Share this page
jin komai ya birkice mishi, fada yaso yayi sosai, amman kananun maganganu ba halayyar shi bace ba, bai kuma saba komai sai yayi magana a kai ba, sun sami matsala da yawa yau Da Nuriyyar bayaso su kara samun wata cikin daren nan. Dan yasan halin sune, kome zai faru iya sune, babu shaidan din da zasu labe a bayan shi tunda watan azumi ne. Bai shirya sanin yana da halaye marassa kyau ba, gara tasan yanda zatayi ta koya, ya dai cika da mamaki, ya dauka koyayane mata sun iya girki tunda abune da sukeyi yau da kullum. Da mai yaci kuwa yana mayarwa da ruwa ya mike, yanajin yanda idanuwan shi sukai zuru-zuru duk da bai kallo mudubi ba. Bacci suka dan koma kafin asuba. Sanda ya dawo masallaci Nuriyya harta sake komawa bacci. Shikam zama yayi yana yin azkar har rana ta fito ya mayar da sallah raka'a biyu ta nafila. Sai daya wuce dakin Waheedah yana samunta tana linke dardumar ta da alama itama sai lokacin ta tashi. Dan ita ta saba mishi da yin nafilar bayan asuba, ko kadan bata wuce ta, ta tunasar dashi tarin ladan da yake cikin hakan. Yanzun harta zame mishi jiki, cikin sanyin muryarta ta gaishe dashi, ya amsa "Kun tashi lafiya?" Sai da ta fara jinjina mishi kai tukunna ta amsa tana dorawa da "In kaje gida yau ka taho da Fajr" Kallonta AbdulKadir yayi, sosai take kewar yaron nata "Ni nace miki zanje gida ne? Ki kirasu a kawo miki shi" Kai ta girgiza mishi "Ni kunya nakeji ai" Dan murmushi yayi "Lallai yarinyar nan, nine sarkin rashin kunya ko?" Dariya Waheedah ta tsinci kanta dayi tana girgiza mishi kai "Haka kike nufi mana, ba zanje ba to, in kina kewar shine ki kirasu da kanki" Ya karasa maganar yana juyawa dan bacci zaije yayi daman zai duba ya suka tashine. "Dan Allah ka dauko mun yarona" Juyawa AbdulKadir din yayi yana harararta ya fice daga dakin yaja mata kofa, dariya take sosai, har ranshi tasan harara ce yake ganin yanayi, amman idanuwan shi basuda girman da zasu juyu har suyi hararar, bata taba gaya mishi bayayi dai-dai ba. Sai dai tasha dariyarta kawai. Ikram ta dauka tana cire mata kaya, dan wanka zatayi mata, itama tayi, sai suzo suyi baccin. * Bacci yayi har wajen sha biyu sannan ya tashi, ya watsa ruwa ya fito yana zaune bakin gado, Nuriyya na kai tana danne-danne waya, dan group dinsu an turo wasu laces masu bala'in kyau. Kuma duk wanda yake cikin group din yace yana son guda daya, ita kadai ce batace a ajiye mata ba, dan taji Hajiya Kaltume mai siyar da kayan tace kudi hannu ne, ba zata bayar da bashi ba wannan karin, da sai ta dauka sai karshen wata. Gashi kowa sai magana yakeyi ita ba zata siya ba, tana ta kallon sune batasan me zatace ba, kar a rainata. "Masoyi" Ta kira cikin sanyin murya, tana saka AbdulKadir din kallonta "Kaga wani lace" Ta fadi tana nuna mishi wayar, kallo yayi yana jinjina mata kai "Yayi kyau" Ya amsa a taqaice yana daukar tashi wayar da take ajiye a gefe. Murmushi Nuriyya tayi dan taga alamar zatayi nasara "Dubu arba'in da biyu" Kai kawai AbdulKadir ya jinjina mata baice komai ba yaci gaba da danna wayar shi, da sauri tace "In dauka zaka biya kudin?" Dago idanuwan shi AbdulKadir yayi yana kallonta kamar bata da hankali "Wai me kika daukeni ne Nuriyya? A bishiya nake tsinko kudi kome? Kin manta kudina da kika kashemun, kin sani saida na taba wasu dana ajiye dan wani abin, har