Share this page
Tuna abin da ya faru a cikin mafarkin ya sa wasu zafafan hawaye su ka fara zuba mata ji ta ke dama da ta yi sallar asuba ba ta koma barcin nan ba da ace irin wannan mafarkin za ta yi gara ta ha'kura da kwanciyar. °°°•••°°°•••°°° Fitowar Fati kenan daga part d'in su ta na hamma za ta nufi dinning ta tsaya cak ta 'kame guri d'aya ganin wanda ya ke zaune a dinning d'in tare da Momy rufe baki ta yi ta na zaro ido a hankali ta juya cikin sand'a ta koma bedroom d'in su da gudu ta na shiga ta fara 'kwalla kira. "Aunty Afifah kin tashi ne ko har yanzu barcin ki ke na zo miki da albishirir"? Afifah da ke kwance jin yadda Fatin ta ke 'kwalla mata kira kamar ba lafiya ba ya sa ta ce "ga ni fa ya akai? na tashi man" kai Fati ta jinjina ta na waiwayen bayan ta kamar shi ne ya biyo ta ta ce. "Aunty Afifah kin kuwa san Yaya boss ya dawo" tashi daga kwancen Afifah ta yi ta na zaro ido ta ce "wanne Yaya boss d'in amma dai yanzu ya dawo ko"?. "A'a ina yanzu ai ina ganin a gida ya kwana". "Ganin sa ki kai da idon ki"?. "K'warai a parlor ba ya na zaune a kusa da Momy a dinning su na breakfast yanzun nan ban 'karasa ba na dawo na fara miki ki fita da shirin ki" dafe goshi Afifah ta yi ta na cewa "Subanallahi ji Yaya discipline da wani tsari shi d'in meya dawo da shi"?. "Ta ya za mu sani maybe hutu ya sake zuwa bari na koma domin breakfast zan yi yau da yunwa na tashi jiya na kwanta ban ci abinci ba" ta fad'a ta na 'ko'karin fita sai kuma ta sake juyowa ta na cewa "please Aunty Afifah ki wanke fuskar ki sosai kar ya gane barcin safe ki ka koma tun da kin san ya hana" mi'kewa Afifah ta yi ta na cewa "tabbas na sani ga Yaya discipline akwai saurin gane yanayin mutum bari kawai ko zuwa jimawa na fita sannan idon na wa ya gama wartsakewa". "Ok" Fati ta ce ta na bud'e 'kofa ta fita tare da le'kawa ta ga iya Momy ce a parlon sai Elham sauke ajiyar zuciya ta yi ta na cewa "yauwa masha Allah haka na ke so" 'karasa fitowa ta yi tana gaida Momy sannan ta wuce dinning Elham da ta bi ta da kallo ta ce. "Ke Teemoh kin san Yaya boss ya dawo kuwa" kai Fati ta jinjina ta na zama ta ce "ni kuwa na san ya dawo tun da na gan shi da ido na". "Au kin gan shi kenan"?. "Na gan shi man tun d'azu ina fitowa fa na gan su tare da Momy a dinning shi ne na juya na je na fad'awa Aunty Afifah" dariya Elham ta yi ta na cewa"au ta sani kenan ai da kin 'kyale ta kamar yadda kowa ya fito ya gan shi ita ma ta fito su had'u". "A'a ba zan iya yi wa Aunty Afifah haka ba da amana me 'karfi tsakanin mu kuma nasan ita ma da ita ce ya dawo ban sani ba za ta fad'a min". "Da gaske? Sannu radio me jini". "Ba wani maganar radio me jini wannan taimakon kai da kai ne". "Uhmm na ji wannan saura wanne"? Tun kafin Fati ta yi magana Momy ta ce "gara ki tsaya ki nutsu ki yi breakfast me kyau da ki ka zauna ki na biye Elham ita ta yi na ta ke kuma ta dame ki da tambaya ki na bata amsa abincin ko dad'in sa ba za ki ji ba" kallon Elham Fati ta yi taga ta na masa dariya harara ta saka mata ta na cewa. "Zan rama ko ba yau ba" gwalo Elham ta yi mata ta na cewa "ai kuwa ba ki isa ki rama ba sai dai ki rame ki 'kai'kashe". "Tom