Share this page
a bakin shi yana soma taunawa tukunna ya ajiye cokalin "Kafadu zaka dagamun?" A kasalance AbdulKadir yace "Me kake so inyi to? Na riga nazo, komawa zanyi in kiraka ince maka zan taho?" Kai Yassar ya jinjina, sosai rashin kunyar AbdulKadir ta karu tun shekarar data wuce, wani abu ya same shi da baisan menene ba, bakomai yake fada mishi ba, amman baya rufe shi har haka, ko kiranshi yayi a waya da cewar zaije Kaduna ya dubashi sai yace mishi babu lokacin da zai ganshi, tun yana zuciya yaqi zuwa harya kula AbdulKadir din na boye mishi ne, saiya dinga share shi baya kiranshi saiya shiga Kaduna tukunna. To har yanzun kuma boye mishi yake, wannan ba kanin shi bane ba. Wayarshi da take a hannun shi Yassar ya danna dan yaga ko karfe nawa, hakan yasa AbdulKadir cewa "Nasan yarinyar nan..." Yana dakuna fuska, danna wayar Yassar yayi haskenta ya dauke, da sauri AbdulKadir din yakai hannu yana fisge wayar Yassar din ya sake dannawa "Kaban wayata AbdulKadir..." Sosai yake kallon hoton fuskar wayar Yassar din "Hawwa ce ko?" Ya tambaya yana mika ma Yassar din wayar daya karba yana fadin "Ban sani ba" Kai AbdulKadir ya jinjina yana ajiye plate din dankalin ya dauki kofin shayin shi daya rike da hannuwa biyu yana kurba "Tun yaushe?" Shiru Yassar yayi ya kyaleshi "Hamma magana fa nake maka... Tun yaushe? Zaka fara dating baka fadamun ba ashe?" Kallon shi Yassar din yayi "Kamar yanda wani abu ya sameka baka fadamun ba kake nufi?" Numfashi AbdulKadir ya sauke dan bashi da abinda zai fada, wani abu ya same shi da gaske, amman kuma ya riga ya wuce, fadar bashida amfani tunda ba wani abune zai canza ba idan yayi hakan. "Me yasa ba za'a hada dana su Hamma Yazid ba?" AbdulKadir ya bukata yana son sake akalar zancen. Yassar yagane hakan, bazai takura shi sai yasan meya same shi ba "Bamu dade ba, ba mufi wata biyu ba, kar wani abu ya canza a gaba..." Kallon shi AbdulKadir yayi "In har kasata a fuskar wayarka kana jinta a ranka Hamma, bana tunanin akwai abinda zai canza..." Murmushi Yassar yayi, wata biyu da fadama Hawwa yana sonta, amman ya dan jima yana yin haka daga nesa-nesa daman, duk sanda zasu zo gidan, kuma suna dan chatting kadan a WhatsApp. Bayaso abinda ya faru da Yazid akan Waheedah ya faru dashi, shisa bai kwauron baki ba, kuma da dukkan alamu itama ta jima tana jinshi din, duk da haka bayason yin gaggawa, duk da zaifi so suyi shagalin bikin nasu tare da Yasir, amman sam Yasir yace mishi shi bai shirya yin aure dan lokacin ba, da alama zai rigashi. "Kayi magana kawai ayi bikin nan duk mu huta" AbdulKadir ya fadi cikin sigar tsokana. Yar dariya Yassar yayi "Lallai yaron nan, to kaima kayi auren mana" Girarshi duka biyun AbdulKadir ya daga ma Yassar "Da wa?" Ya tambaya yana kurbar shayin daya kware shi dajin amsar Yassar din "Waheedah..." Tari yake sosai dan shayin yabi mishi ta hanyar da bai kamata ba, sosai yake kara kurbar shayin ko zai samu sauki, muryarshi a dishe ta fito daga kasan makoshin shi "Wanne irin wasa ne wannan?" Ya bukata yana sa Yassar din hararshi "Karka rainamun hankali AbdulKadir, shekara nawa kana yawo da hotonta a wallet? Dan banyi magana