Share this page
rashin hankali take nuna mishi karara, zai nuna mata duk abinda takeji dai-dai yake da ita. Belt din da yake kafadunta na jakar goyon yake kokarin ballewa, ta ture hannun shi "Me kakeyi?" Ta tambaya muryata cike da tsoro, hannuwanta AbdulKadir ya kama duka biyun yana saka karfi ya rike su, belt din ya kwance duk ihun da Waheedah take mishi, da hannu daya ya zame Ikram yana sauketa daga jikin Waheedah din "Sadauki ka sakeni, dan Allah ka kyaleni, kaga Ikram na kuka" Waheedah ta karasa tanajin idanuwanta sun ciko da hawaye duk yanda ta fadama kanta ta gama yi mishi kuka "Ashe muryarki na sauka haka, harna manta saboda yanda kike dagamun ita a kwanakin nan" Cewar AbdulKadir din yana kama hannuwanta da yake rike dasu ya dagota ya mikar tsaye, zuwa lokacin ta daina kiciniyar kwacewa, dagata yayi yana sabata a kafadar shi kamar ya dibi kayan wanki, yasa hannuwan shi yana mata rikon da tasan ko da wasa ba zata iya kwacewa ba, ikon Allah take saurare kawai tana tabbar da AbdulKadir na da tabin hankali, bata sani bane tuntuni sai yanzun. "Wallahi ka saukeni, wannan kidnapping ne, shekara goma sha biyar zakayi a gidan yari" Dariya AbdulKadir yayi, wannan karin tana fitowa daga bangaren zuciyarshi daya kwana biyu baiji ya buga mishi ba. "Ka saukeni, bana son haka, ka saukeni...ko ka kaini ba zama zanyi ba Sadauki...na fada maka nagama aurenka" Hanyar da zata fitar dashi daga dakin ya nufa yana bude kofar yaci karo da Yassar da ya miko hannu da alama yana shirin kwankwasa kofar ne koya bude. Dan tunda ta shigo gidan yakejin kamar maganganu shisa ya nufo bangaren Waheedah din, muryarta na tabbatar mishi da AbdulKadir na ciki. Yanayin maganganunta ne ya hanashi bankada kofar kar yaga abinda bai kamata ba, tunda yasan AbdulKadir ba hankali gare shi ba ballantana kunya. Sai dai baki a bude yake kallon AbdulKadir din "Ka matsamun Hamma..." Ya fadi yana gyara ma Waheedah zama a kafadar shi "Me kakeyi AbdulKadir? Me kakeyi?" Yassar yake tambaya yana kallon AbdulKadir din kamar a film, dan bai taba ganin abinda yakeyi a zahiri ba, cikin kuka Waheedah take fadin "Hamma kace ya saukeni, dan Allah kayi mishi magana, ni bazan koma gidan shi ba..." Muryar Yassar har lokacin da mamaki yace "Ka sauketa AbdulKadir.... Ka sauketa tun kafin ranka ya baci" Kankance idanuwa AbdulKadir yayi "Ita tace in dauketa a kai in tafi da ita..." Waheedah najin hawayen dake digar mata, ga kanta daya fara tara jini saboda yanayin yanda AbdulKadir din ya riketa "Ni bance mai ba Hamma... Dan Allah kace ya saukeni" Kokari Yassar yakeyi kar murmushi ya kwace mishi, idan AbdulKadir yaga alamar wasa koya take tattare da Yassar din bazai sauke Waheedah ba "Ka sauketa nace maka AbdulKadir..." Baisan ya akayi maganar Yassar din tayi tasiri akan shi ba. Sauketa yayi tana dafa kofar wajen jin zata fadi, tana tsayuwa sosai tasa hannu tana goge fuskarta, dankwalinta batasan ma lokacin daya fadi ba, ga wata irin matsananciyar kunyar Yassar din da ta kamata. Wani irin kallo ta watsa ma AbdulKadir din "Aurenka ko na zobe ne sai ka rabu dani... Kuma wallahi saina fadama Abba" Ta karashe