Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 💞💓️ZUCIYAR ALIYU CE💓💞 WhatsApp no:+234 8160983083 Chat with me YUSRAH MUSA ABUBAKAR DUTSE. ✍️MARUBUCIYAR ✍️ 1_Yarima Abdul-maleek 2_D'an millionaire 3_Safreeyyah 4_Royalty 5_Minister Ashraf 6_Me kamar sarki And now 7_❤️Zuciyar Aliyu ce❤️ Later 8_👑Yarima Aryan👑 Assalamu-alaikum yan uwa masoya barkan mu da shigowa wani sabon littafin nawa mai suna 💓Zuciyar Aliyu ce💓 humm ita fa yarinyar zuciyar Aliyu ce me kuke tunani a cikin wannan labarin abubuwan al'ajabi zasu faru ku dai ku kasance dani ku biyo ni mu shiga ciki tare yau za mu shiga duniyar nishad'i. In the name of Allah the must benefits and the must merciful ALLAH THE MOST HIGH DOESN'T SLEEP ALLAH THE MOST HIGH IS PURE HE ACCEPT ONLY WHAT IS PURE we love our NABI MUHAMMAD SAW no success without him he's the light of every darkness he've no limits ya rasulullah. STORY WRITTEN AND EDITING YUSRAH MUSA ABUBAKAR {maman Fatima Elham little Zaran aunty} I'm here to make u happiness educated hhhhhh! domin nifa I have no girman kai if u're fushi dani so wallahi u're just 'batawa kan k lokaci ni ta kowa ce. Godiya sosai sosai godiya masoya babu bakin da zanyi muku albarka dashi bisa kauna da kuke gwada min saidai nace Allah ya saka muku da mafificin alkhairin sa a duk inda kuke amin. Zarah Musa d'an Adam Naja'at Musa Abubakar Fatima Musa Abubakar Fatima batul Abdullahi Ru'kayyat Abdullahi Asma'u Abdullahi Ruwainah Abdullahi. Ranar kuce masoya maza kada kuyi sanya muyi rausaya 'yan uwa mu taho da baya baya mune muke cashewa a group. @YUSRAH YMA DUTSE PAGE 01 Parking yai da matu'kar 'karfi a cikin tabkekiyar babbar rumfar aje motocin dake 'katuwar harabar gidan su wanda da sauri wani mutum dake sanye da uniform yazo ya bude masa cikin girmama yace "u're welcome sir" fitowa yai cikin taku mai kyan burge mai kallon sa ya nufi kofar da zata kaishi cikin palor yana rike da rigar Army dinshi a hannunsa yaji mamaki har yana d'an zaro kyawawan idanuwan shi waje ganin babu wanda ya kula da shigowar shi hankalin su naga kallo wasu naga waya gyaran murya yai wanda a tare gaba d'ayan su suka juyo suna maida hankalin su kansa duk idanuwa suka zaro kamar zai fito waje dan tsoro da mamaki lokaci guda suka rud'e kowa ya gigice aje waya Afifah tai tana murje idonta ta bud'e ganin da gaske shine a tsaye ba gizo yayi mata ba yasa a rud'e tace. "Yaya discipline kai ne"?. A yadda tai masa maganar yasa ya sake zaro mata idon nasa ta gansu dakyau 'kila ko ta dawo hayyacin ta d'ora hannu tai aka da gudu tabar falon tai stairs tana cewa "wayyo Allah shikenan discipline ya dawo zaman bedroom ya dawo jama'a ku fito ku taya mu kallo" kai ya jinjina a ransa yace "hummm Afifah is so funny zan kama ki zaki bayani" wucewa yai zuwa ciki da kallo sauran suka bishi suna sauke ajiyar xuciya gashi 'kafafun su sunyi nauyi balle su tashi kafin ya dawo su gudu ita kam Momy lamarin su na bata dariya idan taga suna shiga firgici duk lokacin da suka ga Aliyu shigowar Daddy kenan ganin yadda yaran nasa suke yasa shi dakatawa yana karantar yanayin su domin ya sani matukar suna halin lafiya yana dawowa zasu tare shi da farin cikin su sa'banin yau da