Share this page
nan har zan nemi wata yafiya"? Mi'kewa Sameer ya yi yana cewa "shikenan tun da ba ki ga abun neman yafiyar ba ni dana gani na fad'a miki amma tun da kin ce ke ba ki yi komai ba, ba damuwa" shi ma yana fad'in haka ya fita mi'kewa Hajiya ta yi ita ma zata fita ta kalli Umma ta na cewa. "Hauwa Allah ya rufa miki asiri yau da ace ciki ne da yarinyar nan daga ke har ita yau sai dai ku yi kwanan D'an Yana dan wallahi ba ku isa ta haifa mana shege a gida ba to amma tun da maleriya ce Allah ya kawo sau'ki" ta fad'a ta na shirin fita sai kuma ta juyo ta na kallon kwalin sweet dake can gefen Umma ta ce "Hauwa me ye a cikin nan"? Kallon kwalin Umma ta yi tana cewa.. "Chocolates ne a ciki da biscuits" dawowa ciki Hajiya ta yi tana cewa "chocolates da biscuits mi'ko min bibiyu" bud'ewa Umma ta yi ta d'ebo mata ta d'auko leda ta saka a ciki ta mi'ko mata kar6a Hajiya ta yi tana cewa "saura lemuka da pure water nima yau Allah ya rubuta zan ci arzikin duk da ran ku bai so ba bud'e ki d'ibo min tun da aka kawo mata firizar nan daga ke har ita ba ku ta'ba tunanin d'aukar wani abu ku kai min ba sai yau da rabo ya shigo da ni" Umma ba tayi magana ba duk dan a rabu lafiya nan ma ta sake tashi ta bud'e fridge d'in ta d'ebo mata kai Hajiya ta jinjina ta na cewa. "Ahh lallai kam ta yaya Zainab za ta yi aure bayan ba ta rasa komai ba ga sana'o'i ga kuma wadannan gatan da take samu daga aljanin ta tun da nasan da mutum ne yake bata wadannan abubuwan da yanzu ya bayyana mata kan sa Allah yasa ba ba'kin aljani ne ya aure ta ba kar ya hana ta aure" ta fad'a ta na zaro alawa d'aya ta 6are ta saka a baki ta na cewa "garin dad'i ba kusa ba ana shan irin wannan dad'in a gidan nan amma ban sani ba humm! Na gode ni zan tafi Allah ya sauwake zan dawo anjima na sake duba ki lokacin na shanye alawar sai na 'kara kar6ar wata tun da na gani ai na daina barin ku, ku huta" ita dai Umma tari da bai kamata ba ba ta yi ba har Hajiya ta bar 'kofar ta na fita Asabe ta bankad'o labule ta koma d'akin ta na kallon Umma ta ce. "Na san 'karya Sameer da Abdul-Razza'k su ke yi da suka ce Zainab ba ta da ciki dan su kare ta ne amma ai duk inda cikin gaskiya ya ke baya 6uya mu nan mu na zuba ido duk wani motsin ku muna hankalce da shi duk ranar da na ga Zainab ta fita daga gidan nan ko biyu bana rabawa asibiti ki ka tura ta taje a zubar da cikin humm ga sakamakon kwad'ayi nan kun fara gani in dai nadama ce ba ku fara shiga ba sai nan gaba ma aure dama ba ku so ta yi ba kuma ba za ta ta'ba yi ba" ta na fad'in haka ta juya ta fita kai Umma ta girgiza ta na cewa "bakin ki ya fad'i a 'kasa in sha Allahu Zainab za ta yi aure duk daren dad'ewa" ta fad'a ta na sake jan bargo ta lullu'be ta kafin ta koma ta zauna ta yi shiru ta na kallon ta cike da tausaya mata kullum addu'ar ta Ubangiji ya ba ta miji na gari wanda zai ri'ke ta tamkar 'yar da ya haifa ya nuna mata gata domin wannan damuwar da ta sha ta gushe fatan ta Allah ya sa kafin ta bar gidan nan kar ba'kin ciki ya saka ta kamu da hawan jini. 