shikenan za ki gani" ta fad'a ta na mayar da hankalin ta, ta share Elham d'in kamar yadda Momy ta ce su na zaune Afifah ta fito ita ma ta na le'ke-le'ke kallon ta Momy ta yi ta na cewa "lafiya"? Kai ta girgiza ta na cewa "ina ya ke"?. "Wa ye"?. "Yaya discipline". "Ok ko saboda shi ki ka fito ki na wannan le'ken"?. "Dole na le'ka Momy kar na je ya na kusa". "A'a shi kam ba ya nan ya fita tun d'azu" ajiyar zuciya Afifah ta sau'ke ta na cewa "yauwa har na ji dad'i haka na ke son ji bari mu zo mu bararraje mu ci abin da ran mu ke so cikin kwanciyar hankali". "Idan ya na nan ma ba zai hana ki yi abun da ki ke so d'in ba". "Eh amma ba kamar yadda mu ke free haka ba Allah ya sa wannan karon ma Afif ya dawo ni sai na huta" kai Fati ta girgiza ta na cewa "a'a ba Amin ba wallahi haba Aunty Afifah ya dawo ki samu hutu mu kuma mu shiga rud'u mutum biyu sun had'e ma na lokaci guda ko"? Murmushi Afifah ta yi ta na cewa. "Eh man 'yar gari ashe kin gane indai ni zan huta komai normal ne" numfashi Fati ta sauke ta na cewa "a gurin ki ba amma mu kuma fa mu yi yaya kenan"?. "Oho ku, ku ka sani wannan matsalar ku ce in kun ga dama ku bar gidan ko ku yi zaman ha'kuri da su". "Ahhh lallai kam to ai tun da haka ne sai mu kama kan mu kafin Yaya ki sa Yaya Afif d'in ya dawo" Fati ta fad'a tana mi'kewa ta bar gurin dinning d'in ta tafi cikin parlor inda su Momy su ke ta na jin Afifah ta na mata dariya ta 'kyale ba ta sake bi ta kan ta ba. Zainab kuwa tun da ta gama kukan mafarkin da ta yi ta mi'ke ta fito waje ta d'an taya Umma ayyuka da su ka gama ta koma ta gyara d'akin na ta, ta saka turaren wuta ta saki labulen window da na 'kofa wata 'katuwar tabarmar Umma ta d'auko ta shimfid'a a waje ta fito da keken d'inkin ta aje saboda haka kawai yau ta ji ta na son zaman waje ta yi d'inki duk da akwai sanyi bayan sun karya ta had'a kwanukan ta wanke ta kai kitchen wankan safe ta yi harda 'yar kwalliyar ta lipstick da powder ta saka kwalli sannan ta saka doguwar riga fara tas ta yi rolling da mayafin rigar shi ma fari akwai adon golden a jikin sa kamar yadda ita ma rigar akwai stone a jere ta gaban rigar fitowa ta yi bayan ta gama shiryarwa ta hau keke ta fara d'inki. Bilki da ta fito daga d'aki da jaka a hannun ta zata bi Asabe gidan su tun da ta tafi biki ba ta dawo ba shi ya sa yau ta shirya idan ta je sai su taho tare ganin yadda Zainab ta d'au wanka ya sa ta ta'be baki sai da ta zo saitin ta sannan ta tsaya ta na mata kallon uku saura kwata ta ce "hum'um an ji kunya dai wallahi anyi asara duk wannan kyawun a banza sai dai aci kwalliya ba gurin zuwa kuma ba wanda zai gani ya yaba balle ya ji kin burge shi kodan dama wa za ki burge sai dai ki burge keken na ki idan kuma neman saurayi ki ke ai ba wanka za ki yi ki zo ki hau kan keke ba gari zaki mi'ke ki shiga watakil idan kin dace ko d'an bola ki samu ya aure ki" jin abun da Bilki ta ce ya sa Zainab d'agowa ta na kallon ta tace "ke Bilkisu ki kama kan ki ban damu da ke ba kar ki kuskura tsautsayi yasa ki sake fad'a min irin wannan maganar wallahi kin ji na rantse sai na miki mugun duka a gidan nan" dariya Bilki ta yi ta na cewa. "To