kina mun maganar in sai miki abin dubu arba'in da biyu. Ina nagan su?" Kallon shi take dan in jikinta zai zama kunnuwa ba zata taba yarda bashida su ba, da cayai mata ma bazai bayar ba sai yafi mata saukin yarda. Wayar shi AbdulKadir yaci gaba da dannawa yana nemo text din albashin shi ya ajiye wayar kan gadon yana turama Nuriyya data dauka "Bansan kallon me kike mun ba, amman ni ba wasu kudi gareni ba, kinga albashina nan duk watan duniya, a ciki nake duk hidimata, katon gidan nan kudin allowance ne na wasu ayyuka, haka motata, bawai albashina bane, sukuma sai ayi shekaru ba'a same su ba. Idan ban taba fada miki ba yau kisani, ni bamai kudi bane, cikin layin masu rufin asiri ma a tsakiya za'a sakani" AbdulKadir ya karasa yana mikewa ya fisge wayar shi daga hannun Nuriyya yana ficewa daga dakin yabarta a zaune gabaki daya jikinta ya gama mutuwa. Tabbas yau kallon kitse ake ma rogo ne ya tabbata a kanta, wannan albashin na AbdulKadir sam-sam bashi bane burinta ma hamshaqin mijin da take son aure "Tafdin..." Ta fada ranta a jagule, kwata-kwata yanda ta hango AbdulKadir ba haka yake ba. Daga halayen shi har kudin shi, ita da bata hango ckarta shekara daya a gidan batare da tayi motar kanta ba. Da wannan yagalgalallen albashin yaushe harya tara kudin da zai siya mata mota. Wani kunci takeji yana taso mata tun daga yatsan kafarta yana mata zaune a kirjinta. Harma fada mata yake shi ba kudi yake dasu ba dan karta sa ran zai mata wani abin arziqi. Har ranta take jin babu wanda ya cuceta sai Waheedah, babu babbar makira irinta, ita ta dinga nuna mata kamar tana cikin daular rayuwa, ita kuma ta dinga mata hidima kamar AbdulKadir din wani hamshaqin mai kudine, ita taja mata duk wannan abin da take ciki, dan ita ta haska mata AbdulKadir din taga kyallin shi harta kwadaitu da auren shi, amman da duk mintina take ganin abinda bataso a tattare dashi. Gani tayi bakin ciki zai mata katutu, ga whatsapp din data bude harta private Hajiya Kaltume ta mata maganar siyan lace din nan, hankalinta ya kara tashi, hakan yasa ta janyo system dinta, drawer din gefen gado ta janyo ko ta saka earpiece dinta a ciki, taga wata leda da batasan ta ajiye ba, dagota tayi taga kudine a ciki, sai da zuciyarta tai wata irin dokawa, warware ledar tayi tana zazzago kudin kan gadon, ganin su tayi da yawa sosai, da sauri ta tashi ta saka mukulli ta kulle kofar ta dawo, kudine masu yawan gaske dan ba'a dauresu ba, hakan ya sata tunanin da alama ana zararsu ne. Tasan AbdulKadir din kan ciro kudi ya ajiye ana diba, dan tasha zara kuma bai taba ganewa ba tunda bai mata maganar ba. Duk da zuciyarta na dokawa, wani abu kasan ranta na fada mata kar tayi, dubu arba'in da biyu ta kirga ta ware su a gefe, ko kwatar kudin bataga alama sun girgiza ba, tasan ba kirgawa zaiyi ba, da sauri ta gyaggyara su ta mayar cikin ledar tana nannadewa kamar yanda tagani ta mayar ta rufe drawer din. Wanda ta diba din ta mike ta samu jaka ta zuba su a ciki. Kafin ta zauna taji ana kwankwasawa, da yake ta saba dibar kudin Anas ko dar bataji ba, taje ta bude mishi kofa, baice mata komai ba ya rabata ya wuce. 