kofar an bud'e 'kiiiiiii wanda ita da take jiki a jingine tai baya luuuu zata fad'i da sauri matar ta ri'ko hannunta tana dawo da ita ta tsayar ta numfashi Baby ta sauke yayin da doctor daya bud'e kofar ya fito ko inda Babyn take bai kalla ba ya wuce a abun sa sosai ran baby ya 6aci musamman da taga Ammar ne abokin Shareef tasan za'ai haka gabadaya hospital d'in nan su biyun nan sune 'yan jin kai wanda baka isa su tsaya su saurare ka ba 'kak'karfan tsaki taja tana d'aukar handbag d'inta data fad'i gefe matar dake tsaye a gabanta ta kalleta tana cewa.
"Kin gani ko shiyasa a rayuwa ake so ka kyautata bakasan wanda kaima zai taimake ka ba gashi ina tsaye ina ta neman alfarma a wajenki kin 'ki yi min amma gashi wani yazo yayi silar fad'uwarki ni kuma na taimaka miki ko ta haka ya kamata ki d'auki darasi ki daina wula'kanci d'an Adam ba abun wula'kantawa bane kinji"? Maimakon Baby ta d'auki maganar da matar ta fad'a mata sai wani banzan kallo data watsa mata tana cewa.
"Dama nace ki taimake nine mai yasa baki barni na fad'in ba taimakon ki bai 'kareni da komai ba sai takaici kar kisa a ranki naji dad'i balle kiyi tunanin zan gode miki mtwwwe taja mata tsaki" wuce tabar gurin tana masifa ji take kamar ta rufe matar da duka da kallo matar ta bita tana jinjina kai lallai ta dad'e bata ta'ba ganin mara tarbiyya irin Baby ba koda ace gidansu ba manya bai kamata ta aikata abinda ta aikata mata ba itama wucewa tai ta shiga ta baiwar 'yar tata ruwa duk da barci ya d'auke tama tun tana kiran ruwan shiyasa ta tasheta ta bata.
Batun baby kam tana barin gurin kanta tsaye office d'in Shareef ta wuce harta rike handle d'in zata murd'a sai kuma ta tuna yayi mata warning kwanan baya cewa karta kuskura ta sake shiga masa office tsayawa tayi tana juya bayanta can take hango shi sun gitta su uku tare da wannan abokin nasa dayai silar ta kusa fad'uwa yanzu da kuma wata bururwa mai glass da takarda a hannunta da sauri tabi bayansu harda d'an gudunta amma bata gansu ba tsaye tayi tana kallon gabas da yamma ko zata hangon su saidai babu alamarsu kaita jinjina tana juyawa ta koma kofar office d'in nasa ta tsaya tasan duk tsiya nan da a tashi ai zai dawo tana so ta bashi ha'kuri ne akan abinda ya faru kwanan baya gashi shi kuma sai yawo yake mata da hankali.
Haka ta wuni batai aikin daya kawota asibitin ba har aka tashi sai a lokacin taga Shareef ya rufo office d'insa ya fito numfashi ta sauke da sauri ta karasa tana cewa "Shareef dan Allah ka tsaya muyi magana" ko kulata baiyi ba har yaje gurin da motarsa take ya bud'e ya shiga ganin datai yana shirin rufewa ta ri'ke murfin motar tana girgiza masa kai tace "haba dan Allah Shareef ya kamata ka saurare ni man" kamar bazai magana sai kuma yace "kina da abinda zaki fad'a min"?.
"Sosai ma nice nake da abun fad'a dan Allah Shareef kayi ha'kuri abinda ya faru kwanaki ka yafe ni nasan na aikata kuskure amma nayi maka alkawari insha Allahu bazan sake makamancin irin haka ba har abada fatan zaka yafe min"? Shiru yayi yana ri'ke da sityarin motar kusan mintuna biyu ya d'auka har ta fitar da rai akan zaice wani abu sai kuma taji yace.
