Share this page
nan ne ban sake ganin ta ba tun sau d'aya"? Da alamar tambaya ya ce "wacce yarinyar". "Humairah na ke fad'a" gani ta yi ya d'an dafe kai alamar tunani can ya ce "Mami wacece Humairah kuma a ina ta ke"?. "Wannan yarinyar 'kawar nan ta ka fa"?. "Wacece 'kawa ta kuma ni ba ni da 'kawa mace" baki Mami ta bud'e ta na kallon sa ta ce "amma wannan yarinyar da ta ta'ba zuwa gidan nan kwanan baya da d'an dad'ewa ta kawo min ziyara har ta ce hospital d'in ku d'aya"? Dogon numfashi ya ja ya na cewa. "Ok Baby ki ke fad'a"?. "Eh yauwa ita fa na ke nufi wai ta na nan kuwa har yanzu ta na aiki a hospital d'in na ku"?. "Eh ta na yi". "Ayya Allah sarki me ya sa ba ta sake zuwa gaishe da ni ba ne"? Kai Shareef ya girgiza ya na cewa "a'a Mami" da mamaki Mami ta kalle shi ta na cewa "kamar ya a'a ko kai ka hana ta"?. "Eh ni na dakatar da ita". "Haba Shareef akan me"?. "Akan wani dalili Mami ina da babbar hujja ta na hana zuwa d'in" "hujjar ka ta me"?. "Mami dole na hana ta ni ba na son d'anyan kai tsabar rashin hankali yarinyar wai ashe so na ta ke nan d'in zuwan da ta yi ta zo ne saboda ta gabatar miki da kan ta ku saba dan ta shiga jiki na". "Kamar ya ban gane ba"?. "So ta ke ta zama surukar ki"? Dariya Mami ta yi ta kallon sa cikin tsokana ta ce "au masha Allah ashe ma suruka ta ce ban sani ba ita ma auren ta za ka yi kenan rana d'aya da na Nihal ko sai daga baya za ka aure ta"? Girgiza kai ya yi da sauri ya ce "a'a ni ba ni da ala'ka da son da take min kuma na fad'a mata gaskiyar akwai wacce zan aura domin ina yaro na ba za ta saka na auri mata biyu ba saboda ba na son hayaniya". "Haka ne amma ni a nawa ganin tun da ta na son ka ba za ta d'aga hankalin ta a gidan ka ba musamman idan ka fad'a mata sharud'an ka na tabbata za ta amince kuma za ta bi umarnin ka". "A'a Mami ni gabadaya yarinyar ba ta yi min ba ne saboda wad'ansu halayen ta marasa kyau na yi iya 'ko'kari na ta gyara tun shekarun baya amma ta'ki shi ya sa na watsar da ita kawai kuma sai yanzu sama ta kai za ta zo ta ce na aure ta ai Mami ki kwantar da hankalin ki ni wacce za tai miki ladabi ta ba ki girman ki na ke da burin aure ba wacce ni ma idan na fad'a ma ta magana ba za ta saurare ni ba ita kuma irin wad'annan matan ce" jinjina kai Mami ta yi ta na cewa "subanallah Allah ya rufa asiri ni kam gaskiya da na gan ta haka ban ta'ba tunanin za ta aikata wani abu mara kyau sai dai hali ba a kamanni ya ke ba Allah ya kyauta ka yi breakfast ne"?. "A'a zan yi sai anjima" mi'kewa Mami ta yi ta tafi dinning ta na cewa "ok ba damuwa ni bari na yi tun da anguwa zan tafi". "Ina za ki je". "Zan je na sake gano jikin Tasnin". "Har yanzu ba ta warware ba ne"?. "A'a ta samu sau'ki ai da yake ka ga idan ba haihuwa ta yi ba ina za ta samu lafiya". "Ok tun da haka ne kawai bari ni ma na zo na yi sai mu tafi tare na kai ki na gano ta sister guda ba lafiya" ya fad'a ya na rufe laptop d'in shi ma ya tafi dinning Mami za ta yi serving d'in ya ri'ke hannun ta ya na cewa "a'a zauna da kai na zan yi serving d'in ki wannan hakki na ne domin tun ban san waye ni ba ki ke feeding d'ina har na