mutane. Dan dago kanta tayi, shi dinne ba
magagin bacci takeyi ba. Hannu takai tana murza kirjinta inda take jin yana mata wani irin ciwo.
A hankali komai yake dawo mata, hannu takai da nufin tashin shi ya furta mata abinda take son
ji, saita tsinci kanta da kasa yanke mishi baccin nashi, tunda tasan bako da yaushe yake samu
ba, duk da yazo hutune bayan shekara biyu sai yanzun ya sami hutu mai dan tsayi. Kallon shi
take, zuciyarta a dunqule waje daya take jinta, shisa bata motsa mata da duk wata kaunar
Abdulkadir din. Zufa taga yana yi, a hankali jikin shi ke bari, tasan yana cikin duniyar mugayen
mafarkan dakan hana mishi samun wadataccen bacci. Ganin yanda yake zabura yasa takai
hannun ta kan fuskar shi tana shafawa a hankali.
"Sadauki..."
Ta kira a tausashe, hannunta taji ya damqa kamar zai karyata kafin ya bude idanuwan shi yana
sake matse riqon dayai ma hannunta da saida ta runtsa idanuwan ta saboda azaba, sosai ta
dauka ya karyata yau dai.
"Sadauki hannu na..."
Ta fadi, tana saka shi dago fuskar shi daga kan cikin ta yana karema dakin kallo, kafin da sauri
ya saki hannunta yana fadin
"Bansan sau nawa zance ki daina yo kusa dani inkin ganni a yanayin nan ba..."
Dayan hannun ta mai daure da ruwa ta dago tana murza wannan din, idanuwanta harsun tara
hawaye
"Yau dai ka karyani, kayi maganarka ta karshe a bakin yan Amin, an amsa, ka karyani
Sadauki..."
Karamin murmushi yayi yana kamo hannun nata data fisge, karfi yadan saka ya riko hannun
"Kokawa zakiyi dani?"
Ya tambaya yana daga mata girar shi guda daya. Turo mishi labbanta tayi, hannun yake
dubawa, farar fatarta tasa hannun ya fara tara jini, shafa mata wajen yayi
"Ban karyaki ba, in kina tabani ina bacci dai zai faru wata rana, na fada miki bakyajin magana"
Fisge hannun ta tayi tana murzawa.
"Ina yarana?"
Ta buqata a hankali, tana jin kewarsu na danneta
"Fajr na tare dasu Mami nake tunani, Ikram na wajen Anty...bari in karbo miki ita..."
A hankali ta girgiza mishi kai duk da hakan take so, batasan lokacin data dauka a kwance ba,
tasan yarinyar taji yunwa ba kadan ba, amman a karbota daga wajen Anty, abin ya mata nauyi.
Abdulkadir bai saurareta ba ya miqe yana nufar kofar dakin ya bude ya fita, Anty yagani zaune
tana danna waya, da alamar game ne daya kalli screen din.
"Ta tashi Anty, ki bata Ikram wai..."
Batare da tace mishi komai ba ta ajiye wayarta a gefe tanaa kama goyon yarinyar ta kwance ta
mika mishi ita, karbarta yayi yana kallon ta, idonta biyu, ta tsoma hannuwanta guda biyu a
bakinta tana tsotsa. Gyara mata zama yayi a hannun shi daya tukunna ya bude kofar yana
shiga yana mayar wa ya rufe, sai da ya saka Ikram a hannun Waheedah din tukunna ya zauna
inda ya tashi, yana kallo ta miqe zaune tana jingina bayanta da abin gadon, tukunna ta gyarama
Ikram din zama sosai tana soma shayar da ita.
Dago kanta tayi tana kallon shi, zuciyar shi yaji ta doka ganin yanayin nan baibar idanuwan ta
ba.
"Kai nake jira..."
Ta furta a hankali, kallon ta yake yana son fahimtar ma'anar kalaman da ta furta mishi.