maganar wasu hawayen takaici masu zafi na zubo mata. AbdulKadir kuwa Yassar ya kalla "Kagani ko? Hamma kanajin irin rashin kunyar da take mun" Hannu Yassar ya daga mishi "Ka wuce ka tafi" Kafada AbdulKadir ya makale "Ni bangama magana da ita ba" Kai Yassar ya girgiza yana sauke numfashi, so yake yabar wajen kafin dariya ta kwace mishi. "Ka tabbata zakai mata magana kamar mai hankali?" Kai AbdulKadir din ya daga mishi, saida Yassar din yadan tsaya tukunna ya juya. Kofar AbdulKadir ya tura yana mayar da hankalin shi kan Waheedah data dauki Ikram tana kokarin lallashin ta "Babu ribar da zakici a fada dani Waheedah... Ki taho mu koma gida, na baki hakuri.. Kiyi hakuri dan Allah. Kizo mu koma... Kinga ni bana son yin fada dake" Ya karasa maganar yana sauke muryarshi, amman a idanuwanta yake ganin yanda maganganun shi ko kadan basuyi tasiri ba, ci gaba yai da fadin "Kinji Wahee... Kina ta dagamun hankali akan magana karama, Wallahi kwanana biyar a barikin sojojin garin nan, ki kalli fuskata, na manta rabona da wadataccen bacci balle abincin kirki..." Yayi maganar yana kama rigar jikin shi ya daga mata, jinine yayi baqiqirin a gefen cikin shi da duka hakarkarin shi, tana kallo ya juya mata har bayan shi da nan ma jinin ne a kwance, kowanne irin duka akai mishi ba karami bane ba, zuciyarta takeji a bushe babu wani abu da take sonyi banda shakar numfashi batare da igiyar auren shi ta daure mata wuya ba. Sakin rigar shi AbdulKadir yayi "Ban shigo da nufin yin fada dake ba, har kudin hidimar gida na tura miki dazun..." Kalamai yake nema da zai lallasheta dasu, amman ya rasa, saboda basu taba fada ya wuce yini daya ba, koyace bata taba fada dashi ya wuce yini daya ba, tunda ba biye mishu takeyi ba, ita ta saba lallashin shi, shisa komai ya kwance mishi. Takawa yayi ya karasa yana kamo dayan hannunta da yake jikin Ikram yana sakata sake rike yarinyar sosai "Kinga azumi ya kusa, saura kwanaki kadan, ana yafewa juna kafin azumi, bama kyau fada kafin azumi" Cikin idanuwan shi Waheedah ta kalla "Ka saukake mun kafin azumin...dan Allah Sadauki...kaji...ka sakeni in huta nima. Nagaji da auren ka" Ta karasa maganar tana zame hannunta daga cikin nashi ta share kwallar data zubo mata. Wani irin numfashi AbdulKadir ya sauke yana juyawa ya fice daga dakin, bai tsaya ko ina ba sai cikin motar shi, tayar da ita yayi ya fita daga gidan Yassar, a gefen hanya yayi parking yana hade kan shi da abin tuqin motar. Kan shi ciwo yake da bashida alaka da yunwa ko rashin bacci. Wani irin tsoro yakeji da bai taba sanin akwai shi ba. Kalaman Waheedah ke mishi yawo da wani yanayi naban mamaki. Batayi mishi maganar da hayaniya ba, asalima idanuwanta cike suke taf da hawaye, da neman alfarma, bata taba rokon wani abu a wajen shi ba, yaune yake ganin alamar tana rokon shi, kuma rokon farko daya shiga tsakanin su shine na ya rabata da auren shi, si take ya bude bakin shi ya furta mata kalaman da zasu warware igiyar da bai yarda an kullata tsakanin su ba saida nufin mutuwa ce kawai zata raba. Bai taba tunanin cewa zata roke shi wani abu da zai kasayi mata ba, kodan girman matsayinta a wajen