saka su kai waya da Afifah.
Sai ranar asabar da safe sakamakon za ta je islamiyya ta yi wanka da safe ta shirya har ta d'aura nikaf d'in ta ta d'age ta d'auka agogon da Sameer ya bata ta zuba masa ido ji take kamar ta saka kamar kuma kar ta saka mayarwa ta yi ta aje tana kallon sa tare da sauke ajiyar zuciya ta saka hannu a hankali ta sake d'auko sa ta fitar da shi daga cikin kwalin da yake ta d'aura a hannun ta na dama yayi mata kyau sosai kuma ya amshi farar fatar ta sakamakon Brown ne d'aukar jakar ta tayi ta fita.
Da ta je wucewa kamar ta shiga gidan su Afifah ta gani idan bata tafi ba su tafi tare sai kuma ta fasa ta wuce tana shiga gate d'in islamiyyar ta hango ta alamar ita ma bata dad'e da zuwa ba domin jakarta na hannun ta ko aji bata shiga ganin Zainab d'in yasa tace "Aunty Zee-Zee ashe kina tafe yanzu na ke tambayar Rasheedat da Zakiyyah 'yan matan gidan ku ai suka ce min kina gida"?.
"Eh ina gida sun zo kenan"?.
"Uhm har sun wuce ajin su tun d'azu".
"Ya Sayyidi fa ya zo ne"?.
"Ban sani ba wallahi tun da nima yanzu na shigo ko ajin ban shiga ba".
"Tom mu je ajin" wucewa su kai ta fara yin d'orin surar da yake sakamakon ita kad'ai ce ta ke d'aukar ajin sai 'karfe d'aya su ka tashi Afifah dake tsaye tana jiran Zainab ta gama had'e abubuwan ta su tafi ita kuma ta na du'ke tana tattare littafan karaf idon Afifah ya sau'ka akan agogon da ta kai wa Sameer zaro ido ta yi tana kallon Zainab wacce ta d'ago za su tafi ta ce.
"Lahhhh Aunty Zee-Zee wannan agogon ke Yaya Sameer ya barwa dama"? Ta fad'a tana ri'ko hannun Zainab d'in ta d'an shafa shi cike da sha'awa kallon ta Zainab ta yi da alamar tambaya tace "ta ya ki ka san Yaya Sameer ne ya ba ni"? Murmushi Afifah tai tana sakar mata hannu bayan ta d'auki jakar sun fita daga islamiyyar tace.
"Saboda nice na kai masa shi a cikin kwalin sa shi ya sa na fad'a" da mamaki Zainab ta kalli Afifan wacce ita ma take kallon ta tace "ke kuma"?.
"Eh man ni ce na kai masa wallahi ina son agogon nan har na d'auka nawa ne kawai ina ta murna daga baya murnan ta koma ciki aka ce na tashi na kai masa" a razane Zainab ta sake cewa "amma waye ya baki ki kai masa"? D'an murmushi Afifah ta yi ba tare data duba yanayin rud'anin da Zainab d'in ta shiga ba tace.
"Humm Yaya discipline ne ya aiko su guda biyu tun daga can inda yake d'aya ya baiwa wata Amirah 'yar gidan abokin Daddyn mu wannan d'in kuma na d'auka nawa ne saboda tun kafin ya yo aiken ni yace a baiwa idan an kawo ina ta murna kawai ina zaune nayi ready zan bud'e ya kira ni a waya yace na kaiwa Yaya Sameer yana chemist ashe rabon ki ne ke Yaya Sameer zai barwa ai dama nace na mata ne shima sai dai yayi kyauta dashi" shiru Zainab tai gaban ta na faduwa a ranta tace.
"Hakan yana nufin Aliyu ne ya aikowa Yaya Sameer kenan ya ce a bani kar fa ace shine yake min duk wadannan abubuwan ba dai shine yake so na ba"? Jin abinda zuciyar ta tace yasa a razane ta girgiza kai tana kallon Afifah wacce hankalinta yake kan wata 'kawarsu da ta biyo bayan su suka taho tare iya su kad'ai su ke magana amma ban da ita da take tafiya tana had'a hanya da'kyar ta yiwa Afifah sallama lokacin ta wuce gida ita kuma ta mi'ke kai tsaye chemist d'in Sameer ta wuce gabadaya fuskar ta a 6ace ya yi mamakin ganin ta a haka domin ko kad'an bai kawo a ran sa maganar agogo za ta yi masa ba shi ya sa yace.
