Share this page
kewar shi na danne ta. Ga ranar Alhamis ce babu islamiyya balle taje ta rage zafi. Nuriyya kuma bata nan, taje wajen dangin mamanta sada zumunci. Kujera ta dauko ta saka a harabar gidan ta zauna, tunanin ya hadar mata biyu. Gana Abdulkadir, gana Nuriyya da takeyi, dan ta jima tana mata maganar tsoron faduwa jarabawar aji shidda, kasancewar makarantar gwamnatin ba wani tabbacin kirki gareta ba, duk da Nuriyya na da kokari, gashi tunda suka shiga aji hudu su biyun, banda darasin ingilishi da lissafi, babu abinda suke iya samu suyi ita da Nuriyyan, tunda ita Waheedah bangaren Art take, Nuriyyar kuma commerce, a cewarta tana son karantar bangaren kasuwanci dan tayi aiki da wani kamfani babba. Ita kuwa Waheedah turanci take son karanta, ta kuma koyar in ta samu hakan. To satin aka fara biyan jarabawar aji shiddan ta Waec, batasan ta inda zata fara yima Abba maganar Nuriyyan ba, saboda batason dora mishi nauyi fiye da wanda yake kan shi, amman ta tambayo wata makaranta da babu nisa dasu, Green olive, kudin jarabawar kuma kadan zai cika a wanda zai biya mata ita kadai a Sheikh Bashir su zana anan Green Olive din ita da Nuriyya. Kamar daga sama taji an tafa hannuwa a saitin fuskarta daya katse mata tunanin datai zurfi a ciki, tana sauke idanuwanta kan fuskar Yazid dake mata murmushi har dimple din gefen fuskar shi ya bayyana. Kaf dakin Hajja, har matan babu mai kyawun Yazid, ga sumar dake fuskar shi ta kara mishi wani kwarjini naban mamaki, abinka da wanda yake da haske fata "Hamma Yazid..." Waheedah ta fadi tana mayar mishi da murmushin da yake mata "Tunanin me kike haka?" Kai Waheedah ta girgiza mishi a hankali, daga mata girar shi duka biyun Yazid yayi, alamar bai yarda ba. Inda kujerun robar suke ya karasa yana dauko guda daya ya dawo da ita ya kusa da Waheedah ya zauna. "Bansan kanwar tawa da karya ba" A kunyace Waheedah ta sadda kanta kasa tana wasa da yatsunta, sosai yake jin kominta har ranshi. Shi ba mutum bane maison hayaniyar duniya, shisa jininsu ya hadu da Waheedah din, sanyin halinta ya mishi. "Kinsan zaki iya fadamun damuwarki ko?" Ya bukata a tausashe, numfashi Waheedah ta sauke "Da gaske babu komai Hamma" Kai Yazid ya girgiza mata "Aikam zamuyi fada yau" Dan murmushi Waheedah tayi "Ina son inma Abba magana ne, kuma ina jin nauyi" Sake gyara zaman shi Yazid yayi "To ni kimun maganar" Dagowa fuskarta tayi tana kallon yanda ya bata gabaki daya hankalin shi, idan wani yagani zai rantse bashida wani abu mai muhimmanci daya wuce saurarenta. "Ki fadamun Waheedah..." Ya umarta cikin yanayin dayasa ta fadin "Nuriyya ce daman, Waec din da aka fara registration, shine nake so ince ma Abba da kudin da zai biyamun a sheikh Bashir, in da hali ya cika saiya biya mana mu biyun muyi a Green Olive, nasu da sauki na tambayo" Murmushin shi Yazid ya fadada, ya dauka matsalar tata mai girma ce, kaunar da take ma Nuriyya na tsaya mishi a rai, yana musu addu'ar dorewar zumuncin su, dan kamar yanda rayuwa bata da tabbaci hakama mutanen cikinta sukan kasance, yana tsoron aminantaka irin haka, yana tsoron yai kusanci da