Share this page
ta tace "Habibu ashe har yanzu baku fi 'karfin 'ya'yan ku ba ace kamar ni Zaidu d'azu zai ciwa mutunci akan nace ya auri Zainab yana fad'a min wata banzar magana wai akwai wacce yake so 'yar sabuwar 'kofa ce"? Jin abinda tace yasa ran Habibu ya soma 6ata ya gaji da maimaita wannan maganar shiyasa yace. "Hajiya dan Allah tunda duk yaran nan basa son za6in da kikai musu ki barsu kowa ya za6o da kansa a gani na hakan zai fi zaman lafiya dan wallahi idan kika matsa akai auren ba bazai yi 'karko ba babu jin dad'i kullum ana cikin sasanto da rabiyar fad'a ne" kai Hajiya ta jinjina tana kallon sa ya d'auka ta gamsu da maganar da yayi mata ne sai kuma yaji tace. "Habibu kasan abinda kake fad'a kuwa na riga na yanke maganar auren nasu yanzu kuma ka zo min da batun wai wani Zaidu yana da budurwa kai ma abinda zaka ce min kenan baza kuyi abinda nace ba"?. "Ba haka bane Hajiya su fa yaran zamani ne dan Allah ki barsu kowa ya samo matar aure kar ki matsa ayi had'in nan za'a samu matsala ba karama ba gaba ce abun ji muddin hakan da faru sai anyi dana sani akan gagarumar matsalar da zata faru a gaba". "Matsala daga wajen ka kenan tunda naga alamar kaine baka so da ace ka tilasta masa ka nuna 6acin ranka ya isa ya tsalle maganar kane shi d'in banza amma kaima ka nuna baka bu'katar abinda nace shiyasa duk sauran ma suka juya min baya". "Ba haka bane Hajiya anan ina iya bakin kokari na duk dan a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin mu dake da kuma 'ya'yan mu kamar yadda muke a baya amma indai kika matsa sai anyi auren nan wallahi ba karamin ya'ki da tashin hankali za'ai ba bama ga yaran ba harma da iyayen su mata tunda ba so suke ba kina kallo ranar da kikai maganar ba wacce ta yarda" yana rufe baki Hajiya tace. "Duk tsinanniyar da bata so ku saketa ta bar gidan saita koma gidan su taje can tayi isar ta amma ba'a nan ba indai ina raye a wannan gidan ba shegiyar da zatai mulki" murmushin fitinar Hajiya Habibu ya saki ganin bata rasa abun fad'a ko za'a kwana ana zance yace "yanzu dai Hajiya me za'ai"?. "Me za'ai kake tambaya ta Habibu me nake so ayi kuwa bayan wanda na fad'a ko Zaidu baya so sai ya auri Zainab kana kallo yadda suka bar yarinya ta lalace wai itace harda koyarwa ga wani sabon salon 'karya da suka d'auko har wata makarantar boko take zuwa labari yazo min wayar hannunta ma ta dubu d'ari biyu da hamsin ce uban waya siya mata ta kafe a gida ta kama sana'a itace had'a man shampoo da baseline itace yin gireba tuwon madara tsami gaye gullisuwa da iloka tana bi tana rabawa masu shago suna mata balance d'in kud'in ta kamar wata ma'aikaciyar gwamnati ta manta da maganar aure tsabar shashanci kuma shi Abdullahi d'in ya sani amma saboda tana d'ora masa jari idan ya karye shiyasa baya so ta bar gidan sai anyi magana yace aure lokaci ne zan nuna masa cewa nata lokacin yayi ba tare daya sani ba zanje nasa a d'aura mata aure da duk wanda naga dama saiya dawo daga gurin sana'ar sa ya tarar anyi mata rakiya idan nayi haka zan gani zai zo ya hauni da fad'a ne ko kuma zai bita gidan auren nata yace a sake ta ne". "A'a bazai yi haka ba amma kema dan Allah Hajiya na ro'ke ki kar kiyi haka". "Kai karka dame ni sai na yi hakan idan kuma kana da ikon hana hakan sai na ji"?. "A'a