"Zainab lafiya akwai matsala ne na gan ki a haka ba daga islamiyya ki ke ba"? Kai ta d'aga ta na ciro masa agogon da yake d'aure a hannun ta tace "Yaya Sameer waye ya baka agogon nan ka ba ni"? Bin agogon ya yi da kallo kafin ya mayar da hankalin sa kan ta yana cewa.
"Me yasa ki ka tambaya kuma bayan abu ya wuce"?.
"Saboda ina son sani dan Allah ka ji Yaya Sameer ni a guna bai wuce ba ka fad'a min ko na samu kwanciyar hankali"? Kar6ar agogon ya yi yana bud'e zip d'in jakar ta ya saka a ciki ya na cewa "kar ki damu za ki sani amma ba yanzu ba sai lokacin daya d'iba ya cika shi da kansa zai bayyana miki kansa ki gan shi nan ba da dad'ewa ba ya na tafe kin ji ko"? ya fad'a yana harhad'owa wanda ta samu a zaune magani kallon sa take da idonta wanda suke gani dishi-dishi gabadaya kan ta juyawa ya ke ta rasa me ya ke mata dad'i za ta samu kwanciyar hankali ne kawai idan Sameer ya fad'a mata wanda ya bata wannan agogon .
Saida ya baiwa mutumin magungunan ya yi masa allura ya tafi sannan ya kalli Zainab ya na murmushi zai yi magana ta girgiza kai tana cewa "Yaya Sameer Aliyu ne ya baka yace ka ba ni"? Yayi mamaki da yaji ta kama sunan Aliyu lokaci guda waye ya fad'a mata fargaba yaji ta kama shi amma dan kar ya sake d'aga mata hankali akan yadda ta ke ciki sai ya dake yana 'kure ta da kallo yana d'auke gira yace.
"Wanne Aliyun ki ka fad'a"? Muryar Zainab har rawa take da'kyar ta ce "Aliyu Yayan Afifah" huci ya fitar ya na sake duban ta yana cewa "
"Waye ya fad'a miki"? Kai ta girgiza ta na cewa "ba kowa bane ya fad'a min ganin sa Afifan tayi a hannu na d'azu na je islamiyya da shi ina tattare littafai tace Aliyu ne ya aiko su guda biyu daga inda yake d'aya ya baiwa 'yar abokin baban su d'ayan yace a kawo maka haka ne"? Jin ta kamo magana daidai ya san babu ta yadda za'ai ya kawo mata wata hujja shi ya sa yace.
"Eh haka ne abin da ta fad'a mi ki" wata irin bugawa zuciyar Zainab ta yi kan ta ya d'auki ciwon damuwa lokaci guda ta nemi dukkan nutsuwa da jarumtar ta ta rasa runtse ido ta yi ta na son hawa hawayen daya taru mata a ido fitowa ta ce.
"Kenan Yaya Sameer Aliyu Yayan Afifah shi ne abokin naka da ya ke so na"? Shiru yayi bai bata amsa mata jin bai yi magana ba ya sa ta bud'e ido tana kallon sa ta ce "Aliyu shi ne ya ke min duk wadannan abubuwan"? Nan ma shiru ya yi bai bata amsa ba sake dafe kanta ta yi jin ta ko'ina ciwo ya ke mata addu'a ta fara karantawa a cikin ranta tana wannan hali ta ji muryar Sameer ya ce.
"Zainab kar ki rud'a kan ki akan haka kar kisa cewa Aliyu ne ya ke miki duk abinda na ke baki bana so ki fitar da wannan zancen har wani yaji zaki jawowa kan ki matsala a gidan nan ki na zaune lafiya wallahi iya bakin mutune ma ya ishe ki ke ma sheda ce".
"Kenan hakan ya nuna da gasken shi ne ya ba ni"? Kai ya jinjina yana cewa.
"Zainab ki na ji....................
ZUCIYAR ALIYU CE
@YUSRAH MUSA DUTSE
PAGE 37
Katse shi ta yi "Yaya Sameer idan shi ne ka fad'a min na daina tunani ina wahalar da kai na" ganin da yai ba za ta bar zancen ba yasa ya had'e rai yana cewa "Zainab kin san ba na son irin wadannan abubuwan ko na fad'a miki abin da ya kamata kin kasa ganewa idan kuma na baki number sa ne sai ki kira shi ki tambaye shi da kan ki kiji idan shine ya baki ma zai baki amsa tunda naga kamar haka kike so ko"? Kaita girgiza a damuwance tace.