shi, amman sai ta tambayeshi abinda yakejin duk duniya babu wanda ya isa ya sakashi yin shi. Wani irin tsoro yakeji daya danne duk wani abu da yake damun shi. Lumshe idanuwan shi yayi yana hango yin rayuwa babu Waheedah, da sauri ya bude su yana dagowa daga jikin motar, dan jin shi yayi duniyar tai mishi wani irin girma, ga kadaici naban mamaki daya lullubeshi. Da aurenta yasan akwai abinda babu a rayuwar shi sai bayan ta shigota, daga randa igiyar aure ta hadasu zama a karkashin inuwa daya bai kara hasko wani lokaci a rayuwar shi da babu ita a ciki ba. Ko tunanin mutuwa yake bai taba hango zata riga shi ba, abu ne da tunanin shi ma baya hasaso mishi. Film idan yana kallo indai za ai mutuwa, yafi son yaga mijinne ya mutu yabar matar, dan baisan yanda zaiyi da sauran rayuwar shi idan babu ita a ciki ba. "Bazan iya sakinki ba Waheedah... Ko meye nai miki me zafi haka hakuri zakiyi ki dawo. Inke zaki iya barina ni bazan iya barinki ba wallahi... Bazan iya ba" Ya karasa maganar yana dafa fuskarshi da duka hannuwan shi biyu. Yafi mintina talatin a cikin motar kafin ya tayar da ita yana nufar gida...! #TeamAbdulkadir #TeamWaheedah #LubnaSufyan [7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan IG: SufyanLubna Email: Calmlubna@gmail.com Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43 *ABDDULKADIR* *LubnaSufyan* 26 To UMMU ABDUL, Hajjan AbdulKadir, Chairlady ta yan Fikra, Tauraruwar MSU. Thank you, SonSo a ko da yaushe. Tun daya tunkari kofar yake jin kauri ya cika mishi hanci, yana bude kofar ya saka kafafuwan shi cikin falon Waheedah yakejin kaurin na karuwa, bangaren Nuriyya ya karasa yana ganin hayakin dayake fitowa daga kitchen din ya turnuqe falon, gaban shi yaji yayi wata irin mummunar faduwa, da gudu ya shiga kitchen din, hayakin na shaqe mishi kafofin shige da ficen iska, yana soma tari, ta inda kaurin yake fitowa AbdulKadir ke nema. Kafin idanuwan shi sukai kan tukunyar da tayi wani irin baki. Hannu yakai yana kashe gas din ya fito daga kitchen din yana takawa zuwa dakin baccin Nuriyya. Tunda AbdulKadir din ya fita, ta tashi tana dora ruwa ta zuba shinkafa a ciki dan ita ba tsayawa zatayi sai ruwan yayi zafi ba. Dawowa tayi ta dauki wayarta tana ganin text, dubawa tayi taga dubu arba'in, murmushi tayi hankalinta da yake a tashe taji ya kwanta. Daman ko da AbdulKadir din bai dawo ba ita ba tunanin abinda ya same shi ko abinda ake mishi ne a gabanta ba, tunanin abinda zai mata idan ya dawo shine matsalarta, tunda kuma ya tura mata kudi kamar yanda yakanyi duk wata, hakan na nuna alamar babu abinda zai faru. Ko fadama bai mata ba, shisa ta wuce dakin baccin. Akwai wasu takalma da aka turo a group dinsu na mata da kawarta Safara'u ta sakata ciki, takalman sun mata kyau, har ta private Safara'u tai mata magana ko zata siya, sai dai ta kashe kudin hannunta tas, tayi niyyar ta nunama AbdulKadir din daman inya kwana biyu ya huta, sai ga Waheedah tazo tana asibiti ita kuma. Batasan cutar da har yanzun take damunta da bata warke bama, takalmin tace tana so dubu bakwai da dari biyar, ta tura kudin, saita turama Safara'u balance din