mata. AbdulKadir ya gama sakata a kunya, batasan
ya zata fara hada idanuwa dasu Anty Ramatu ba yanzun, sosai taji dadin zuwan Anty Talatu
wajen dan a kasan zuciyarta take jin yanda AbdulKadir yake gab da tsulama Anty Ramatun
rashin kunya. Tana nan tsaye kanta a kasa harya bude mata murfin motar, alkyabbar jikinta ta
tattara tukunna ta shiga, zama tayi ta rufe murfin motar tana wasa da yatsun hannunta da ta
ajiye kan kafafuwanta.
Bai mata magana ba shima, motar yaja suna kama hanyar gida. Zai iya rantsewa da duk wani
abu na jikinshi harta gashin dake bayan wuyanshi yana sane da zamanta a gefen shi. Fuskarta
yake son gani ko yayane, amman hular alkyabbarta ta kare mishi. Ko kunshinta baigani ba
sosai, ta turo mishi hotunan da tace ana mata, amman da aka gama baigani ba, yaita jira ko
zata tura mishi amman shiru, sai bai tambayeta ba tunda zaizo yagani da kanshi. A nutse yake
tukin har suka karasa gida sannan ya samu waje cikin harabar gidan yayi parking.
Fitilar dake cikin motar ya kunna haske na gauraye su. Gyara zaman shi yayi yana kai hannu
yaja hular alkyabbarta yana sauketa daga saman kan nata. Hakan yasa Waheedah da tayi zurfi
cikin tunanin da ba zatace gashi ba ta juyo tana sauke mishi manyan idanuwanta da kwalliyar
da akai musu ta saka su kara girma. Wani irin numfashi AbdulKadir ya tsinci kanshi da ja yana
furzawarwa hadi da yawata idanuwan shi akan fuskarta da tayi mishi kamar ba tata ba. A
hankali yake jin bugun zuciyarshi na karuwa musamman data motsa labbanta da yake komai
dan ganin baisaka yatsan shi akai yaji ko janbakinta nada maikon da yake gani marar walqiya
ko kuma idanuwan shine suke haska mishi hakan.
"Hamma..."
Ta kira cikin sanyin muryarta da yaji ya saukar mishi da wata kasala taban mamaki.
"Me yasa kika kashe wayarki? Kinsan zan kira meyasa kika kashe?"
Maganar tashi ta fito a matsayin tsegumi maimakon fadan da yayi niyya, ta gama kashe mishi
duk wani fada da yakeji, kanshi ya jingina jikin kujerar motar yana kar kankance mata
idanuwanshi
"Banda chargy ne shisa, wayar mutuwa tayi..."
Waheedah ta fadi tana kallon yanda shaddar jikin shi tai matukar karbar kalar fatarshi.
"Kayan nan sun maka kyau"
Ta tsinci kanta da furtawa tana sakashi dakuna mata fuska
"Nama kayan kyau dai..."
Dariya tayi da ta saka shi runtsa idanuwanshi yana budesu akanta, wani irin kyau tai mishi da
bai taba sanin tana dashi ba. Kamar kullum ya dinga ganin fuskarta dauke da kwalliya haka.
Har shigar mishi ido da haskenta yakeyi yau ya nema ya rasa, farin nata yaji yayi mishi dai-dai.
"Kinyi sallah?"
Ya bukata yana kallonta har lokacin, kai ta girgiza mishi tana tuna mishi da yanda ita kadaice a
fadin rayuwarshi da take amsa mishi magana batare data bude bakinta ba, kuma ya karbi
amsar. Ita tunda aka fara hidimar bikin a dai-danta take. Ko zata samu tsarki sai zuwa
washegari.
"Zaki je kiyi saiki dawo? Lokaci na tafiya"
AbdulKadir ya sake fadi, dan sallah na daya daga cikin abubuwan da baya wasa dasu a
rayuwar shi, bakuma yabari duk wani makusancin shi yayi wasa da ita. Sai dai ga mamakin shi
kai ta sake girgiza mishi, tana saka shi fadin
"Me yasa?"