ba baya nufin ban kula ba, itama kuma ina kallonta, bata kula kowa, ban tana ganin ta fita zance da wani ba..." Kallon Yassar yake da dukkan alamu Hausa yake mishi, amman da wani yare daban yakejin maganganun Yassar din na dira kunnuwanshi saboda yanda ya kasa fahimtarsu, yanayin fuskar AbdulKadir din Yassar yake kallo, mamaki na bayyana akan tashi fuskar "Tsaya... Me kake son ce mun?" Ya tambaya yana kasa gasgata abinda yake gani a fuskar AbdulKadir din, kai Yassar yake girgizawa "AbdulKadir..." Ya kira yana cigaba da girgiza kai, AbdulKadir din bai magana ba har lokacin, kallon Yassar din kawai yake kamar qaho ya fito mishi a tsakiyar kai "AbdulKadir..." Yassar ya sake kira a karo na babu adadi, yana jinjina abinda yake gani a fuskar kanin nashi, har ranshi, duk tsayin shekarun nan ya dauka soyayya suke da Waheedah din, yana kuma da tabbacin bashi kadai bane yake zaton hakan. Wani zafi yaji kirjinshi nayi, ya hana Yazid furta mata yana sonta saboda a tunanin shi AbdulKadir din nasonta, yana kuma da tabbacin idan shi baya sonta ita tana son shi, dan yanda take tambayarshi akan AbdulKadir din kawai ya tabbatar mishi da haka daga nata bangaren. "Me yasa?" Yassar ya tambaya, sai lokacin AbdulKadir yace "Me yasa me?" Kai Yassar ya jinjina "Tana sonka AbdulKadir..." Yassar yai maganar can kasan makoshin shi, tausayin yarinyar na cika zuciyarshi, plate din dankalin shi AbdulKadir ya dauka yana diba ya cika bakin shi dashi taf yana cigaba da taunawa, maganar Yassar din na mishi yawo a duk ilahirin jikin shi 'Tana sonka AbdulKadir' Ko a mafarki mai nisa bai taba hango soyayya da Waheedah ba, ko kadan, soyayya fa, da Waheedah, tana da muhimmancin dashi kanshi baisan iyakarshi ba a rayuwarshi, amman soyayya da ita, shine karshen abinda yake hangowa. Sai dai soyayya da kowama a yanzun ba abu bane da yake tunanin zai faru, bayajin yana da wannan lokacin. "AbdulKadir..." Yassar ya kira ganin yanda yake cin abincin "Karka kware..." Bai kulashi ba, dankalin kawai yake zubawa a bakin shi yana taunawa. Hakan yasa Yassar mikewa ya fice daga dakin da tunani kala-kala a ranshi. Tari AbdulKadir ya somayi yana fita, babu shiri ya dauki shayi yana kora dankalin bakin shi dashi, hadiyewa yayi yana sauke numfashi. Kafafuwan shi ya ja yana dorasu kan gadon hadi da kwanciya yaja bargo ya rufe jikin shi. Pillow din daya dora kan shi yaji ya soma isar shi, dan ba haka yake kwanciya da pillow ba, dagawa yayi yana dora pillow din akan hannun shi tukunna ya dora kan shi a sama, yadanji dai-daito a kwanciyar. Yassar yasa kashi abinda bayason yi, idan akwai abu na biyu da bayason bayan raini, tunani ne, ko kadan bayason ya zauna yana tunani, taya Yassar zaice Waheedah na son shi, ita Waheedah din bata da bakin da zata fada mishi kome yake faruwa, kanshi ya bala'in daurewa cikin yanayin da bai taba tsintar kanshi a ciki ba, komai yake ji ya cakude mishi haka kawai. Tun ran daurin auren Nuriyya rabon dayai tunanin wani aure, yanzun kuwa gabaki daya tunanin ne a ranshi. Ta ina zai fara? Wacce yarinya zai fara tunkara? Yaushe ma zai ganta? Duk da yasan indai yana da rai da lafiya aure abune da