Share this page
amma wa zai iya kallon wannan kayan 'kyan'kyami haka" kai ya jinjina yana d'agowa ya kalle ta ita kuma ta juya ta fita ta bar sashin a wani guri inda wasu kafafun kujeru su ke ta zauna ta na jiran sa kafin ya fito jin ana kiran wayar ta yasa ta fito da ita daga cikin jakar ta ganin Badiyah ce ya sa ta ja tsaki ta na maida wayar ta d'auko ruwa ta bud'e robar shi ma kur6a kad'ai ta yi ta mayar ta d'aure ta d'auki karamin towel ta goge bakin ta tare da kallon agogon da yake hannun ta taga lokacin tashi ma ya yi dafe goshi ta yi tana buso iska daga bakin ta tare da mi'kewa ta fara zaga gurin kafin ya fito ta d'an jima amma har lokacin shiru tunani ta fara yi kodai ba zai fito bane shanya ta ya yi ta na cikin haka ta hango shi sun fito tare da wancan doctor d'in ya mi'ka masa hannu sun gaisa ya koma Shareef kuma ya taho wajen inda ya gano ta numfashi ta sau'ke ta na d'aukar jakar ta, ta nufe shi fara tafiya su kai akan doguwar verandah irin ta asibiti. "Uhum fatan dai lafiya ina jin ki me ya faru"? Dakatawa da tafiyar da take ta yi ta na fuskantar sa sosai ta zuba mi shi ido kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta ce. "Shareef da gaske ne"?. "Da gaske ne me"?. "Da gaske ne aure za ka yi"? Zaro ido ta yi farko da ta ga ya girgiza masa kai ta d'auka ko bai san da zaman wancan littafin ba har ta fara jin sanyi a ran ta sai kuma ta ji ya ce. "Ana aure da wasa ne"?. "Kenan abin da na gani d'azu ba 'karya ba ne"?. "Me ki ka gani"?. "Memo na engagement d'in auren ka da wannan yarinyar". "Wacce yarinya kenan"?. "Kai zan yiwa wannan tambayar tun da ka fi ni sanin ta ai" kai ya jinjina su na ci gaba da tafiya ya ce "ya yi kyau" daga haka bai sake magana ba ita ma shiru ta yi tunani iri-iri sun cika mata zuciya har su ka 'karasa ya rufe office d'in sa sannan su ka je wajen aje motoci tana tsaye ya shiga ya tafi ba maganar da ta sake had'a su kamar ta had'iyi zuciya ta mutu haka take wani irin takaici da d'aci ya na ma ta yawo a ma'kogoro da'kyar ta tafi gurin motar ta ita ma ta shiga ta nufi gida tu'kin ma ba sosai take kula da titi ba hankalin ta duk nema ya ke ya fita daga jikin ta kafin ta je gida zazza'bi ya rufe ta, ta na parking kuwa ko key ba ta zare ba balle ta tsaya d'aukar handbag kawai kofar parlon su ta bud'e ta shiga Mom d'in ta tana zaune ganin a yadda ta shigo tana layi kamar wacce tasha abun maye yasa tasowa da sauri ta na cewa "Subanallahi Baby ke Baby lafiya"? Ba ta iya ba ta amsa ba sakamakon idonta ya gama rufewa ba'ki kawai take gani luuuu hajijiya ta d'ebe ta tayi baya zata fad'i da sauri Hajiya Fatima ta tare ta tana ri'ke ta a jikinta tare da 'kwalla kiran........🖋️ Typing sai gobe in sha Allahu. ZUCIYAR ALIYU CE. ................PAGE 66 "Aminah Aminah ki na ina sauri ki zo" da sauri wata mace ta fito daga wata kofa da kayan aiki a jikinta da alama kitchener ce karasowa tayi tana cewa "gani ranki ya dad'e" a rud'e Hajiya Fatima tace "d'auko min ruwa a fridge yanzu kiyi sauri Baby ce ta ke suma" juyawa tayi ta gudu ta d'auko mata kar6a tayi ta bud'e ta d'an tsiyaya ta shafa mata a fuska ta 'kara shafa mata shiru kamar gawa sai numfashin ta da yake kai komo shi ne kad'ai zai tabbatar maka tana da rai kusan awarsu guda sannan ta sauke nannauyan numfashi amma ba ta bud'e ido ba cikin kulawa Hajiya Fatima ta d'an girgiza ta tana cewa. "Baby Baby bud'e idon ki" a hankali Baby ta ke jin tashin