"Ok" yana fad'in haka yaja murfin motar ya rufe ya tada yabar gurin kamar Baby ta d'ora hannu aka tayi ta rusa kuka haka taji wani irin ba'kin ciki ya rufe ta me yake nufi da cewa ok anya Shareef ba so yake yaga gawarta ba ta sani tana matu'kar son sa tana so ta aureshi amma ya kasa tsaya ya fahimci irin halin da zuciyarta ta samu kanta a ciki saboda shi kawai akan 'karamin abu ya d'auke mata wuta data san haka abinda taiwa Nihal zai zama to da ta rabu da ita a wancan ranar ko kallonta bazata yi ba amma ba wanda yasan mezai faru a gaba zata zauna tayi nasari akan yadda zata shawo kansa tunda tana sonsa haka zata yi ha'kuri da duk abinda yayi mata kodan ta samu damar shiga jikinsa ta nuna masa manufarta a kansa huci mai zafi ta fitar tana kallon zanen tayun motarsa kafin ta juya ita ma ta nufi tata motar ta shiga tabar asibitin amma ta saka a ranta saita binciko gidan su gara tasan komai nasa idan ya'ki ha'kuri ya yafe mata saita koma 6angaren mahaifiyar sa duk tsiya idan yaga tana kyautata mata tun kafin ya aureta zai kamu da sonta.mm........................
YUSRAH MUSA ABUBAKAR
ZUCIYAR ALIYU CE.............
@DUTSE JIGAWA
PAGE 21
Karfe takwas da rabi Zainab tana d'akinta tana d'inki Bilki ta banko kofa ta shigo ba sallama tana zuwa ta ri'ke kan keken tana cewa "gaskiya bazai yuwu ba haba wacce irin masifa ce wannan da safe baki barmu munji dad'i ba da rana baki barmu munji dad'i ba da daren ma muna so muyi barci dan jaraba bazaki barmu mu huta ba kamar a kanki aka fara neman kud'i to gaskiya bazai ta'ba sa6uwa ba wallahi dole kisan yadda zakiyi" ta karasa maganar tana sake ri'ke kan keken sosai harda jijjiga kallonta sosai Zainab keyi cike da mamakin ta tace.
"Bilkisu sake min kan keke" a masife Bilki ta sake ri'kewa tana cewa "bazan sake ba wallahi bazan sake ba tun karfe bakwai nake so nayi barci amma dan mugunta 'karar wannan tsinannan keken ya hana ni yanzu kuma nayi magana harda wani na sake miki ban saki d'in ba ki 'kwace daga hannuna" jin abinda tace yasa Zainab mi'kewa ranta a 6ace ta kama hannun Bilki ta 6an6are daga kan keken nata sannan ta tattarata ta had'ata waje ta tura kofar d'akin tasa sakata ta ciki ta koma taci gaba da d'inkin ta.
Bilki kam ganin abinda tai mata yasa bayan ta mi'ke daga fad'uwar datai ta kad'e jikinta komawa kofar d'akin tayi tana dannawa jin ta saka masa sakata ta ciki yasa tace "idan kin cika ke isashshiya ce kuma kin haifu a cikin uwarki ki bud'e min kofar nan na shigo wallahi saina 6a66alla keken nan" jin abinda tace yasa Zainab mi'kewa ta bud'e kofar tana kallon ta tace.
"Na isa harna wuce inda kike zato na dan Allah Bilki indai kin haifu 'yar halak ce ki ta'ba min keken nan yau saidai ki kwana da kumburarran jiki wallahi saina miki d'an iskan duka a gurin nan" baki Bilki ta ta'be tana cewa "wallahi saina ta'ba ki dake ni ki daki masifa duk yadda kike jin rashin mutunci nawa ya dame naki ya shanye ba'ayi budurwar da nake tsoro ba kaf gidan nan ba babu 'yar iskan data isa na raga mata wallahi" murmushi Zainab tai tana jinjina kai tace.