ya zame mishi dole, ko dan gujin fadawa halaka, tare da Waheedah yana da tabbacin ba zata taba raina shi ba. Asalima raini na daya daga cikin abinda yasan bazai taba shiga tsakanin su ba. Kuma a yanda yakeji bazai iya kallon idanuwan kowacce yarinya da sunan soyayya ba a yanzun, bashida ma da wannan lokacin, da anyi posting dinshi zuwa inda zai fara aiki kuma zai kara samun karancin lokacin duk wannan abubuwan. Tashi yayi zaune, karo na farko a tsayin lokaci da yaji zuciyarshi na dokawa da abinda yake shirinyi. Wayarshi ya dauko yana kunna data din, WhatsApp dinshi ya bude, sunan Waheedah ne farko da saqonninta da suketa shigowa, sosai bugun zuciyarshi yake karuwa, bude sakkonin yayi: 'Me kaci?' 'Karka kwanta da yunwa Hamma' 'In dafa maka indomie? Ko zaka sha Tea?' 'Shine baka fadamun zaka zo ba ko?' Dubawa yayi yaga tana online, rubutu ma takeyi, jikinshi yakeji har kyarma yake mishi, a hankali ya soma rubutu yana tura mata: 'Waheedah...' Rubutun da take yaga ta tsayar, hakan yasa shi cigaba: 'Waheedah...' Runtsa idanuwan shi yayi yana sake budesu kan screen din wayar 'Hamma' Ta amsa, ya karanta sunan nashi da muryarta, bayason yin abinda zai dana sani, sanin ba zata taba raina shi bane abinda yabashi kwarin gwiwar rubuta 'Kina so na?' Karanta tambayar tashi yayi, ganin bata fara ko typing ba, ba lallai ma tagane kan tambayar tashi ba 'Ba so na yan uwa ba Waheedah... So na aure. Kina so na?' Tana online har lokacin, amman bata ko fara rubutu ba, kuma yaga ta karanta, zuciyarshi yakeji har cikin makoshin shi saboda dokawar da take mishi. 'Ki amsani, zan kirga daya zuwa goma. Karki amsa sai kina da tabbaci, idan bakida shi karki amsa, nida ke zamuyi kamar ban tambaya ba, maganar ba zata sake hadamu ba har abada' Ya fadi yanajin yanda maganganun nashi suka zauna mishi, ita dashi suna da daqiqan da zasu dauke shi ya kirga daya zuwa goma, amman zai karya idan yace baya tsoron shirunta. 'Daya...' 'Biyu...' 'Uku..." Rubutu yaga ta soma, hakan yasa shi barin kirgar da yake, can kuma yaga ta daina 'Hudu...' 'Biyar...' 'Shidda...' Rubutun ta sake cigaba dashi, tana sake dakatawa bayan wani lokaci "Ki kasheni kawai Waheedah" AbdulKadir ya furta a fili, yana jin alamar zufa a goshin shi da bayan wuyan shi 'Bakwai...' Zuwa lokacin hannuwan shi kansu zufa suke fitarwa, shi baima taba tunanin soyayya da ita ba, yanzun hakan baisan rashin hankalin daya kaishi yin abinda yayi ba, baisani ba, gashi yazo yanajin bugun zuciyar da bai taba tunanin zai iyaji bama akan jiran amsarta, Yassar bai tabbatar ba, hasashe yakeyi, bai tabbatar da Waheedah nason shi ba, kilama tana da wanda take so, yai tunanin yanajin wani tuquqi na tokare mishi makoshi. 'Takwas...' Ya tura, yana jin yanda zaibar garin Kano da sassafe, yanajin yanda yaima kanshi karya da tunanin amsarta ko rashin amsarta bazai canza komai ba, da gaske baya tunanin zai iya hada idanuwa da ita idan bata amsashi ba. Duk da bayajin yana dana sanin tambayarta din, Yassar yasa shi son sanin ko tana son shi ko bata son shi. 'Tara...' Ya tura yana gyara zaman shi hadi da fitar da wani irin numfashi mai nauyin gaske, idanuwan shi ya runtsa a hankali ya bude su kan screen din wayar. 