"A'a a'a ba sai ka bani ba abun ne ya d'aga min hankali akan me Aliyu zaice yana so na shi ba sa'an aure na bane".
"Saboda me"?.
"Saboda ya fi 'karfi na ni y'ar talaka ce shi kuma fa d'an minister guda bayan haka bamu kasance mutane irin su ba kai ma ka sani Yaya Sameer".
"Zainab so ba ruwan sa da duk wadannan abubuwan da kika lissafo sannan so yana da abun mamaki kuma shi ne zai kai ki inda baki ta'ba tunanin zaki je ba a rayuwar ki kamar dai hakan babu yadda zaki yi idan Ubangiji ya 'kaddara miki cewa shi ne mijin naki" ya na rufe baki a rud'e ta fara girgiza kai tana cewa "innalillahi wa inna ilaihi raji'un wacce irin makauniyar 'kaddara ce wannan ta same ni abin da ban ta'ba kawowa a raina ba shi ya same ni Yaya Sameer bazan saka hakan a rai na ba balle ya dame ni indai akan Aliyu ne".
"Me ya sa Zainab""?.
"Saboda d'an mai kud'i sai 'yar mai kud'i haka nima ina matsayin 'yar talaka ya barni na auri d'an talaka daidai da ni ba zan kai kaina inda Allah bai kai ni ba zan tsaya iya matsayi na ni ba zan auri Aliyu ba" tana fad'in haka ta juya ta fita daga chemist d'in murmushi Sameer yayi bayan wucewar ta ya girgiza kai duk da bai so tasan cewa Aliyu ne ya bata wannan agogon ba kwata-kwata sha'afa yayi da ya san zata saka har Afifah ta gani da ya barshi a gurin sa daga baya idan tasan Aliyun ne yake son ta sai ya d'auka ya bata sai dai mai faruwa ta riga ta faru yanzu kuma za'a shiga sabon babin abubuwan tunda har ta fara zargin Aliyu ne yake son ta komai zai ba ta da Aliyun za ta danganta shi ta daina zargin wani.
Saboda Zaid ya san in dai Hajiya ta ji labarin ya had'o kayan lefe za ta ce babu in da za'a fita dashi sai dai ya auri Zainab shi ya sa su ka bari saida dare Asiya ta saka su ka fita da shi daga gidan aka kai gidan wata aminiyar ta washe gari da safe sai ta saka Adama da Mairo su je su had'u a gidan ta a kai lefen kawai idan ta ji an kai duk tsiya ai ba za tace a dawo da su ko aje a kar6o ba.
Amma me a garin fita da shi Rasheedat ta na waje tare da saurayin ta kuma ta ga lokacin da Asiya ta tsayar da me Napep ta shigar da akwatunan guda uku ta shiga su ka wuce kai ta jinjina bayan sun gama maganar da za su yi sun yi sallama da sauri ta fad'a gida kai tsaye ta wuce 'kofar Hajiya cike da gulma ta yi sa'a kuwa iya Hajiyan ce ita kad'ai a waje ta shimfid'a 'katuwar tabarma tana zaune cire takalman ta ta yi tana zama tace "Hajiya albishirin ki"? Kallon ta Hajiya ta yi tana cewa "ba na son yawon munafirci fa kema kar ki zo ki fad'a min irin abin da Haule ta fad'a ran nan ki sa na fita a banza".
"A'a Hajiya ba wannan ba ne wani abu na gano miki yanzu".
"Me ya faru"? Cire hijab Rasheedat ta yi tana cewa "ki ce min goro mana sai na fad'a miki"?.
"Ke ba na son shashanci wai me ya faru ko munafirci na ki ka ji tsinannun matan gidan nan su na yi".
"A'a gagarumin abu na gano miki wanda yafi gulmar ki wai kin san Yaya Zaid ya had'o kayan kuwa"?.
"A'a ta ya zan sani dama ya had'a ba su zo sun fad'a min ba saboda 'yan ba'kin ciki ne gado ba'kin hali Asiya ce ko"? Dariya Rasheedat ta yi tana cewa "au nan d'in jira ki ke su zo su fad'a miki sun gama had'awa? Tabd'ijan ai kuwa gara ki daina saka rai indai ba bayan auren zaki je gidan nasa matar tasa ta nuna miki kayan ba" wani kala Hajiya tai tana cewa.