"Ai shiyasa nace ga keken nan idan kin isa ki ta'ba tunda bakya tsoron kowa yau zan nuna miki kalata" tsaki Bilki taja tana juyawa ta fita daga d'akin tana cewa "a tari gaba gamon mu dake bazai Miki kyau ba yau dai kinci sa'a barci𤣠nake ji amma badan haka ba wallahi saina nuna miki niba kanwar lasa bace" d'an karamin tsaki Zainab tayi tana komawa kan kekenta taci gaba da d'inki harta had'a rigar ta d'auko skirt d'in shima ta fara had'awa Sameer yayi sallama yana tsayawa daga kofar d'akinta yace.
"Taso ki kar'ba Zainab zan wuce d'aki nane" mi'kewa tai tana zuwa kofar d'akin inda yake tace "barka da dare Yaya Sameer" kaiya d'aga yana d'auko kayan dake wata babbar leda ya mi'ka mata sannan ya d'auko kwalin indomie itama ya bata da mamaki tabi kayan da kallo kafin ta d'ago ta kalleshi tana cewa.
"Yaya Sameer wannan fa"?.
"Sa'kon kine" da sabon mamaki tace "sa'ko na kuma"?.
"Eh".
"To amma waye ya bani"?.
"A'a kiyi godiya kawai Zainab amma karki nemi sanin wanda ya baki yanzu saboda tsaro ri'ke wannan" kallon hannun nasa tayi taga kud'i yakai wajen dubu ashirin haka ko talati bata kar6a ba ta girgiza kai tana cewa "Yaya Sameer kar kasa na kasa barci man wadannan abubuwan daga ina"? Murmushi yayi yana mayar da kud'in cikin aljihunsa yace .
"Ok tom bari na aje miki kud'in a gurin na idan kin tashi bu'kata saiki fad'a min na baki wadannan kayan da kike gani wani bawan Allah ne ya umarce ni dana siya na kawo miki kyauta" cikin sabon rud'u Zainab tace "wani bawan Allah amma meye sunan sa"? Ta tambaya tana 'kure Sameer da kallo duk tunanin ta ko Yaa sayyadi ne ya bayar a bata amma kuma zuciyarta bata amince shi d'in bane..............
Ji tayi Sameer yace "karki damu ki kwantar da hankalinki zan fad'a miki sunan sa amma ba yau ba" yana fad'in haka taga ya wuce zuwa d'akin sa shiru tayi zuciyarta na harbawa cike da tsananin fargaba da'kyar ta iya d'aukar kayan jiki a sanyaye ta shiga dasu d'aki ta aje kwalin sannan ta zauna ta fara fito da kayan cikin ledar takalmi ne da handbag da kuma hijab sai nikaf guda biyu da sar'ka numfashi ta fitar tana sake bin kayan da kallo kafin ta d'auko d'ayar ledar ita kuma kayan kwalliya ne a ciki had'asu tayi guri d'aya ta d'auke tasa cikin wardrobe d'inta kasa komawa taci gaba da d'inkin tayi duk tunani yabi ya dama mata lissafi karshe fita tayi ta d'auki buta tayi alwala kawai tazo ta shimfid'a sallaya ta fara nafila tun lokacin da take yin bai 'karasa ba.
Washe gari da sassafe bayan ta gama karatun al-qur'ani tayi azkar tashi tayi ta karasa skirt d'in da bata gama ba a lokacin da nefa na d'auki iron ta jona ta goge kayan ta saka a leda d'auka tayi ta fita d'akin Umma ta aje saboda mai su zuwa jimawa zata zo ta kar6a ita kuma makaranta zata tafi bayan ta aje kayan lokacin Umma tana karatu itama shiyasa bata gaida ita ba fitowa waje tayi ta shiga d'akin Abban su ta gaida shi taje kofar d'akin Asabe ma ta gaida ita duk da ba koda yaushe take amsawa ba wani lokacin kuma ta amma mata 'kasa-'kasa tsintsiya ta d'auka ta share kofar tas sannan ta had'a kwanuka ta wanke lokacin gari ya waye rana ta fito d'akin Umma ta koma ta gaida ita sannan ta fito ta zuba gawayi a mangal ta saka 'kyallen da take d'inki ta hura wuta sannan ta koma d'aki kafin ya kama.