mutane su shiga jikin shi su cutar dashi, dan yasan yana da raunin zuciya, ba komai yake da karfin dauka ba. "Su Green Olive din nawa ne?" Ya tambaya, cikin sanyin murya tace "Dubu talatin da uku" Kai Yazid ya jinjina yana mikewa tsaye hadi da fadin "Kiyi mata magana, ta shirya gobe in shaa Allah da na daukoku daga makaranta, kafin lokacin sallah yayi sai muje ni dake da ita Green Olive din muji ya abin zai kasance" Da wani irin murmushi da yasa zuciyar shi kumbura ta cika kirjin shi taf Waheedah ta kalle shi "Zakai ma Abban magana ne?" Kai Yazid ya girgiza mata, sosai yake jinta a ranshi har jikin shi yakejin yana daukar dumi da halin da zuciyarshi take ciki a kanta "Zan biya mata" Ware idanuwa Waheedah tayi da mamaki, kafin ta dago hannuwanta duka biyu tana rufe bakinta data bude cikin mamaki, kafin ta sauke su, tana sake kallon shi, dariya Yazid yake sosai "Ki fada mata yau dan ta zama cikin shiri, kina ji?" Yai maganar yana juyawa, farin cikin dake fuskarta zai jima yana tare dashi. "Hamma!" Waheedah ta kira tana jin yanda yagama mata komai a yar karamar duniyarta, idanuwanta cike taf da hawayen farin ciki take kallon Yazid daya juyo "Nagode da karamcinka... Nagode fiye da yanda zan iya fada da kalmar..." Kai kawai Yazid ya jinjina mata yana juyawa, yanzun kam yanda yake jin zuciyar shi a cike ba iya kirjin shi ta tsaya ba, har ko ina na jikin shi yake jinta. Da gaske yana son Waheedah, yana mata son da yake tunanin dakyar ya iya hakura ta karasa aji shiddan nan bai furta mata ba. Sai dai yana duba kankantar Waheedah din, yana ganin kamar yayi wuri, amman har Abba da bikinsu Babangida saida yai mishi magana cewar me yake jira? Idan aikine yana dashi, yana da muhallin dazai zauna tunda Allah yai mishi budi dai-dai gwargwado Kasancewarshi Engineer yana kuma aiki da kamfanin gine-gine babba da yake nan garin Kano. Bai fadama Abba cewar matar tashi a gida take ba, saboda yana son ya fara furta mata tukunna. Idan suka san wacece zasu daina mishi surutu kan aure, sosai yake jin lokacin da zata sani yayi. Da wannan tunanin a ranshi ya nufi bangaren su...! *#TeamAbdulKadir* *#TeamYazid* *#TeamWaheedah* *#AnaTare* *#FWA* [7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: ©️ 📖✏ FIKRA WRITER'S ASSOCIATION Facebook: Lubna Sufyan IG: SufyanLubna Email: Calmlubna@gmail.com *ABDDULKADIR* *LubnaSufyan* 11 Mami ce data fito daga daki ta kalli Waheedah da take kwance, tana murmushi tace "Ki tashi an kusan kiran sallah" Hannun kujerar Waheedah ta kama tana miqewa dakyar, kanta take jin kamar baya liqe da jikinta saboda rashin nauyin da yai mata. Tunda aka fara azumi babu wanda ya bata wahala kamar na karshen nan, ita bata damu da duk wani aikin gida ba. Amman tana azumi ace ta fita sosai take wahala. Gashi a dakinsu kowa zai sha ruwa ranar tunda girkin Mami ne. Amatullah da zata tayasu wani abin wuni tayi gidan kitso, bata jima da shigowa gidan ba. "Mami hanjina kamar an kwashe" Waheedah ta fadi tana taba cikinta da yake a shafe. Dariya Mami tayi "Idan wani yaji saiya dauka zakici wani abin kirki..." Kai Waheedah ta jinjina tana