kafin ta fice da sauri kamar zata fadi, saida ya tura kofar tukunna
wata irin dariya ta kwace mishi, yana mamakin yanda Waheedah ta kasance mai hankali kuma
marar hankali duk a lokaci daya. Hannu yasa ya shafi tabon da haukanta yake mata tunanin na
bindiga ne.
"Wai yaqi..."
Ya fadi yana karayin dariya
"Wallahi Waheedah bata da hankali... Yaqi fa"
Abdulkadir din yake maimaitawa har lokacin yana dariyar da yakejin fitowarta tun daga zuciyar
shi. Abincin shi ya karasa cinyewa tas yasha ruwa, tukunna ya ajiye farantin a kasa, gani yai
uku da kusan rabi, hakan yasa shi mikewa ya kwance takalman kafar shi, tukunna ya shiga
bandaki dan ya dauro alwala, fuskar shi ya kalla a mudubi, murmushin da yake bayyane a
jikinta nasa shi janye idanuwan shi daga kan mudubin, dan yanayine da ya zame mishi baqo, ya
kwana biyu baiyi nishadi irin nayau ba. Tsintar kanshi yai da murmushin har ya idar da alwala ya
fito, waje ya samu ya zauna yana jira a kira sallah dan ya wuce masallaci.
*
Dinner zasuyi da daren ranar, duk da Abba ya nuna duk wannan bidi'ar bason ta yakeyi ba,
haka ya hakura ya kyalesu ganin sun kafe. Dogayen riguna ne sukai anko iya su yan cikin
gidan, material din wine color, yayi matuqar kyau. Mami tai ma Nuriyya ankon da duk sauran
dinkunan da taima Waheedah. Yanzun ma tare duk suka fito da za'a tafi, yanayin dinkin ya
zauna ma Nuriyya sosai, da wahala ta gitta baka sake kallonta ba, ko dan kwalliyat data sha,
kusan duka yan gidansu Waheedah din Nuriyya tai musu kwalliyar su, ga kunshi ansha, kamar
sune amaren. Nuriyya ta rataya mayafinta a kafada, yanda su Zahra ma sukayi.
Itakam Waheedah fuskarta fayau take, banda hoda data murza sai Vaseline data shafa ma
labbanta, daurin dankwalinta ma mai sauqi tayi, saidai kalar kayan ta amshi farar fatarta, ta yafa
qaton mayafinta a kafadunta duka biyun, duk da haka wani iri takeji, wuyanta da yake a bude,
itakam wannan mayafin asarar kudine, dan tasan ana gama bikin zata ajiye shi, tafi gane
hijabanta. Motar da za'a dauke su ciki ta cika tsaf, bata samu waje ba.
"Yanzun dan Allah saiku tafi kubarni?"
Waheedah ta fadi cikin sanyin murya, tana dorawa da
"Nuriyya dan Allah ki rungumeni..."
Dariya Nuriyya tayi
"Ki yamutsemun riga? Wallahi bazai yiwu ba"
Sake marairaicewa Waheedah tayi
"Toni ki tashi in rungumeki"
Maryam, yar yayan Abba dake zaune gefen Nuriyya ta kwashe da dariya.
"A wacce cinyar zaki rungumeta? Mansur muje dan Allah..."
Maryam ta karashe maganar tana miqa hannu ta ja murfin motar dan taga alamar in suka
biyema Waheedah zasu kara bata lokaci, ba zata rasa wanda zata biyo ya kawota ba. Kuma
za'a daddawo daukar sauran mutane dole daman. Waheedah din kanta tasan hakan, kawai dai
taso ta bisu dinne tunda duk sa'anninta na cikin motar, ga Nuriyya kuma, kafin dai ta gama
sanyin jiki duk sun shige, tsaye tayi a wajen tana jin idanuwanta sun cika da hawaye.
"Waheedah ke baki tafi ba?"
Taji muryar Yazid, juyowa tayi, kwalla cike da idanuwanta
"Wai ba waje..."