Fitowar Bilki ganin wani ya kunna wuta duk da tasan bazai wuce Zainab ko Ummanta ba amma tsabar neman rigima saita shiga kitchen ta d'auko yar tukunya ta cikata da ruwa haka kawai ba wani abu zatai dashi ba taje ta d'ora kafin ta d'auko brush da toothpaste ta d'auki buta ta tafi inda ake alwala daidai Zainab ta fito da mamaki take kallon tukunyar da aka d'ora taga bata Umma bace ta Asabe ce kuma tasan yau girkin Asaben ne shiyasa ma ta fito zata had'a d'an abinda zatai breakfast kafin ta tafi school domin duk ranar girkin Asabe bazata fito ta d'ora akan lokaci ba saboda kar Zainab ta tsaya karyawa kuma idan ta tafi bazata raba da ita ta baiwa Umma ba haka baban su ma wani lokacin saidai ya ha'kura da karyawar a gida idan ya tafi can gurin sana'ar sa ya karya duk da shi mutum ne wanda bai son cin abincin waje ko kad'an.
Zainab tana kallon Bilki tana brush batai magana ba saida ta gama tazo zata wuce sannan tace "Bilki kece kika d'ora wannan tukunyar"? A gadarance Bilki tace "eh nice sai akai ya"?.
"Babu abinda akai amma dai nice na hura wutar saboda sauri nake zan tafi makaranta ina so na had'a abun karyawa" ba'ki ta ta'be a she'ke tace "au saiki bari na gama uzuri na da mangal tunda na riga ki d'orawa kuma dai mangal d'in bana kowa bane na baban mune tunda shiyasa siyo balle kice zakiyi min gadara dashi" kai Zainab ta girgiza tana cewa "bazan miki gadara dashi ba kuma ni ban tambaye ki dan kiyi min rashin kunya ba kar kice zaki zage ni".
"Idan na zage kin zaki dake ni ne"?.
"Bazan dake ki ba amma dai na fad'a miki karki kuskura ki zage ni" harara Bilki ta sakar mata tana jan tsaki tace "kanki ake ji wawa da rad'a Nina wuce sai kici gaba da haushin ke kad'ai tunda kin zama karya" tana fad'in haka ta wuce d'akin su sosai ran Zainab ya 6aci shiyasa kawai da taji zuciyarta tazo wuya gashi ita ta hura wutar amma zata tsaya tanai mata raini shiyasa ta wuce kitchen ta d'auko tasu tukunyar ta zubo ruwa daidai yadda zata dafa indomie guda biyu tazo ta sauke tukunyar Bilki ta d'ora tata kafin ta koma d'aki.
Duk abin nan da ake babu wanda ya sani tsakanin Umma ko Asabe balle Sameer da yake d'aki a 'kofar sa a rufe amma idon sa biyu duk yana jin abin da ya ke faruwa Bilki bata sake fitowa ba har ruwan da Zainab ta d'ora ya tafasa ta zuba indomie ta dafa ta shiga kitchen zata d'auko plate ta juye Bilki ta fito ganin tukunyar data d'ora a gefe yasa ta saki wara ba'kar ashar tana kallon kofar d'akin Zainab da gudu ta nufo gurin murhun tana zuwa tasa kafa tayi bol da tukunyar indomie ta zube a kasa ruwan tukunyar tata ta d'auka ta kwara akan garwashin mangal d'in ta kashe wutar sannan tasa takalminta ta tattaka indomie Zainab na tsaye tana binta da kallo na tsananin mamaki harta gama sannan ta d'ago tana huci tace.