'Namiji munafuki' Ta fadina ranta, daman akance namiji bazai taba nuna maka samun shi ba, yau ta kara yarda, yanzun ya nuna mata wani alert kamar mai gaskiya, jibi kudin da ta gano. Daman tanata tararrabi anya ace bashida kudin da take tunani. Tana kallo ya bude drawer din ya dauki ledar ya sake zuwa ya fice, dakin ta tura. Ta koma kan gado tana daukar wayarta taba Hajiya Kaltume amsa 'Ni banda kudi a banki, Cash ne bansan ya za'ayi ba, gashi yau bazan fita ba, ni nake da girki' Ba'ayi mintina biyu ba Hajiya Kaltume ta amsa ta 'Kibani address din zan turo yaro yazo ya karba' Tura mata tayi kuwa tana komawa kan gado ta zauna. Ko da kirgawa AbdulKadir yayi yagane an diba sai ta bashi hakuri, fadane zaiyi saita toshe kunnuwanta ta kyale shi, in aka kawo lace din ta daura a jikinta zai wanke mata haushin shi da zataji na dan wani lokaci. Ko mintina sha biyar ba aiba, taga kira yaron harya iso kofar gida. Kudin ta dauka ta saka hijabi ta leqa ta kai mishi, saida ya kirga a gabanta tukunna ta dawo gida, tana jin wani abu yadan kwanta cikin bacin ran data shiga. * "Hamma kasan fa bani da lafiya, gashi ana rana, ina azumi ka fito dani" AbdulKadir ya fadi yana mika mishi ledar kudin da sun kai kwana goma a ajiye a wajen shi, dan Yassar din yayi cinikin mota zai sake wata, tashi nata bashi matsala, daya ciro kudin sai cinikin bai yiwuwa ba, yana jin qwiyar komawa bank ya kuma san halin shi, ko Hauwa yaba ta ajiye saiya bi ya karba ya kashe. Amman idan AbdulKadir dinne ba zai bashi ba sai dai ko in lalura. Yanzun ma dan yace ga motar an kawone an gama komai, kudinne kawai zai basu, tashi motar ma har wanda ya siya ya dauka tukunna AbdulKadir din ya fito da kudin. Ya daukama dakin Waheedah ya ajiye, dan yaje yana nema, ta taya shi basu gani ba, kafin ya tuna dakin Nuriyya ya ajiye. "Kai kamar ba soja ba" Kankance mishi idanuwa AbdulKadir yayi "Ina gida yanzun, kabarni. Kuma ma dan ina soja sai akace duk wahala in dinga jureta" Kai kawai Yassar ya girgiza mishi yana karbar kudin ya basu. Suna tsaye aka kirga "Dubu dari hudu ne babu arba'in da biyu" Da mamaki Yassar yace "Bangane ba" Dan yasan kudin shiya ciro su da kan shi "Eh babu dubu arba'in da biyu" AbdulKadir ya kalla yana fadin "Ka taba kudin nan ne AbdulKadir?" Kai AbdulKadir ya girgiza dan baima ji me suke fada ba, hankalin shi nakan wayar shi da yake duba sako "Me ya faru?" Ya bukata yana mayar da hankalin shi kan Yassar din "Wai basu cika ba, babu dubu arba'in da biyu" Dagowa AbdulKadir yayi daga jikin motar shi "A kara kirgawa dai" Ya fadi saboda bayason abinda ya fara zuwa kan shi ya tabbata, sam bayaso, mutumin kuwa bai musu gardama ba, wannan karin duk a tare suka kirga kudin, babu dubu arba'in da biyun. Wallet din shi AbdulKadir ya zaro yana dauko ATM din shi ya mikama Yassar "Kasan password din" Wani irin kallo Yassar ya watsa mishi kafin yace "Bana son iskancin banza da wofi" Kai kawai AbdulKadir ya jinjina yana mayar da ATM din inda ya dauko shi, batare da yace komai ba ya bude murfin motar shi, ran shi ya dade bai baci ba irin haka. "AbdulKadir me ya faru? Ka fito daga motar nan muyi magana" Yassar ya fadi ganin yanayin fuskar AbdulKadir din, amman mukullin motar shi ya murza yana tayar da ita, duk maganar da Yassar din yake mishi baiji ba ya fisgi motar yana hawa titi...! #TeamAbdulKadir #TeamWaheedah #LubnaSufyan [7/16, 9:56 PM] +234 802 111 7692: Facebook: Lubna Sufyan IG: SufyanLubna Email: Calmlubna@gmail.com Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43 