💓ZUCIYAR ALIYU CE💓 @YUSRAH MUSA PAGE 55 Koda lokacin tafiya islamiyya ya yi ma bata samu lokaci ba sakamakon zazza'bin bai sauka ba waje Umma ta fito mata da shimfid'a ta kwanta a 'kofar d'akin ta tana nan a kwance ganin Bilki ta fito daga d'aki da shirin islamiyya ya sa Zainab tashi zaune tana jingina da jikin bango ta ce. "Bilkisu islamiyya za ki je"? Jin abin da tace ya sa Bilki hararar ta tana cewa "a'a gidan rawa zan je" numfashi Zainab ta sauke sakamakon jin irin amsar da ta bata da har za ta 'kyale sai kuma ta ce "dan Allah idan kin je ki fad'awa Yaa Sayyidi ba ni da lafiya" taki Bilki ta ta'be tana cewa "wallahi ba zan fad'a ba ina ruwa na da wani Yaa Sayyidi" ta fad'a ta na shirin fita da kallo Zainab ta bita tana cewa. "Bilkisu yanzu ba za ki fad'a masa ba ni da lafiya ba"? Kai ta jinjina tana cewa "eh ba zan fad'a ba sai akai ya"? Shiru Zainab ta yi ba ta sake magana ba tsaki Bilki ta ja ta na ficewa tana fita Asabe ta fito daga d'aki ta kai kwanuka gurin wankewa sannan ta juyo tana zuwa kan Zainab ta tsaya tare da kallon ta tace "ke a tunanin ki Bilkisu 'yar aiken ki ce? Tsabar rainin hankali ita ce za ta fad'awa wani Yaa Sayyidi ba ki da lafiya? Ai da tace za ta fad'a masa na fito sai na yi mata dukan ala tsine a gidan nan yadda ba ki d'auke ta 'kanwa a gidan nan ba har abada ba za ta yi miki kallon yaya ba ai ba ita kad'ai ce take zuwa islamiyya a gidan nan ba da za ki ba ta wani banzan sa'kon ki uban wa ya hana ki zuwa ai ba zazza'bin gaskiya ki ke ba wannan zazza6in na ciki ne kuma in sha Allahu sai kin haife shi" ta na fad'in haka ta juya ta bar gurin Zainab kam dama tun da ta fara magana kan ta yake 'kasa har ta gama ta juya kuwa ba ta d'ago ba domin ta tabbata ko Umma da ta na nan ba za ta tankawa Asaben ba balle ita da ta ke matsayin 'yar cikin ta kuma ko ba haka bama yadda Sameer ya ke son ta ya ke kula da ita bai kamata ace ta na yiwa Asabe rashin kunya ba duk ranar daya shigo ya tarar da hakan ba zai dad'i ba wannan dalilin ya sa ko Asabe za ta rufe ta da duka ba za tace ma ta komai ba.................. Kiran wayar ta da akai ta mayar da hankalin ta gurin Sameer ne d'agawa ta yi tana cewa "assalamu-alaikum Yaya Sameer ina yini"? Jin ta ambaci Sameer ya sa Asabe daina wanke-wanken da ta ke ta tsaya tare da juyowa ta na kallon ta, ta ji me za tace Zainab kam hankalin ta ba'a kan Asaben ya ke ba balle ta san me ya ke faruwa kawai da Sameer ya ce mata ya jiki ta ce. "Da sau'ki". "Zazza'bin ya sauka ko har yanzu da saura"?. "A'a ya sauka ba zafin jikin sai juwa da na ke ji idan na mi'ke tsaye". "Ba ki ci abinci bane"?. "Eh". "Me ya sa to ba'a yi bane"?. "An yi shinkafa ce da wake salad ne babu shi ya sa ban ci ba" jin abin da ta ce ya sa yace "ok ina zuwa" ya na fad'in haka ya katse aje wayar Zainab ta yi Asabe da ta gama wanke kwanukan ta na shirin barin gurin ta ce "to munafika gadon 'karya da sharri inji uban waye ya ce ba'a siyo salad ba har ki ka fad'a masa kodan dama 'karya abincin ki ce" shiru Zainab ta yi ba tai magana ba Asabe data shiga kitchen ta d'auko salad a leda ta wurgo mata ta na cewa "kin ce masa ba salad saboda ga gidan fatararru yanzu wannan uban meye a ledar inace uwar ki ce ta yi abinci da shi jiya tsabar ba'kin hali ta'ki yanka shi yadda zai isa ta 6oye kuma gashi asirin ta ya tonu har salad d'in ya fara zama yellow ba ta