sha fad'a mata idan ya ba ta ba ya so ta ri'ka cewa a'a tun da ba shi ya ke bata ba ciki ya shige ita kuma ta fita.
YUSRAH YMA DUTSE
** * **
WRITER
Yarima Abdul-maleek
D'an millionaire
Safreeyyah
Royalty
Minister Ashraf
Me kamar sarki
And now
Zuciyar Aliyu ce
Later
👑Yarima Aryan👑
@DUTSE YMA JIGAWA
PAGE 31
Sakamakon yau weekend ne ba ranar aiki bace kuma Baby ta tabbata idan ta kira Shareef ba lallai ya d'auki kiran na ta ba shi ya sa ta yanke shawara kawai bari ta je gidan nasu domin tasan gidan wata rana an tashi daga asibiti ta bi bayan sa a mota ta ga gidan su ta so fad'a masa tsoro ya hana ta shi ya sa yau ta ke so ta yi masa bazata.
Shiryarwa ta yi duk da zuciyar ta tana d'ar-d'ar ba ta san wanne irin kallo zai yi mata ba idan ya gan ta a gidan su sai dai takai ma'kura ne ta kasa jurewa da shariyar da ya ke mata son sa ya na neman yi mata illa amma daga zarar ya ga ta fara zuwa gidan su ta na yiwa mahaifiyar sa alkhairi komai d'auke kan sa dole ya dawo ya kula ta kuma ya so ta 'karshen zancen ya aure ta wanda hakan shine babban burin ta.
Ba ta je da mota ba kawai napep ta hau ta gidan a lokacin iya Mami ce a parlon tana zaune ta ji sallamar Baby.
"Assalamu-alaikum" d'agowa ta yi tana kallon ta tace "Amin alaiki salam shigo man" karasawa shigowa parlon ta yi tana dur'kusawa cikin tsananin ladabin neman gurin zama ta ce "ina yini Mami"?.
"Lafiya kalau".
"Dan Allah nan ne gidan su Shareef"?.
"Eh nan ne Allah ya sa lafiya"? Numfashi Baby ta sauke ta na cewa "eh lafiya dama na zo gaishe da ke ne".
"Ok ayya to sannu na gode ki zauna mana ki ka dur'kusa tashi ki zauna" daga can inda ta ke ta baro ta karasawa shigo ainihin inda Mamin ta ke ta zauna tana d'an kallon gidan Mami kuma ta mi'ke ta na cewa "bari na dawo ina zuwa" hanyar kitchen ta wuce Baby kam ganin ya rage sai ita kad'ai kai ta jinjina tana ri'ke baki tace.
"Tabd'ijan dole Shareef ya ri'ka d'age min kai ya na wulakanta ni ashe d'an manya ne kalli gida dan Allah kamar wanda akai ginin da diamond humm ai kuwa na ga gurin zuwa wallahi daga yau na saka d'ambar kawowa mahaifiyar ka ziyara har sai ka amince min na zama surukar gidan na...............
Shiru ta yi jin takun tafiya yasa ta nutsu Mami ce ta dawo tana zama ta kalle ta tana cewa "yi ha'kuri na bar ki ke kad'ai na shiga kitchen ne gurin me aiki" kan Baby a 'kasa ta'ki d'agowa ta fuskanci Mami dan Mamin tace tana da kunya a sanyaye tace "ba komai Mami".
"Amma ba ki fad'a min daga inda ki ke ba"?.
"Daga tudun yola na ke ni abokiyar aikin Shareef ce hospital d'in mu d'aya to kullum yana yawan bani labarin ki da irin son da yake miki shine nace bari na zo na ga Mamin nan nasa na kawo miki ziyara" kai Mami ta jinjina ta na murmushi tace "masha Allah gurin ku d'aya ke nan gaskiya na ji dad'i sosai kuma na yi farin ciki ashe har a hospital an san ni"?.
"Mun sanki sosai Mami saboda yawan ambaton ki da ya ke yi koda yaushe yace Mami komai Mami duk wani motsin sa Mami za ki ji ya ce gaskiya kin yi dace wallahi Shareef d'a ne na gari mai kishin iyaye mai son walwalar su".
"Ai haka yake ko a gida ma bashi da motsi sai ni ina matu'kar alfahari da shi".
D'an shiru Baby tai tana kallon photon sa dake manne a parlon yayi kyau sosai numfashi ta sau'ke tana cewa "amma Mami sai yaushe zai yi aure"?.
