Share this page
had'u sai dai bani da 'kwarin gwiwar zuwa inda ya ke tun da yana tare da wad'ancan mu'karraban na sa da kamar shi kad'ai ne yau sai na je gurin sa na gwada sa'a ta" dariya Rasheedat tai tana cewa "ke Bilki mai zai kai mutum can su karya masa 'kafa mu dai tsaya daga nan mu yi ta kallon abun mu, mu na jin dad'i" 'karasa bud'e 'kofa Zainab tai ta fito tare da kallon su ganin ba ma su lura da ita ba gashi sun tare hanyar fitar yasa tai gyaran murya domin su matsa mata daga hanya ta wuce amma a banza ba su ji ta ba mamaki ne ya kama ta harma ta kalli inda suke kallo dan ta ga abin da ya d'auke musu hankali Aliyu ta gano zaune akan kujera cikin katuwar rumfar kofar gidan su ya sha ado da kayan gado wato dai shi waccan a haka rayuwar sa zata 'kare kullum da 3Quater kamar dashi aka haife shi ga Sameer a gefen sa da kuma wani soja Mansur shi ma d'an anguwar ne guri d'aya su ke aiki da Aliyu sai dai shi Mansur bai dad'e da shiga aikin ba d'an tsaki ta ja za ta wuce ta gefen su Rasheedat tace. "Ahhh me ye abun tsakin dan kawai mun kalli abin da yai mana"? Hararar ta Bilki ta yi ta na cewa "'kwarai ko ke nasan kin 'kyasa shi dan kawai ace miki ta Allah wato malama shine ki ka 'ki nunawa zuciyar ki ta na dan'kare da soyayyar sa ai Aliyu 'karshe ne" wani kallo Zainab tai musu saidai damuwar da ke tare da ita ba za ta bari ta musu magana ba kawai ta wuce. "Au ai da kin yi magana mu na daidai da kowacce budurwa a gidan nan yau da sai mu ba ki kunya wajen nan za mu cire miki hijabin da Nikaf d'in a layi kowa yau ya zo ya ga abin da ki ke 6oyewa" tana jinsu ta share domin rashin tarbiyyar ba a su bane a uwayen sune da basu ba su ta gari ba tana cikin tafiya ta kusa kofar gidan kafin ta 'karasa kawai taga an sha gabanta tana dagowa taga Mansur d'an team d'in su Aliyu ne ran ta a bace ta ce "wai maye haka ina tafiya za ka tare ni a layi"?. "Ki yi ha'kuri amma yalla6ai ne ke son magana dake" had'e rai ta kuma yi "waye wani yallabai"? Nuna mata Aliyu ya yi ya na cewa "sir Aliyu Ahmad na ke nufi" wani irin fad'uwa taji gaban ta yayi akan wanne dalili Aliyu zai ce yana son magana da ita yana wancan gun bayan ga Sameer shima duk su na tare 'kara had'e rai tayi tana cewa. "Ka bani hanya na wuce". "Zan barki ki wuce ne kawai idan har kika saurare shi" cike da takaici tace "bazan saurare shi d'in ba ka bani guri na wuce bana son irin haka" "Na fad'a mi ki zan barki ki wuce ne kawai idan ki ka saurare shi". "Wai Mansur meye haka ne ka ban hanya na wuce bani da lokacin sa" hard'e hannu a 'kirji ya yi yana cewa "kai uban gidan nawa"? "Koma waye na ka kaga malam ka matsa min na wuce ko nayi maka kama da irin matan dake tsayuwa a layi suna magana ne"? Kai ya girgiza ya na cewa "a'a baki min kama dasu ba nafi kowa sanin ki Zainab kuma zan bada sheda a kanki ke kamila ce kuma me saukin kai". "Naji to ban hanya na wuce". "Karki sa nai laifi ki taimaka min ki je" "A'a ni baza ni gurin sa ba me zanyi mai"? "Dan Allah Zainab ki rufa min asiri ba ki san waye sir Aliyu ba tun da ba tare da shi ki ke ba rashin zuwan ki zai iya haifar min da hukuncin sati ina wahala kin ji"? D'agowa tai ta kallo inda Aliyu ke zaune ta cikin nikaf d'in ta taga ya d'auke kai daga saitin su kamar bai san da tsayuwar duk su biyun ba haushi ne ya 'kara kama ta za ta wuce da sauri Mansur yace. "Zainab dan Allah ki