YouTube: https://youtu.be/WwocHslDAYk *ABDDULKADIR* *LubnaSufyan* 33 To my fav Aunt (Rabi'atu). Allah ya shiga lammuran ki. Amin thumma amin Tunda ta gama baccin safenta ta gyara bangaren ta tsaf, sannan tayi wanka ta shiga kitchen. Dan wanke-wanken da take dashi tayi. Ikram na kwance cikin kekenta tana bacci. Fridge din ta duba taga tana da naman rago, kawai sai marmarin tuwon semo da miyar dan yar kubewa ya kamata. Fito dashi tayi dan ya huce, yayi kankara, ta dauki Ikram suka fito ta kulle kitchen dinta. Daki ta koma ta kira Naziru a waya tace yaje ya siyo mata danyar kubewa ya kawo mata in yazo sai ta bashi kudin. Hakan kuwa akayi, dadewar da yayi har bayan azahar yasa ta dauka ma ya manta dan tasan shiriritar shi. Kitchen din ta koma ta samu kwando ta juye kubewar a ciki, tana da yawa, inta ajiyeta ma kafin ta sakeyin wani tuwon zata iya yin yaushi, gara tayi miyar ta saka a fridge. Tasan zata waiwayeta. Ajiyewa tayi ta wuce daki ta dauko wayarta ta dawo, Tafsir din Sheikh Albani ta kunna kan yanda zaka kara gyara ibadunka. Ta rage karar dai-dai kunnenta tunda ba earpiece ta saka ba, duk da ita kadai ce ta riga ta saba. In akwai abinda yake saurin sosa mata rai bai wuce tana zaune waje wani ya kunna waka ko wani abin ya kure sauti ba. Sam mutane basa tunanin ko wanda yake kusa dasu baya jin dadin su abinda suke saurara din, ko baya cikin yanayin son saurarar komai. Wasu suna ganin ai karatun Qur'ani ne, musamman lokacin azumi, kuma zaka iya shiga hakkin wani, shisa aka saukaka da akai earpiece, ka saka kaji duk abinda kake so dai-dai kunnuwanka batare daka takura kowa ba. Kubewarta ta wanke tana dauko abin gogawa ta dauraye shima ta ajiye su gefe dan taga naman ya saki, gara ta dora shi ta dafa, har cefane ta dauko, lokacin ba wahala gare shi ba, gashi tana son dafa zobo. Aikinta take a nutse taga giccin AbdulKadir da wani irin sauri da ya sakata leqawa, yanayin tafiyar shi ya tabbatar mata da ranshi a bace yake sosai. "Allah ya rufa asiri" Ta furta a hankali tana komawa taci gaba da aikinta. AbdulKadir kuwa duk azumin da yake bai hana shi zira kai ta murfin mota yana ma mutane masifa a hanyar shi ta zuwa gida ba, dan gani yake sun tare mishi hanya, sun hana shi isowa da wuri, wayar shi ma da Yassar ya ishe shi da kira kasheta yayi. Ba zai tuna ranar karshe da yaji kunyar Yassar irin yanda yaji ba yau. Tunda can ma akan Yassar ne fara sanin yana iya jin nauyin wani dan adam haka, kan shi tsaye zai iya fadama Hajja abu, har Abba ma, koya tambaye su abu, amman Yassar saiya jima yana juya maganar kafin ya samu ya fito da ita. Lokutta da dama yanajin kamar shine ya kamata ya fito ciki daya da Yassar, su kwanta a mahaifa daya saboda kusancin da yake tsakanin su. Sai dai haka Allah Ya kan tsara lamurra, wani lokacin ma sai kaga shakuwa a tsakanin mutanen da basu hada jini ba, Yassar na daya daga cikin abinda yake godema Allah da samu a duk sallar shi ta duniya tunda ya mallaki hankalin shi. Ta ina Nuriyya take so ya fara hada idanuwa da Yassar din? Me take so yace mishi bayan yau? Ta mishi abubuwa da yawa, kanana da manya da ya dauki idanuwa ya saka mata, abubuwan da duk ya tsarama kan shi ba zai dauke su a wajen macen da yake aure ba. Sai dai ita din ba Waheedah bace ba, yanajin ranar da duk zai waiwayi abinda tayi