"Ban gane ba me ki ke nufi"?.
"Bari na fad'a miki gaskiya Hajiya domin ko kowa zai ci amanar ki ban da ni maganar Allah yanzun nan na ga Umman Yaya Zaid ta fita da akwatuna guda uku daga gidan nan ta tare me Napep ta shiga ban san inda za ta kai su ba" a zabure Hajiya ta dafe 'kirji ta na zaro ido tace "ke 'yar nan da gaske ki ke yi kuwa"?.
"Wallahi Hajiya da gaske na ke da idanu na na gan ta lokacin da ta hau Napep d'in" kai Hajiya ta jinjina tana cewa "wato akwatin Zaidu za su kai wani gurin ba tare da na sani ba ko"?.
"K'warai Hajiya ni ganau ce ba jiyau ba alamu ya nuna ba su mai da ke komai ba baki da amfani tun da da sauran ran ki ma sun daina saka ki a cikin al'amarin su balle kuma nan gaba so su ke ki mutu ma na sani".
"Kan bala'i ai kuwa sai nace uban duk shegen dana samu da goyon bayan sa a gidan nan bari Habibun ya dawo sai naci uwar matarsa yau sai ta bar gidan nan sai dai ta yi kwanan Hotoro tun da mitsiyaciya ce" jin abinda ta ce ta had'o abun har da Habibu kuma in dai ya san ita ta had'a bomb d'in uban ta zai ci shi ya sa cewa "amma fa Hajiya kar kice nice na fad'a miki" a masife Hajiya tace .
"Saboda me"?.
"Saboda za su ji haushi na".
"Na buge uban wanda yaji haushin naki dan uban su tashi ki raka ni 'kofar ta ku kafin Habibun ya dawo ya sai naci mutuncin duk wanda na samu da hannunsa a cikin lamarin tashi mu je"...................
ZUCIYAR ALIYU CE
@YUSRAH YMA
PAGE 38
Gyara zama Rasheedat ta yi tana cewa "ni dai gaskiya Hajiya ba zan je ba haka kawai ba za a gan mu tare ki jawo min duka a gurin baban mu ba".
"Yadda ya ban haushin nan ya dake ki ai sai na tsine masa ta so mu je".
"A'a Hajiya ki zauna bari Zakiyyah ta shigo sai mu raka ki mu biyu kin ji"?.
"Ba na so idan ba za ki raka ni ke kad'ai ba ki barshi bari na je" ganin ta mi'ke tana shirin saka takalmi ya da hankali a tashe Rasheedat ta ce "kin ga Hajiya ki zauna bari na je na gano miki idan abban namu ya dawo sai na zo na fad'a miki ki je" jin abinda ta ce yasa Hajiya fasa fita amma ba ta zauna ba tace "shi ke nan dubo min" da sauri Rasheedat ta mi'ke saboda tana son fitar da kan ta ta d'auki hijab ta maida ta saka takalmi zata fita Hajiya ta ce "kuma kar ki dad'e kiyi sauri ki dawo ki fad'a min dan a wuya na ke" fita Rasheedat ta yi amma da ta je 'kofar ta su kasa shiga ta yi tana tsaye ta bayan ta taji an ce.
"Waye wannan"? A firgice ta juya ganin baban su ya sa ta matsa gefe tana cewa "sannu Baba" kallon ta yayi yana cewa "yauwa tsaiwar me ki ke anan"? Cike da rashin gaskiya ta ce "uhm uhm am wannan da.dama wai Hajiya ce tace na zo na kira ka" da mamki ya ce "Hajiya kuma? Me ya faru"? Kai ta girgiza tana yin 'kasa da kai gani ta ke kamar zai gane da'kyar ta ce.
"Ni ma ban sani ba kawai cewa ta yi na kira ka" juyawa ya yi yana nufar 'kofar Hajiya d'in ya bar Rasheedat a gurin a tsaye wacce tsoro ya hana ta koma ta raka6e ta ji me Hajiya za ta ce masa kuma ta kasa shiga 'kofar ta su saboda gudun kar sai ta shiga d'aki ta je Hajiyan ta fad'a masa ita ta kai gulmar ya shigo ya dake ta ci gaba ta yi da tsaiwa a gurin ta na jiran ta ga a yadda zai fito ta na tsaye ta ga Asiya ta dawo daga kai akwatunan ta shiga 'kofar ta su kai ta jinjina tana sake sabuwar tsaiwa tun da har ta ga ta dawo yanzu sabuwar guguwa za ta tashi.
