Share this page
zabure ya na cewa "wanne kalar aiki ne wannan da za'a ba mu kud'i masu yawa haka ki fad'a mana kawai babu wani abu da baza mu iya yi miki ba" kai ta jinjina ta na bud'e handbag d'in ta, ta d'auko photunan Zainab guda tara ta mi'kawa ogan su tabar d'aya a handbag d'in nata tana kallon sa tace "ka rabawa yaran ka d'ai-d'ai duk wanda ya ri'ki photo d'aya yana da dubu hamsin wannan budurwar ta jikin photon ita nake so ku samo min kawai idan kun samo min ita na yi muku alkawarin zan ba ku rabin million d'aya". "Za'ai yadda ki ka ce zamu nemo miki ita za mu kamo ta mu kawo miki ita nan ko 'yar waye ita a garin nan sai mun samo ta sannan duk tsaron da aka zuba mata ba zai hana mu samu nasarar d'auko ta ba mu kawo miki ita" wani irin daddad'an numfashi Amirah ta sauke ta na cewa "ok ka bani number ka ni ma bari na, baka number na ta yadda idan kun samo min address d'in ta sai ku kira ni ku fad'a min". Takarda da biro ta d'auko ta rubuta musu sannan ta biya su kud'in neman kafin su samo mata ita ta cika musu alkawarin rabin million d'in da ta yi musu kar'ba yayi yana jinjina kai yace "shikenan Hajiya in dai ita ce wannan karki damu zamu nemo miki ita" juyawa ya yi ya na cewa "kai Laburos ku taso mu je yau mun samu na busawa Rakwah kai kuma shiga ka fito mana da Napep mu tafi". Amirah tana tsaye har suka fito da Napep sai da taga sun shiga sun bar gurin ta cije lips tare da sakin murmushi tace "tun da na biya wad'annan 'yan 'kwayar na tabbata maybe a yau buri na zai cika ina da tabbacin zasu nemo min ita dole ta bar min Aliyu idan ta'ki ta bakunci lahira domin zan saka suyi mata mugun fayd'e a cikin wannan kangon bari daga nan na samu Napep ya kai ni gidan su Afifah ba zan koma gida ba zuwa zan yi na nuna mata photon nan maybe ita ma ta san ta" fitowa ta yi daga kangon ta tari me Napep ya kaita a lokacin Afifah tana bedroom su Momy suna parlor ta wuce tana shiga tun kafin ta zauna ta d'auko photon tana cewa. "Afifah kin san wannan"? Kar6a Afifah tayi tana kallo ganin wacce ke jikin photon yasa ta zaro ido waje tare da hangame baki Amirah da take kallon ta ganin ta zaro ido yasa ta fahimci ta san ta kenan humm akwai 'kura kai ta jinjina ta na cewa. "Ya kin san ta ne"? Har lokacin Afifah ba ta iya rufe bakin ta da kyau ba ta ce "eh na san ta man Aunty Zee ce" hura hanci Amirah ta yi ta na cewa "wacece Aunty Zee kuma"? "Wata 'kawa ta ce" d'an zabura kad'an Amirah ta yi jin zatayi karamin hauka a susuce tace "kawar ki ce"?. "Eh man 'kawa tace a ina ki ka samu photon ta"? Daurewa Amirah ta yi duk da yanayin tashin hankalin da take ciki ba ta baiwa Afifah amsa ba sai tambaya da ita ma ta yi mata "a wanne anguwa ta ke"? Ita ma Afifan kai ta girgiza ta na cewa "a'a ni tambayar ki na ke inda ki ka samu photon" ta'be baki Amirah ta yi ta na cewa. "Tsintar sa na yi man a ina ki ke tunanin zan samu ni da ba ta'ba ganin ta na yi ba balle na san ta kawai na gan shi a 'kasa ne ana takawa na d'auke" da mamaki sosai Afifah ta sake kallon photon ta na cewa. "Ki ka tsinta kuma"?. "K'warai a kan hanya ba". "Tabd'ijan dan'kari abun mamaki gaskiya Aunty Zainab ba za ta zubar da photon ta haka kawai a layi ba" huci Amirah ta yi ta na kallon Afifah ta ce "naji