Share this page
a kasa. Akwai randa suna cikin waya amai ya taso mata, ta ajiye wayar, ashe yanata magana, sai da tagama aman ta dawo hayyacinta ta kira shi. "Wahee ban samu Hajja ba, na kira Abba amman, yace za'a turo wani" Babu kalar salatin da batayi ba, balbaleta da fadan shi yayi, me yasa bazai kira Abba ba, ai ba abin kunya bane ba, su da zasuje da baby gidan harma su bashi. Meye dan yasan babyn na hanya. Shiru tayi harya gama ya kashe kiran, tayi murmushi kawai. Rigimar shi babu kalar da bata sani ba, akwai kalar da ta kasa sabawa da itane har yanzun kawai. Nabila tazo tayi mata su shara da mopping, anan ta kwana, da safe ma sai da ta soya mata dankali da kwai tasa a kula, ta dafa ruwan zafi, har taliyar Hausa da Waheedah din tace tana so a bayar ai mata saida Nabila ta dafa mata, tukunna ta wuce gida. Da Fajr ta wuce, itama ta samu sauki. Tana da tabbacin dai AbdulKadir zaije ya dauko shi inya iso. Ta ga ma har goma da rabi, wayar shi take kira taji yana ina, in yabi motar dare da sassafe yake isowa. Taji sallamar shi, sanyi takeji saboda zazzabin da take ta fama dashi tunda dare, da ruwa mai zafi tayi wanka, amman duk da haka sanyi takeji. Wando ne a jikinta dogo, baqi, ta saka tshirt, ta dauki rigar sanyin AbdulKadir din ruwan toka mai hade da hula ta saka. Kalba ce manya a kanta da Nabila ta taimaka tayi mata, ko dankwali bata saka ba, hular rigar sanyi taja ta saka a kanta. Kafin ya bude kofar ta sakko daga kan gadon, a tsakiyar dakin suka hadu tana rungume shi, ya zagaya hannuwan shi a bayanta ya lumshe idanuwan shi, kamshin turarukanta sun canza mishi "Sannu da zuwa..." Ta fadi tana sake makalewa a jikin shi, wata irin kewar shi take ji tana danneta duk da yana tsaye a gabanta, tana jin dumin shi a jikinta "Turarenki ya canza mun" AbdulKadir yace maimakon ya amsa mata sannun da tayi mishi. Murmushi tayi, batasan kalar sabon da yayi da komai nata ba, da kuma kalar kula da yakeyi, ko a whatsapp suke chatting in yaga tana amsa shi kayi dai-dai sai ya fara tambaya me yai mata bata mishi hira. Bayaso yaga canji a tare da ita kowanne iri ne. Murmushi tayi "Akwai kamshin da bana so a wancen, shisa..." Dagota yayi daga jikin shi yana saka dayan hannun shi ya taba kuncinta dashi zuwa wuyanta. "Zazzabi kike ko? Ina hijab dinki muje asibiti" Kai take girgiza mishi tun kafin ya karasa maganar "Nasha paracetamol ai, zai tafi, yana mun haka wani lokacin" Kankance mata idanuwa AbdulKadir yayi "Waheedah..." Ya kira cike da alamar tambaya da rashin yarda da ita, yana kara taba jikinta, dariya tayi tana kama hannun shi ta sauke daga wuyanta "Da gaske" Numfashi yaja yana fitarwa "Nikam cikin Fajr ba haka yayi bafa, baki sha wahala da yawa ba..." Sanin halin shi yasa ta canza maganar da fadin "Abinci ko zaka fara watsa ruwa?" Dan jim yayi, dan yanajin yunwa sosai. Amman yafi so yaci a nutse, jakar daya dawo da itama a falo kan kujera ya ajiye. Tare suka shiga bandakin, ya korota karta taba ruwa tunda yaganta da rigar sanyi, ta mishi wani irin fayau, kamar cikin yasa ta kara haske sosai. Wanka yayi ya fito, kaya ma shiya dauko da kan shi, dan tana gefen gado ta zauna. Tare suka fita zuwa kitchen din, ya dauko mata kula da plate. Shayin shiya hada a kitchen ya fito dashi, ita ta zuba taliyarta da manja, tunda babu abinda ta iya sakama cikinta. Zama sukayi, AbdulKadir ya dan fara shan shayin da yake tunanin kamar ya mishi yawa ma, gashi sukarin