Dariya Yazid yayi, yarinyar bata da wahalar kuka ya kula, sai dai akwai wani abu tattare da
sanyin halinta da yake ji har kasan zuciyar shi.
"Yanzun Abdulkadir zai fito, saiku wuce tare...ina zuwa zanyi abu"
Yazid ya karasa yana wucewa da sauri, aikam Abdulkadir dinne ya fito, jikin shi da shadda
ruwan toka mai cizawa, ta manta ranar karshe data ganshi da manyan kaya, sosai taga yai
mata kyawun da taji yasa zuciyarta ta matse waje daya. Sai kamshi yake zabgawa, hular da
take hannun shi ya saka saman kan shi yana karasowa inda take, ya miqa mata wallet din shi
da agogo yana da links din hannuwan rigar
"Riqe mun..."
Hannuwanta biyu ta ware mishi ya saka a ciki, yana daukar link guda daya ya fara sakawa a
jikin hannun rigar yana zabga tsaki
"Meyasa Hamma zaimun wannan hannun shirmen?"
Da sauri Waheedah tace
"Kawo in sa maka?"
Kananun idanuwan shi ya kara kankance mata
"Kin iya?"
Kai ta daga mishi, kayan hannunta ya karba, yana miqa mata dayan hannun shi, kamawa tayi
tana dan rausayar da kanta gefe
"Saika dago hannun ka"
Ta fadi a hankali, gyara mata hannun Abdulkadir yayi yana kallon yanda ta nutsu tana saka
mishi link din, sai yaga kamar tafi dazun yi mishi haske, ko dan kwan fitilar da ya haske mata
fuskane, bai sani ba.
"Dayan hannun..."
Cewar Waheedah tana jin wani gajimare na mata yawo a kanta. Miqa mata Abdulkadir yayi
yana ware mata tafin hannun shi ta dauki link din. Saka mishi tayi, sai ya tsinci kanshi da miqa
mata agogon, karba tayi ta daura mishi, wallet din ya miqa mata, yasan yana da aljihu a wando
da rigar kayan da suke jikin shi, kawai yanajin bata ta riqe mishi ne.
"Kin shirya? Muje?"
Ya tambaya, tana daga mishi kai, harya numfasa yai mata maganar ta bude bakinta ta amsa
shi, saiya tuna Waheedah ce, ta saba amsa mishi magana da kai, saboda shiya saba kyaleta
duk idan tayi. Wucewa kawai yayi tana bin bayan shi, saida suka karasa tukunna taga dayar
motar Abba ce zasu fita a ciki, zagayawa Abdulkadir yayi yana bude motar ya shiga, harya
kunna baiga alamar Waheedah zata shigo ba, numfashi ya sauke yana rasa kalar Waheedah,
kafin ya miqa hannu ta ciki ya bude kofar, yana ganin tayi baya tana murza hannunta da alamar
ya bugeta.
"Sai nace ki shigo?"
Ya bukata a fadace, yanajin gajiyar da baisan daga inda ta fito ba. Idanuwanta take ware mishi,
dan taji ba cayai ta shiga din ba, tambayar ta yayi, kai ta girgiza mishi a hankali, da alama tana
jiran ya bata umarni ta shiga din tukunna, numfashi ya sake saukewa a karo na farko, bayajin
zai iya masifa
"Shigo Waheedah..."
Ya fadi da gajiya a muryarshi, shigowar tayi, tana rufe murfin kofar, tana jin yanda kamshin da
yake ya cika motar...!