"Ke 'yar gidan mitsiyaciya wallahi kinyi kad'an 'karyarki tasha karya banza jaka saboda kinga ina d'aga miki kafa shine kowanne irin rainin wayo kika tattaro kaina zaki sauke shi to bari kiji ni nafi 'karfin ki idan ma ke mayya ce saidai kici kanki"........................
ZUCIYAR ALIYU CE..............
JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION.
@YUSRAH DUTSE
PAGE 22
Tana rufe baki ta ji saukar lafiyayyan mari a fuskarta mai mugun zafi ihu ta kurma tana dafe kumatunta duk zaton ta Zainab ce saida ta d'ago taga Sameer zaro ido tai zatai magana ya sake d'auketa da sabon marin tare da ri'ko hannunta kuka ta fashe dashi cike da tsoro ta soma zunduma kiran Asabe wanda gabadaya a gigice kowa ya fito daga Umma har Asaben ganin abinda yake faruwa yasa Umma tahowa da gudu tana zuwa ta kokarin kwace Bilki 'kin sakinta Sameer yayi Asabe itama dake ihu tana cewa.
"Anya Sameer kana da hankali kuwa kashe min 'yar zakai akan 'yar wani wallahi wallahi bazan yarda ba dole wannan shari'ar aje gaban Hajiya tayi mana iyaka da ku matsiyatan mutane masu mugun hali" ta karasa maganar itama ta ture Umma gefe tayi taga-taga zata fad'i da sauri Zainab ta tare ta Asabe kam sai kici kicin kar6ar Bilki take a hannun Sameer wanda ke ta jibgarta ganin yana neman fitar mata da jini Asabe tace.
"Sameer idan baka saketa ba saina tsine maka wallahi idan ka sake dukan ta bazan yafe maka ba har abada baza ka bari ba Sameer zanyi maka Allah ya isa fa"? Jin abinda tace yasa ya saki Bilki wacce jin ya sake ta yasa ta fad'i a kasa tana burgima da kururuwa har 'yan gidan suka jiwo nan da nan tasa kofar ta cika dam da mutanen gidan sai tambaya ake lafiya meya faru.
D'ago Bilki dake kasa tana kuka Asabe tayi tana cewa "wallahi Sameer sai naci kan uwarka akan bambanci da kake nunawa yarinyar nan ba'kin mugu azzalumi ka tsaya kayi bincike ne daga fitowa zaka hau dukan ta sai kace wanda tayi maka sata kaga yadda kabi ka kumbura mata jiki"?.
Dariya Rasheedat tai tana cewa "to da alama dai akan Zainab komai ya faru dan nasan ba wanda Sameer yake 'kauna a gidan nan kamar ita" ta'be baki Haulat tai tana cewa "ai kuma son na banza ne tunda yana bata komai amma ya kasa samar mata mijin da zata aura indai yana kaunarta ai bazai rasa wanda zai had'ata dashi ba ko a cikin abokan sa" jin abinda Haulat tace yasa sauran yan matan suka kware da dariya wanda hayaniyar da ake ya hana Sameer ko su Umma su ji abinda yake faruwa.
Fitowa Sameer yayi yana d'aukar bokitin wanka ya fita daga kofar batare daya tsaya ya kalli kowa da duk da hayaniyar da ake yi tsakanin matan gidan da kuma Asabe da Umma Zainab dai da taga abun bana 'kare bane gashi kowa laifin Umma yake gani alhali batasan da komai ba yasa tabar gurin kawai ta koma d'aki tayi shiru zuciyarta na turiri da 'kuna can taji Asabe na cewa.
"Muje gurin Hajiya na nuna mata na rantse da Allah akan wannan banzar yarinyar Sameer bai isa ya sake dukan ki ba tunda ni ban isa dashi ba zan kaishi gurin wacce zatai min maganin sa" numfashi Zainab ta sauke lokacin da taji sun bud'e kofa sun fita jiki a sanyaye ta mi'ke tana fita daga d'akin Umma ta hango tana share indomie da Bilki ta zubar da sauri ta karasa tana girgiza kai ta kar'bi tsintsiyar ta tattare tasa ruwa ta wanke gurin tasa tsumma ta goge ta tattare komai duk Umma na tsaye tana kallonta saida ta gama sannan ta d'ago ganin yadda Umma ke binta da kallo fuskarta a cike da tsananin damuwa yasa taji hawaye masu zafi suna taruwa mata a ido kasa tayi da kanta murya a tausashe tace.