kina ce mata Aunty Zainab ko budurwar Aliyu ce"?. "A'a ba budurwar sa bace dama haka nake kiran ta tun da dad'ewa kuma bayan haka dama ai ta fi ni ba sa'a ta bace kawai dai mu na mutunci ne". "Ok ya yi shi ke nan sai ki bata abun ta tun da dama tsintar sa na yi". "A ina kika tsinta ne anan anguwar"? "A'a a titin bayan anguwar mu wajen wa su 'yan 'kwaya". "Kai Subanallahi 'yan 'kwaya kuma? Gaskiya wannan abun mamaki ne sosai da al'ajabi amma shikenan bari kawai na aje shi a guri na" jin abin da ta ce ya sa Amirah cewa "a'a ki tashi mu kai mata kawai har gidan su me za ki yi da shi idan kin ajiye a gurin ki gara ki tashi na raka ki, ki ba ta abun ta maybe ma ta fad'a miki yadda akai photon na ta ya je anguwar mu" girgiza kai Afifah ta yi ta na cewa. "Uhm uhm gaskiya ba zan je a ba idan na kai mata zata damu sosai gara nayi shiru da baki na ba za ta ta'ba sani ba har abada" ganin da Amirah ta yi za ta rusa mata tsari ta ce "saboda me ba za ki iya kai mata ba? Ai gara ki kai mata". "A'a fa ba zan kai ba". "To ki nunawa Aliyu man". "Shi kuma me ye had'in sa da wannan photon idan ya tambaye ni a ina na samu fa" kafad'a Amirah ta d'aga ta na cewa "sai kice masa nice na tsinta a wajen bayan layin anguwar mu". "A'a gaskiya ba zan kai masa ba ina ruwan Yaya discipline anan"?. "Da ruwan sa man ba kince 'yar nan anguwar bace maybe ai ya san ta". "Eh ya santa man sosai ma tun da mu na mutunci" kai Amirah ta jinjina jin abin da Afifah ta ce kamar ta fad'a mata gaskiyar abin fa ya faru sai kuma ta yi shiru kawai ta ce "hummmm" alamar da magana fa wanda sai da ta saka Afifah ta kalle ta ganin irin kallon da take mata yasa ta saki fuska da murmushi saboda kar ta zargi wani abu ta ce "gaskiya kuwa kyakkyawa ce masha Allah" ita ma Afifan murmushin ta yi tana cewa "hum kyau sai kin gan ta a fili ma har d'aukar ido take musamman ki ganta ba Nikaf". "Oh har nikaf take sakawa"? "Ai ita kullum jikin ta a rufe yake ko mayafi bata sakawa hijab ma har kasa yake zuwa mata sannan kafarta da safa ba abin da zaki gani a jikin ta koni da muke islamiyya d'aya kuma muke 'kawaye ne idan ba a gurin alwala ba bana ganin fuskar ta kwata-kwata" kai Amirah ta jinjina mamaki ya gama cika mata zuciya a ran ta tace "to in dai haka ne bata bayyana fuskarta a fili ba taya Aliyu ya san ta shida ya dad'e baya kasar nan sannan da ya gama karatu ma ya dawo ba zama yayi ba ya fara aikin soja sai yayi shekaru bai zo ba gida ba"? Ashe a fili ta yi magana ji ta yi Afifah ta ce. "Nima ban san da yadda akai ya san ta ba" d'an huci ta fitar tare da rufe ido Allah ya sa ba wani abun tashin hankali ta fad'a ba balle har Afifan ta gane sake cewa ta yi "kwarai ki ka ce Zainab sunan ta ko?. "Eh Zainab sunan ta". "Kuma inkiyar gidan su fa"? Ta tambaya ta na 'kure ta da kallo ta ji wacce amsa za ta ba ta "eh to anan anguwar dai kamar an fi cewa gidan su Alhaji Habibu headmaster ko kice gidan su Aminu d'an sanda ko gidan su Sameer me chemist in dai mutum d'an anguwar nan ne kina fad'a masa haka gaskiya gidan su ba a 6oyayye bane" wani irin murmushi farin ciki Amirah ta yi tana jinjina kai tace "ok ya yi nifa tafiya ma gida zan yi". "Ki tafi gida dai yanzun"?. "Eh man". "To amma d'azu ina kika je ba sallama