*#TeamAbdulKadir*
*#TeamWaheedah*
*TeamNuriyya*
*#AnaTare*7/27, 1:13 PM] +234 816 124 4732: ©️
📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
08
Idan akwai abinda yakeyi a nutse a rayuwar shi bai wuce tuqi ba, ko Yassar daya koya mishi
tuqin idan zasuje wani waje yakan ce mishi
'Abdulkadir kana taka mota kaman zata cijeka. Dan Allah ka kara gudu'
Shikam baiga saurin da yake ba. Yanzun ma a nutse yake tuqin shi, kamar yanada duka lokacin
da yake bukata. Waheedah kuwa ta nutsu a gefe tana wasa da wallet din shi da take hannunta,
zuciyarta na doka mata a kirjinta kamar zata fito waje. Ga shirun da yake cikin motar da take jin
kaurin shi kamar tasa hannu ta dangwalo yai mata yawa. Rasa abin yi yasata balle maballin da
yake jikin wallet din tana wasa dashi.
"In kika lalata mun saina zane jikin ki"
Abdulkadir yai maganar hankalin shi nakan tuqin da yakeyi, dan yanajin yanda maballin yake
bas bas duk idan ta bude ta sake rufewa, yasan wasa take dashi. Badan ba zaiyi abinda yace
din ba, ya zaneta tasan ba wani abu bane, ba zai zama ma farko ba, bata dai san dalilin da
yasa maganar shi ta bata dariya ba.
"Na zama sa'anki ko?"
Ya buqata jin sautin dariyarta, bata amsa ba, bai kalleta ba kuma har lokacin, amman yasan kai
take girgiza mishi. Bata mayar da maballin jikin wallet din ba, hakan yasata budewa tana sa
hannu ta shafa wajen da taga alamar I.D card dinshi ne, hannu tasa ta janyo tana kokarin ganin
hoton da yake jiki, sai lokacin Abdulkadir yadan juya ya kalleta, yana mayar da hankalin kan
tuqin da yakeyi, yaga yanda take daga I.D card din wajen gilas din kofar dan tagani, hannu ya
miqa ya kunna fitilar dake cikin motar yana sata rufe idanuwanta ta sake budesu da wani yanayi
dayake nuna bata tsammaci hasken daya gauraye gaban motar ba.
Tukunna ta kalli Abdulkadir din da idanuwan shi suke kafe kan titi, numfashin da batasan dalilin
shi ba ta sauke tana mayar da hankalinta kan ID card din da yake hannunta taci gaba da
dubawa, dan yatsanta babba na shafa kan hoton shi da yake manne a gefe. Mayar mishi da ID
card din zatayi wajen data ciro shi taga dan qaramin hoto a wajen tasa hannu ta zaro tana
karema hoton da alamu suka nuna bai jima da daukar shi ba, dan askin da yake kanshi yanzun
shine a jikin hoton. Wani abu dayai mata tsaye a makoshinta take kokarin hadiye wa amman
yaki tafiya
"Hamma..."
Ta kira muryarta can kasan makoshi, saida tai tunanin bazai amsa ba tukunna yace
"Menene?"
Dan yaji ta kira sunan shi, bai amsa bane yana jiran taci gaba da magana, jin tayi shiru yasa shi
amsawa, yasan zasu iya kaiwa inda zasu kai batai maganar ba tana jiran saiya amsa ta. Dan
gyara zamanta tayi tana kallon Abdulkadir din, gudun zuciyarta na karuwa da tambayar da take
shirin yi mishi, kafin ta tattaro duk wani kwarin gwiwar da zata iya tace
"In dauka?"
Dan daquna fuska yayi duk da bai kalleta ba, yanayin nasa idanuwan shi qara kankancewa
"Meye?"
Numfashi taja a hankali tana sauke shi da fadin
"Wannan hoton?"
Sake rage gudun motar yayi yana dan kallon hoton da ta nuna mishi, dan yasan akwai qananun
hotuna da yawa a cikin wallet din tashi, baisan kowanne take cewa ta dauka ba, hoton ya kalla,
da alamu a kafadarshi da yake nuna yana therma III yanzun a NDA, hoton bai dade ba, kafin ya
taho din nan ne ya dauka, shine hoton shi na karshe dayai zuwa yanzun. Fuskar shi har lokacin
a daqune take, kan titi ya mayar da hankalin shi yana kara gudun motar yanda yake da kafin ya
rage. Ba tambayarta bace ta bashi mamaki, baiga me zatayi da passport din shi bane ba, hoton
dako kyau baiyi ba.