baiji ba, Waheedah ita data zuba inya sha sai yaji yayi dai-dai. "Shayin salaf..." Ya fadi yana kara kurba "Baka zuba sukari ba?" Kankance mata idanuwa yayi "Na zuba" Taliyarta take cakudawa "Kaje ka kara..." Kafada ya makale mata, dan a gajiye yakejin shi, kuma zaman ya mishi dadi. Tashi tayi yaba binta da ido, ta dauko kwalin sikarin ta ajiye a gaban shi, kallonta ya sakeyi "Guda nawa zan saka" Dayan hannunta da babu manja ta saka ta dibi guda uku ta jefa mishi a kofin ta cakuda, dan gara mata Fajr da tabarar AbdulKadir lokutta da dama, sai da ya dauka ya kurba, tace mishi "Yayi?" Kai ya jinjina mata yana soma cin dankalin "Ni baki bani taliyar ba Waheedah..." Ta bakinta ta hadiye tukunna ta amsa shi "Sadauki taliyar hausa ce... Kwanaki dana dafa cakayi mun wacce irin taliya ce wannan?" Shayin shi ya sake kurba "Amman bance banaci ba ai, kuma wannan ba irin waccen bace, da manja fa, inata kallon ki tun dazun, baki bani ba. Kuma raina ya biya..." Murmushi tayi, ta tsame hannunta daga taliyar tana mika mishi kwanon, ita kenan Nabila ta dafa mata, dan bata dauka zaici ba, mikewa tayi ta wanko hannunta a kitchen ta dawo. Ta same shi ya cinye taliyar yana fadin "Ki kara dafa mana anjima.... Irin wannan" Kai ta jinjina mishi kawai, shiya kwashe kwanonin ya dawo. "Bacci nake ji" Ya karasa maganar yana mika mata hannun shi, ta kama tana mikewa. Ta riga tasan ko batajin bacci saita kwanta, rigimar AbdulKadir bata karewa, ko da Fajr na jariri haka ta dinga fama dasu biyun. Sai dai ta saka Fajr daga gefenta, AbdulKadir na bayanta. Dakinta suka wuce, duk da yana da nashi bangaren da bata ga amfanin shi ba, sai ta kwana hudu ma bata taka sashin ba, takan shiga ta share inyai kura, haka ya siyi gidan bangare biyu, dayan bangaren bai kai nan inda take girma ba, amman da falo da bedroom da bandaki, harda kitchen. Nata kuma bedroom biyune, kitchen harda store, kuma akwai bandakin baki daban ta cikin falon nata. Har kujeru da komai AbdulKadir ya zuba a dayan bangaren, kitchen dinne kawai babu komai, wasu lokuttan in yana nan, takan ja shi su shiga, su zauna, kafin aljanu su samu wajen labewa. Ko minti sha biyar ba suyi da kwanciya ba, bacci ya dauke shi, itama gyara kwanciyar ta tayi tana rufe nata idanuwan tana jiran bacci yai gaba da ita. * Bacci suka wuni yi, da sukai azahar ma komawa sukai har la'asar, garama AbdulKadir ace ramuwar bacci yake. Ita kam cikinne yake sakata wani irin bacci kamar kaza. Taliyar ta dafa musu suka ci. Suka zauna suna kallon wani indiyan film, gabaki daya AbdulKadir ya langabe mata, duk da zazzabin da take ji ya sauka, jikinta babu karfin kirki. Amman ya tattara kafafuwan shi ya dora kan kujerar dan ya kwanta a jikinta. "Ka karyani Sadauki... Sai ka huta kaga" Waheedah ta fadi jin yanda ya sake naniqe mata. Sake gyarawa yayi bai kulata ba, tunanin da bashi da daliline bayason yi. Nuriyya kuma ta addabi rayuwar shi, tunda ya shigo gidan ya kashe wayarshi ya ajiye. Yasan yana kunnawa zaici karo da sakkoninta. Baisan me take so dashi ba, bayan bata jira shi ba, aure tayi abinta ta kyale shi, tunda batasan tana son shi ba sai yanzun. Shisa bata samun amsar shi, bacin ran dayai tunanin ya binne a NDA ne ta taso mishi dashi gabaki daya. Bakuma yaso ana taso mishi da abinda ya rigada ta wuce shisa. Kusancin nan da Waheedah yasa yaji sanyi-sanyi. Tunda ya shigo ya dora idanuwanshi akanta cikin rigar shi da tayi mata yawa yaji komai ya