fadin "Haba ai yau yunwar da nakeji zan baku Mami" Murmushi kawai Mami tayi tana shiga kitchen ta dauko robar dabinon data dauraye ta fito da ita tana dorawa kan hannun kujera. Kitchen din ta sake komawa tana dauko babban kwanon tangaran din da yankakkun kayan marmari ne a cikinsu ta ajiye tsakiyar dakin. Ta miqa hannu ta dauko robar dabinon daga kan hannun kujera, samarin gidan na soma shigowa da sallama, dai-dai lokacin da aka kira sallah. Wasu dabinon kawai suka dauka suna ficewa daga dakin dan tafiya masallaci, Mami ma daki ta shige dan gabatar da sallar Magrib. Dakyar Waheedah takai hannunta tana daukar kankana hadi dayin Bismillah tukunna ta saka a bakinta. Zata rantse da Allah inuwar shi ta banbanta da ta kowa, shekara daya da kwanaki "Assalamu alaikum..." Muryarshi ta daki kunnuwan ta, tana sa tari kwace mata saboda ruwan kankana da yabi mata ta hanyar da bata shirya ba, zuciyarta da take wani irin dokawa bata taimaki yanayin da take ciki ba. Yace mata zaizo da sallah, tun satin take baza ido ta inda zai bullo amman shiru, kallo daya Abdulkadir yai mata yana ganin yanda take tari sosai, takawa yayi zuwa kitchen yana dibo ruwa a cup ya dawo ya mika mata. Karba Waheedah tayi tana shan ruwan hadi da sake yin tari, tukunna tayi gyaran murya. Maqoshinta kamar zai ciro take jin shi. A hankali ta dago tana kallon Abdulkadir din da yake tsaye yana kallon ta, ta dauka akwai shekarun da mutum yake kaiwa ya daina kara tsayi ko girma, amman banda Abdulkadir din. Zata rantse yafi lokacin dayazo tsayi da girma. Kalar askin da yazo dashine wancen karin, jikinshi sanye da farar riga mai dogon hannu sai wando daya rufe gwiwar shi da kadan, baqi yana da igiyoyi daga jikin kafafuwan. Wani irin kyau yai mata har zuciyarta na matsewa waje daya. Hannu taga ya miqo mata, dube-dube take tana neman abinda zata bashi "Kofin... Kiban kofin Waheedah..." Abdulkadir ya fadi a gajiye, babu abinda ya canza a tattare da ita, sai girma da ta kara mishi. Kofin ta miqa mishi ya karba yana wucewa ya mayar kitchen, yana fitowa hanyar kofa ya nufa, sai lokacin Waheedah ta samu bakinta ya motsa saboda wani irin yanayi da take ji da bazai misaltu ba "Baka dauki komai ba" Dawowa yayi ya dauki kankana guda daya yasa a bakinshi tukunna ya fice daga dakin. Cikin sanyin jiki Waheedah ta miqe daga falon, har wani zazzabi-zazzabi take ji yana shirin kamata, yanayi ne da kusanci da Abdulkadir ne kadai yake haifar mata dashi. Gama aji shidda, cin nasara a duk matakin da daliban da suke son samun gurbin karatu a jami'ar Bayero suke bukata baisa Abdulkadir yabar zuciyarta ko na minti daya ba. Bataji dadi ba da Nuriyya bata samu gurbin karatu a Bayero ba itama, sai nan Poly Abba yai mata cuku-cuku ta samu Business administration, kuma karfin karatun tun daga kan kudin makaranta da komai shiya fadama mahaifin Nuriyyan zai biya, hakan ba karamin zumunci ya kara tsakanin gidajen nasu ba. Su dukan su sai bayan sallar zasu fara registration. Zuwa yanzun tasan cewar son Abdulkadir din take, wani irin so take mishi da rashin algus din da yake ciki har mamaki yake bata. Son