d'auke ba" tafa hannu Asabe ta yi tana cewa "kai jama'a gaskiya akwai azzalumai a gidan nan ni dai ana zalunta ta ba abin da zan ce sai Allah ya saka min daga ke har uwar taki idan an gan ku shiru-shiru ba'a san lunbu-lunbu ne ba uwar 'kai'kayi sai mutum ya zauna da ku zai ga sharruka iri-iri gashi a haka gani ake kamar ni ce na ke cutar ku saboda ni ina da baki hummm kowanne shege haka nan zai gan ni ya, barni dan na zama ciwon ido zama da ni sai ha'kuri" ta fad'a tana komawa cikin kitchen d'in ita dai Zainab har lokacin ko tari ba ta yi ba sai dai ta ji mamakin ya akai da salad d'in amma ba'a yanka ba ai duk zaton ta babu shi ya sa ta'ki cin abincin da ta san da akwai koda kan ta za ta iya yankawa tun da Umman ba ta nan sallama Sameer ya yi yana shigowa ya zo ya aje leda a kusa da ita sannan ya shiga kitchen Asabe ta na tsaye ya gaida ita ba ta amsa ba sai tambaya da ta jefo masa ganin ya d'auki plate da wu'ka da cokali tace. "Kai uban me za ka yi da su"?. "Zan yankawa Zainab salad ne ta ci abinci". "Humm dama na san sai dai Zainab d'in da nice nake jinyar nan Sameer ko kallo na ba za ka yi ba amma da ya ke Zainab 'kanwar uwar ka ce daga tace maka ba za ta ci abinci idan ba salad ba shine har ka rarumo ru'kui-ru'kui jiki na rawa ta kawo mata kuma hakan bai isa ba saboda ta mayar da kai bawan ta sai ka yanka mata" kallon ta Sameer ya yi yana cewa. "Umma wannan fa duk ba abun fad'a ba ne dan na kyautatawa 'yar uwa ta". "Sannu me 'yar uwa sakaran banza da an yi magana ka ce 'yar uwar ka zan ga tsiyar da za ta tsinana maka nan gaba da ka nace sai ita aikin banza kawai" juyawa ta yi ta bar gurin Sameer dai bai sake magana ba ya yanka mata salad d'in ya d'ebo gishiri kad'an ya wanke mata ya yanka mata cocumber tumatur da albasa ya aje mata ledar da ya shigo da ita ya bud'e ya d'auko wani 'katon kifi a ciki ya 6are shi ya fitar mata da 'kayar sannan ya zuba mata abincin ya shiga d'akin ta ya d'auko mata pure water a fridge ya kawo mata tare da zama a gefen shimfid'ar ya na cewa. "Ki ci man ki ka tsaya ki na kallon abincin"? Kai ta d'an girgiza ta na cewa "ba zan iya ci ba" da mamaki Sameer ya ce "ba za ki iya ce ba kuma"? Nan ma kai ta sake d'agawa ta na d'an zamewa daga zaunen da take zata kwanta ganin haka ya sa Sameer cewa. "A'a la'asar ta yi koma ki zauna kar ki kwanta rana ta yi 'kasa" d'agowa ta yi ta dawo zaune yadda ta ke duk da ta na son kwanciyar abincin Sameer ya gauraya mata cikin kulawa da lallami na mara lafiya ya soma ba ta ya na cewa "kin ga ki d'an kar6a ki ci ko loma d'aya ce" idan yaga ta kar6a sai ya sake d'ebowa ya ce "yauwa 'kara d'aya" da haka kamar da wasa har ta ci da yawa ya bata pure water ta sha murmushi ya yi yana kallon ta ya ce. "Yauwa to alhamdulillah" mi'kewa ya yi ya na cewa "idan an jima ki d'auki d'ayan kifin da ya ke ledar ki cinye shi kafin na shigo bari na koma na baro chemist d'in a bud'e" kai ta d'aga a hankali ta ce "na gode Yaya Sameer Allah ya saka da mafificin alkhairi" "Amin ya ce ya na fita daga 'kofar ta su Asabe da ta yi shiru ta na kallon su ganin ya fita ya sa ta taso da gudu ta na zuwa ta yi wuff kamar shaho ta d'auke ledar kifin ta na hararar Zainab ta ce. "Mayya