yaga damuwa a fuskokin su hannun karamar ya ri'ko yana mikar da ita tsaye yace. "Auta na miye yake faruwa ne"? Kafin tai magana Fati dake gefe tai wuf tace "Daddy ka taimake mu wallahi ya dawo" cikin rashin fahimta Daddy yace "waye ya dawo kuma"?. "Yaya boss" Elham dake gefe tai maganar kamar zatai kuka kallon ta Daddy yai da d'an mamaki a fuskarsa yace "wai Aliyu Haidar d'ina ne ya dawo gida d'ana ya dawo my son is back" duk zaro ido waje sukai jin abinda Daddyn yace ga kuma farin ciki ya bayyana a fuskarsa d'aya bayan d'aya ya kalle su yana murmushi yace "haba koda naji gaskiya shiyasa naga kun nutsu kowa ta kama kanta masha Allah yanzu wace a cikin ku zata je ta kira min shi"? Duk shiru sukai suna sunkuyar da kai aka rasa mai tari 'yar dariya Daddy yai yana girgiza kai yace. "Ke Elham je ki kira min shi". Kallon Daddy tai hawaye ya kawowa a idon ta lokacin data mi'ke da d'an mamki Daddy yace "wai duk meye hakan Aliyu Yayan ku ne d'an uwan kune fa amma sai ku ri'ka nuna damuwarku idan ya dawo me ya sa"? Goge hawaye Elham tai tana cewa "Daddy ba gudun shi muke ba lamarin yaya Aliyu ne sai shi". "Ok kinga bar kukan je ki kira min shi" wucewa tai yayin da Daddy ya bita da kallo yana murmushi kafin ya kalli sauran yaran nasa da duk sun kasa sukuni tafiya Elham take tana tsara da yadda zata iya shiga dakinsa tai masa magana a hankali ta bud'a kofar falon ta shiga ganin baya nan yasa ta wuce bedroom d'an kwankwasa kofar tai amma shiru ta sake ba amsa hakan yasa ta bud'e ta le'ka yana kwance a kan gado ya zubowa kofar ido yaga wanda zai shigo ganin ya ganta yasa ta tsaya daga jikin kofa tana cewa. "Yaya kazo Daddy na neman ka" tana fad'in haka ta juya da sauri tai waje kamar tana tafe yana bin bayanta haka ta ganshi a parlon daidai Afifah ta sauko ya jawota yana tuma mata dundu a bayanta 'kara ta saki ganin an fara daga kanta da gudu tai yin bayan Daddy tana 6uya Elham kam tunda ya fito jikin ta yad'au rawa bata farga ba ta ganshi a gabanta ri'ko hannun ta yai yana mi'kar da ita tsaye fuska a had'e sosai cikin fad'a ya soma magana. "Ke dan uban ki ni sa'an wasan kine da zaki min magana ta kofa"? Da mamaki Momy tace "yau nake ganin ikon Allah a gurin ka Aliyu to da ta ina zatai maka magana ta window"?. "No Momy yarinyar nan dan rainin hankali babu sallama taje tana min ihu a kofar bedroom harda gudu kamar taga mala'ika". "To da meye kai mala'ikan yara ne mana kaga sakar min hannun yarinya kar ka karya ta" Momy tai maganar tana kallon yadda idanuwan Elham d'in duk suka fito waje sakar mata hannun yai yana bata ran'kwashi mai zafi a tsakiyar kan ta wanda yasa da sauri ta dafe kan na ta kallon Afifah yai yana cewa "ke discipline ya dawo Fati matsalar ki ya dawo Elham damuwar ki ya dawo Husnah kukan ki ya dawo mai hana ku shan iska mai dad'i kamar yadda kuka ce ya dawo kusa Allah a ranku ban canza ba ina nan yadda nake yadda kuka sani har nafi da na dawo babu wacce zata sake jin dad'i a cikin ku" ri'ke ha6a Momy tai tana kallon sa tace "nikam yau nake ganin wata 'kaddara ayi mutum fad'a kamar kububuwa dan Allah ka rika shan ruwan sanyi Aliyu". "Momy wadannan yaran naki basa jin magana gabaki d'ayan su kuma zan