'Ina son ka, ina son ka da aure Hamma AbdulKadir' Sake karantawa yayi yana sauke numfashin da baisan yana rike dashi ba. Wayar ya ajiye gefe yana dafe kanshi da hannuwanshi duka biyun, wani irin numfashi yake saukewa mai nauyin gaske, kafin ya mike yana zira takalman Yassar dake bakin kofa ya fice daga dakin yanayin hanyar wajen bangaren nasu. Takawa yake zuwa bangaren Abba yanajin shi kamar wanda yake tafiya a gajimare, jinshi yake kamar yana yawo a wata duniya da batashi ba, kamar yana gefe yana kallon wani mafarki dashi a ciki. * Dakin Abba ya shiga da sallama, ya same shi a tsakiyar falon a zaune, Mama nakan kujera "AbdulKadir..." Abba ya fadi da fara'a yanajin dadin ganin dan nashi. "Abba..." AbdulKadir yace yana karasawa ya zauna gefen shi. "Abba zanyi magana dakai" Murmushi Abba yayi "Soja manyan kasa, ina saurarenka ai" Daga kai AbdulKadir yayi yana kallon Mama dake zaune, yana saka Abba kara fadada murmushin shi, mikewa Mama tayi, batason sake shiga hancin AbdulKadir din kafin ya tona mata asiri wajen Abba. "Bari in baku waje kuyi sirrinku" Cewar Mama tana dora murmushi kan fuskarta, lokacin daga fice daga dakin. Kallon Abba yakeyi a nutse yace "Aure zanyi Abba... Kafin in koma nake so a daura" Da mamaki bayyane a fuskar Abba yake kallon AbdulKadir din, kafin ya numfasa da fadin "Aure AbdulKadir?" Kai AbdulKadir ya daga mishi, yana jin maganganun na fitowa daga zuciyarshi "Eh Abba..." Wannan karin Abba ne ya jinjina kai, maganar na dirar mishi da wani yanayi, yana kuma son karbarta da budaddiyar zuciya, idan har AbdulKadir din zai bude baki da maganar aure to yana kokarin ganin ya gujema fadawa halaka ne, kuma yanzun yana da sana'ar da Abban yake da tabbacin zata riqe mishi mata, sai dai shi bayason yin abu cikin gaggawa, musamman magana ta aure. "Yaushe zaka koma?" Jim AbdulKadir yayi kafin ya amsa "Sati biyu in na dade" Numfashi Abba ya sake saukewa "Maganar aure a sati biyu AbdulKadir, abune da bazance bazai yiwu ba, amman gaggawa ba abu bane mai kyau. Aure kuma yana bukatar shiri. Nasan kana da aikin dazai rike maka mata, amman wajen zama fa? Lefe da sauran hidindimun biki" Dakuna fuska AbdulKadir yayi shi baiyi wannan tunanin ba kwata-kwata. Yama manta ana wani abu waishi lefe a maganar aure, ya kuma manta ana neman wajen zama. Magana Abba yaci gaba dayi "Ana iya maganar auren, idan kana ganin zaka iya shiryawa nan da watanni shidda sai a hada dana su Yazid duk ayi..." Kai AbdulKadir ya jinjina, hakan ya mishi, zai tara kudin da zasu ishe shi yin lefe, wajen zama zasu iya farawa da barikin sojoji tunda yasan za'a bashi muhalli, amman ko kadan ba dadewa zai ba, kafin ya tara kudin dazai mallaki nashi ne zasu zauna. Baya son yaranshi su tashi cikin bariki, badan wani dalili ba, ra'ayin shine kawai hakan. Dariya maidan sauti yaji ta kubce mishi, yadan girgiza kai. Da gaske ya samu matsala, shine da maganar aure harda tunanin rayuwar yaranshi da yanda yake son ta kasance. "Hakan yayi Abba... Zan tara kudin sai in bama Hajja ta siyo abinda ya kamata..." Murmushi Abba yayi, AbdulKadir din ya kalle shi