Share this page
maka wahala idan wani ya zama sanadin farin cikin ka, ko da zama na yau da gobe bai taba wannan farin cikin naku ba, rabuwa ta kaddarar rayuwa ko mutuwa kan iya giftawa, sai kayi yaya? Aure kan samar da farin ciki, amman baya nufin duka farin cikin naka zai zamana a zagaye da shi auren. Mata sunfi kowa yin wautar nan, musamman a zamanin da muka tsinci kan mu a ciki. Zamanin da yasa idan mace ta samu jinkirin auren da ba laifinta bane za'a dameta da yawan surutai har ya sata jin yin auren ne kawai hanya daya ta samun farin ciki, a wasu lokuttan kuma idan yarinya bata tashi cikin wadata ba, bata kuma da wadatar zuciya sai ta dora ginshiqin aurenta da samun farin ciki akan auren mai kudi, wasu kuma hange-gange shine yake halakar dasu, kinga mace cikin rufin asiri, kinganta daga sama da mijinta suna cin me kyau su sha me kyau, sai wannan kyallin ya haska miki shi, sai kiga kamar ta samu duk wani abu da shine burinki a zaman aure. Bakisan yanda zaman aurenta yake tare da mijinta ba, bakisan me take jurewa ba, bakisan shima me yake jurewa a zama da ita ba, zamantakewa ta tsakanin ma'aurata sirrine da yake a lullube, abinda idanuwanki suka gani baya nufi shine komai, zai iya yiwuwa mijin wadda kika kyalla idanuwanki a kai bashi bane abinda burinki yake bukata. Karki so mutum dan abinda kike tunanin kin ga matar shi ta samu a tare dashi, ko da zatonki ya zama gaskiya ba kida tabbas ke zaki samu irin wannan a tare dashi. Duk da wasu matan ma na da laifin ganin mijin su nasu ne su kadai, wasu kance 'Ta auri mijin wata'. Dan kawai ta shiga a ta biyu. Babu wani abu mijin wata daga lokacin da musulunci ya halarta karin uku bayan ke tun kafin wanzuwarki, mijinki nata ne itama. Wahalhalu da yawa mutane su suke dorama kan su ita, kwanciyar hankali baya zuwa idan baka neme shi ba. AbdulKadir ko kadan bai zaci ta aure shi da wata manufa da ta wuce ta son zama dashi kamar yanda yake son zama da ita ba, shisa ya juya yana ficewa daga dakin. Takawa yake dan ya fita daga gidan ya tafi wani waje, koma ina ne inda ba zaiga Nuriyya na wani lokaci ba kafin ta tunzura shi ya yanke musu hukuncin da su duka ba zai musu dadi ba. Amman sai ta biyo shi, a falon Waheedah ta sake shi zai wuce ta gaban kitchen din shi tana kama mishi riga ta janyo shi saida ya juyo "Nuriyyaa" Ya sake kira cikin wani sabon kashedin, Waheedah taji takun tafiyar shi tun kafin ya fito, ta kuma ji muryar su dan tana hango kafar shi guda daya, da yake kujera ta saka ta zauna a kitchen din ta jingina bayanta da lokar kitchen din ta dora roba kan cinyarta tana gurza kubewa "Ka dawo ka saukake mun wannan kaddararren naka, dan Wallahi ba zanje gidanmu babu wata shaida ba, ni dama nagaji da zama da kai..." Numfashi AbdulKadir ya sauke ya kama hannunta yana banbarewa daga rigar shi yana fadin "Kin gaji da zama dani right? Ki jirani Nuriyya, duk mu huta da rashin albarkar da take bin mu" AbdulKadir ya karasa dan shi kan shi yanajin yagaji da bala'in nan, yanzun nan kuma yanajin rashin albarkar iyaye ce take bibiyar shi shisa a kasa da sati biyu komai ya jagule musu shida Nuriyyar, shima a gajiyen yake jin shi, maganganun kowa da suka fada mishi sun tabbata, hankalin su ya kwanta, sai su kalli idanuwan shi suyi mishi dariya su fada mishi da yaji maganar su daga farko da baizo inda yake ba yanzun. Dakin Waheedah ya wuce, Nuriyya na tsaye