kwance mishi. Nuriyya na manne cikin kan shi, amman Waheedah ta saka shi jin nutsuwar da ita kadai take saka shi samu. Saboda haka bazai kulata ba, ta saba cewa zai karyata daman, ko hannunta ya riko sai ta fara cewa zai karyata. Ko shi farkon auren su lallabata yake kamar yana tsoron da gasken zai karyata. Amman zai iya rantsewa daman can Waheedah din dan shi akayita. "Matar kowa daga kashin hakarkari ake cirota, na sha taba nawa hakarkarin Waheedah, kasusuwan nada kauri, ki kalleki dan Allah..." Ya taba ce mata, lokacin daya kamo damtsen hannunta yaji shi kamar babu tsoka a jiki, tayi dariya kamar me ranar, amman fuskar AbdulKadir din ko alamar murmushi babu, dan daga zuciyarshi yai maganar. Har saka mata ido yayi kan abinci, amman tanaci lafiya kalau, kawai jikin 'yan matan kenan. Yanzun daya gane ba zai karyata ba, shikenan kuma. Inma ta fada sai dai yayi dariya kawai. Ture shi Waheedah tayi tana mikewa ta nufi kitchen ganin biyar hartayi. Wake ta dibo ta dawo tana zama kan kafet hadi da fadin "Ta so ka tayani tsince wake..." Kafada ya maqale yana sake kwanciya cikin kujera "Ni kibarni... Nagaji. Jikina ciwo yake mun" Murmushi tayi, neman tsokana ne yasa ta cewa ya tayata din daman. "Ko zakaje kaci abinci a wajen Hajja?" Cike da rashin fahimta yake kallonta yana jiran karin bayani kan dalilin da zaisa yaje gida cin abinci bayan ga gidan shi, ganin tayi shiru yasa shi fadin "Saboda ban tsince wake ba shisa ba zaki bani abinci ba?" Dariya Waheedah takeyi tana girgiza mishi kai "Abincina yanzun da mai da yaji ne, ko kana so kaci da miya, ko kamshin nama banaso... Shisa nace ko zakaje can" Kai ya girgiza mata "Kome kika bani kinsan zanci ai, zanci da mai din nima" Shiru tayi batace komai ba, tasan halin shi da abinci ne, shisa tace ko yaje wajen Hajja din yaji, har ranta hakan ba komai bane ba, indai zaici abinda yake so ya wadatar da ita. Amman AbdulKadir ne, ko yana so din ba zaije ba, gani zaiyi tunda shine sanadin kin cin miyar tata, sai suci kome ya samu a tare. Kallon suka ci gaba dayi, ta karasa tsintar waken taje ta wanke ta dora. Da zai fita da magriba binshi tayi ta kulle kofar daga ciki, duk da akwai maigadi a bakin kofa. Dan yace mata zaije gida ya gaishe dasu Abba. Tasan kuma zai iya kai karfe tara bai dawo ba, dan har wajen Yassar saiya biya. * Gidan Yassar din kuwa ya fara biyawa. Kowa a gidan na mishi mitar baya zuwa a gaisa. Banda Yassar babu wanda yake ganin shi, baya kulasu, ko Hajja ta mishi fada fushi yake mata. In gaisuwa ce sunayi a waya, kuma sukan hadu a gida, idan anyi wani abu na rashin lafiya in yazo ta fada mishi yakanje ya duba su. Baiga dalilin da zaisa a takura mishi da cewar sai yaje gidajen su ba, kuma da karamar sallah duk ana haduwa har wanda suke nesa ma suna zuwa. A masallacin unguwar su Yassar yai isha'i, tukunna yahau babur zuwa kofar ruwa. A hanya ya kunna wayar shi yana jin sakonni nata shigowa ya kuma san Nuriyya ce. Jinta yake a wuyan shi, a rayuwar shi bayason abinda duk zai saka shi tunani, kuma ba zaima kanshi karya akan abinda yakeji a kanta ba. Kofar gidansu babur din ya ajiye shi, ya sallame shi, yana saka canjin a wallet zai mayar aljihu ya hango Nuriyya tsaye ita da wani a bakin motar shi. Ko babu fitilar kofar gidan su AbdulKadir din da ta haska mishi ita, yana da tabbacin zai gane ita din ce. Wani irin tuquqin kishi da yajine idanuwan shi har lumshewa suke ne abinda bai tsammata ba. Baisan