Abdulkadir take irin soyayyar da ta ginu domin Allah, soyayyar da babu wani tsammani a cikinta, soyayyar da take jin ko ta samu kwatankwacinta ko akasin hakan duk ba matsala bane ba, zuciyarta abu daya take gane mata, shine son Abdulkadir. Nuriyya kadai ta furta ma data kalleta sau daya tana ci gaba da abinda take a lokacin, bata sake mata maganar ba, itama kuma Nuriyyar bata tayar mata da zancen ba. Hakan yasa Waheedah dauka ko Nuriyya tana tunanin wasa take mata. Dakyar ta iya wucewa dakin su, inda ta samu Amatullah na sallah. Bandaki ta wuce itama ta gabatar da alwala, dakyar tayi gefe da tunanin Abdulkadir ta gabatar da sallar Magriba. Ko da ta fita falo duk suna nan, an cika falon ko ina tarkace ne ana hidimar shan ruwa. Kan kujera Waheedah ta zauna, Yazid na tashi daga inda yake ya koma kusa da ita, hannun shi riqe da kofin shayi "Na dauka ai ba zaki fito ba" Ya fadi yana kallon Waheedah, da tunda Mami ta aike su cefane da yamma take fada mishi yanda azumin yake wuju-wuju da ita. Murmushinta tai mishi da yake jin yana nutsar da wani abu da baisan a tashe yake ba cikin kirjin shi. Duk idan tai mishi murmushi haka yakan ji kamar ya bude bakin shi ya furta mata yanda ya gama tsara gabaki daya rayuwarshi da ita, amman ya rasa abinda yake danne shi, gani yake kamar har yanzun da sauran yarinta a tattare da Waheedah din, hakan kuma nada alaqa da tazarar shekarun da yake tsakanin su. Waheedah tasan ya kamata taci wani abu, amman idanuwanta kafe suke kan kofa tana jiran shigowar Abdulkadir 'Dan Allah Hamma baka shigo ina sallah ka sake ficewa ba. Dan Allah karkai mun haka, bamu gaisa ba, ban gaisheka ba' Take fadi cikin zuciyarta. Yazid fuskarta yake kallo yana tunanin abinda yasa ta nutsuwa haka "Waheedah..." Ya kira a hankali yana sata raba idanuwanta daga kan kofar tana sauke su akan shi "Kici wani abu... Tun dazun kike kiran yunwa" Batare da tace komai ba ta miqe tana nufar kitchen. Akwai wake da shinkafar da Mami tayi musu jiya, jallof ce tasha busashen kifi da nama, sosai tayi mata dadi shisa data rage ta kwashe ta saka a fridge. Daukowa tayi tana saka robar a microwave ta kunna dan ta dumama. Tsaye tai a kitchen din har saida ta fara jin kamshin abincin alamar yayi, ta fito da robar kenan taji muryar Abdulkadir "Menene kike dafawa? Ina ci..." Juyowa tayi da murmushi a fuskarta, tana jin kusancin shi fiye da tazarar dake tsakanin su, tana jin shi har kasan zuciyarta. "Hamma..." Kananun idanuwan shi ya kankance mata "Yaushe kazo? Ashe zaka zo" Numfashi Abdulkadir ya sauke yana amsa ta da "Banyi niyyar zuwa gida ba yanzun. Ba yanzun naso zuwa ba" Cike da rashin fahimta Waheedah take kallon shi, idanuwan shi daya sauke cikin nata na saka wani abu tsirga mata har tsakiyar kanta "Hamma..." Ta furta muryarta can kasan makoshi, kai Abdulkadir ya dan daga mata, da gaske yake har zuciyarshi, baiyi niyyar zuwa gida ba sam, saboda tunda ya tafi Nuriyya na manne a wani waje tare dashi, duk kokarin dayai na ganin ya cirota daga duk inda take maqale dashi ya kasa. Bakon abune a gurin shi, tun tasowar shi abinda duk yasa ranshi sai