bakin kofar kitchen din Waheedah din tana girgije-girgije, ta wutsiyar ido Waheedah ta ganta, ko dagowa batayi ba, kubewarta take gurzawa a hankali tana bin karatun daya shigo na Suratul-Mulk cikin muryar Qari Sheikh Ghamdi da ke nutsar da abubuwan da batasan a tashe suke a tattare da ita ba. Bata kalle su bane saboda basu bane a gabanta, saboda fadansu bai shafeta ba, asalima bata da alaka da shi. Nuriyya na nan tsaye AbdulKadir ya dawo da takarda a hannun shi, dayan da biro rike, fuskar shi kawai zaka kalla kasan ran shi a matuqar bace yake "Gashi nan, na sake ki saki daya" Runtsa idanuwan ta Waheedah tayi tana jiran taji ko zata girgiza tare da abinda ya girgiza daga kalaman sakin aure da AbdulKadir ya furta, asalima tana bude idanuwanta ji tayi kamar tare da sakin Nuriyyar ya dauke mata wani katon dutse daga saman kai. Nuriyya kuwa bata karbi takardar ba, kallon AbdulKadir din takeyi bata son sake hada wata hanya dashi ko ta wasa ce, wani auren zatayi na mai kudi inda ba za'ai mata tijara kan dubu arba'in da biyu ba "Daka haifu cikin Hajja da ka karashe biyun ai, kaga duk sai ka hutar damu" Sosai AbdulKadir yake kallon ta, a duniya babu wanda ya taba zagin shi haka, babu wanda ya taba kallon shi ya zage shi haka, saki daya ko uku, har a bayan zuciyar shi yanajin kamar yanda ya nuna babu wanda ya isa ya hana shi lokacin daya aureta, sai wata kaddarar da baiyi fata ba, haka yakejin yanzun ma babu wanda ya isa ya saka shi sake zaman aure da ita ko da su kadai suka rage a fadin duniya, saboda bayason gauraya yaran shi da matar da ta fada mishi maganganun da Nuriyya ta fada mishi. Takardar ya yaga yana komawa cikin dakin, ko mintina biyu baiyi ba ya fito da duka littafin a hannun shi yana dago kafar shi daya ya dora littafin a jiki yai rubutu ya yago ya mika mata. "Na sake ki saki uku...na saukake miki gabaki daya kaddararren aurena Nuriyya" AbdulKadir din ya karashe yana mika mata takardar da ta karba ta linke batajin digon dana sani ko daya, asalima wani irin sakat taji ta, tana kallon shi ya ajiye takardar da biron akan kujera ya taka ya fice daga gidan, ta dauke idanuwanta daga kan kofar tana kallon kitchen inda Waheedah take gurza kubewa kamar bata da wata damuwa a duniya, sai Nuriyyar taji shine abinda yai mata tsaye a makoshi, yanda Waheedah take nuna kamar bata da wata damuwa a duniya "Zaki iya nuna farin cikin ki, ga mijinki nan nabar miki sai ki jika kisha" Nuriyya ta fadi da wani malolon bakin ciki daya taso ya danne mata zuciya, amman inda take ma Waheedah bata kalla ba "Banza wawiya kawai" Ta kara fadi tana jan wani irin tsaki ta wuce ciki dan ta hada akwatunanta. Waheedah bata kulata bane duk yanda zuciyarta take tunzurata da tayi hakan, ta fada mata maganganu, ta gaya mata yanda ta ture amintar su ta aure mata miji, ta zageta kamar yanda take so, amman azumi takeyi, ita ko bata azumi ma batajin akwai wasu maganganu da Nuriyya zata fada mata da zai tunzurata kuma, babu wani abi a tattare da ita da zai bata mamaki, daga ranar da ta iya auren AbdulKadir bata kara bata mamaki ba. Taji maganganun Abba da yace mata karta taba bari bakin halin mutane ya canza kyakkyawar dabi'arta, ko jiya ta karajin wa'azin Mufti Menk akan mu'amala da mutane. Sai dai wani lokacin zuciya bata da kashi, mutane basu da kirki, babu uzuri a cikin lamurran su, kai sai suyita maka rashin arziqi, idan ka