mishi da wahala alaqarsu ba zata samu tangarda ba, shisa yake kauda kai yana kyaleta. Yau ne ta kai shi saman kanta ga ba jikin bango bama, da shi ta taba, da kudin shine, watakila ba zai ji abinda yakeji ba yanzun, da kudin ma na wani ne daban da yasan in ya mayar mishi zai karba duk abin zai zo da sauki. Kudin na Yassar ne, kuma ko jiya sai da yai mishi mitar bashi da kudi, yai ma Hawwa gyaran mota, yana so ya kara tara wasu kudin itama ya sake mata wata, zai iyayin abubuwa da dubu arba'in da biyun shi, ko kayan abinci zai siya ya ajiye, ko yayi hidimar sallah da take gaban shi cikin kwanaki kasa da talatin. AbdulKadir na da tabbacin bashi kadai bane yake tsara komai na rayuwar shi. Ciki harda yanda kashe kudin shi yake tafiya. Bakin kofar dakin Nuriyyar ya tsaya yana rike da handle din kofar, idanuwan shi ya lumshe ko zai tuna wani dalili da yasa zuciyar shi doka mata tun daga farko amman ya rasa, ba halayenta bane, saboda baisan su ba lokacin da ya fara son ta, bai san su ba lokacin da zuciyar shi ta sake doka mata bayan ya rufe shafinta daga rayuwar shi. Baisan ko kadan cikin halayyarta ba lokacin da ya amince ma aurenta, halayenta sun fito mishi ne bayan ya aureta, a kasa da sati daya bayan ya aureta ya fara kula dasu, sun sake fito mishi bayan ta tare a cikin gidan shi, zama ya hada su, tana saka shi fahimtar dalilin da yasa mutane ke cewa zaka iya shafe shekaru da mutum ba kasan ko da kashi ashirin cikin halayen shi ba, saboda akwai boyayyayun halayen da ba mutum bane yake boye su dan kar a sani, basa fitowa ne sai zama na a kwana a tashi karkashin inuwa daya ya kama suke bayyana. Auren Nuriyya yasa ka shi fahimtar abubuwa da dama duk da ba zama yakan yi yai tunani akan hakan ba. Akwai kuma dalilin da yasa akan auren Nuriyyar bayan ta tare Hajja ta kira shi a waya tana ce mishi 'Soyayya ce take dibarka yanzun AbdulKadir, kuma ita kadai bata isa ta rike aure ba, akwai lokacin da zaku tashi ku duka ku nemi digon soyayyar nan ku rasa, wallahi idan har baku gina zaman ku akan abinda ya girmi soyayya ba, in kuka shiga cikin irin yanayin nan zai muku wahala ku samu dai-dai to. Ba zance maka kacokan zaman aure kan ginu akan halaye bane kawai, amman su din kan zama ginshiqi mai girma na zaman aure. Ga ka ga Nuriyyar nan, itama ga ta ga ka nan, ba baki zan maka ba, amman akwai halayenka da nake da yaqinin Waheedah ce kadai macen da zata iya jurewa' Bayason ya tsaya tunanin hakanne a baya, dan zai saka tunanin cewa sai da kowa da yake son shi yai mishi magana akan auren Nuriyya din yai biris da su, ko Yasir da ba shiga harkar juna suke ba sai dole sai da yace mishi 'Da yawan lokutta mukan so abinda ba alkhairin mu bane ba, zaka iya son abu ka rayu babu shi, zaka iya kin abu ka rayu dashi AbdulKadir. Dan kana son yarinyar nan baya nufin in baka aureta ba wani abu zai sameka, da yawan lokutta mukan yi hakuri da abinda muke so dan zaman lafiyar mu' Shima yai watsi da shi, kashe wayar shi ma yayi. Shisa duk wani karamin abu da Nuriyyar zatai mishi baya daga kai, yasan tunanin maganganun da kowa ya fada mishi kan aurenta ne zai danne shi. Ya kuma tsani kalaman dake biyo bayan dana sani na 'Sai a wane ko wance suka fadamun ban ji ba' wani lokuttan kuma sai kaji ana 'Daman ance mun kaza da kaza'. Duk bayason wannan tunda ba zasu canza