Share this page
mata sukeyi na zaman aure akwai wanda yakai girki bata lokaci da wahala. Bata taba tunanin suyar dankalin zatai mata wannan rashin mutuncin ba, barin shi tayi yadan karayi, tukunna ta kwashe, bata jira man ya tsane ba ta juye a wani kwano da ta dauko. Sauran dankalin ta zuba, tana komawa falo ta zauna. Da fitilar wayarta take ta amfani, kasancewar har lokacin basu dawo da wuta ba. Ga AbdulKadir ya jima, balle yazo ya kunna musu generator, ko kallo tayi ta rage zafi. Shima sauran dankalin haka taita juya shi duk ya dagargaje mata, ta kwashe tana kallon yanda a ido ma baiyi kyawun gani ba. Gashi sai tayi wata sauce kuma. Badan tana tsoron fadan AbdulKadir din ba, kwai zata soya su hada dashi. Sauran kayan miyar da ta dauko kitchen din Waheedah ta fito dashi ta juye a tukunya tana dorawa kan gas. Tukunna ta dauko albasa ta fara yankawa, ga yajin albasar daya cika mata ido, ga kayan miyar daya fara kamawa, banda tsakinta bakajin komai na tashi a kitchen din, sai kuma kauri. Albasar ta zuba ciki, tukunna ta zuba mai wajen ludayi takwas, dan kusan na kaskon da tayi suyane ta kusa juyewa, cakudawa tayi, taga kamar ta mata yawa, ta fara saka ludayi tana rage man. Ganin miyar na kara konewa yasa ta kashe gas din "Wanne irin bala'i ne wannan?" Tai maganar kamar zata saka kuka, tunawar da tayi bata saka maggi ba, guda takwas ta dibo ta bare, dandanqa shi tayi ta zuba a ciki tana cakudawa, sai taga kamar miyar ta kara baqi. Tabe baki tayi, dan kanta harya fara daukar alamar ciwo. Sanda ta fito daga kitchen din ana Isha'i, tana da alwalar ta, hakan yasa ta wuce daki, tana idarwa ta fara kiran lambar AbdulKadir, sau hudu tana kira bai daga ba. Na biyar dinne ta ji ringing din wayar a cikin gidan ta bangarenta. Hakan yasa ta fito tana dora murmushi a fuskarta "Sannu da zuwa..." Kai kawai AbdulKadir ya iya daga mata yana zama kan kujera, wayar shi ya ajiye a gefe. "In zubo mana abinci?" Da kai ya sake amsata, ta wuce kitchen din, plate ta samu ta juye dankalin a ciki, tana samun karamun wajen zuba miya ta zuba, ta hado ta fito, a kan kafet ta ajiye. Tana kallon AbdulKadir da gabaki daya hankalin shi ba'a kanta yake ba. Kafarshi ta taba, ya sauke wani numfashi mai nauyi. Waheedah ba zata saka shi kin cin abinci ba, bata isa ta daga mishi hankali yana zaune lafiya ba. "Meye wannan Nuriyya?" Ya bukata yana kallon dankalin da ya koma kamar dambu a cikin plate. Zuciyarta taji ta doka a cikin kirjinta, nan take idanuwanta suka ciko da hawaye. Ranshi AbdulKadir yaji ya kara baci, inda Waheedah ce ya shigo tana kallon shi zata gane halin da yake ciki, kuma kome zaice mata ba zata nuna ranta ya baci ba dan tasan nashi a bace yake, balle tayi shirin mishi kuka. "Bana son Kukan banza da bashida dalili, tambayarki nayi, ki bani amsa, meye wannan?" Hawayen take kokarin dannewa, amman sosai suke mata barazana. Muryarta can kasan makoshi tace "Wallahi bansan ya akayi yai haka ba nima..." Kai AbdulKadir ya jinjina, yasan ana samun akasi wajen girki, a ranakun da ranshi ba a bace yake ba, zai mata uzuri da cewar dan Adam baya wuce kuskure, amman yau haushin shi yake son hucewa akan kowa ya samu, ita kadai ce kuma a gaban shi. "Hannu zan saka?" Ya sake bukata yana kankance mata ido, kai ta girgiza mishi da sauri, tana mikewa ta wuce kitchen din, sai da ta matse kwallar da ta taru cikin idanuwanta, tukunna ta dauko cokula guda