ware rana daya kai magana akan hakan sai ace da hakuri aka sanka, ba'a tunanin yanda akwai zuciya a kirjinka kaima, babu wanda zai maka uzurin cewa kaima din fa dan adam ne kamar kowa, amman kai mutane sai su saka ransu a cewar yi musu uzuri ya zame maka dole. Yanzun dai ta zabi kin kula Nuriyya dinne, daga yau zata fara addu'ar yanda ta fita daga rayuwar su, ko a hanya kar kaddara ta sake hadasu da ita, mikewa tayi da kubewar da ta gama gurzawa tana ajiyeta ta share wajen ta wanke hannuwan ta, sai take jin iskar da take shaka ma daban take dirar mata. Nuriyya kuwa data wuce daki ta sauko akwatinan ta ta fara hada kayanta, harda ghana must go ta zuba takalmanta da jakunkunanta a ciki. Sai da tagama hada kayan tsaf ta dauki hijab ta saka tukunna ta fita daga gidan, bakin hanya taje ta taro mai napep ta dawo, ta kula da kitchen din Waheedah din a kulle yake kamar bata ciki, munafukar ta fadi a ranta. Akwatinan ta dinga janyowa tana fitowa dasu tana loda wa mai napep din da ta ajiye a kofar gida, har maigadi yayi kokarin tayata fita da akwatin data fara fitowa dashi "Na rokeka ne? Banason tsinanniyar gulma da bakin munafunci kamar baka gane sakina akayi zan bar gidan ba" Cewar Nuriyya tana saka shi ya koma inda yake ya zauna, haka ta dinga fitowa da kayan tana dirka nishi, kayan kitchen dinta tazo da akori kura ta kwashe abinta dan ba barinsu zatayi ba, ko siyarwa tayi tai amfani da kudin, wani sama-sama take jin kanta da take alaqantawa da nishin da take saboda fito da kayan. Komawa ciki tayi dan ta dauko karamar jakarta. Tana daukowa ta fito ta ga wayam, babu mai napep babu alamar shi, rasa inda zata nufa tayi, titin haggu ko na dama, dawowa tayi tana turo kofar muryarta a karye take kallon mai gadin "Dan Allah kaga inda mai napep din nan ya nufa?" Wani irin kallo yake mata, daman kayan da zai tayata dauka dan ya zata matar gidance har lokacin, ba hurumin shi bane tsoma baki a al'amuran gidan AbdulKadir din, amman har ranshi ya tsani Nuriyya, saboda yasha ganinta ita da Waheedah din idan tazo gidan ta rakota, lokaci daya yaga ta shigo gidan a matsayin matar gidan, ko ba'a fada mishi ba yasan auren cin amana ne akayi, ga ta da wulakanci kuma, sai ya gaisheta ta watsa mai mugun kallo tana amsawa dakyar, ga aiken rashin daraja da take mishi. "Tsinanniyar gulma da bakin munafunci bai barni na ga inda yai ba" Kallon maigadin tayi hawayen bakin ciki na tarar mata a ido, kafin ya tura kofar har yana bige mata yatsun da take yarfewa dan azaba. Hawayenta na samun damar zubowa, gabaki daya sutturarta ce ya tattara yai gaba da ita, karyarta da mutuncin da take shiga kawaye na ganinta dashi duk ta silar kayan ce. Sai yanzun wani abu kamar guduma ya dakar mata tsakiyar kai,da asalin abinda barinta gidan AbdulKadir din zai haifar, ina zataje yanzun, bata manta kashedin da Baba yai mata ba, duk da watannin nan idan taje gida ta gaishe dashi yakan amsata babu yabo babu fallasa, ta ina zata fara? "Na shiga uku na" Ta fadi wasu sababbin hawayen na zubo mata...! #TeamAbdulKadir #TeamWaheedah #LubnaSufyan [7/16, 9:57 PM] +234 802 111 7692: Facebook: Lubna Sufyan IG: SufyanLubna Email: Calmlubna@gmail.com Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43 YouTube: https://youtu.be/WwocHslDAYk *ABDDULKADIR* *LubnaSufyan* 34 Baisan inda zai nufa ba, da duk dakika da yanda zuciyar shi take kara mishi zafi. Tsintar