na neme ki na rasa ko dama ba gida ki ka tafi ba"? "A'a gida na je ai shine na tsinci photon a hanya". "Ok na gane sai dai duk da haka ya kamata ki zauna zuwa la'asar sai ki tafi ko"? "A'a tafiya fa zan yi Afifah". "Kai dan Allah Amirah ki zauna please mu na 'yar hirar mu yanzu za ki ga fa la'asar d'in ta yi ba wuya kin ji"? Ganin da ta yi Afifan ba ta son tafiyar ta ya sa ta ce "ok" tare da komawa ta zauna "yauwa ko ke fa bari na zo" Afifah ta fada tana mi'kewa ta fita Amirah kuma ta cire mayafin ta tana cewa "humm masha Allah dama anan anguwar take harna zauna wahalar da kaina ina ba da kud'i a nemo ta zan je na same ta dole ta rabu da Aliyu ko bata so in ta'ki na aikata inda idan an tafi ba'a dawow............. Kiran wayar ta da akai ba'kuwar number yasa ta d'aga ta na cewa "hello waye"? daga can 6angaren ta ji an ce "Hajiya ni ne wanda ki ka baiwa number ki d'azu mun samu wani mutum yace ya san ta har gidan su ma ya sani" kai Amirah ta jinjina ta na cewa "ok nima na samu wacce ta santa an fad'a min har adireshin gidan su amma duk da haka ina zuwa gurin ku yanzu domin aikin bai 'kare ba". "To Hajiya mu na jira" aje wayar ta yi tana mi'kewa da sauri ta d'auki mayafin ta ta mayar shi kafad'a ta d'auki handbag ta fita parlor da mamaki Afifah wacce ta d'ebo musu kayan cinye-cinye daga kitchen ta ce "ina zuwa haka kuma da sauri"?. "Gida zan tafi". "Wai Amirah ba za ki zauna ba"? "Eh tafiya zan yi zan dawo yanzu Nansy ta kira ni ta ke fad'a min wani d'an uwan Maman mu ya zo gidan ya na nema na zan je mu gaisa sakamakon mun dad'e ba mu had'u ba" kai Afifah ta d'aga ta na cewa "ok tom shikenan sai kin dawo" ta na rufe baki Amirah ta yi waje cikin gaggawa ta tari d'an Napep ta shiga kai tsaye gurin 'yan 'kwayar ta koma ta kar6i photunan tunda ta gama aikin ta dasu ta tafi gida ta 'kone photunan dan wanda ta baiwa Afifah ma d'auko kayan ta amma shi ba ta 'kone shi ba tun da aikin bai 'kare ba. Da daren ranar da'kyar Amirah ta iya runtsawa tsabar yadda ta matsu gari ya waye ta je ta samu Zainab tun kafin asuba ta tashi ta zauna har akai kira duk ta na zaune sai da ta ji za'a shiga sallah sannan ta tashi ta yo alwala ta yi sallah gari ya na d'an yin haske ta shiga wanka shaf-shaf ta fito ta shirya a lokacin Nansy ta tashi a barci ita ma ta yo alwalar kallon Amirah ta yi ta na cewa. "Dan Allah Aunty Amirah idan kin tashi ki ri'ka tashi na sallar asuba d'in nan" tsaki Amirah ta yi ta na cewa "uban wa yasa ki saki baki ki na barci wato ni ce baiwar ki me tashin ki daga barci? Ba zan tasa ba idan kin ji haushi ki koyi tashi da kan ki" ta fad'a ta na juyawa ta ci gaba da shiryarwa Nansy ba ta ce mata komai ba ta juya ta fara sallah ganin haka ya sa Amirah d'aukar handbag d'inta ta yi waje ta d'auki mota ta bar gidan a d'ari. Lokacin da ta zo anguwar tambaya ta yi tayi akai mata kwatance ta zo har 'kofar gidan sannan 'karfe bakwai daidai ba ta fito daga motar ba ta ci gaba da zama har kusan bakwai da rabi sannan ta bud'e murfin motar ta fito waje tare da jingina a jiki ta na 'karewa gidan kallo ganin yadda gate d'in ya yi tsatsa ga shi duk fentin gidan ma ya kod'e kamar ba'ai ba tsaki ta ja ta na zubar da yawu tare da d'aukar towel ta toshe hancin ta da