rufa min asiri ki je dan Allah ba dan ni ba wallahi idan ba ki je ba ina cikin matsala" tsayawa tai tare da juyowa tace "shikenan karka damu saboda kai ya ci albarkacin ka amma in dai dan shi ne ba zan ta'ba zuwa ba" zaro ido Mansur yai tare da saurin girgiza kai ya na cewa "ki daina cewa haka idan yaji sai hukunci na yafi na 'kin zuwan ki" sauke ajiyar zuciya tai ba tare da ta sake ce masa komai ba ta soma takawa a hankali ta kusa isa rumfar ta ja ta tsaya cak ta kasa d'aga 'kafar ta taci gaba sakamakon wani irin kallon da ta ga Aliyu ya na mata ji ta yi 'kafafun ta sun yi mata nauyi sam ba za ta iya 'kasarawa ba gashi yana cikin rumfar sai taje har can fasa kasawa tayi kawai ta juya ta nufi gate d'in gidan mi'kewa Aliyu yai ya na bin bayan ta ba tare data sani ba balle ta tsaya amma da ta je securities sun hana ta shiga saita cire nikaf gurin wa tazo 'yar waye ita wa take nema daga ina take?. Tambayoyi masu ban haushi suka ri'ka yi mata wacce bata basu amsar ko d'aya ba kawai gara ta koma gida ta kira Afifah ko su Elham su fito su zo su kar'ba mata amma indai saita basu wad'annan amsoshin ne data shiga gidan ta ha'kura har abada ji ta yi d'aya daga cikin su ya ce "kin ga madam idan baki da amsar tambayar mu zaki iya barin gurin nan ba kalar gurin tsayuwar kowa bane" taji muryar wani security wanda yake tsaye daga gefe fuskarsa a had'e ba alamar wargi sosai ran ta ya sake 6aci jin abin da yace da sauri ta juya za ta bar gurin kusan karo su kai da Aliyu wanda yake tsaye a bayan ta cikin tsananin firgici ta ja da baya da sauri a razane ta yada littafin hannunta sosai jikinta ya d'au rawa wanda kana gani kasan ba 'karamar tsorata tayi ba ita ba ganinsa ne ya tsorata ta ba karon da suka kusa yine innalillahi wa inna ilaihi raji'un da yanzu jikin mu ya had'u? Ta fad'a cikin ranta numfashinta har lokacin yana fita da sauri kamar wacce tayi gudu a 6angaren Aliyu ido ya zuba mata sosai yana kallon ta cikin wata iriyar tsaftacecciyar soyayyar ta da yaji tana sake tunkaho shi musamman a yanzu daya samu kusanci da ita ji yake inama ace matarsa ce inama ace ya riga ya aureta inama ace ita mallakinsa ce kullum addu'ar sa kenan baida burin daya wuce ya ga wannan rana numfashi ya sauke tare da kallon littafin da yake 'kasa kafin ya du'ka ya d'auko bai bata ba ya danna wani abu dake ri'ke a hannun shi kamar na'ura saiga gate d'in ya bud'e da kansa tare da fitar da wani sauti wasu fararen fitilu dake jikin gate d'in suka kawo haske 'kamewa masu tsaron kofar sukai tare da bashi girma juyawa yayi yana bata littafin har sannan jikinta bai daina rawa ba da'kyar ta iya saka hannu ta karba cikin sauri ta shige gidan saida ya bari ta wuce ya kallesu fuskarsa a murtuke yace "wannan yarinyar 'kanwa tace kada ku sake hana ta shiga daga yau gidan su ne" cikin girmamawa su ka ce "Yes Sir". Juyawa yai bai shiga gidan ba ya koma gurin Sameer wanda yake kallon su yana mamakin wanne kalar so Aliyu yake wa 'yar uwarsa bai ta'ba gani ba Aliyu yayi matukar damuwa da Zainab sonta a cikin jininsa da ruhinsa yake yawo. Da sallama ta shiga katafaren parlon wanda Afifah dama tana jiran tane ta d'au ado kamar saurayin ta ne zai zo ganin ta daidai ta sauko daga stairs hango Zainab da tayi yasa da gudu ta sauko tana rungume ta tace "oyoyo oyoyo Aunty Zee-Zee oyoyo gaskiya na yi murna sosai yau kin zo min