"Abinda na fada maka dazun, bana ce ka saukake mun auren ka ba? Ko baka jini ba in sake
maimaitawa?"
Yanzun ya gama tunanin ta dawo hayyacin ta, ashe bata dawo ba har yanzun, wacce irin
buguwa tayi haka. Dole zai magana da likitocin nan, inma barin kasar ya kama Allah ya mishi
rufin asirin da baya tunanin zai gagare shi.
"Kayi shiru..."
Waheedah ta fadi tana sake tallabo Ikram din jikin ta, wani irin yanayi taje ji da batasan yanda
zata misalta shi ba, har wani kaikayi take ji a jikinta da son jin ya furta mata kalaman da zasu
datse igiyar da ta qulleta dashi.
"Kin buga kanki da yawa..."
Abdulkadir ya fadi can kasan makoshi, shine kawai bayanin dazai fassara abinda yake faruwa
yanzun. Idan ba kanta ta buga ba Waheedah ba zata nemi saki a wajen shi ba, karma azo
maganar saki ba zata kalle shi cikin ido tana mishi magana da yanayin rashin kunya haka ba.
"Ban buga kaina ba, sakina nake son kayi..."
Ta fara bata mishi rai, yana jin yanayin na barazana da hakurin shi.
"Kibar mun maganar nan, ki bari, nace kin buga kanki da yawa ne..."
Ya karasa yana jan kujerar shi baya ya miqe tsaye
"Ina zaka je?"
Dan dafe kanshi yayi yana sauke hannun shi
"Zan magana da likita..."
Wani murmushi Waheedah tayi, tana rasa meyasa kalamanta suke mishi wahalar fahimta haka.
"Kayi magana dashi, idan ya tabbatar maka lafiyata kalau, saika dawo ka saurareni"
Kallon ta Abdulkadir yake yi, maganganunta na zauna mishi, a hankali ya girgiza kai, idan ya
zaman bata buga kanta ba, idan ya zamana tana cikin hayyacinta baisan me zaiyi ba, baisa ina
take so ya ajiye kalaman ta ba. Babu shiri ya koma ya zauna yana kiran sunan ta
"Waheedah..."
Kallon shi kawai tayi batare data amsa ba, wani abu daya zo wuyan shi ya tsaya yake kokarin
hadiyewa amman hakan ya gagara.
"Saboda hakurina ya kwace a karo na farko a zaman mu yasa kike furta mun kalaman nan?"
Kai ta girgiza mishi a hankali
"Kamun abinda yafi nayau, kasani kuma, nayau dinne dai zai zamana na karshe In shaa
Allah..."
Wata gajeriyar dariya yaji ta kubce mishi
"Kin san girman kalaman da kike furta mun?"
Ikram ta janye daga jikinta dan hartayi bacci, tana gyarawa tukunna ta jinjina mishi kai.
"Ba zai yiwu ba to, idan ma da gaske baki buga kanki ba, ba zai yiwu ba Waheedah..."
Ya fada da wani yanayi a muryar shi da yasa ta tambayar
"Meye bazai yiwu ba? Sakin nawa?"
A hasale Abdulkadir yace
"Waheedah...kina son sake gwada hakurina ba?"
Cikin idanuwa ta kalle shi
"Meye zai faru? Zaka sake dagamun hannu ne yanda kayi? Nace idan na gwada hakurin ka
zaka sake dagamun hannu ne Abdulkadir?"
Yanda taja sunan shin kamar ta kafa abin gurza kwakwa a zuciyarshi taja haka yaji ta karce
wajaje da yawa a cikin kirjin shi. Ko a mugun tunani bai taba hango Waheedah zata taba yi
mishi rashin kunya ba, mamaki yake har kasan ranshi daya kai karshe wajen baci, ya mata
kuskure bawai bai mata ba, amman hakan bashi bane dalilin dazai sa ta kalli kwayar idanuwan
shi tana fada mishi son ranta, bai tsaya kalmar neman saki ba, harda rashin kunya tana daga
mishi murya.