"Ban sani ba domin ina tunanin ko budurwa bai da ita har yanzu ni dai ina so ya kawo 'yata gidan nan amma har gobe idan na yi masa magana sai dai yace akwai lokaci ko sai yaushe lokacin zai zo oho".
"Ai Mami yadda Shareef ya ke da d'auke kai gaskiya zai dad'e bai yi budurwa ba balle ya yi aure saidai idan ku ne za ku yi masa domin ko kallon 'yan mata ba ya yi balle ya samu wacce za tai masa shawara kawai ku ne zaku matsa masa".
"Wannan gaskiya ne mu na ta zance baki fad'a min sunan ki ba"?.
"Suna na Humairah amma Baby ake ce min kowa da haka ya san ni shi kan sa Shareef d'in idan ba Baby ki ka ce masa ba bai san ni da Humairah ba" kai Mami ta jinjina daidai Rabi ta fito da kaya a hannun ta daga kitchen ta zo ta aje kallon ta Momy tai tana cewa.
"Kawo mata nan muna zance ba sai ta je dinning ba" to Rabi ta ce tana d'aukowa daga can take kawo gaban Baby ta aje ta bud'e fridge ta d'auko mata juice da ruwa shi ma ta aje sannan ta koma kitchen d'in.
"Bismilllah Baby ga abun ta6awa nan ki ci" kai baby ta girgiza tana cewa "a'a alhamdulillah na gode tafiya ma zan yi".
"Ah ya tafiya kuma mu na 'yar hirar mu ki bari sai zuwa jimawa man" gyara zama Baby tai domin dama ba niyyar tafiyar ta ke ba kawai dai kar Mami d'in ta ga za'kewar ta ta yi yawa shi ya sa ta ce hakan amma tun da ta bu'kaci ta ci gaba da zama bari ta zauna d'in.
"Amma Mami na ce kamar Shareef ba ya gidan nan ko"?.
"Eh ba ya nan ya je anguwa tun d'azu ya fita".
"Zai dad'e ne kafin ya dawo"?.
"Eh to maybe ya jima d'in dan fitar ta sa sa'a ce yanzu zan iya ce miki ba zai dad'e ba sai kuma ya dad'e d'in ko kuma na ce zai dad'e ki ga ya dawo haka na ke fama da shi" kai Baby ta jinjina ta na d'an sakin murmushi tare da mi'kewa ta ce "bari na tafi Mami sai na sake dawowa".
"Ba za ki tsaya ya dawo ba"?.
"A'a ba sai mun had'u ba kawai dama bazata na so nayi masa sai dai ma had'u a hospital ranar Monday".
"Ai da kin tsaya amma dai ba damuwa na gode sosai Baby na gode Allah ya yi miki albarka".
"Amin Mami ki huta lafiya sai wani lokaci".
"To ki gaida gida sai na gan ki".
Fita Baby ta yi tana sake waigowa ta kalli gidan kamar kar ta tafi haka ta ke ji saidai ba za ta so Shareef ya dawo ya same ta a gidan ba in dai ba so take ta shiga uku ya yi mata wula'kanci ba Allah ya sa hakan ma kar ya tare da maganar ta zo gidan su ranar Monday ko kuma ya yi mata iyaka da gidan.
Numfashi ta sauke lokacin da ta fita daga gidan ji ta ke kamar ta fita daga wata ni'ima ne gaskiya ba ta san wanne irin azababben so ta kewa Shareef ba tana tsoron kar son sa ya zama ajalin ta tsaye ta yi a bakin titi kawai ta na kallon anguwar daga baya kuma ta tsare d'an napep ta shiga ta tafi.
Barin ta anguwar bai fi da minti talatin ba Shareef ya dawo gida sai dai ya ji mamakin yadda ya ga Mami tana bin sa da wani kalar kallo daga baya ya ga ta yi murmushi ta na d'an girgiza kai kallon ta ya yi yana cewa.
"Mami akwai magana a bakin ki ko"? Kai ta jinjina tana cewa "kwarai ma kuwa maganganu masu yawa".
"Me ya faru"?.
"Ai d'azu bayan tafiyar ka nayi ba'kuwa".
"Ba'kuwa dai"?.
"Eh man".
"Amma daga ina ta ke"?.