biyu ta dawo, mika mishi tayi ya karba, yana sakawa cikin miyar daya rasa gane wace iri ce, ga man da yake kwance a miyar zai iya ganin fuskar shi in ya leqa cikinta. "Me yasa baki saka mana nama ba? Wacce irin miya ce wannan?" AbdulKadir ya karasa tambayar yana jujjuya cokalin shi cikin miyar, kafin Nuriyya ta amsa ya sake fadin "Ni sauce nace kiyi mana, ita Waheedah takeyi idan ta soya mana dankali" Yau ne karo na farko da Nuriyya taji takaicin rashin iya girki a rayuwarta, dan shine karo na biyu a rana daya da AbdulKadir ya hada girkin ta dana Waheedah, kishin da takeji kuwa kirjinta har zafi yake mata. Shikuwa sunan Waheedah daya fadi yasa ranshi kara baci, babu shiri ya dibo miyar ya zuba akan dankalin daga gefe yana cakudashi kamar shinkafa ya dibo da cokalin yakai baki, yana jin kaurin daya cika mishi hanci daga cikin bakin nashi. Hadiyewa yayi batare daya tauna ba, dakyar ya iya cokali hudu, yunwar da yake tunanin yanaji ya nemeta ya rasa. Mikewa yayi kawai, Nuriyya na binshi da ido harya fice daga falon. Tsoron kar yai mata fada yasa bata tambaye shi inda zaije ba. Ita kanta a dole takecin dankalin, sai da taji cikinta ya cika tukunna ta kwashe kwanukan ta mayar kitchen, ta dawo ta zauna, jin har lokacin AbdulKadir bai tashi generator yasa tayi tunanin ko ta kira wayar shi, sai taganta ajiye akan kujera. Salama ta sakama ranta taci gaba da danne-danne wayar da rashin abin kallo ya sakata. Dan ita ba ma'abociyar chatting bace ba, daman karatu ne, nan tafi kwarewa, to duk litattafan da take bi, ba'a dora sabon cigaba ba. AbdulKadir kuwa waje ya fita yana samun waje kan matattakalar shiga gidan ya zauna. Yana kallon farin watan da ya haske harabar gidan, yana kuma daukar tunanin shi ya watsa satin su na biyu da tarewa a gidan shi da Waheedah. * Tunda sukaje gida ta samo fina-finai wajen Nabila, data gama aiki bata komai sai kallo, daya tambayeta wanne irin film ne tace mishi Korean, jiya daya farka yaganta tana kallo, da kan shi ya kashe system din, sai da ya zare mata ido da gaske tukunna ta hakura ta kwanta, da ta shagwabe fuska zatai mishi kuka. Yau ma aikin kallon takeyi da gab yake da haramta shi saiya bar gidan, tunda ta rage samun lokacin shi. Hidimar shi ya gama yi ya fita sallar isha'i. Fajr na dakin shi yana bacci, dan shi da anyi Magriba cikin shi ya dauka sai bacci, inba yanajin rigima ba. A matattakalar shiga gidan ya sameta zaune, jikinta sanye da rigar sanyin shi da ba hannun bane kawai yai mata yawa, har da rigar gabaki daya, sai dai Waheedah ce, haka take mishi, sai dai yaga rigunan shi a jikinta, inyai magana zata ce kamshin turarukan shi take so, kuma gasu a ajiye. Yakan ce ta fesa ta ajiye mishi rigar shi, dariya takeyi kawai "Kamshin ai ya hadu da naka...." Shine amsarta lokutta da yawa. Murmushi kawai yakanyi, a duniyar shi gabaki daya, ita kadai take mishi abinda take so, ita kadai yake cewa tayi abu ta maqale mishi kafada alamar ba zatayi ba, kuma ya hakura, wani lokacin ma kai kawai zata girgiza, idanuwanta na cikowa da hawaye, sai yaji gabaki daya gwiwoyin shi sunyi sanyi. "Me kike a waje?" Ya bukata yana karasowa ya zauna kusa da ita. Hancinta da sanyi ya cika ta ja, tukunna ta amsa shi "Wata nake kallo" Murmushi ya kwace mishi mai sauti "Wata?" Ya maimaita cike da alamar tambaya, yana kallon ta, kai ta daga mishi. Gabaki daya film din da ta gama kallo ya tafi da imaninta, duk