sallah a hanya. Har haushin Yassar yaji
da yace
'Matar ka bata da hankalin da zaka wuni baka koma gida ta nemeka ba ko?'
Duk da gaskiya ce ya fada, Nuriyya din ko flashing batayi mishi ba, ya kuma ji haushi sosai, dan
shi mutum ne mai bala'in son kulawa, shisa tunda ya dawo yake shashareta, ya kuma ga bata
damu ba, hidimarta kawai takeyi, yayi alkawarin zai dafata a ruwan sanyi, dan bazai dauki
wannan halin ko in kula din nata ba, inma ba da gangan takeyi ba, bangaren Waheedah ya
shiga yana samun ta ta fito daga bandaki, da alama alwala tayi, bata ce mishi komai ba ta dauki
hijab dinta, shima bandakin ya shiga ya daura alwala yana fita masallaci, zuciyar shi a nutse
yake jinta har aka idar da sallah. Ko azkar bai tsaya yiba ya dawo gida, dan so yake yagan shi a
kusa da ita.
Ita kam Waheedah zafi taji ya isheta ta sake watsa ruwa tana idar da sallah, doguwar riga ta
saka ta material dinki bubu, yadin blue mai haske, ta dauki hula kalar shi mai cizawa ta saka a
kanta, tana jin dadin wutar da suka dawo da ita, dan fitilar waya take ta amfani da ita a dakin,
torchlight dinta babu caji a jiki. Duk da darene jambaki ta tsinci kanta da shafawa a labbanta,
tana dan murza mai a hannuwanta, ta feshe jikinta da turaruka masu sanyin kamshi. Sanda
AbdulKadir ya shigo ta sauke ikram kan katifarta, tana kara gyara gadon da yake a hargitse.
Tsaye yayi a tsakiyar dakin, kamshin ta na saka shi lumshe ido, wata irin kewarta na dabaibaye
shi.
Har inda take ya taka yana rungumeta ta baya ya sumbaci kuncinta, cikin kunnenta yace
"Ki yafemun Waheedah, dan Allah ki yafemun"
Tanajin yanda maganar ta fito daga zuciyar shi, zame jikinta tayi daga nashi, tana juyowa ta
fuskance shi, fuskar shi take kallo sosai, tana saka hannuwanta ta rike kuncin shi, tanajin yanda
sai da tadan daga kafafuwanta, girman shi harya daina bata mamaki, kallon shi tayi na wasu
dakika kafin ta sauke hannunta batare da tace mishi komai ba, a shirunta yake karantar yafiya,
duk yanda idanuwanta suke tabbatar mishi yana da sauran lokaci kafin ta sauka daga fushin da
take, zaiyi komai, indai tana kusa dashi duk mai sauki ne.
Gadon ta karasa gyarawa, ta dauki Ikram dake ta bacci ta mayar da ita kan gadon tana ficewa
daga dakin zuwa kitchen, tanajin AbdulKadir na biye da ita, mukulli tasa ta bude kitchen din
tana turawa, tabar mukullin a jiki, tsugunnawa tayi tana bude kwalaye da ledojin siyayyarta,
AbdulKadir na tsaye yanata binta da idanuwa kamar bai taba ganinta ba, ta mishi kyau sosai.
Da ance mishi lokaci zaizo da zaiji shakkarta zai karyata, amman yanayin dake fuskarta yasa
shi hakura da duk yanda yake son sumbatarta. Yanzun ma kasa hakura yayi ya tsugunna kamar
zai tayata fiffito da kayayyakin da take ya kamo hannunta da yasha lalle yana dago shi ya
sumbata.