kan shi yayi a kofar gidan su. Aka bude mishi ya shiga da motar shi ciki, kan shi tsaye bangaren Hajja ya nufa, ya shiga babu ko sallama. Fajr da ya rugo ya rike mishi kafafuwa ya kama yana daga yaron cik ya sauke shi a gefe tare da fadin "Fajr kabarni nikam, ina Hajja?" Shagwabe mishi fuska Fajr yayi "Tana bacci" Kai AbdulKadir ya jinjina ma Fajr din yana wucewa yabar shi a wajen. Dakin Hajja ya nufa ya kwankwasa, cigaba yayi har saida yaji muryarta dake cike da bacci ta amsa shi, tukunna ya tura dakin yana shiga. Kallo daya tayi mishi tagane a hargitse yake "AbdulKadir..." Ta kira cike da damuwa tana dorawa da "Lafiyar ka?" Kai AbdulKadir ya girgiza mata yana kallon ta kamar zai fashe da kuka, yanayin da yasa Hajja mikewa zaune. "Me ya faru?" Tsayen dai yake yana kara kankance mata idanuwan shi "Kai mun magana mana AbdulKadir" Takawa yayi ya zauna kasa yana dora kan shi akan kafar Hajjan kamar karamin yaro "Hajja nayi kuskure.... Na sake biyewa zuciyata nayi kuskure babba" Cikin tashin hankali Hajja tace "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un...me kai ma Waheedahr kuma?" Kai AbdulKadir ya girgiza mata "Ba Waheedah bace ba, na saki Nuriyya...Hajja na saketa" Numfashi Hajja ta sauke, duk da saki ba abin so bane, musamman ita mace data fahimci abinda hakan yake nufi. Amman zatai karya in tace bataji wani sanyi a kasan zuciyarta da tasan ba Waheedah bace ba. Tayi iya kokarin ta na ganin ta bata kasance cikin irin iyayen mijin dake daukar tsana ta babu gaira babu dalili sun dora akan matan yaran su ba, amman sam zuciyarta ta kasa aminta da auren AbdulKadir din da Nuriyya. Ko kadan bata son yarinyar, hakan dai ba zai hanata fada mishi gaskiya ba "Subhanallah, me ya faru AbdulKadir? Cikin azumin nan? Yanzun ita tana ina?" Kan shi ya kara kwantarwa a jikin cinyarta, kirjin shi zafi yake kamar ana hura mishi wuta. Maganganun Nuriyya sun ruguza wani abu a cikin zuciyar shi da baima san dashi ba. Komai yai mishi tsaye, ya kasa yarda cewar ya saketa din, duk da ko ba gabaki daya ya datse igiyoyin auren su ba, ta fada mishi maganganun da yake da tabbacin alaqarsu ta samu tangarda ta har abada, badai zai hana zuciyarshi jin zafin abinda ya faru ba. "Bata so na, abinda aurena zai iya bata shi take so" Ya furta muryar shi na fitowa da wani irin yanayi da yasa Hajja runtsa idanuwanta tana sake bude su "Wannan kawai bai isa zama dalili ba" Dago kai yayi yana kallon Hajja, kafadun shi yadan daga mata "Na riga nayi, na saketa, saki uku Hajja, dalili ko babu dalili ba zai canza hakan ba" Wannan karin ware idanuwanta Hajja tayi "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un.... AbdulKadir saki uku? Idan Allah ya jarabceka da son ta kuma fa?" Ta karasa maganar hankalinta a tashe, dan sam abin bai mata dadi ba, kome ya faru kuwa, duk yanda bata son shi da Nuriyyar. Murmushi yayi me sauti yana dan dafe kan shi da yake sarawa kafin ya sauke hannun shi yana kankance idanuwan shi akan Hajja, wanne soyayya kuma banda wadda yai mata tasa kafafuwa ta ture, itace mace ta farko da zuciyar shi ta fara dokawa, ita ce mace ta farko da ya fara tunanin zaman aure da ita. Ba yajin akwai wata jarabta ta bangaren soyayyar Nuriyya da zai same shi ya bashi mamaki. Itace macen da yaso, sai dai ba ita bace macen da ta dace dashi. Yanda zaka so abu ya zamana ba alkhairinka bane bazai daina bashi