kafafuwan shi na takawa ba sai da yagan shi tsaye a gabanta. Ita kanta ta girgiza dan bata tsammaci ganin shi ba, tun da safe take kiran wayarshi a kashe, ga sakonnin duk da ta tura basu nuna alamar sun shiga ba, ya kirata jiya da dare ya dorata kan tsanin buri, da safen nan ya girgizata ta fado. Har kuka tayi, tunanin shine yai mata yawa shisa ma ta fito zancen ko bakomai zata rage dare, inta koma ta sake kiran shi in bata samu ba ta hakura ta gwada kwanciya ko bacci zai saceta, shine tunaninta lokacin data fito "Masoyi..." Ta fadi murmushi na kwace mata, kallo daya AbdulKadir yai ma yaron da yake tsaye ya zagaya ya shiga motar shi yajata yana barin wajen. "Me kike tsaye da wancan yaron Nuriyya?" Ya bukata ranshi a matukar bace, saboda baiga dalilin da zaisa ta addabi rayuwar shi idan tasan zata dinga kula wannan yaran ba, baisan me yasa zata ce tana son shi ta fito tana kula kananun yara ba. Kafin ta bashi amsa ya dora da "Me kike so da ni? Me yasa zaki dameni kuma ki fito kina kula wannan yaron? Da wannan yaron zaki hadamun soyayya Nuriyya? Raini kike son ja mun?" Kai take girgiza mishi, gabaki daya yanayin shi ya tsoratata, muryarta a karye tace "Ka aureni, ka aureni....in baka son ganina da kananan yara ka aureni" Murmushi AbdulKadir yayi mai sauti da ko kadan bashida alaka da nishadi, tana maganar aure kamar abune mai sauqi, shisa ta zabi tayi auren tabarshi tun daga farko. Magana zaiyi yaga ta matsa da sauri tana boyewa a inuwar shi. Hakan yasa shi juyawa ya kalli inda idanuwanta suka bari, baisan waye ya shiga gidan su ba, amman bazai wuce wani cikin kannen shi ba. Hankalin shi ya mayar kanta "Me kike boyewa?" Idanuwanta cike taf da hawayen da batasan ta inda suka taso ba ta tsinci kanta da fadin "Naziru ne ya wuce..." Lokacin da tace tana son shi, bata hango girman hakan ba, asalima idanuwanta a rufe suke da tunanin samun shi, ta manta alakar da take tsakaninta da Waheedah da zata iya saka auren shi ya zame mata abu mai matuqar wahala. "Me yasa zaki boye?" AbdulKadir ya sake tambaya, Nazirun ba bakonta bane, baiga dalilin da zaisa ta boye ba. "Zai ganmu a tsaye" Ta amsa a sanyaye, tana saka hannu ta share kwallar data taru a gefen idanuwanta, wata irin soyayyar AbdulKadir din na dafa ruhinta "Me yasa kika ce kina sona idan kananun abubuwa irin wannan zasu dameki?" Idanuwanta ta sauke cikin nashi tana rasa abinda zata ce mishi, numfashi AbdulKadir ya sauke, gabaki daya kanshi yayi nauyi, bayaso abu ya dame shi, yaga alama kuma Nuriyya zata dame shi "Kina sona da gaske?" Kai ta daga mishi, inta ce kalamai zatayi amfani dasu ba zasu isheta ba, kalar son da take mishi har mamaki yake bata. Kai ya jinjina mata "Zai zo karshe in na sake ganinki tsaye da wani, bana so, raina zai baci idan naganki da wani" Kan ta sake daga mishi "Bana so ana mun magana da kai, ki bude bakinki insan kin fahimci abinda nake fadi" Wani abu dayai mata tsaye a wuya ta hadiye tana kallon fuskar AbdulKadir din "Ba zaka sake ganina da kowa ba" . Wannan karin shiya jinjina mata kai, ya juya yana barinta a tsaye a wajen, sai da taga ya shiga gida tukunna itama ta wuce, zuciyarta na wata irin dokawa taban mamaki. AbdulKadir kuwa wani irin yanayi yakeji da bai taba tunanin zaiji ba, cikin gida ya shiga yana wucewa bangarensu. A daki ya samu Hajja da ko gaisheta baiyi ba, sallamar da yayi ma bai jira ta amsa shi ba yace "Hajja ina Abba?" Cike da mamaki take kallon