Zuciyarta take ji ta dawo makoshi saboda gudun da take, amsar shi take jira, in yace karta
dauka zata mayar ta ajiye mishi, tun da daga farko ma batasan meyasa ta tambaye shi ta dauka
din ba, ta ciro hoton kuma taji tana son kasancewa dashi, tana son samun wani abu daga wajen
shi kafin ya sake tafiya, tunda ba ranar dawowa gare shi ba. Wani abu da zai riqeta harya sake
dawowa. Batasan kalaman da zatai amfani dasu su fassara dalilinta ba, kusan hakan dai shine
abinda take ji.
"Kaji Hamma... In dauka?"
Ta tsinci kanta da sake fadi, dan daga mata kafada Abdulkadir yayi yana juya steering wheel din
ya sha round din dake gaban shi, jitai wani abu na narkewa a zuciyarta da batasan akwai shi
ba, yanayin shi da abinda yai da kafada nasa numfashin ta yi mata barazana. Dakyar ta iya
cewa
"In dauka?"
Wannan karin Abdulkadir dinne ya sauke numfashi
"Komai ne sai nayi surutu?"
Dan murmushi tayi
"Baka ce in dauka ba ai...haka kayi da kafadun ka"
Ta karasa tana daga nata cikin son nuna yanda yai da nashin. Kai kawai Abdulkadir ya girgiza
dan sun karaso wajen da Yazid din yai mishi kwatance za'ayi dinner. Baiyi tunanin zai gane ba,
sai dai yawon da suke sha a garin Kano ba dan kadan bane ba. Waje ya samu yayi parking
yana bude motar ya fice. Hoton Waheedah ta mayar inda ta dauko shi, tukunna ta bude murfin
motar itama tana ficewa. Sai da yaga ta fito tukunna ya rufe motar ya soma tafiya, bin bayan shi
Waheedah tayi dan gani tai yana sauri sosai
"Kaji Hamma, in dauka?"
Take fadi tana mayar da numfashin daya sashi juyawa ya kalleta, sauri take kamar zata fadi
tana kai hannu daya ta dafe mayafin dake jikinta, dayan riqe da wallet dinshi tana kokarin
tattare doguwar rigarta ko zata kara sauri, juyawa yayi yanajin murmushi na shirin kwace mishi,
bai taba ganin kalar Waheedah ba, baisan meyasa yaji yana so ya kure rashin hankalinta ba.
Sauri ya kara yana bi ta duk inda yaga turmutsun jama'a duk da ga hanya nan dazai iya
wucewa, sai da yai wajen mintina biyar a hakan har yana hango kofar wajen tukunna ya tsaya
yana juyawa, hangota yai can cikin jama'a an matse ta, sai kokarin turmutsowa take da
hannuwanta da suke mishi kama da sandar siririn rake.
Murmushin da yake ta dannewa ne ya kwace mishi, kai ya girgiza
"Wallahi yarinyar nan bata da hankali..."
Abdulkadir ya fadi yanajin nishadin da ya rasa daga inda yake fitowa, komawa yayi baya dan
yaga alamar mutane na gab da ture Waheedah ta fadi kasa, in wani ya takata yana da tabbacin
karyewa zatai bal, hannunta ya kama yana janta, banda maida numfashi babu abinda takeyi,
hanyar da babu mutane yabi da ita, dakyar take tafiya saboda batasan wahala irin wannan a
rayuwarta, dakyar ta iya cewa
"Hamma sauri kake kamar zaka tashi sama wallahi...."
Dariya yaji ta kubce mishi
"Lalaci ne yai miki yawa"
Ya fadi yana ci gaba da janta, binshi take da duk saurin da zata iya har suka shiga wajen daya
qawatu babu laifi tukunna Abdulkadir din ya rage saurin da yakeyi yana sakin hannunta,
numfashi ta mayar tana fifita fuskarta da wallet din shi saboda zufar wahalar da take jin tanayi.
