wannan wofantacciyar jakar da'ki'kiyar tambayar ta ki kin gane ina da abubuwa masu mahimmanci daya fi wannan shirmen banzan ina ruwa na da wani Aliyu me ye had'i na da shi ba ala'kar komai tsakanin mu na rasa wanda zan aura sai shi? Ba had'in hanyar mota da jirgi zan tafi Idan kin ga dama ki ci gaba da tsaiwa a nan har 'karshen rayuwarki" tun da ta fara magana Amirah ta bud'e baki da ido ta na kallon ta nuna kan ta tayi ta na cewa.
"Keee ni ki ke fad'awa haka"?.
"Amfad'a miki hakan d'in ke wace ba haihuwan ki akai ba kamar kowa ba fad'a min dame ki ka fi wani? kin ga dan Allah ki kama kan ki bada iri na ake wannan shashancin ba bana iya jure magana da ta6a66iya".
"Ni ce ta6a66iyar"?.
"Tambayi kan ki ni ba ni da lokacin ki sannan zan gargad'e ki daga yau kar ki kuskura ki sake had'a ni da Aliyu idan ran ki yayi dubu sai ya 6aci domin zan d'auki matsakin da ba ki ta'ba zato ba" ta na fad'in haka ta juya ta bar gurin ta yi shigewa gida 'kamewa guri d'aya Amirah ta yi tare da d'auke numfashi na wani d'an lokaci tsananin mamakin Zainab ya kama ta kai ta jinjina ta na sauke ajiyar zuciya lallai tana da aiki a gaban ta da Aliyu da Zainab kusan halin su d'aya akan iya fad'ar magana amma ta san yadda za ta bi da su shiga motar ta tayii ta bar gurin amma ta san a ran ta sai ta sake dawowa gurin Zainab nan da 'yan kwanakin nan ba za ta'ba kwantar da hankalin ta ba sai ta ga Zainab ta amsa mata babu ita ba Aliyu domin yanzu ma ba ta yarda ba soyayya su ke ba gani ta ke kamar ta 6oye mata gaskiya ne.
Zainab kam ta na barin gurin Amirah da ta koma gida ganin Umma ta 'karasa wanke-wanken ya sa ta cire hijab d'in ta, ta na zama a kujera ta fara d'inka kayan data yanka..
Amirah gida ta koma amma sakamakon jin zuciyar ta sai bugawa ta ke ta kasa samun kyakkyawar nutsuwar da za ta iya yin breakfast ma 'kara mi'kewa ta yi ta na d'aukar key d'in motar ta, a hankali ta bud'o 'kofa ganin ba kowa maybe Nansy ba ta gidan tun ba ta gan ta ba tun shigowar ta, da sauri ta fita harabar gida ta sake d'aukar mota ta yi gidan su Aliyu ta so ace ya na nan ta je ta same shi yau ayi ta, ta 'kare amma ganin ba alamar sa ya sa ta wuce zuwa gurin Afifah ta yi sa'a kuwa ita kad'ai ce ta na kwance akan gadonsu da littafin linguistic students a hannun ta, ta na karantawa zama Amirah ta yi ta na huci gabadaya kishi ya rufe mata ido takaici ya gama cika ta da'kyar ta ce.
"Afifah dama da gaske ne Aliyu ya na da budurwa"? Ba tare da Afifah ta daina karantun ba sama-sama ta ce "me ya sa ki ka tambaye ni"? Fuskar Amirah a tamke ta ce.
"Saboda ina so na sani"? Kai Afifah ta girgiza ta na cewa "ni wallahi Amirah ban sani ba idan ya na da ita d'in ko ba shi da ita Allah masani" Afifah na rufe baki Amirah ta ce "ya na da ita man".
"Ok shi ne ya fad'a miki ko ganin ta ki kai"? "Hum'um Aliyun ne zai fad'a min ganin na yi da ido na" jin abin da ta ce ya sa Afifah tashi zaune da sauri ta na zaro ido da mamaki ta ce "kai dan Allah tare ki ka gansu".
"A'a".