yana fadin "Waheedah ce Abba... Waheedah zan aura" Kallon shi Abba yake da mamaki shimfide akan fuskar shi "Waheedah? Waheedah ta nan gidan?" Ya karasa tambayar da alamar rashin yarda a muryarshi da fuskarshi gabaki daya. Akance sai halayya tazo daya ake zama guri dayama har a qulla alaqa, Abba na ganin karyar zancen a abinda AbdulKadir yake fada mishi, dan ta kowacce fuska AbdulKadir bai dace da Waheedah ba, halayyarsu da komai nasu ya banbanta, bai kuma hango ta yanda akai suka fara soyayyar ba. "AbdulKadir ka tabbata? Ita Waheedah din ita tace tana sonka?" Kai AbdulKadir ya dagama Abba, inda batace tana son shi ba, bazai taba zuwa ya furta ma Abba zancen aurenta ba. "Allah mai iko... Oh Allah" Abba yake fadi har lokacin da AbdulKadir din ya mike jinjina maganar yake, dan kai kawai ya iya daga ma AbdulKadir batare da yaji kome yace ba, harya fice daga dakin. Sosai yake jinjina al'amarin auren Waheedah da AbdulKadir, shikam zai kira Waheedah ya tabbatar daga wajenta kafin ya yanke kowanne hukunci, dan jikin shi na mishi wani iri akan auren, sanyin Waheedah yai yawa, zafin AbdulKadir ko su da suka haifeshi addu'a suke binshi da ita, yana kaunar su biyun duka, yana jin Waheedah har kasan zuciyarshi, zai komai dan ganin ba'a cutar da marainiya da sa hannun shi ba...! *#TeamAbdulKadir* *#TeamWaheedah* *#AnaTare* [7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan IG: SufyanLubna Email: Calmlubna@gmail.com Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43 *ABDDULKADIR* *LubnaSufyan* 16 Tun da ta kwanta tunanin abinda yaci takeyi, ko kadan zuciyarta taki samun nutsuwa, ita kanta Amatullah ce ta dafa musu taliya, da bata zuba musu tare ba, tana da tabbacin babu abinda zata saka a cikinta. Dan ta nemi yunwar data kwaso tun daga makaranta ta rasa, duk da tasan ba lallai ya amsata ba, bai hanata daukar waya ta bude manhajar sada zumuntarta na whatsapp ba. Sunan shine a sama dan shine mutum na karshe da tayi magana dashi. 'Me kaci?' Ta tambaya, tana dorawa da 'In dafa maka indomie? Ko zaka sha Tea?' Amatullah dake kusa da ita ta gyara kwanciyar ta tana fadin "Adda Wahee... Ki rage hasken wayarki mana" Hannu takai tana rage hasken wayar hadi da fadin "Yi hakuri..." Bargo kawai Amatullah taja tana rufe jikinta har kai batare da tace komai ba. Hakan ya ba Waheedah damar mayar da hankalinta gabaki daya kan wayar, dan ba surutun take so ba daman. 'Shine baka fadamun zaka zo ba ko?' Ta sake rubutawa tana tura mishi, da tasan zaizo din da ta dafa mishi wani abu, lumshe idanuwanta tayi tanajin da dare bai farayi ba ita kam ko indomie ce data dafa takai mishi, a kasan zuciyarta take addu'ar karya zauna da yunwa. Alamar shigowar saqo da taji yasata ware idanuwanta kan screen din wayar da wani irin bugun zuciyar da bazai misaltu ba 'Waheedah...' Lumshe idanuwanta tayi data karanta sunan nata da muryarshi, tana bude idanuwan da murmushi a fuskarta 'Waheedah...' Taga ya sake rubutowa, saida ta goge hannunta jikin wandon kayan baccin da take sanye dasu saboda zufar da taji ya mata, tukunna ta iya amsa shi da 'Hamma' Rubutu taga yayi, babu shiri ta tashi zaune, da ita