abinda ya riga da ya faru ba, shisa yau yake tsaye bakin kofar yana so ya tuna koma menene da zai saka shi yadan sauka daga dokin zuciyar da yake kai, ko da kuwa sharrin shaidan ne, amman azumi akeyi, babu wani shaidan a cikin abinda yake ji sai Nuriyya. Numfashi yaja yana fitar dashi da wani irin bacin rai ya tura kofar, a tsaye ya sameta tana linke hijab. Kan lace din da tayi saurin jefa hijab din sama idanuwan shi ya fara sauka kafin yaji kamar ta watsama wutar da take ci a zuciyar shi galan din fetir.. "Me yasa?" Ya tambaya muryar shi can kasan makoshi yana kafeta da idanuwa "Me yasa me?" Nuriyya ta tambaya tana son yin kamar bata fahimci abinda yake nufi din ba, duk da yanayin shigowar shi yasa ta gane yasan ta dibi kudin, ita tabarmar kunya da hauka akan nadeya. Tana bacci ma wayarta ta fara ihu, ta dauka taga Hajiya Kaltume ce tana fada mata yanzun za'a kawo lace din ma, dan ya iso, ta dauka sai dare. Ta karbo kenan ta shigo ta tsaya waya da Asma, ta manta shaf bata kulle kofar ta dauke lace din ba taji shigowar shi, da yasa zuciyarta yin wani irin tsalle, shisa ta jefa hijabin a sama tana fatan Allah yasa baigani ba. Tana kallon yanda yasa hannun shi ya dafe goshin shi yana runtsa idanuwan shi kafin ya sauke hannun yana ware su a kanta. Sosai yake kokawa da duk wani abu dake zuciyar shi yana tuna mata da in ta manta akwai igiyar aure a tsakanin su da Nuriyya da ta hana mishi dukan ta saiya fitar mata da yanda ko a gaba ba zatai kokarin raina hankalin wani mai suna irin nashi ba, akwai azumi a bakin shi, watan Ramadan ne, wata mai albarka da yake cike da son yafiya da aikata alkhairai. Amman tafin hannun shi har kaikayi yake ya amsa tambayar rainin hankalin da tayi mishi akan kuncinta, marin da sai taga taurari "Ki tauna maganar da zaki fadamun Nuriyya, Wallahi gab nake da wanka miki mari. Karki gwada wasan banzar ki a kaina yau, ba zai mana dadi ba. Me yasa kika daukar mun kudi?" Kallon shi Nuriyya tayi tana jin zuciyarta na ci gaba da dokawa, bata taba ganin shi cikin irin wannan yanayin ba, amman a kasan tsoronta akwai yanda maganganun shi suka bata mata rai, taya zaice zai mareta tana matar shi, ita alkawari taiwa kanta daga ranar da namiji zai tabata ya taba auren shi tunda ita ba jaka bace da zai kamata yana duka. "Wai wanne kudi?" Ta tambaya tana karasa kwance sauran hankalin da AbdulKadir yakeji yana rike da kwakwalwar shi ya kuwa dauketa da wani irin mari da yasa tajin kamar idonta daya ya fado, da sauri ta saka hannu ta dafe idon tana lalubawa taji kwayar na cikin shi, wani irin numfashi take ja tana son kukan ya kwace mata ko zai rage mata radadin da takeji, AbdulKadir na kallon ta, wani irin dana sani yake ji yana shirin lullube shi, alkawari yaiwa kan shi da ba zai sake taba wata mace da zata kasance karkashin igiyar auren shi ba, saboda yanda addini ya haramta mishi hakan, yanda al'ada bata yardar mishi da hakan ba, amman Nuriyya ta saka shi ya karya alkawarin nan da azumi a bakin shi. "Na fada miki ki tauna maganar da zaki fadamun baki jini ba, uban me yasa ni da gidana ba zan ajiye kudi inda nake so ba? Me yasa zaki dauka? Me yasa zaki daukar mun? Rashin hankalin ki bai fada miki kudin zai iya kasancewa ba nawa bane? Ban nuna miki salary dina ba Nuriyya?" Ba sosai take jin maganganun AbdulKadir din ba