saita musu zama badai farin ciki suke da tafiya ta ba gani na dawo babu me sake runtsawa mai kyau a cikin su har na koma". "Shikenan to idan ka gama fadan ka zauna mu gaisa daga dawowar ka duk ka hargitsa mana gida" zama yai suka gaisawa sukai masa sannu barka da dawowa domin ya dad'e baya gida sai yanzu ya samu yazo sosai suka saka shi a gaba cikin so suna kallonsa suna sake tambayarsa ya wajen aikin nasu shi yana fad'a musu abinda ya cancata ya fad'a akan aikin nasa wanda zai sanyaya musu rai amma ina soja ina samun kwanciyar hankali saida suka gama zancen nasu Daddy ya tambaye shi "Aliyu yaushe zaka koma amma dai bada wuri ba fatan zaka dad'e"?. "A'a Daddy karamin hutu na kar'ba maybe three weeks ma na koma" ya fad'a yana kallon Afifah da Elham lokacin da suka tafa cikin murna murmushi yai yana jinjina kai lallai yaran nan basu da hankali amma yana daidai da zamanin su maida hankalin sa kan Daddy yai jin yace "haba dai sati uku fa Aliyu da wuri haka shekarar ka uku da mun shiga ta hud'u fa baka zo gida ba sai yanzu amma kace sati biyu kawai zakayi meyasa baza ka dad'e ba"?. "Kuyi hakuri Daddy yanayin aiki ne haka" kai Daddy ya d'aga yana cewa "babu komai munsan da haka Allah ya taimaka ya kuma albarkaci rayuwarka da zuriyar ka". "Amin Daddy na gode" kiransa da akai a waya ganin mai kiran yasa ya mi'ke yana kallon Daddy yace "ina son zan fita". "Ok ba matsala Aliyu ka kula" murmushi Aliyu yayi domin dama yasan wannan a zaune take sai Daddy ya fad'a matu'kar zai fita sai yace masa ka kula saboda son da yake masa ganin Sameer ya sake kiran sa a karo na biyu yasa ya fita suna ganin ya bar gidan suka fara sauke ajiyar zuciya da sauri Afifah tazo gaban Daddy tana durkusawa tace "dan Allah Daddy idan Yaa discipline ya dawo kasa shi ya koma yai hutun sa acan" kallon ta Daddy yai kamar zaiyi dariya ganin duk tabi ta burkice yace "me kika ce Afifah Aliyun nawa zance ya koma inda ya fito yai hutun sa acan ko agola bazan yiwa haka ba balle shi d'an da na haifa d'ana nefa yaushe rabo na dashi ku bakwa taya ni kewarsa ne"? Tura baki Afifah tai tana cewa "amma Daddy kana ganin abinda yake mana daga dawowar sa"?. "Eh na gani ai baifi gyara ba dama kun manta yaushe rabon da ku shiga cikin nutsuwar ku kamar yau hakan ya min dad'i sosai ina so na ganku a nutse" yana rufe baki Afifah ta mi'ke tana cewa "tunda kace haka Daddy wallahi zaman lafiya na kawai naje na hada kayana gara na tafi gidan su Momy kafin yai hutunsa ya koma dan na tabbata idan na zauna ko burbushi na baza'a samu ba a gidan nan muddin Yaa discipline yana nan" ta fad'a tana nufar hanyar hawa stairs muryar Daddy taji yace "kada ki soma had'o kayanki a gidan nan zaki zauna babu inda zaki je har ya gama hutunsa ya koma" tuntu'be Afifah ta kwasa jin abinda Daddy yace yasa ta tsaya cak ta kasa gaba ta kasa baya kuma ita bata juyo ba cigaba Daddy yayi "Afifah idan baki tsaya kun fahimci juna ba a matsayin ku na 'yan uwa sai yaushe ko sai bayan ran mu sannan za kuyi zumuncin idan kunga babu mu? Ki nutsu ba wani abu bane bana so na sake jin wata magana ki dawo ki zauna cikin 'yan uwan ki" dawowa Afifah tai tana zama batare da ta sake cewa komai ba yayin da Elham