har ba ya iya 6oyuwa".
"To amma kai me ka gani dangane da ni"? Jin tambayar da ya yi masa ya sa Sameer kallon sa cikin tsokana ya ce "ni dai ban ga wani abu ba ta yi maka kenan"? Kai tsaye Aliyu ya ce "a'a".
"To ka na son ta"? Nan amsar d'aya ce "a'a" da 'karfi Sameer ya ce "amma tun da ita ta na son ka za ka iya auren taaa"? Yana rufe baki Aliyu ya taka wani irin burki wanda sai da Sameer ya bugi kujera juyowa ya yi yana kallon sa dariya Sameer ke yi har da ri'ke ciki ya kasa magana ganin yadda Aliyu ya yi da fuskar sa dafe saitin 'kirjin shi ya yi jin yadda zuciyar sa ta ke bugawa ya sa ya d'ago ya na kallon Sameer ya ce.
"Amma wallahi kai dai Sameer ba ka da mutunci wata rana in dai ina yawo dakai sai dai aga gawa ta saboda maganganun ka masu kama da saukar tsawa" rufe baki Sameer ya yi ya na cewa "sorry Marshall dama na jarraba ka na yi".
"Kuma ka rasa ta yadda zaka jarraba ni sai da haka"?.
"To ai na ga ba wani abu ba ne a ciki dan kawai na tambaye ka".
"Eh ba wani abu bane mana tambaya mai muhimmanci ya kamata ka yi min".
"Wacce iri kenan"?.
"Ka fi ni sani"
"Ohoo so ka ke nace maka ka na son Zainab? Ta yi maka? Za ka aure ta abin da ka ke son ji kenan ba"?.
"Eh shi ne nake so naji ba waccen shirmen ba".
"Shikenan to yanzu dai tada mota mu yi sauri mu isa gida".
"Ka na da uzuri ne"?.
"Ni ko na ke da uzurirrika zan bud'e chemist kuma kai ma ka manta za ka had'u da Zainab".
"Haka" Aliyu ya fad'a ya na tada mota su ka ci gaba da tafiya suna karya kwanar anguwar su kuwa sai gan ta ita da Afifah sun fita daga gate din islamiyyar su d'an murmushi Aliyu ya yi ya na tsaida motar ya ce "ya ka gan ta Sameer"? Ya fad'a ya na sauke numfashi tare da d'an lumshe ido jin yadda lokaci guda bugun zuciyar sa ya canza sakamakon ganin ta kad'ai da ya yi ido shi ma Sameer d'in ya zuba ma ta yadda suke tafiya a tsari cikin nutsuwa ita da Afifah kafin ya juyo ya kalli Aliyu da shi ma ya bud'e na sa idon ya na ci gaba da kallon ta ya ce "ita ce yarinyar da ta saka na rasa nutsuwa ta ita ce duk duniya na ke fatan mallakar ta nake addu'a saboda ita a kowacce rana da son ta nake rayuwa ba na jin bayan Zainab zan iya son wata yarinya a duniya ya Allah ka taimake ni Ubangiji ka 'kaddara yarinyar nan ta zamo mata ta" ya 'karasa maganar ya na fitar da huci me zafi wanda ya sa Sameer juyowa ya kalle shi da murmushi kawai amma bai yi magana ba da yake dama Aliyu iya tsayawa ya yi ba kashe motar ya yi ba sai ya ja kawai su ka ci gaba da tafiya su ka sake zuwa su ka wuce su Afifah a hanya da mamaki Afifah da ta bi bayan motar da kallo ta ce.
"Wannan Yaya discipline ne to ina ya je na ga kuma da ya tsaya a can"?.
"Maybe shi d'in ne sun je anguwa tare da Yaya Sameer" Zainab ta fad'a ta na d'an sauke ajiyar zuciya kai Afifah ta d'aga ta na cewa "eh tabbas motar sa ce na yi mamakin tsayawar sa a can ne amma d'azu ina gida lokacin da ya shirya za su tafi".
Daidai sun fito daga motar ganin yadda kowanne ya d'au wanka ya sa Afifah ta ri'ke baki ta na cewa "to fa irin wannan d'aukar zafafan wanka haka sai ka ce angwaye" Zainab kam da mamaki ta ce "wai dama Afifah Aliyu ya na irin wannan shigar amma rai da rai sai dai ki gan shi daga shi sai vest da three quarter d'in wando sai kace wanda ya rasa kayan sakawa"? Dariya Afifah ta yi ta na cewa "ai indai lamarin Yaya discipline ne sai ha'kuri haka ya ke ya na son wannan shigar".