"Dan Allah kiyi hakuri Umma duk nice sila laifi nane wallahi da nasan idan nayi mata magana abun zaizo da haka dana ha'kura na tafi makarantar batare dana karya ba tunda Yaya Sameer yana bani kud'in napep dubu d'aya tana isa ta" ta karasa maganar hawaye yana shararo mata numfashi Umma ta sauke ba walwala ko kad'an tace "meya had'a kune Zainab ko laifin kine"? Kai Zainab ta girgiza tana goge hawayen fuskarta tace.
"Wallahi Umma ba nice na fara kulata ba gawayi na zuba a mangal na hura wuta ina d'aki kafin na fito ita kuma ta d'ora tukunya akai shine dana tambaye ta take min rashin kunya gashi ni kuma sauri nake idan na tsaya lokaci zai 'kure min shine na sauke mata tukunyar a gefe na d'ora indomie idan ta dahu saina mayar mata to a lokacin dana gama dafawa na shiga kitchen zan d'auko plate na juye kawai ita kuma ta fito daga d'aki tazo tayi min bol da tukunyar indomie ta zube sannan ta d'aga ruwa ta kashe wutar ta fara zagi na ni ban san ma Yaya Sameer ya na d'aki yana jin mu ba sai naga ya fito ya na dukan ta" ajiyar zuciya Umma ta sauke tare da girgiza kai kamar itama ta fara zubar da hawayen ko ta samu d'an sassauci haka take ji tasan yau kam watakil bazata sake kwana anan ba saidai ta tafi D'an Yana domin indai Asabe ce sai tayi mata 'kazafin da Hajiya zata koreta daga gidan..................
Tunanin tane ya dawo jin maganar Sameer yana cewa "Zainab kiyi wanka muje na raka ki school d'in" yana fad'in haka ya shiga d'akin sa bayan ya aje bikitin da yayo nasa wanka a band'akin su na samarin gidan wucewa Zainab tayi ta d'auki baho ta saka ruwa ta kai bayi Umma kuma ta wuce d'aki data fito ganin kofar d'akin Sameer tayi ya rufe shiyasa data shiga nata d'akin da sauri ta shirya saboda kar yazo yana jiranta amma me ta saka hijab kenan ta d'aura nikaf naji wani yaro a cikin yaran gidan ya shigo d'akin tana cewa.
"Aunty Zainab wai Hajiya tace kije yanzu" wani irin mummunan fad'uwa gaban Zainab yayi har saida ta dafe saitin zuciyarta tana jin yadda take harbawa da sauri rufe idonta data fara ganin ido tayi ga kanta yana juyawa tsabar tunanin abinda Hajiya zatai mata idan taje da'kyar tace.
"Kace mata ina zuwa" to yace yana juyawa ya fita ita kuma ta d'auko jakarta da wayarta ta fito d'akin Ummanta ta shiga sai taga bata nan tayi tunanin ko tana band'aki ta d'an tsaya ta fito taji shiru har na d'an wani lokaci can ta kuma ganin yaron ya sake dawowa yace "wai tace ko baza ki zo bane ita tazo"? Jin sa'kon da Hajiyan ta aiko mat yasa ta fahimci to lallai itama Umman tana can bata bashi amsa ba a wannan karon kawai daya fita ta jawo kofar d'akinta ta rufe ta rufe da Umma sannan ta fita had'uwa sukai da Sameer ya shigo ganin yadda take a hangitse yace "lafiya meya faru"?.
"Hajiya ce take nema na".
"Take neman ki me zakiyi mata"? Kai Zainab ta girgiza tana cewa "ban sani ba amma bazai wuce akan wannan abun daya faru d'azu bane".