mu umarnin ki muke bi duk abinda kike ce shi za'ayi ko muna so ko bama so" a she'ke Hajiya tace "a hakan ko duk kuna bin umarnin nawa kuka kasa saka y'ay'an ku su bi magana ta"?. "Ki yi ha'kuri Hajiya zan zauna da su za mu tattauna duk abinda muka yanke zan zo na fad'a miki kin ji"?. "Shikenan zan gani ai idan ma 'karya ka ke yi" kai Habibu ya girgiza yana mi'kewa yace "saida safe za mu yi magana da su ranar weekend" Hajiya batai niyyar magana ba saida taji abinda yace da sauri ta kalle shi tana cewa "yanzu kai ranar weekend zakai magana dasu har wani lokaci kake sakawa sai kace gwamna? To ni a gobe nake son kuyi meeting d'in ka gane"? Kaiya d'aga yana cewa "to shikenan Hajiya za mu yi yadda ki ka ce" daga haka bai sake cewa komai ba ita ma Hajiyan haka ya juya ya fita daga gurin ta kofar baban su Zainab ya tsaya yana sallama. "Assalam-alaikum Abdullahi ka na ciki ne"? Abba dake d'akin sa a zaune jin sallamar babban yayan na su yasa ya mi'ke yana d'auke labule ya le'ko ya na cewa "eh ina nan Yaya bismilllah 'karaso" ya fad'a ya na shirin kokawa yaji Habibu ya ce "a'a basai na shigo ba fito magana za mu yi" jin abinda ya ce yasa Abba baro kofar d'akin yana d'aukar takalman sa ya saka ya fito a tsaye ya same shi a gurin a kidi'ime ya ce. "Allah ya sa dai lafiya Yaya na ga kamar fuskar ka da damuwa"?. "Eh to lafiya ba lafiya ba dama Hajiya ce ta kira ni d'azu tana sake jaddada min aure tsakanin Zaidu da Zainab ko d'aya daga cikin su ba ya so sai anyi har ta na ikrarin laifin mu ne da ace mu na bin umarnin ta su ma ba za su juya ma ta baya ba yanzu ya kake ganin za'a yi"? Shiru Abba yayi ya na tunanin ta yadda zata su 6ullowa al'amarin can ya ce "to Ina ganin kawai abinda za'ai shi ne ka samu Zaidu d'in ka 'kara fad'a masa ni ma zan yi magana da Zainab kamar hakan idan mu kayi shi ne mafita daga mu har yaran a gurin Hajiya idan kuwa aka samu sa6ani dama zata ce ba mu so ba taya yaran za su so amma ya ka ce"? Jinjina kai Habibu ya yi yana cewa "tabbas abunda ya kamata ayi kenan kafin mu yanke hukunci shikenan Allah ya rufa asiri dama kiran da na yi maka kenan gara na fad'a ma ka tun yau kafin gobe da safe ka je gurin Hajiya ta ji labarin ban fad'a ma ka ba ta tsiyata ni" yana rufe baki su ka saki dariya dukkannin su saboda tuna yadda Hajiya ta sako su a gaba da fitina iri-iri ta na caza mu su kai Abba yace. "Ba damuwa Allah ya tashe mu lafiya" "Amin" Habibu yace ya na juyawa zuwa kofar sa shi kuma Abba ya koma d'akin sa har ya kwanta ya sake tashi zaune ya yi shiru ya na tunani tabbas ya na so yaga Zainab a d'akin mijin ta amma irin wannan auren had'in ba tunda ba su suke son juna ba akwai matsala koda Hajiya za ta ce ya goyi da bayan 'yar sa indai Zainab ba ta son auren Zain ba zai yarda ta takura kan ta ba saboda ya na sone tayi rayuwar aure mai cike da farin ciki a gidan auren ta ba rayuwar aure mai cike da 'kunci ba sauke ajiyar zuciya yayi ya na tashi ya sake fita kofar d'akin Zainab ya je ya tsaya yana cewa. "Zainab kin yi barci ne"? Jin muryar Abba yasa ta tashi zaune daga kwancen da ta ke ta na cewa "a'a Baba ido na biyu". "To maza ki zo yanzu d'aki na magana za mu yi" jin abinda yace yasa ta mi'ke tana d'aukar hijab d'in ta tace "to Baba ga ni nan" jin shiru yasa ta fahimci ya