ziyara sannu mu 'karasa parlon" kai Zainab ta d'aga ta na cewa. "To mu je amma ina Momyn ku ta ke"?. "Tana part d'in ta". "Gaishe da ita nake son yi kafin na tafi". "Ok muje part d'in na ta sai ki gaida ita" Afifah ta fad'a tare da ri'ke hannun Zainab wacce ta dakata ta na cewa "tsaya Afifah da kin kira ta parlon kamar hakan ya fi ko"?. "Me ya sa"?. "Saboda kin ga ba ki sani ba ko tana wani uzuri ne kar mu katse ta sannan kin ga ba sanarwa za mu shiga ai babu dad'i" girgiza kai Afifah tai ta na sake jan ta tace "kai a'a babu abin da take mu je" har Zainab za ta sake magana sai kuma ta yi shiru shiga su kai suka same ta a parlor tare da Daddy suna zaune abin da Zainab ta yi gudu kenan ga shi kuwa ya faru Husnah ta na gefe ta na rubutu 'kwace hannun ta Zainab ta yi da sauri za ta juya Afifah ta ri'ke ta ta na cewa. "Haba dan Allah Aunty Zee ki tsaya ku gaisa man bayan ga shi har da Daddy" tsayawa tai tana juyowa ta yi sallama amma ta'ki yarda ta fito normal su gan ta tana bayan Afifah kamar wacce tai laifi ko ta ke jin tsoro murya 'kasa-'kasa tace "Afifah ban san Daddyn ku yana nan ba ke kuma baki fad'a min ba me ya sa za ki min haka? Kin sa naji kunya wallahi" 'yar dariya Afifah tai zatai magana Momy tace. "A'a malama Zainab kin shigo kenan ai Afifah ta fad'a min zaki zo tun d'azu"? Dur'kusawa Zainab tai tana gaida su amma dai ta'ki fitowa daga bayan Afifan sai kare kan ta take kamar mara gaskiya murmushi Momy tai tana cewa "Ya kike ra'bewa ki shigo sosai mana karaso nan" Zainab na dur'kushe a gurin murya a nutse tace "Daddy ina kwana"? sai a lokacin Daddy ya d'ago shima yana kallon yadda take faman jan Afifah tana 6oyewa kai ya girgiza yana cewa "nidai bazan kar'ba daga nan ba" jin abinda yace yasa dole ta mi'ke tana d'an karasawa cikin parlon ta d'an zauna a kasan carpet ta gaida su da fara'ar su suka amsa mata lallai yarinyar nan akwai nutsuwa sanadin ra6arta da Afifah keyi a islamiyya yasa itama ta kasance mai hankali suna godiya da samunta matsayin 'kawar 'yar su. "Zee-zee taso mu je part d'in mu" Afifah ta fad'a tana kallon yadda ta sunkuyar da kai 'kasa ta'ki d'agowa saida tai magana sannan ta mi'ke suka fita da kallo Momy ta bisu tana d'an yin murmushi bayan sun fita Daddy ya kalli Momy da Asma'u ta mi'ko mata rubutun datai tana duba mata yace "ni dai ina yiwa Aliyu kwad'ayin yarinyar nan sai dai kin san jiki da jini ba lallai shi kuma tai masa ba" numfasawa Momy itama ta yi ta na cewa "haka ne amma ai ba shi zamu biya ba mezai hana kawai muyi magana a junan mu damu da iyayen ta a aura masa ita ba dole sai yana sonta ba kyawawan halayenta sune zasu sanya ya damu da ita idan ma dai yana da wacce yake so daga baya saiya aureta" jinjina kai Daddy ya yi ya na cewa "haka ne kema kin kawo magana amma bana son abinda zai zama damuwa a tare dasu damu gara a fara tuntubar sa idan yana ra'ayi shikenan idan yace a'a sai a 'kyale shi ni Ina ganin kamar hakan zaifi sau'ki akan mu je gurin iyayen ta kai tsaye". "Ai ko nasan Aliyu da son mace mai tarbiyya bazaice a'a ba domin yasha fad'a min kud'i ba su bane samun mace ta gari shi yake so saboda tarbiyyar 'ya'yan sa kuma ma bayan haka yace min yana da wacce ya ke so". "Wacce ya ke so kuma a ina take"? "Ni kaina ban sani ba domin bai fad'a min ba sai dai na sake tambayar sa". "To ki tambaye shi ina fata ta kasance wannan