"To ya akai ki ka san budurwar sa mu kuma ba mu sani ba"? Cije lips Amirah ta yi tuna yadda su kai da Zainab d'azu da ta je gurin ta, ta ce "saboda bai shafe ku ba" komawa Afifah ta yi ta kwanta ta na cewa "ai kuwa dai ina ya shafe mu Allah ya taimaka ashe Aunty na ta kusa zuwa gidan na mu kenan tun da har magana ta fara fita manyan 'kawayen Yaya discipline sai ku fara shiri domin gaskiya bikin na ku ne" ta fad'a ba tare da ta kalli yanayin da fuskar Amirah take ba wacce ta cika da 6acin rai kamar zuciyar ta ta fashe haka take ji a wannan lokacin musamman da Afifah tace Auntyn ta, ta kusa zuwa gidan wani irin ba'kin kishi ne ya sake lullu'be ta ta ji ran ta ya cika da fushi ba tare da ta sake cewa Afifah komai ba ta mi'ke ta bar bedroom d'in ita ma Afifan sakamakon ba ta so idan ta na karatu ta ri'ka tsayawa ko tambayar inda za ta je ba ta yi ba har ta fita.
Amirah kam da ta fito cikin sauri kamar za ta tashi sama ta yo harabar gidan daidai Aliyu ya shigo ta 'karamar 'kofar gate d'in numfashin ta na fita da a sukwane cikin azama ta yi wajen inda ya ke tsabar sauri kamar za ta kifa takalman 'kafar ta ma da ya ke masu santsi ne ji ta ke sun hana ta tafiya da kyau zubar su ta yi ta tafi haka ba takalmi gudun kar ya bud'e 'kofar da ya ke iya shiga part d'in sa idan ba ya son bi ta parlor kuma Momy ta na nan balle ta zagaya ta shiga da 'karfi ta ce.
"Aliyu tsaya dan Allah ina so za mu yi magana" ta fad'a muryar ta na rawa dakatawa ya yi ya na kallon ta tabbas ba ta cikin yanayi me kyau ka na ganin ta ka san cewa a hargitse ta ke 'karasawa gurin sa ta yi ta na huci da'kyar ta ce "Aliyu ashe dama wannan ce budurwar taka da ka ke 6oye min da ka 'ki fad'a min ma ni da na damu na san wacece ita na binciko ta da kai na" jin abin da ta ce ya sa shi kallon ta ya na cewa.
"Wacece a ina ki ka gan ta"? Kau da kai Amirah ta yi duk da ta na son kallon na sa amma 6acin ran da ta ke ciki ba zai bari ta ji dad'in kallon na sa ba.
"Tambayar ki fa na ke wacece a ina ki ka gan ta"?.
"A gidan su" da mamaki Aliyu ya kalle ya na cewa "a gidan su kuma"? Kai ta jinjina "k'warai gidan su zuwa na yi mu yi magana da ita a kan ka duk da ta 'ki ba ni had'in kai".
"Mee? Kin yi hauka ne me ki ka ce mata"? Had'e rai ta yi ta na cewa "wannan kuma bai shafe ka ba tsakanin mu ne".
"Please Amirah me ki ka fad'a mata"? Ta'be baki ta yi ta na cewa "ka je ka tambaye ta man ai ka fi ni kusa da ita saboda tsabar ta raina min hankali ni za ta yiwa karatun ta na goge hadda har da nuna min ita ba wani abu tsakanin ku saboda ga mahaukaciya ni kuma sai na yarda ta na wani abu kamar wacce ba ta san komai ba ni za ta mayar 'karamar yarinya har da wani wai ba ta san ka ba kar na raina mata wayo babu soyayya tsakanin ku mtwwww" ta fad'a tana jan tsaki tare da bud'e wayar ta, ta nuna masa video da ta yi wa Zainab ba tare da ta sani ba a lokacin da su ke maganar kar6a Aliyu ya yi ya na kallo kafe shi Amirah ta yi da ido ta na jiran ta ji me zai ce murmushi ta ga ya yi tare da jinjina kai ya mi'ka mata wayar ta bayan ya yi delete d'in video sannan ya ce.
"Ya yi kyau tabbas kin yi 'ko'kari ya kamata a jinjina miki" ya na fad'in haka ya wuce ta zai bud'e 'kofa da sauri ta sake shan gabansa idon ta ya fara kawo 'kwalla ta ce "Aliyu wai me ka ke yi haka ne, kenan ka za6i bare sama da ni shekarar mu nawa a tare ka san ni ka san hali na babu wani abu nawa wanda ya yi saura ba ka sani ba a ina matsalar ta ke ka fad'a min na gyara dan Allah" had'e rai ya yi ya na cewa.