shi ta na cewa. "Yanzu dama Aliyu ya rasa in da zai ji ya na son matar aure sai a irin wannan da'ki'kin ru6a66en gidan da talauci ya gama samun gurin zama a cikin sa? Anya nan ne gidan kuwa wancan budurwar ta jikin photon ba ta yi kama da 'yar talakawa ba ko dai wad'anda na tambaya ba su fad'a min gaskiya ba amma bari tukuna na fara aikawa idan ba nan d'in ba ne sai na ji" ta na rufe baki ta ga wani yaro almajiri ya fito daga gidan da robar barar sa a hannun sa alamar abu ya kar6o Kiran sa ta yi bayan ya zo ta ce. "Kai a nan gidan ka ke"? Kai ya girgiza ya na cewa "a'a daga makarantar mu na ke zuwa ni almajirin gidan ne aiki na ke musu" da mamaki Amirah ta ce "almajirin gidan me na sama ya ci balle ya baiwa na 'kasa yanzu wannan fatararren gidan har d'an aiki su ka ajiye amma dai aikin zubar da shara ka ke mu su ko"?. "Eh da zubar da shara da d'iban ruwa" . "Humm na canka daidai kenan dama sai dai zubar da sharar kuma idan ka zubar me su ke baka". "Abinci su ke ba ni safe da rana". "Ok yanzu wannan abinci ne kenan ka kar'bo bud'e mu gani" bud'e murfin robar ya yi taga tuwon masara da miyar ku6ewa ta sha manja jawur da ita amma tsabar wula'kanci da sauri ta ja baya ta na sake toshe hanci harda yun'kurin amai bud'e jakar ta, ta yi ta d'auko sweet ta jefa a bakin ta tare da sauke ajiyar zuciya ta ce. "Allah ya tsare gidan da ake karyawa da tuwo anan Aliyu ya 'karar da soyayyar ta sa wato ma budurwar da ya amince da ita rainon wahala ce humm" yaron ta sake kallo ya na tsaye bai tafi ba kafin ta kalli gidan a 'kyamace ta ce "shiga ka ce wai ana sallama da Zainab a waje idan ka fito zan baka dubu d'aya ka ji"? Da sauri yaron ya d'aga kai ya na cewa "to" ya juya ya shiga gidan a 'kofar su Zakiyyah ya ke aiki dan haka can ya fara nufa had'uwa su kai da yaron 'kofar zai fita ya ce. "Nan ne 'kofar su Zainab"?. "A'a ba nan ba ne zo in nuna maka" juyawa su kai tare da yatsa ya nuna masa ya na cewa "ka ga wancan 'kofar ta 'karshe can za ka je" wucewa almajiri ya yi ya na shiga in da aka nuna masa ya ce "assalamu alaikum wai Zainab ta na nan"? Juyawa Zainab dake gurin wanke-wanke ta yi ta na cewa "eh ina nan waye ya aiko ka"?. "Nima ban san ta ba wata ce ta na waje ita ce ta turo ni" kai Zainab ta d'aga duk da ta ji mamaki da aka ce wata ce a waje ta ce "kaga ka je kace mata ta shigo" to ya ce ya na fita Zainab da har lokacin ta kasa daina mamakin wacece ta tsaya a waje take neman ta maimakon ta shigo gidan ta san dai ba Afifah ba ce kuma ba su yi alkawari da wata ba balle ta ce ko d'inki aka kawo mata to kodai matar Yaa Sayyidi ce? Tabbas ita c......... Dawowar yaron yasa Zainab kallon sa ta ce "ya akai ta na ina"? "Tana wajen wai tace ki fito". "Na fito sai kace wata namiji zan fito mata waje idan bazata shigo ba ko ma wacece ta koma inda ta fito je ka kawai" juyawa yaron ya yi zai tafi Umma ta fito daga d'aki ta dakatar dashi da cewa "kai tsaya kace tana zuwa" jin abin da Umma ta ce ya sa a damuwance Zainab tace "Umma". "A'a Zainab ke ce ya kamata kice wa wani babu kyau wula'kanta d'an adam kije ki gani idan jira ta ke ki fita ki shigo da ita fa? Ba lallai ta ta'ba shigowa gidan ba tashi ki je" mi'kewa ta yi duk da ran ta bai so ba amma ita ma yanzun