ba ni wato bayan wanda ki ka ci harda saura ya rage miki zuwa jimawa ki ci, humm ni dai wannan abu ya na ba'kanta min zuciya amma ba komai in dai asiri ku kai masa zan je awarware daga ranar asirin munafiki zai tonu" ta na fad'in haka ta juya ta bar gurin ta shige d'akin ta numfashi Zainab ta sau'ke tare da rufe ido kawai ta yi shiru kamar me barci............................... ZUCIYAR ALIYU CE @YUSRAH MUSA PAGE 56 Ganin da Afifah ta yi Zainab ba ta je islamiyya ba har aka tashi shi ya sa da taga tawagar su Bilki za su tafi gida ta tare su ta na cewa "am dan Allah yau ya akai Zainab ba ta zo islamiyya ba"? Dukkan su Bilki su ke kallo ganin ta'ki magana ya sa Rasheedat cewa "sai dai ki tambayi Bilki ita ce 'kofar su d'aya" jin abin da Rasheedat ta ce ya sa Bilki zafga mata harara ta na cewa "ni ma ban san dalilin ta na 'kin zuwan ba". "Ok ba ta gidan ne ko ta yi tafiya"? Afifah ta sake tambaya kai Zakiyyah ta girgiza ta na cewa "in dai ba d'azu ta tafi ba gaskiya Zainab ta na nan da yake bata da lafiya tun safe ta ke amai ina ga shi yasa ba ta zo ba" d'an zaro ido Afifah ta yi ta na cewa "Subanallahi wayyo Aunty Zee-Zee dama ba ta da lafiya? Allah sarki Zainab d'ina shi ya sa na yita kiran ta a waya na ji a rufe ashe ita ta kan ta, ta ke yi bari na wuce na dubo ta" jin abin da Afifan ta ce ya sa suka fara kallon kallo tsakanin su na ta6e baki Bilki kuwa ji ta yi kamar ta d'auke Afifah da mari tsabar takaicin yadda ta damu da Zainab d'in, tare su ka shiga gidan Bilki da Afifah su ka wuce can 'kofar har lokacin Zainab ta na waje ba ta koma d'aki ba Abba ya na kusa da ita ya na mata sannu dawowar sa kenan daga gurin sana'ar sa ko d'aki bai shiga ba ganin ta yi ba'kuwa ya sa ya mi'ke dur'kusawa Afifah ta yi ta gaida shi ya amsa ya na nufar 'kofar d'akin sa zama Afifah ta yi tana kallon ta ta ce. "Sannu Aunty Zeey ya jikin na ki"? D'aga kai Zainab ta yi ta na cewa "da sau'ki Afifah", "Allah ya 'kara lafiya ashe tun safe ba ki da lafiya ban sani sai yanzu da mu ka taho na ke tambayar 'yan gidan nan suka ce min tun safe ki na kwance har da amai ki ke". "Uhm zazza'bi ne". "Yaya Sameer ya duba ki"?"eh tun safen ya duba ni na samu sau'ki ba kamar d'azu da ko zama gagara ta ya yi ba" zaro ido waje Afifah tai ta na cewa "zama ya gagare ki? Caf Allah ya rufa asiri Allah ya kawo sauki". "Amin" Umma ce ta fito daga d'aki ta na cewa "Afifah ashe ke ce ki ka zo"?. "Ni ce Umma ina yini"? "Lafiya kalau ya mutan gidan na ku"?. "Lafiya kalau su ke ya me jikin"?. "Ga ta nan da sauki". "Allah ya 'kara sau'ki" "Amin an gode sosai Allah ya yi albarka" Umma ta fad'a ta na wucewa ta d'auki buta za ta yi alwalar sallar magriba kallon Zainab Afifah tai ta na mi'kewa ta ce "Aunty Zee bari na tafi kin ji an fara kiran sallah" kai Zainab ta d'aga ta na cewa "to Afifah na gode ki gaida Momy"?. "To in sha Allahu za ta ji sai da safe" ta fad'a ta na fita bayan Umma ta yi alwalar dawowa gurin ta ta yi tana cewa "zaki iya tashi ki yi alwalar ne"? "Eh zan iya" ta fad'a ta na tashi tsaye duk da har lokacin ba ta jin 'karfin jikin ta ko kad'an shimfid'ar Umma ta d'auke ta mayar mata d'aki sannan ta fito ta shiga na ta ita kuma Zainab ta yo