koma fita ta yi ko takalmin ta bata d'auka ba ta shiga d'akin nasa da sallama tana dur'kusawa cikin ladabi ta ce. "Ga ni Baba". Kallon ta ya yi zuciyar sa falda tunani yace "amm Zainab dama tambayar ki zanyi ki na da saurayi ne"? Ba tai tunanin abinda zai tambaye ta ba kenan shiyasa a firgice ta d'ago ba shiri ta na kallon sa shi ma yaga yadda ta firgita d'in da yatsa ya nuna mata wata farar kujerar roba dake kusa da ita ya ce "zauna a kan nan saboda kar kafin mu gama zancen 'kafar ki tayi ciwo" jiki a sanyaye ta tashi ta koma kan kujerar ci gaba Abba ya yi. "Ina fatan ba ki yi mamakin wannan tambayar da na yi miki ba saboda kin san da ajiyayyiyar maganar ko"? Kai ta d'aga a hankali ta ce "eh". "Yauwa yanzu kiran da Yaya ya yi min duk akan hakan ne Hajiya ta sake kiran sa ta yi maganar dole sai Zaidu ya aure ki amma ni ban isa na hana Hajiya abinda ta ga dama ba kamar yadda su Yaya ba su da ikon hakan sai abinda ta ce shiyasa na ga ya kamata na kira ki mu tattauna domin wannan al'amari ne mai girma kuma mai cike da sar'ka'kiya da 'kalubale yanzu ki na da wanda ki ke sone ko a'a"?. "Eh da akwai". "A ina ya ke"?. "Malamin islamiyyar mu ne". "To amma ya na zuwa gurin ki ne"?. "Eh ya na zuwa amma sai lokaci zuwa lokaci". "Da gaske da aure ya ke son ki ko kuma kawai zuwa ya ke"? D'an shiru ta yi kamar mai tunani ta rufe ido ta na sakin numfashi ta ce "kwarai da gaske ya ke so na". "Shikenan na fahimta amma duk da haka ba zan fad'awa Hajiya ba sakamakon ta na jin wannan labarin sai mun nemi nutsuwar mu mun rasa domin ta daina bari na huta har sai ta ga kin yi aure kin bar gidan nan ni kuma kullum ina tashi da dare yayin da kowa yake barci na tsaya tsayin daka nayi ta ro'kon ubangiji ya baki miji na gari wanda zai ri'ka ki da kima ya girmama ki kuma ya ji tausayin ki shiyasa ba na so ace Hajiya ta matsa akan auren ki da Zaidu domin tunda ya furta akwai wacce ya ke so kin ga an samu akasi" ya d'an yi shiru ya na kallonta sannan ya ce "shikenan ba komai dama dalilin kiran kenan tashi ki je" mi'kewa ta yi jiki a mace da'kyar ta iya ce masa "saida safe" kai ya d'aga ya na bin ta da kallo yace "Allah ya tashe mu lafiya". Fita ta yi ta koma d'akin ta amma tunanin maganar da su kai da Abba ya hana ta samun sukuni balle ta iya runtsawa sai juyi da ta ke faman yi har lokacin ya fara ja dare yana yi ba ta ji barci yazo mata ba 'karshe tashi ta yi ta fita tayo alwala ta zo ta fara nafila domin ta ro'ki ubangiji ya za6a ma ta abinda yafi alkhairi a rayuwar ta................... 💓ZUCIYAR ALIYU CE💓 @YUSRAH YMA DUTSE PAGE 30 POV AMIRAH Tun da Aliyu ya tafi Amirah ba tai kiran sa ko sau d'aya ba saboda ya 6ata mata rai sosai rashin sanar mata komawar ta sa gashi d'an zuwan da yake su gaisa da mamar ta wannan karon bai zo ba shiyasa ta d'auki niyyar har ya dawo ko shekara d'ari zai yi a can ba za ta ta'ba kiran sa ba dole ta koyi ri'ke mutunci da kimar ta matsayin ta na mace koda ace ita ce take son sa ba shi ne ya ke son ta ba duk inda aka san mace an san ta da kamun kai in dai ba ballagaza bace. Tana kwance a bedroom tana barci safe Aliyu ya yi ta kiran ta kusan kira uku amma ba answer sakamakon barci take sai da 'kanwar ta Nana ta shigo ta ga ana kiran ta 'karasawa ta yi ta duba ganin me kiran yasa ta d'an