"Saukake miki a hannuna yake ko? Ba zai faru ba to, kina jina bazai faru ba"
Wasu hawaye taji masu zafin gaske suna zubo mata, ji take wani abu yana yamutsawa cikin
kanta, rashin hankalin da yake mata tunanin take ji yana gab da cimmata idan bai saukake
mata auren shi ta huta ba yau.
"Wallahi baka isa ba"
Ta fadi muryarta na karyewa da kukan da takeyi, kujerar shi yaja baya yana mikewa, wani irin
tuquqin bacin rai yake ji har idanuwan shi ke lumshewa
"Ki kalleni..."
Ya furta ta tsakanin hakoran shi, kukan ta taci gaba dayi
"Ki kalleni Waheedah!"
Ya fadi cikin wata irin murya data sata sauke idanuwanta da suka fara rinewa da kuka cikin
nashi
"Na isa...Ni Abdulkadir Ahmad Bugaje na isa har nayi yawa. Bansan me yake damunki ba, ki
kwanta kiyi bacci, bana bata lokacina akan abinda ya riga da ya wuce ke kin sani, zanyi kamar
komai bai faru ba..."
Ya karasa maganar yana juyawa dan jikin shi ya soma bari da bacin ran da yake ciki
"Sadauki karka fita baka saukake mun ba..."
Waheedah ta furta kamar baiyi magana ba, kamar bata ji abinda yace ba, bai juyo ba, saboda
baida tabbas kan abinda zai iya faruwa idan baibar dakin ba, yanda ya doko kofar saida ya
firgita Ikram data zabura tana fashewa da wani irin kuka, riketa Waheedah tayi tana jijjigata cikin
alamar lallashi dan itama kukan takeyi. Yana fita Anty ta shigo tana kallon Waheedah dake
faman share hawaye. Dan haka ta karasa tana karbar Ikram din daga hannunta ta goya
yarinyar da dakyar ta samu tayi shiru.
"Dan Allah kubi komai a hankali, kinji Waheedah? Kinga baki da lafiya..."
Saida ta share hawayen da sunqi daina zubar mata, da wani daci a makoshin ta tace
"Ni bance wani abu ba Anty, ko a musulunci an bani damar neman saki idan naga bazan iya
zama dashi ba... Me yasa bazai mun abinda nake so ba?"
Yanayin karayar dake muryarta yasa Anty karasowa ta dafa ta, itama tana jin idanuwan nata
sun ciko da hawaye dan Allah yai mata wata irin zuciya da ko bata sanka ba taga kana kuka
itama tayaka takeyi, balle kuma Waheedah da hankalin yarinyar yasa take jinta har ranta. A
raunane tace
"Ku dai bi komai a hankali, karki yanke hukunci cikin fushi..."
Wasu sabbin hawayen na zubar ma Waheedah tace
"Anty ki aramun wayarki dan Allah"
Batare da wata gargada ba Anty ta cire lambobin sirrin data rufe wayar dashi ta mika mata,
wajen kira ta shiga tana fara saka lambobin mutum dayan da take da yakinin shi kadaine zai iya
saka Abdulkadir yai mata abinda take so, shi kadaine kuma bazai ce tayi hakuri ko abi abun a
hankali ba. Danna kira tayi tana kara wayar a kunnenta, ringing daya tayi a na biyun ya daga da
sallamar data kasa amsawa sai ma wani sabon kukan da taji ya kwace mata. Dakyar ta iya
cewa
"Abbah..."
Tana jin muryar shi daga dayan bangaren ya amsa da
"Waheedah?"
Cikin son tabbatar da ita dince, kai take daga mishi kamar yana ganin ta, wasu hawayen na
zubar mata
"Abbah..."
Ta sake kira cikin kukan ta
"Subhanallah... Waheedah me yake faruwa ne? Lafiya dai ko?"