d'ago ni ma ya kamata na rama miki" ya fad'a ya an amsar serving spoon d'in ya saka mata ya aje a gaban ta sannan shi ma ya zuba na sa kallon sa Mami ke ta yi kawai ta na tuna baya ta na jin takaici da ba'kin ciki idan ta tuno cewa ba ita ce ta haifi Shareef ba yadda ya ke son ta ya ke nuna mata kulawa, hawaye ne ta ji sun cika mata ido amma gudun kar ya gani ya damu ta yi saurin gogewa, ganin ba ta fara ci ba ya sa ya d'ago ya na kallon ta ya ce. "Mami ya ba ki fara ci ba ko bashi ki ke so ba"? Murmushin dole ta yi ta na d'an sake fuska ta ce "a'a zan ci man". "To ki ci dan Allah Mami mu tafi" kai ta d'aga ta na d'aukar spoon ta d'iba sai da ya ga ta fara ci sannan shi ma ya ci gaba. **** Kamar yadda Aliyu ya cewa Amirah nan da kwana biyu zai shigo gidan su ya gaida Mama haka ta yi sabon kitso ta je ta yi jan lalle ta bari ba'kin ko ranar da zai zo ta yi, gari na wayewa ta kira shi ta ji yaya zai zo ne ko ya fasa ya ce mata zai zo amma sai 'karfe biyu ai kuwa ranar kamar sallah haka ta ke jin wani irin farin ciki ya cika ma ta zuciya yau Aliyu zai zo gidan su, hummm ai kuwa za ta dage ta had'a masa abinci me shiga rai haka ta gayyaci Nansy su ka tafi ta yo siyayyar abubuwan da za ta yi amfani da su haka ta d'age tun safe take shirye-shirye sha biyu daidai ta fara had'a masa savoury stuffed yam balls da porridge with ganache mix domin ta san ya na son wannan duk abubuwan da ta san favorite foods d'in sa ne sai da ta yi ma sa sannan 'karfe d'aya da rabi ta na yi tayi sallah ta d'auki hijab d'in ta, ta je wani shagon lalle da ke anguwar ta su a gaggauce aka zana mata ba'ki sakamakon an riga an yi ma ta jan, ana gamawa ta dawo gida ta yi wanka Nansy dai ta na zaune ta na bin ta da kallo har ta gama shiryarwa ta d'auko wayar ta ta na danna kiran Aliyu. "Hello Aliyu kun taho ne"?. A lokacin Aliyu ya fito parlor daga part d'in sa kenan ta kira shi agogon hannun sa ya kalla ya na cewa "a'a ina gida amma yanzu zan taho" murmushi ta yi ta na cewa "yauwa ina jiran ka" "ok" ya fad'a ya na sauke wayar ya 'karasa fitowa ainihin cikin parlon duk yaran gidan su na gurin Momy a zaune ganin sa ya sa su kai tsit kowa ya yi shiru su na jiran su ji me zai ce mu su. "Kai ZAMAN uban me ku ke yi anan ba ku tashi kun yi shirin islamiyya ba ko duka ku ke jira"? Da sauri su ka fara girgiza kai d'aya bayan d'aya su ka fara tashi su na girgiza kai su ka bar gurin har rige-rigen shiga part d'in su, su ke kallon sa Momy ta yi ta na cewa "Aliyu ina zuwa na ga ka d'au wanka haka kamar wani ango"? Ta fad'a da murmushi "Momy gidan su Amirah zan je na gaida Mama saboda wancan zuwan da na yi har na tafi ban je ba" kai ta d'aga ta na cewa "ok eh gaskiya ne ya kamata ka je Allah ya kiyaye sai ka dawo" "Amin" ya ce yana fita daga parlon ya fito harabar gida ya d'auki motar sa ya kai ta waje sannan ya kira Sameer ya ce ya fito su tafi a lokacin Sameer shi ma ya yi wanka ya gama shiryarwa ya fito kenan ya ga Umma ri'ke da cooler abinci kallon sa ta yi ta na cewa. "Amma ba fita za ka yi ba ka ci abinci ba"?. "Eh Umma fita zan yi wani guri za mu je" kai ta d'aga ta