Kankance idanuwan shi yayi a kanta, kafin ya mayar da hankalin shi kan harabar wajen yana
nemo tebir din da yaga babu kowa da kuma kujerar mutum hudu tukunna yaja hannun
Waheedah batare daya damu da mutanen dake binsu da kallo ba suka karasa wajen, kujera
daya yadan ja baya yana jan hannunta ya zagaya da ita, zama tayi dan tagaji kam.
Ta gefenta Abdulkadir ya zagaya ya zauna yana kallon yanda take mayar da numfashi.
Hannunta Waheedah ta sauke kasan tebir din tana murzawa da dayan, tana jin kamaf
Abdulkadir yabar mata shatin nashi hannun a wajen da yanayin dayai mata tsaye a zuciya.
"Bakace in dauka bafa"
Ta fadi tana kallon Abdulkadir daya dauki robar ruwan da take ajiye a wajen yana murzawa da
nufin budewa da alama. Kananun idanuwan shi ya kafeta dasu da yasata sauke nata idanuwan,
zuciyarta naci gaba da tsalle a cikin kirjinta. Ruwan shi Abdulkadir ya kwance, yana son ganin
yanda tsoro kan cika idanuwanta, kai robar yai bakin shi yana shan ruwan sosai tukunna ya
mika robar kusa da Waheedah yana fadin
"Ki sha ruwa..."
Hannu tasa ta dauki robar ta cire murfin dabai daure ba sosai tana kaiwa bakinta ta kurbi ruwan
tukunna ta mayar ta rufe, ba kishi take ji ba, tasha ne kawai dan yace tasha, dan shine ya bata
bazata iya ce mishi batajin kishi ba. A hankali ta ajiye robar tana soma kalle-kalle ko zata hango
su Nuriyya. Amman ko alamun su bata gani ba. Yazid ne ya karaso wajen yana jan kujera ya
zauna hadi da fadin
"Kai jama'a, wallahi jikina ciwo yake mun"
Kallon shi Waheedah tayi cike da tausayawa, abinda yafi ciwon jiki ma tasan zaiyi, tunda
hidimar bikin ta fara shi yake zirga-zirga. Cikin sanyin muryarta tace
"Sannu... Kaine baka huta ba ai Hamma..."
Murmushi yayi yana sauke idanuwan shi akanta, tun dazun ya kula da yanayin fuskarta kafin su
taho, baisan lokacin da abinda yake ji ya fara ba, kawai ta gitta ta gaban shi ya tsinci zuciyar shi
da doka mata. Tunda yazo wajen yake cin karo da yan mata kala daban-daban, dukkan su
fuskokinsu dauke suke da kwalliya taban mamaki. Yanda tata take fayau ya mishi, lokaci zuwa
lokaci taken sake gyara zaman mayafinta a kafadarta, ya kula da a takure take jinta saboda
rashin hijab dinta
"Me yasa baki saka hijab ba?"
Ya bukata, bayason ganin yanda take a takure, dan murmushi tai mishi cikin yanayin sanyinta,
baisan koshi kadai yake ganin kyanta ba, da dan bakinta da yasan mata da yawa zasu shafa
abubuwa da dama dan kalar labbansu tayi ruwan hoda haka kamar nata, idanuwanta sunfi
komai daukar hankalin shi a fuskarta, yanda suke maiqo kamar da hawaye a cikin su koda
yaushe kan saka shi murmushi koshi kadai ne.
"Su Zahra zasu dameni"
Kai Yazid ya jinjina
"Ki daina yin abinda zaki takura saboda mutane..."
Kai Waheedah ta rausayar gefe, bazai fahimta ba, bata takura kanta bane saboda su, idan ta
saka hijab din yanda zasu takurata zaifi yanda take a takure yanzun, ta zabi abinda yafi mata
sauqi ne kawai. Abdulkadir hankalin shi ya mayar kan hidimar da ake wajen dinner din, ganin
hirar Yazid din da Waheedah ta fara dakushe mishi nishadin da yake ciki.