Habibu kam yana shiga Hajiya ta rufe shi da fad'a "yanzu kai Habibu saboda bankad'a ta same ka ka na kallo Zaidu bazai rufawa 'yar uwarsa asiri ya aure ta ba shi ne da nasa a had'o akwati ku kai taro ba tare dana sani ba kuka d'auke kuka kayi gidan wadancan budurwar tasa ko"? Da mamaki Habibu ya ce "Hajiya wa ye ya fad'a miki"?.
"Au waye ya fad'a min ka ke tambaya ba abinda na ce ayi zakai ba? To bari ka ji ba sabuwar 'kofa ba ko tsohuwar 'kofa wancan budurwar ta ke ku je ku kar6o kayan ku dawo da shi" shiru Habibu ya yi cikin rashin sanin abun yi ya sani yanzu muddin ya fad'i wani abu in dai ba batun da Hajiya ta ke so bane shi za ta d'orawa laifin komai.........
"Wai ina magana ka yi shi ko ba ka ji abin da na ce ba"? Ya ji Hajiyan ta sake jefo masa tambaya kai ya girgiza ya na cewa "shikenan Hajiya ba damuwa in sha Allahu zan yi masa magana za'a kar6o" ya na rufe baki tace "idan ya'ki kar6owa ma sai ya had'o wani ya auri Zainab ko zai mutu na gama yanke magana tashi ka bani guri".
"Ki yi ha'kuri Hajiya".
"Zan ha'kura ne kawai idan ka saka d'an ka ya yi min abin da na ke so" jin abinda ta ke sake maimaitawa ya san indai ba Zain ne ya auri ba bazai ta'ba hutawa ba kuma kome zai ce mata bazai fita daga zargi ba fita yayi ya koma 'kofar sa a d'aki ya samu Asiya shi ya sa ya zauna yayi mata bayanin yadda su kai da Hajiya su kai da Hajiya sannan ya tambaye ta duk inda ta kai akwatunan ta dawo da su kawai Zain ya ha'kura da wancan yarinyar ya auri Zainab d'in nan komai ya wuce.
Kai Asiya ta girgiza ta na cewa "yanzu tsakani da Allah ba za ka iya tausar Hajiya ta ha'kura da batun zuwa a kar6o kayan nan ba wacce irin rayuwa ce wannan"?.
"To ya zanyi Hajiya ba za ta ta'ba ha'kura da batun nan ba tun da ta saka a ran ta" baki Asiya ta ta'be tana cewa "an riga an kai kayan fa ta ya za'a koma a kar6o"?.
"To me ya sa ku ka bayar da kayan aka kai ba tare da kun sanar min ba hakan kun yi daidai kenan"?.
"Ka yi ha'kuri ba dan na 6ata maka rai ba ne saboda gudun fad'an Hajiya ne ya sa nayi haka kuma gashi mun gudu ba mu tsira ba ba yadda za'ai mu saka a koma a kar6o kayan nan".
"Ki na ji Asiya ni fa baza ku jawo min matsala ba indai batu akan Hajiya ne ban san yadda zan yi da ita ba" ganin kamar goyon bayan Hajiyan ya ke akan abin da ta ke so yasa Asiya cewa "da yadda zakai man rayuwa ba'a dole shi fa Zaidu yace baya son had'in auren gida ka ga kuwa ai abu ba mai yuwa ba ne tun da shi zai zauna da ita ba mu ba kuma yace ba ya so" numfashi Habibu ya sauke gabadaya sun saka shi a hau duk gurin wanda ya je daga Hajiyan har Asiya kowa murd'add'an kan sa ne kallon yadda take ke huci ya yi yana cewa.
"Yanzu ya ku ke so ayi ke da Zaidun"? Gyara zama Asiya ta yi tana cewa "kawai yanzu abu mai sauki zuwa za ka yi ka fad'awa Hajiya gaskiyar abin da Zaidu ya ce shi bazai auri Zainab ba wannan shi ne magana" kallon mamaki ya mata ya na cewa "me ne kin san abin da ki ke fad'a kuwa ni ne zan tunkari Hajiya da wannan maganar so ki ke ta tsine min"?.