"Ba ni hanya na wuce kin ji na ce ki na da wata matsala ne"? Kai ta girgiza a rud'e ta ce "to indai haka ne dan me za ka yi soyayya da wancan budurwar"?.
"Wa ya fad'a mi ki soyayya mu ke yi da ita"? "Ba fad'a min a kai ba da ido na, na ga photon ta akan fuskar laptop d'in ka da kan secreen d'in wayar ka ko nan za ka ce min ba ita ba ce"? Tamke gira ya yi ya na cewa "eh ita ce man ki na tunanin zan 6oye miki ne"?.
"Aliyu me ka ke nufi na ga gidan su ba gidan arziki bane ba 'yar mai kud'i bace hatta gate d'in gidan ya yi tsatsa ya lalace fentin gidan duk ya kod'e ga shi abincin da su ka karya da shi yau ma tuwon masara da miyar ku6ewa ne wanda ya kwana me ye abun so a irin 'yar wannan gidan a yadda ka ke da kyau da ajin nan kamata ya yi ka samu 'yar manyan mutane irin ka, ka aura wacce ta dace da tsarin rayuwar ka domin yanzu auren 'kwarya tabi 'kwarya ake yi"?.
"A ina kenan"?.
"A ko'ina ma kuma ka tambaya ka ji d'an mai kud'i irin ka sai da 'yar mai kud'i iri na sannan d'an talaka sai ya auri 'yar talaka irin sa an raba kowa ya auri sashin sa" zuba mata ido ya yi yana kallon ta kamar me nazarin maganar ta daga baya ya yi murmushi ya na nuna ta da yatsa ya ce "kenan yanzu campaign ki ke yi wa kan ki a waje na"? Ba kunya ta jinjina kai ta na cewa.
"K'warai kuwa ka na tunanin zan ji nauyin fad'a maka abin da ya ke damun zuciya ta ne"?.
"Hakan gani ki ke kin burge"?.
"Tabbas".
"To me ye ribar ki a nan"? "Riba ta shi ne ka yarda da abin da nace ka bani soyayyar ka da zuciyar ka ni kuma na yi maka alkawarin zan kula da kai fiye da yadda ka ke tunanin waccan budurwar za ta yi maka za ka samu farin ciki da kwanciyar hankali tare da ni" kai ya girgiza ya na gyara tsaiwar shi ya ce "Amirah ba zan 6oye mi ki ba ina da zuciya a 'kirji na amma tamkar babu ita domin na riga na yi kyautar ta na dad'e da mallakawa wata ita babu gurbin da zan iya saka soyayyar kowacce 'ya mace bayan ita ina so ki fahimci abin da na ce miki ita wancan yarinyar da ki ke magana a kai 'yar talakan wanda ba komai ba ita ce rayuwa ta burin na ta zama uwar 'ya'ya na duk wani motsi da son ta na ke yi bana jin koda mutuwa ta yi zan iya maye ta da wata ita kad'ai ce a gaban Aliyu ita ce mudubin da yake duba rayuwar sa ita d'in ba iya zuciyar sa bace duniyar sa ce gabadaya kin gane" Juyi sosai kan Amirah ke yi ta na kallon sa dishi-dishi numfashin ta ya na neman d'aukewa da'kyar ta ke jan iska sosai yadda zuciyar ta ta ke bugawa kuwa zai wahala idan nan gaba bata samu ciwon zuciya ba wani irin yawu mai d'aci ta had'iye da'kyar ta ce.
"Aliyu ka na fad'ar wad'annan kalaman ne dan ka ga yadda zan yi"? "A'a ba ina fad'a ne saboda dad'in baki ba ina fad'a miki abin da ya ke zuciya ta ne Amirah ki tsaya iya matsayin ki na 'yar gidan abokin mahaifi na kar ki sa kan ki inda Allah bai kai ki ba tun da mu ke da ke ban ta'ba ji a rai na daidai da rana d'aya na aure ki ba kawai dai na d'auke ki matsayin 'kanwa gare ni ba kamar ke yadda ki ke d'auka a zuciyar ki ba kin gane" shiru tai ta kasa magana sai huci da turiri da ya ke faman fitowa daga ran ta kamar ta mutu ta huta haka take ji hawaye fal idon ta, ta ce.