AbdulKadir din "Lafiya? Me ya faru?" Kai AbdulKadir ya girgiza mata "Lafiya kalau Hajja, ina son magana dashi ne, yana ina?" Ita ba girkinta bane ba, Mami ke da girki, dan haka tace ma AbdulKadir din "Yana bangaren shi..." Kai ya jinjina mata ya fice zuwa bangaren Abba, da sallama ta shiga, ya samu Mami tana hada kwanonin abincin da alama Abba ya gama ci. "AbdulKadir.... An iso kenan" Abba ya fadi da fara'a a fuskar shi. Murmushi AbdulKadir din yayi shima yana gaishe da Mami da ta amsa shi cike da fara'a, kunya irin tata bata iya tambayarshi ya Waheedah ba, ta fice daga dakin tana barinsu. Kan hannun kujera AbdulKadir ya zauna "Abba..." Ya kira yana dorawa da "Ina wuni" Gyara zama Abba ya sakeyi kan kafet din "Lafiya kalau, ya aikin? Ka samu kowa lafiya dai ko?" Kai AbdulKadir ya jinjina yana tsintar kanshi da daburcewa a karo na farko a rayuwar shi "Abba.. Daman zanyi magana dakai ne... Zamuyi magana..." Ya rasa kalaman daya kamata yayi amfani dasu. Cike da kulawa Abba yace "Allah yasa lafiya" Numfashi AbdulKadir ya fitar da baisan yana rike da shi ba, sakkowa yai daga kan kujerar yana zama a kasa a gaban Abba din, muryarshi can kasan makoshi yace "Aure zanyi Abba..." Maganar Abba yaji kamar daga sama, yanda yajita yafi yanda maganar auren AbdulKadir din daga farko ta dirar mishi. "Aure AbdulKadir?" Abba ya tambaya cike da shakku, duk da matan shi hudu, hakan bai hanashi jinjina maganar AbdulKadir din ba, dan yasan yan zamanin su da zamanin su AbdulKadir din akwai banbanci, adalci nama yaran yanzun wahala, kuma da yawa sukanyi auren ne badan ra'ayin hakan ba, sukanyi ne saboda dalilai da kala-kala, da yawa dan suna samun matsala da matan su na gidane. Maimakon su tsaya su fuskanci matsalar su shawo kanta, sai a dinga basu shawarar su kara aure, kamar hakan zai zama sanadin batan matsalar da suke fama da ita. Wasu kanyi dan su huce haushin wani abin da matarsu ta gida tayi ko take musu, wanda duk dalilai ne da basu kamata a dubasu wajen karin aure ba, shisa ga sunan, yara kanana suna fama da mata biyu da basu san yanda zasuyi dasu ba, tunda ta farkon ma tana neman fin karfinsu. Bayaso AbdulKadir ya kasance cikin mazan da zasu duba wannan dalilin wajen kara aure. Duk a cikin yaran shi babu wanda yake da mata biyu, a matan dai akwai wanda suke da abokan zama. Jin AbdulKadir din yayi shiru yasa shi dora tambayar tashi da "Me yasa kake son kara aure? Kuna samun wata matsala da Waheedah ne?" Kai AbdulKadir din ya girgiza mishi da sauri, bazai ce a zamansu da Waheedah basu taba samun matsala ba, amman inzai fadi gaskiya yafi bata mata rai fiye da yanda take bata mishi rai, dan ko abu yai mata bata taba daga mishi murya ba, in tai mishi maganar ya balbaleta da fadan shi sai dai ta bashi hakuri ta wuce daki, da duk idan ya bita kuka yake samun tanayi. Waheedah macece da yasan maza da yawa zasu so samun irinta, bata taba bashi wani dalili na dana sanin aurenta ba, asalima hukuncin aurenta na daya daga cikin abubuwa mafi girma na alkhairi daya sami rayuwar shi. "Kawai ina son kara auren ne, babu wani dalili bayan haka Abba..." AbdulKadir ya karasa maganar da yakeji tana fitowa daga zuciyar shi. Kai Abba ya jinjina,haka kawai yakejin maganar ta kasa zauna mishi. Har ga Allah duk lokacin da zai ga Waheedah a gidan sai yaji gabanshi ya fadi, dan yana tunanin ko AbdulKadir din yayi mata wani abu, amman har gashi aurensu na dosarma shekaru biyar ko a