yayi shi yakeyi, ko da su Hajja zasu karya shine kuwa. Shisa kasa cire Nuriyyan yake bata mishi rai. Suna shawowa kwanar gida shi da Yassar da yaje ya dauko shi komai na sake danne shi. Saima daya fito daga mota yana sauke idanuwan shi kofar gidansu, da zuciyarshi a makoshi saboda dokawar da take ya shiga gida. Har yanzu kuma ranshi a bace yake jin shi, saboda bayason fara tunanin abinda mannewar da Nuriyya tai mishi yake nufi, sam bayaso, babu abinda hakan zai haifar mishi banda raini. Yana ganin yanda waje kadan Nuriyya take jira ta samu ta raina shi, ba sai an fada mishi ba, a yanayinta da fuskarta ya karanci akwai wannan halayyar a tare da ita. Shikam a duniya raini ne babban abinda bayaso, ko wanda suke da tazarar shekaru a tsakanin su bayaso su raina shi, shisa yake bala'in rike girman shi. Watan shi biyu da komawa Kaduna yaji yanda kwata-kwata bayason komawa Kano. Koda zai koma din banan kusa ba, a qalla ya kara daukar wasu shekara biyun tukunna, wataqila hoton Nuriyya ya disashe mishi daga cikin kai. Amman duk idan ya kwanta ya rufe idanuwanshi baya ganin komai sai fuskar Waheedah da alkawarin da yai mata na cewar zai zo hutun sallah. 'Da gaske zaka zo? Dan Allah kazo Hamma, kaji... Kazo dan Allah' Shine abinda yake mishi yawo duk lokacin dayai tunanin kin zuwa hutun sallar, ran shi a bace yake, baisan wazai dorama ba, shisa ya zabi ya raba bacin ran da ita, tunda itace dalilin sakashi dauko kafafuwan shi daga Kaduna zuwa Kano. "Ke kika sa nazo...alkawarin danai miki yasa ni zuwa. Jibi zan koma" Yai maganar, kallon da yake mata nasaka tajin wani radadi a kirjinta da ba zatace ga daga inda yake fito ba. Kallon ta yake yana dora mata laifin zuwan dayayi, duk da hakan bai hana zuciyarta jin dadin zuwan nashi ba, koba komai tagan shi. Amman ita bata ce yai mata alkawarin zaizo ba, batasan me yasa yake kallonta ba. "Ki bani abinci nikam" Abdulkadir yace yana dauke idanuwan shi daga kanta, bayason ganin yanda take kallon shi kamar tana son sanin dalilin dayasa yake dora laifin zuwan shi akanta. Bayan ita ce dalilin da yasa shi zuwan tun daga farko, da bata kalle shi da idanuwanta din nan ba, da bata kalle shi da farar fuskarta tasa shi alkawarin da yake dana sani ba, babu abinda zai kawo shi Kano. Sai dai bacin ran da yake ciki bashi da alaqa da abinci. Bai taba fushi da abincin ba, cikin shi daban, abinda yake faruwa dashi daban. Plate Waheedah ta dauko ta dauraye, gabaki daya wake da shinkafar ta juye mishi, tana kallon shi ya dauko cokali kafin ta gama zubawa. Mika mishi plate din tayi ya karba, yana shirin juyawa tayi saurin fadin "Hamma..." Sai dai sauran kalaman sun maqale mata, batama san me take shirin ce mishi ba, gashi ya kafeta da kananun idanuwan shi da suke rikita mata lissafi, kanta ta sauke kasa tana kallon kafafuwanta. Yakai mintina biyu a tsaye, ganin batada shirin magana yasa shi juyawa. Mami daya gani a falon zaune ya kalla da fadin "Sannu da shan ruwa" Da fara'a ta amsa shi tana dorawa da "Abdulkadir. Saukar yaushe?" Duk yanda yaso yayi murmushi ya kasa, ranshi a bace yake har lokacin, a gajiye