"Ta ce min hospital d'aya ku ke aiki kuma ka na yawan yi mata zance na shi ya sa tace bari ta zo ta gan ni ta gaida ni".
"Ni d'in da yaushe na ke maganar ki da wata a hospital har ta zo gidan nan ba tare da na sani ba"?.
"Ce min ta yi bazata take son ta yi maka ba nacin da ban yi akan ta jira ka dawo ba ta ce a'a tafiya za ta yi".
"Wacece wannan yarinyar Mami"?.
"Ta ya zan san ta Shareef bayan ko ta'ba ganin ta ban yi ba sai yau" shiru ya yi yana tunani shi fa ba ya kula 'yan mata a hospital wacce ma'karyaciyar aka samu ta zo gurin Mami ta yi masa sharrin ya na zancen ta idan ya je ko dai Baby ce? Ya tambayi zuciyar sa ai kuwa ba wacce za ta yi masa haka sai ita amma me yasa ta yi masa hakan wannan yarinyar muguwar 'yar rainin hankali ce wato ta nan ta 6ullo masa uban wa ya fad'a mata address d'in gidan su har ta zo ta shirga masa 'karyar da bai san ya yi b.....................
"Shareef ka na lafiya"? Yaji muryar Mami ta katse shi kai ya jinjina "eh Mami lafiya ta 'kalau me ne sunan yarinyar da ta zo d'azun"? Dariya Mami tai tana kallon sa tace "dama na san sai haka ta ce min Humairah sunan ta amma am fi sanin ta da Baby" hummm hasashen sa ya zamo gaskiya kenan wato Baby ce dai ta zo ai kuwa zai gyara mata zama dole ya gargad'e ta ya taka mata burki kar ta sake wannan gangancin in dai ta na son zama lafiya.
"Na fahimta Mami ziyara ta kawo miki kenan ko ni tace miki ta zo nema"?.
"A'a ziyara ta kawo min ta ce saboda yawan ambato na da ka ke yi yasa tace ita kuma sai ta zo ta gan ni" Mami na rufe baki Shareef ya furzar da iska ran sa ya soma 6aci jin 'karyar da ta zo ya yarfa sai dai ba ya bu'katar Mami ta fahimta kar ta yi tunanin ko da akwai wani abu a tsakanin su bari kawai ya share hakan zai fi, bai sake magana ba duk da abun yana ran sa kuma ya yi 'ko'kari ya danne ya fuskanci Mami su ka ci gaba da hirar wani abu can daban kamar yadda koda yaushe su ke yi domin ba ya so ta sake masa magana akan Babyn ko da nan gaba ne.
J♠W♠A
Sayyidah Fad'imah R.A
❤️Ahlin girma mafi tsarki Nana Allah ya kadaita ki babu me matsayi irin naki Nana gashi mijin ki ne zaki Haidara sirrin ma'aiki na❤️.
** **
=====♣YUSRAH♣=====
@YUSRAH YMA DUTSE
PAGE 32
Zainab tana kwance a d'akin ta misalin 'karfe tara zuwa da rabi Umma ta shigo d'akin tana tsayawa a jikin keken d'inkin ta tace "Zainab har kin kwanta baki ci abinci ba"? Kai Zainab ta girgiza tana cewa "yau abincin ne bana son ci".
"Ke nan a haka za ki kwanta da yunwa"?.
"A'a Yaya Sameer na ke jira ya shigo na ba shi kud'i ya siyo min awara kuma har yanzu na ji shiru".
"To ai shi Sameer ya shigo ya d'auki abincin sa ya sake fita" tashi zaune ta yi tana cewa "to gaskiya ban ji shigowar sa ba ne".
"Eh lokacin ki na sallah ne daman kuma ba zama yayi ba ya juya dan dama abincin kad'ai ya zo d'auka ko d'akin sa bai shiga ba" jin abinda Umma ta ce yasa Zainab mi'kewa dan ta san ba sake shigowa zai yi ba sai lokacin kwanciyar sa yayi hijab ta saka tana cewa "bari na je ya raka ni na siyo kawai na dawo" ta fad'a tana d'aukar kud'in ta fita daga 'kofar ta su Umma kuma ta koma na ta d'akin.