Cike da wata irin kunya da rabon da tajita a tsakaninsu ta manta ranar ta sauke idanuwanta
daga cikin nashi tana fadin
"Hamma mana..."
Dan ware idanuwanshi yayi cike da fahimta, da murmushi a fuskarshi yace
"Oh...okay... Nagane. Duk yau me kikaci?"
Ganin ta sake sadda kanta kasa yasa shi fadin
"Yau ma bakici komai ba Waheedah? Jiya bance kici wani abu ba? Meyasa bakici ba? Saboda
kin rainani ko? Ban isa in sakaki abu kiyi ba..."
Dagowa tayi ta kalli fuskarshi da take dauke da yanda rashin yake a bace
"Hamma..."
Ta kira cikin sanyin murya tanaso ya fahimci badan ta raina shi yasa bataci abinci ba, ba kuma
dan bataji yunwa bane ba, anata hidima ita basu bata abincin bane shisa, amman tasan halin
shi, idan tace ba'a bata abinci bane shisa bataci ba fadan karuwa zaiyi.
"Ki jirani ina zuwa..."
Yai maganar yana bude murfin motar ya fice. Gyara zamanta tayi sosai, tasan anacan ana
nemanta watakila, ba zata iya rikicin AbdulKadir ba da tace mishi zata shiga cikin gidan dan kar
a nemeta. Tana wannan tunanin AbdulKadir din ya dawo ya bude motar yana shigowa, robar
take away da abinci a ciki ya dora akan cinyarta yana gyara zamanshi cikin motar ya rufo
murfin, robar ruwan a jikinshi ya ajiyeta yana daukar robar dake jikin Waheedah ya bude ya
saka mata cokalin da bata kula yana hannun shiba a ciki, kamshin fried rice din da tasha kayan
hadi da nama ta daki hancinta tana kara mata yunwar da takeji.
Batare da tunanin komai ba tasa cokalin ta dibo abincin takai bakinta ta tauna, Lumshe idanuwa
tayi dan ya mata dadi na fitar hankali, batasan ko hakan nada alaka da yunwar da takeji ba,
hadiyewa tayi tana kara dibowa, yanda take cin abincin da sauri yasa AbdulKadir fadin
"Slow down, karki kware Waheedah..."
Kai ta girgiza mishi, tana hadiye abincin da yake bakinta
"Hamma yunwa nakeji sosai, banci komai bafa duk yau... Bazan kware ba"
Ta karasa maganar tana kai wani cokalin a bakinta. Sosai taci abincin dan kadan ta rage da taji
ta koshi har cikin makoshinta. Ruwan AbdulKadir ya kwance yana mika mata, ta karba kuwa
tana kaiwa bakinta. Yabi kunshin da yake hannunta da kallo. Ruwan data sauke ya karba yana
sha shima, makoshin shi ya bushe batare da dalili ba tunda ba kishi yakeji ba. Numfashi
Waheedah ta sauke wata nutsuwa na saukar mata, cokalin ta gyarama zama cikin robar ta rufe,
tana jin yanda AbdulKadir yake binta da idanuwa, kafin yasa hannu ya dauki robar abincin yana
dorawa gaban motar ya ajiye. Gyara zaman shi AbdulKadir yayi yana jingina da kujerar motar
sosai ya lumshe idanuwan shi.
"Hamma..."
Waheedah ta kira ganin kamar shirin bacci AbdulKadir din yakeyi a cikin motar.
"Karki dameni da surutu Waheedah, hutawa zanyi"
Ya fadi batare daya bude idanuwan shi ba, gabaki daya bayajin karfi a jikinshi, saida yai sallar
isha'i kafin ya karasa wajen kamun, amman bayajin shiga cikin gida ya kwanta a daki. Anan
cikin motar inda take yake son hutawa, kokawa yake da abinda keson dora koda kanshine a
jikinta yayi bacci, ba sai yayi tsayi ba, awa daya ma ya isheshi. Ba sosai yake samun bacci ba
tunda ya tafi, yanzun ganinta yasa duk wata gajiya da yake rike da ita saukar mishi. Ita kadaice
a rayuwarshi yake iya nunama kasawarshi ko gajiyarwar shi.