Kallon shi Waheedah tayi tanajin yanda ko meye tasa ta lullube kaunar shi dashi yana soma
budewa, hakan yasata zame hannunta daga cikin nashi
"Aiki nake Sadauki"
Ta fadi tana dauke idanuwanta daga kan shi, ta dauki ledojin maggi tana dorawa kan kantar
kitchen din ta dauko robobinsu ta bude kowane tana juye shi a mazaunin shi. Baice mata komai
ba, kayan ya tayata shiryawa, suna cikin aikin Nuriyya ta karaso wajen da murmushi a fuskarta,
wutar da aka kawo yasa ta fitowa falon sai taji motsin yayi yawa shisa ta fito, sosai taji sanyi a
ranta na ganin Waheedah din, taliya ce ta samu ta dafa fara, tanayin miyar da ko a ido batai
mata kyau ba.
Tunanin abinda zasuyi suhoor dashi takeyi da yanda zata kaya musu washegari, ranta duk baya
mata dadi, amman yanzun tasan indai girki ne ta kare, fadansu da ta hango ita da AbdulKadir
kan hakan ya wuce. Sosai hankalinta ya kwanta
"Waheedah... Ashe kin dawo"
Ta fadi tana saka Waheedah din da AbdulKadir juyawa a tare, Waheedah najin wani abu ya taso
mata daga dan yatsan kafarta zuwa tsakiyar kanta yana dawowa kirjinta ya tokare, AbdulKadir
kuwa wani irin tsoro da baiyi tsammani ba yaji ya lullube shi, kar Nuriyya din tayi kokarin rike shi
a gaban Waheedah, da sauri yazo ya rabata ya fice daga kitchen din yana wucewa bedroom din
Waheedah ya turo kofar, jikin shi yakeji har bari yake mai, dan baisan ya zaiyi ba, a karo na
farko a rayuwar shi da komai ya kwance mishi.
Waheedah kuwa wani kallo tayi ma Nuriyya din da yasa taji gwiwoyinta sunyi sanyi. Ba zatace
tun zuwanta gidan suna hira da Waheedah din ba, ko kuma sunci gaba da zama kawaye,
amman suna gaisawa kullum, kuma tana shigowa bangaren Waheedah din ta zauna a falo, har
remote take dauka tayi kallo, musamman in tajiyo kamshin girki, data kula ko batazo ba tana
bata abinci saita rage zuwa sai AbdulKadir na nan. Amman Waheedah daman ta daina fara'a a
gabanta, sai dai bata mata irin wannan kallon, bata mata kowanne kallo ma.
"Sannun ki"
Waheedah ta fadi tana juyawa taci gaba da abinda takeyi, watakila ko dan batajin dadine,
Nuriyyar tayi tunani, hakan yasa ta wuce ta koma bangarenta dan bata kula da sanda
AbdulKadir ya fice ba. Tsaf Waheedah ta karasa gyara kitchen din tana share shi, fridge dinta ta
bude taga an dibar mata robobin kayan miya, ta kuma san Nuriyya ce, daga yau kuma ta kare,
can gidan kasa ta tsugunna, tana janyo kwami ta ciro roba fara mai murfi, dakyar ma ta fito da
ita dan tayi kankara. Farfesun kayan cikine a ciki, tukunya ta dauko ta saka robar a sink tana
sakar mata ruwa dan yadan saki.
Doya ta yanka da zata isheta iya cikinta, ta fere tana zuba dan mai a abin suya, ta soyata
fararta, tana kwashewa a plate. Lokacin farfesun ya saki, iya wanda zai isheta ta diba ta zuba a
tukunya tana mayar da sauran a fridge. Ta dora, da yake yasha kayan kamshi, kafin kace wani
abu gidan ya budade da kamshin daya fito da AbdulKadir yazo kitchen din yana fadin
"Me kike dafa mana?"