mamaki ba. Inda yasan hakan zai faru, da yana da ilimin sanin abinda gobe zata haifar ba zai soma auren Nuriyya ba, ciwon da zaiji na hakan ba zai taba kai wanda yakeji yanzun ba. "Magana nake maka fa" Hajja tace tana saka AbdulKadir din mikewa tsaye "Hajja ni kirjina ciwo yake mun, dan Allah kiyi hakuri..." Ya karasa maganar yana zagayawa ya mika hannu ya dauko pillow daya daga kan gadon ta yana jefa shi a kasa. Sai daya cire takalman kafafuwa shi tukunna Hajja ta kula da su. Sabon shine shiga ko ina da takalma tun yana da karancin shekaru, bakinta har ya gaji da magana kan hakan. Yanzun ma da idanuwa take bin shi harya zauna kan kafet din dakin nata ya gyara pillow din shi ya kwanta "AbdulKadir..." Ta kira "Hajja kunyar Hamma nake ji shisa nazo wajen ki...Allah zan tafi in baki barni ba" Mikewa tayi, ta riga da tasan halin AbdulKadir din, duk da alamu sun nuna yana cikin hali, in ba da kanshi yake son yin maganar ba bazai yi ba. Yana jinta ta fice daga dakin, gyara kwanciyar shi yayi yana lumshe idanuwan shi ko kirjin shi zai rage zafin da yakeyi. Bacci yayi har la'asar, har yaje masallaci ya dawo yanajin kirjin shi bai daina zafi ba. Dakin Hajja ya sake komawa yai kwanciyar shi. Tana shigowa tagan shi tace "Wai kai AbdulKadir ba zaka tashi ka tafi gidan ka ba?" Sake juya kwanciya yayi "Yanzun Hajja dan nayi aure shikenan bazan zo gida duk sanda nake so in kwanta in huta ba?" Ya karashe maganar kamar zaiyi kuka, dan baiga dalilin da zaisa Hajja ta dinga korar shi shida gidan Abban shi ba, amman da Waheedah tazo babu wanda yace ta koma sai da yazo ya dinga binta yana bata hakuri "Idan kuma yaji nayo fa? Sai ki koreni kice in koma?" Dariya Hajja take da AbdulKadir din baiga dalilinta ba, dan shi da dukkan gaskiyar shi yake maganar da yakeyi din. "Allah ya shiryamun kai AbdulKadir" Hajja ta fadi har lokacin tana dariya ta fice daga dakin, sai da yagaji da kwanciyar tukunna ya fito zuwa falon yana zama Fajr na shigowa da nama a hannun shi yanaci "Paapi kaga, Mami tabani" Ya karasa maganar yana zuwa ya zauna a jikin AbdulKadir din "Mami ta kyauta, ka gode" Sake shigewa jikin AbdulKadir din Fajr yayi yana kwanciya sosai, yana sa AbdulKadir din fadin "Kaifa ka cika son jiki Fajr, baka azumi zaka bini ka danne" Baisan inda yaron ya koyi son jiki ba, gashi dan mitsitsi dashi abinda yake so shi zaiyi, maganar shi ba zata sa Fajr din ya sauka daga jikin shi ba, sai dai in dukan shi zaiyi. Amman wani ido ko magana ba ko yaushe suke tasiri akan Fajr ba, baisan inda ya kwaso halayen nan ba, dan shi ba haka yake ba. Anan ya zauna har aka kira sallah, dabino da kankana ya dan sha yayi alwala, Fajr na rigimar sai ya bishi "Ka tafi dashi mana" Cewar Hajja "Baiga takalmin shi daya ba, har anyi raka'a daya" AbdulKadir ya fadi yana zame hannun Fajr din daga cikin nashi, yaron na bude baki ya fara kuka, wani irin mari Abdul ya dauke shi dashi da yasa Hajja fitowa daga kitchen ta kama Fajr din "AbdulKadir baka da hankali? Wannan ai sai ka ji mishi ciwo" Ta karasa tana daukar Fajr da jikin shi ko ina ke bari, yama kasa fitar da sautin kuka. Ficewa daga gidan AbdulKadir yayi dan baida amsar ba Hajja, bayason kukan banza marar dalili, Fajr ya cika rigima har ta banza, inda Hajja tasan dukan da yake sha da ba zatai magana dan ya mare shi ba. Daya dawo masallaci ma ruwan shayi kawai ya iya sha, dan ko yunwar ma