"Za'a nemeni Hamma..."
Waheedah tai maganar kamar zatai kuka, tana saka shi bude idanuwanshi ya duba agogon da
tun wanda ta sai mishine
"Karfe takwas da rabi, tara da rabi saiki tafi"
Duk da yayi maganar babu wajen musu bai hanata fadin
"Hamma tara da rabi"
Idanuwan shi ya sauke cikin nata
"Musu zamuyi dake?"
Ya bukata yana sata girgiza mishi kai.
"Good..."
Ya fadi ya gyara zaman shi cikin kujerar yana lumshe idanuwan shi.
"Ki zauna sosai"
Yai maganar batare daya bude idanuwan shi ba. Ita kam bataga ta zama sosai ba, awa daya
AbdulKadir yake son tayi a zaune cikin motar, badan batason zama dashi ba, har ranta awa
dayama yai mata kadan tare dashi, amman za'a nemeta tasani, da ba'a hidima ba zata damu
ba.
"Inajin sautin tunaninki har nan Waheedah...babu inda zakije kuma"
Shagwabe mishi fuska tayi duk da idanuwanshi a lumshe suke.
"To inje in dauko wayata?"
Ta bukata, ko wayar ta latsa kafin awa daya ta cika, zatafi mata sauri, hannu yasa a aljihunshi
yana zaro wayarshi ya mika mata, hannu tasa ta karba ganin idanuwan shi a lumshe suke.
"Waheedah"
Ya fadi yana sauke numfashi. Cike da rashin fahimtar kiran sunanta da yayi take kallon shi,
kamar yaji hakan yasa shi fadin
"Password din Waheedah"
Zuciyarta taji ta kumbura ta cika fam, sunanta ne mukullin sirrin wayarshi, dannawa tayi kuwa
taga wayar ta bude, murmushi tayi tana gyara zamanta, takasa daina murmushi, abinda
batasani ba shine kowanne abu nashi da yake bukatar mukullan sirri sunanta ne, hotunan shi ta
shiga tana dubawa, duk wanda tagani saita shiga WhatsApp dinta ta turawa kanta shi. Batasan
awa daya ta cika ba, batama san ya bude idanuwan shi ba, saida taji ya fisge wayar daga
hannunta yana fadin
"Me kike mun da waya..."
Yana dubawa, hotunanshi yagani ta tura ma kanta ta WhatsApp, yana da tabbacin gabaki daya
hotunanshi ne da suke cikin wayar. Kai kawai ya girgiza, da tace yabar mata wayar ma taje ta
tura ba saita karar mishi da data ba. Mukullin motar ya zare yana zagayawa ya bude mata,
fitowa tayi. Hamma yayi saboda bacci yakeji sosai
"Saida safe..."
Yace mata yana murza idanuwanshi cikin yanayin da yai mata kyau. Ganin ta tsaya tana kallon
shi yasa shi fadin
"Ko in rakaki?"
Da sauri ta girgiza mishi kai. Zata lallaba ta shiga bangaren Anty, inta dan jima anan saita koma
gida, ba saiya rakata kowa yasan tare suke ba. Juyawa ma tayi ko saida safe batai mishi ba,
kafin rikicin shi ya yanke mishi hukuncin rakata.
*
Washegari hidimar tafi hade musu, tun karfe bakwai aka gama musu kwalliya ita da Zahra, wata
doguwar rigace ruwan kwai, wuyan rigar dogone irin wanda ake kira high-neck a turance, sosai
ta karbi su duka biyun, daga daurin dankwalayensu zuwa yanayin lullubinsu zaka gane amare
ne ko baka kalli kunshin dake hannuwansu ba. A harabar gidan aka fito dasu dan ayi hotuna.
AbdulKadir yafi duka mazan dake wajen tsayi, shima yana sanye da shadda fara kal da babban
rigarta kamar sauran angwayen. Abin gwanin ban sha'awa, sosai akai musu hotuna, angwayen
da amarensu su kadai, su duka gabaki daya, sai kuma da sauran mutane da abokan arziqi.