bubbuga pillow da ta ke kwance a kan sa ta na cewa. "Aunty Amirah Aunty Amirah ki tashi wai har yanzu ba ki tashi daga barci ba sai kiran wayar ki ake yi" juyi Amirah tai cikin muryar barci ta ce "waye ya ke kira na"? Sake kallon secreen d'in wayar Nana ta yi gudun kar ta yi mistake ganin dai Aliyun ne a rubuce yasa ta ce "Aliyu na gani" ta fad'a tana d'ago ma ta wayar zaro ido Amirah tai ta na cewa "Aliyu kuma duba min kira nawa ya yi"? Sake duba secreen d'in ta yi ta na cewa "kira uku ne kuma wannan ba number Nigeria bace" jin abinda ta ce yasa a zabure Amirah ta tashi zaune ta na cewa. "Mi'ko min wayar" mi'ka ma ta tayi jiki na rawa ta kar'ba ganin da gaske Aliyu ne ya yi mata kira uku yasa ta dafe kai ta na cewa "innalillahi wa inna ilaihi raji'un yanzu ba lallai ya d'aga ba idan na kira shi amma bari na gani" gwada danna kiran nasa tayi ta shiga tana ta ringing ba'a d'aga ba dama ba ta jin a ran ta zai d'aga mata kiran har ta katse za ta sake kira ta ga nasa kiran ya shigo abun nema ya samu da sauri ta d'aga tana cewa. "Hello Aliyu barka da safiya" bai amsa mata ba sai tambaya da ya jefo mata "a ina ki ka aje wayar ki ina ta kira ba ki min picking ba"? Jin abinda ya ce yasa ta gyara zama ta na cewa "kayi ha'kuri dan Allah wallahi barci na ke saida Nansy ta shigo sannan ta tashe ni ban san ka na kira ba domin ko ringtone d'in ban ji ba". "Ok dama irin agogon nan da ki ka gani tun mu na Spain a lokacin da ki ka gama karatu kuma zan siya miki na manta ke kuma har mu ka taho baki tuna min ba d'azu na je shopping na gan shi, shi ne na siya miki amma guda biyu ne d'aya na ki d'ayan kuma ki kaiwa Afifah" jin abinda ya ce yasa ta zaro ido tana cewa "dan Allah Aliyu¿ Wow gaskiya na gode sosai wallahi naji dad'i Allah ya saka da alkhairi". "Amin". "Yaushe za ka dawo kenan"?. "Ba yanzu ba bayarwa zan yi a taho muku da shi da akwai wani aboki na d'an Lagos ne zai taho kwanan nan zan ba shi ya taho da su idan ya zo gida daga nan zan bashi number ki da address sai ya baiwa masu mota a taho miki da shi idan ki ka d'auki na ki saiki kaiwa Afifah d'ayan" kaita d'aga tana murmushi cike da jin dad'in yadda ya nuna ma ta kulawa ga abinda ta dad'e ta na so ta ce "Allah ya 'kara arziki na gode Aliyu na gode sosai da kulawar ka gare ni". "Ba godiya tsakanin mu" ya na fad'in haka ta ji wayar tace d'it d'it alamar ya katse kiran sauke numfashi tai tana kallon agogon dake bangon bedroom d'in nata ta ga 'karfe goma da rabi na safe tashi ta yi ta sauka daga gadon ta shiga toilet tai wanka da brush ta fito ta shirya ta fita zuwa parlor ba kowa shiyasa kawai ta wuce dinning ta yi breakfast daga nan ta mi'ke ta d'auko mayafinta ta tafi gidan su Afifah domin ba za ta iya ha'kuri har sai agogon ya zo ba gara tayi mata albishir tun kafin zuwa kyautar ta na shiga kuwa tayi sa'a da yake weekend ne duk su na parlor harda Daddy da sallama ta shiga bakin ta ya'ki rufuwa tsabar farin cikin da ta ke ciki zama ta yi tana gaisar da Daddy ya amsa sannan ta gaida Momy ganin su na gurin yasa ba ta fad'awa Afifan ba ta bari su shiga bedroom kawai wayar ta ce a hannun ta tana chatting har Daddy ya tashi ya bar parlon sai lokacin ta samu damar d'agowa tana kallon Afifah wacce ke gefe d'aya ta na haddar karatu ta ce. "Afifah