"Ai kuma kamata yayi ki fad'a masa ya daina" Zainab na rufe baki Afifah ta zaro ido ta na "ni wa? Rufa min asiri so ki ke ya ci uba na kenan".
"Dan kawai kin fad'a masa gaskiyar idan ke ki na tsoro ki fad'awa Momy man ita ai za ta masa magana" "to ban 'ki ba sai dai Momyn ita ce za ta fad'a masa yanzun dai ga su can sun alwalar la'asar sun yi masallaci sai anjima Aunty Zee ko sai gobe ma kai zan ce tun da ba 'kara had'uwa za mu yi ba" "to Afifah Allah ya ba mu alkhairi" shiga gida Afifah ta yi Zainab kuma ya wuce.
Aliyu su na fitowa daga masallaci gida ya shigo a lokacin Momy ta na zaune ita da Husnah zuwa ya yi ya zauna a kusa da ita ya gaisar da ita kallon sa ta yi bayan ta amsa ta ce "har ka dawo daga gidan su Amiran dama ba dad'ewa za ka yi ba kenan"?.
"Ai na dad'e Momy na yi 'ko'kari tun da na kusa awa biyu".
"Awa biyu ka ce Aliyu ita kuma Amiran da ta ke zuwa ta yi mana sati biyu cif a gidan nan fa"? "Kuma ni ai ba zan had'a kai na da ita ba ba ta da aikin yi ni kuma ba mashiririci ba ne".
"Meye abun shiririta a ziyara"? "Babu Momy amma ni da ita akwai bambanci ita mace ce ni namiji ne"? "Haka ne dama Aliyu ina ta so na tambaye ka wani abu tun wancan zuwan da kayi wai ba za ka yi aure bane"? Bai ta'ba tunanin abin da za ta tambaye shi ba kenan shi ya sa ta na fad'a ya d'ago ya kalle ta kai Momy ta girgiza ta na sake cewa "na ce ba za ka yi aure ba ne"?.
"Zan yi Momy".
"To ai na ga shiru-shiru ne lokaci sai sake ja yake na d'auka tun wancan zuwan na ka zaka ce min aure za kayi kafin ka koma sai kuma naga sa6anin abinda nake tunani gashi ka sake tafiya yanzu shekara uku ka dawo wannan karon babu inda za ka tafi har sai ka fad'a min budurwar ta ka an gama magana kafin ka tafi"? Murmushi yayi yana d'agowa ya kalli Momy ya ga ta girgiza masa kai ta na cewa "ba kallo ba da gaske nake Aliyu ko baka da wacce kake so ya kamata ka nema kafin ka tafi Allah maganar gaskiya ina so kayi aure to kai ma baka yi ba wa yake batun Afif tun da dama shi ba isa auren ya yi ba kai ne dai ya kamata ka yi ka ji"?.
"Kar ki damu Momy na fad'a miki akwai wacce na ke so dama lokaci ya yi d'in da zan bayyana muku ita dalilin da ya sa ban yi maganar ba school ta ke yi yanzu kuma ta gama" "yauwa alhamdulillah a ina take"?.
"A nan garin".
"Ok wacce anguwa"?.
"Zan fad'a miki daga baya idan na gama shawara" "tom Allah ya za6a maka mafi alkhairi wacce ta dace da rayuwar ka".
"Amin Momy na gode" ya fad'a tare da mi'kewa ya nufi part d'in sa Elham dake ra6e da gudu ta karaso gurin ganin ya tafi dariya ta zauna ita kad'ai ta na yi Momy dake kallon ta da mamaki tace "ke kuma fa lafiya sai kace sabuwar kamu"?.
"Dole na yi dariya na 'kara Momy farin ciki na ke da naji Yaya boss yace yana da budurwa kwanan nan zamu samu Aunty ashe"? "Aw kin ji maganar da mu ka yi da shi kenan? "Kwarai Momy kowacce kalma na ji tun daga farko har 'karshen" jinjina kai Momy ta yi ta na "ya yi kyau saura kuma ki fad'a har ya ji ni babu ruwa na ina kallo zai daki banza" zaro ido Elham ta yi ta na cewa.