yarinyar ce ina so ta zama d'aya daga cikin ahli na" hannu Momy ta d'aga tana cewa "Amin Alhaji Allah ya amshi ro'kon ka" murmushi Daddy yayi yana kallon ta ya ce "ya amsa ma in sha Allahu yanzu idan ya shigo kiyi min magana da shi kice ina neman sa idan kina ganin kamar a naki 6angaren da matsala". "Ba wata matsala amma dai gara ka tambaye shi da kanka". "Ok shikenan idan ya shigo ki fad'a masa ya same ni a part d'ina yanzu zan fita ko zuwa dare ne idan na dawo za mu yi magana da shi" ya fad'a yana mi'kewa itama Momy mi'kewar tayi suka fita tare tayi masa rakiya suka bar iya Asma'u a parlon tana ci gaba tracing d'in rubutun da take yi. Su Zainab kam suna fita parlor ta mayar da nikaf d'inta kan fuskarta kamar yadda yake dariya Afifah tai tana kallonta tace "kai dan Allah a gida ma bazaki cire ba nan fa ba layi bane ko dama haka kike zama ko a gidan ku"? Kai Zainab ta girgiza tana cewa. "A'a". "Oh meyasa anan ba za ki cire ba kodan saboda akwai samari a gidan"? "Eh" shine amsar da ta bata "to ai kuma iya Yaya discipline ne a gidan shi kuma ya riga ya sanki Afif ne ma dai zan ce da sau'ki kuma shi da baya nan garama ki cire abin ki kisha iska". "A'a basai na cire ba". "Kai wai da gaske ki ke, me ya sa bakya son a kalli fuskar ki ne Zainab"? "Saboda na tsare kai na daga shiga fitina ina yiwa wanda zai aure ni tattalin kai na da taya shi kishi kar kowanne d'a namiji ya ga fuskata sai shi" dariya sosai Afifah keyi tana tafi tare da jinjina kai tace. "Gaskiya ne Zainab ni kai na da nake mace kuma 'kawar ki zan iya 'kirga sau nawa naga fuskar ki ba dan kina yin alwala ba kuma saboda mutane kar su gani bakya yin alwala sai kowa ya gama shima ba dan nasan muryar ki ba fuskar dai zai min wahalar ganewa ko dan ina ganin ta a islamiyya lokaci zuwa lokaci ko Yaa Sayyidi shima alwala za ki yi kika cire nikaf ya ga fuskar ki shikenan ya rud'e ya kamu da son ki haka ne"? "Hummm" kawai shi ne abin da Zainab ta ce wanda yasa Afifah dariya tana cewa "humm me"? "Ba komai" ta fad'a daidai Fati da Elham sun fito ganin har tazo yasa suka karaso suna cewa "Aunty Zainab ina kwana"? A sake tace "lafiya kalau ya ku ke"? "Muna lafiya" Fati ta d'ora da cewa "dan Allah Aunty Zainab na d'auko littafi na, na d'an biya ki ji ko ina da gyara"? Tun kafin Zainab ta yi magana Afifah ta harari Fati ta na cewa. "Ke ba d'ori ta zo yi muku ba kar ku takura ta ki bari sai kin je islamiyyar man" murmushi Zainab tai tana cewa "a'a bari na d'ora mata d'auko Fati" jin zata biya mata yasa Elham ma tashi kowa ta d'auko na ta al-qur'anin su ka dawo d'age nikaf d'in Zainab tayi sannan ta fara gyara musu Afifah dake gefe tana murmushi so take ta yi dariya tasan tana yi indai Zainab ta fahimta yanzun nan zata mayar da nikaf d'in ta yadda yake Aliyu kam daga kofar gidan su tashi yayi domin ya shigo gida zai d'auki abu kawai tun yana wajen kofar parlon su kafin ya bud'e yake jiwo tashin karatun ta tsam ya tsaya a guri d'aya yayi shiru yana saurarar ta daga baya kuma ya sauke ajiyar zuciya yana cewa "alhamdulillah" sannan ya bud'e kofar ya shigo idon sa ne ya sauka akan kyakkyawar fuskar ta da ke bayyane rabon da yaga fuskar ta a fili kamar haka har ya manta wani abu yaji ya sake dira a cikin zuciyar shi ji yake ina ma yadda take zaunen nan ace ba zuwa ta yi zata tafi ba kyan abun ace ta riga ta zama matar sa a gidan sa