fa sannun ki da 'ko'kari wa za ki wa mugun dukan amma dai ba da ni ki ke ba domin ni dai ba zan 'kyale ki ba sai dai mu daku tare amma ke dai ba zan ta'ba tsayawa ki iya duka na ba" kai Zainab ta jinjina ta na mayar da hankalin ta kan aikin ta ta na cewa "tun da ki na ganin ba zan iya d'in ba ki ci gaba idan kin isa ki sake fad'a min wata banzar magana anan wajen ki ga yadda zan yi da ke" nuna kan ta Bilki ta yi ta na cewa "ba yadda za ki dani nan gani nan bari ni Bilkisu na fi 'karfin ki fad'a da ni sai kin shirya domin yanzu na yi miki nisan da ko kin hau tsani ba za ki taro ni ba 'karshen wasan ba zai wuce ki had'a ni da Yaya Sameer ya dake ba to bari ki ji 'karyar ki tasha 'karya mai duka na a yanzu sai ruwan sama amma ba dai wani d'a ba". "Ya yi kyau tun da har kin yarda da kan ki ba me iya dukan ki sai ruwan sama dan Allah ki sake fad'a min irin maganar da ki ka fad'a min lokacin da ki ka tsaya anan ni kuma yau sai na targad'a ki a gidan nan" bud'e baki Bilki ta yi za ta yi magana Sameer ya shigo da sauri ta ja bakin ta tayi shiru tare da barin gurin kallon ta ya yi yana cewa "ke ina za ki je na gan ki da jaka"? Jin tambayar da ya yi mata ya sa ta fara sosa jiki ta na cewa. "Uhmm uhmm". "Ke ina wasa da ke ba tambayar ki na ke ba gidan uwar wa za ki je yanzu har da d'iban kayan a jaka"? Ja da baya Bilki ta yi tana cewa "gurin Umma zan je sai mu taho tare" hararar ta ya yi ya na cewa "kin san inda za ki je d'in amma tsabar raini na tambaye ki kika kasa ba ni amsa ki fad'a min gaskiya kafin ki ji duka". "Wallahi Yaya Sameer can zan je". "Ok kuma tsaiwar me ki ke d'azun dana shigo na gan ki a gaban Zainab"? Zaro ido Bilki ta yi tana fatan Allah ya sa bai ji komai ba ta ce "uhmm gaishe da ita na yi kuma shi ne na ke tambayar ta ina da atamfar da zan bata ta d'inka min idan zan samu da wuri"? Ta fad'a tare da d'agowa ta kallo Zainab wacce ita ma da saurin ta d'ago ta na kallon ta jin ba'kar 'karyar da ta sharara wai gaida ita za ta yi kai wannan yarinyar akwai sharri buhu-buhu kai ta girgiza ta na ci gaba da d'inkin ta ba ta bi takan maganar da Bilkin ta yi ba ji ta yi Sameer ya ce. "Munafika ke d'in ce zaki gaisar da Zainab 'karya ki ke yi" "Da gaske na ke kuma ka tambaya ta za ta fad'a maka" kallon Zainab wacce gabadaya hankalin ta ya na kan d'inki ya yi yana cewa "wai haka ne abin da ta ce"? Murmushi Zainab ta yi ta na jinjina kai ta ce "ni ba zan ce komai ba". "Humm dama na san za'ai haka" juyawa ya yi ya koma waje Bilki ta bud'e baki za ta yi magana ta gan shi wuff ya sake shigowa ya wuce d'akin sa d'an 'kasa ta yi da murya ta na kallon Zainab ta ce "wai dama za ki iya rufa min asiri ko da ace na yi miki 'karya"? Kallon Zainab ta yi jin tambayar da ta yi kamar ta share ta sai kuma ta ce. "Me ye riba ta idan na tona miki asiri ya dake ki ko kuma ya yi miki wani abu ta sila ta ni bana irin wannan sharrin a rai na kin gane"? Kai Bilki ta jinjina ta na ta'be baki ta ce "ya yi kyau masu kyakkyawar zuciya ni kam da ni ce wallahi ba ki isa na rufa miki asiri ba" murmushi Zainab ta yi ta na cewa "ai ni dake ba d'aya bane je ki da halin ki" tsaki Bilki ta ja