kadaice a dakin tsaf zata yi dan ihun murna ko ya yake, yanzun ma gudun tashin Amatullah daga barcine kawai ya hanata yin hakan, amman kanta har wani lilo yake, kamar tana saman gajimare haka take jinta, kafin ta karanta saqon shi daya shigo da wani yare daban da ya saka komai yi mata tsaye cik 'Kina so na?' Karantawa takeyi tana kara maimaitawa cike da son fahimtar kalmamomin da take jin kamar ba'a yaren da take fahimta yayi su ba, bai bari ta gama fahimtar su ba ya kara mata da 'Ba so na yan uwa ba Waheedah... So na aure. Kina so na?' Wayar ta ajiye jin kamar ta dauki wani irin dumi da yake barazar qona mata hannuwa, sauka tayi daga kan gadon, fankar dake cikin dakin takejin ta mata kadan, zafi takeji bana zazzabi ba, zafi take ji daya girmi ta dora shi akan tsantar girgiza da mamaki. Littafin Amatullah da tayi assignment tagani a ajiye, da sauri ta dauka tana fifita fuskarta da duk wani waje a jikinta da zata iya. Zuciyarta kanta ta nutsu wani waje a cikin kirjinta dan taji abinda basu taba mafarkin ji ba su dukansu. Sakon da taji ya sake shigowa ya sata dauki wayar saidai ta kasa zama sam 'Ki amsani, zan kirga daya zuwa goma. Karki amsa sai kina da tabbaci, idan bakida shi karki amsa, nida ke zamuyi kamar ban tambaya ba, maganar ba zata sake hadamu ba har abada' Gefen gadon ta zauna tana mayar da numfashi a hankali, ta runtsa idanuwanta ta budesu kan saqonnin nashi yafi sau ashirin, so take ta tabbatar ba mafarki takeyi ba. Ba kuma tunaninta yake hasaso mata abinda zuciyarta take burin ji ba, amman duk sanda zata bude sakon AbdulKadir din yake sake mata sallama. 'Daya...' 'Biyu...' 'Uku...' Ta karanta kafin zuciyarta ta fara mata ihu tana sanar da ita yanda take musu wasa da dama kwara daya tal da suka samu a wajen AbdulKadir din. Tasan shi, kamar yanda ya fada ne, idan harya gama kirga goman da yace maganar ba zata sake hadasu ba har abada. Sai dai yanzun ma batasan yanda akai maganar ta hadasun ba, ko a mafarki bata taba tunanin hakan zata faru da ita ba 'Hamma... Hamma kace wani abu, ka gayamun ba mafarki nake ba, kabani wani tabbacin banda wannan...' Ta rubuta, sai ta tsinci kanta da gogewa 'Hudu...' 'Biyar...' 'Shidda...' Kai take girgiza mishi tana soma rubuta "Ina sonka, bansan ko tun yaushe nake sonka ba, ina sonka fiye da yanda zan taba fada maka Hamma AbdulKadir, tare dakai zuciyata ta fara bude idanuwa, kai zuciyata ta fara dokawa...' Batasan meyasa ta sake gogewa ba, kalamai take nema, amman ta rasa, har lokacin jin komai take kamar a mafarki, kamar tana tura mishi amsar zata farka 'Bakwai' Kai ta sake girgiza wannan karin a fili tace "Ka tsaya Hamma, dan Allah ka tsaya..." Idanuwanta ta lumshe tana sake budesu kan wayar tata 'Takwas..." Wani irin yanayi ne ya bayyana kan fuskarta, muryarta a karye tace "Hamma mana, dan Allah ka tsaya..." Nutsuwarta take son tattarowa ko da abinda yake faruwa zai kasance mafarki, bataso ta manta komai, sakkonin nashi ta sake karantawa tana lumshe idanuwanta ta adana su wajen da tasan ba zasu taba bace mata ba koda ta farka tukunna ta bude idanuwan nata. 