Kai ta girgiza mishi
"Abbah kai ma Abdulkadir magana ya sauwaqe mun... Dan Allah Abbah"
Ta karasa maganar kuka mai sauti na kwace mata, jim yayi daga dayan bangaren da alama
yana juya zancen tane, kafin yace
"Hajiya Halima na kusa dake?"
Dakyar ta iya cewa
"Eh..."
"Ki bata wayar..."
Anty dake tsaye Waheedah ta miqa ma wayar, tana jan kafafuwanta ta hade su da jikinta hadi
da dora kanta saman gwiwoyinta hawayenta naci gaba da zuba...!
*#Abdulkadir*
*#FWA*
*#AnaTare*
[7/27, 1:13 PM] +234 816 124 4732: ©️
📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
03
Tunda ya shiga gida bangaren Waheedah ya wuce, dakin baccin su ya shiga, yana zama gefen
gadon. Kan shi sarawa yake tunda ya fito daga asibitin, baisan ta inda zai fara tarar matsalar da
Waheedah take son janyowa rayuwar su ba, dan baisan meya shiga kanta ba, kafafuwan shi ya
janyo da nufin dorasu kan gadon yaga takalman shi dabai kwance ba.
"Bazan cire ba..."
Ya fadi a fili, da Waheedah yake, dan ita ce bataso yana shigo mata da takalma har daki,
abinda take so shi take mishi yau, shima abinda yake so zaiyi, hannu yasa ya dafe kan shi,
yana kuma saukewa hadi da ajiye numfashi mai nauyi. Idan matsalar kwakwalwa ce ta samu
Waheedah, yaga alama harshi takw son gogawa tunda ya fara magana shi kadai. Hoton su
dake durowar gefen gadon ta ya dauka yana tsayar da idanuwan shi akai. So yake yagane
wanne kalar kayane a jikin Waheedah din, yadai ga farare ne, dankwalin da ta nade kanta dashi
ma farine, zai iya tuna da wayarta ta dauke su hoton, tana lafe a jikin shi, ya zagayo da
hannunshi daya kan cikinta data dora nata hannun akan nashi, ya kankance mata idanuwan shi
daba girman kirki ne dasu ba daman, da dariyar nan tata a fuskar shi.
Dan yatsan shi ya saka ya shafi dai-dai fuskarta, yasha ganin hoton a ajiye a gurin, hade da
sauran hotunan shi da bazaice ga lokacin data dauke su ba, amman zai karya idan yace ya
taba tsayawa ya kula da hoton da yake hannun shi, balle ya tambayeta lokacin data kai aka
wanko hoton har aka saka shi a frame hakan, baisan meyasa sai yanzun yake son tambayarta
ba. Sake shafar fuskarta yayi
"Me yake damunki yau? Me kike son janyo mana Wahee? Me kike son janyo mana haka?"
Ya tsinci kan shi da tambaya, shirun dakin na saukar mishi da wani irin yanayi daya saka shi
ajiye hoton inda ya dauka. Baisan abinda ya kamata yayi ba, wani abu makamancin wannan bai
taba faruwa da shi ba, asali yau ce rana ta farko da rikici ya soma hadashi da Waheedah, shisa
yake jin komai ya kwance mishi, ba zaice baya fada da ita ba, ita dince dai bata taba biye mishi,
komin fadan dazai sauke mata hakuri kawai zata bashi, baisan me yake damunta ba yau.
Aljihun shi ya taba, wayarshi bata ciki, waige-waige ya fara yana neman inda ya ajiye ta, babu
shiri ya mike, duka inda tunanin shi zai iya kaiwa cikin dakin saida ya duba amman bai ganta
ba, takawa yayi zuwa falon su, zuciyar shi na wani irin dokawa da ya sauke idanuwan shi kan
table din da Waheedah ta fada kai, ga jini da harya fara bushewa kan kafet din, kafafuwan shi
da yake ji sun soma rawa yaja zuwa hanyar kitchen, wani karamin bokiti yagani ya dauka ya
tara ruwa a ciki, kan window din kitchen din ya dauki omo ya zazzaga a ciki. Abin goge-goge
yake nema, bai gani ba sai wani towel karami.