Juyowa tayi tana kallon shi
"Daga dawowata zan karbi girki? Banda lafiya ko ka manta, sai jibi nikam"
Da mamaki AbdulKadir yake kallonta
"A'a ba abin tashin hankali bane ba, sai in koma gida, jibin in dawo"
Kai ya girgiza mata da sauri, shi bashida karfin fada koyin gaddama da ita. Duk da yaso jinta a
jikin shi daren yau, kwana biyu bazai canza wani abu ba, sanin tana cikin gidan ya ishe shi, ran
shi ya biya da abincin sosai, wata yunwa da baisan yanajin taba ta taso mishi. Dan waje ta
samu ta juye farfesun a ciki, AbdulKadir din yakai hannu zai dauki guda daya ta doke hannun
shi
"Ni ban dafa da kai ba Wallahi"
Tana janye kwanon ta ajiye gefe, kallonta yake, yayi mata laifi yasani, ya bata hakuri kuma
"Ba kyau horon yunwa"
Ya fadi can kasan makoshi, Waheedah nayin kamar bataji shi ba, duk abin ya mishi wani iri
sosai dan bai saba ba, sau nawa take hakura da abu tabar mishi, amman yau itace take cewa
tayi girki banda shi, zuciyar shi batai mishi dadi ba sam, tukunyar data bata take wankewa. Sai
ga Nuriyya ta shigo kitchen din tana ta washe baki, dan tana sallar isha'i take jiyo kamshin,
yawunta sai tsinkewa yake, kwana biyu bataci abu mai galmi-galmi ba.
"Kamshi duk ya cika gidan, me ake dafa mana ne"
Ta fadi kamar yanda ta saba, AbdulKadir na kallonta a karo na farko yaga kwadayi a fuskarta,
baisan ko dan shima an hanashi bane yasa shi jin haushin kwadayin nata. Ga mamakinta ko
inda take Waheedah bata kalla ba, asalima plate din doyar ta dauka da kwanon farfesun tana
zuwa ta gabansu,
"Kudan fita zan rufe kitchen din"
Ta fadi tana ganin suka fita bakin kitchen din suna ta kallonta, sai da ta janyo kitchen din tasa
mukulli ta rufe tukunna ta wuce da fadin
"Sai da safen ku"
Su biyun suna binta da kallo cike da mamaki
"Ina namu?"
Nuriyya ta fadi bayan Waheedah ta shige lungun da zai kaita dakin baccin ta, dakuna fuska
AbdulKadir yayi
"Nima bata bani ba"
Ya amsa ranshi a jagule yana wucewa bangaren Nuriyya din, da duk da mamakin da take bai
hanata jijjiga kitchen din ba taji da gaske a kulle yake, dan Waheedah bata taba rufe kitchen
dinta ba. Tsaye tayi a wajen ta kasa yarda da abinda ya faru...!
#LubnaSufyan
#TeamAbdulKadir
#TeamWaheedah
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
31
Da wani irin sanyin gwiwa ta karasa bangaren ta, watakila har yanzun Waheedah batajin dadi,
in baka da lafiya daman komai fita ranka yake shisa. Ko kuma taji haushine dan batai mata ya
jiki ba, ita kuma sai lokacin tunanin yazo mata. A haka ta karasa bangarenta, ta samu
AbdulKadir kan doguwar kujera a zaune. Karasawa tayi ta zauna a gefen shi, yanajin
shigowarta, ran shi a bace yake, ga yunwa da yakeji kuma. Baisan me yasa sai yanzun yake jin
haushin ta ba, dana kudin shi da ta kashe, da kuma na yau da ko kadan bata neme shi ba
ballantana tasan bashida lafiya harya yini a asibiti.
Har yanzun yaga alama batasan waye shi ba, ko dan rashin Waheedah a kusa dashine yasa
yake ganin komai ma bashida muhimmanci, yanzun da yasan ba zata barshi ba, ya samu
natsuwar da zai fuskanci sauran matsalolin shi. Bayason kashe kudin da bashida dalili, komai
nashi a kan tsari yake, sosai yakan yi tunanin abinda takeyi da kudi, kuma ba a dan zaman sun
nan ya kula da idan ya ajiye kudi a wallet tana kwashewa ba, ko yazo yin kwana biyu, indai zai
mata nata kwana dayan saita dibar mishi kudi. Idanuwa ya dauka ya saka mata yaga gudun
ruwanta, yanzun ne ta gama kawo mishi wuya.