na cewa "to shikenan ga abincin ka zan saka maka a d'aki idan ka dawo". "Ok Umma na gode" ya fad'a ya na wucewa Zainab da ta fito daga d'aki za ta yi wanka ta yi shirin islamiyya ganin sa da kwalliya ya sa ta ce "Yaya Sameer ina zuwa"? "Anguwa za mu je". "Kai da wa"?. "Tare da Aliyu za mu je gidan su wata yarinya ko za ki raka mu"? Ya na rufe baki da sauri ta girgiza kai ta na cewa "a'a Allah ya kiyaye sai ka dawo" kallon ta ya yi ya na cewa "ok ba za ki raka mu ba"?. "Ni ba inda zan je da dai kai kad'ai ne zan iya zuwa sai dai kuma islamiyya zan tafi". "Ai mu biyun ma za ki iya raka mu kin ga mu, mu na gaba ke ki na baya ana tafiya ana hira ko"? Zaro ido ta yi za ta yi magana sai kuma ta fasa ta wuce dariya ya yi ya na cewa "me ya faru na ga kina zare ido"?. "To tsakani da Allah Yaya Sameer na rasa da wa zan had'a tafiya sai Aliyu"?. "Eh me ye a ciki"?. "Akwai man ni dai a nawa 6angaren har abada ba na fatan tafiya ta had'a ni da shi". "Kaii saboda me"?. "Ni dai kawai na fad'a" kai Sameer ya jinjina da murmushi akan fuskar sa ya ce "ai kuma ba ki sani ba idan 'kaddarar ki ce dole sai kin had'a tafiyar da shi ko bakya so". "Hum'um Allah ya sauwake wallahi dan Allah Yaya Sameer ka daina fad'a" . "Ok shikenan na daina fad'a sai na dawo za mu samu zama mu yi magana" ya na fad'in haka ya fita daidai kiran Aliyu ya sake shigo ma sa ya d'aga ya na cewa "sorry Marshall afuwan gani nan" 'karasa fita ya yi daga gidan da sauri saboda biyu har ta cika ya je ya same shi a mota ya na shiga su ka wuce. "Sorry na bar ka, ka na ta jira na" Aliyu hankalin sa ya kan titi ya ce "ba damuwa ni ma damuna Amirah ta yi ni kuma ba na son takura shi ya sa ka ga na sake kiran ka ka ga tsaraban da zan kai mata nan tun safe na saka a motar saboda kar na manta amma yanzu ma za mu sake bi na dad'a mata wani abu" murmushi ya yi ya na cewa "hummm ni ma da Zainab mu ka tsaya bayan na shirya na fito dalilin da ban 'karaso da wuri ba kenan" kai ya jinjina ya na sauke numfashi ya ce "ok ta na gidan har yanzu ba ta tafi islamiyya ba"? "Eh lokacin da na fito za ta shiga wanka". "Sun gama exam"?. "Sun gama yau kusan kwana goma sha da har zan kira ka na fad'a maka amma sakamakon na san sai ka ce ta yi murnan graduate kawai na yi shiru abu". "Saboda me ka 6oye min Sameer yanzu a rayuwa komai na ke saboda ita ne tun da ita ce komai na wa a rai na, na ke jin ta idan ka fad'a min ta gama dan kud'in da zan ba ta, ta yi graduate shi ne ka 'ki fad'a" kai Sameer ya girgiza ya na cewa "gaskiya Aliyu abubuwan ne na ga sun yi yawa daga wannan sai wancan ka na 'ko'kari ya kamata ka ri'ka hutawa". "Kai ne ka ke ganin ina wahala amma ni indai akan Zainab ne gani na ke har yanzu ban yi ma ta komai ba Sameer ka san yadda na d'au wannan yarinyar a rai na kuwa? Ba za ka ta'ba sani ba kuma ba za ka fahimta ba ni kad'ai ne na ke jin abin da na ke ji" tsayawa yayi ya na girgiza kai shi kad'ai huuuuuhhh ya fitar da numfashi me 'karfi ya na cewa "Sameer lokaci ya yi da ya kamata na bayyana kai na Zainab ta san ina son ta ko zan samu sauki dama school na ke jira ta kammala yanzu ta gama a