Share this page
cable ya zani rashin kunyar da tai mishi, ya kuma zane wadda takejin zatayi mishi a gaba. Amman matarshi ce, baisan da wanne ido zai kalli Abba idan ta fada mishi ya mareta ba, dan a gaban shi Abba kan fadi duk namijin daya daga ma yarinyar shi hannu ya sani sai dai kaddara amman ya daki auren shi. Sai dai ya bata hakuri, ya kamata ta hakura, ta sake bashi wata damar, kome zata ce mishi, duk rashin kunyar da zatayi mishi ba zaima kulata ba ballantana ya daga mata hannu. Tashi zaune AbdulKadir yayi yana dafe kan shi da hannuwan shi biyun, komai yakeji ya hade mishi waje daya, baisan dame zaiji ba, ranshi dayake bace da Nuriyya da ko kadan bata kula hankalin shi ba'a kwance yake ba ta kara bata mishi rai, ko da Waheedah da ta hargitsa duk wani kwanciyar hankalin shi. Yasan da baiyi rashin kunya lokacin da aka bashi damar yin bayanin karar shi da Major yakai ba, da wahala ma ya kwana, tunda bayani kawai zaiyi suce mishi yaja ma matar shi kunne, sai yaba Major hakuri, amman bazai iya wannan ba. Rashin kunya ya tsula har Major din ya sa mishi hannu, da sukayi detaining din shi kuma ya sake jibgar wani a cikin cell din. Shisa yai kwanakin da yayi, gashi sai yanzun yakejin ciwon da jikin shi yake mishi. Waheedah ko wannan bata duba ba take kara kallon idanuwan shi tana cewa ya rabu da ita, shikam bashi da wannan zuciyar, hakuri zatayi ta yafe mishi ta dawo suyi zaman su. Dan shi bazai taba iya rabuwa da ita ba. Yanzun ma ji yake yanda ranshi yake a bace in bai ganta ba akwai matsala, wata irin kewarta yakeji tana danne shi kamar bai ganta awanni kadan da suka wuce ba, a gigice yakejin rayuwar shi da wata irin rashin nutsuwa da kusancin Waheedah kawai yake samar mishi. Tashi yayi yana laluba aljihun shi yaji mukullan motar shi suna ciki. Ficewa yayi daga gidan ya shiga mota, wajen Abba zashi, in Waheedah bata dawo gidan shi yajita a kusa dashi ba yau baisan yanda zaiyi da tunani ba. * Tsintar kan shi yayi da kasa nufar bangaren Abba kai tsaye, dan haka ya wuce wajen Hajja, a falo ya sameta zaune da remote a hannunta, Zainab da itace Autarta kuma tana aji daya a jami'a a yanzun tana zaune gefen Hajja din "Hamma ina wuni" Ta fadi bayan Hajja ta amsa sallamar AbdulKadir din, kai kawai yadan daga ma Zainab din data mike tabar musu falon. Inda ta tashi AbdulKadir ya koma ya zauna, yana dafe kan shi cikin hannuwan shi dan ya rasa abinda zaice. Kallon shi Hajja tayi, tunda ya shigo tagan shi a firgice, kamar ba AbdulKadir din ta ba, kamar ba sojan gidanta ba, cikin kwanaki bakwai gabaki daya ya fita hayyacin shi. Ba zatace auren soyayya sukai da Alhaji Ahmad ba, asalima baifi sau biyu tagan shi kafin a tsayar da maganar auren su ba. Ba kuma kasafai take fahimtar soyayya irin ta yaran yanzun ba, amman akan AbdulKadir da Waheedah tasan cewa kaddarar data hadasu mai girma ce, dan ko ita sosai ta jinjina al'amarin sanin yanda Waheedah take da sanyin hali, shekarun da taga suna wucewa batare da matsala ko daya daga gidan AbdulKadir din ba ya nutsar da hankalinta, ta sake jinjina kaddarar zamansu lokacin da taji ya auri Nuriyya, duk idan taga Waheedah a gidan sai taita kallonta tana mamakin yanda ta shanye wannan cin amanar. Dan ita kam tasan ba zata iya ba, da saninta ma a auren Alhaji Ahmad saida takai zuciya nesa, har gobe kishin sauran matan shi kan motsa mata ba kadan ba, shisa batason wani abu ya sami auren dan nata da Waheedah, babu