wani abu da akai a film din taji tana sonyi itama, balle kuma kalar soyayyar da aka zuba. Sai dai akwai haukan da ita kanta tasan ba zata fara tunkarar AbdulKadir da shi ba. Shisa ta fito ta kalli watan abinta. "Me yasa zaki fito kallon wata?" Ya kara tambaya har lokacin yana kallon ta, shagwabe fuska tayi "Ba'a magana fa Sadauki, shiru akeyi a kalli kyan watan... Da yan....Subhanallah...." Waheedah ta karashe tana mikewa babu shiri tana fara zazzage skirt din dake jikinta tana dorawa da "Cinnaka... Hamma cinnaka wallahi..." Skirt din take zazzagewa tana murza cinyarta da take da tabbacin cizon daya manna mata ya wuce biyu. AbdulKadir take kallo da yake dariya harda rike ciki "Ba abin dariya bane, da gaske cinnaka ne..." Kai kawai AbdulKadir ya iya daga mata saboda dariyar da yake, dakyar ya iya cewa "Sannu... Mu karasa kallon watan..." Kafin ya rufe baki ta fara girgiza mishi kai, tana murza cinyarta da azaba ta isheta "Akwai dalilin da yasa bama yin wasu abubuwan a najeriya..." Wata dariyar AbdulKadir yaji ta sake kubce mishi "Mu koma daki..." Waheedah ta fadi tana wucewa, yabi bayanta, kasa ta zauna kan kafet tana cigaba da murza cinyarta, AbdulKadir din ya zauna kusa da ita, hadi da riko hannunta, da murmushi a fuskar shi har lokacin, yanzun ya tabbatar da abinda tagani a film ne taso gwadawa, saboda bata da hankali "Ki daina murzawa..." Hannunta ta kwace, ya sake riko shi, yana saka karfi wannan karin, skirt din ya kama da dayan hannun shi ya daga sama, yana duba inda cinnakan ya cijeta, wajen haryayi burdi, abinka da farar fata, har yayi ja. Duk da tausayinta da yaji bai hana shi cewa "Baki da hankali Waheedah..." Shiru tadanyi, tana tunanin abinda tayi, kafin dariya ta kubce mata, tana saka AbdulKadir din jin wata sabuwar dariyar shima, dariya suke kamar babu wani abu da zai iya taba farin cikin su. * Yanzun ma dariyar yake yi da sautin ta ya dawo dashi hayyacin shi, yana saka wani abu matsewa a kirjin shi, dariyar na dishe mishi, kan shi ya dafe da hannuwa biyu "Waheedah....Waheedah karki mun haka dan Allah... Ki rufamun asiri..." Yake fadi shi kadai. Bai san iya lokacin daya dauka zaune a wajen ba, kafin sauron da yake ta girbar shi yasa shi mikewa ya koma cikin gidan, dakin Nuriyya ya wuce, ya sameta a kwance, da alamar tayi bacci, dan ta kunna fitilar wayarta ta dora akan drawer din gefen gadon. Kayan jikin shi ya rage ya wuce bandakin yana watsa ruwa. Fitowa yayi ya saka gajeran wando ya zagaya ta gefen gadon ya hau yana kwanciya. Baifi mintina goma ba yaja karamin tsaki ya sauko, wayar Nuriyya ya dauka ya haska har zuwa falon ya dauki tashi wayar. Anan ya tsaya yana kiran lambar Waheedah, ta kuwa shiga, da alama ta kunna wayar, dagawa tayi, ya numfasa zai magana ta kashe wayar a kunnen shi, tana saka shi dawo da fuskar wayar ya kalla dan ya tabbatar da kashe mishi waya tayi a kunne. Wata irin dariya da bata da alaka da nishadi yayi, yana sake dannawa ya kirata, a kashe yaji wayar. Wata dariyar ya sake yi "Zaman lafiya ne bakya so Waheedah, tashin hankali kike nema dani shisa kika kashemun waya a kunne" Ya fadi yana wucewa daki ya koma ya kwanta, juyi kawai yake yana duba agogon wayar da yaga kamar baya tafiya dai-dai, dan yaqi yin sauri. Gari yake so ya waye, asuba a gidan Yassar zatai mishi, zaiji dalilin da zai sa ta kashe mishi waya a kunne, bayan tafi kowa sanin bayaso. * Bai samu bacci