Naji sauki" Numfashi AbdulKadir ya shaqa yanajin komai ya mishi dai-dai. "Sannu" Murmushi tayi mishi da yasa yakai hannu yana taba labbanta, yanda baya dangwalo janbakin ta yana bashi mamaki, muryarshi can kasan makoshi yace "Idan babu matsala zata zauna a gidan nan, bangarena tunda bana amfani dashi" AbdulKadir yai maganar yana sa tanajin kamar tana da zabin da bataga dalilin da zaisa ya bata shi ba, batako hango auren shi ba, gashi dashi yanzun, kamar yanda yake da iko da kan shi, haka yake da iko da gidan shi. "Banda matsalar komai" Ta fadi tanajin ta sama-sama, kamar gangar jikinta ce a zaune tare dashi. Ruhinta na tsaye a gefe yana kallon abubuwan da suke faruwa kamar bai shafe shi ba. Gyara zama AbdulKadir yayi yana kwantar da kanshi a kafadarta, ita din alkhairi ce a rayuwar shi fiye da yanda zata taba sani. Tasa yanajin saukin abinda ko a labarin da yakeji mai matuqar wahala ne. "Nagode. Nagode da yanda kikasa komai yazo mun da sauki" Batace komai ba, dan batasan me ya kamata tace ba, yakai mintina goma a zaune yayi luf a jikinta, kafin ya tashi. "Sai ina?" Ta tambaya "Akwai kayanta a mota, zan shigo dasu" Mikewa Waheedah tayi "Baka fadamun yau zata zo ba, ba'a kara share wajen ba" Dan daquna fuska AbdulKadir yayi "Bansani ba nima, kayan ne dai kawai. Ba zakiyi shara baki da lafiya ba" Kai ta girgiza mishi "Amman a haka za'a saka mata kaya babu shara?" Idanuwa AbdulKadir ya kankance mata, a halin da take ciki ba zata iya karawa da fadan shi ba. Shisa tayi shiru, wajen ta bishi har bakin mota, duk da ya hanata daukar komai. Tsaye tayi tana kallon shi yana kwasar kayan yana kaiwa, jinta take kamar a mafarkin da zata iya farkawa ko da yaushe. Harya gama kwashe kayan tas. Tukunna ya kama hannunta suka koma cikin gida. Harya zauna ya tuna da kwakwar daya siyo mata tana mota, ya sake fita ya dawo da ita a leda. Guda biyar duk sun bare mishi. Mika mata yayi "Na dauka ka manta" Kai ya girgiza mata, ya zauna, ita tana mikewa ta nufi kitchen. Guda daya ta wanke, ta saka sauran a fridge, wuka tasa ta huda ta tsiyaye ruwan tana shanyewa ta yanka kwakwar da tasan cikine kawai ya saka mata sha'awarta, dan sai dai in zatayi kunun aya tadan balla, amman ba damunta tayi ba, a cup ta zuba ta dauka tana komawa falo, wuta tagani "Yaushe suka kawo?" Ta tambayi AbdulKadir "Yanzun fa, kina tashi" Zama tayi, komai a kunne yake, remote din na hannun AbdulKadir yana yawon shiga tashoshi dashi. "Wahee baki bani kwakwar ba...yau ba kina cin abu baki bani ba" Murmushi tayi mai sauti, duk da batajin wani nishadi "Yi hakuri... Wallahi na manta ne" Langabar da kai yayi, bata saba mishi ba, kome takeci tana bashi, bai saba tambayar ta ba. Mika mishi kofin tayi, yasa hannu ya dauka. Kallo suke suna hira jefi jefi har aka kira magriba. Ita tayi daki, shikuma ya fita masallaci. Ya dawo ne ya samu text din Nuriyya 'Masoyi duk sanda ka tashi kazo mu tafi, na fada musu, na gama hada sauran kayan kuma' Wayar ya mayar aljihun shi. Yana cewa Waheedah "Yau zata zo" Idanuwanta ta ware akan fuskarshi, kafin ta daga mishi kai a hankali, cike da wani yanayi a idanuwanta da yasaka shi karasawa inda take ya zauna, ya kama hannunta yana rikewa "Wahee kimun magana dan Allah... Ki daina kallona haka... Kimun magana zaifi" Murmushin karfin hali tayi "Abinne yake mun bakunta, shine kawai" Numfashi ya sauke yana yawata idanuwan shi kan fuskarta, duk da bata saba mishi karya ba, haka kawai zuciyarshi ta kasa nutsuwa waje daya. Baice mata komai ba ya sumbaci hannunta yana mikewa. "Saina dawo" Kai Waheedah tadan daga mishi "Allah ya tsare hanya" Tana sake kwanciya cikin kujerar. AbdulKadir kuma ya fice daga gidan. Yana motane yake tunanin haka yaso bikin shi da Waheedah, yaje ya dauko matar shi su tafi, babu wannan al'adar na cewa sai an rakota, ya dauka duk sai anyi su Walima da kamu kamar auren shi da Waheedah. Anty Talatu ce take fada mishi, ko da za'ayi wani abin sai dai ko ita Nuriyya in zatai walima, kuma batace mishi zatayi din ba. Hakan yafi mishi, badan zai hanata in tasoyi ba, amman yana ganin daurin aurene kawai ya zama dole, kuma yake da muhimmanci, shi bayason duk wani abubuwa da bai zame mishi dole ba. Sai dai abinda ya dinga mishi yawo bayan yaje ya dauko Nuriyyan a hanyarsu ta zuwa gida shine yanda Babanta bai bukaci yagan shi ba, ko ita Mama din ma, a tunanin ko za'ayi musu wata nasiha kamar yanda aka saka shi a gaba lokacin auren Waheedah. Sai yaga ta bude mota ta shiga batare da tace mishi iyayenta nason ganin shi ba. Wata zuciyarta sai take darsa mishi ko haka aure na biyu yake, tunda ana ganin babu wata kuruciya a tattare dasu biyun, kuma duk an rigada an fada musu abinda ya kamata a aurensu na farko. * A hanya ya tsaya dasu yai siyayyar abinda yake tunanin zasu bukata, saboda Nuriyya din, dan yasan Waheedah ba komai ta keci ba yanzun. Ya dai siya mata apple ko zataci, tunda yasan tana so sosai. Tukunna suka karasa gidan. Sai da Nuriyya ta ganta a cikin harabar gidan tukunna taji wata irin faduwar gaba da bata taba tunani ba. Da bata damu ba data fadama su Baba cewar AbdulKadir din yace zaizo su tafi. Su duka Allah ya kiyaye sukai mata batare da sun kara wasu kalaman a kai ba. Ita tana cikin nishadin da fushin da suke da itane karshen abinda yake ranta. Amman yanzun tunanin fuskantar Waheedah ya dawo mata da komai sabo, wani irin tsoro takeji har kafafuwanta na mata rawa. Da AbdulKadir ya zagayo ya bude mata motar sai da ya mika mata hannun shi tukunna ta kama ta fito daga motar, ya mayar ya rufe, yana sakin hannunta ya bude bayan motar ya dauko dayan akwatinta yana soma jan shi zuwa cikin gidan. Da wani irin sanyin jiki na mamaki take bin

Chapter 25 of 37