"Dan Allah Aliyu da gaske ne ya akai har ta yi nisa a cikin zuciyar ka haka ka ba ta babban matsayi ba tare da na ankara ba har ta yi min nisan da ta sa na kasa banbamce fari da ba'ki mene asalin ta yaya ka d'auke ta ita d'in wacece"? Kai tsaye ba tare da wani gargada ba ya ba ta amsa.
"Zuciyar Aliyu ce" zaro ido waje ta yi ta na kallon wannan hawaye ta ya'ki dannuwa sai da su fito waje shar-shar su na bin kuncin ta, ta kalle shi ta na cewa "Aliyu ita d'in zuciyar ka ce"? "Eh ita d'in she's my whole life ba iya zuciya ta ba ce" baki ta bud'e za ta yi magana ta kasa kai ya girgiza mata ya na cewa "kome zan fad'a miki yanzu ba za ki fahimce ni ba amma daga baya za ki gane gida za ki tafi ko wani wurin za ki je daga nan"? Tsabar takaici ko iya bashi amsa ba ta yi ba sai wucewa da ta yi da sauri taje ya d'ebi takalmin ta nufi gurin motar ta, ta bud'e ta shiga kawai ta kife kan ta, ta kama kuka sai da ta yi me isar ta idon ta ya yi jajur ta koma sauke ajiyar zuciya sannan tai wa motar key ta bar gidan koda ta koma gida su Mama duk suna parlor da ta yi sallama gudun kar su ga idon ta kawai ta wuce da sauri ta shiga part d'in su jin numfashin ta ya fara sama-sama alamar Asmar ta na son tashi ta d'auki anhela da sauri ta bud'e murfin ta fesa a bakinta sau uku sannan ta aje tana huci toilet ta wuce ta wanke fuskar ta, ta fito tare da zuwa gaban mirror ta zubawa kan ta ido tai shiru kamar me tunani can ta ja tsaki mai 'karfi tana baro gaban mirron ta dawo bakin gado ta zaune tare da dafe kan ta da hannu biyu kawai maganar da su kai da Aliyu d'azu ne take dawo mata sabuwa tana mata yawo a cikin 'kwa'kwalwar ta sabin hawaye ne masu zafi suka ci gaba da zuba mata gudun kar Nansy ta shigo ta same ta yasa ta tashi ta sakawa kofar lock sannan ta dawo ta fad'a gado tana fashewa da kuka tayi ta yi kamar baza ta daina ba daga baya dole ta yi shiru 'karshe barcin damuwa da ba'kin ciki ya d'ebe ta wanda ko nisa barcin nata bai yi ba ta fara mafarkin Aliyu suna tare da Zainab a gida d'aya ita kuma ta je ta zuba musu ido ta na gefe tana kallon su a firgice ta farka tana tashi zaune ta soma kalle-kalle ganin a d'akin ta take yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da runtse ido jin yadda kanta yake wani irin mugun sara mata da ciwo idonta a rufe ta koma ta kwanta domin duk ciwon da kan na ta ke mata bai kai maganganun da sukai da Aliyu d'azu ciwo ba kuma wannan ciwon kan kawai zai warke ne idan har Aliyu ya daina furta mata kalmar cewa ba gurbin da zai saka wata a zuciyar sa.
*** * **
Sakamakon Zainab ta riga ta yi graduate yanzu ba school ta ke zuwa ba sai iya islamiyya shi ya sa kullum ta na gida sai lokaci zuwa lokaci ne ma dai ta ke d'an zuwa gidan Aunty Murjah ta wuni ta taho d'inkunan mutane da su ke hannun ta, a ta ke son 'karasawa yanzu D'an Yana take son zuwa idan an yi hutun islamiyya can ne ta dad'e ba ta je kuma Aunty Murjah ta fad'a mata idan ta saka lokacin tafiya ta kira ta fad'a mata za su tafi tare ita ma ta yo kamar kwana uku sai ta taho ta baro Zainab d'in a can.