ba sai bayan sallar Asuba, dan yanda yaga rana haka yaga dare, da safen ma ciwon kai ne ya saka shi kwanciya. Tunda Waheedah na gidan Yassar babu inda zataje, in yayi baccin ya tashi sai yaje ya sauke mata. Ba zaice ga abinda yake faruwa ba, dan bacci yake daya kwana biyu bai samu irin shi ba, yaji kamar ana taba shi, wata irin damqa ya kaima hannun Nuriyya da yasata sakin ihu, idanuwan shi da suke cike da bacci ya sauke akan ta, tukunna ya saki hannunta da yake rike dashi. "Masoyi da ka karyani..." Ta fadi a shagwabe, kan shi yakeji kamar ana buga ganga a ciki saboda ciwon da yake yi "Ki kira sunana in zaki tasheni daga bacci, karki tabani..." Kai taje daga mishi tana murza hannunta "Zan fita ne daman..." Cike da rashin fahimta yake kallonta, hakan yasa ta dorawa da "Nace maka zanje wankin kai, tun shekaranjiya..." Kai ya jinjina mata, dan ya manta sunyi maganar, idanuwan shi ya fara lumshewa da alamun shirin komawa bacci tace "Masoyi...." Batare daya bude idanuwan nashi ba ya amsa ta da fadin "Nuriyya ki duba wallet dina ki dauki kudi, dan Allah kibarni nikam" Turo labbanta tayi tunda ba ganinta yake ba, ya bata kudi tun randa tai maganar, hakan dai ba zai hanata sake dauka ba, tunda ya manta. "Daman in dauki motar ka tunda bacci kake, ko zaka fita?" Ko kadan bayason dogon surutu, tsoro ya hana Waheedah koyon tuqi tun lokacin daya siyi mota, ba yanda baiyi daya koya mata ba, ya gaji ya kyaleta, Nuriyya kuwa da kanta ta nuna mishi tana son koya, ko sati biyu basu hada ba ta fara hawa babban titi, karambanin ta yana burgeshi lokutta da dama. Zai fita da motar shi, indai Nuriyya ce yasan zata bata lokaci kafin ta dawo, amman bayason yin surutun shisa yace mata "Allah ya tsare, ki karamun mai... Karki dade kuma" Murmushi tayi, sai da ta sumbaci fuskar shi tukunna ta zagaya gefen shi tana daukar wallet din shi da take ajiye kan gado, kudin ciki ta kirga taga dubu bakwai ne, duka ta kwashe tunda yace ta kara zuba mishi mai. Mayafinta ta dauka ta saka, tukunna ta dauki mukullin motar ta fice. Ranta kal take jin shi, zata fito a matar hamshaqin da take jinta, tun daga shigar jikinta, da leshi ne daya sha dinkin doguwar riga zuwa takalman kafarta da mayafinta, tasan ta wuce rainin kowa. Gata matar soja, wanda taga dama zata taka babu abinda zai faru. Haka ta shiga gidan man da ta fara samu a hanya, sosai ta kosa saboda layin da yake gidan man a ranar kamar anayin wata hidimar, duk da watan azumi ya gabato, amman sauran wajen kwanaki takwas, ballantana ace siyayyar azumi ce ta saka garin cunkushewa, danne danne waya takeyi a cikin motar tana hade rai ita kadai, ta sauke gilasan motar daman yanda za'a fi hangota, tana kuma jin dadin yanda duk wanda ya kalleta saiya kara kallon ta. Man dubu uku ta zuba, ta ja motar kenan da nufin fita daga gidan man wayarta ta fara ruri, kawarta ce da sukayi FCE tare. Bata kashe motar ba ta tsaya amsa wayar, barkewa sukayi da labari, tana fada mata auren wata bazawarar kawar su da za'ayi da kuma kalar shagulgulan da suka tanada. Honking taji an isheta dashi, taja karamin tsaki hadi da zuro kai ta window din motar, har lokacin bata sauke wayar daga kunnenta ba, a wulakance tace "Idan sauri kakeyi, kayi juya ka fita ta inda ka shigo mana" Shima mutumin da yake cikin motar shi qirar golf leqo da kai yayi "Bangane in juya in fita ba, Hajiya bakiga layin da yake bayana bane? Ke ai yakamata