albishirin ki"¿ Da mamaki Afifah ta d'ago ta na kallon ta tace "albishiri na kuma ni Afifan"¿ kai Amirah ta d'aga da murmushi tace "eh ke Afifan man please ki ce min goro dan Allah wallahi abun dad'i zan fad'a mi ki dalilin zuwa na ma kenan". "Ok goro fad'a min ya akai"¿ Gyara zama Amirah tai ta na cewa "d'azu mu kai waya da Aliyu ya ke fad'a min ya siya ma na wani agogo ni da ke" da alamar tambaya Afifah tace "ban gane ba wanne irin agogo kuma"?. "Agogo dai irin wanda ki ka sani na kwalliya". "Kuma shi Yaya discipline d'in ne ya ce miki har da ni ya siya ko ke ce ki ka fad'a"?. "A'a shi ne ya fad'a min dama tun mu na Spain na ga agogon na ce masa ina so to ya manta bai siya min ba wai sai d'azu ya je shopping ya ganshi shi ne ya siyo su guda biyu ya ce zai baiwa wani abokin sa d'an Lagos ya taho da shi idan yazo daga Lagos d'in zai bashi number ta da address sai a sako a mota a kawo ma na" d'an zaro ido Afifah tai ta na cewa. "Kai da gaske"?. "Da gaske man". Murmushi Afifah tai ta na girgiza kai ta mayar da hankalin ta kan littafin dake hannunta ta na cewa "ni kam jin wannan maganar na yi kamar tatsuniya zan yarda ne kawai idan na ga sa'kon ya zo" tana fad'in haka ta ci gaba da karatun ta kallon ta Amirah ta yi ta na cewa "amma dai kin san Aliyu ba ya 'karya ko ya ta'ba miki alkawari ya sa6a"? Kai Afifah ta girgiza ba tare da ta d'ago ba ta ce "ni na fad'a miki kar ki had'a ni da shi na shiga uku kawai dai mamaki na yi sakamakon jin abinda ki ka ce min" Afifah na rufe baki Elham ta ce. "To idan haka ne me ya sa mu bai had'o da mu ba sai iya Aunty Afifah"? D'an ta'be baki Amirah ta yi tana cewa "wannan kuma shi za ku tambaya ni kam iya sunan ta na ji ya kama". "Ke ma dai Elham da kayan haushi ki ke bayan kin san waye Yaya boss me ye abun cewa bai had'o da mu ba dama za mu had'a kan mu da su ne"? Fati ta yi maganar ta na kallon yadda Amirah ta ke wani kad'a kai ta na yau'ki alamar su ne na gaban goshi a gurin Aliyu su ne masu lokaci da su ya ke ra'ayin sa kai Elham ta jinjina ta na cewa. "Na san da haka amma ya kamata a ri'ka yin abinda 'kuda zai bi". "Kar ki wani d'aga hankalin ki idan ya kawo mu su mun ga kalar sa sai mu fad'awa Daddy mu kuma ya siyo ma na dad'in abun mu na da uba balle mu yi kuka". "Ke Elham dama mu sa'annin ki ne da zaki nemi dole sai an yi miki abinda a kai mana"? Jin abinda Amirah tace yasa Elham kau da kai ba tare da ta amsa ma ta ba domin ta san ba mutunci gare ta ba yanzun nan sai ta kwakkwara ma ta ashar ba kunya ko a gaban Momyn ne balle ba ta nan ta tashi. Ba wanda ya sake magana ma akan hakan har Momy ta fito tare da Husnah su ka fita anguwa ta bar iya su kad'ai mi'kewa Amirah ta yi akan kujerar da ta ke three seater ta saka pillow kujerar ta kwanta ta koma barcin ta............. J.W.A ZUCIYAR ALIYU CE **** YUSRAH ** MUSA **** @YMA DUTSE JIGAWA PAGE 31 Yau Zainab ba da wuri za ta tafi school ba shi yasa ta rage d'inkunan mutane kafin ta tafi sai da akai kiran sallah ta tashi ta yi wanka ta yi sallah ko abinci Asabe ba ta gama had'awa ba da yake Sameer ya siyo mata katon d'in biscuit da lemo wani lokacin da shi ta ke tafiya idan ta dawo ta ci abincin bayan ta gama shiryarwa ta shiga d'akin Umma ta yi ma ta sallama ta fita har za ta wuce 'kofar Hajiya amma