Tayi sa'a kuwa ba ta had'u da kowa ba daga samarin gidan har 'yan matan ba kowa saidai shagon 'kofar gidan yana bud'e yayan Rasheedat ne a ciki shi ma kuma ba ganin ta ya yi ba wucewa ta yi ta 'kara gaba kad'an ta had'u da Sameer shi kuma ya na tahowa gida tsayawa ya yi yana kallon ta da mamaki ya ce "dama ke ce na yi tantama farkon da na hango ki na san babu abinda zai fito da ke 'karfe goma ta kusa ina zuwa yanzun"?.
"Yaya Sameer dan Allah ka raka ni na siyo awara a can layin kar na kwana da yunwa har na kwanta naji ba zan iya ba dama ina ta jiran ka sai da Umma ta shiga d'aki na yanzu ta ke fad'a min har ka shigo ka d'auki abincin ka".
"Eh ai na le'ka d'akin da ki ke na ga ki na sallah ne shi ya sa na fito abinda aka dafa d'in ne bakya so"?.
"Ai ni Yaya Sameer ka san ban damu da tuwon shinkafa ba bana son shi".
"Ok jira na zo mu tafi" ya fad'a yana shiga gidan ita kuma ta koma gefen hanya ta tsaya jiran sa ya d'an jima sannan ya fito suka wuce daidai Haulat ta sauka a Napep ta ga giftawar su iya Zainab da hijab d'in ta ta gane amma tsabar gulma ko tsayawa ta ga tare da Sameer take ba ta yi ba da sauri ta sallami mai napep ta shiga gida kamar zata tashi sama haka ta fad'a kofar Hajiya 'kwalla mata kira "Hajiya Hajiya kina ina Hajiya yau na ga abinda ya fi 'karfin ido na ki na ina ne Hajiya"? Hajiya dake d'aki a zaune jin kira kamar zata tsaga gidan yasa ta mi'ke tana cewa "ga ni 'yar jarabar kira me ye hakan ne zaki zo ki na min kira na d'aga hankali"? Da gudu Haulat ta fad'a d'akin tana cewa "Hajiya albishirin ki yanzun nan na ga Zainab ta yi bayan layin nan tare da wani namiji Ina tunanin ma kamar shi ne kwarton na ta da take zuwa gurin sa kullum da dare yana iskanci da ita yana bata kud'in da take kashewa" zaro ido Hajiya tai tana cewa "kwarto kuma mun shiga uku ke Haule ba na son 'karya fa a ina ki ka gan ta"?.
"Ba fa 'karya na ke miki ba Hajiya da ido na na gan ta su na tafiya ita da shi sun yi wancan layin nan ki zo muje kar suyi nisa" jiki na 6ari Hajiya ta d'auki mayafi takalmin ma ba iri d'aya ta saka ba kowanne daban-daban ne suka fita tare da Haulat a lokacin fitowar Rasheedat daga kofar su kenan ta hango su suna sauri za su yi kofar gate da gudu ta taho tana cewa "Hajiya ina zuwa haka ko anguwa za ku je na zo nima na raka ku"? Jikin Hajiya ya na mazari tace "ina wata anguwa Haule ce ta ga Zainab sun yi bayan layin nan tare da wani kwarto shi ne ta fad'a min can za mu tafi" zaro ido Rasheedat tai tana cewa "kai kwarto kuma bari mu ma mu je kar mu tsaya a bamu labari gara ayi komai a gaban mu" bin su ta yi su ka fita daga gidan daidai Zaid shi kuma ya na shirin shiga tsayar shi Hajiya tai tana cewa.
"Yauwa Zaidu gara da mu ka had'u da kai dama dole sai dai mu je tare da namiji dan abun ya fi 'karfin mata" tsayawa Zain ya yi yana cewa "me ya faru Hajiya ina za ku je a haka".
"Wai Zainab ce ta bi wani saurayi su kai bayan layin nan Haulat ce ta gan ta yanzu can za mu je taho dan Allah ka raka mu yadda za ka kama tsinanne ka yi masa duka ka sumar da shege" kai Zain ya jinjina yana cewa.
"Shi ke nan mu je" wucewa su kai su na tafe Hajiya sai fad'a ta ke tana zage-zage Zaid da ke murmushin jin dad'i yace "kin ga Hajiya ta nuna miki wace ita ashe dama 'yar iska ce ki ke so na aure ta ta zama uwar 'ya'ya na"?.