kiyi gaba saiki amsa wayar... Wannan ai rashin tunani ne..." Bude baki Nuriyya tayi tana kallon shi cike da mamakin kalaman shi da take dauka a matsayin tsantsar rainin hankali, tunda can ma ba hakuri gareta ba, dan ko matar babanta sai da tace ta dauka aure zai sa ta rage fada, amman hausawa kan ce mai hali baya barin halin shi. "Asma zan kiraki, ina zuwa..." Ta karasa tana sauke wayar daga kunnenta ta bude murfin motar ta fito, zuwa lokacin hankalin mutane da yawa ya fara dawowa kan su, musamman zagin da Nuriyya ta fara sirfawa mutumin, ganin kalar motar da ya fito daga ciki da kuma yadin jikin shi, sam bata kula da su biyu bane, dayan babban mutum ne, zai kai shekaru arba'in da biyar ko da doriya ma. Jikin shi sanye da shigar kananun kaya, rigar mai dogon hannu. Fuskar shi manne da farin gilashi. "Hajiya daga cewa ki fita zaki fara zagin shi? Kanki daya kuwa" A hasale Nuriyya ta mayar da hankalinta kan shi "Ko zaka rama mishi ne?" Jinjina kai mutumin yayi, yana rufe murfin motar ya zagaya a fusace, hakan yasa dayan abokin tafiyar tashi rike shi, da sauran mutane ma, harda ma'aikatan gidan man da suke ta ba Nuriyya hakuri ana so ta wuce ta tafi, amman ina, jinta take matar soja ce ita, sojan ma AbdulKadir, tana da tabbacin babu wanda ya isa ya tabata. Mutumin da ake rikewa kuwa fadi yake "Alhaji Mannir ka sakeni in ci uban yarinyar nan..." Kafin wani ya kula, hannun Nuriyya ya tashi sama ta kuwa yi nasarar zira shi tana dauke mutumin nan da marin da yasa wajen yin shiru na mintuna, kafin a taru a shiga tsakani. Huci kawai take tana girgije-girgije. Wasu mata da suma sukazo shan mai suka fito daga motar su suna kama Nuriyya din suka janyeta gefe, kuka ta fashe dashi tana fadin "Dan sun gani mace shine zasuci mun mutunci, wallahi sai na kira mijina... Dan bazan yarda ba" Daga gefe mutumin da har lokacin bai daina kokarin kwacewa ba yace "Ki kira shi fa, dan yau ina son ganin uban da ya tsaya miki a fadin garin Kano da ketaren ta..." Sosai mutane suke kokarin bashi hakuri, dan dayan abokin tafiyar daya kira da Alhaji Mannir ne ya samu ya fitar musu da motar su sukayi parking daga can gefe suka tsaya. Duk da mutane da suke basu hakurin cewar su tafi, kafin rigimar tayi nisa, tunda da alama Nuriyya din matar wani babban ce shisa taja rigimar. Ita kuwa Nuriyya AbdulKadir ta kira tana saka mishi kuka cewar wasu sunci mutuncinta a gidan mai. Sai da ta fada mishi sunan gidan man ta kuma ji yace mata ta jirashi, tukunna ta kashe wayar ta koma gefe tana matse hawaye. Mutanen gurin kowa da abinda yake fada, wanda ba'a fara rigimar a gabansu ba suna tambayar me ya faru, da yawa da aka fara a gabansu kuma suna tir da hali irin na Nuriyya din, wasu ma tafiya sukayi, da yawa kuma sun ma sha man, amman suna tsaye dan ganin karshen rikicin. * Gajeran wando ya saka, ya dauki farar riga ya dora, wayar shi ya saka a aljihu ya dauki wallet din shi, dubawa yayi yaga babu kudi a ciki, bazai iya tsayawa ATM ba, ran shi in yai dubu a bace kowanne yake, tun jiya yake neman inda zai huce haushin da yakeji, bai samu ba. Sai yanzun da Nuriyya ta katse mishi baccin da yakeyi, ga yunwar da yake ji har hanjin shi kullewa yake. Fitowa yai ya wuce dakin Waheedah. Cikin jakunkunan ta ya dauko ya duba, dari biyar ya dauka a ciki yasaka a aljihu yana ficewa. Mai babur ya tara zuwa gidan man, jikin shi har bari yakeyi daya karasa ya samu wanda