'Tara...' Ta karanta "Bansan yazan ci gaba da rayuwa bayan abin nan ba Hamma, idan mafarkine ka tabani ta fannin da banajin zan koma dai-dai wannan karin... Ka fifitamun wutar burina ka dawomun da komai baya..." Ta karasa maganar da wani irin sanyin murya, sosai take jin in har mafarki take a gefen soyayyarshi da take wahalar da ita, burin samun shi zai zauna, zata dinga kallon shi tana jiran ya sama mata wajen zama a rayuwarshi ko da bata samu a zuciyarshi ba. 'Ina son ka, ina son ka da aure Hamma AbdulKadir' Ta tura mishi tana jiran taji ta farka daga baccin da take, alama tagani na cewar ya karanta sakon, kafin taga ya sauka daga kan WhatsApp din, wani irin numfashi da batasan tana rike dashi ba ta saki, itama kashe data din tayi ta ajiye wayar hadi da mikewa. Bandaki ta shiga ta tara ruwa tana wanke fuskarta, har lokacin numfashi take mayarwa kamar wadda tayi gudu. Zuwa yanzun bata da kalaman da zata fassara abinda takeji. Takai mintina goma tsaye a bandakin ta dafe sink, amman idan ka tambayeta ba zatace ga asalin abinda take ji ko take tunani ba. Alwala ta daura ta fito daga bandakin, doguwar hijab din da take sallah da ita ta dauko ta saka jikinta. Dardumar da tayi sallar isha'i tana shimfide bata nade ba, kai tahau ta fara jero salloli tana rokon tabbatar alkhairi a koma menene yake shirin faruwa tsakaninta da AbdulKadir din, dan tun daga yanda take son shi tasan abin yafi karfinta, yanzun ma ba zata iya ba, ba kuma zata bata darenta tana tunanin abinda baya karkashin ikonta ba, gara ta bude ma Allah zuciyarta, sosai kuma ta samu nutsuwar da take jin ta kwace mata, akan dardumar bacci mai nutsuwa ya dauketa. * Tana da darasin safe, gashi ta tashi da wani irin sanyin jiki, har iskar da take shaqa daban take jinta yau din, bata sake shiga wani yanayi ba saida taci karo da sakon Abba 'Aslm. Waheedah ki sameni kafin ki wuce makaranta' Haka kawai taji zuciyarta na mata rawa, duk da ba yau bane ranar farko da Abban yakan mata irin sakon ko idan zasuyi magana ko kuma zai bata wani abin. Yau dinne dai takejin kiran kamar zai zamana daban. Sanda tagama shiryawa saida ta biya dakin Mami tai mata sallama tukunna ta fita zuwa bangaren Abba. A bakin kofa ta tsaya ta kwankwasa, saida taji yai magana tukunna ta tura dakin da sallama tana shiga. Waje ta samu kan kafet din ta zauna dan shima anan yake zaune ya miqe kafafuwan shi. "Ina kwana Abba..." Ta gaishe dashi cikin sanyin muryarta "Waheedah..." Ya kira yana dorawa da "Kin tashi lafiya? Ya makarantar?" Hijab dinta da taji ta danne ta dan daga tana gyara zamanta sosai "Alhamdulillah..." Wani numfashi Abba yaja yana kallon yanda take komai nata cikin sanyi. Da tunaninta ya kwana a ranshi, har zuwa safiyar ranar yana jinjina ma kaddarar data hadata da AbdulKadir, dan ko a tunaninshi ya kasa dai-daita dacewarsu. Idan zabi za'a bashi na ya aurar da ita cikin yaranshi, yanajin Yazid kadai zai iya aura ma ita hankalin shi a kwance, yana da tabbaci akan Yazid zai riketa da amana, dan bazaice ga rana daya da yaji anyi wata hayaniya dashi ba tun yarintar shi. Muryarshi dauke da nauyin da yake jin dukkan jikin shi yai mishi ya soma magana "AbdulKadir ya sameni jiya. Nasan halin