"Mu me zamu ci?"
Nuriyya ta bukata muryarta a sanyaye, dan sosai ta saka ranta a abinda Waheedah din ta girka.
Sai takejin da wahala ta iya cin taliyar da ta dafa
"Ke ba mace bace? Baki dafa naki bane?"
AbdulKadir din ya bukata yana tsareta da idanuwa, duk da maganganun shi sun mata zafi,
murmushi ta danyi
"Na dafa mana taliya"
Baice mata komai ba, ganin hakan yasata mikewa ta samu plate ta zubo musu taliyar, har miyar
ta hade. Tare sukaci, AbdulKadir na rasa ranshi da yake a bace ne, ko taliya ce da bai cika so
ba, ko kuma girkin ne bashida gabas, dan ko gishiri-gishiri na miyar ma baiji ba, sai wani
daci-daci. Turawa kawai yayi, ita kanta Nuriyya da tana da wani zabi sam ba zata ci taliyar nan
ba, sa ma ranta cin girkin Waheedah da tayi yasa taliyar kara fitar mata daga rai. Tana kai
kwanon kitchen dakin baccinta ta wuce, ta dauki wayar ta. Tallar littafin Hauwa A Usman
Jiddarh tagani na Saki Reshe, tana tunanin sarkakkiyar da take ciki na yanda za'ayi jarumin ya
kasance gagarumin dan fashi.
Ba'a kai da fara shi ba, hakan yasata jan dan karamin tsaki, daman jiya littafin Fadime na Bingel
ta maimaita dan sosai takejin dadin littafin, soyayyar da aka shimfida ciki na tuna mata dalilin da
yasa ta auri AbdulKadir tun da farko, amman yanzun ta fara gajiya dan taci karo da abinda
bashi take tsammani ba. Ganin babu abinda zata karanta yasa ta dauko system din ta, daman
tana lallaba fina-finan da take dasune, tana budewa sai ga AbdulKadir ya shigo dakin, karasawa
yayi kan gadon yahau yana saka hannu yaja system din
"Masoyi..."
Ta fadi tana kallon shi, bai mata magana ba yasa hannu yana kashe system din dauketa daga
kan gadon gabaki daya ya dora kan drawer din da take gefen shi ya juyo yana tsura mata
kananun idanuwan shi da suka sata yin shiru
"Ki kashe mana wuta"
Ya fadi, dan makunnin ba'ayi shi a kusa da gado ba, mikewa Nuriyya tayi tana zuwa ta kashe
wutar ta dawo ta kwanta itama, sai dai ga mamakinta, juya mata baya AbdulKadir yayi da
alamun bacci zaiyi. Wani abu taji yai mata tsaye a makoshi, batason ya sauke mata fadan shi,
shisa ta hakura bata dauki system din ba, wayarta taci gaba da dannawa, tana ganin yanda
status din kowa ya gauraye da maganar ganin wata
"Anga wata"
Ta fadi, AbdulKadir ya jita, surutunne ba zaiyi da ita ba yau, asalima niyyar azumi ya daura a
zuciyar shi, sake gyara kwanciya yayi yana fuskarta, wayar da take hannunta ya fisge yana
sakata a key ya ajiye a tsakiyarsu tare da fadin
"Ki kwanta Nuriyya"
Muryarta can kasan makoshi tace
"Banajin bacci wallahi, bakasan baccin da na sha ba yau daka fita"
Shisa bata neme shi ba, baccin ta yafi jin inda yake muhimmanci. AbdulKadir ya fadi a ran shi,
zuciyar shi na kara jagulewa
"Bazan sake magana ba..."
Cewar AbdulKadir din cikin iko da gadarar shi da take bata mata rai. Gyara kwanciya tayi, ranta
in yayi dubu a bace yake, batasan iya lokacin data dauka a haka ba har bacci ya dauketa itama.