fuskar yarinyar bai taba ganin damuwa ba. Yafi kowa murna, dan baiyi tunanin akwai macen da zatai hakuri da baudadden halin AbdulKadir na tsayin lokacin ba. Shisa yaji auren bai zauna mishi ba, yana jin yaron har kasan zuciyarshi, bayason yana zaune lafiya ya jajibo abinda zai zame mishi matsala. Numfashi mai nauyi Abba ya sauke "Kayi tunani akan maganar nan dai AbdulKadir, aure ba abu bane da zaka tashi kaji kana sonyi, yana bukatar natsuwa a cikin shi" Kai AbdulKadir yake girgizawa, bayason abu ya dame shi, gudun tunanin ne yasa shi yanke hukuncin yin auren. Baiga dalilin da Abba zaice mishi ya kara yin wani nazari ba "Nagama duk tunanin da zanyi... Auren kawai nake sonyi, shisa nazo na fada maka" Shiru Abba yayi kafin yace "Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi, yar gidan wacece? Wacce unguwa take? In yaso sai kayi mata magana su saka mana rana, ni da Alhaji Hamisu da Alhaji Hadi sai muje ayi magana" Goshin shi AbdulKadir ya tana yana share zufar da yaji alamar tana tarar mishi. Bai taba tunanin muryarshi zatayi saukar da tayi yanzun da yake furta "Nuriyya ce Abba?" Kallon shi Abba yayi yana jiran ya tabbatar mishi da rashin hankalin da Hajja kance yana tattare dashi. Wani abu da yaji ya tokare mishi wuya AbdulKadir yake hadiyewa, ko kadan bayason kallon da Abba yake mishi "Abba ita Nuriyyar...Dan Allah karkace wani abu...ita nake so in aura" Abba bai taba tunanin akwai ranar da zai so wanke fuskar AbdulKadir da mari haka ba, da auren shi harda yaro. "Ban taba yarda da baka da hankali ba sai yau AbdulKadir, wallahi yau ka tabbatar mun da cewar baka da hanlali. Nuriyya kake magana, kawar Waheedah, Nuriyya aminiyar matarka, ita kazo kana fadamun kana so ka aura" Kallon Abba AbdulKadir din yake yana rokon shi daya fahimce shi, yasan lokutta da daman mutane na barin abinda addini ya halarta musu dan al'ada na ganin hakan bai kamata ba, kuma tun da ya fara tako kafarshi da niyyar furta maganar auren Nuriyya yasan zai fuskanci wannan matsalar, amman shi mutum ne da surutu irin wannan basa damun shi sam, bayajin akwai wani abu da addini zai halarta mishi kunya ta hanashi yi. "Bafa haramun bane Abba" AbdulKadir din ya fadi yanajin yanda ranshi ya soma baci, Hajja ce ya tsammaci zatai mishi wannan maganar ba Abba ba, tunda shi namiji me zai fahimta. "Idan baka fitar mun daga daki ba, wallahi saina wanke ka da mari, marar kunyar banza da wofi..." Mikewa AbdulKadir yayi yana fadin "Babu abinda nayi da ba dai-dai ba Abba, nikam zan aureta..." Dafe kai Abba yayi, yanajin zagin da bai taba tunani ba na mishi yawo a cikin kai, da yana da tsohon hawan jini bacin ran da yake ciki yanzun zai taso mishi dashi. Yanajin AbdulKadir din na sake cewa "Zan mata magana sai a ta fadi ranar da zakuje din" Kafin yaja mishi kofar yana ficewa daga dakin...!!! #Teamwaheedah #TeamAbdulKadir #LubnaSufyan[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan IG: SufyanLubna Email: Calmlubna@gmail.com Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43 *ABDDULKADIR* *LubnaSufyan* 22 INA GODIYA DA ADDU'O'IN KU DA DUKKAN SAKKONIN KU. KEEP THE COMMENTS FLOWING, NAGODE, NAGODE, NAGODE. Har ya shiga gida ran shi a bace yake jin shi. Yana jin Waheedah tun da ta amsa mishi sallama tai mishi sannu da zuwa tana bin shi da ido. Yasan ta fahimci ran shi a bace yake. Kitchen ta shiga ta samu babban plate ta zuba musu abinci a ciki, manja ta zuba musu ta saka