ke mata dariya a boye ganin yadda take kumbura fuska tana cika da batsewa. Fitar Aliyu daga gida Sameer ne yai kiransa a babbar rumfar dake kafe a kofar gidan su ya ganshi har lokacin yana sake gwada kiransa ganin ya fito yasa ya kalle shi yana aje wayar yace "haba Aliyu tun d'azu inata jiran ka baka fito ba bayan kasan labari na kai min ka dawo ina barci bansan lokacin da nayi tsalle daga kan gado na sauko 'kasa ba saboda farin ciki amma ina ta kiran ka baka d'aga ba"? Karasawa Aliyu yai yana cewa "sorry kayi ha'kuri na tsaya gurin Daddy ne muna magana kasan sauka ta fa kenan ba jimawa nayi da zuwa ba" hannu Sameer ya mi'ko masa yana cewa "ok barka da zuwa gida bayan lokaci mai tsawo muje ka bani labarin inda kuke fatan komai lafiya"? Bai amsa masa ba sai wucewa da sukai Aliyu na cewa "am Sameer yaya ajiya ta take fatan tana lafiya right"?. Murmushi Sameer yai yana cewa "ayya Marshall albishirin ka ajiyar ka tana lafiya ina kula da ita yadda ya kamata babu wani abu daya same ta". "Ka tabbata"?. "Kwarai aboki na". "Bana son wasa Sameer please idan da matsala ka fad'a min na sani dan Allah"? "No nima da gaske nake maka ka yarda dani Marshall ba wasa abinda nake fad'a maka tsantsar gaskiya ne tana lafiya sosai". "Ok shikenan amma zan iya ganin ta yanzu kuwa ko sai zuwa jimawa"? Murmushi Sameer yai yana jinjina kai yace "eh zaka iya ganinta sosai mezai hana muje na nuna maka ita" fita sukai daga harabar rumfar suna tafiya wani gida suka shiga mai gate saidai ya tsufa har tsatsa yake kuma a hakan ta waje yafi ta ciki dama-dama domin gidan a ru'be yake ta ko'ina magidanta maza uku ne a gidan kowa da kofar sa da iyalan sa da tsohuwar gidan mahaifiyar su tana nan a raye itama da nata part d'in ba tsananin talauci ne ke damun gidan ba a'a ido ne yai musu yawa mazan gidan kowa bazai fidda kudi ya gyara shi kadai ba kuma su had'u su gyara rashin hadin kai ya hana d'aya headmaster ne na secondary daya Mopal ne dayan shine baya aikin gwamnati amma yana d'an kasuwancin sa ba laifi kuma yana samun kud'i shima gida ne daya tara mutane da mata da 'ya'ya masu yawa gidan ya tara gwarama akwai gulma munafinci yida wani hana zaman lafiya da akwai matan aure shida a gidan kowa macen shi biyu ga kuma samari da 'yan mata kofar tsohuwar gidan suka fara shiga da domin Aliyu ya gaishe da ita yara da yawa suka tarar zaune a gurin ta ganin tayi ba'ki yasa suka fara mi'kewa d'aya bayan d'aya suna fita zama sukai bayan sun gaisa kaka dake cin goro tace "Samar waye ne wannan d'in na kusa dakai"? Had'e rai Sameer yai yana kallon ta yasan dama sai tayi magana yace "kai hajiya wai dan Allah meyesa kike ce min wani Samar nifa bana son wannan sunan ki gyara" aje goron tai tana masa da'kuwa tace "naci gidan ku tun kafin na haifi ubanka nake rayuwa nasan komai shima nice na raine shi saida ya taso na nuna masa komai zakai min wata magana". "To hajiya ke d'ince da kayan haushi shi yasa ban cika shigo miki ba saboda fad'a muke idan ma nazo". "Karka sake shigowa daga yau ai ba kai kad'ai bane jika na gasu nan da yawa baza su 'kirgu ba saina za'ba". "Basai kin za'ba ba Hajiya kowa jikan kine". "Nidai akwai wadanda ba jikanu na ba domin ni