bayaji, tukunna yaima Hajja sallama ya sake ficewa ya shiga motar shi yana nufar gida. * Ba zatace ga iya lokacin da ta dauka a kofar gidan ba, zafin ranar da ake kwallawa shi yasa ta yanke hukuncin takawa zuwa bakin hanya ta tare wata napep din ta shiga zuwa gidan su. Lokaci zuwa lokaci take saka hannu tana share kwallar dake zubo mata. Bayan kayanta da aka gudu dasu, tasan akwai wani abin da yake nuqurqusarta da bata son tsawaita tunani a kai. Dari biyu ta ba mai adaidaita sahun tana wucewa ta shiga gida da sallamar da Mama ta amsa mata. Tana zaune kan kujera a kofar daki tana tsintar shinkafa. "Ki dauko tabarma mana" Mama tace mata ganin Nuriyya din na shirin zama kasa kan siminti, batayi musu ba ta shiga daki ta dauko tabarma tazo ta shimfida. Gaisawa sukayi, Mama taci gaba da tsintar shinkafarta batare da ta ko kalli inda Nuriyyar take ba, ballantana kuma tace mata wani abu. Gabaki daya jikinta Nuriyya taji ya kara mutuwa, wasu sabbin hawayen na kara zubo mata da ba zatace ga dalilinsu ba. "Mama ya sakeni, AbdulKadir ya sakeni" Ta furta wani abu na tasowa daga dan yatsan kafarta yana zuwa kirjinta ya samu wajen zama. Sosai yanzun abinda hakan yake nufi ke zauna mata, ga yunwar azumin dake bakinta data fara kulle mata ciki, ga shinkafar da taga Mamar na tsinta ta kuma tabbar da ita dince abincin buda bakinsu, sai dan kunu da kosai da ba kullum ake samu ba. Da yanzun tana daki a kwance da fanka in sun kawo wuta, komin ta lalace kuma akwai nama a fridge dinta, ko soyawa zata iya yi. Watanta kusan tara rabonta da shinkafar hausa. "Allah ya rufa asiri ya kyauta" Mama ta fadi tana mikewa da farantinta takai dan karamin kitchen din gidan ta ajiye. Itacen ta iza tana bude waken taga ko alamar dahuwa baiyi ba, shisa ta dora shi da wuri inta dafa saita ajiye. Anjima ruwa zata kara daya tafaso ta zuba shinkafa. Badan tayiwa auren Nuriyya da AbdulKadir din baki ba, amman har a kasan ranta taji alamun babu inda zaije, ko badan auren cin amana bane, Nuriyya na da son zuciya da son abin duniya da in batai wasa ba zai hanata zaman aure, dan zata cigaba da gina aurenta akan hakan, duk namijin daya gane kuwa da wahalar gaske yaci gaba da zama da ita. Hidimarta Mama ta karasa ta shige daki tana barin Nuriyya anan zaune, ganin hakan yasa itama ta tashi tana komawa dakinta na da, yana nan yanda yake babu abinda ya canza, banda yan kayan sawa da aka ajiye. Ta kuma san na Mama ne, tunda ita bata da yara mata, nata duk mazane, dakin su kuma daban yake. Jakarta ta ajiye ta samu waje kan katifa tana kwanciya, a jikinta take jin banbancin katifar da ta gidan AbdulKadir. Wasu sabbin hawayen na sake silalo mata, musamman da tunanin Waheedah nacan kwance a daki tana jin dadin tabar mata gidan, sai taji wani malolon bakin ciki ya taso mata kamar zata hadiyi zuciya ta mutu ta huta. Kafin yamma wani zazzabin tashin hankali ya rufe ta, banda tsinuwa da fatan tifa ta take mai napep din da yai mata dibar albarka babu abinda takeyi. Ga kuma tashin hankalin abinda zai faru idan Baba ya dawo gidan ya ganta, dan sosai kashedin shi yake dawo mata. Ita kam bataga inda zata fara zuwa ba a yanzun, bata da wani waje daya wuce nan din, haka ta wuni juye-juye. Ta kulla ta saka, hadi da addu'o'i kala-kala, cikin su harda na samun mijin da yafi AbdulKadir komai tana gama iddarta tayi aure inda zata huta ta shakata, amman tasan hakan