"A'a ni ba haka na ke nufi ba amma.................
"Amma me? Kin ga Asiya idan ke bakya gudun 6acin ran Hajiya ni ina gudun sa saboda mahaifiya ta ce idan ta min baki zai kama ni dan haka ba ruwa na shawara ta rage ta ku idan Zaidu ya shigo ko da safe ne ki fad'a masa sa'ko daga Hajiya ya sake sabon lefe na auren Zainab ko ku je ku kar6o wancan da ku ka kai idan kun 'ki zan yi mata bayani domin na fitar da kai na" yana fad'in haka ya mi'ke ya fita daga d'akin ya tafi na sa baki Asiya ta ta'be bayan fitar sa tace.
"Wallahi tallahi na rantse da Allah ba lefen da zai sake had'owa tsinke ba zai 'kara siya ba ban ga ta yadda za'ai na amince ya auri Zainab ba tun da ba ya sonta baza'a takura masa ba ai ba shi kad'ai ne namiji a gidan ba ni na goyi bayan sa ko da Hajiya zata saka a sake ni sai dai a sake ni d'in akan na bari Zaid ya auri Zainab....................
ZUCIYAR ALIYU CE
🖋️J♣W♣A🖋️
@YMA YUSRAH DUTSE
PAGE 39
Zaid kam bai shigo 'kofar su a daren ba sai washe gari da safe ya shigo gaisar da Asiya ta tsayar da shi ta ke maimaita masa yadda su kai jiya da Habibu akan kayan lefen da Hajiya ta samu labarin an had'o shi ya sa tun daren jiya ta d'ebe akwatunan daga gidan ta kai gidan aminiyar ta.
Jin sa'kon da Hajiya ta bayar a fad'a masa ya sa yace "wallahi Mama babu inda za'a je a kar6o wani akwatuna na riga da na bayar a kayi kawai tsabar zubar da girma sai ku koma ku kar6o wai me yasa Hajiya ta ke min haka ne ba wanda ta takurawa a gidan nan sama da ni kowa an bar maganar auren da zai yi amma ni ta dage sai na auri Zainab wallahi Allah ba zan auri yarinyar nan ba".
"Kai kar ma ka 6ata bakin ka nima ina goyon bayan ka kuma ko a gaban Hajiyan ne ta kira ka kar kaji wani tsoro ko shakka ka fad'a mata cewa kai baza ka auri Zainab ba baka son ta mu gani me zata ce maka duk tsiya ai ba za ta kore ka daga gidan ba dan na ga gadarar ta kenan da an yi magana za ta ambaci gida kamar ita ba za ta mutu ta bar shi ba ko me za tace maka kar kayi shiru ka mayar mata da martani".
"Balle ma me zata ce duk abin da zata fad'a ina daidai da ita".
"Yauwa Zain na san idan ka yi kmata 'karyar baka da kud'in da zaka sake yin sabon lefe zata iya cewa kawai ka bada sadaki a d'aura muku ba sai ka yi mata lefen ba idan ka je ka fad'a mata abin da yake ran ka kai Zainab d'in ce ba ta yi maka ba idan ka 'ki kana kallo ko Abban ku sai ta saka ya biya maka sadaki an aura".
"Kai haba wallahi fa bazan aure ta ba tunda na rantse akan hakan ko tsautsayi yasa an je wajen aurin aure na naji an sake aura min ita wallahi ina dawowa gida zan rubuta mata takarda saki uku sai dai na bar gidan nan akan haka".
"Allah ma ya sauwake akan wata baza ka je ko'ina ba kana nan zama diss ba yadda za'ai da kai wallahi ka zama ciwon ido zama da kai sai ha'kuri nan gani nan bari d'umamen mayya" mi'kewa Zain ya yi yana cewa "har na ji rai na ya 6aci iya wannan maganar da mu ke bari na je gurin Hajiyan yanzu" kallon sa Asiya ta yi tana cewa.
"Me za ka je fad'a mata"?.
"Zan fito fili na fad'a cewa ba zan ta'ba auren Zainab ba har abada koda ta rasa mijin aure ne garama ta daina min tallar ta saboda ba na so kuma ba zan yi abinda zai takurawa rayuwa ta ba ina matashi wannan tsohuwar ba za ta d'ora min ciwon zuciya da hawan jini
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 34