kuma ta yi tunanin ko jira ta ke ta fita ta shigo da ita sai dai ta yi mamaki ne saboda ba'a ta'ba yi mata hakan ba duk masu kawo mata d'inki kan su tsaye su ke shigowa, d'aki ta shiga domin ta d'auko hijab ran ta fal da wasuwasi yayin da Umma ta maye kujerar ta da ta tashi za ta 'karasa wanke kwanukan. Fita almajirin ya yi Amirah na ganin sa ta ce "ka ce ta fito waje ina jiran ta"? "Eh na fad'a mata yanzu za ta fito" numfashi Amirah ta sauke cikin jin dad'i ta ce "yauwa ga dubun ka amma ba zan ba ka ba sai ka zubar da wannan tuwon anan gurin ka je ka sayi abinci me kyau wanda zai bi lafiyar ka ka ci ko? Ganin almajirin yai shiru ta ci gaba "kaga idan ka zubar zan 'kara maka wata dubun ka had'a guda biyu ka ji"? Kai ya girgiza ya na cewa "a'a ni ina son tuwo na kuma Malam ya fad'a mana ba kyau wula'kanta abinci" jin abin da ya ce ya sa Amirah kallon sa ta ce "ok kar6i ka je" mi'ka masa dubun ta yi ya kar6a ya yi mata godiya ya juya ya tafi da kallo Amirah ta bi shi ta na jinjina kai dama ta saka ya zubar ne ta yadda idan Zainab ta fito za ta ya6a mata magana akan haka ta caccaka mata rashin mutunci wanda har ta mutu ba za ta manta ba sai kuma akai sa'a yaron me hankali ne. Fitowar Zainab da dogon hijab d'in ta kamar kullum tana shirin sa nikaf Umma da ta kalle ta ta ce "haba Zainab nan da 'kofar gidan sai kin saka Nikaf kuma fa yaron yace mace ce ina shigowa da ita za ki yi kawai"? Sauke ajiyar zuciya Zainab ta yi ta na aje Nikaf d'in akan keken d'inkin ta dake kofar d'aki sannan ta fita kusan karo su kai da Asabe wanda da sauri Zainab ta matsa mata hanya cikin ladabi amma duk da haka sai da ta biyo ta saitin ta, ta bangaje ta na cewa. "Ni sa'ar kice za ki tare min hanya ba dake nake kishi ba da tsohuwar kine dan haka ki fita idona mara kunya kawai" kallon mamaki Zainab ta yi ma ta ba tare da tace komai ba ta bi ta gefen ta, ta wuce kallon ta Asabe ta yi ta na cewa "ke sumore ina za ki je yau kuma babu dan gadon (nikaf) ko kanki ya gwaro da bango shine zaki koyi fita haka babu nikaf d'in ki nunawa samari fuskar ko Allah zaisa wani ya kwashi tsiya yakai gidansa"? Tari da bai kama Zainab ba ba tai mata ba ta na jin ta amma ta share duk da ya da girma da Asabe take a gurin ta daidai da ranar daya ba ta ta'ba mata rashin kunya ba tana mata kallon uwa matsayin ta na matar ubanta fita Zainab ta yi daga gidan can ta hango Amirah tsaye a jikin mota da waya a kunnen ta alamar magana ta ke duddubawa Zainab ta yi ko za ta ga me kiran na ta domin ba ta ta'ba kawowa a ran ta cewa Amirah ba ce tun da ba sanin ta, ta yi ba kuma ba ta'ba ganin ta, ta yi ba amma ba kowa sai ita d'in dai 'karasawa ta yi gurin ta har lokacin wayar ta ke ba ta daina ba za ta yi magana ta ga ta d'aga mata hannu alamar ta dakata takaici ne ya kama Zainab sosai domin ta tsani rainin wayo ita kuma wannan budurwar kamar ta ga haka abun ya ke ba ta'ba ganin ta tayi ba sai a yau juyawa ta yi za ta tafi ta ji Amirah ta kamo hijab d'in ta kallon ta tai sai kawai taga ta girgiza mata kai ta na sauke wayar tare da zare glass d'in idon ta, ta ce. "Barka da safiya malama Zainab na san ba ki san ni ba baki ta'ba gani na ba sai yau hakan zai baki mamaki amma wata 'yar bazata nazo miki da ita