zai jibga, ko canji bai tsaya karba ba, ya shiga cikin gidan man, inda take yake neman, kafin ya hango motar shi, da kuma Nuriyyar da take jingine a jiki. Har yayi hanyar ya hango kamar Major M. Alkali a tsaye jikin wata golf, sake dubawa yayi kuwa, shi dinne, dan sunyi aiki tare a Lagos. Mutum ne shi da matsayin shi da kakin shi bai taba sa ya wulakanta kowa ba, duk da yana da zafi in an tabashi, kuma yana cikin sojojin da AbdulKadir yasani da suka tsani wanda yake amfani da kakin shi yaci zarafin mutane. Fasa karasawa yayi inda Nuriyya take, sai da ya karasa can wajen shi yana kai gaisuwa, amsawa yayi baima iya tambayar AbdulKadir din abinda yake a gidan man ba. Ganin kamar ran shi a bace yake yasa AbdulKadir din yi mishi sallama yana takawa ya karasa wajen Nuriyya da ta fara fifita fuskarta da mayafin jikinta tun daga lokacin da ta hango AbdulKadir din ya karasa ya sarawa mutumin da ta wanke da mari. Hawayen ne wani nabin wani yake saukar mata "Ki daina kuka... Su waye? Waye ya tabaki?" AbdulKadir yake tambaya, sai dai ta kasa amsa shi, kuka take kamar zata shide mishi, baki ya bude zai sake magana, kamar daga sama yaji muryar Major M. Alkali yana fadin "Matarka ce ta wanke ni da mari kenan? Shine ta kiraka kazo kayi amfani da kakinka kaci mun mutunci..." Cikin tashin hankali AbdulKadir ya juya yana kallon Major, kafin ya juyo ya kalli Nuriyya da ta ja mishi bala'in da baisan ta inda zai fara fita daga cikin shi ba. "Nuriyya..." Ya kira muryar shi dauke da wani yanayi. Kuka take tana girgiza mishi kai, dan ita kanta batasan kalar tashin hankalin da zai biyo baya ba kenan, da tasan soja ne, sojan ma da alama yaiwa mijinta fintinkau da bata fara tsayawa ba, tun sanda ake cewa ta tafi, da lokacin ta shiga motarta ta wuce. "Muje ko..." Major ya fadi yana kallon AbdulKadir. Shikuma ya kalli Nuriyya kafin yabi bayan Major din, da sauri Nuriyya take shirin bin bayansu, wani irin kallo AbdulKadir ya watsa mata daya saka ta jin gabaki daya kayan cikinta na yamutsawa, idanuwanta cike taf da sababbin hawaye take kallon su, har suka karasa wajen golf din su Major da ta raina har tayi musu dibar albarka, boot din motar taga ya bude, AbdulKadir ya shiga ya kwanta, ya kuma mayar da murfin ya rufe, suna shirin shiga su tafi. Ai bata san lokacin da ta kwasa da gudu tayi wajen su tana fadin "Ina zaku kai shi? Ina zaka tafar mun da miji? Ka rufamun asiri, dan Allah kayi hakuri... Ka rama marinka ka kyalemun miji" Wani irin kallo Major ya watsa mata "Marin zai fita a jikin mijinki, karki damu" Ya bude motar ya shiga, suka wuce suna barin Nuriyya nan tsaye ta dora hannunta saman kai tana fadin "Na shiga uku na..." #TeamAbdulKadir #TeamWaheedah #LubnaSufyan[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan IG: SufyanLubna Email: Calmlubna@gmail.com Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43 *ABDDULKADIR* *LubnaSufyan* 20 MAFARI Rigima ce ta saka shi biyo mota daga Lagos zuwa garin Kano, dan tashi motar in ba hutun karshen shekara zai zo ba, baya tahowa da ita, babu yanda Waheedah batayi dashi akan ya biyo jirgi ba, yace mata bashi da kudi, wata yayi nisa, ga hidimar gida da sauran hidindimun dake gaban shi. Saida tace mishi ya biya kawai, akwai kudi a hannun ta, Abba ya bata kyautar kudi, batayi amfani dasu ba, akwai kuma kudin da shima yake bata, duk bata siyi komai ba, amman yaki. Jikin shi babu inda baya