alwalar ta zo ta shiga za ta yi sallar. Afifah ta na komawa gida ta tarar da Momy a parlor ta na zaman jiran dawowar ta ganin ta shigo ya sa Momy kallon ta tana cewa "Afifah a ina ki ka tsaye ne sai yanzu ki ka shigo gida har an fito daga masallaci bayan ba ki saba yin hakan ba"? Kai Afifah ta d'aga ta na cewa "tun lokacin da aka taso na taho Momy na wuce gidan su Zainab na dubo ta ne". "Ba ta da lafiya"?. "Eh ashe tun safe ta ke zazza'bin ni ban sani ba da yake na kira wayar ta a kashe na d'auka ba ta da caji ne ashe ba ta jin dad'i ma ita". "Ayya Allah ya sauwake idan na samu lokaci ko gobe ne zan je har gida na duba ta Allah ba ta lafiya". "Amin" Afifah ta ce tana wucewa part d'in su Momy ma tashi ta yi ta koma na ta dama dalilin fitowar da ta yi rashin ganin shigowar Afifan a lokacin da ta saba ne amma tun da ta dawo kuma ta ji inda ta je ba matsala. Da yake tun da daren da Zainab su kai waya da Aunty Murjah ta fad'a mata ba ta da lafiya shi ya sa washe gari da safe wajen 'karfe goma da rabi na safe ta sake kiran ta, ta duba ta sannan ta ce mata da dare za su shigo tare da Auwal su sake duba ta Afifah ma ta sake shigowa da safen kafin ta tafi school ta duba ta harda Fati da Elham su ka zo da kayan dubiya. Sakamakon shi ma Yaa Sayyidi bai san ba ta da lafiyar ba a jiyan ya ga yau ma still ba ta le'ko islamiyyar ba shi ya sa ya tambayi Afifah ko lafiya ta fad'a masa ai ba ta jin dad'i ne tun daren shekaran jiya sosai ya yi kewar rashin zuwan ta musamman ajin da ta ke d'auka dole jiya da yau duk shi ya ke shiga mu su.............. ZUCIYAR ALIYU CE STORY WRITTEN ND EDITING YUSRAH MUSA ABUBAKAR✨ @YUSRAH YMA DUTSE PAGE 57 POV. YAA SAYYIDI Da ya koma gida bayan sallar magriba ya shigo anguwar ta su amma a d'an nesa da gidan ya tsaya saboda haske kiran ta ya yi a waya ta fito ya duba ta ba ta ta'ba tunanin zai zo har gida ba ta d'auka tun da ya kira ta d'azu shikenan idan gobe ta koma islamiyyar ya duba ta. A lokacin ta na kan sallaya ta yi sallah kenan ya yi kiran ta, tashi ta yi ta d'auki Nikaf ta d'aura ta shiga d'akin Umma ta sanar mata sannan ta fita had'uwa su kai da Sameer da mamaki ya kalle ta ya na cewa "Zainab ina zuwa haka ke da ba ki da lafiya"? Numfashi ta sauke a hankali ta ce "Yaa Sayyidi ne ya kira ni a waya ya ce na fito ya na waje ya zo duba ni" jin abin da ta ce ya sa Sameer ya kalle ta da sauri cike da mamaki ya ce. "Wai Yaa Sayyidin dama har yanzu bai daina zuwa gurin ki ba"? Kai ta d'aga ta na cewa "eh ya na zuwa amma ba koda yaushe ba sai lokaci zuwa lokaci" 'kak'karfan numfashi Sameer ya sauke ya na kallon ta ya ce "tabd'ijan amma akwai............... Koda shikenan je ki kawai idan kin dawo gida sai mu yi maganar kar na tsayar da ke shi kuma ya na jiran ki ba damuwa je ki kawai" ya fad'a ya na wucewa shiru Zainab ta yi a ran ta, ta na cewa "tabbas akwai abin da Yaya Sameer ya hango min wanda ni ban gano ba amma bari idan na dawo zan tambaye shi" bud'e 'kofa ta yi ta fita a inda ya saba tsayawa idan ya zo anan ta same shi yasha wankan jallabiyya shi yasa mutumin nan ya ke burge ta kuma ta ke jin cewa za ta iya auren sa ko mata uku ne da shi ta shiga gidan matsayin ta hud'u ta amince sallama