*
Dan mudubin da ta saka a cikin yar jakar hannunta ta dauko tana saka shi ta karkashin teburin
wajen ta duba fuskarta, kowa yace mata tayi kyau, daga yan gidansu Waheedah zuwa abokan
wasan su da suka zo bikin, sai dai kamar koda yaushe akwai murya a kasan ranta da take fada
mata kyawunta bai kaiba, kyawunta bazai tana isa ba, kamar yanda bazai cike mata gurbin
abubuwa da yawa da bata dashi a rayuwarta ba. Ta jima tana tsara kwalliyarta yau, amman
Waheedah na fitowa saita raina duk wani kyau da take tunanin tayi. Batasan menene a tattare
da fuskar Waheedah din dako hodar kirki bataji ba.
Tana da tabbacin ba ita kadai take ganin wani sanyi da yake cikin idanuwan Waheedah a koda
yaushe ba, yau dinma batare da wani yunkuri ba taga Waheedah din tayi kyau, da pink lips
dinta da take jin kamar ta cire ta mayar a tata fuskar, duk da inta kalli yanda zubin kirarta yake
takan ji sanyi ta wani fannin, duk kyan Waheedah da hasken fatarta ba zata nuna mata dirin jiki
ba, duk da itama a sirantakarta Allah yai mata wadattacen cikar kirji da Nuriyya take jin bai
kamace taba, yanda take siririya yakamata komai nata ya zamana a shafe, ta fito a asalin
zanen lamba dayanta.
Tunda suka zo takan tashi ta yawata a cikin wajen ko zata ga Waheedah din, amman ko
alamunta bata gani ba, yanzun ma zagayawar take tana dube-dube, kafin idanuwanta su sauka
kan Waheedah din da take murmushi cikin yanayin da yakan kara mata kyau. Karamin tsaki
Nuriyya taja, tana jin wani daci har a kasan zuciyarta da batasan daga inda yake taso mata ba.
A hankali take karasawa, idanuwan mazan duk data gitta yana kanta, amman ko kadan bata
kula dasu ba, gabaki daya hankalinta yana kan Waheedah da Yazid da alamu ya nuna hira
sukeyi, akwai wani namijin tare dasu da batasan kowaye ba, saboda ya bata baya.
Takawa tayi harta karasa inda teburin yake tana fadin
"Inata neman ki tun dazun"
Saukar maganar Abdulkadir yaji saman kanshi, dan a bayan shi Nuriyya ta tsaya, gyara zaman
shi yayi tukunna ya juya a hankali dan yaga wacce marar tunanin ce take mishi magana
tsakiyar kai, batare dako sallama tayi musu na ballantana ta gaishe su tukunna tai maganar da
zatayi, idanuwan shi ya fara saukewa kan fuskarta, kafin ya kankance su yana kare mata kallo,
wani abu yake ji yana dokawa cikin kunnuwan shi daya rasa daga inda yake jin sautin shi, dan
bashida alaqa ko kadan da kidan da yake tashi a wajen.
Zai karya idan yace bai manta da wata Nuriyya a shekarun nan ba, saurarawa yayi dan gane
inda yake jiyo sautin, kafin yagane zuciya shi ce take dokawa a kirjin shi, alaqanta hakan yake
da mamakin girman da yarinyar tayi.
"Baki iya sallama ba?"
Abdulkadir ya fadi har lokacin yana rasa dalilin da zaisa zuciyar shi ba zata daina bugawar da
take ba. Ware idanuwanta Nuriyya take akan Abdulkadir din, batasan yazo ba, Waheedah
batace mata yazo ba, duk da a shekarun nan biyu daya tafi, ta tabbatar babu wanda Waheedah
take damu da zancen shi idan ba ita ba. Bata taba ganin shi cikin manyan kaya ba tunda take,
ba tun yanzun yake mata kyau ba, hankalin data kara yasa kyawun nashi bayannar mata sosai
yanzun. Gashi yayi wani irin girma.