macen da zata iya zama dashi tana da wannan tabbacin, Nuriyyar ma ba baki tai musu ba, babu inda auren zaije ko bana cin amana bane, saboda ta kula da yarinyar tana da ji dakai da son abin duniya. "AbdulKadir..." Hajja ta kira tana ganin ya dago fuska yana sauke mata kananun idanuwan shi "Kaci abinci?" Kai ya girgiza mata, yunwar ma ya nemeta ya rasa. Mikewa Hajja tayi, da sauri AbdulKadir din yace "Hajja na rasa yanda zanyi...na bata hakuri Hajja... Bansan ya zanyi ba kuma. Wallahi bazan iya rabuwa da ita ba" Numfashi Hajja ta sauke, tausayin shi na cika mata zuciya. Kitchen ta wuce ta zuba mishi shinkafa da miya da lettuce. Ta dawo tana mika mishi, karbar plate din yayi ya ajiye akan kafet "Ba abinci ba Hajja... Matata..." Numfashin Hajja ta sake saukewa "Kaci abincin AbdulKadir... Zan roki Abbanku sai a bata hakuri kaji..." Kallon Hajja yake "Za'a bata hakuri da gaske? Abba yace ba zai saka baki ba fa... Hajja haka yace ya daina saka baki a lamurrana, dan Allah shima ki bashi hakuri... Nikam rayuwata na cikin wani yanayi" Yanda ya karasa maganar takeji har cikin ranta, bata taba ganin dan nata yayi laushi haka ba, da bakin shi yake kiran a bama Abba hakuri yau, tura takai bango. Shisa take jinjina ma kokarin maza, zasu dauki shekaru suna musgunawa mace, ko a fuskarta da wahala a gane, amman rana daya idan ta ware ta rama sai kagani a fuskar shi namijin. Sai kaji an fara bata rashin gaskiya saboda halittarta da juriya aka santa. Yanzun wanda duk zaiga AbdulKadir din saiya tausaya mishi, da yawama zasu manta cewa koma me yake faruwa dashi yanzun laifin shine, wasu ma zasu ce me yasa Waheedah ba zata hakura ba tunda harya bude baki ya bata hakuri. Amman yarinyar kawai tasan abinda ta hadiya tunda har take neman ya saukake mata "Kaci abinci AbdulKadir, zan ma Abban naka magana" Kai AbdulKadir ya jinjina mata, shi abincin ma yau ba damun shi yayi ba. Sai da Hajja ta sake dauko plate din ta mika mishi a hannun shi, cakudawa yayi gabaki dayan shi ya fara ci, taunawa yake yana hadiyewa da wani irin nisantaccen yanayi shimfide a fuskar shi...! #TeamAbdulKadir #TeamWaheedah #LubnaSufyan [7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan IG: SufyanLubna Email: Calmlubna@gmail.com Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43 *ABDDULKADIR* *LubnaSufyan* 27 AbdulKadir Comments Zauren Biebee Isa Wattpadians Daukacin makaranta AbdulKadir Godiya mai tarin yawa #SonSo saboda Allah A waya Hajja ta kira mishi Abba, amman ca yayi bayason ganin AbdulKadir din, idan sulhu yake nema yaje wajen Waheedah, shi kam ba zai saka musu baki ba. Da wani irin sanyin jiki AbdulKadir yabar gidan. Amman tsintar kan shi yayi da nufar hanyar gidan Yassar, ba zai iya zuwa gida ba, har a kasusuwan shi yakejin bukatar Waheedah a kusa dashi. Bai taba zaton zaiyi kewarta irin haka ba, ko watannin da yakan shafe batare da ita ba, inya tuna cewar tana gidan shi, tana jiran komawar shi kan nutsar da wani bangare na zuciyar shi. Amman yau yana gari daya da ita, da auren shi a kanta ace ta kwana bakwai bata cikin gidan shi, gidan su, abin yana ci mishi zuciya fiye da yanda zai iya fadi. Gidan Yassar ya karasa yana parking din motarshi, a jiki yabar mukullin yana fitowa, ya karasa bakin kofa yaci karo da Yassar din da yake girgiza kai "AbdulKadir..." Katse shi AbdulKadir yayi da fadin "Hamma dan Allah, banajin tashin hankali, magana kawai zan mata, dan Allah