Kasancewar daurin auren na karfe takwas ne, Zahra kanta ba a Kano zata zauna ba, Katsina
ne, ga Yazid da matarshi shima. Dan haka aka saka bikin da safe don ana dawowa za'a tafi da
amaren. Suna gama daukar hotunan, babban masallacin dake nan kofar ruwa inda za'a daura
auren suka dunguma suka nufa su dukkansu da abokan su. Ran AbdulKadir a bace yake, tun
da safe daya samu Hajja da tambayar
"Wai da gaske za'a kai Waheedah ne itama?"
Cikin rashin fahimta Hajja tace
"Bangane za'a kai Waheedah ba"
Dakuna mata fuska yayi
"Ina nufin rakiya... Yanda za'a raka Zahra har katsina, itama za'a rakata har Minna?"
Kai Hajja ta jinjina sai lokacin ta fahimci abinda yake fada
"Eh, Hajiya Talatu, Hajiya Aisha, Dadda, Da waye naji suna maganar, su bakwai daine zasu
rakata, saboda sauran zasu raka Zahra"
Girgizama Hajja kai yakeyi tunda ta fara magana, shi bayason wannan al'adar, a tsarin shi koda
na wani gari bane yazo da mota ya dauki matarshi su tafi, su Anty Talatun da take magana su
sukaje sukai jeren kaya har Minna din tun satin bikin. Hakan ma ya isa, Allah ya amfana ba sai
sun raka mishi mata ba, bayason wannan al'adar ko kadan
"Kice musu su zauna abinsu Hajja, nida ita kawai zamu tafi da na dawo daurin auren..."
Kallon shi Hajja take kamar bashida hankali
"Bangane me kake son cewa ba"
Numfasawa yayi
"Wani rakiyar amarya nake magana... Ni banaso... Su zauna"
Wata dariyar takaici mai sauti da bata da alaka da nishadi Hajja tayi, tana sa AbdulKadir fadin
"Koni in gaya musu suyi zamansu?"
Cike da takaicin da ta kwana biyu bataji irin shi ba take kallon AbdulKadir din
"Wallahi idan baka bacemun daga nan ba saina kwasheka da mari..."
Kallonta AbdulKadir din yakeyi shima
"Mari fa Hajja...me nayi ni? Me nayi?"
Yake tambaya yana son sanin dalilin da Hajja zatace zata mare shi dan ya fadi ra'ayin shi, yaga
kirkine shi su Anty Talatun zasuyiwa, kuma yace bayaso ba sai ayi abinda yace ba tunda matar
tashi ce.
"Saina marekan zaka barmun daki ko?"
Dakuna fuska yayi
"Ai bansan me nayi bane ba... In fada musu zan dauki matata ko zaki fada musu"
Numfashi Hajja ta sauke, idan ta biyema AbdulKadir ba mari ba kawai, rufeshi da duka zatayi.
Batasan ranar da zaiyi hankali ba, har ranta taji dadin hadin auren shi da Waheedah, ko
bakomai tana fatan hankali da nutsuwar yarinya su tausasa halayyar AbdulKadir din, har dadi
takeji ganin tunda aka fara hidimar bikin babu wanda yai kuka da shi, babu wanda yace yayi
mishi rashin kunya. Amman yanzun yana son jama kanshi zagi da bakin mutane.
"Al'adace hakan, ba kuma za'a canzata daga kanka ba, daga nan har Minna zakace abarka ku
tafi ku kadai saboda kai baka da hankali..."
Hajja take maganar cikin fada
"Hajja..."
AbdulKadir ya kira tana katse shi da
"Wallahi idan baka bacemun dagani ba sai ranka yayi mugun baci... Kuma inji ka sami wani da
maganar nan dan Allah... Yau ka nunamun ban isa dakai ba AbdulKadir kai musu maganar
nan..."
Hajja ta karasa tana mikewa taci gaba da hada kayanta da takeyi lokacin daya shiga dakin.
Tunda ya fita ranshi a bace yake harya karasa shiryawa suka fito suna hotunan nan sama-sama
yake jinshi, addu'a yake kar wanda ya tabo shi ballantana ya sauke mishi bacin ran da yake ji.