"Taya na san 'yar iska ce ba dan yau da asirin ta ya tonu aka gan ta ba waye ya san tana zuwa gurin samari da dare ba na jin uban ta ya san da wannan labarin amma uwar ta zata sani tunda ba uwar arziki ba ce watakil ma ita ce ta ke saka ta yawon dan ta ri'ka samar mata kud'i tun da ba sana'ar uwar komai ta ke yi ba".
Kai Zaid ya jinjina ya na cewa "humm ai kuwa sai na gasa mata magana wacce za ta saka ta kasa jin dad'in zaman duniya bari mu je gurin dama ai nasan munafirci ne ya sa ta ke saka wannan nikaf d'in ba dan ta tsare mutuncin ta ba ne kawai dan ta mayar da mutane shashashu ne ace ta na tsoron Allah bayan gashi duk dare mazan banza ta ke bi wallahi yau sai ta gane ruwa ba sa'an kwando ba ne bari mu je ba 'kwarton nata ba har ita zan had'a naiwa d'an banzan duka" ya fad'a suna shan kwanar layin Hajiya dake ta faman sauri kamar za ta kifa ta ce "kai dai muje kawai burina na ga wanne d'an matsiyatan ne ya ke bata kud'i har ta iya fitowa da dare ta zo gurin sa" ta'be baki Zaid yai ya na cewa "Hajiya ko bai bata kud'i ba Zainab za ta iya bashi kanta kyauta kar ki ja akan hakan" zaro ido Hajiya tai ta na shirin magana Haulat ta ce "yauwa mun kusa ku taho dai" ita ce a gaba ba su yi nisa da shiga layin ba su ka fara hango su daga can nesa tare da Sameer sai dai ba su gane shi ba da yake da nisa tsakanin su shi kam har ya raka ta sun siyo sun dawo da mamaki yake kallon Hajiya tun daga nisa ya gane ta.
"Su kuma wadancan ina za su je haka a wannan daren gayyar su guda"? Da alamar tambaya Zainab tace "su wa ye"? ta fad'a tana kallon sa domin ita ko kad'an ma ba ta lura da wasu su Hajiya da suke tahowa ta gaban su ba saida Sameer ya nuna mata gaban na su da yatsa yana cewa "ga su can su Hajiya ne" kallon gurin ta yi ta ga yadda suka d'ebo gayya haka kawai ta ji fargaba lokaci guda ta dirar mata ta san ba lafiya ba babu abinda zai fito da su yanzu kuma abun mamakin har da Hajiya ma.
"Amma me ye zai fito da su yanzu"? Ta sake fad'a cike da zulumi kafad'a Sameer ya d'aga yana ta'be baki yace "oho mu su wannan matsalar su ce koma menene ya fito da su d'in" shiru Zainab ta yi tana kallon su daidai sun had'u aka tsaya ana kallon kallo tsakanin su ba wanda ya yi magana sai Zainab da ta ga duk ita suke kallo me ye hakan Sameer ne ya fara magana "Hajiya ina zuwa haka da sauri"? Zainab ta nuna da yatsa tana cewa "ga wacce mu ka biyo ina saurayin da su ke taren fatan ka yi masa duka ba ka barshi ya gudu ba"? Da mamaki Sameer ya ce.
"Wanne irin saurayi ki ke magana kuma Hajiya"? Wani kallo ta yi masa ganin kamar hankali ya ke son raina mata tace "au me ka ke nufi kai ma munafirtar tawa za ka yi saurayin da aka gan ta yanzu da shi sun yo nan layin tare maganata ta tabbata kenan Zainab bin maza ki ke da uban wa aka gan ki yanzu kin yi bayan layi iye"? Hajiya ta fad'a tana kallon Zainab wacce ta zaro ido a rud'e jikin ta ya fara d'aukar rawa tsabar yadda maganar an gan ta tare da wani saurayin ta daki ran ta had'e rai Sameer ya yi yana cewa.
"Wai Hajiya wa ye ya je yace miki an gan ta da wani ta yi bayan layi har ki ka yarda ki ka fito"? A masife Hajiya ta ce "uban ka ne yaje ya fad'a min wato nan kare ta ka ke yi saboda kar mu zarge ta kenan ko me"?.
"Ni nace miki kare ta na ke yi ba kawai dai zan fad'a miki gaskiyar abinda baki sani ba kuma baki da tabbaci a kan sa".
"Me kake nufi Samar yanzun ba zuwa kayi ka taho da ita ba"?.