atamfofin da ta dauka wancen watan dubu goma, ta kuma turama mai dinkinta shima dubu goma. Kafin wani lokaci dubu hudu ce ta rage mata a banki. Kwanciya tayi kan gadon da yake a hargitse tana manta cewar ta dora wani girki tunda ba sabawa tayi ba. Hankalinta ya nutsu kan littafin DAN ADAM na Rufaida Omar da take karantawa, dan littafin saika nutsu zaka fahimce shi yanda ya kamata. Ranta kal take jin shi, ko kadan bataji shigowar AbdulKadir daya nutsar da hankalin shi kanta ba, ya dauka ma wani abinne ya sameta harta dora girki yai wannan kamun ko kaurin shi bataji ba. "Nuriyya..." AbdulKadir ya kira ranshi a matukar bace, da alama batama jishi ba, dan tayi rufda cikine da waya rike a hannunta "Nuriyya!" Ya sake kira da karfi wannan karin yana sakata juyowa a tsorace, ganin shine yasa ta tashi zaune tana ajiye wayar hadi da fadin "Sannu da zuwa" Da idanuwa AbdulKadir ya kafeta "Bakida hankali ko? Baki da hankali zaki dora girki ki dawo daki ki zauna kina danna waya. Gobara kike son ki hadamun a gida Nuriyya?" Gabanta ne yai wata irin mummunar faduwa tana mikewa tsaye "Ina zakije?" AbdulKadir ya bukata "Wallahi na manta ne" Ta amsa tana wani irin sauke murya da ya kara bata mishi rai "Saboda girkin bashi bane a gabanki, ya zaki dora girki har yai wannan konewar kina fadamun kin manta" Idanuwanta Nuriyya taji sun ciko da hawaye, ta manta ranar karshe da aka tusata gaba ana mata fada haka, daman shine in yana nan baya rasa abinda zatayi da zai mata fada. "Masoyi mantuwa ce, kowa nayi kuma" Idanuwan shi AbdulKadir ya kankance a kanta, yanajin yanda ranshi yake kara baci, bazai dauki wata rashin kunyar bayan wadda Waheedah ta gama sauke mishi ba. Karasawa yayi ya kama hannunta yana fara janta zuwa hanyar da zata fita dasu daga dakin, binshi kawai Nuriyya take har kitchen din tana ganin hayakin da har lokacin bai gama fita ba "Meye a hancinki? Danna waya yafi miki muhimmanci, ki kalli kitchen dinki, yaushe rabonki da shara Nuriyya? Wanke-wanke fa?" Hannunta daya damka take murzawa da dayan, tana jin wani hawaye mai dumi ya zubo mata "Karki mun kukan banza da bashida dalili wallahi..." AbdulKadir din ya fada, dan bayason kukan banza. Rabata yayi ya wuce yana fita daga kitchen din, daki ya koma ya shiga bandaki, yana ganin yanda farin tiles din yai duqun-duqun, bangon har wani dallakin daudar da baisan ko tun ta yaushe bace ba, ga kayan wanki kaca-kaca. Tsintar kanshi yayi da kasa amfani da bandakin, ya fito yana ganin bedroom dinma a hargitse. Kai kawai ya girgiza yana tunanin kalar Nuriyya, inda zaman kallone ko danna waya babu wanda zai nuna mata. Bangaren Waheedah ya wuce yana shiga bandakin ya gama abinda zaiyi ya fito. Bangaren Nuriyyan ya koma ya zauna a falo yana dora kafafuwan shi kan kujera dan jin kasar da yake takawa kan kafet din. Yanajin kacafniyar kwanoninta a kitchen din. Da alama wanke-wanke take, aikam abinda takeyi kenan, ranta a bace yake, batasan yanda zata sake mishi maganar yar aiki ba, idan azumi yazo mata Waheedah bata dawo ba ta gama yawo tasani. Kugunta taji ya gaji lokacin data gama tana share kitchen din, fitowa tayi ta samu