"Ni kuwa ina zam fad'a ai ba wanda zai ji mutuwar sarki a baki na wallahi bazan ta'ba fad'a ba duk ranar da maganar ta fito fili kowa ya ji yanzu nasan ina fad'a abun ya koma kunnen sa cewa zai yi waye ya fad'a a ce nice ya ci ubana" hakan dai ya fi miki alkhairi ki yi shirun da bakin na ki" Momy ta fad'a daga haka ba ta sake magana ba ita ma Elham d'in haka.
** *** **
Yau Baby ba ta je hospital ba sakamakon zazza'bi da ta tashi da shi a bedroom ta wuni har magriba ba ta samu ta fito parlor ba sai da Daddy ya dawo sannan Hajiya Fatima ta shiga ta yo mata magana sai lokacin ta fito duk da zazza'bin bai gama sakin ta ba zama ta yi ta na gaida shi ya amsa ya na kallon ta ya ce.
"Baby ko bakya jin dad'i ne"? Kai ta d'aga hawayen shagwa'ba su na zubo mata ta ce "tun safe da shi na da zazza'bi" "Subanallahi zazza'bi Allah ya sauwake dama magana mu kai da aboki na Mustapha na fad'a masa matsalar da ta ke damun ki amma ya ce na bar ki, ki ci gaba da zuwa aikin ki kar na yi miki transfer shikenan ya wuce ki koma bakin aikin ki idan Allah ya kai mu gobe kin ji"? Kai ta d'aga shi kuma ya ci gaba "sannan Baby magana ta 'karshe ya ce ya na nemawa d'an sa auren ki" wata iriyar zabura Baby ta yi jin numfashin ta ya na neman barin jikin ta da wani irin mugun sauri ta fara girgiza kai ta kasa magana 'karshe ta fashe da kuka ta na cewa "a'a Daddy ni ba zan yi aure ba kawai zan ci gaba da aiki na har iya tsawon rayuwa ta ba zan auri kowa ba" zaro ido Hajiya Fatima ta yi ta na kallon ta, ta ce "kin yi hauka ne uban ba za ki yi aure ba kai ka ga shashashar yarinya idan kin 'ki yin aure saboda shi ki na tunanin shi zai fasa na sa auren saboda ke ne, ina ruwan sa da ke, ke ce ki ke naki yi shi kam ai ya na can hankalin sa a kwance ya na rayuwar sa cikin jin dad'i da walwala ke kin zo ki matsawa kan ki a banza" kai Daddy ya jinjina ya na cewa "bakya son sa Baby amma ai da kin bari kun had'u ko ma menene daga baya sai ki yanke hukunci" har lokacin kuka Baby ke yi ta ce "ni Daddy ba sai ya zo guri na ba, ba na bu'katar ganin sa".
"Ok ba damuwa tashi ki je" mi'kewa ta yi ta na jin yadda sabon zazza'bi ya dad'a lullu'be ta lokaci guda a hankali ta bud'e 'kofa ta shiga tare da rufowa tsaki Hajiya Fatima ta yi bayan wucewar Babyn ta ce "anya wannan yarinyar ba ta fara samun 'kwacewar kai dalilin yaron nan ba, ace tsabar hauka har da wai ba za ta yi aure ba a rayuwar ta hummm ai kuwa ba ta isa ba sai ta yi".
"Dama ai ba wai yin ne ba za ta yi ba a'a yanzu ta na kan zafin abun idan ta huce ita da kan ta za ki ga ta na batun auren sannan ko da ace ta 'ki amincewa ta yi d'in ni kam ba zan bar ta ba wannan d'an gidan abokin na wa ya na hankali sosai da shi zan had'a ta tun da har mahaifin sa ya furta ni kuma Mustapha ya fi 'karfin komai a guri na" numfashi Hajiya Fatima ta sau'ke ta na cewa
"Yauwa masha Allah yanzu na ji magana"
"Au duk maganar da mu ke da ba ki ji ba kenan"? Dariya ta yi ta na cewa "a'a na ji sai dai ba irin wacce na ke son ji ba ce amma abin da ka fad'a yanzu ya wanke min zuciya".