jikanu na suna da farin jini". "To kuma waye mai 'bakin jini a gidan nan"?. "Ban sani ba matse ni saina fad'a maka" zaro ido Sameer yai yana cewa "wa nina isa na matse ki indai nima ba so nake su Abba sun matse ni ba kinga hajiya duk mubar wannan ga jikan ki yazo gaida ke" ya fad'a yana nuna mata Aliyu kallon sa Hajiya tai tana cewa "waye ne ban gane shiba d'an nan daga ina"? Samir ne ya bata amsa "Aliyu ne daga gidan Daddy Ahmed". "Tofa waye dad'i Ahmad kuma"?. "Bafa dad'i Ahmad ba Hajiya Daddy Ahmed nace". "To ai ban gane ba kamin yadda zan fahimta mana ni bazan iya fad'ar abinda kace ba" ganin zata d'ora masa wahala yace "Hajiya nan kusa damu nake nufi gidan Alhaji Amadu minister yanzu kin gane"? 'Yar zabura hajiya tai tana zaro ido cike dake da son zuciya tace "ayya yaron daya ya ke soja ne kaga marmari daga nesa ku ake wa kirari tuwon 'kaya Allah sarki yaro ashe ka dawo kullum saina yi sallar dare saboda kai da safe na sayo 'kosai nayi sadaka nace kuna can jeji ba gida ba gari fata na ka dawo lafiya sai kaga kwatsam kayya rayuwa" hajiya ta karasa maganar tana fashewa da kuka shiru Aliyu yai yana kallonta Sameer dake dariya yace "ki daina kuka hajiya ai tafiya ba mutuwa bace ba gashi ya dawo ba"? Kai Hajiya take girgizawa tana share hawaye da gefen zaninta tace "ka barni nayi Samar ka barni wannan abun kokawa dole ayi kuka a kai". "Shikenan to hajiya zamu tafi" mikewa sukai kud'i Aliyu ya ciro yana bawa Sameer ya mi'ka mata wanda dama tana goge idanu tana kallon shi ta tsananin yatsun ta da sauri ta kar'be tana masa godiya suna fita da sauri ta daga fulo ta saka tana cewa "haba malam zamanin nan saida basaja saida farauta ba gashi na samu kud'in 6atarwa ba daga zuwan d'an arziki Allah yasa gobe ma su sake shigowa" ta karasa maganar harda d'aga hannu sama ta shafa a fuskarta. @YUSRAH YMA DUTSE PAGE 02 Fitar su daga gurin Hajiya daidai 'yan mata biyu zasu shigo gidan su kuma suna shirin fita wacce tafi shishshigin da sauri ta tari Sameer tana cewa "Yaya Sameer waye wannan kamar Yaya Aliyu na gidan su Afifah ko"? Wucewa sukai Sameer na cewe "ba kama bace shine" zaro ido tai tana dafe'kirji tare da binsa da kallo tace "wow lokacin wanka yazo lokacin sa kyawawan kaya da lalle akai akai yazo zuwa gyaran jiki saloon ba kama hannun yaro bari naje gurin hajiya" tai maganar tana kallon wancan d'ayan data ta'be baki daidai sun ci gaba da tafiya kamar baza tai magana ba sai kuma tace "ai bake kad'ai ce kike son shi ba sannan ba ke kad'ai ce a 'yan matan gidan nan yake burge ki ba muje gurin hajiyan tare nima a wana 6angaren haka abun yake Ina jinsa a raina Allah ya baiwa me rabo sa'a domin nasan sama da mutum biyar ne ke sonsa a gidan nan kinsan da haka"? Kai Rasheedat ta jinjina tana cewa "eh tabbas na sani amma ina ganin duk na fiku son sa ai" da sauri Bilki tace. "A'a Rasheedat a yadda kike ji a ranki ba amma na tabbata idan bud'e tawa zuciyar za'ai sai kin tsorata saboda girman son da nake masa" murmushi Rasheedat tai kamar zata tanka mata sai kuma ta share har suka shiga gurin Hajiya dake kishingid'e a d'an parlonta tana sauraron radio kallonsu tai tana cewa "zancen me kuke kuda kullum kuna tafe kuna magana