cokulla guda biyu a cikin abincin, maggi ta dauka da robar yaji ta fita falon. AbdulKadir na zaune inda tabar shi akan kujera, so take ta tambaye shi waya bata mishi rai, amman batajin dadin jikinta, ba tajin zata iya da fadan shi da daren, shisa tayi shiru. A kasa ta ajiye abinci da robar yajin ta dora maggin a sama. Kitchen ta koma ta dauko wani plate din da kofuna guda biyu, ta bude fridge ta dauko pure water guda biyu, sai robar da cittarta take a ciki, in dai an kawo ruwan roba gidan AbdulKadir ne yazo ya fita ya siyo shi, barnar kudin nan bada ita akeyinta ba, akwai gidan ruwa a unguwarsu, maigadi take ba ya siyo mata leda goma ta zuba a fridge din, sai ta kwana biyu bata nemi ruwa ba. Danma Fajr na mata barnar shi, idan yagan shi a roba kuma bakinta baya hutawa da surutu, babu qishin da yake ji, zai dauko ne kawai dan yasata magana. A kasa ta samu AbdulKadir ya sakko, itama ta ajiye ruwan ta samu waje ta zauna. Maggin ta barbada ta bude robar yaji ta zuba, duka ta cakuda, tasan AbdulKadir zai tsaya kallonta sai ta cakuda inda zataci suci wajen tare, ko ta cakuda mishi na gaban shi, in sunje gidan su har mamakin yanda yake komai da kan shi take, amman da sun dawo yaga su kadai ne zai shagwabe mata. Badan batason hakan ba, wani lokaci abin kanyi mata yawa, gashi, ga Fajr. Abincin suke ci, bakajin komai na tashi a dakin sai karar cokulla. Sun gama kenan ta zuba mishi ruwa ta mika mishi kofin sukaji sallamar Yassar. Ita ta amsa mishi sallamar tana kallon yanayin shi ko zata fahimci dalilin zuwan shi da dare haka. Murmushi yai mata yana amsa gaisuwar ta hadi da dorawa da "Duk suna lafiya. Ya jikin ki?" Sunkuyar da kanta tayi kasa a kunyace, tana amsawa can kasan makoshi, idanuwa Yassar ya sauke kan AbdulKadir, hakan da Waheedah ta kula da shi yasa ta mikewa ta dibi kwanonin ta wuce kitchen, acan tasha ruwa tukunna ta fito tana ma Yassar sallama ta wuce daki. Kowa ya batama AbdulKadir din rai tasan bazai wuce a gida bane, tunda taga Yassar yazo. Shisa tabasu waje, in AbdulKadir yana so taji da kanshi zai fada mata, ita kam kaya zata sake ta kwanta abinta. Yassar mikewa yayi, baisan yanda akayi ya iya dora murmushi a fuskar shi ba, bayan abinda yake so yayi daya shigo shine wanke fuskar AbdulKadir din da mari. Abinci zaici Abba ya kirashi rai a bace yake fada mishi abinda AbdulKadir din yake shirin yi da ko a mugun mafarki Yassar bai taba hango faruwar lamarin ba. "Magana nake son yi da kai" Kallon shi AbdulKadir yayi yana kankance idanuwan shi, ran shi ya kara baci, Abba kiran Yassar yayi ya fada mishi kenan, kuma baiga dalilin yin hakan ba, tunda zai fadama Yassar din da kan shi, magana ce da ba boyuwa zatayi ba, dan baiga abinda zaisa shi ya fasa ba, ya rigada ya furta. "Ina jin ka ai" Ya amsa, mikewa Yassar yayi, idan AbdulKadir bashida hankali, shi yana dashi, da alama Waheedah bata sani ba, ba zaiso ta faraji daga bakin shi ba. "A waje zamuyi magana ba anan ba" Cewar Yassar yana ficewa daga dakin, tashi AbdulKadir yayi yabi bayan shi har wajen motar shi, suka tsaya. Sun kai mintina biyu Yassar nason hadiye abinda yakeji yana taso mishi ko zai samu nutsuwar yima AbdulKadir din magana batare daya dura mishi ashar ba. "Abba ya kirani...." Shiru AbdulKadir din yayi, yana jira Yassar ya fada mishi wani abu da bai sani ba, wannan tsohon zance ne tunda gashi tsaye a gefen shi yana huci kamar sabon biredi. "Ka ce mun wasa kake

Chapter 22 of 37