take ya aure ta kawai abin da ya kawo a ransa ke nan Zainab bata lura da wucewar sa ba saida ya d'auko abinda zai d'auka ya dawo zai fita jin 'karar bud'e 'kofa yasa ta d'ago karaf su ka had'a ido da sauri ta d'auke kai gaban ta na fad'uwa ta mayar da kallon ta kan al-qur'anin da'kyar tace. "Ina kwana"? K'ofar fita ya nufa can 'kasa ta ji muryar sa yace "lafiya" numfashin da ya tsaya mata a 'kirji ta samu ta fito da shi tana d'an daidaita nutsuwar ta ta ci gaba da yi musu gyaran saida suka gama Afifah ta tashi tana cewa "Zainab ta so mu koma bedroom d'in mu tun da gashi tun ba'a je ko'ina ba abun da kike gudu ya faru taso mu je" kai ta girgiza tana mi'kewa ta ce "a'a tafiya zan yi na baro d'inkunan mutane da dama kuma an kusa bikin". "Kai dan Allah Aunty Zee please mu karasa ki wuni man" zaro ido Zainab tayi tana kallon ta tace "wuni fa ki kace? A'a tafiya zan yi" ta fad'a tana yun'kurin nufar kofar fita da sauri Afifah ta ri'ko hijab d'in ta tana girgiza mata kai tace "wai dan Allah Zainab me ya sa bakya son zuwa gidan mu kuma yau ina ta murna kin zo sai ki ce tafiya za ki yi................ Muryar Momy ce ta katse maganar da Afifah ke yi "Ina zata je amma ba har gida za ta tafi ba"? Kai Afifah ta d'aga tana cewa "eh wai sai ta tafi nace ta tsaya ta wuni ta'ki" "A'a haba Zainab daga zuwan ki ki bari man ko zuwa jimawa sai ki tafi" "Nima fa abun da nace kenan ta tsaya ta wuni". "Ko bata wuni ba amma tunda yanzu 'karfe sha biyu tayi ta bari idan tayi sallah taci abinci sai ta tafi bari na zo" ta fad'a tana nufar wata 'kofa kallon yadda Zainab ta yi shiru Afifah tai tana cewa "kin ji ko Zainab dan Allah ki dawo ki zauna kin ga Momy ma ta saka baki baza ta ji dad'i ba idan ki ka tafi" dole babu yadda Zainab ta iya duk da ta na son tafiyar amma tun da har da Momy ita ma ta saka baki ya za ta yi bedroom suka wuce acan ma da'kyar ta cire hijab d'in jikin ta gabadaya tafi so ta koma gida ko dan kar a kai gulmar ta gurin Hajiya jan ta Afifah ta yi tayi da hira har ta d'an ware sukai zance da aka 'kare lunch ta je ta d'ebo musu yin duniya Zainab taci abincin nan ta'ki saida Afifah ta rantse cewa indai bata ci ba sai ta zuba mata a cooler ta tafi da shi jin haka yasa taci abincin su na gamawa ta yi alwala tayi sallah shaf-shaf ta d'aura nikaf ta tashi daga kan sallayar Afifah data fito daga toilet ita ma tayo alwalar ganin yadda har ta gama shiri yasa ta saki murmushi ta na girgiza kai batare da ta ce komai ba ta d'auki hijab d'in ta ta saka. "Afifah zan tafi" taji muryar Zainab juyowa inda take ta yi tana cewa "ok bari na yi sallah sai na raka ki" tana fad'in haka ta juya ta fara sallah tsaye Zainab tai har Afifan ta idar tayi addu'a sannan ta tashi ta d'auke sallayar tana cewa "mu je to" sauke numfashi Zainab ta yi tana bud'e kofar suka fito daga part d'in su Afifah duk sauran suna dining Momy Aliyu Elham Fati da Asma'u suna cin abinci sallama ta yiwa Momy da sauri ta fita saboda ta ga yadda Aliyu ya ke bin ta da wani kallo wanda yake firgita mata lissafi a ranta tana tunanin watakil baza ta sake shigowa gidan ba sai dai idan Aliyu ne ba ya nan tsayar da Afifah Momy ta yi tana cewa. "A cikin dogayen rigunan nan guda biyu da Daddy ya siya miki kwanan baya naga baki saka su ba ki d'auko mata d'aya ai za ta yi mata daidai" kai Afifah ta d'aga tana cewa "to" tare da juyawa ta