Shi ya dauka ya saka cikin bokitin yana daukowa ya fito daga kitchen din, gefen da jinin yake
akan kafet ya ajiye bokitin yana tsugunnawa, towel din ya fiddo ya matse yana soma gogawa a
wajen, sosai jikin shi ya dauki dumi da alamar zazzabin da yake da alaqa da dana sanin da ya
lullube shi, yana mayar da towel din cikin bokitin yaga yanda ruwan ya sake launi yaji wani abu
na tattarowa daga zuciyar shi ya hadu a wuyan shi ya shaqe shi, a hankali kuma shige da ficen
numfashin shi ya fara canzawa. Towel din yake gogawa a wajen da dukkan karfin shi.
'Jinin Waheedah ne duka anan'
Wata karamar murya ta furta cikin kunnuwan shi, numfashin shi na fita da sauri-sauri kamar
wanda yai gudu.
'Bana bata lokaci akan abinda ya riga ya wuce, bana tunani akai saboda bazan iya komawa in
canza ba'
Yake fadi cikin kwakwalwar shi ko zuciyar shi zata taimaka ta bashi hadin kai. Iya abinda zai iya
gogewa daga jikin kafet din ya goge yana daukar bokitin ya mayar kitchen, wajen wanke-wanke
ya juye ruwan, kalar shi nasa cikin shi yamutsawa, baisan lokacin da jini ya fara daga mishi
hankali haka ba, fanfo ya bude kan ruwan dan ya wuce da wuri, bayason ganin shi, ya tara
hannuwan shi a jiki ya wanke, har fuskar shi ya wanke ko zata rage mishi zafin da yaji tanayi, ya
kashe fanfon ya fito. Tunawa yayi wayar shi yake nema, yaci gaba da duddubawa, baisan
lokacin da yace
"Waheedah! Ina wayata?"
Idanuwan shi ya runtsa, bai gama tunanin yanda shima yake gab da samun tabin hankali ba yaji
karar wayar. Hakan na sashi bude idanuwan shi babu shiri, inda yake jin karar wayar yake bi,
harkan kujera daga gefe, hannu ya saka ya janyo wayar da rabin ta ya fara shigewa cikin lokon
kujerar, sai dai kiran harya yanke, dangwala jikin gilashin wayar yayi tunda babu wani mukulli a
jiki ta kuwa bude, mamakine bayyane a fuskar shi ganin Abba ne ya kira, bawai dan baya kira
ba, lokacin daya kira dinne yaji ya mishi wani iri.
Yana shirin bin kiran sai gashi ya sake shigowa, amsawa yayi yana kai wayar kunnen shi da
fadin
"Abba..."
Daga dayan bangaren Abba ya amsa
"Abdulkadir, kome kake kazo gida yanzun"
Zuciyar shi yaji tai wata irin dokawa
"Abba lafiya?"
Ya bukata yanajin sautin muryarshi daya fito a tsorace
"Ka dai zo..."
Kai ya girgiza
"Ni dai ka fara fadamun ko menene a waya tukunna"
Abdulkadir ya fadi, dan yanda zuciyar shi take bugawa sam bai aminta da kiran Abban ba.
"Abdulkadir..."
Abba ya kira cike da kashedi
"Ba zanyi tuqi a nutse bane idan bansan meye dalilin kiran ba Abba, ni dai ka fadamun dan
Allah. Kaji"
Ya sake fadi
"Bari in aiko a dauke ka to"
Cewar Abba da alamun ranshi ya fara baci, kai Abdulkadir ya girgiza yana jin komeye yake
shaqe da wuyan shi yana kara shaqe shi.
"Akan Waheedah ne ko?"