karka cemun wani abu, na roke ka" Da bayanannen mamaki Yassar yake kallon AbdulKadir, yasan kaf gidan su daga su Hajja sai shi AbdulKadir kan dagawa kafa lokutta da dama, amman Yassar yasan su Hajja kawai yake saukewa murya irin haka, ya kasa yarda da AbdulKadir ne a gabanshi yake rokon shi alfarma yau. Mutane kan ce in da ranka ka sha kallo, kallon yake sha yanzun. Rabashi AbdulKadir yayi yana wucewa cikin gidan, yaji dadi da baici karo da Hauwa ba har ya karasa dakin da Waheedah take ya kwankwasa tukunna ya murza hannun kofar yana shiga. Ta sake kaya, rigar bacci ce a jikinta, doguwa har kasa. Kalar rigar bata dami AbdulKadir ba, idanuwan shi na kan fuskar Waheedah da take kallon shi da gajiya shimfide cikin idanuwanta, takawa yayi ya karasa gefen gadon yana kama hannuwanta ya dumtse cikin nashi "Me yasa zaki karya alkawarin ki? Kince ba zaki barni ba, da bakin ki kin sha fadamun zaki kasance tare dani.... Wahee in ke zaki iya barina ni bazan iya barin ki ba.... Wallahi ba zan iya ba" Kallon shi Waheedah take tunda ya fara magana, amman zuciyarta a bushe take ballantana kalaman shi suyi mata tasiri, a hankali ta tara abinda ya kawota inda take yanzun, batajin akwai kalaman da zasu canza ra'ayinta. Hakan AbdulKadir ya kula dashi, ya sake dumtse hannuwanta da ta fara zamewa daga cikin na shi. "Waheedah ni ne fa, ki kalle ni, ni ne, ban aureki dan in rabu dake ba..." Ya karasa maganar da wani nisantaccen yanayi a muryar shi, yana kasa yarda Waheedah ce take son barin shi. Yana tuna lokacin da aiki ya kaishi tsakiyar inda ake tarzomar yan boko haram a Maiduguri. * Ta dauka tashin hankalinta kan aikin shi ya fara tsagaitawa, sai da aikin ya daukar mata miji yayi Maiduguri da shi. Tana da cikin Fajr wata kusan bakwai. Ko yaushe wajen awo ca suke mata ta kwantar da hankalinta, amman tasan ita da kwanciyar hankali sunyi hannun riga har sai AbdulKadir ya dawo gida. Kasancewar in da suke babu network, duk Asabar yana samu ya fito ya kirata, idan bai kirata ba, wani idan ya fito cikin abokan aikin nashi zai turo mata da sakon AbdulKadir din. Yanda kwanaki kan wuce mata tsakanin Asabar zuwa wata Asabar din ba zatace ba. Sai dai duk wani tashin hankali da take tunanin ta taba shiga, ko ta taba jin labari bai kai wanda take ciki a yanzun da satika uku suka wuce batare da labarin AbdulKadir ba, wata na hudu yake nema lokacin a Maiduguri, bai kuma taba wuce sati biyu bataji daga wajen shi ba. Ya fada mata idan sati hudu suka wuce bai kira ba, ko sakon cewar yana lafiya bai sameta ba, to wani abin ya faru dashi, tayi mishi addu'a. Kukanta bai tsananta ba sai da satika hudun suka cika babu labarin AbdulKadir, musamman da su Hajja suka fara kiranta suji ko AbdulKadir din ya kira, Anty ma ca tayi zata zo ta dauketa su koma gida, tunda ga cikin ya tsufa, ga kuma tashin hankali, sai dai ba zasu gane ba. Ba gida take son zuwa ba, mijinta take son sanin yana lafiya. Ba zata ce ga abinda take tunani ba, safiyar asabar din da AbdulKadir ya cika sati biyar bai kirata ba. Zata iya tuna sauka daga kan gado ta shiga bandaki, yanda tayi wanka bata sani ba, dan hankalinta yayi nisan da ba zata iya taro shi ba. Da kayan data shiga bandaki ta fito, hijab kawai ta dora a saman su, ta dauki jakarta tana zuba duka kudin data ciro na hidimar gida a ciki, ta saka wayarta da bata da wani amfani yanzun a wajenta ta dauki jakar, takalma ta karasa ta zira a kafafuwanta, batare