Ta na zaune a d'aki ta na had'a shampoo ta kunna wa'azi a wayar ta Afifah ta kira ta murmushi ta yi lokacin da ta d'aga ta ce "hello Afifah ya ki ke"? "Lafiya lau Aunty Zainab kwana biyu shiru idan babu hello ai akwai hay ba 'kira mai zaici gawayi"?.
"Tofa da na yi me"?.
"Kai ji dai ina ta kiran wayar ki a rufe kuma kin san Yaya discipline ya na gari ba zai bar ni na fito ba shi ya sa ban zo naga ko kalau ki ke ba"
"Ayya Afifah yi hakuri lafiya 'kalau na ke waya ta ce shekaran jiya haka kawai ta d'auke ita kad'ai na baiwa Yaya Sameer ya duba min jiya kuma ta wuni a rufe shi ya sa ki ka kira ba ki same ni ba.
"Oh na san dai halin lafiya ba za ki bar wayar ki ta kwana a rufe ba dama na kira ki ne dan Allah littafi na ya na gurin ki"? "Eh ya na nan littafan na ki ai guda biyu ne ba d'aya ba".
"Yauwa to dan Allah ta ya zai same ni yanzu ni ba za a bar ni na fito a kawo" kai Zainab ta d'aga ta na cewa "tom bari na nemi yara sai na ba su, su kawo mi ki yanzu" ta na rufe baki da sauri Afifah ta ce.
"A'a Aunty Zee".
"Kamar ya a'a"? "Uhmgaskiya a'a ni ke nake so ki kawo min da kan ki".
"Amma me ya sa sai ni Afifah shampoo na ke had'awa" marairaicewa Afifah ta yi ta na cewa "dan Allah Zainab kwana biyu ba mu had'u ba yau kam ki zo ki d'an ta ya ni hira ban san me ya sa ba bakya son shigowa gidan mu ba"? Shiru Zainab tai cikin rashin jin dad'i za ta iya rantsewa ba ta shiga gidan su Afifah sau uku ba tun da take a rayuwar ta yanzu har ta manta ma yanayin tsarin sa...................
"Kin yi shiru Zainab ko na turo su Fati su zo su kar6a min"? "A'a kar ki damu ba sai kin turo su ba gani nan zuwa yanzu zan kawo mi ki" murmushi Afifah ta yi ta na cewa "yauwa masha Allah ko ke fa Aunty Zee-Zee na har kin sa na ji dad'i ina jiran ki" ta na fad'in haka ta sauke wayar ta na mi'kewa ta ce "alhamdulillah bari na hada mata liyafa domin a rayuwa ta ina tunanin kamar yau ce rana ta farko da Zainab za ta shigo gidan mu".
"Wacce Zainab kenan" Elham tai maganar ta na kallon Afifah "Zainab fa ta gidan su Yaya Sameer man abokin ya discipline ai kun san ta a islamiyya tun da ta na shiga ajin ku".
"Oh malama zaki ce min sai nafi ganewa ayya ai Aunty Afifah kin yi dacen 'kawa sosai bari ma ni na dauko littafi na daga ta zo ta dora min kafin lokacin tafiya islamiyya ya yi".
"To kin gani dai bari ni na sama mata abubuwan tarbar ba'ko domin tun da mu ka taso ban ta'ba ganin ta a gidan nan ba yau d'in ma kamar mafarki na ke ji sai dai idan na gan ta ta zo da gasken d'in sannan ne zan yarda" dariya Fati ta yi ta kallon ta tace "kai wallahi Aunty Afifah ke ma dai".
"Ah to dole nace haka kunga laifi na ne"?.
"Ina a'a bari mu ma mu taya ki had'awa" mi'kewa su kai cikin zumud'i Afifah ta ce "yauwa 'yan 'kannai na ku mu je" gabadayan su, su ka nufi kitchen Aliyu na kallon su kome suke sai dai ya ji d'an mamaki da ya ji suna cewa wai Zainab za ta zo gidan anya ba kunnen sane bai ji daidai ba idan kuwa da gaske za ta zo d'in yana fatan Allah ya sa har ta tafi Amirah ba za ta zo ba domin akwai matsala idan su ka had'u anan tun da 'yan gidan ba su sani ba gashi ita ma Zainab d'in ba furta mata ya yi ba da zarar Amirah ta ta'bo ta fad'a hakan zai wargaza masa tsarin sa".