"Hamma..."
Nuriyya ta fadi tana murmushin da Abdulkadir din yaji zuciyarshi ta kara gudun dokawar da
take.
'Tana da kyau'
Wata murya ta fada a cikin kanshi. Sake kankance idanuwan shi yayi kamar zata iya karantar
abinda yake tunanin akan fuskar shi, idan akwai abinda ya tsana a rayuwar shi bai wuce raini
ba, yara kuma a shekarun su Nuriyya sukafi jin tashen raini, saboda kuruciyar girma na dibarsu,
shi bai saba yima kanshi karya bane kawai, yaga tana da kyau, ya kuma yi acknowledging kyan
nata a ranshi.
"Sannu da dawowa"
Nuriyya ta fadi tana shirin dorawa da
'Yaushe kazo'
Yanda Abdulkadir din ya daure fuska ya hanata fito da maganar a fili, juyawa yayi batare daya
amsa Nuriyyar ba hadi da gyara zaman shi, tukunna kamar an mishi dole yace
"Yawwa"
Wani abu Nuriyya taji ya tsaya mata a makoshi, har ranta taji dadin ganin nashi, ya tuna mata
yanda yake mata kyau naban mamaki, a lokaci daya kuma ya tuna mata yanda daga kawar
Waheedah da suke gaisawa kan dole bata wuce nan ba, bakuma zata taba wuce nan ba,
batasan meyasa yanayin yai mata ciwo na gaske ba. Waheedah kuma Abdulkadir din take
kallo, yanayin shi na nuna alamar gajiyar da yai da zaman wajen.
Inda idanuwan Waheedah suke Yazid yabi da kallo, kafin ya sake mayar da kallon shi kan
fuskarta, yana runtsa idanuwan shi ya bude su hadi da kauda tunanin da yake shirin dirar mishi
'Duka nawa Waheedah din take'
Ya fadi a ranshi yana mikewa
"Ina zaka je? Yanzun fa kake fadin kagaji"
Waheedah tai maganar tana dauke idanuwanta daga kan Abdulkadir din
"Zan huta Waheedah...bari inzo"
Yazid ya karasa dan yaga ba'a fara rarraba abin ci a wajen ba, dare nayi, sunce kuma ba zasu
jima ba sosai, ya kamata ayi abinda za'ayi a tashi kowa ya kama gabanshi.
"Wai ta ina kuka zauna, nima inata duba ku"
Waheedah ta tambaya, hararta Nuriyya tayi tana matsawa ta zauna inda Yazid ya tashi taja
kujerar kusa da Waheedah sosai, dai-dai kunnenta tace
"Ko ko fadamun Hamma ya dawo"
Dan murmushi Waheedah din tayi, muryarta can kasa ta amsa Nuriyyar
"Bamu zauna bane shisa, kuma dawowar bazata yayi"
Dan tabe baki Nuriyya tayi, kamar rashin zaman su na hana Waheedah din mata zancen
Abdulkadir, ba tun yanzun tagane Waheedah nason Abdulkadir din ba, ita daice har yanzun
take son raina mata hankali kamar yanda ta saba, take nuna kamar bata san abinda take ji
akan Abdulkadir din so bane. Ko dan tasan ba samun shi zatayi ba shisa take son nuna kamar
batasan tana sonshi ba oho. Duk idan Nuriyya tai wannan tunanin takanji sanyi a ranta, a karo
na farko Waheedah bata samu abinda take so ba, wannan karin itama zataji yanda zafin rashin
samun komai da kake so yake.