data kula na wanka bane. Lokaci zuwa lokaci take share kwallar dake bin fuskarta. Maiduguri zataje neman shi, batasan ina yake a Maiduguri din ba, amman zaifi mata zaman da zatayi cikin gida batare da sanin halin da yake ciki ba. Fita tayi daga gidan, tana tsaye tana kulle gidan da rashin nutsuwa yasa ta kasa saka mukullin a mazaunin shi harta rufe gidan, ga idanuwanta da suke cike taf da hawaye, a cikin kanta kawai ta kasa yarda tayi tunanin cewar wani abu ya sami AbdulKadir din. "Wahee...." Taji muryarshi cikin kanta, dan jim tayi na wasu dakika, kafin ta share wasu hawaye masu dumin gaske da suka zubo mata, jin muryarshi cikin kanta ba bakon abu bane ba, yau dinne tajita kurkusa sosai. "Waheedah..." Ta sake ji ya kira, juyawa tayi tana sauke idanuwanta akan AbdulKadir dayake tsaye, duka hannuwanta biyu ta saka wannan karin ta share hawayen fuskarta, tsaye yake cikin uniform harda hularsu ta sojoji, hana sallah a saman kan shi, hannun shi daya rike da jaka. "Yanzun kuma gizo kake mun Sadauki?" Ta furta wasu sababbin hawayen na sake zubo mata. Kai AbdulKadir ya girgiza mata, yana jin da akwai sauran hawaye tattare dashi babu abinda zai hanasu zuba, ya riga ya fitar da rai da sake ganinta, tashin hankalin da ya gani a watannin bai dauka zai fito da ran shi ba, inya fito da ran nashi ma bai dauka batare da wata nakasa ba. Duk da akwai tabbai na tsofin ciwuka da sababbin da ko warkewa basu gama yi ba, dan dinkine waje hudu a fuskar shi, akwai wasu guda uku cikin kan shi da hular da ya saka ta boye. Sai jikin hannuwan shi da cikin shi. Sai dai ganin Waheedah ya saka duk wani radadi da zugi da yakeji bace mishi. "Waheedah" Ya kira a karo na uku, yana kallon yanda ta ware mishi manyan idanuwanta cike taf da hawaye, kafin ta soma kokawa da numfashinta cikin yanayin da yasaka shi karasawa yana riko damtsen hannunta, amman har lokacin kokawa take da daidaiton numfashinta, da gaske AbdulKadir din ne a gabanta, ba gizo yake mata ba, jikinta ko ina bari yake, batasan ta yarda jakar da take hannunta ba, tana saka hannunta kan fuskar shi cike da son tabbatar ma kanta shine. "Sadauki..." Ta kira wani irin kuka me sauti na kwace mata, hannuwan shi AbdulKadir din ya zagaya yana riketa gam, batare da damuwa da yanda katon cikinta yake tokare shi yana hana mishi riketa yanda ya kamata. Kuka take da yasa ko ina na jikinta bari. "Babu abinda ya sameni Waheedah.... Gani... Babu abinda ya sameni" AbdulKadir yake fadi yana jijjigata, kukan da take yana taba zuciyarshi, sai da ya tabbatar jikinta ya daina bari tukunna ya dauki jakarta, har lokacin tana jikin shi, da dabara ya jasu yana bude kofar suka shiga cikin gidan, jakunkunan ya ajiye, yana kama hannun Waheedah da take sauke ajiyar zuciya ya zaunar da ita a kasa, yana kallon yanda sai da dabara ta samu ta zauna. Ruwa yaje ya zubo a kofi ya kawo yana bata, da sauri ta karba ta shanye tas tana mika mishi kofin, ajiyewa yayi a gefe ya zauna. Ko takalman kafarshi bai yunkurin cirewa ba, kanta Waheedah ta kwantar a jikin shi, ya kara matsawa yana riketa a jikin shi sosai. Idanuwan shi ya lumshe yana jero duk wata addu'a ta godiya ga Allah daya dawo dashi gida lafiya, ya bashi damar rike matar shi a jikin shi haka. Dayan hannun shi ya dago ya dora kan cikinta, saida ya sumbaci kanta tukunna yace "Ya kuke?" Hannu Waheedah takai ta share wasu hawayen da tambayar AbdulKadir din ta fito dasu, muryarta a dishe