"Da sabulu na wanke miki zuciyar na ki ko da Klin"? Jin abin da ya ke ya sa kawai ta fara dariya ta na cewa "gaskiya Alhaji ba ka da dama wannan idan ka zauna da me cutar hawan jini tuni zai warke saboda abun dariyar ka gaskiya ka na saka ni nishad'i sosai" kai ya jinjina ya na cewa "alhamdulillah ai ni kullum abin da zai faranta miki shi na ke so kin ga yanzu misali ki d'auki wannan maganar da mu kai a matsayin........................
Kiran wayar sa da akai shi ya hana ya fad'i maganar da ya ke fad'a ya d'aga kiran Hajiya Fatima ta na gefe ita kad'ai sai murmushi ta ke ran ta fal da farin ciki.
Sanin da Amirah ta yi Aliyu ya na gari Shi ya sa kwana uku tsakanin zuwa gidan su da ya yi ita ma ta zo sai dai ta yi mamaki domin tun ta zo a parlor ta ke ita da sauran yaran amma ko kad'an ba ta ga ya fita ko ya shigo ba, ba ta san a ina ya ke ba yanzu har su ka baje su ka bar ta a gurin Afifah ta ce mata ta karasa bedroom d'in su amma saboda so take ta ga ba kowa ya rage sai ita kad'ai ta shiga part d'in Aliyu 'kin 'karasawa ta yi ta ce ta yi gaba ta na zuwa daga baya.
Sun dad'e da barin parlor amma dai shiru ta na ta zauna ta d'auka ya na nan a part d'in sa fitowa ne baiyi ba gajiya ta yi ta mi'ke ta shiga gurin su Afifah tare da aje handbag d'in ta da mayafin ta kwanciya ta yi akan gadon ta rufe ido na d'an mintuna har barci ya fara d'aukar ta amma sakamakon mafarki da ta yi ga Aliyu tsaye tare da mace da sauri ta bud'e ido a gigice ta mi'ke tana d'aukar mayafin na ta ko yafawa ba ta yi ba ta fita daga 6angaren su Afifah da sauri ta nufi parlor ganin ba kowa ya sa ta ja dogon numfashi ta lalla6a tana waige-waigen ko wani yana kallon ta lura da tayi babu kowa yasa wuf ta fad'a part d'in Aliyu a guje tana shiga parlon sa domin ta duba idan yana nan bata samu kowa ba shiru amma dai ta ga wayar sa da laptop d'in sa akan table 'karasawa ta yi ganin photon mace akan fuskar laptop d'in d'an du'kawa ta yi tana 'kure photon da kallo gaban ta na mugun fad'uwa zuciyar ta na bugu kamar ganga "na shiga uku wace wannan a ina take kar dai ace ita Aliyu ke so? Lokaci guda ta ji kan ta yana juyawa idon ta ya na neman rufewa sake bud'e idon ta sosai ta yi akan photon ba ta ta'ba ganin wannan budurwar ba taya zata nemo ta wa zata tambaya wa ye ya san ta a ina take"?.
Wayar sa da ka kawo haske alamar shigowar message ya sa ta mayar da hankalin ta gurin nan ma dai wani photon macen ta sake gani akan secreen d'in wayar da sauri ta d'auka hannun ta ya na rawa ta kalli photon lokaci guda ta zaro ido waje numfashi ya na fita da mugun gudu ganin wacce ke fuskar laptop d'in na sa ita ce akan wayar ma kenan dai hakan ya na nufin ita ce wacce Aliyu ya ke so ko ba'a fad'a mata ba kusan su6ucewa wayar tayi daga hannun ta cikin sauri Amirah ta ajiye jikin ta yana rawa sosai hawaye ya cika mata ido ta fara girgiza kai ta na cewa "innalillahi wa inna ilaihi raji'un na shiga uku me yake shirin faruwa ne dama da gaske Aliyu yake da yace min yana da wacce yake so ban ta'ba yarda ba saida na ganta da ido na a ina wannan budurwar take ta ya zan same ta"? kuka ta fashe dashi tana dur'kusawa a gurin tare da kife kanta a jikin table d'in wanda laptop da wayar suke kai kawai ta fara kuka mai 'karfi sai da tayi ta gaji sannan ta d'ago idonta yayi jajur ta mi'ke fuska a murtuke ba rahma a ranta ta fara magana.