yace "Dazun..." Kai Mami ta jinjina sanin halin Abdulkadir, wucewa yai abin shi, har ya kusa kofa yaji Yazid na tambayar "Yaushe kuka karaso?" Juyowa yayi yana kankance ido yace "Meka sa a kunnen ka?" Kai Yazid din ya girgiza mishi "Bansa komai ba" Ya amsa cike da rashin fahimtar tambayar Abdulkadir din "Me yasa kake tambayata abinda na amsa yanzun to? Salon in magana kace na maka rashin kunya?" Murmushi Mami tayi tana mishi addu'ar shiriya a ranta kafin ta mike tabar wajen. Ba za'ayi koma menene a gabanta ba. Hannuwa Yazid ya daga cikin nuna alamun saduda "Allah ya baka hakuri..." Juyawa Abdulkadir din yayi da shirin ficewa daga dakin, yaga Nabila tsaye a bakin kofa, taga alamar ranshi a bace yake, shisa tai tsaye dan kar ya sauke tambotsan akanta "Ubanki kike a bakin kofa?" Ya tambaya yana watsa mata harara, juyawa tayi da niyyar komawa inda ta fito, wani dogon tsaki Abdulkadir din yaja ya fice daga dakin yana nufar bangaren su. Nuriyya na manne dashi ya rasa yanda zai ya cirota, haushin kowa yake ji, komai yaci karo dashi qara bata mishi rai yake. Kofar dakinsu yagani adan bude, dubawa yayi yaga takalmine ya tokareta. Tsugunnawa yayi, plate dinshi a hannu daya, yasa dayan hannun ya dauko takalmin yana juyawa yai cilli dashi, kiris ya make Yasir da yake tahowa "Anzo an ajiye wani banzan takalmi salon sauro ya cika mana daki" Yake fadi shi kadai yana sauke numfashi. Karasowa Yasir yayi yana kallon ikon Allah "Kai kuma kaida wa? Kake ta huci kamar kububuwa" Batare da Abdulkadir ya juyo ba yace "Ban sani ba..." Ya wuce yana shigewa cikin dakin. Yasir baisan meyasa yanayin Abdulkadir din ya bashi dariya ba, dariya yake sosai a bakin kofar daya kasa karasa shiga ma. Har cikin ranshi Abdulkadir yake jin dariyar Yasir din, kofar dakinshi ya tura yana shiga hadi da rufeta da karfin gaske. Idan harya koma yaima Yasir magana fada zasuyi, yanda yake jin ranshi a bace, kan wanda zai huce yake nema. Abincin yacinye tas yasha ruwa, ganin idan ya zauna tunanin da baya buqata zai danne shi, fitowa yai ya tafi masallaci abinshi. * Kirjinta take ji kamar an dora dutse, tana isha'i ta wuce daki ta kwanta abinta, daya daga cikin hoton Abdulkadir din da yake cikin qaramin pillow dinta ta saka hannu ta zaro tana dubawa, shigowar Amatullah dakin yasata saurin mayar da hoton inda ta dauko shi. Waje Amatullah ta samu gefen gadon ta zauna tana ajiye robar dake hannunta a kasa tana fadin "Hajiya Adda ai saikin sauko kasa ko?" Cikin rashin fahimta Waheedah tace "In sauko kasa in miki me?" Ware idanuwa Amatullah tayi "Lallai Adda Wahee... Kunshin fa" Numfashi Waheedah ta sauke, sam ta manta da wani maganar kunshi, kitso daman Nuriyya tai mata, guda goma tace ma. Nuriyya bata saurareta ba tayi mata qanana duk da kan bawani gashin kirki yake dashi ba. Ba zata iya bin layin wani baqin qunshi ba, amman Amatullah ta iya jan lalle kala-kala, duka yan gidan ita tai musu. "Ni na manta da wani kunshi. Dakin barni Amatu, jikina ciwo yake mun" Tunda ta fara magana Amatullah ke girgiza mata kai "Wallahi baki isa ba Adda, tunda ba takaba kike ba. Lallena dana