saboda kukan da tasha ta amsa shi da fadin "Ka tsorata mu, Sadauki ka tsoratani" Sumbatarta ya sakeyi yana riketa gam a jikin shi. Cikin kuka tace "Karka barni, dan Allah karka barni, bansan inda zan saka rayuwata ba, banma san ta inda zan farata babu kai a ciki ba" Shiru yayi, baya yarda bakin shi ya bude da alkawarin da bashida ikon cikawa a tsakanin su, tunda rayuwar ba a hannun shi take ba, a lokacin cikin kan shi ya roki Allah ya bashi aron rayuwa mai tsayi a tare da ita. "Ina zaki je da?" Ya bukata cikin sanyin murya "Maiduguri" Waheedah ta amsa tana saka AbdulKadir din kallonta da murmushi a fuskar shi "Bansan me zanyi bane ba...baka barni da zabi da yawa ba" Kai AbdulKadir yake girgizawa, Waheedah da ko bindiga ya shigo da ita gidan inta sani sai dai bindigar ta kwana wani daki, su su kwana dakinsu daban. Itace zata bishi Maiduguri "Baki da hankali ko? Ta ina zaki fara nemana?" Kafadunta ta daga mishi, itama bata sani ba, binshi dinne abinda ya fara zuwa mata a kai "Karki kara tunanin yin wannan kasadar" Jin tayi shiru yasa AbdulKadir dagota daga jikin shi yana kallon cikin idanuwanta "Da gaske nake Waheedah..." AbdulKadir ya fadi yana dorawa da "Bambanci kowacce rana na tare da yanda take kara kusantani dake" Dan sanin cewa tana gida tana jiran shi ya ishe shi kwanciyar hankali "Nutsuwar da take ragemun shine sanin kina lafiya, kina gida a kwance, kina lafiya, karki hargitsamun da tunanin ko kina shirin bina inda nake. Kullum maganarki kar in barki... Kin taba tunanin ke idan kika barni ya zanyi?" Yanayin dake fuskar shi yasa idanuwanta sake cika da hawaye "Babu inda zani, bazan barka ba, mutuwa ce kawai abinda zata saka in barka" Ta tabbatar mishi tana saka shi jinjina mata kan shi kafin ya riketa a jikin shi. * Yanzun ma hannunta ya dago yana dorawa kan fuskar shi "Kin ce babu inda zaki barni, me yasa kika bari na yarda da hakan bayan kinsan karya kike?" Hannuwanta take zamewa daga cikin nashi, wannan karin bai hanata ba, wata irin gajiya yakeji har cikin zuciyar shi, numfashi ya sauke kirjin shi na wani irin ciwo. Cikin sanyin murya yace "Fajr fa?" So takeyi ta amsa shi, yanayin shi takejin kamar zaiyi tasiri a kanta, shisa ta zabi yin shiru. Dan ko kusa bata tunanin komawa gidan shi, tana jin shi ya mika hannu ya dauki Ikram dake bacci, rike yarinyar AbdulKadir yayi a jikin shi, ya nutsu yana kallon yanda take bacci batare da tunani ko damuwar wani abu ba, yanajin kamar suyi musayar matsayi da yarinyar, ya kai mintina biyar a zaune a wajen, kafin ya mayar da Ikram inda ya dauketa. Numfashi yaja yana sake fitar dashi, kafin ya mike, Waheedah yake kallo da taki dago fuskarta ballantana su hada idanuwa. "Sai da safe Wahee, kiyi hakuri nikam, bazan iya fadan nan ba wallahi, dan Allah kiyi hakuri. Zan dawo gobe in shaa Allah, ki kula da ku" AbdulKadir ya karasa maganar yana juyawa ya fice daga dakin yana nufar hanyar da zata fitar dashi zuwa harabar gidan. Ko da ya shiga motar shi ya dade zaune a ciki, ya hade kan shi da abin tuqin yana rasa abinda ya kamata yayi, rayuwa bata taba gwada karfin halin shi ta irin wannan fannin ba, yanzun da hakan ya faru yake gane shi raggo ne na gaske, dan kam bayajin zai iya jurewa. Tuqi yake a karo na farko ba tare da nutsuwa ba, yanajin mutane na zagin shi, bata su yake ba, gida kawai yake son karasawa batare daya kashe wani ko wani ya kashe shi ba, daya gan shi cikin gida ma bazai ce ga