Ko da ake musu hotuna da Waheedah, yana jinta tai magana dai-dai kunnen shi
"Waya tabamun kai Sadauki?"
Taso tasa murmushi ya kwace mishi, tun randa ta fara furta mishi sadaukin nan yaji sunan ya
mishi dadi sosai. Sai dai hakan baisa bacin ran ya tafi ba, ko amsa ma bata samu ba har suka
bar wajen. Da bacin ran ya karasa masallacin, haka har aka gama daurin auren aka fito daga
masallacin, a kasan ranshi yakejin wata irin nutsuwa taban mamakin da igiyar data kulle
tsakanin shi da Waheedah. Nanma saida aka tsaya bata lokaci wajen daukar wasu hotunan,
danma Abba yace musu a tafi gida, akwai tafiya a gabansu.
*
Babbar rigarshi ya cire dan jinshi yake a takure yana sake kayan, duk da wata shaddar ya sake
sakawa, amman bayajin nauyinta kamar wanda ya cire, ninke su yakeyi yaji Yassar ya shigo
dakin da sallamar da ya amsa yana ci gaba da linke kayan da yakeyi.
"Kayi sauri, an fara shirye-shiryen tafiya..."
Kai kawai AbdulKadir din ya dagama Yassar yana saka shi fadin
"AbdulKadir..."
Bai amsa ba tunda kunnuwa ne suke jin magana
"AbdulKadir..."
Ya sake kira, kananun idanuwanshi ya sauke kan fuskar Yassar
"Kunnuwane suke ji Hamma... Kasan ina jinka ai"
Numfasawa Yassar yayi
"Zaka dauki yar mutane zuwa wani gari, AbdulKadir ba'a aura maka ita dan an gaji da ita ba, ba
kuma a aura maka ita dan an gaji da kula da ita ba. Rokonka nake karka kuntata mata, karka
cutar da ita..."
Idanuwan shi AbdulKadir ya kankance
"Dan ba'a jarabawar samun limanci da nace ka yanki form Hamma..."
Kai Yassar yake girgiza da murmushi a fuskar shi
"Dan ubanka ba maganar wasa nake dakai ba, nasiha nake maka"
Ware mishi idanuwa AbdulKadir yayi
"Abinda yasa nace limanci zai maka kyau kenan"
Dafe kai Yassar yayi, baisan ranar da AbdulKadir zai fara daukar abubuwa da muhimmanci ba,
ganin babu alamar zai saurare shi yasa shi mikewa yana fadin
"Abba na kira..."
Dakuna fuska AbdulKadir yayi
"Dan Allah Hamma kace ba wata nasihar za'aimun ba... Wai ita Waheedah ba za'ai mata bane
ba? Nima ai aurena aka bata, me yasa ni kadai za'a dinga yiwa.... Itama kaje kace ta riqeni
amana, karta cutar dani..."
Kofar Yassar ya bude kamar baiji abinda AbdulKadir din yace ba
"Hamma magana nake kana tafiya..."
Ficewa yayi yana jan kofar, fuska ya kara dakunawa yana dibar kayan ya tura cikin karamar
jakar daya shirya duk kayanshi da zai iya dauka a ciki, yawanci kananun kayane, manyan fiye
da rabi anan gida yabarsu. Jakar ya bari kan gado yana fita daga dakin zuwa bangaren Abba
yana shiga da sallama, babu kowa sai Waheedah da take zaune a gaban Abba, ta sake rigar
dazun, bai gama ganinta ba sosai cikin rigar ta sake, yanzun bayama iya ganin fuskarta dan
lafayane a jikinta anja shi an rufe fuskarta gabaki daya, yanayin yanda kafadunta suke rawa
yasa shi gane kuka takeyi.
Gefenta ya zauna yana fadin
"Abba gani...Hamma yace kana kirana"
Kai Abba ya jinjina yana kallon yaran nashi, yanajin kaunar su fal cikin ranshi, yana kuma
mamaki har lokacin yanda kaddarar rayuwa ta kawosu inda suke yanzun. Cikin ranshi yake ma
Allah godiya yana karawa da musu fatan zaman lafiya da rayuwar aure mai inganci.