duk da hargowar da yakeyi kamar kiris yake jira ya rufeta da duka "Abinda nake miki bai isheki ba sai kin daukar mun kudi? Kin dauka ban san kina zarar mun ba duk idan na ajiye? Ban miki magana bane saboda ina guje mana zuwa inda muke yanzun. Kinsan kudin wa kika dauka? Kinsan kunyar da kika sakani a ciki? Me kike so in ce mishi? Ni na dauki kudin? Ko ke kika dauka? Me yasa zaki mun haka?" Zuwa lokacin radadin da take ji ya fara yin kasa, sai hawayen bakin cikin da suke silalo mata suna busar da tsoron shin da takeji, tunda ba mala'ikan mutuwa bane ba, ta dauka yafi karfin dubu arba'in da biyu da har zai zauna yana mata tijara akan su "Ni na dauka, saboda na tambayeka ka hanani shisa nagani na dauka, me yasa kai baka fadamun ka ajiye kudin ba? Me yasa kai baka fadamun ba naka bane ba?" Nuriyya ta tambaya cike da tsantsar rashin kunya tana saka wani murmushin takaici kwacema AbdulKadir din "Akan dubu arba'in da biyune zaka mareni? Ni ba jaka bace da zan zauna kana jibgata" Kai AbdulKadir ya girgiza, idan yana ganinta a gaban shi, idan taci gaba da magana zai daketa saiya ji wani daga cikin kasusuwan ta yayi kara alamar karyewa, zai daketa sai ta kasa ko nishi balle alamar kuka, ballantana ta sami bakin da zata tsaya tana kallon shi cikin idanuwa tana mishi rashin kunya, zai zabar musu abinda zai fi musu sauki, muryar shi a hankali ta fito kamar yana dandana duka kalaman shi "Kije gida Nuriyya, kije gidan ku ki dan huta, nima in huta" Sheqeqe Nuriyya take kallon shi, tana jin auren shi yau kamar sartse a makoshin ta, bambancin su da Anas na bayyanar mata "Ni babu inda zanje babu wata shaida, sai inje musu saqaqa ince me? Yaji na yo? Ka sakeni mana sai in tafi da Hujja" Ta karashe maganar tana watsa mishi wani kallo kafin ta dora da "Ni ba kai bane mijin dana dauka na aura, ba haka Waheedah take fadarka ba, ba haka take nuna ka ba" Da mamaki AbdulKadir yake kallonta "Kin aureni akan abinda Waheedah take fada ne daman?" Dan sosai yake son ya kwantar da bacin rai ya fahimci maganganunta, amman su kansu tunzura shi sukeyi, ba shi ta aura ba, mijin Waheedah ta aura shine abinda take son fada mishi. "Me zanyi da kai? Wallahi AbdulKadir ba kai bane mijin da nake burin aure, kudinka da halayenka basuyi mun ba, ba zan iya zama da kai da wannan bakaken halayen ba" Nuriyya ta karasa maganar tana jin zugin da kuncinta yake na marinta da yayi, garama ya saukake mata auren shi, Asma tace mata da kyawunta ta zauna namiji na wahalar da ita, kuma gaskiya ne, in yau ta gama iddarta tana da tabbacin samarine zasu dinga mata layi. Numfashi AbdulKadir yake ja yana fitarwa idan taci gaba da magana tabbas zai datse igiyar dake tsakanin su, maganganun da take fada din na kara tunzura shi sosai da sosai, dan bai kara sanin yanda zuciyar shi take doka mata ba sai yanzun da take fada mishi maganganun da yasa shi jin kamar ita din bata taba son shi ba. Abinda take tunanin auren shi zai samar mata shi take so. Abinda taga kamar auren shine ya samarwa Waheedah shi ta biyo. Lokutta da dama kuma ba mata kawai ba, har maza na wannan wautar, ba a karin mata ta biyu ba maza kanyi kuskuren nan, a ta farkon ma, da yawa kan dauka auren wata mace shine cikar farin ciki, idan har baka da farin cikin da kaine silar samarwa kanka shi, cikar shi zatayi

Chapter 34 of 37