kamar wasu ta'ba'b'bu"? Zama sukai a gabanta Rasheedat na cewa "akan Aliyu ne dan gidan ministan nan alhaji Ahmed san kowa" jin abinda suka ce yasa Hajiya gyara zama ta tashi zaune tana kallonsu tace "to meya faru kuke magana a kansa"? tai musu tambayar tana sake zaune fulon da tasa kudin da Aliyu ya bata domin tasan matu'kar suka gani saita basu wani abu shiyasa take 6oyewa matsowa kusa da ita Bilki ta sake yi tana cewa " "babu komai Hajiya kawai son shi muke dukkan mu" zaro ido tai tana cewa. "Da gaske kuke yaran nan"?. "Allah hajiya". K'asa Hajiya tai da murya sosai gudun kar wani yazo shigowa yaji tace "yauwa 'yan albarka haka nake son ji kwanan nan zan ji'ke da kud'i idan d'ayar ku ta aure shi na tabbata yaron nan zai jiyar dani dad'i ku dage yasan daku yasan kuna son sa idan bai so wata ba zai so wata tunda naga yana da mutunci d'an arziki ne ya gaji halin mahaifin sa" ta 'karasa maganar tana d'auko kud'in daya bata ta nuna musu tana cewa. "Kun ga yanzu nan Samar ya kawo min shi kalli alherin daya min idan kuma akace yayi aure a gidan nan kullum jalaf d'in taliya da kifi ga zobo mai sanyi nasan shine abinci na dare da rana dan Allah yaran nan kada kumin bakin ciki kun ji"? Kallon juna sukai suna sha'kewa da dariya suka ce "sai hajiyan mu muna yinki za'ai yadda kike so" washe baki tai yauwa ko kufa haka nake son ji". Cikin wayo Bilki tace "amma hajiya kinsan bazai so mu a haka ba dole sai muna kyawawan shiga irin ta 'ya'yan masu kud'i muna kwalliya kuma ga shi bamu da kud'i yanzu ni saurayi na yayi tafiya" dariya Rasheedat tai tana cewa "nima nawa garan yayi tafiya shekaran jiya kuma banda ko sisi hajiya a cikin kud'in daya baki zaki bamu ko dubu biyar ce muje mu fara rage wasu abubuwan tunda kema kina son shiga cikin tafiyar" zaro ido hajiya tai tana mayar da kud'in ta cikin inda ta d'auko shi tace "caf dubu me zan baku dubu biyar naji kunce lallai yaran nan baku da hankali ko biyar bazan bayar ba balle dubu biyar kuje gurin iyayen ku su baku man dama dan ina so kuma nice zanyi muku jagorancin komai kenan"?. Hada ido sukai suna 'kiftawa Rasheedat tace "shikenan hajiya zamu nema amma ki sani idan yazo yace yana son mu ya aure mu kada muga yar 'kafar ki a gidan idan ma kinje zamu sa securities suyo waje dake mu nuna bamu sanki ba daga mu sai iyayen na mu tunda haka ne" shiru hajiya tai jikin ta yayi sanyi ganin batai magana ba Bilki tace "kefa Rasheedat ki rabu da ita da alama bata bu'kata dubu goman daya bata zata isheta rayuwa tashi mu je" ganin da Hajiya tai suna kokarin tashi da sauri tace "a'a ku tsaya badai dubu biyar bane gashi" ta fad'a tana d'auko kud'in ta basu badan ranta yaso ba tace "saidai na baku Kowaccen ku dubu biyu nima fa dubu goma ne kawai" kar'ba sukai suna mi'kewa Rasheedat tace "karki damu Hajiya dubu bibiyun ma tayi mana raba arne da makami ibada ce" a hasale Hajiya tace "kuma dan ubanki nice arniyar saboda ke ba 'yar mutunci bace"? Ta'be baki Rasheedat tana kallon ta da gefen ido tace "sai an kula kucaka take yanga ke kike yi mukam munyi nan" ta fad'a suna fita da ashar Hajiya ta raka su tana mi'kewa ta biyo bayansu tana cewa "ubanku ya make uwarku kuzo ku

Chapter 1 of 34