ciwo, ga rashin wadataccen bacci tunda motar dare ya biyo, da safe ya iso garin Kano. Tunda Waheedah ta hada mishi ruwan wanka ta tafiyarta kitchen taci gaba da aikin kifin da ta fito dashi dan ya huce tun da asuba, tunda yayi kankara a fridge. Sanda ya fito daga wanka, ta dauko mishi riga da wando marassa nauyi, sakawa yayi yana binta kitchen din. Bude-buden kulolin duk da yagani yakeyi, ko kallon shi Waheedah batayi ba, kifinta take gyarawa, tana jinshi ya karaso inda take, yana dora kanshi a kafadarta, ta baya. Ture shi tayi "Sai na saka maka karnin kifi ko?" Kankance mata idanuwanshi yayi "Ni kike ta sharewa ko Wahee? Yunwa nakeji, ki bani abinci, tun jiya banci komai ba" Kwandon da ta zuba kifin a ciki ta dauka ta dora cikin wani kwano, tana saka omo ta wanke hannuwanta da sink din wanke-wanken ma, tana son kifi, amman sosai karnin shi yake damunta, shisa duk abinda zatayi amfani dashi bata iya ajiyewa, saita wanke. Karamin towel ta dauka ta goge hannuwanta, sai lokacin ta kalli AbdulKadir sosai, daya biye mata, tun jiya da suna tare, yanzun idan ya tafi tana iya wata uku ko fiye da haka bata saka shi a idanuwanta ba, dan ma manhajar Imo data shigo, suna video call sosai, amman ba kamar dai yana kusa da ita ba. "Duk lokacin dana samu na ganinka yana da muhimmanci a wajena, kamun asarar kwana daya saboda bakajin maganata" Ta karasa tana hararshi, murmushi yayi yana fadin "Kin san wa kika aura Wahee, kinsanni" Kai ta jinjina mishi, ita kuwa ta san shi fiye da kowa da yake da kusanci dashi, wucewa tayi ta gaban shi tana fita daga kitchen din "Da gaske yunwa nake ji, Allah banci komai ba" Wannan karin ita tayi dariya, har mamakin yanda yake rayuwa a matsayin soja takeyi, da wajajen da ya shiga, da wanda tasan zai shiga anan gaba. In yana bata wasu labaran, takan tambayeshi ya yakeyi da abinci. Dan daga mata kafadu yakan yi 'Tunanin ko zan sake ganinku, ko zan sake samun damar rike ki a jikina baya barina yin wani tunanin, Hajja kan zo mun a rai, amman tana da wasu yaran, rashina zai mata sauqi duk idan ta kalle su, bana son barinki, tunanin yanda zakiyi yana sani jure komai, ciki harda rashin abinci ko na tsayin kwanaki nawa' Ranar farko daya fada mata hakan, kasa magana tayi, sake shigewa jikin shi tayi, tana kokarin mayar da hawayen da suke cike da idanuwanta, banda nemawa kanta sauqin mutuwa da kariya daga azabar kabari, ta manta ranar karshe da tayiwa kanta wata addu'a, dukkan sujjadarta cike take da neman Allah ya tsare mata mijinta. Matan sojoji ne kawai zasu iya fahimtar wannan fargabar da take ciki a duk ranar da baya kusa da ita, ko bata ji muryar shi ba, ko ta nemi wayarshi bata shiga. Zuwa yanzun zata iya cewa sai zazzabi yayi da gaske yake kwantar da ita, dan sunyi wani irin sabo na ban mamaki. Wajen cin abincin ta, sai dai ta janye kujerun ta goge, ta kakkabe su, inba randa tayi baqi ba. AbdulKadir ba so yake takai mishi abinci can ba, yafi so ya zauna a kan kafet, harya saba mata itama, ko baya nan kan kafet take zama taci abincin ta. Yanzun ma ta riga ta fito da kulolin da flask din shayi. Saida ya zauna tukunna yace mata "Ina yaro na?" Numfashi ta sauke, tana zama itama "Hamma Yassar ya dauke shi tun jiya" Daquna mata fuska AbdulKadir yayi "Kinsan zan zo.... Me yasa zaki bar shi ya tafi dashi? Ni zanje in dauko yaro na" Bata ce mishi komai ba, dankalin da ta soya ta zuba

Chapter 20 of 37