AbdulKadir din a zaune "Yunwa nakeji nikam" Ya fadi yana kallonta, dan zaman da yayi waje daya yasa yunwar taso mishi. Nuriyya kamar zatayi kuka tace "Nikam me zan baka? Kaga abincin ne na dora ya kama, ko zaka yo mana takeaway?" Kai ya girgiza mata, yanda yakeji bazai iya fita ba "Ko indomie ki dafa mun, bazan iya fita ba Nuriyya" Robobin lemukan ta karasa tsincewa dana ruwa tan komawa kitchen din, ranta inyai dubu ya gama baci. Ita har ranta batayi niyyar cin indomie ba, batama tunanin tana da indomie din, dubawa tayi, sauran data rage matace ta dafa jiya. Fitowa tayi tana kallon AbdulKadir din, muryarta can kasan makoshi tace "Babu indomie" Juyawa yayi yana kallonta da mamaki "Baki siya bane wancen watan?" Kai Nuriyya ta girgiza mishi, ita wancen watan kudin da ya batane gabaki daya ta tattara ta siyi zobon gwal karami, dubu biyu kawai ta cika. Babu abinda ta siya, ta dauka ma shi zai siyo musu. "Ki duba kitchen din Waheedah" AbdulKadir din ya fadi da alamar gajiya a muryarshi. Wucewa tayi ta dibo indomie din guda hudu ta dawo "Masoyi" Ta kira tana dorawa da "Yaushe Waheedah zata dawo? Jikinne har yanzun?" Kai AbdulKadir ya jinjina mata "Zata dawo, tana gida....data kara warwarewa" Wucewa Nuriyya tayi batare da tace mishi komai ba. Ranta ya kara baci ba kadan ba, ashe gida Waheedah ta wuce abinta saboda bakin hali. Nan da nan ta dafa indomie din, dan zatace duk a abinci ita kadai take dafawa babu wata matsala, a plate ta zubo musu ta saka cokula tana fitowa da ita ta ajiye, cokalin AbdulKadir ya dauka, duk yunwar da yakeji bata hanashi fadin "Baki dafa mana kwai ba? Haka zamu ci?" Batare da Nuriyya ta kalle shi ba tace "Banda kwai ni" Da alamar kosawa a muryarta, ta kula ba a iyama AbdulKadir din, ta samu waje ta zauna "In zakiyi mana siyayyar azumi ki siyo mana, ina so ni fa" Cewar AbdulKadir din yana fara dibo indomie din da tai mishi zafi yana jira ta huce, kallon shi Nuriyya take cike da rashin fahimta "Bakai zaka siyo ba?" Kai AbdulKadir ya girgiza mata "Me yasa zan tura miki kudin idan ni zan siyo" Hanjin cikinta Nuriyya taji sun tattaru sun kulle waje daya "Wanne kudin?" Ta tambaya cikin bayanannen tashin hankali, indomie din daya dibo yakai bakin shi ya tauna yana hadiye tukunna ya kalli Nuriyya "Na tura miki dubu arba'in dazun, baki gani bane?" Kai Nuriyya ta daga dan dakyar ta hadiye indomie din dake bakinta "Na siyayya ne daman?" Cikin rashin fahimta AbdulKadir yake kallonta kafin yace "Nuriyya..." Saboda yanayinta daya gani duk ta daburce, ya kirata ne yana tambayar ko lafiyarta, amman ita bata fahimce shi ba, ta dauka koya gane bata da gaskiya ne "Wallahi bansan na siyayyar azumi bane Masoyi, nasan kana bani kyautar kudi" Kallon nata AbdulKadir yakeyi, yana son fahimtar inda kalamanta suka dosa, kallon ne takejin yana kara rikitata "Na siyi takalma a ciki, daman wancen watan akwai atamfofin dana dauka, shine na cika kudin.... Saina biya kudin dinki kuma" Cokalin AbdulKadir ya ajiye cikin abincin yana kallon Nuriyya "Bangane me kike cemun ba, kudin dana tura miki dazun dinne kika siyi su takalma da atamfofi?" Kai Nuriyya ta daga