Ya tambaya muryar shi can kasa, yana kuma jin bugun zuciyar shi har cikin kunnuwan shi,
idanuwa ya runtse yana jiran amsar Abba, a ranshi kuwa rokon Waheedah yake
'A'a Waheedah, bakimun wannan tonon asirin ba, baki mun haka ba, ba zaki taba mun haka ba'
Bude idanuwan shi yayi dajin Abba yace
"Akan ta ne, kazo yanzun ina jiran ka"
Kafin ya furta wani abu Abba ya kashe wayar, tayi yar karar alamun an kashe daga dayan
bangaren cikin kunnen shi, sauke wayar yayi yana fadin
"Abba mana, Abba banaso ana kashe mun waya cikin kunne, da gaske bana so..."
Ya karasa maganar da furta
"Yaa Ilahee..."
Komai yake ji ya kwance mishi, takawa yayi yana fita daga dakin, gurin motar shi ya nufa,
budewa yayi yana jefa wayar a ciki, harya daga kafarshi daya ya saka cikin motar yaji an kira
sallah
"Ni sai nayi Sallah wallahi"
Ya furta kamar wani yace kar yayi sallah, cikin gida ya koma ya daura alwala, sai dai bayajin
yana da nutsuwar da zai iya zuwa masallaci, anan dakin baccin su ya nemi darduma ya
shimfida yana tayar da sallah. Sai dai ga mamakin shi kokawa ya soma yi sosai da nutsuwar
shi, dakyar ya samu yai sallar tunani fal cikin ranshi, ko addu'a baiyi ba ya mike yana barin
dardumar anan. Fita yayi ya shiga motar yana kunnuwa hadi da janta ya juya, maigadin kofar
nashi ya bude mishi gate ya fice ya nufi hanyar da zata kaishi da gidan nasu da yake a kofar
ruwa.
**
Dakyar Anty ta samu likitan yabar su suka taho gida, shima da alkawarin cewa zata dawo da
Waheedah a ranar, komai a asibitin suka baro shi. Ita kanta Antyn taso koma menene abar shi
sai Waheedah ta samu sauqi sai ayi, amman ita da Abbanta sunki yarda da hakan. Har suka
shigo gida addu'ar Allah ya kawo musu sauqi takeyi. Waheedah da kanta ta fara jan Anty zuwa
bangarenta, badan bata son ganin Mami ba, bata son kowa yace tayi hakuri ko tabi komai a
hankali, batason jin duk wannan.
Kujera ta samu tai zamanta a dakin Anty, lokaci zuwa lokaci take saka hannu ta share hawayen
dake biyo fuskarta, Ikram ma data qara bata tasha Anty ta miqama yarinyar. Tana nan zaune
Abba ya shigo da sallama, tana sauke idanuwan ta cikin nashi wani irin kuka ya kwace mata, a
hankali Abba ya karaso cikin falon yana neman waje ya zauna.
"Waheedah..."
Abba ya kira sunanta muryar shi cike da rauni, kanta da yake nade da bandeji ya fara bi da
kallo, tukunna ya tsayar da idanuwan shi kan fuskarta da duk kumburin da tayi da alamun kukan
da tasha bai hana yanda ta rame matuqa nunawa ba. Kukan da take yasa ta kasa amsa shi
"Waheedah kiyi hakuri kinji..."
Abba ya furta yana jin yanda zuciyar shi take a jagule, muryar Waheedah a dishe ta dago
jajayen idanuwanta tana kallon Abba, kai take girgiza mishi tana sauke ajiyar zuciya a hankali
"Dan Allah Abba..."
Ta soma fadi tana jin zuciyarta kamar zata fado
"Dan Allah... Karkace in koma... Karka ce inyi hakuri Abba... Wallahi nagaji... Inajin idan na
koma zuciya ta Abba..."