"Idan da wani yace mun zaku zo nan a rayuwar ku ko na yarda zan jinjina lamarin..."
Abba ya fara magana yana dorawa da
"Ko da kukejin ana kiran hakuri a zaman aure, badan yana jigon auren bane gabaki daya, sai
dan yana taka muhimmiyar rawa a zamantakewa ta yau da kullum. Abu daya zan fada muku,
karku bani kunya, ku dukanku karku bani kunya. Matsalar aurenku kuyi kokarin ganin kun
shawo kanta da kanku, sirri na daya daga cikin abubuwan da suke da muhimmanci a aure... Ku
rike sirrin junanku kamar fitar dashi zai iya zame muku matsala.
Dan nace hakan kuma ba ina nufin ya baku damar da zaku cutar da junanku dan zaku rike a
matsayin sirri ba. A duk lokacin da hakan ya faru, kuke ganin ba zaku iya ba ku daga waya ku
kirani, shine kawai mutuntakar da zakuyi mun, ku sanar dani kafin yanke hukunci mai girma..."
Su dukansu sunyi shiru suna sauraren Abba, Waheedah daman tunda aka rakata wajen Mami
take kuka, har aka kawota wajen Abba, yanzun ma kukan takeyi sosai. AbdulKadir kanshi Abba
yasa jikinshi yin sanyi, tabbas aure abune mai girman gaske, bazai tuna ranar karshe da Abba
ya zaunar dashi yana mishi nasiha har yanajin kaunar shi a tare da kalaman shi ba sai yau.
"Allah yai muku albarka a zamantakewar ku, Allah ya tabbatar muku da dukkan alkhairi..."
Abba ya karasa da wani yanayi mai nauyi a muryarshi, har a kasan ranshi ya fara jin kewar
yaran nashi.
"Mungode Abba..."
AbdulKadir ya fadi yana mikewa, amman Waheedah ta kasa mikewa, magana zai mata Anty ta
shigo, bata ce mishi komai ba tazo ta kama Waheedah tana janta suka fice daga dakin. Kukan
da take yai mishi tsaye a makoshi. Bin bayansu yayi yana wucewa bangarensu dan ya dauki
jakarshi, yasan zai kwana biyu bai shigo Kano ba, makarantar Waheedah ma transfer akai mata
zuwa Minna din, badan Abba yasan mutane ba da hakan yai musu matuqar wahala. Kuma
yanda yakeji bazai iya barinta a Kano ba, inda duk yasa kafa nan zata mayar da tata. Saidai ta
hakura da makarantar.
MINNA
Gajiya takeji har a kasusuwan ta, wannan ne karo na farko a rayuwarta da ta taba zuwa wani
waje daya wuce kauyen bugaje. Jitai kamar zasu je karshen duniya, kamar tafiyar kwanaki ce a
maimakon ta yini daya. Sosai ta gode ma Anty Aisha data hada mata ruwa mai zafi tace taje tai
wanka. Sosai tadanji dadin jikinta, wasu kayan ta samu an dauko mata, doguwar rigace ta
atamfa sabuwa fil, dauka tayi ta saka tukunna ta dauki hijabin da tagani dan gabatar da sallar
magriba tabi data isha'i tunda ta samu tsarki.
Hakan kuwa tayi, lokacin data idar an kawo musu abinci kala-kala a take-away da alama siyowa
akayi. Guda daya aka ajiye mata a gabanta, ta cire hijabin ta dora kan gadon da yake dakin
kenan tana shirin bude robar abincin dake gabanta da batajin yunwar cin shi ko kadan saboda
kewar gida da takeyi ga kuma gajiya, aka kwankwasa dakin.
"Waye? Shigo..."
Anty Talatu ta amsa, AbdulKadir ya shigo da sallama, a bakin kofar yai tsaye yana fadin
"Anty sannunku da hidima... Waheedah dan zo"
Wata irin kunya taji ta rufeta ganin gabaki daya su Anty ne a wajen, harda danginta na wajen
uba guda biyu.