koma bedroom d'in su ta d'auko harda turare ma ta had'o mata guda d'aya ta sa'ko su a wata 'yar jaka da nufin daga baya ta kawo mata jakar fitowa tayi tacewa Momy "bari na je ta raka ta" ta fad'a tana bud'e 'kofar parlon ta fito harabar gida amma abun mamaki duk zaton ta Zainab tana harabar gidan tana jiran ta sai ta ga bata nan wucewa ta yi ta fita ko alamar ta babu humm Zainab kenan har ta gudu gida bari na bita wucewa tayi ta bi bayan ta a lokacin da ta shiga da Rasheedat suka fara karo ta na tsaye tare da Zakiyyah da sauri cikin shishshigi tace "Lah Afifah ina yini"? "Lafiya kalau ya kike"? Ta fad'a tana d'an tsayawa kad'an cikin cushi Rasheedat tace "ina lafiya kwana biyu ban gan ki ba fatan ki na lafiya"?. "Eh lafiya alhamdulillah" tana fad'in haka ta wuce da kallo Rasheedat ta bita tana cewa "wallahi a rayuwa ina so mu yi mutunci da wannan Afifan ko dan na ri'ka shiga gidan su amma sam daga gaisuwa bata tsayawa ayi wani zance da ita" dariya Zakiyyah tayi tana kallon Rasheedat tace "eh idan kin duba ita da masu aji take harkar ta". "Su wa ye masu ajin"?. "Zainab man a gidan nan da wa take 'kawance bayan ita gurin wa kika ta'ba gani ta tako ta zo idan ba ita ba"? Ta'be baki Rasheedat ta yi tana cewa "ai itan ma a shishshigin ne ya sa tayi suna a gurin ta idan ba haka ba tana matsayin 'yar mai kud'i zata zo har gida neman ta ne"?. "To indai da shishshigi Zainab ta samu suke 'kawancen ke wa ya hana ki yi mata ke ma kuyi"? Zakiyyah ta fad'a tana kallon Rasheedat wacce ta ce "ai ina mata kawai har yanzu ban samu 'kofa bane". "Hummm" kawai shine abinda Zakiyyah tace domin ita kam har ga Allah bata ga abun shishshigi a wanda ba ta kai yake ba duniya da fad'i idan wani ya'ki kuyi 'kawancen wani kana zaune zai zo ya kawo maka katin gayyatar ka yi abotar to meye a ciki. Afifah kam tana shiga da sallama d'akin Zainab ta shiga ta same ta har ta hau kan keke tana d'inki murmushi ta yi tana cewa "kaga Hajiya chef Tailor mad'inkiya tsakani da Allah Zee-Zee baki kyauta min ba daga bari na zo na raka ki shikenan nan ki ka gudo"? "Eh akwai dalilin da yasa na yi hakan"?. "Wanne dalili"?. "A'a basai na fad'a miki ba". "Ok shi ke nan Momy tace a fad'a miki ta gode sannan ga wannan" ta fad'a tana fito da doguwar rigar da turare ta aje mata zaro ido Zainab ta yi tana girgiza kai tace "a'a Afifah na gode dan Allah ki mayar mata" da mamaki Afifah tace "kamar ya na mayar mata"?. "Saboda ni ban je dan na saka ta wahala ba" "Kuma amfad'a miki dama ita ce ta ba ki rigar tawa ce fa Daddy ne ya siya mana kowa bibbiyu kwanan baya shine na d'auko miki". "Duk da haka ki koma da ita na gode" mi'kewa Afifah ta yi tana kallon ta tace "wallahi tunda na kawo miki ita bazan koma da ita ba saidai ki mayarwa Momyn da kan ki ni na tafi sai zuwa jimawa idan mun je islamiyya" tana fad'in haka ta fita ta saka takalmin ta ta koma gida. Aliyu kam sakamakon Momy ta ce masa Daddy yana neman sa shiyasa ya fasa zuwa in da zai je ya jira shi tukuna ya dawo idan su kai maganar ya tafi kar yazo yana neman sa Daddy kuwa bai dawo ba tun sha biyu da ya bar gida sai dare bayan sallar isha ya shigo shiyasa Aliyu ya bari da yayi wanka ya huta ya je a lokacin shi kad'ai ne yana garden a zaune sakamakon ko'ina da haske tarrr kamar da rana yana karkashin wata bishiya akan kujera da securities mutum biyu a

Chapter 33 of 34