mai 'karfi har Sameer ya jiyo daga d'akin sa ya ce "waye wannan ya kewa mutane tsaki"? Tabd'i da gudu Bilki ta fita daga 'kofar wanda ya sa Zainab ta yi dariya wato yarinyar nan 'yar rainin hankali ce ga fatsara da rashin kunya ga kuma uban tsoro. Fitowa Sameer ya yi ya na saka takalman sa ganin Bilkin ta fice kuma ya san ita ce ta yi tsakin, humm za ta dawo gidan ta same shi ai ba tabbata za ta yi acan d'in ba idan ta je kallon Zainab ya yi yana shirin fita ya ce "wai yau ko anguwa za ki je"?. "A'a ba inda zan je lecture ne kuma sai 'karfe d'aya da rabi zan tafi" "Ok ai da naga kin ci kwalliya ne haka shi ya sa na yi tunanin ko akwai inda zaki je d'in"?. "A'a d'inki kawai zan yi". "Ya yi kyau bari na koma chemist ban rufe ba kuma na baro shi ba kowa". "To Yaya Sameer Allah ya taimaka" "Amin" ya fad'a ya na fita Umma kam ta na can nesa da su ta na aiki ba ta san me ya ke faruwa ba tasowa ta yi daga gurin ta dawo wajen 'kofar d'akin ta, ta zauna za ta yanka albasa d'an kallon ta Zainab ta yi ta na cewa "wai Umma yanzun har abincin rana za ki d'ora"? Kai ta d'aga tana cewa. "Eh man gara na gama da wuri ai na huta kuma kin manta Hajiya idan ka kai mata abinci a makare sai ta yi maka tas kamar za ta dake ka sannan ta kar'ba idan ma za ta ci kenan" "hummm Allah ya rufa asiri" kawai shi ne abin da Zainab ta ce ba ta sake magana ba. Fitar Sameer kam ya na komawa chemist ya ga Aliyu a ciki ya na zaman jiran sa shiga ya yi shi ma ya na zama akan kujera ya ce "barka da dawowa Marshall ashe har ka fito tun wuri haka na d'auka yau wuni za ka yi a gida ka na hutun gajiya sai kuma na ga ka fito"? Kai Aliyu ya d'aga ya na cewa"ta ya zan iya wuni a gida ba tare da na fito na ga zuciya ta ba yanzu haka ba abin da na ke muradi kamar na gan ta fatan ta na nan ba ta je ko'ina ba"?. "Eh ta na nan ba inda ta je dama D'an Yana ne gurin zuwan na ta kuma ka ga ba'ai hutu ba balle ace ta samu d'an lokacin da za ta je d'in" ajiyar zuciya Aliyu ya sauke ya na mi'kewa ya ce "mu je" da alamar tambaya Sameer ya ce "ina mu je"? Kai tsaya ya ce "gidan ku"? Zaro ido Sameer ya yi yana cewa "kai Marshall da gaske sai ka iya shiga". "K'warai ba abin da zai hana tun da ba sani akai ina son ta ba gaba ne dai zan daina shiga" jinjina kai Sameer ya yi yana mi'kewa ya ce "shikenan mu je" fita su kai daga chemist Sameer ya rufe sannan su ka tafi kamar yadda ya saba in dai ya shiga gidan 'kofar Hajiya su ke fara shiga ai kuwa ta na ganin su ta zaro ido ta na bin Aliyu da kallo ta ce. "Ikon Allah wa na ke gani kamar Aliyu" zama su kai ya gaisa da ita sannan ya ce "eh Hajiya ni ne" ri'ke baki ta yi ta na cewa "ohh Allah mai iko dama ka dawo ne d'an nan ya fama da 'ko'kari"?. "Alhamdulillah Hajiya na same ku lafiya"?. "Lafiya 'kalau Aliyu Allah ya yi maka albarka tun da har ba ka ta'ba mantawa da ni duk lokacin da ka dawo sai kazo ka gaisar da ni". "Ba komai Hajiya ai ke kaka ta ce" kai Hajiya ta jinjina cikin jin dad'i ta ce "kwarai kuwa ni matsayin kaka na ke a wajen ku" kallon Sameer ta yi ta na cewa "kai Samar ba dan darajar Aliyu ba yau ka shigo min yaushe rabon da na gan ka tun ranar da mu kai