Su dukkan su baccin suke, shi AbdulKadir baccin daya kwana biyu baiyi bane ba, ita kuma
Nuriyya baccin da batayi da wuri bane, ko ma da wurin ta kwanta shi yake tashinta sallar asuba,
inba haka ba sai dai ta makara, dan in baya gari makara takeyi. Hakan yasa ko kiran sallar
farko basuji ba, sunata bacci har karfe shidda saura.
Haske AbdulKadir yagani cikin idanuwan shi, kasancewar window din dakin baccin Nuriyya din
daga waje yake, duk da wanda yake waje ba zai iya hango su ba, su da suke ciki zasu iya
hango shi, haka gilashin window din yake. Amman bai hana hasken da yake nuna alamar gari
ya waye shigowa ba. Murza idanuwanshi yayi da hannu yana kara runtsa su, kafin ya bude su
cikin tashin hankali yana mikewa zaune babu shiri, hasken da yagani cikin dakin bai saka shi ya
yarda ba, saida ya dauki wayar Nuriyya da take gefen shi ya danna, yana ganin shidda saura
minti goma.
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
AbdulKadir ya furta yana kai hannu ya jijjiga Nuriyya
"Ki tashi mun makara"
Ya fadi yana hasaso kalar yunwar da zaiji a yinin yau, dan shi azumi baiyi suhoor ba rayuwar shi
na cikin tashin hankali.
"Nuriyya..."
AbdulKadir ya kira yana bubbugata, idanuwanta ta bude dakyar tanayin mika
"Dilla ki tashi karfe shidda fa"
Wata irin mikewa Nuriyya tayi tana kallon shi
"Karfe shidda? Shidda fa? Bamuyi Suhoor ba, baka tasheni ba"
Wani irin kallo AbdulKadir ya watsa mata yana jan tsaki
"Ban tasheki ba? Bake ya kamata ki tashi ba, ki dafa mana abinda zamuci, nine zan tasheki?"
Shagwabe fuska tayi, tanajin idanuwanta na cika da hawayen bakin ciki, duk yanda sukai
zaman rashin mutunci da Anas yana tashinta lokacin azumi, tunda yaga randa batai suhoor ba
ta zama abin tausayi, a kwance ta wuni shame-shame. Shine AbdulKadir zai sauke mata fada
kamar akwai inda aka rubuta cewar ita ya kamata ta tashe shi dole dole.
"Kaima idan ka tasheni ai ba wani abu bane Masoyi"
Ta fadi wani abu na tokare mata wuya, kankance idanuwan shi AbdulKadir yayi
"Magana zaki fadamun?"
Ya bukata cike da neman ta furta wani abu ya sauke mata fadan shi, kai ta girgiza a hankali,
hawayenta na kara taruwa, qwafa yayi yana sauka daga kan gadon ya wuce bandaki, abin na
hade mishi waje daya, ga bakin cikin rashin suhoor ga asuba daya rasa, ga Nuriyya da zatai
mishi kukan rashin dalili. Saida yadan watsa ruwa a gaggauce tukunna yayi alwala ya fito, bama
shida kaya a dakin nata, dole sai yaje bangaren Waheedah. Nuriyya ya kalla da bata ko nuna
alamar tashi ba
"Ke ba zakiyi sallah ba?"
Kafafuwanta ta sauko daga kan gadon
"Ba zakiyi wanki ba kuma? Bandakin ki baya shigar miki ido, me yasa bakya wankewa ne?
Dakyar nayi wanka a ciki"
AbdulKadir ya karasa yana wucewa ta fice daga dakin. Wannan karin hawayen ta taji sun zubo.
Wani malolon bakin ciki na tokare mata kirji, a haka ta dauro alwala ta dawo ta gabatar da sallar
asuba. Tana idarwa ta koma bandakin, tasa tsintsiyar da take a ciki ta wanke shi sama-sama,
ko omo bata saka ba. Ba zata fara karar da karfinta a bandaki tun yanzun ba, dan wani sharri
ma, cikinta harya fara murdawa da alamar yunwa. Wani zaninta ta dauka ta hada duka kayan
wankin da suke cikin bandakin ta kulle su, ta dawo ta cire zanin gadonta dan yayi dauda sosai
shima takai bandaki ta ajiye akan wancen kayan wankin, zata fitar dasu tunda Waheedah ta
dawo.