kalli ki gani" ta fad'a tana nuna mata photo a wayarta kallon photon Zainab ta yi sosai idan ba gizo idanuwan ta ke mata ba Aliyu ne zaune tare da wannan budurwar a wani kyakkyawan guri da alama ba Nigeria bace wata 'kasar ce domin ta bayansu ta ga yanayin gine-ginen 'kasar sannan ga fararen mutane a bakin ruwa su kai photon. "Wannan ya baki amsar tambayar da ke zuciyar ki ta ko ni wacece kuma daga ina na ke haka ne"? D'agowa Zainab ta yi ta na kallon ta tace "to me ye had'i na da wannan"?. "Au tambaya ki ke me ye had'in ki da shi? To amma tsaya ma dai tukuna na tambaye ki kar na yi kwafsi ba ke ce Zainab ba"?. "Eh ni ce" wani irin kallo Amirah ta yi mata ta na cewa "ke ce kuma amma za ki bani irin wannan amsar ba ki ga abin da na nuna mi ki ba"?. "Na gani me ye damuwa ta da shi"?. "Ok ba ki da damuwa da hakan amma ta ya zan yarda da ke ko ki na tunanin wannan kakkaucewar da ki ke ba zan iya gano ki ba ne kin wani fuske kamar ba ki san komai ba ni za ki rainawa hankali"? Sosai ran Zainab ya soma baci jin zata mayar da ita shashasha kamar yadda ta mayar da kanta ta ce "ke saurara kin ga dan Allah ban san akan me ki ke magana ba za ki iya tafiya bani da lokacin wannan banzan shirmen". "Shirme? Ni ce nake miki shirme? Har yanzu baki fahimci maye ma'anar zuwa na nan wajen ba kenan amma ki kalle ni da kyau kin san dai matsayi na da girma na nafi 'karfin tsayuwa a irin wannan 'kofar gidan amma na cire duk wani girma nazo saboda mu daidai ta dake ki fita daga cikin rayuwa ta" da mamaki Zainab ta nuna ta da yatsa ta na cewa "rayuwar ki"? Jinjina kai Amirah ta yi ta na cewa. "Eh rayuwa ta ko har yanzu ba ki gane ba tun d'azu dana nuna miki photo na da Aliyu"? Shiru Zainab tai domin kanta ya gama kullewa ta rasa abun da Amirah ta ke nufi ganin haka ya sa Amirah yin murmushi ta na cewa "ko har yanzu ba ki fahimta bane bari na sake nuna mi ki dalilin zuwa na gurinki da kuma abin da za mu yi magana a akan sa" sake kunna wayar ta yi ta na juyo mata da ita yadda za ta gani sosai ta ce "ga abin da ya kawo ni gurin ki" kallon secreen d'in wayar ta yi taga photon Aliyu ne wanda ya ke shi kad'ai da kayan dai da bata son ganin sa da su wato 3Quarter ba'ki sai farar singilet ya na zaune akan kujera da wata flower a kusa da shi tsabar takaici Zainab ba ta san lokacin da ta ja tsuka ba tana kau da kai fuskar ta a had'e ta ce "wai ke me ye haka ne"?. Sauke wayar Amirah ta yi ta na kallon ta, ta ce "fatan kin san waye wannan da matsayin sa kin san ya fi 'karfin d'iyar talaka irin ki dan haka na zo na miki gargad'i a kan sa ne ki fita hanyar sa domin shi d'in da ki ke gani ya kasance masoyi na ne ni kad'ai zai aura mu yi rayuwa tare ba zan ta'ba had'a kishi da kowacce yarinya ba duk matsayin ta balle kuma 'yar talaka irin ki" wani razanan nan kallo Zainab ta yi mata ran ta a mugun bace jin zata raina mata hankali a gidan uban wa take son Aliyu waye ya fad'a mata har zata zo tana mata ihu Allah ya sauwake ta rasa wa za ta aura sai Aliyu tabd'ijan tashin hankali ai gara ta zauna haka babu aure har abada.................... "Tambayar ki fa nake kin yi shiru ki bani amsar da nake son ji" zuciyar Zainab na turiri ta ja tsaki ta na cewa "ba ni da lokacin amsa

Chapter 31 of 34