sakamakon ta san in ba ta shiga ta gaida ita ba sai ta yiwa Umma shi ya sa kawai ta shiga a waje ta same ta ta shimfid'a sallaya ta zauna akai da radio a gefen ta ta na sauraron labarai 'karasawa ta yi ta dur'kusa har 'kasa ta ce. "Hajiya ina yini"¿ Kallon ta Hajiya ta yi ta kalli school bag d'in ta da littafin dake ri'ke a hannu ta kamar ba ta san inda za ta je ba tace "ina za ki je na gan ki da littafi har da jaka ko D'an Yanan zaki koma"¿ Girgiza kai Zainab ta yi duk da ta san gatse Hajiyan ta yi mata amma sai ta ce "a'a makaranta zan ta fi" humm hali a jikin rai ta na rufe baki Hajiya ta ce. "Yanzu ke Zainab an ya rayuwar da ki ka d'aukarwa kan ki hakan a gare ki daidai ne wannan rayuwar ki ka za6a a ganin ki makaranta tafi aure makarantar da ki ke zuwa ba za ta kankaro mi ki da mutunci ba amma aure fa" shiru Zainab ta yo kan ta a 'kasa ba ta iya cewa komai ba domin ba ta san me za ta ce ba Hajiya ta ci gaba "Fad'a min idan kin gama karatun kuma fa me za ki samu wanne ci gaba zai kawo mi ki ko wata tsiya aka ce miki za ki samu idan kin yi karatun ko kishi kike da su Zaidu to ai su maza ne iyali za su ri'ke ke kuma da zaki auri wani me za ki yi"? Har lokacin Zainab ba ta iya cewa komai ba. "To bari ki ji wallahi tallahi na rantse da Allah idan tsautsayi yasa ki ka d'aukowa mutane abun kunya sai kun bar gidan nan ke da uwar ki ba za ku sa duniya ta zage mu ba tunda baki da aiki sai shige da fice ki na cud'anya cikin samarin banza duk ranar da na ji labarin ciki a tare da ke na lahira sai ya fi ki jin dad'i da kaina zan kira mi ki hukuma su tafi da ke su yanke miki hukuncin kisa domin shi ne ya dace da ke wai wanne irin shashanci ne wannan so kike sai kin zama tsohuwa kin diddige sannan ki auri tsoho ko kuma sai kin yi shekara talatin a gidan nan baki tafi d'akin mijin ki ba fad'a min ko Dan a jinin ku masifar take yayarki Murjah ma kafin ta fidda miji saida mu ka sha wahala kuma ke ma gashi duk hud'ubar Hauwa ce dad'in abun ma Allah ya rufa asiri daga ke ba wani gara da bata hayayyafa sosai da mu ba haba me za'ai da ba'kin gado gadon tsiya irin wannan wallahi gara da yaran da ta haifa duk suka mutu ku biyun da ku kai saura gashi kun zame mana annoba d'aya ta wuce saura ke". Sosai idon Zainab ya cika da hawaye sosai kawai ta yi shiru ta na saurarar Hajiya wacce ita ma daga haka ba ta sake cewa komai ba. "Ba ki gaji da zama a gaban nawa bane ko me tashi ka ban guri idan kin ga dama kar ki yi auren ki ci gaba da karatu har sai kin ga 'karshen biro da takarda 6acewa gani na" mi'kewa Zainab ta yi jikin ta babu 'karfi balle 'kwarin gwiwa ta fita ta na sharar hawaye had'uwa su kai da Sameer ya shigo ganin ta tana kuka yasa ya ce. "Zainab me ya faru lafiya kukan me ki ke"? Kai ta girgiza ba tare da ta yi magana ba sake kallon ta ya yi yana cewa. "Ki fad'a min mana"?. "Ba komai Yaya Sameer ni da Hajiya ne ka ga kuwa wannan sababban abu ne tsakanin mu ba wanda za'a yi tambaya a kan sa bane" tsaki ya ja yana cewa "dama na san sai dai Hajiyan gaskiya wannan tsohuwar ta na da matsala a rayuwa humm yanzu school za ki tafi"?. "Eh". "Ok ba damuwa kar6i" ya fad'a ya na zaro mata dubu d'aya a aljihun shi har za ta yi magana sai kuma ta fasa kawai ta kar6a ta yi masa godiya saboda ya

Chapter 13 of 34