yanda ya karasa ba. Mukullin a jiki yabar shi tunda ya shigo da motar, ya wuce cikin gida, kan shi tsaye ya nufi bagaren Waheedah, bedroom ya shiga ya kwanta yana lumshe idanuwan shi batare da yasan tunanin da yakeyi ba. * Yanda taga dare haka taga rana, da safe fuskarta a kumbure ta tashi da ita, saboda rashin bacci da kuma kukan da tasha. Dadinta daya, a satin su Fajr sukai hutun makaranta saboda gabatowar azumi. Ikram ta fara yima wanka ko da ta tashi, ta bata tasha da taga tayi bacci ta ajiyeta taje tai wanka itama. Saida ta fita suka gaisa da su Hauwa da suketa sauri da alama sun makara, tukunna ta koma daki, kusa da Ikram ta kwanta jin idanuwanta har yaji suke mata saboda rashin bacci. Ta lumshe idanuwanta taji Fajr a jikinta, hannu tasa tana dagashi "Fajr ka kwanta a katifa.... Karka dameni dan Allah" Kallonta yayi, da alama yanayin fuskarta yagani yasa shi zagayawa ta dayan bangaren ya hau gadon ya kwanta, juya kwanciya tayi ta fuskance su, tana kama hannun Ikram da kamar tajita, ta damqe dan yatsanta guda daya. Murmushi Waheedah tayi zuciyarta na cika fam da kaunar yarinyar, kullum sai ta dauka babu yanda za ayi taso yaranta fiye da son da take musu, sai suyi wani abin da zaisa zuciyarta cika fam da wata irin kaunar su. Bata san lokaci na tafiya ba, baccin kuma bai dauketa kamar yanda tayi tsammani ba. Babu komai cikin kanta daya wuce su Fajr da take kallo sun nutsu suna bacci. Kwankwasa kofar da taji anayi ne yasata lumshe idanuwanta dan a tunanin ta AbdulKadir ne, muryar Anty taji "Waheedah..." Da sauri ta diro daga kan gadon tana zuwa ta bude kofar. "Anty..." Ta fadi cikin sigar gaisuwa tana dan matsawa Antyn ta shiga cikin dakin, mayar da kofar Waheedah tayi ta rufe tukunna ta karasa gefen gadon kusa da Anty ta zauna suna gaisawa sosai. "Ya jikin ki?" Dan rausayar da kai gefe Waheedah tayi "Alhamdulillah... Naji sauki" Kai Anty ta jinjina, tausayin Waheedah na cika zuciyarta. Duka cikin su babu wanda yasan da maganar auren AbdulKadir din, Nabila ce taje gidan ta dawo musu da labarin, ita Anty tafi awa daya a zaune jin Nuriyya ce AbdulKadir ya aura, kafin daga baya taje har bangaren Mami tana sauke takaicinta a can, dan ca tayiwa Mami lokacin suje su taho da Waheedah din tunda AbdulKadir bashida hali ballantana kunya, murmushi kawai Mami tayi duk da a idanuwanta zakaga tsantsar damuwar da take tattare da ita. Kawaici irin na matar har mamaki yake ba Anty. Shisa take ganin girmanta ba kadan ba, dan da Waheedah yarta ce ikon Allah ne kawai zaisa ba zata kashe aurenta da na AbdulKadir ba, tunda farko ma bataga dalilin da zaisa ta dauki yarinya ta bashi ba, musamman mai sanyin hali irin na Waheedah. Numfashi Anty ta sauke "Bansan me kikai ta bari a ranki har zuwa lokacin nan ba, ni bazan baki hakuri ba Waheedah, amman kije gida kiyi magana da Maminki, nasan kawaici ba zai barta furta komai ba, kije taga kina lafiya ba wai a waya ba" Hannu Waheedah takai tana share hawayen da taji sun zubo mata. Cikin sanyin murya tace "Idan gidan zaki koma bari mu wuce tare" Kai Anty ta jinjina mata, ba gida zata koma ba, amman hidimarta zata jira, inta sauke Waheedah din saita sake fitowa. Hijab dinta ta dauko, sai jakar goyon Ikram din ta sakata a ciki tana goyata ta gaba ta tallabe, Fajr zata tasa Anty ta hanata, sabar yaron tayi a kafadarta, wayarta kawai Waheedah ta saka a jaka ta rike a hannu, mukullin da Hauwa ta bata na gidan guda