maganar akan video da ka kawowa Zainab" juyawa 6angaren Aliyu ta yi ta na cewa "ka gan shi nan Ali sai mu kwana gida d'aya mu tashi yaron nan Samar bai le'ko ya ga lafiya ta ba ko tunani ya ke zan ro'ke shi ya bani wani abu ne oho masa". "Kin gani ko Hajiya ai ke matsala ta da ke zargi ni da yaushe na fad'a miki haka maganar ba na shigowa gurin ki wannan gaskiya ne sai lokaci zuwa lokaci amma ai na san ki na lafiya tun da da ace ki na ciwo zan ji labari a gurin 'yan gidan ko". "Ai ka ji shi ko Ali nema min jinya ya ke saboda ba ya so ya shigo ya gan ni cikin walwala gaskiya Samar ka nuna min matsayi na yanzu dole na san irin zaman da na ke da kai". "Wanne irin zama ki ke yi da ni"?. "Ka fi ni sani ai ba sai na fad'a maka ba". "Ok shikenan Aliyu tashi mu tafi Hajiya idan za ka kai dare anan ba za ta daina maka zance ba yadda ka gan ta nan ba ta rasa abun fad'a duk rintsi". Mi'kewa Aliyu ya yi kamar yadda ya saba ya aje mata kud'i su ka fita daga gurin ta sai albarka ta ke yi mai shi ya sa take son zuwan Aliyu ba ya ta'ba fita sai ya aje mata abun arziki. Fitar su daga gurin Hajiya kai tsaye 'kofar su Sameer ya nufa har lokacin Zainab ta na yadda take ta na d'inki........ "Assalamu-alaikum" da sauri ta dago jin muryar namiji ba zato ta na d'agowa idon ta ya sauka akan fuskar Aliyu su ka had'a ido ya d'au wanka da wani irin mugun sauri ta sauke kan ta 'kasa jikin ta ya d'au rawa haka kawai mafarkin da ta yi d'azu ya fad'o mata gani take kamar da gaske ne musamman da ta gan shi sai ta ke ganin kamar shi ma ya yi mafarkin irin na ta shigowa su kai Sameer ya na cewa. "Ina Umma ta ke"? Ya tambaye ta ya na kallon yadda ta kasa ci gaba da abin da ta ke yi d'an daidaita nutsuwar ta, ta yi da'kyar ta iya ce masa "ta na d'aki" sannan a hankali ta ce "Ina kwana" Aliyu ya san da shi ta ke ba Sameer ba shi ya sa ya ce. "Lafiya". Ya fad'a ya na wucewa numfashi ta sauke lokacin da suka shiga d'akin Umma da har za ta tashi ta shiga d'aki idan sun fita ta fito ta ci gaba sai kuma ta fasa ta kalli 'kofar d'akin Umman haka kawai ta zubawa takalmin Aliyu ido ganin yadda ya ke d'aukar ido ya na she'ki wai yau Aliyu ne a gidan su har cikin d'akin su ita dai damuwar ta Allah ya sa ba shi ne ya ke mata kyautukan nan ba, sai kuma zuciyar ta, ta ce "idan kuma shi ne fa ya za ki yi"? ji ta yi numfashin ta ya na neman daina tafiya yadda ya kamata cikin azama ta girgiza kai da sauri ta kawar da tunanin a ran ta sannan ta daina kallon gurin gabadaya ta na nan a zaune sun d'an dad'e daga baya ta ga sun fito za su fita. "I love you Zainab" Aliyu ya fad'a a zuciyar shi wanda ya yi daidai da kamar ta ji a fili ya fad'a kawai ta d'ago gani ta yi ya kalle ta sannan su ka fita da Sameer su ka bar ta zuciyar ta na harbawa cike da tunani "me ya sa Aliyu ya ke mata irin wannan kallon kodan yau ya gan ta ba nikaf ne kenan fuska ta yake kallo"? Hannu ta saka ta na shafa fuskar ta ta tabbas fuskar ta ya ke kallo innalillahi ai ba ta san za su shigo ba da ba za ta fito waje ta yi d'inki ba gara ta yi abun ta a d'aki................... "Zainab kin ga Aliyu d'an albarka kalli shigowar su abin da ya bani" ta