irin wannan lokacin shi ne daidai da na aure ta domin dama kawai na biya mata ta yi karatu ne saboda ni da kuma yara na ba dan ta yi aikin gwamnati ba babu abin da za ta nema ta rasa a guri na babu ce kawai ba zan ba ta ba ita ma da ana ganin ta zan ba ta" kai Sameer ya jinjina ya na cewa. "Masha Allah ashe kwanan nan za mu sha biki"?. "In sha Allahu domin ba zan bari auren ya ja lokaci ba" ya fad'a ya na horn a 'kofar gate d'in su Amirah me gadi ya bud'e masa su ka shiga Amirah kam dama tun da su ka gama waya ta na tsaye a jikin window ta na jiran shigowar sa ganin motar sa ta shiga ya sa ta ji kamar ta saki gud'a jiki na rawa ta bar jikin window d'in ta d'auki mayafin ta, ta na kallon Nansy ta ce "ke sun 'karaso" kai ta d'aga da wayar ta a hannun ta, ta na chatting ta ce. "Ok sannun su da zuwa". "Ba za ki taso mu je tarar su ba"?. "A'a je ki kawai zan fito daga baya" d'an ta'be baki Amirah ta yi kamar za ta sake magana amma tuna maybe yanzu sun shigo ya sa ta bud'e 'kofa ta fita a can main parlor ta tarar da su suna gaisawa da Mama murmushi ta yi cikin zumud'i ta 'karasa tare da zama ta na cewa "sannun ku da zuwa ya gida Samer har da kai kenan"? Kai ya d'aga ya na cewa. "Eh tare mu ka zo". "Sannun ku to ku taso mu 'karasa" ta fad'a ta na mi'kewa dakatar da ita Aliyu ya yi da cewa "zuwa ina kenan"? Juyowa Amirah ta yi ta na kallon sa yadda ya d'au wanka ajiyar zuciya ta yi ta na cewa "dinning za mu je ku ci abinci". "A'a mun gode"? Zaro ido Amirah ta yi ta na cewa "kai dan Allah Aliyu ka zo ko ruwa ne ku sha" sake girgiza ma ta kai ya yi yana cewa "a'a" kamar za ta fashe da kuka tsabar takaici ganin duk wahalar da ta yi a banza amma in dai ba su ci ba yau idan ta shiga d'aki ta rufe har dare za ta kai ta na kuka........... Ji ta yi Mama ta ce "a'a Aliyu tashi ku je ko ruwa ku sha domin an yi tanadin ku sosai ta zauna ta shirya mu ku abinci da abun sha ba za ku tafi ba sai kun ci" jin abin da Mama ta ce ya sa Amirah sakin wani daddad'an numfashi ta na kallon Aliyu ta ce "yauwa ta so dan Allah ku 'karaso" gani ta yi, ya yi shiru tamkar bai ji abin da ta ce ba mi'kewa Mama ta yi ta na cewa. "Aliyu ku 'karasa dan Allah ku fa ba ba'ki ba ne a gidan nan gidan ku ne amma sai jayayya ake da ku" ta na fad'in haka ta bar parlon ta shige part d'in ta shiru parlon ya d'auka Amirah ta na tsaye ta na jiran ta ga sun taso amma kamar an dasa su dawowa Amirah ta yi ta na kallon Sameer ta ce. "Dan Allah ku ta so mu je" d'an murmushi ya yi, ya na d'aga mata kai ya ce "ok mu na zuwa" ajiyar zuciya ta sauke ta na juyawa ta tafi wajen dinning d'in kafin su 'karaso Aliyu kam ko kad'an bai da niyyar tashi sai ma d'ora 'kafa d'aya kan d'aya da ya yi, ya na d'auko wayar sa ya fara dubawa Amirah da ta zauna ta na jiran ta ga sun taso hango shi ta yi ya na danna waya kawai alamar ba zuwa dinning d'in nan zai yi ba kamar ta d'ora hannu ta fasa 'kara da ihu haka ta ji ido kawai ta zuba masa hucin takaicin sa ya na fitowa daga zuciyar ta, kusan minti biyar Nansy ta fito ta gaisar da su ganin Amirah a dinning ta mugun had'e rai kamar ta je ya yi ma ta magana