shi, nasan bazai sameni batare da amincewarki ba, amman ina so in tabbatar daga bakinki Waheedah, amana ceke a wajena kamar yanda suma suke amana, banma kowa maganar ba tukunna, ki fadamun idan kin amince da auren shi..." Kanta a kasa yake tunda ya fara magana, bata taba tsintar kanta cikin kunya irin wadda takeji ba, wasu zasuce kamar kasa ta tsage su shige, a irin kunyar da take ciki ba tajin zata iya jiran kasar ta tsage, ita take so ta narke ta sulale tabi kasar ta shige cikinta. Ga zuciyarta da take wata irin dokawa kamar zata fito daga kirjinta "Kimun magana Waheedah, karkiji nauyina, idan har baki amince dashi ba yazo ya sameni ki fadamun, wallahi indai ina numfashi babu wanda zai miki dole akan komai na rayuwa..." Shirun ta sakeyi tana kara sadda kanta kasa, numfashi Abba ya sauke "Aure ba abu bane da akanyi dan kowa nayi, ba kuma abu bane da ake fatan idan anyi a fito, aure abune da ake fatan idan har anyi ya zamana har muddin rai, shisa ba'a son gaggawa a cikin duk wani abu daya shafe shi, ba'a kuma son tursasawa, da fahimtar juna ma dole sai an hada da hakuri a zamantakewar da za'a tashi a kwana karkashin inuwa daya. Kimun magana Waheedah, bazan samu nutsuwa akan maganar nan ba..." Kanta da takejin yaima siririn wuyanta nauyi naban mamaki yau ta samu ta motsa tana dagashi a hankali, da ace nutsuwar Abba bata kanta da bazai ga daga kan ba "Kin amince da auren shi?" Abba ya tambaya yana son tabbatar wa, kan ta sake daga mishi a hankali. Wani numfashin ya sauke, yana jinjina ma karfin kaddara da take zuwa karkashin ikon Allah. Kai ya jinjina "To Alhamdulillah, Allah ya tabbatar mana da alkhairi..." Kafafuwanta Waheedah ta tattara, har lokacin ta kasa dago fuskarta, jikinta gabaki daya ya dauki dumi da kunyar Abba da takeji, mikewa tayi dakyar tana juyawa cikin sauri da nufin barin dakin "Kizo ki karbi kudin makaranta..." Abba ya fadi yana saka hannu a aljihun shi, amman kamar maganarshi ta kara tunzurata, da gudu ta fice daga dakin tana ja mishi kofar. Murmushi Abba yake "Oh Allah mai iko..." Ya fadi, ya jima wani abu bai bashi mamaki ba irin na daren jiya zuwa safiyar yau. Da gaske AbdulKadir da Waheedah sukeyi, yanda yake jinshi zai kwana biyu yana jinjina al'amarin. Wayarshi ya dauka ya kira Mami dan ya sanar da ita kafin ya samu dangin Baban Waheedah din da maganar, duk da sun jima da nuna mishi yana da damar yanke hukunci akan rayuwar Waheedah din bazai hanashi nuna musu godiya da halaccin da sukai mishi ba, zai samesu da maganar duk da yasan ba zasuki kowa yake son hadata dashi ba, balle kuma idan sunji jinin shi ne. * "Ina zaki je?" Muryarshi ta sauka cikin kunnuwanta, tana sakata gyara zaman jakar dake kafadarta tukunna ta juya tana sauke idanuwanta akan shi. Jikin shi sanye da riga fara kal, sai wandon sojoji gajere da silipas din wanka a Kafafuwan shi. "Hamma..." Ta kira da wani yanayi a muryarta, wani irin son shi taji ya taso mata har yana ma numfashinta barazana. Tasan ya kamata ta sauke idanuwanta daga kanshi, ta daina kallon shi, amman zuciyarta ce da iko kan idanuwanta wannan karin, ta kuma nuna mata bata gaji da kallon shi

Chapter 16 of 37