Tai maganar tana kai hannunta a kirji inda take jin zuciyarta kamar zata fashe, numfashi take ja
tana fitarwa amman iskar bata kai mata inda take so, dakyar take iya magana
"Abba zuciyata ina jin kamar zata fado, dan Allah karkace inyi hakuri, karka tambayeni me ya
faru... Bansan ta inda zan fara maka bayani ba, kawai nagaji ne, nagaji sosai"
Anty dake tsaye hannu tasa tana share hawayen da taji suna shirin zubo mata, a muryar
Waheedah take karantar kuncin da Allah kadai yasan tun yaushe take danne shi, a muryat
Waheedah take jin ciwon da take ciki, ya kuma taba zuciyarta ba kadan ba, sosai tayi niyyar
lallaba yarinyar takoma dakin mijinta domin shi aure dan hakuri ne, kowa kaganshi zaune a
gidan mijin shi komin dadin zaman su akwai hakurin da suke da juna ta fannin da bazai
bayyanu ba.
Sai dai kuma batasan har yaushe za'a dinga labewa a bayan hakuri ana cutar mata a
zamantakewa ta auratayya ba, batasan sai yaushe mutane zasu fahimta shi kan shi hakurin
yana da qa'ida ba, a al'adance ma hakuri na da iyaka, balle addini daya sauqaqa matakin
komai, batasan lokacin da mutane zasu fahimci duk da hakuri jigone na zaman aure bai sa ya
zama ibadar auren gabaki dayan ta ba.
"Dan Allah Abba..."
Roqon da Waheedah tayi ya katse ma Anty dogon tunanin da takeyi, wani radadi takeji
zuciyarta nayi, kuncin Waheedah na tuna mata da duk hakurin da tayi a nata gidan auren, yana
sa tana tuna rashin sauqin da yake tattare da hakuri, sai mai matuqar karfin zuciya ake yiwa ya
kauda kai. Abba kan shi numfashi ya sauke yana furta
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un... Abdulkadir...Halima kinga yaron nan saida ya kure hakurin ta
ko?"
Abba ya karasa maganar yana jinjina kanshi, a raunane Anty ta amsa shi da
"Ai shikenan, ya kyauta, ya kuma yima kan shi wallahi"
Hajja ce ta shigo dakin da sallama, tana kare musu kallo, dan sallah take lokacin da Abba ya
aika a kirata. Mami daman da Anty taje da kanta catai duk suna wajen ita kam bataga zuwan
me zatayi ba, ta san zasuyi yanke duk abinda ya kamata akan Waheedah din. Duk kawaicin
Mami, Anty tasan Waheedah ta ninka ta, yau kam tura takai bango.
"Allah dai yasa lafiya..."
Hajja ta fadi bayan Anty ta amsa mata sallamarta, kafin ta zagayo ta samu waje gefen Abba ta
zauna, sai lokacin ta kula da Waheedah da tun shigowar Abba ta sauko daga kujerar da take ta
zauna kan kafet din dakin
"Subhanallah, Waheedah? Ashe dai ciwon da yawa haka... Zainab tazo tana fadamun, yanzun
nake shirin in idar da sallah saimu koma asibitin gabaki daya. Amman kamar bai kamata su baki
sallama da wuri haka ba..."
Anty ce ta amsa Hajja da
"Basu bayar da sallama ba suma, zamu koma zuwa anjima..."
Da mamaki Hajja tace
"Ikon Allah... Lafiya dai ko?"
Tai tambayar tana kallon Abba daya girgiza mata kai
"Abdulkadir ne..."
Zuciyarta Hajja taji tayi wata irin dokawa jin sunan dan nata
"Yau kam dai ya kure hakurin yarinyar nan. Saki take nema..."
Cikin tashin hankali Hajja tace
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un...saki kuma Alhaji? Meya faru? Me yai mata?"
Dan rausayar dakai Abba yayi, dan baida wannan amsar, ba kuma shi da karfin zuciyar da zai
tambayi Waheedah din tunda har roqon shi tayi dakar ya tambaya. Waheedah dake share
kwalla Hajja ta kalla
"Waheedah me ya faru?"