ji muryar Umma ta katse mata tunanin da ta ke yi kallon hannun ta tayi ta ga kud'i ga kuma turare da alama zai yi tsada domin ka na ganin sa ka san ba turaren 'yan ya ku bayi ba ne, saboda kar Umma ta fahimci a rud'e ta ke ya sa dole ta d'an saki fuska ta yi murmushin da iyakacin sa la6en ta, ta na jinjina kai amma ba ta yi magana ba komawa Umma ta yi ta aje ta na fitowa ta d'ora aikin ta. Komawar su chemist Aliyu da ya tsaya daga 'kofar shiga ya ce "Sameer wai dama har yanzu Zainab ba ta daina d'inki ba"? Kai Sameer ya d'aga ya d'aga ya na kallon sa ya ce "eh ba ta daina ba ta na yi duk ranar da ta samu lokaci idan ba school ko kuma da dare kafin ta kwanta". "Har da dare lokacin da ya kamata ta kwanta ta huta gaskiya ya kamata ka fad'a mata ta daina wannan aikin 'karfi ne da 'kafafun ta take takawa abun ya na juyawa akan kud'in da baifi dubu nawa ba ni bana son ta ri'ka shan wahala" ya fad'a fuskar sa na bayyanar da rashin jin dad'in da zuciyar sa ke ciki murmushi Sameer ya yi ya na cewa. "Ai kuma ta riga ta saba ba za ta iya dainawa ba ko na fad'a mata" huci Aliyu ya fitar ya na cewa "a nan kenan amma idan na aure ta wallahi ba zan bari ta yi ba ko ta je da shi sai dai ta ri'ka kallon sa da ido ko na yi kyauta da shi" dariya Sameer ya yi jin abun da ya ce kuma ya ga da gaske ya yi maganar ya ce. "Ba na jin za ta amince koda auren na ta ka yi" ya fad'a ya na tabbatar da hakan a ran sa ya tsaya akan cewa lallai Zainab ba za ta ta'ba amincewa ta rabu da keken ta ba. "Idan ta'ki yarda sai ta fad'a min nawa ta ke samu a wata sai na ri'ka biyan ta kawai" zaro ido Sameer ya yi ya na cewa "to fa abu ya yi nisa kenan"?. "Da gaske na ke Sameer hakan ya fi min kwanciyar hankali ba zan iya jurar ganin wadda na ke so ta na wahala ba mun yi waya da Amirah tun ina can zuwa nan da kwana biyu za mu je gidan su na gaida Mama sakamakon wancan zuwan da na yi har na tafi ban je ba za su ga kamar yanzun saboda ba ala'kar karatun Amirah a hannu na ne shi ya sa na daina zuwa gurin su" kai Sameer ya jinjina ya na cewa "ok ba damuwa Allah ya kai mu". "Amin bari na koma gida gurin Momy za mu yi magana da ita sai na fito" "ok ka gaida ta" fita Aliyu ya yi ya tafi gida ya bar Sameer ya na mamakin maganar da ya fad'a na cewa ba zai iya barin Zainab ta ci gaba da d'inki ba gara ta fad'a masa nawa ta ke samu a wata ya ri'ka biyan ta. @YUSRAH Yau weekend Shareef ya na gida bai fita ko'ina ba ya na zaune a parlor ya d'ora laptop d'in sa akan table ya na duddubawa Nihal ta kira shi bai d'aga ba ya katse ya kira ta d'agawa ta yi sun fara magana kenan Mami ta fito ganin ta ya sa Shareef cewa Nihal ta kashe kiran ya na zuwa zai kira ta daga baya, aje wayar ya yi bayan ya ji ta katse sannan ya bar kallon laptop d'in ya tattara dukkan hankalin sa da nutsuwar sa ya na cewa. "Barka da kwana Mami na fatan kin tashi lafiya"? Murmushi ta yi ta na kallon sa ta jinjina kai alamar eh ta ce "lafiya 'kalau na tashi Shareef dawa ka ke waya da safen nan"?. "Surukar ki ce Mami". "Shareef" ya ji ta kira sunan sa "na'am Mami" numfashi ta sauke ta na cewa "dama tambayar ka zan yi ina yarinyar

Chapter 28 of 34