"Ok to baza kije ba wuce mu tafi" jin abinda yace yasa ta sake girgiza kai tana cewa "Yaya Sameer idan har na tafi makaranta banje gurin Hajiya ba akan Umma zata sauke fushin ta ni kuma bazan so hakan ba dan Allah ka jira ni yanzu zan fito mu tafi".
Shima ya gamsu da hakan tunda yasan halin Hajiyan ya tabbata muddin Zainab bata je ba ta tafi school d'in nan tofa Abban su ma sai ransa ya 6aci idan ya dawo laifin har shi zai shafa shiyasa da tace bari taje shima yaga hakan shine yafi cancanta waje ya fita wajen samarin gidan inda suke zaune daya daga cikin sune ya bud'e rumfa yake siyar da shayi a gurin d'ayan kuma ya bud'e shago.
Da sallama Zainab ta shiga gurin Hajiya duk da babu mai jinta saboda tsabar hayaniyar da suke yi masu gulma da masu had'a husuma suna gefe suna dariya gabadaya gurin ya cika dam gaban Hajiya Zainab taje tare da dur'kusawa tace "ina kwana"? Wani irin kallo Hajiya tayi mata tana cewa "munafika ina kwana kike tambaya ta? Yana kwano nace yana kwano ko baki ji ba yana kwano uban me Bilki tayi miki har kika saka Samar ya dake ta da sanyin safiyar nan saboda da ba'kin hali da muguwar zuciya to wallahi bari kiji idan dama kin 'ki yin aure ne saboda ki zauna ki zama shed'aniya a gidan nan baki isa ba bana son annamimanci ke kad'ai a gida kin bi kin hana mutane su zauna lafiya gashi ke ba wata uwar kike tsinanawa ba saidai kici ki kwanta ba aikin fari balle na ba'ki" jin abinda Hajiya tace yasa Haulat matsowa cike da gulma tace.
"La Hajiya ta samu aiki fa dama bata fad'a miki ba"? Caraf Rasheedat tace "aikin me amma saidai wanke-wanke a gidan masu kud'i ko ba aikin gwamnati kike nufi ba"? Dariya Haulat tai tana cewa.
"Ba aikin wanke-wanke ba ai an d'auke ta koyarwa a islamiyya yau kusan wata shida tana d'aukar albashi dama bata fad'a kin taya ta murna ba saboda karta baki d'an kud'in 6atarwa"?.
"Taya zata fad'a kamar kin manta wace Zainab gadon ba'kin hali ce ai bata so a sani saboda kar wani yace tayi masa hanya" Zakiyyah ta fad'a tana ta'be baki taci gaba "kinga fa saboda kusan munafika ce kalli makarantar boko ma da nikaf take zuwa wai saboda kar maza suka fuskarta bayan jikin ma nasu ne".
"Ai kuwa gashi nan shiyasa tayi ba'kin jini ba wanda ya ta'ba xuwa gidan nan yayi sallama da ita tunda ta d'ago".
"To waye zai zo bayan yaga tana fita da siffar munafikai".
"Ai kuwa zata tsufa a gida bata samu saurayi ba indai taci gaba da fita a haka nifa ke garama ki canza rayuwa ki bud'e fuskarki kowa ya gani kya samu wani sokon ya diba yakai gidan su".
"Wazai d'auki masifa ya shiga uku indai ba so yake a raba shi da duniyar ba na tabbata wannan yarinyar zata iya kisa".
"Kwarai kuwa tsaf zata kashe mutum ta binne batare da kowa ya sani ba tunda mugunta a zuci take".
"Kai amma anyi asara kyawun d'an maciji baiyi ba".
"To dai gashi duk kyawun nata ya tashi a banza ba wanda ya gani ya yaba".
"Tirrr anji kunya kuma anyi asara ai bazata ta'ba samun mijin aure ba sai kowacce budurwa tayi aure a gidan nan ita
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 34