"Ki tashi kije mana"
Anty Aisha ta fadi, kafafuwanta da matukar nauyi taja su tana mikewa, mayafinta da aka fito
dashi shima sabo ta dauka, sai lokacin AbdulKadir ya mayar da kanshi yana fita daga dakin,
kafafuwanta babu karfi ta wuce tana fita daga dakin, ji takeyi kamar idanuwansu nakanta duk da
tana jin suka cigaba da hirarsu kafin taja musu kofar. Kamar hakan AbdulKadir yake jira ya
kama hannunta yana fara janta
"Ina zamuje?"
Ta tambaya, juyowa yayi yana kafeta da idanuwanshi da suka sakata yin shiru, saida taga suna
shirin nufar hanyar da zata fita dasu daga gidan tukunna tace
"Takalmana Hamma..."
Hannunta ya saki yana kallon kafafuwanta, hanyar bedroom din da suka baro ya nufa, tsinin
takalmanta yasa shi gane sune ya kwaso mata yana dawowa ya ajiye mata su, sakawa tayi ya
sake kama hannunta suna fita. Sai lokacin take karewa barikin sojojin kallo, saidai saurin da
AbdulKadir yakeyi ya sata maida hankalin ta kanshi tana binshi kamar wadda aka jona ma
battery. Tafiya sukayi har bakin kofar wajen tana mamakin ganin motar Yassar, dan batasan
dasu da abokan AbdulKadir din akazo rakoshi ba, hotel suka kama, sun dauka rashin son
hayaniya yasa AbdulKadir kama nashi dakin daban, kuma nesa da nasu, tunda gidan nashi daki
biyune kuma su Anty anan zasu kwana suma.
Saida yace ma Hajja a gaya musu karsuzo, kowa yai zaman shi ta balbale shi da fada kamar
yai mata laifi. Ga gidan nan suyita kwana, shikam da matarshi a hotel zasu kwana. Batace mishi
komai ba har suka shiga motar yaja su, a gajiye take jinta.
"Hamma nagaji wallahi, jikina ciwo yake..."
Ta fadi ganin har lokacin basu kai inda zasu kai ba
"Mun kusa..."
Ya fadi yana shan kwanar da zata kaishi hotel din, shiga ciki yayi ya samu waje yai parking din
motar. Tukunna ya bude mata ta fito, a gajiyar da takeji bin AbdulKadir da yake rike da
hannunta tayi duk inda yayi da ita, har suka karasa bakin wani daki ya bude yana jan hannunta
suka shiga ya mayar da kofar ya rufe. Hannun nata ya sake kamawa yajata kan gadon ya
zaunar da ita, takalmanta ta cire tana kare ma dakin kallo, tana mamakin yanda batajin tsoro ko
dar a zuciyarta, sanin AbdulKadir din bazai tabayin abinda zai cutar da ita ba.
Abinci taga ya dauko yana fadin
"Sakko muci..."
Kai ta girgiza mishi a hankali
"Jikina namun ciwo..."
Gira ya daga mata
"Shine ba zakici abinci ba? Sauko kafin ranki ya baci"
Turo labbanta da har lokacin da sauran janbakin kwalliyar data wanke a jiki tayi tana saukowa,
hannu yasa yana zare mayafin da taki cirewa ya ajiye shi a gefe batare dayace mata komai ba.
Itama batai magana ba ta dauki cokalin tana sakawa cikin abincin, tare sukaci, turawa kawai
tayi, tagode ma Allah da bai mata magana ba. Mikewa taga yayi ya shiga bandakin dake cikin
dakin, karar ruwa ya tabbatar mata da wanka yakeyi, ya jima kafin ya fito. Tanajin wayarshi na
kara, bata ko motsa daga inda take ba ballantana tai kokarin daga wayar.
Harya fito daure da towel a kugun shi dayasata dauke idanuwanta daga kanshi, wayar ya
karaso ya dauka. Anty Talatu ce, hidimar bikin yasaka shi samun lambarta. Dagawa yayi yana
fadin
"Hello..."