ta yi su ka gaisa ya kalle ta shi ma cike da burgewa ko'ina a rufe ya ce. "Fatan kin samu sau'ki ko ashe ba ki ji dad'i ba"?. "Wallahi ban ji dad'i ba jiya a kwance na wuni shi ya sa ban samu na shigo islamiyya ba yau ma kuma na tashi babu 'karfin jiki shi ya sa ban zo ba na bari sai gobe". "To Allah ya kai mu ai haka Afifah Ahmad ta ke fad'a min yau da na tambaye ta ki na ina na san dama ba za ki ta'ba yin tafiya ba ki fad'a min ba". "Ba tafiya na yi ba zazza'bi ne ya same ni". "Shikenan ba damuwa Allah ya 'kara lafiya dama kawai cewa na yi bari na shigo na duba ki daga nan sai na je gurin wani malami da ya ke bayan layin ku mu gaisa da shi ga wannan" ya 'karasa maganar ya na d'auko ba'kar ledar da ke gefen sa ya mi'ko mata kai ta girgiza ta na cewa "lah a'a ka barshi ba komai iya duba ni da ka zo ka yi ma na ji dad'i sosai". "A'a ki kar'ba ai niyya na yi ba saka ni ki kai ba sannan kin san ba kyau mai da hannun kyauta baya ko"? Shiru ta yi ya ci gaba "dan Allah Zainab ki kar'ba na tafi" ya fad'a ya na sake mi'ko mata da'kyar ta saka hannu ta d'an risina ta kar6a ba don ran ta ya so ba sai dai dan kawai ba ta son musu. "Na gode sosai Yaa Sayyidi Allah ya saka da alkhairi". "Amin ba damuwa sai da safe na tafi" ya na fad'in haka ya juya ya tafi ita kuma ta shiga gida ba ta samu Sameer ba domin har ya gama abin da zai yi a lokacin ya fita d'aki ta koma ta jira sallar isha lokacin ta ya 'karaso ta yi sannan ta d'an kwanta kafin su Aunty Murjah su zo kwanciyar ta ke da wuya barci ya fara d'aukar ta, ta ji sallamar su tashi zaune ta yi ta na kallon kofar shigowa d'akin ta gani ta yi an bud'o labule Ikram ta shigo da murnar ta, ta zo ta zauna a kusa da ita ta na cewa. "Aunty Zainab ina wuni"? Murmushi Zainab ta yi tana d'aukar ta, ta d'ora ta akan cinya ta ce "lafiya kalau Ikiki na ina ki ka bar Daddyn ki"? D'aga yatsa ta yi ta na cewa "a can"?. "A can gida ku ka baro shi"? Ikram na wasa da kayan 'kyallayen d'inki ta ce "eh Aunty Zainab za ki d'inkawa baby na kayan ta"?. "Aw Baby ce da ke"?. "Eh Daddy ne ya siyo min". "Lallai Daddyn nan na ki ya na son ki to ina Momyn na ki"?. "Ta na d'akin Umman ta" d'an zaro ido Zainab ta yi tana kallon ta tace "ke ba Umman ki ba ce"? "Eh ni Momy ce Momy na" kai Zainab ta jinjina ta na d'auko biscuit mi'ka mata daidai Aunty Murjah ta shigo da sallama ganin ta a zaune yasa ta ce "ahh masha Allah ashe kin samu lafiya"? Ta fad'a ta na zama kusa da ita ta ce "sannu ya jikin"? Murmushi Zainab ta yi tana kallon ta tace. "Da sauki ina yini"?. "Lafiya kalau ya 'karfin jikin"?. "Na samu lafiya wai ku kad'ai ku ka zo ban da Abban Ikram"? Kai Aunty Murjah ta girgiza ta na cewa "tare mu ka zo man" "Kai amma Ikki ta ce min iya ku ne"?. "A'a ba mu kad'ai ba ne ya na gurin Abban mu" mi'kewa Zainab ta yi tana d'aukar mayafi ta ce "bari na je mu gaisa da shi" tashi Aunty Murjah ta yi tana cewa "mu je ina son za mu gaisa da Hajiya" kallon ta Zainab ta yi kamar za ta yi magana sai kuma ta fasa su ka fita ganin takalman Auwal a 'kofar d'akin Abban su ya sa ta fahimci har lokacin ya na d'akin waje su ka nufa Aunty Murjah ta shiga 'kofar Hajiya ita kuma ta tsaya tare da Ikram har

Chapter 23 of 34