*
AbdulKadir kuwa dakin Waheedah ya wuce yana turawa wani kamshi ya cika mishi hanci, dakin
a gyare yake tsaf. Ta sake zanin gado, ko ina tsaf tsaf, tana zaune kan gado ta mike
kafafuwanta, ta goya Ikram ta gaba tana kwance akan kirjinta, hannunta daye rike da Qur'ani.
Ba zaice ga kalar dinkin jikinta ta yanda take zaune ba, amman atamfa ce, ta daura dankwalin
atamfar, fuskarta fayau babu kwalliya. Amman ta mishi kyau har zuciyar shi dokawa take. Sai da
ta idar da ayar da take kan karantawa, tukunna ta dago idanuwa ta sauke su kan AbdulKadir din
"Ina kwana"
Ta furta cikin sanyin muryarta tana dan mishi murmushin da yaji zuciyar shi ta dan nutsu
"Wahee... Ya kuka tashi?"
Dan langabar da kai tayi
"Alhamdulillah..."
Idanuwan shi AbdulKadir ya kankance mata
"Shine baki tashe mu ba? Mun makara, yanzun fa muka tashi, ko sallah banyi ba"
Ware mishi idanuwa Waheedah tayi, ita ba Suhoor takeyi ba, sai dai inta tashi tayi brush tasha
ruwa, in tana da kankana ta dan sha dan samun ladan suhoor din, ko taci dabino wasu lokuttan,
yau dinma hakan tayi. Zatai karya idan tace batayi tunanin duba ko AbdulKadir din ya tashi ba,
tunda tasan yanda yake wahala idan baiyi suhoor ba, kawai dai ta tsinci kanta da share koma
meye yake son yin tasiri a kanta
"Na dauka kun tashi, kasan ni ba Suhoor nake ba"
Kai kawai AbdulKadir din ya iya jinjina mata, ba sai ta fada mishi ba, yasan fushin da takeyi
dashi ne, koya tashi Waheedah zata kara kiran wayar shi ta tabbatar da hakan, wahala take son
yasha, kuma zai shata din yau ya sani. Kaya ya wuce ya dauka, yana ganin yanda Waheedah
batace ya bari ta dauko mishi ba
"Ka dauki na kwana biyu ka wuce dasu Sadauki, inka dauki kaya kaje dasu bangarenta ka cire
acan kabar mata acan, karka dawo mun dasu nan dan Allah"
Ta karashe maganar da rokon shi kamar yana da wani zabi
"Ki zo ki dauko mun to"
AbdulKadir yace kamar karamin yaro, Qur'anin ta ajiye tana tallabe Ikram ta sauko daga kan
gado, kaya ta dauko mishi, riguna da gajerun wanduna, harda na ciki kala bibbiyu, tunda shi ba
manyan kaya yake sakawa ba, yana dasu, in tayi magana kan ya saka bakinta ne zai tsini, ba
zaisa ba, bayason manyan kaya. Hannun shi ta dago tana saka kayan a ciki, tayi mishi
murmushi har hakoranta suka fito, idanuwa AbdulKadir ya kankance mata
"Ko turare baki fesa mun ba"
Kallon shi tayi
"Bafa kayi sallah ba, lokaci na wucewa kuma"
Wani irin shagwabe mata fuska yayi, ta wuce tana komawa tayi zamanta, tana daukar Qur'ani
taci gaba da karantawa a bayyane da muryar data tsaya dai-dai kunnuwanta. Da kan shi yaje
wajen mudubinta yana daukar turaruka ya feshe kayan dashi, ko inda yake ma Waheedah bata
kalla ba, balle yai tunanin zatai mishi magana. Harya gama ya fice daga dakin, ta sauke
numfashi tana cigaba da karatunta. Ko da ta idar, bata fita ba sai wajen karfe goma, da Ikram ta
fita karta ajiyeta ta farka taita kuka dan wanki zatayi kafin su dauke wutar su.