kwaba fa? Waye zai amfani dashi. Bama zai yiwu bane ba, har Mami tayi jan lalle....ni wallahi da ina da farin ki da anga lalle" Yar dariya Waheedah tayi, Amatullah din ba baqa bace, amman kuma ba zaka kirata fara ba, tana da hasken fata irin na yawancin yaran gidan Bugaje din. "Kifa sauko..." A kasalance Waheedah din ta sauko daga kan gadon. Tasan halin Amatullah idan ba'ayi kunshin ba fushi zata dauka da ita. Tsegumi kam sai kanta ya fara juyawa, gara tayi ta huta. Hira suke tabawa ita da Amatullah din har ta gama saka mata lallen a duka kafafuwa da hannuwanta, ita ta taimaka mata tahau kan gado ta kwanta, gabaki daya duniyar take ji ta tattaru a hannuwanta da kafafuwanta da suke a daure da ledoji. Ita kam bataga komai a cikin kunshi banda wahala ba. Batajin zata iya bacci da wannan ledojin a jikinta, da wannan tunanin bacci ya dauketa cike da mafarkin Abdulkadir. * Washegari kasancewar safiyar sallah, yanayin garin kanshi yayi sanyin da safiyar sallah ce kadai kan haifar. Tunda suka tashi suke hidimar su, Waheedah bata ga kunshin taba sosai saida gari ya fara wayewa tunda babu wutar lantarki. Kyau yai mata sosai, gashi ya kama har wani ruwan kasa-kasa mai cizawa yake. Da gudu ta taho tana rungume Amatullah da take tsaye ta baya "Kinsan ina son ki ba?" Ta fadi, Amatullah din na tureta "Soyayya da sokamun kasusuwa?" Dariya Waheedah tayi tana sake komawa ta riqe Amatullah din dake kiciniyar kwacewa gam "Adda Wahee mana" Amatullah ta fadi tana samu ta ture Waheedah din, da murmushi a fuskarta, Mami ce ta fito ta gansu "Mami kalli kunshina" Cewar Waheedah tana daga ma Mami hannuwanta, jinjina kai Mami tayi "Ma shaa Allah. Yayi kyau sosai kuwa, yanzun kika zama yan mata" Shagwabe fuska Waheedah tayi "Me kike nufi Mami?" Amatullah ta karbe zancen da amsa ta "Kinfi kowa sanin me take nufi" Numfashi Mami ta sauke "Nikam ku matsamun ina da aikin yi" Matsawar sukai ta wuce, suna rufa mata baya zuwa kitchen din. Wanke-wanke sukayi ita da Amatullah din. Sun gama kenan, Amatullah ta fice daga kitchen din, Nuriyya tai sallamar da Mami ta amsa mata tana dorawa da "Nuriyya idonki kenan?" Dariya Nuriyya tayi, dan kwana biyu bata shigo gidan ba, itama sunata hidimar sallah "Wallahi Mami inata kitso ne fa. Ina kwana" Murmushi Mami tayi "Lafiya kalau, ya kowa da kowa?" Da murmushi a fuskar Nuriyya take amsa Mami data fice daga kitchen din bayan sun gama gaisawa. Hijab dinta Nuriyya ta cire tana dorawa kan window din kitchen din, yanayin da yasa Waheedah kallon ta "Naga kin cire hijab" Kai Nuriyya ta jinjina "Bazan cire in sha iska ba?" Yar dariya Waheedah tayi, idan wani yaga Nuriyya ta cire hijabin zaiyi zaton aiki zata tayata, ita da yake tasan hali bata saka a rai ba, dan Allah ya zubama Nuriyya qwiya, ko aikin gida aka sakata sai ta zuba ha'inci a ciki, wani lokaci Maman su na kallonta zata tsallaketa tayi aikinta, a cewarta ko wanke-wanken Nuriyya ba fita suke ba, haka zakaga maiqo cikin kofuna. "Ke jiya Anas yazo da daddare, saima bayan isha'i tukunna" Nuriyya ta fadi wani tattausan murmushi na bayyana a fuskarta da yake nuna alamun