daya, ko da zata fita ta dauka, sannan tabi bayan Anty. Kulle gidan tayin suka nufi motar Antyn, a cunkushe Waheedah takejin kanta da zuciyarta gabaki daya. Da tunani fal a kanta suka nufi gida. Har suka karasa gida Waheedah batama sani ba, sai da taji Anty ta bude mata kofar motar ta bangarenta, saukowa tayi da Ikram tallabe a kirjinta. Fajr ya tashi bata ma sani ba, jakarta ta dauka tana ratayawa ta kama hannun shi, ko sallama bataiwa Anty ba ta wuce tana nufar bangaren su, Antyn ma mota ta koma ta fice daga gidan, zuciyarta cike da tunanin Waheedah din. Da sanyin jikinta ta karasa gida tana shiga da sallama, a falo ta samu Mami a zaune, Fajr kam bai bita ciki ba ya wuce bangaren Hajja, ita ma batabi ta kan shi ba. Sallama tayi tana cire takalmanta ta karasa, tunda Mami ta amsa ta taji idanuwan ta sun cika da hawaye. Kan kujera ta zauna kusa da Mami tana sauko Ikram ta kwantar da ita a gefe, hijabinta ta cire, tana saka dan yatsa ta share kwallar da ta taru a gefen idanta, kallon ramar dake kasan idanuwanta Mami tayi, zatai karya idan tace bata kwana da yarinyar tana tashi da ita a rai, kwanakin nan yinsu kawai take badan suna mata dadi ba, duk da Yassar kullum da safe saiya kira ya hadata da Waheedah din sun gaisa, baccin kirki ma ba sosai take samun shi ba, haka takan raya daren da salloli tana yima Waheedahr addu'a. "Waheedah..." Mami ta kira tana rasa ta inda zata fara mata magana, maganar cewar bata taya Waheedah jin abinda Nuriyya tai mata ba baima taso ba, har kasan zuciyarta taji zafin abin, musamman ita da tafi kowa sanin yanda Waheedah ta dauki Nuriyyar, amman rayuwar haka take tafiya, wanda yafi kusa dakai shi yafi kowa samun damar cutar ka, yanzun mutanen kirki basu bane wanda zasu dauki abu su baka, mutanen kirki sune wanda zakuyi tarayya tare dasu basu cutar da kai ba. Auren da AbdulKadir din yayi bai saba addini ba, ya taka matakai da yawa na rashin kyautawa ne kawai a al'adance. Taso yima Waheedah maganar sai tace mata 'Babu komai Mami, ya rigada ya faru, ki mana addu'a Allah yasa hakan alkhairi ne' Duk da tabar zancen, wani abu a kasan ranta saida ya fada mata Waheedah na boye kishin da tasan yana damunta ne, ta kuma jima tana tsoron rana irin wannan. Tana kallon yanda Waheedah take kai hannu tana share kwallar da take tarar mata lokaci zuwa lokaci, numfashi Mami ta sauke "Waheedah..." Ta sake kira a tausashe, wannan karin kamar hakan Waheedah take jira wani irin kuka mai sauti ya kwace mata, jikin Mami ta kwanta tana kukan da takeji yana fitowa daga kasan zuciyarta inda yake mata ciwo na gaske. Kuka take da bata tabayin irin shi ba a rayuwarta, kukan ranar da AbdulKadir ya fada mata ya kara aure ta text saboda bai darajata ba, kukan ranar da ya shigo mata da kawarta, Nuriyya da ta dauka yar uwa a matsayin kishiya, kuka take da duk ranar da Nuriyya ta rike AbdulKadir din a gabanta, kuka take daya kamata tayi shi watanni takwas da suka wuce, ta jima tana rike da shi a ranta, yanzun da ta fara bata san ya zata daina ba, muryarta a karye cikin wani irin kuka ta dago daga jikin Mami tana fadin "Ma... Mami duk mata... Duk matan garin Kano da inda aiki yake kai shi... Mami baiga kowa ba sai Nuriyya....me yasa Nuriyya?" Waheedah ta karasa maganar tana kai hannu ta dafe kirjinta da yake wani irin ciwo kamar zai tsage. Kishi takeji har wani duhu-duhu take gani. Riketa kawai Mami tayi, tasan kukan ma Rahma ne,

Chapter 28 of 37