Daga dayan bangaren yaji tace
"Ina kukaje AbdulKadir? Kasan dai kowa ya kwaso gajiya ko? Kwanciya zamuyi ka dawo da ita
haka"
Kankance idanuwan shi yayi
"Kuyi kwanciyarku kawai, zamu kwana a hotel"
Ya fadi
"Hotel?"
Anty Talatu ta maimaita da matuqar mamaki a muryarta
"Hotel fa AbdulKadir..."
Dakuna fuska yayi yana fadin
"Saida safe"
Ya kashe wayar tashi gabaki daya. In ba zasu kwanta ba su nemi motar Kano su juya a daren.
Bayason wani dogon surutu shisa ya kashe wayar gabaki daya. Towel din ya kwance yana barin
gajeran wandon dake jikinshi ya koma bandaki ya ajiye. Kan gadon ya karasa yana shirin
kwanciya kenan yaji ana kwankwasa mishi daki, tashi yayi yaje ya bude kofar yana tsayawa a
bakinta ganin Yassar na sauke waya daga kunnen shi
"Daukota kayi ka kawo nan? Saurin me kake AbdulKadir?"
Dakuna ma Yassar fuska yayi
"Ina da ikon dauko matata in kaita duk inda yaimun"
Ya ba Yassar din daya dafe kai amsa
"AbdulKadir... Oh Allah na, ka tashi ka mayar da ita... Meyasa zaka daukota? Kasan surutun da
zaka jama Hajja kuwa? Me yasa baka da kunya ne"
Hamma AbdulKadir yayi dan bacci ne a idanun shi
"Wallahi bazan mayar da ita ba, ai nace ma Hajja karsu zo, kar suzo saboda za'a takurani, za'a
shiga rayuwata, bata fada musu ba. Ni kabarni..."
Baki a bude Yassar yake kallon shi kafin yace
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
Kallon shi AbdulKadir yakeyi
"Ka daina yi kamar anyi mutuwa fa... Ba zaisa in mayar da ita ba. Da ka wuce ka kwanta zaifi
maka alkhairi..."
Ya karasa maganar yana rufe kofar a fuskar Yassar da yake tsaye. Cikin dakin ya shigo inda ya
samu Waheedah a zaune tanajin duk wata kunyar duniya ta tattarar mata waje daya, batajin
zata iya komawa gidan nan ta hada idanuwa dasu Anty. Amman batasan ya zatayi da
AbdulKadir bane ba. Yanzun ma hannunta ya kama yana mikarwa ya dora kan gadon. Hawa
yayi shima yana kai hannu ya kashe musu kwan dakin, kwanciya yayi yana jan Waheedah ya
kwantar da ita kan kirjin shi yanajin wata irin nutsuwa na saukar mishi.
Yanda yakejin bugun zuciyarta a kirjinshi yasa murmushi kwace mishi
"Baki da hankali Waheedah... Kiyi bacci nima bacci zanyi..."
Yai maganar yana kara gyara mata kwanciya a jikin shi, da gaske yake mata baccin zasuyi.
Bayajin yin bacci shi kadai ne shisa yaje ya dauko ta, addu'a yayi tana jinshi ya tofa musu,
amman ta kasa koda runtsa idanuwanta ne balle bacci ya dauketa, saida taji numfashin shi ya
canza alamar bacci yake da gaske tukunna ta sauke wata irin ajiyar zuciya da batasan tana rike
da ita ba. Hannunta daya ta dora kan kirjinshi tana gyara kwanciyar ta, tana godema Allah daya
nuna mata zama matar shi.
Kanta ta gyara kan kirjinshi, bugun zuciyar shi na nutsar da wani abu a cikin nata kirjin har
baccin gajiya yai gaba da ita...!
*#TeamAbdulKadir*
*#TeamWaheedah*
*#AnaTare*
*#SonSo*
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
18
"Waheedah..."
AbdulKadir ya sake kira a karo na hudu, fuskar shi dauke da murmushi, baisan kalar gajiyar da
tayi ba, sallar asuba ma daya tasheta kallon shi ta dingayi kamar ya kwace mata wani
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 37