Abdulkadir zaice ya kwana biyu wani abu bai gwada karfin halin shi irin yau ba, kokawa yake da
idanuwan shi karsu kalli inda Nuriyya take zaune amman hakan na neman gagarar shi. Ita
kanta Nuriyyan ta kasan idanuwanta take kare mishi kallo tana ganin yanda fuskarshi take a
daqune babu alamar wasa ko kadan akanta. Zungurin Waheedah tayi da alamar su tashi subar
wajen. Dan kallon Abdulkadir tayi itama, tana son zama dashi din ko ba zasuyi magana ba, tana
kuma son zagayawa ta zauna cikin su Zahra dan nan ne kawai zatafi more bikin, wannan ne
karonta na farko da ta taba zuwa wata hidimar biki.
Duk da anayi a dangin Abbah sosai, su Amatullah kanje harsu kwana, ita kam tana zama gida,
duk da ko a fuska babu wanda ya taba nuna mata banbanci, kawai dai hayaniyar ce bata cika
so ba. Mikewa Nuriyya tayi tana kara taba kafadar Waheedah din data mike itama, hakan naba
Abdulkadir damar da yake nema ta kallon su biyun, sai dai idanuwan shi nakan Waheedah.
"Zamuje wajen su Amatu..."
Ta fadi tana kallon shi, kai Abdulkadir ya girgiza mata yana fadin
"Idan na tashi tafiya wallet dina fa?"
Sai lokacin Waheedah ma ta tuna wallet din shice a hannunta, bin hannun nata da kallo Nuriyya
tayi wani abu na tokare mata kahon zuciya dan alamu sun nuna tare suka zo da Abdulkadir din.
'Allah ya rabaki da naci Waheedah'
Nuriyya ta fadi kasan zuciyarta. Wallet din Waheedah take shirin mika mishi, yanda ya kafeta da
kananun idanuwan shi nasata kasa motsa hannunta, kallonta Abdulkadir yake har saida ta
koma ta zauna. Baisan dalilin shi na hanata tafiya ba, kawai yanda yakejin zuciyarshi na
dokawa har lokacin cikin bakon yanayin daya kasa fahimta yasa bayason ya zauna shi kadai.
Ganin ta Waheedah ta koma ta zauna yasa Nuriyya din fara shirin zama itama.
"Ki wuce inda zakije"
Abdulkadir ya fadi yana watsa mata wani kallo dayasa ta barin wajen batare data ko yima
Waheedah sallama ba, ta tsorata sosai, ranta kuma inyai dubu ya gama baci, meyasa zaima
Waheedah magana kamar tana da muhimmanci a wajen shi, ita kuma yai mata magana kamar
ita din bakomai bace, yana nuna kamar Waheedah yar uwarshi ce, bayan babu wanda baisan
agola bace a gidan nasu, itama din bakomai bace a wajen shi. Harta koma inda ta fito ta zauna
ranta a bace take jinshi, bikin gabaki daya yagama fita daga ranta.
*
Numfashi Abdulkadir ya sauke da barin Nuriyya wajen, gabaki daya abinda yakeji baqone a
wajen shi, bakuma zai yiwu yar mitsitsiyar yarinya kamar Nuriyya ta saka zuciyarshi wannan
gudun ba, kawai dan tana da kyau. Baya son raini, komai tattare da Nuriyya na nuna mishi idan
ta samu fuska zata raina shi.
"Sai muzo tare ki tafi kibarni..."
Yai maganar yana kallonta, a lokaci daya yana rasa yanda akai ita kadai take ganin bangaren
shi haka, yanda yakejin ita kadai zai iya nuna ma bangaren shi haka batare da tunanin zata
raina shi ba. Dan kallon shi Waheedah tayi tana sauke idanuwan ta dan akwai wani abu tattare
da nashi idanuwan da yake karya duk wata garkuwa ta jikinta, komai tattare da Abdulkadir
daban take ganin shi. Batasan me zatace mishi ba, dan haka shiru tayi kawai tana lafewa cikin
kujerar da take zaune a wajen.
Abinci aka kawo aka ajiye kan teburin da suke zaune, abincine wajen kala uku a cikin faranti
daya, sai tsire a tsinke, harda hadin salad a gefe, a koshe
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 37