"Wannan yarinyar ce Aliyu yake so dama a kanta ya 'ki saurarar tawa soyayyar? Kan bala'i ai kuwa wallahi bata isa ba ni na fara sanin Aliyu kafin ita ni na fara son sa ni na zauna da shi tsawon lokaci watakil ma sannan bai san da zaman ta a duniya ba bazai yuwu ina kallo wata jakar 'kauye tazo ta aure shi ba, inaaa! never in history zan binciko ta duk a inda take a fad'in 'kasar nan sai naje na same ta ko ta bar min Aliyu ta je ta samu wani ko kuma na sanya ta cikin masifar da duk dangin ta idan sun taru basu isa fitar da ita daga cikin bala'in da zan jefa ta ba" ta karasa maganar tana cije lips ta jinjina kai d'auko wayar ta tayi saboda tasan Aliyu baya saka password a wayar sa da sauri ta tura photon sannan ta aje masa wayar ta juya ta fita ko sallama ba ta yiwa Momy ba ta fice ta d'auki motarta ta koma gida a lokacin Nansy tana bedroom d'in kawai sai jin Amirah ta bud'o kofa tana kuka ta yi da mamaki ta d'ago tana kallon ta har tazo ta fad'a gado tana sake fashewa da sabon kuka sosai Nansy ta zuba mata ido tana kallon ta matar da ta bar gida cike da farin ciki kuma me yasa ta dawo ta na kuka lallai akwai dalili amma bari ta tambaye ta tashi tayi ta karasa tana dafa ta cikin kulawa ta ce.
"Aunty Amirah lafiya kuwa"? Kai Amirah da ke kwance tana faman kuka ta girgiza ba ta iya magana ba yadda kukan ya ke zuwa ma ta ba 'kak'kautawa "Aunty Amirah dan Allah ki daina kukan nan tunda baya magani ki fad'a min me ya 6ata miki rai na san dai lafiya 'kalau ki ka bar gida"? Tashi zaune Amirah tayi tana goge hawayen fuskarta da towel d'in ta dake aje akan gadon muryar ta a dashe tace "Nana ni da Aliyu ne shi ne silar kuka na"
"Subanallahi Yaya Ali-Zaki shi ne ya 6ata miki rai kuma"?.
"Kwarai Aliyu ne saboda yau na ga abin da ya kusa tarwatsa min rayuwa ta ina jin zuciya ta kamar ta buga a halin yanzu domin bana ganin komai daidai" zaro ido Nansy tai tana sake sabon zama tace "ni fa Aunty Amirah ban gane ba ki yi min bayani yadda zan fahimce ki wani abu ne ya faru tsakanin ku"? "Tabbas Nana abu ne ya faru da nasan idan na shiga part d'in sa abin da zan gani kenan da nasan zan ci karo da ba'kin ciki da tashin hankalin da zai hana ni zaman lafiya da ban je gidan ba ma kwata-kwata na yi dana sanin zuwa na gidan su Aliyu yau kuma zan dad'e ban koma ba" kai Nansy ta girgiza ta na cewa.
"Haba Aunty Amirah akan me"? "Nana ko ke ce idan na fad'a miki abinda ya faru ba za ki sake marmarin zuwa gidan akan lokaci ba".
"Ok me ya faru ina jin ki"?.