"Daga Ina na je na taho da ita"? Cikin fad'a Hajiya tace "daga d'akin tsinannan saurayin da aka ce an gansu tare yanzu" tsaki Sameer ya ja yana cewa "wai Hajiya wa ye ya fad'a miki tare da wani aka gan ta ni ne fa ba wani ba ne" yana rufe baki Haulat dake gefe tana aikowa da Zainab harara da sauri ta matsa kusa da Hajiya tana cewa "wallahi Hajiya ba gaskiya ya fad'a miki ba kare ta yake amma ni naga wanda suka tafi tare shi wancan gajeren wando ne a jikin sa🙊 kawai dai ban san shi bane amma shi ne d'an iskan nat.........................
Tun bata gama fad'ar abinda ta ke shiryawa ba taji saukar mari me mugun zafi Sameer ya sauke mata shi a fuska 'kara ta fasa cike da azaba ta ja baya tana fashewa da kuka nuna ta da yatsa ya yi yana cewa "ke 'karamar mara kunya ki gyara kalaman ki akan 'yar uwa ta bata kasance 'yar iska ko mazinaciya kamar yadda ku ke neman d'ora mata sharri ba na rantse da Allah daga rana irin ta yau duk tsinanniyar yarinyar da ta sake cewa ta ga Zainab ta yi wani layi da saurayi sai naci bura uban ta ina daidai da ku matsiyatan yara marasa mutunci" yana rufe baki Zaidu yace.
"Kaine babban matsiyaci amma ba 'kanwa ta ba amfad'a mata 'yar iska ce ba ta yi bane"? ya fad'a yana kawo masa mari zai ramawa Haulat ri'ke hannun sa Sameer ya yi ransa a mugun 6ace ya yi masa wani irin kallo yana cewa "kai Zaid ka kama kan ka kar ka kuskura tsautsayi yasa bakin ka ya sake furta kalmar iskanci akan Zainab ka iya bakin ka kafin na fasa maka kai wallahi dukkannin ku ina daidai da zamanin kowanne shege zaku gani kuma" fisge hannun sa Zaid yayi yana huci.
Ganin kamar ya fusata shi ya sa yace "rama mata za ka yi? To bismilllah ga fuska rama ma ta wallahi yau da kaga ikon Allah saidai kayi kwanan asibiti" yana rufe baki Zain yace "saidai mu yi kwanan asibiti tare yaro wallahi baka da 'karfin da ka isa ka min dukan da za'a kai ni asibiti kai kuma ka zauna a gida saidai a kai mu tare domin ko a dawa giwa ta san zaki ka gane"? kai Sameer ya jinjina yana cewa "ban gane ba amma idan kai d'an halak ne ka d'aga hannu ka mare ni sannan ne zan san ka cika ni kuma wallahi tallahi na rantse da wanda numfashi na yake hannun sa yau sai kayi kwanan asibiti mari ka gani" ya fad'a yana mi'ko masa fuska shiru Zain yayi yana huci domin yasan tsaf Sameer zai aikata abinda yace tun da masifaffe ne shiyasa da yaji ya fad'i haka kawai ya ja tsaki mai 'karfi yana hararar Zainab cikin son huce haushin sa ya ce.
"Yar iska kawai uban wa zai aure ki kin gama zubar da kimar ki a gurin wasu Allah ya sauwake min auren mace me fuska biyu irin ki"? 'Bangaren da Hajiya take tsaye ya juya yana cewa "yanzu Hajiya a hakan kike so na aure ta Allah ya rufa asiri tun wuri ta nemi mijin aure d'an iska irin ta kafin lokacin ya 'kure ma ta amma ni dai nafi 'karfin auren mace 'yar duniya mai fuska biyu da safe ta saka dogon hijab har jan 'kasa yake ta rufe fuska da nikaf kowa yana mata kallon mutuniyar arziki amma da dare ta tafi gurin maza ta na basu jikin ta su na biyan ta tirrr.......................
Sha'ko wuyan sa Sameer yayi yana cewa "gurin mazan uwar ka ta je nace gurin mazan uwar ka ta je da uban wa ka ta'ba ganin ta tare da shi fad'a min ko na kashe ka a gurin nan" ya fad'a cikin tsawa yana wujijjiga shi ganin zasu fara fad'a a layi su jawo hankalin jama'a gurin a zo ana tambayar me ya faru lafiya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 34