mishi, cikin tashin hankali take fadin "Dan Allah kayi hakuri, wallahi bansan na siyayya bane" Kallonta AbdulKadir yake yana rasa abinda ya kamata yayi, ranshi da yake kokarin kwantarwa ne Nuriyya take ta batawa tunda ya shigo. Tsaye yake akan gidan shi, indai kayan sawa ne duk bayan wata biyu ko uku yake ba Waheedah kudi ko zata siya, itama Nuriyyar ya fara bayan watanta biyu da zuwa, to tana yawan tambayar shi kudi, ko zatayi ankon suna kona bikin kawayenta, ko zata siyi wani abin, shisa ya daina bata. Akwai kudin daya ware na siyayyar kayan sallar su daman. "Kudin kayan abincinne kika siyi takalma dasu Nuriyya? Abinda duk nake miki bai isheki ba saikin tabamun wannan kudin?" Kai Nuriyya ta girgiza mishi "Baki da takalma? Baki da kayan sawa? Kin tambayeni kudin takalma na hanaki ne?" AbdulKadir yake tambaya yana kallonta, kai kawai take girgiza mishi, mikewa AbdulKadir yayi abincin gabaki daya ya fita daga ranshi, itama Nuriyyar mikewa tayi tana dana sanin fada mishi, hannun shi zata kama yace "In kika tabani saina mareki Nuriyya..." Tsaye tayi tana zare idanuwanta da suke cike da rashin gaskiya "Yau ya zama ranar karshe da zakimun amfani da kudin hidimar gida kan wani abu daban, wallahi ranki zai mugun baci tunda naga alama ke baki da hankali" AbdulKadir ya karasa maganar ranshi a bace "Dan Allah kayi hakuri" Nuriyya ta fadi, wani irin kallo AbdulKadir din ya watsa mata, hakurin da take bashi ne yakejin yana kara bata mishi rai, wucewa yayi yana komawa bangaren Waheedah, dan idan yana ganin Nuriyya komai zai iya faruwa. Kan kujera ya kwanta yana lumshe idanuwan shi. Da Waheedah na nan ma koyayane zuciyarshi zatai sanyi, amman tayi tafiyarta saboda ta daina damuwa dashi, abinda yafi tsana fiye da komai ya tsinci kanshi tsundum a ciki, tunanin safiyar ranar da sukayi fada da ita. * Kwanan shi biyu da zuwa, yana kula da yanayinta tunda yazo. Shirunta ya mishi yawa, bai dai tambaya ba sai safiyar ranar tana kitchen tana soya musu fanke ya shiga yai tsaye yana jingina bayan shi da kantar kitchen din "Wahee me yake damun ki?" Ya tambaya, da wani nisantaccen yanayi a fuskarta ta girgiza mishi kai "Lafiya ta kalau" Ta fadi tana cigaba da aikinta, da idanuwa AbdulKadir din yake binta harta gama ta dauki kulolin tana wucewa falo. Har suka karya idanuwan shi na kanta, shirun nata tabashi yake har kasan zuciyarshi, ranar ta karbi girki, tunda hutu zaiyi kwanan shi biyu a wajen Nuriyya. Sake binta kitchen yayi ya samu tana wanke-wanke "Shirunki yamun yawa" Batare da ta kalle shi ba ta amsa a takaice "Babu komai" Kasa fita yayi daga kitchen din harta gama wanke-wanke tana goge kitchen din, ta dauki karamin towel na goge-goge ta sake fitowa falo, AbdulKadir din na binta. Tana jin shi, batada abinda zatace mishi, bata kuma jin yin surutun, yana tsaye Nuriyya ta fito tana fadin "Masoyi..." Goge-gogenta Waheedah ta cigaba dayi duk da zuciyarta da takejin kamar zata bude kirjinta ta fito, ta gefen idanuwanta taga Nuriyyar ta karaso ta kama hannun AbdulKadir din tana saka wani irin tukukin kishi taso mata. Batasan me suke cewa ba saboda zafin da kirjinta yakeyi