Batare data dago ba ko hawayenta ya daina zuba tace
"Dan Allah Hajja karki tambayeni meya faru, kiyi hakuri, duk kuyi hakuri, takardata kawai nake
son a karbar mun a wajen shi..."
Maganar daga zuciyar ta takejin tana fitowa, ta dauka rashin Abdulkadir a kusa da ita zai
barazana da rayuwarta, bata taba tunanin zama dashi ne abinda zai haifar da hakan ba, in baya
kusa da ita ko numfashi batajin tana fitarwa dai-dai, amman yanzun tunanin kusanci dashine
yake barazana da dai-daiton numfashin ta. Ba tasan lokacin da rayuwa ta bude musu wannan
shafin ba, sai dai ko ba zata iya wuce shi ba, zatai duk wani kokari da zata iya ko dansu Fajr.
Salati Hajja take tana kara wani
"Ke kam Waheedah kiyi hakuri mana, kinji tunda duk muna nan kibari a kira shi in shaa Allah
koma menene yake faruwa zamuji sai a dai-daita ku...tunda haihuwa ta shiga tsakani ko dan
yara sai a duba lamarin..."
Kai Abba ya girgiza ma Hajja
"Karkuyi amfani da yaranta ku danne ta..."
Rai a jagule Hajja ta kalle shi
"Karka cemun kana tunanin yin abinda take so ne batare daka duba lamarin ba?"
Kafin ya amsa Abdulkadir ya shigo dakin, kallo daya zakai mishi kasan babu nutsuwa a tattare
dashi ballantana ai maganar kwanciyar hankali. Ko sallama baiyi ba, zagayowa yayi yana zama
kan hannun kujera, zuciyar shi kamar zata fito daga kirjin shi saboda tsallen da takeyi
"Abba me tace na mata?"
Ya tambaya, rashin gaskiya shimfide a fuskar shi. Kallon shi kawai Abba yakeyi, Hajja ce ta
watsa mishi harara
"Me kai mata Abdulkadir? Me ka sake yi mata?"
Cike da rashin fahimta yace
"Bangane me na sake mata ba Hajja? Na mata wani abune banda nayau?"
Girgiza kai Anty tayi tana fadin
"Hmm..."
Dan batason tayi magana, Abdulkadir rashin kunya zai mata tasan shi sarai
"Dan ubanka baka san me kai mata ba?"
Fuskar shi babu walwala yace
"Hajja mana..."
Ko kadan bayaso a saka shi a gaba ana mishi fada, ko dacan ma bayaso balle yanzun da ba
yaro bane shi, sai dai baiga laifin su ba, Waheedah ce, duk laifin nata ne da tai mishi wannan
tonon sililin, tafi kowa sanin yanda yake son sirri a rayuwar shi, abinda ya faru yau din
tsautsayine da zasu iya magance shi tsakanin su, baisan me yake damunta da ta kwaso
matsalarsu tana fadama su Abba da baiga ta inda abin ya shafe su ba.
"Ka kyauta Abdulkadir... Ka ji... Ka kyauta"
Hajja ta karasa muryarta na karyewa, idan ranta yai dubu a bace yake. Abba ya sake kallo
"Dan Allah Abba me tace nayi mata?"
Kai Abba ya girgiza mishi
"Batace kai mata wani abu, aurenka ne kawai ta gaji dashi"
Cikin wani irin tashin hankali Abdulkadir ya kalli Waheedah da ta sauke mishi rinannun
idanuwanta. Da nashi idanuwan yake tambayarya me take? Me take yi musu haka?
"Abba zanyi magana da ita... Kaji... Hajja kunji..."
Ganin suna kallon shi yasa shi dorawa da
"Dan Allah..."
Abba ya fara miqewa, shikam batun yanzun ya sallama da lamurran Abdulkadir ba, tsakanin shi
da yaron idone da addu'a, amman shikam yace yayi ko kar yayi bakin shi ya daina wannan
asarar. Ganin da gaske bar musu dakin zasuyi yasa Waheedah fadin
"Abba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 37