Sai da ta fara share dakin wankin tukunna ta koma dakinta ta dauko jakar da suka dawo da ita
da. Tana cikin firfito da kayyakin wankin sai ganin Nuriyya tayi kamar mikiya, ta diro dakin
wankin, da katon zanin gado da alamar kayan wankine a ciki
"Lafiya?"
Waheedah ta tambaya tana tsare Nuriyya da idanuwa cikin yanayin da yasa Nuriyyar jin duk ta
daburce, Waheedah din na mata wani irin kwarjini naban mamaki, dan ko babu fara'a a fuskarta
bata hade girar sama da ta kasa haka.
"Ina kwana"
Nuriyya ta fadi saboda ta rasa abinda zatace kafin tayi saurin dorawa da
"Ya jiki?"
Sai da Waheedah ta kalleta na wasu dakika, tana sata jin duk ta tsargu, kafin ta amsa da
"Lafiya"
Tana cigaba da hidimarta, tsaye Nuriyya tayi mamaki duk ya gama cikata. Kayan wankin ta ajiye
tana juyawa ta fice daga dakin. Wankin ta Waheedah tayi dan bashida yawa, ta kwashe ta zuba
a wata babbar roba, Ikram tazo ta kwantar akan doguwar kujera tana saka pillow din ta tareta,
dan yarinyar ta cika juye-juye, karta fado. Tukunna ta koma ta dauki robar ta fita bayan gidan
inda igiyoyin shanya suke, ta shaya kayan ta dawo. Wanda Nuriyya ta ajiye ta kwashe tanajin
nauyin shi, bangaren Nuriyyan da tunda ta shigo gidan zata kirga lokacin da kafafuwanta suka
taka ta nufa, a tsakiyar falo ta ajiye mata kayan tana juyawa, dakin wankinta ta janyo ta saka
mukulli ta rufe ta dauki Ikram suna shigewa ciki.
Nuriyya kuwa fitowa tayi dan ta kawo wata hijab da tagani da datti, taci karo da jibgin kaya ajiye
a falo. Tsaye tayi turus tana kallon kayan cike da mamaki, ba rashin lafiya bace take damun
Waheedah, wani hali na banza ne ta dauka da ba nata ba, dan bata santa dashi ba. Ranta a
bala'in bace ta dibi kayan wankin tana komawa dasu ciki ta ajiye a tsakiyar bandakin, itama tana
da injin wankin ai, bawai bata dashi bane ba, kitchen ta koma ta dauko ledar omo ta dawo tana
kallon AbdulKadir da yake a kwance yana danna waya
"Masoyi..."
Ta kira shi muryarta na fitowa a karye, hakan yasa shi dago idanuwan shi ya kalleta
"Ya ake amfanin da abin nan?"
Dakuna mata fuskar shi yayi
"Wanne abu?"
Ya tambaya, yana sa kunya ta rufeta, dan ta tsani ace duk irin wannan abubuwan na gayu ita
bata iya ba, muryarta can kasan makoshi tace
"Na wanki"
Mikewa zaune AbdulKadir yayi yana kallonta cike da rashin fahimta, hakan na sata sake fadin
"Injin wankin, ya ake amfani da shi"
Har lokacin kallon ta AbdulKadir yakeyi
"Da ina kikaje da kayan? Ba naga kin fita dasu ba"
Maganar shi nasa ranta kara baci
"Bangaren Waheedah..."
Ta amsa a taqaice tana kin mishi bayani, wannan karin fuskar shi ce dauke da tsantsar mamaki
"Me kike nufi da bangaren Waheedah?"
Kanta ta saddar kasa ganin irin kallon da AbdulKadir din yake mata
"Ita kika kai tayi miki wankin saboda baki da hankali?"