sai kuma ta fasa ta juya ta koma part d'in su . "Aliyu ba dan ni ba dan girman Allah ka taso ku 'karaso dinning d'in nan ka ga idan ka tafi ba ka ci komai ba ka tuna ba ni ba hatta Mama ba za ta ji dad'i ba kuma ka ga ta yi maka magana kafin ta tashi dan Allah ku 'karaso ka ji"? Amirah ta yi maganar ta na jin kamar ta tashi ta je ta fisgo shi, gani ta yi ya mi'ke ya na tahowa har ba ta san lokacin da ta saki ajiyar zuciya ba wacce shi kan sa ya ji ta zama ya yi Sameer da ya taso daga baya ganin yadda kowanne ya had'e rai a cikin su sai abun ya ba shi dariya kai ya girgiza ya na zama ya kalli Aliyu zai yi masa magana ya nuna ma sa da ido alamar ya yi shiru kar ya ce komai murmushi Sameer ya yi bai fad'i abin da ya ke son fad'a ba, Amirah ta yi serving d'in su duk abubuwan da ta yi ba wanda ta rage sai da ta zuba mu su kafin ta koma ta zauna cikin jin dad'i. Saboda kar ta ce ya wula'kanta ta ya sa ya ci abinci kawai ba wai dan ya na ra'ayi ba ita dai Amirah ta na zaune ta zuba ma sa ido ta na murmushi kamar ta d'auko wayar ta, ta yi ma sa video amma gudun kar ya gan ta a samu matsala ya sa ta ha'kura can kuma ta kalle shi sosai ta na cewa. "Amma dai Aliyu fatan abincin ya ma ka dadi ko"? Bai amsa mata ba Sameer da ya ke lura da yanayin kowanne a cikin su ita ta na cike da farin ciki da shaukin shi kasancewar sa a gidan su kuma a na sa 6angaren ya kame cikin attitude sam ya'ki ba da fuska balle a yi maganar arziki kai Sameer ya jinjina ya na dariya ya ce. "Marshall da kai fa take ka amsa mata shin abincin ya yi maka"? Ganin har lokacin ya yi banza kamar ba da shi ake ba ya sa cikin tsokana Sameer yace "ni bari na wakilce shi tun da naga shi ba zai amsa ba gaskiya abincin ya yi bala'in dad'i sosai yadda ba kya zato dad'in ne ma ya sa Aliyu rud'ewa ki yi hakuri Amirah dad'in abincin ne yasa ki ka ga bai iya yi miki magana ba" murmushi jin dad'i Amirah ta sake yi jin yabon da Sameer d'in ya yi ta, ta kalli Aliyu ta na cewa. "Dan Allah da gaske ka ke Sameer abincin ya yi dad'i sosai ni ce fa na dafa da kai na ba 'yar aiki ba na iya kenan"? Kai Sameer ya jinjina mata shi ma yana murmushin ya ce "ai wannan dalilin shi yasa ki ka ga bai amsa miki ba ya na zilama santi ba zai bar shi ya amsa miki ba" Sai lokacin Aliyu ya d'ago tare da kallon Sameer sakamakon jin abin da ya ce shi kam Sameer dama ya na gama fad'ar haka ya kau da kai ya na dariya dama da niyya ya fad'i haka dan ya ji me Aliyun zaice mata ne ya d'auka zai yi magana sai kawai ya ga ya aje spoon d'in hannun shi tare da mi'kewa ya bar gurin ya nufi hanyar fita daga parlon cikin gaggawa Amirah ta mi'ke a gigice ita ma da sauri ta na cewa. "Aliyu ya haka na ga za ka tafi ko akan abin da Sameer ya fad'a ne? Please ka yi ha'kuri ka dawo ko 'koshi ka yi shi ya sa tashi"? Banza ya yi ta na tsaye ta ga ya bud'e 'kofa ya fita da gudu ta bi bayan sa har harabar gidan inda ya aje motar sa ta na huci da mamaki ta ce "wai me ya faru ne na ga ka tashi tafiya za ku yi"? Kamar kar ya kula ta sai kuma ya ce. "Eh tafiya za mu yi mun gode" shi ne amsar da ya bata ya na bud'e murfin motar tare