bazai yiwu babu suttura ba. Ta yanke hukuncin siyar da duka kayan kitchen dinta, ta siyi kaya saita ajiye sauran kudin tana kashewa a hankali kafin ta samu garan da zata wanka. Wannan tunanin shiya nutsar da ita har aka kira sallar Magriba, tukunna ta fito daga dakin tayi alwala tana sake komawa, sanda ta idar da sallah, Mama ta kawo mata kunu da kosai da taketa jin kamshin shi tana kwance, hakan ya tabbatar mata da ba siyowa akayi ba, Mama ta soya da kanta. Ci tayi dan ya mata dadi sosai, rabon da taci abu mai nutsuwar wannan tun girkin Waheedah. Tas ta shanye kunun ma da yasha kayan kamshi ta samu waje ta zauna, wata nutsuwa da koshine kadai ke samar da ita na saukar mata. Tanajin sallamar Baba taji hanjin cikinta ya hautsina, komai ya tsaya mata. Tashi zaune tayi, daman dakin fitilar wayarta ce ta haska, itama kashewa tayi, tai zaune cikin duhun tanajin zazzabinta ya dawo sabo. Ba zatace ga iya lokacin da ta dauka a dakin ba kafin taji Baba na fadin "Auren ta kaso? Shine kika barta ta zauna mun a gida? Ban gaya mata ta nemi wani wajen ba?" Baba ya karasa maganar yana daga labulen dakin da Nuriyyar take ciki "Fito....aina fada miki idan kika kaso auren nan ki nemi wani wajen, na fada miki bazan kaffarar rantsuwa ta ba" Wani irin kuka Nuriyya take tunda Baba ya fara magana. Mama ce ta kama labulen daga hannun shi tana saukewa da fadin "Aikam hakuri zakayi kai azumin kaffara saboda babu inda zataje" Da matukar mamaki Baba yake kallon Mama, kai ta daga mishi, dan sosai iyaye suke wannan kuskuren, tasan bacin rai abune da ba'a iya guje mishi idan yazo. Amman bataga dalilin da zaisa iyaye su gindaya sharadi kan cewar idan yara suka tsallake su nemi wasu iyayen ko kuma su bar musu gida ba. Akwai dalilin da yasa Allah ya zabi ya basu amanar yaran, batace babu hakkin iyaye akan yaransu ba, amman akwai hakkin yara akan iyaye suma. Amana ce mai wahalar rikewa, amana ce da rikonta yake cike da kalubale kala-kala. Amman korar yara daga gida da nufin son su gane kuskurensu ba hanyar gyara bace ba, lokutta da dama hakan baya janyo komai banda kara lalacewar su, ga fushin iyaye da ko basu koresu ba zaici gaba da bibiyarsu har sai lokacin da suka furta sun yafe ko suka kudurta a ransu, ga tangaririya a filin duniya batare da tudun dafawa ba. Ba mata kadai hakan yake faruwa dasu ba, har mazan, da yawa in basu fada sace-sace dan su sami abin ciyar da kansu ba, zasu fara shaye-shaye dan rage damuwa, da duk wani abinki da zai iya fin wanda yai sanadin korar su daga gida muni. Akwai kaddarar da take tafiya da son zuciya, kamar ta Nuriyya, halin da take ciki laifinta ne, amman hakan baya nufin ba kaddararta bace ba. Da yawan mutanen da zasu zageta idan sunji halayenta marassa kyau su kansu basu wuce jaranta da irin kaddararta ba, bata saka musu baki a cikin al'amuran su, amman tana da yara, duk da maza ne, ba za'a hadu da ita ayi wannan kuskuren da Baba yake shirin yi ba "Ina kake so taje? Idan tabar gidan nan ina kake so taje? Bazan maka magana akan cewa hannunka baya rubewa ka yanke ka yarda ba, saboda ban taba yarda da wannan kalaman ba, lokacin da azaba zata isheka, idan baka roki wani ya yanke maka ba, zaka sami wuka ka yanke da kanka, neman sauki abune mai ban mamaki" Cewar Mama tana dorawa da "Amman nasan yara amana ne a wajen iyayen su, nasan idan tasa kafa ta fita daga gidan nan ka

Chapter 35 of 37