Anas din ba karamar hidimta mata yayi ba. Sun hadu ne lokacin da suka kai mishi dinkin uniform din Nuriyya na Green Olive, Yazid ne ya hadasu dashi a cewar shi yakan mishi dinki wasu lokuttan, basu da nisa dashi sosai tunda suna kofar ruwa ne, shikuma yana Kurna babban layi ta wajen yan doya. Kusan tun lokacin ya manne ma Nuriyya, da yake ana barinta fita zance, sukam gidansu saika gama sakandire tukunna. Anas ya gama diploma dinshi a yanda Nuriyya take fadama Waheedah, sai dai baici gaba ba, shine babba a gidansu, kuma Allah yaima mahaifinshi rasuwa, hakan yasa yai tsaye kan sana'arshi ta dinki da take kawo mishi rufin asiri dai-dai gwargwado. Dan a cikin sana'ar yake ma kanshi da mahafiyarshi harma da yan uwanshi duk wata hidima, duk a yanda Nuriyya take sanar da ita, yana da gidanshi na gado mai daki falle-falle guda biyu, sai bandaki da kitchen, dan in yanzun Nuriyya ta bashi dama a shirye yake daya turo a tsayar da magana. Abinda baisani ba shine ko kadan Nuriyya bata jinshi a ranta, duk da Anas bashida wata makusa a matsayinshi na matashi, yana da kyau na misali da cikar zarrah, ga nutsuwa da kamala shimfide a fuskar shi. Ko kadan Anas ba tsarin aurenta bane ba, bashi bane mijin da take buri. Tana kulashi ne saboda hidimar da yake mata, hannun shi a bude yake, ko yaushe cikin mata hidima yake, sau biyu yakanzo a sati, duk zuwan da zaiyi da kalar kayan ciye-ciyen da zai kawo mata. Da sallar nan kaya yai mata kala uku, mayafi harda jaka da takalmi, shi yai mata dinkunan, ya kuma kawo dubu biyu ya bata tayi kitso da kunshi. Sosai Waheedah take son Nuriyya da Anas din saboda yanda yake da nutsuwa da kuma son Nuriyyan da take gani a tattare da yanayin shi. "Turarenki yana gida..." Nuriyya ta sake fadi tana yar dariya. Tana kara jin dadin yanda haduwa da Anas take bata damar yima Waheedah kyauta irin haka. "Dan Allah fa... Turare ya kawo miki?" Waheedah ta tambaya cike da jin dadi itama, kai Nuriyya ta daga mata "Har guda uku ma" Dan bude baki Waheedah tayi "Aikam baki isa ba saina zaba... Mai kamshin cikin nake so" Yar dariya Nuriyya tayi "Banza in munje gidan duk wanda kike so saiki ta dauka. Ina da wasu ai" Karasa share kitchen din Waheedah tayi suna hirar Anas din da Nuriyya "A fara poly Anas ya turo musha biki" Hade fuska Nuriyya tai waje daya "A'a kin manta, uwar biki zaku sha" Dariya Waheedah takeyi "Ki daina mun wannan wasan, nace miki ina son shine?" Kai Waheedah take girgiza mata "A'a amman kina karbe mishi kaya ai, wallahi Nuriyya kar Allah ya kamaki" Tsaki Nuriyya taja tana daukar hijab dinta daga kan kofa tana sa Waheedah tambayar ta "Ina zakije?" Ko kulata Nuriyya batai ba, ta saka hijab dinta, dan ta gama bata mata rai, wato fatan ta auri Anas take mata, dan karta huta. Ko a hanya aka ganta ansan batai kalar auren tela ba, diplomar da yake da ita ya fada mata bashida niyyar cigaba, tunda yana da tsayayyar sana'a, ita kam sai wanda yake zuwa office, babu abinda zatai da tela. "Hamma yazo..." Waheedah ta fadi cikin sanyin muryar da yasa zuciyar Nuriyya wani irin dokawa, da sauri ta juyo "Haba

Chapter 11 of 37