ya dauke mata hankali daga kan su. Bayau ta fara gani ba, wani lokaci suna zaune a kujera Nuriyyar zata fito daga bangarenta tazo ta zauna gefen AbdulKadir din, ko ta kwantar da kanta a jikin shi, ko ta rike hannun shi, duk wani abu da jikinsu zai hadu a gaban Waheedah din ta kula shi takeyi. Bata taba daga kai ta kalle su ba, ballantana tayi magana, tasan idan aka tsaya tambayarta kalar soyayyar da take yiwa AbdulKadir ba zata iya misaltata ba. Sai dai koda wasa batayi tunanin tana da zafin kishi ba sai da taga Nuriyya a kusa da shi. Bata kara sanin zafin kishinta ya girmama ba sai lokacin da AbdulKadir din ya fara mata hirar Nuriyya da batason ji, baya kuma kula da bata tanka mishi duk idan yanayi. Ko film take kallo in sun kalla da Nuriyya saiya fara bata labari har abinda Nuriyya din ta fada kan film din. Babu abinda tagaji dashi sai yanda ran girkinta ko ba ranar girkinta ba sai dai tagansu a bangarenta zaune suna jira tagama girki suci, idan girkin Nuriyya dinne ma inta zuba musu tare suke ci mata abinci a falo. Bata taba jin tagaji dasu biyun ba irin wannan karin, daga Nuriyyar har shi AbdulKadir din daya kwaso mata ita ya ajiye mata a gida tagaji dasu, ko ganin su bata son yi. Ji take idan bata dan fita tasha iska koyaya ba komai zai iya faruwa. Tanajin kamar daga randa Nuriyya ta shigo gidan wani abu mai kama da bomb ya kunnu a cikin jikinta, abinda ganin Nuriyyar da AbdulKadir ke karama gudun lokacin fashewa, yanzun tanajin yana gab da tarwatsewa kuma ba zaiyi kyau ba. Muryar AbdulKadir din taji yana fadin "Wai zata fitane da, kuma ta fasa" Dagowa Waheedah tayi tana kallon shi, kafin taji Fajr ya riko mata hannu "Omma banga socks ba, nasa uniform din" Kai ta jinjina mishi "Zan duba idan na shiga daki Fajr" Sakin hannunta yaron yayi yana komawa kan kujera inda ta kwantar da Ikram "Karka tasar mun yarinya bangama aikina ba" Tace mishi, hakan yasa shi matsawa gefe ya zauna. Hankalinta ta mayar kan AbdulKadir "Zanje gida anjima..." Tana kallon yanda yake girgiza mata kai tun kafin ta karasa maganar "Zaki barni ni kadai... A'a kam, ba yau ba Wahee" Cikin idanuwa ta kalle shi wannan karin "Ni ina so inje, dan Allah kabarni" Ta karasa maganar wani abu na mata tsaye a makoshi, kai AbdulKadir ya kara girgiza mata "Karma mu fara jan maganar nan, ba zakije ba" Hawaye taji sun cika mata idanuwa da take da tabbacin basu da alaka da hanata fita da yayi, kawai tagajine har cikin kasusuwan jikinta "Gaskiya Sadauki sai naje... Ina so inje gida nikam" Da bayanannen mamaki a fuskar shi AbdulKadir yake kallon ta, bata taba mishi magana da wannan yanayin ba, baya kuma son ta fara "Ba zakije ba to" Ya fadi yana kankance mata idanuwanshi, sai dai rikicin da yake cikin nata yafi nashi "Zamu gani" Ta fadi tana juyawa da nufin komawa kitchen ta wanke towel din da yake hannunta "Me kika ce?" AbdulKadir din ya tambaya ranshi a bace, juyowa tayi tana saka idanuwanta cikin nashi "Kajini ai, ca nayi zamu gani" Murmushi AbdulKadir yayi me sauti "Zamu ga me?" Ya tambaya, wuce shi Waheedah tayi ta ajiye towel din tana fitowa, bataso kome takeji ya tarwatse mata cikin