AbdulKadir yake fadi yanajin ranshi na kara baci fiye da yanda yake a bace, dan bai taba ganin
irin wannan rashin hankalin ba, shisa ya sai mata nata injin wankin itama, yanda ma ba sai taje
bangaren Waheedah din ba gabaki daya akan maganar wanki. Yana daukar abubuwa da yawa
a rayuwar shi amman bayason raini
"Ajiyeta kikai da zaki kai mata wanki Nuriyya?"
Kanta ta kara saddarwa, hawaye na tarar mata cikin idanuwa a karo na biyu daga wayewar
garin yau, ko kadan bata saba a sakata a gaba ana mata fada ba, ko a gida daman Baba ne
yake mata fada in tayi wani abin, to sai tayi abu goma, Mama bata fada mishi ba. Ranta baci
yake yi duk idan akai mata fada, balle kuma yanzun da take jin tayi girman da duk wannan
abubuwan bai kamata ana mata su ba, ranta a bace tace
"Karka ce haka..."
Tunda shi ba zama yake gidan ba, kuma Waheedah din na wanke mata da, bai sani bane ba
"Dama can nake kaiwa, yaune kawai ta dawo dashi"
Sosai AbdulKadir yake kallon ta
"Wankin kike dauka daga nan, sai ki kai bangaren ta, sai ta wanke miki?"
Yayi tambayar yana saka Nuriyya jin kamar tayi wani laifine, wata yar dariya AbdulKadir yayi da
ko kadan batada alaka da nishadi kafin ya sauko daga kan gado yana ficewa daga dakin ya
doko kofar kamar zai karyata. Bangaren Waheedah ya nufa ko sallama baiyi ba yanda ya tura
dakin yasa ta bude idanuwanta daga baccin daya soma fisgarta
"Wanki kike ma Nuriyya? Akan wanne dalili?"
Ya bukata yanajin yanda ranshi yakai koluluwa wajen baci
"Baka taba kula ba sai yanzun?"
Waheedah ta bukata a sanyaye, dan yana gidan Nuriyya take kwaso wankin ta kawo mata
bangarenta, shisa ta dauka yasani.
"Karki amsa mun tambaya da tambaya, karki kara batamun rai Wallahi"
Yanda yai maganar da yanayin fuskar shi yasata sauke idanuwanta daga cikin nashi, akwai
yanayin da tasan ba zata fara gwada hakurin shi a cikin su ba, yanzun na daya daga cikin su
"Ko ban sai mata engine wanki ba, akan wanne dalili zakiyi mata wanki? Ajiyeki tayi?"
Numfashi Waheedah ta sauke
"Ina azumi nikam"
Kankance mata idanuwa tayi
"Ni nace miki bana azumin ne?"
Kai ta girgiza mishi a hankali, tana jin murmushin da yake shirin kwace mata, tayi kewar rikicin
shi
"Allah ya baka hakuri Sadauki, yanzun ai zata wanke abinta kaga, kuma menene dan na hada
na wanke?"
Kallon da yai mata yasa ta yin murmushi
"Yi hakuri"
Tsaki kawai AbdulKadir yaja yana ficewa daga dakin, su duka biyun haukata shi suke sonyi
yaga alama. Akwai halayen Nuriyya da yawa da yake kula dasu yanzun da baya ganin su da,
dakin ya koma yana samunta inda yabarta, bandakin ya wuce ran shi a bace har lokacin, tsayen
da Nuriyya taga yayi ne yasata bin shi, nuna mata yanda zatayi amfani da injin wankin yayi,
bama komai tagane ba saboda a masife yake nuna mata komai, yana gamawa ya fice daga
dakin, falo ya koma ya kwanta kan doguwar kujera yana huci shi kadai. Ga hanjin shi daya
tattaru ya kulle waje daya. Bacci yake son yi, rana na karawa kuma, yana so yadan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 32 Chapter of 37