Tashi Zainab ta yi bisa dole dan kada Afifan ta ji babu dad'i shi ya sa za ta je sai dai ba ta so tana baya baya da Afifah ne saboda ba ta son ayi mata kallon mai son zuciya tun da ita 'yar talaka ce su kuma masu kud'i ne sannan masu mu'kami sanannu d'an gyara jikin ta yi ta shafa powder da d'an lipstick ta d'ebo litattafan daidai zata fita kofar su ta had'u da Umma da mamaki ta ce.
"Umma ina ki ka je harda hijab"? "Mun shiga gurin hajiya ne taron mu tai matan 'ya'yan ta wai kwana biyu ta ga sun daina bata kud'in kashewa ko mune mu ka hana su ba ta" murmushi Zainab tai ta na d'an girgiza kai ta ce "wato hajiya ba za ta ta'ba daina rigima ba saima abinda ya 'karu tun da kullum tsufa take haka za ku yi ta hakuri da ita".
"To ya mu ka iya Zainab Hajiya uwa ce dole mu bita duk yadda ta ke so kawai dai fatan mu shi ne mu rabu da ita lafiya" d'aga kai Zainab ta yi ta na sauke ajiyar zuciya ta ce "Umma zan fita" da mamaki Umma ta kalle ta tana cewa "Zainab ina za ki je"?.
"Ehmm dama neman ki zan je na fad'a miki zan d'an shiga gidan su Afifah ne na kai mata littafin ta".
"To shikenan sai kin dawo kar ki dad'e kin ga d'inkunan mutane sun yi yawa ga bikin gidan Dattijo ya kusa kuma ko mutum biyu ba ki wa ba".
"Eh Umma ba zan dad'e ba yanzu zan dawo in sha Allahu" ta na rufe baki su ka ji daga bayan su ance "lalalahhhhh kai jama'a gaskiya zilama ba tai ba a rayuwa wato Zainab gidan wannan Minister d'in Alhaji Ahmad za ka shiga ko harda fakewa da daukar littafi dan munafinci bayan maula za ki je Allah ya sauwa'ke a haka za ki 'kare ba aure sai yawo a gari kamar ledar pure water" had'e rai Umma tai ta na nuna Asabe da yatsa ta ce "Asabe ki iya bakin ki akan 'yata domin baki isa ki ramar min ita ba alhamdulillah ko yanzu kasuwa ta tashi d'an koli ya ci riba kuma riba mai yawa ma kuwa bari ki ji na fad'a miki kaf gidan nan daga wad'anda su kai auren har da 'yan matan ba za a ta6a samun wacce za ta kama 'kafar Zainab ba a komai ta wuce in da bakya tunani ba dan cin fariya ba na fad'a miki haka sai gaskiya" ta'be baki Asabe tai ta na saki gud'a da shewa ta ce "ahayye nanaye yau nake ganin sabon salo kiran sallah da usur ji min mace wato ke ce mai goya mata baya shi ya sa ta'ki aure sai cin kud'in wannan bawan Allan ku ke me ye ma sunan sa? Yaa Sayyadi malamin islamiyyar ku ko"? Ta fad'a tana kallon Zainab wacce ta sunkuyar da kan ta 'kasa.
"kuka ki ke ne dan na fad'i gaskiya"? D'ago fuska Zainab tai tana kallon ta tare da girgiza kai za tai magana Umma ta dakatar da ita "tafiyan ki Zainab ke 'ya ce a gurin ta koda bata son haka ni ce daidai da ita" wucewa Zainab tai cikin damuwa domin ba ta son yiwa Umman musu shi ya sa da tace ta tafi kawai ta wuce d'in amma ba dan haka ba yau sai ta fad'awa Asabe maganar da har ta mutu ba za ta ta'ba mantawa da ita ba.
Ta na turkarar 'kofar fita tun daga ciki ta fara jiyo muryar Bilki da Rasheedat a waje suna dariya wato su dai wad'annan suna son zaman 'kofar gida sai kace wasu maza ta na bud'e 'kofa ta ji Bilki ta ce "wow! Dan Allah Rasheedat ki kalle shi gwanin burgewa kyakkyawan saurayi d'an gayu ga kud'i gaskiya fa ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 32 Chapter of 34