gidan. Ta gaban AbdulKadir din tazo wucewa "Bafa inda zakije Waheedah...kinjini ai" Ikram ta gyarama kwanciya, ganin kamar zata fado tana cewa "Sai kai tayi kuma" Sosai AbdulKadir yake kallonta "Rashin kunya zakimun Waheedah?" Ya tambaya yanajin kanshi har dumi yake dauka saboda bacin rai, dagowa tayi tana matsowa kusa dashi "Idan rashin kunya nai maka me zai faru?" Mamakin da yakeji ne yake kokarin danne yanda ranshi yake tafasa, da za'a tambayeshi zaice babu rana daya da Waheedah zata iya daga mishi murya balle harta kalli cikin idanuwan shi tana fada mishi magana. Murmushin takaici ya sake kwace mishi, juyawa yayi da nufin yabar mata dakin, dan komai zai iya faruwa yaji tace "Na dauka wani abin zakayi ai..." Baisan me ya shiga kanta haka ba, har tambayarta yayi da yaga kamar wani abin yana damunta tace mishi bakomai "Waheedah ki kiyayeni, Allah ki kiyayeni, karkice zaki fara mun rashin kunya. Gidane ba zakije ba, duk kwanan nan ma babu inda zakije, ba gida kawai ba ko ina ne ma" Dariya Waheedah tayi da take nuna mishi shidin bai isa ba, tana kara bata mishi rai "Lallai..." Ta fadi tana sakeyin wata dariyar, runtsa idanuwan shi yayi yana budesu a kanta, ranshi in yayi dubu a bace yake, ya manta ranar karshe da wani abu ya bata mishi rai irin hakan, bayajin ma a duniyar shi gabaki daya akwai wanda ya isa ya bata mishi rai har haka, sai dai ita din. "Ban isa ba kenan ko me kike son ce mun?" Ganin kallon da take mishi ya tabbatar mishi da abinda take nufi kenan "Waheedah..." Ya fadi cike da kashedi "Meye Sadauki? Nifa sai na fita, kaji na fada maka ma" Juyawar yayi yana soma tafiya, gidan zai bar mata gabaki daya, idan ya daina jin bazai dauke ta da mari ba sai ya dawo yaji ta inda rashin kunyar nan da ba halinta bane take fitowa. Bin shi Waheedah tayi tana riko hannun shi, in bata fita ta shaki wata iska daban da ta gidan ba tanajin matsala zata samu, kirjinta zafi yake "Kace mun inje ni dai, kaji... Dan Allah" Hannun shi ya zame daga cikin nata "Ki sakeni kafin in mareki" Wannan karin mamakine karara fuskar ta "Saboda zan fita shine zaka mareni? To ka mareni dan Allah... Ka mareni kaga in zai hanani fita" Hannun shi AbdulKadir ya zame yana ci gaba da tafiya, sake riko shi tayi, ko kadan baisan ya akai hannun shi ya sauka kan fuskarta ba yana hadawa da tureta, ya manta yanda ko kadan bata da kwarin kirki, kafin ya rikota takai kasa kanta na buguwa da table din da yake ajiye a wajen, lokacin dayai kasa yana rikota har jini ya fara taruwa inda da alama ta fasa kanta ne. A rikice yake girgizata "Waheedah...Waheedah..." Tunda yake a duniya bai tunanin zaiga tashin hankali kalar wanda yake gani yanzun da take rike a hannun shi kamar bata numfashi ba. Baiyi tunanin akwai abinda zai gigita shi kamar wannan gigitar ba, sai yanzun da yakejin duniyar ta hade mishi waje daya. * Gyara kwanciya yayi yana sauke wani irin numfashi, kuskurene yayi da baisan ta inda zai fara gyarashi ba, na lokacin ya manta yanda Waheedah matarshi ba kanwarshi ba, da tana kanwar shi har lokacin zai dauketa ya kaita asibiti, in taji sauki suka dawo gida zaisa

Chapter 27 of 37