da shiga ya zauna kallon sa ta yi ta na cewa "to amma Aliyu ai ba ka biya kudin abincin ba za ka tafi". "Me na biya ki dama restaurant na zo ko hotel"? Ya fad'a da mamaki sosai a fuskar sa kai ta girgiza ta na cewa "a'a amma Aliyu............. Katse ta ya yi "amma Aliyu me? Kin ga Amirah ba na son wasa ki rabu da ni kar ki 6ata min rai". "Ba wasa na ke maka ba idan saurayi ya je gurin budurwa ta masa liyafa ko ya ci ko bai ci ba biya ya ke". "Waye zai biya kin? Dama na ce ki dafa min abinci ne bayan ma ko dad'i bai yi ba" had'e rai ta yi jin abin da ya ce wato ma bai yi dad'i ba kai ta jinjina kamar ta ja 'kwafa sai kuma ta fasa ta na cewa "to yanzu ni dai ba wannan ba ka biya kawai kafin ku tafi". "Na biya me kin yi hauka ne"? Amira za ta yi magana Sameer da ya ke tsaye a can gefe ya na dariya 'karasowa ya yi ya na cewa "kai fa malam ba wani hauka da ta yi haka ake yi" ta'be baki Aliyu ya yi ya na cewa. "Haka ake me"?. "Haka ake biyan 'yan mata idan an ci abincin su" Sameer na rufe baki Aliyu ya ce "ba zan biya ba saboda ba ni nasa ta ba ra'ayin ta ne za ka iya shigowa mu wuce idan kuma ba bu'katar hakan na tafi dan na ga kamar dad'in tsayuwa da ita ka ke ji". "A haba kai fa Marshall? Kai ma ka na ji". "Ka ga ni kar ka damu da ni ka ji da kan ka idan kuma ta yi maka ne na saitawa kai na hanya na bar ka tare da ita"? Dariya Sameer ya yi ya na girgiza kai ya ce "a'a ni bance maka haka ba malam daga fad'ar gaskiya kar ka fassara ni" ya fad'a ya na juyawa gurin Amirah wacce ta kafe Aliyu da kallo ya ce "kin ga Amirah ki yi ha'kuri abincin ki ya yi dad'i kuma mun gode nawa ne kud'in da za'a biya ki"?. "Kawai kai dai ka bayar yadda ya kamata ai ba nice zan fad'a ba abin da ku ka ji zuciyar ku ta yanke mu ku shikenan" d'auko kud'i Sameer ya yi wanda ya kasance na Aliyu ne canjin da su ka yo mata shopping ya ba ta kar6a ta yi ta 'kirga ganin dubu goma ya sa ta d'ago ta na cewa. "Wannan ai ko kud'in drinks ba ku biya ba dubu goma kawai me zan yi da ita"? Kallon mamaki Sameer ya yi mata jin abin da ta ce lallai ta d'auko da zafi ya ce "ai ba iya shi kad'ai mu ka zo miki da shi ba" ya fad'a ya na bud'e motar ya d'auko mata shopping din ya na cewa "haka ne kin yi gaskiya Amirah sai dai ba komai ake nema a samu ba kin gane" mi'ko mata ya yi amma kunya ta hana ta kar6a kuma ta kasa cewa komai balle ta yi godiya ganin irin kayan kud'in da su ka jibgo mata ga shi ita kuma ta bada kan ta da'kyar ta ce. "Thanks na gode sosai Aliyu"hannun Aliyu ya na ri'ke da sityarin motar ba 6agaren da su ke ya ke kallo ba ya ce "ba ni za ki godewa ba wanda ya ba ki" ya na fad'in haka ya tada mota shiga Sameer ya yi ya na rufe murfin Aliyu ya ja motar ya nufi 'kofar gate da kallo Amirah ta motar har su ka fita sannan ta d'ebe kayan farin ciki da murna ta shige gida. A hanya bayan sun taho Sameer ya ke cewa "kai amma fa ka iya kafce Marshall" kallon sa Aliyu ya yi cikin alamun tambaya ya ce "wanne irin kafce"?. "Irin wanda kai wa Amirah yanzu". "Haka ne"?. "Eh mana da dukkan alamu Amirah fa ta na son ka matu'ka son da ta ke maka ga shi nan

Chapter 29 of 34