"Basai na fad'a miki ba saboda bana son abun tashin hankali ko kuma su Mama da Daddy su ji labarin rai na ne zai sake 6aci fiye da yanzu kawai ki 'kyale ba zan iya fad'a miki ba sai a gaba" "shikenan ba damuwa Allah ya rufa asiri" Nansy ta fad'a tana mi'kewa ta fita jim kad'an ta dawo da ruwa a hannunta tana mi'kawa Amirah kai ta girgiza mata batare da ta yi magana ba Nansy dake tsaye da kofin ruwa tace "idan ki ka sha ruwan sanyi zai rage miki rad'ad'in da ki ke ji a cikin ran ki shiyasa ma na kawo miki" jin abinda tace yasa Amirah kar6ar ruwan tayi kar'ba d'aya ta mi'ka mata tana cewa
"Ki d'auko min paracetamol a cikin drawer yanzu nasha naji na fara jin sanyi maybe zazza'bi ne zai kama ni" ta fad'a tana kwanciya "ok bari na dubo miki" Nansy ta fad'a tana aje mata ruwa ta fita tun da zata sha magani zuwa tayi ta d'auko ta kawo mata ta tashi tasha sannan ta koma ta kwanta ta yi shiru idon ta a rufe kawai photon d'azu take gani fuskar Zainab dake d'auke da murmushi da sauri ta bud'e ido har da kamar ta firgita nannauyan numfashi ta sauke tana sake sabon juyi ta zubawa guri d'aya ido kawai ta rasa abinda yake mata dad'i Nansy tana gefe tana kallon ta ba tare da tasan taimakon daya dace ta bata ba tunda ta'ki fad'a mata abinda ya same ta balle ita kuma ta san me zatai mata ganin ta juya mata baya yasa ta le'ka fuskarta ta gani ko barci tayi sai taga idon ta biyu ganin hakan ya sa kawai ta tashi ta fita a bedroom d'in jin 'karar bud'e 'kofa da rufewa yasa Amirah jan 'kwafa tana cewa.
"Wallahi Aliyu ka yi da 'yar halak zan nuna maka ba'a biyu dani koma wace wannan budurwar zan nemo ta zan tsananta buncike a kan ta har sai na samo inda ta ke zan iya kawar da kowa dan na mallake ka a shirye nake na fara ya'ki domin na 'kwatowa kai na soyayyar ka a kan ka saidai a mutu wannan alkawari nane kuma sai na cika shi saika aure ni Aliyu na rantse bazan yi kaffara ba sai na aure ka ko ka na so ko ba ka so" ta 'karasa maganar ta na sake sabon juyi a ran ta ta ce.
"To amma ban san ta ba ban ta'ba ganin ta ba ban san a wacce jiha ta ke ba ta ya zan nemo ta? Ta tambayi zuciyar ta can wani tunani ya fad'o mata mi'kewa ta yi ta shiga toilet ta wanke fuskar ta duk da kana ganin ta kasan ta yi kuka ko bata fad'a maka ba saboda kar Mama ta gane shiyasa ta d'auki ba'kin glass ta saka a idon nata ta d'auki handbag d'inta da wayar ta ta fito Nansy tana ganin ta, ta fito da sauri ta ce
"Aunty Amirah ina zuwa kuma bayan kin ce zazza'bi ki ke ji"? "Zan je wani wuri ne yanzu zan dawo" da mamaki Nansy ta ce "ai gidan su Yaya Aliyun za ki sake komawa" kai Amirah ta girgiza ta na cewa "a'a ba can bane nan anguwar ne ina dawowa ba dad'ewa zan yi ba".
"Ok bari tun da haka ne na zo na raka ki"? Da sauri Amirah ta ce "a'a ina dawowa kar ki biyo ni" tana fad'in haka ta fita daga parlon ta yi waje wani shagon photo a bayan layin su ta je photon Zainab data d'auka na wayar ta ta nuna masa tana cewa "S.S Smart dan Allah wannan photon nake so ka wanka min kamar guda goma ka gane"? Kai ya d'aga ya na kar6ar wayar ya ce "ok yanzu ma kuwa tsaya ki tafi da shi" murmushi Amirah ta yi tana samun kujera ta zauna ba jimawa ya fito ya mi'ka mata wayar ta sannan ya bata photunan guda goma cif kamar yadda tace bud'e handbag d'inta ta yi ta zaro kud'i dubu goma ta mi'ka masa tana tashi tsaye tace.
"Kai ma ga ladan ka nan duk d'aya na d'auka shi matsayin dubu d'aya goma saboda girman abin da zan yi" "yauwa irin ku ake so Hajiya Amirah na gode sosai Allah ya biya ki".
"Amin kar ka damu" ta na fad'in haka ta juya ta tafi daga nan shagon data fita kai tsaye facemask ta saka a fuskar ta akwai wasu 'yan 'kwaya da suke taruwa a wani guri can gefen anguwar su gurin su ta je ta same su sun taru kuwa da d'an yawan su ta ce.
"Aiki na ke so kuyi min kowanne ku zai samu dubu hamsin wanda kuma ya samo min abinda nake so nayi masa alkawari rabin million d'aya" su na jin ta ce haka kowa ya d'ago a
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 30 Chapter of 34