maganar mahaifiyar tata da'kyar ta bud'e idonta da sukai nauyi suka zama ja tana kallon ta kafin ta yun'kura a hankali ta tashi zaune d'aga ta Hajiya Fatima ta yi ta 'karasa shiga da ita parlon ruwan dake gora na hannun ta, ta mi'ka kur6a d'aya tayi ta aje tana dafe kai ido Hajiya Fatima ta zuba mata tana mamakin meya sameta ta fita lafiya 'kalau ta dawo a haka. "Baby ki na lafiya"? Kai ta girgiza numfashin ta na fita da zafi ta ce "Mom kai na ciwo ya ke kamar zai fashe jiki na da zazza'bi na dawo zuciya ta zafi ta ke min" ta fad'a ta na dafe saitin zuciyar ta zaro ido Hajiya Fatima ta yi tana kallon ta ta ce "Subanallahi har da zafin zuciya Baby wai me ya same ki ne nasan dai lafiya kalau ki ka fita daga gidan nan ko wa ya 6ata miki rai fad'a min"? Shiru Baby ta yi hawaye ya na zuba mata da ace yadda take samun komai daga gurin mahaifan ta yadda ba ta san rashi ba ina idan ta sanar musu su yi 'ko'kari su taimake ta kar ta rasa Shareef a rayuwa yardar sa da auren sa kawai yanzu shi ne matsalar ta............... "Wai Baby ba za ki fad'a min abin da ya ke damun ki ba ki na ganin kukan shi ne mafita"? Kai baby ta girgiza ta na cewa "koda na fad'a miki ba ki da maganin matsala ta Mom duk duniya ba wanda zai iya min maganin ta sai Allah". "To ai ke ki na da matsala kuka ba zai kai ki ba tashi za ki yi kije ki yi alwala sai ki yi sallah ki fad'awa Ubangiji damuwar ki zai yaye miki duk wani ba'kin ciki da ki ka tsinci kan ki haba dan Allah kamar bakya zuwa islamiyya ya kamata ki dawo hayyacin ki mana komai yai zafi maganinsa Allah ne ki share hawayen ki, ki tashi ki je kiyi sallah" kai Baby ta d'aga tare da mi'kewa ta shiga part d'in ta shiru Hajiya Fatima ta yi cike da tunanuka iri-iri a ran ta akan abin da ya ke damun Babyn tun da har ta ga ta'ki fad'a mata to fa ba 'karamin abu bane. Ta na nan a zaune har Daddy ya shigo shi ya sa ko numfashi bai gama saukewa ba ta fad'a masa komai ya ce ta kira masa Babyn tashi ta yi ta shiga kamar yadda take tunani haka ta tarar ta a zaune ta zuba uban tagumi da hannu biyu ta yi shiru kai ta girgiza ta na cewa. "Baby". Shiru ba ta amsa mata ba alamar tunanin da take ta yi zurfi 'karasa shiga Hajiya Fatima ta yi ta na d'an girgiza ta ta ce "Baby" a firgice ta d'ago da jan idon ta tana kallon Hajiya Fatima wacce ta ce "wai ke meye haka ne sai kin kashe kan ki yau d'aya mtwwww ki zo Daddyn ki ya dawo ya na son ganin ki" ta na fad'in haka ta juya ta fita ajiyar zuciya Baby ta sau'ke tare da mi'kewa jiki a sanyaye ta fita tun su ka ganta duk su ka zuba mata ido kowa cike da tsantsan mamakin yadda ta mayar da kan ta abar tausayi lokaci guda, zuwa ta yi ta zauna tare da yin 'kasa da kan ta tace "Daddy ina yini"? Kai ya jinjina ya na cewa "lafiya 'kalau daughter me ya same ki ne yau"? Jin tambayar da ya yi mata yasa ta 'kara 'kasa da kan ta ba ta ba shi amsa ba". "Ok ba za ki fad'i abin da ya ke damun ki ba sai na kira miki Hakeem ko"? Jin ya ambaci Hakeem yasa ta girgiza kai da sauri ta na cewa "dan Allah Daddy ka yi ha'kuri". "Na ji amma zan ha'kura ne kawai idan har ki ka fad'a min gaskiyar lamari me ya ke damun ki"? Hawaye ne ya fara zuba mata bakin ta ya'ki bud'uwa balle ta samu damar iya fad'a masa kuka kawai ta fara yi tun ta yin sa a hankali ciki-ciki har ya fito fili daskarar da su ta yi suka saka ta a gaba kamar TV su na kallon ta babu wanda ya ce ta yi shiru a cikin su waya Daddy ya d'aga ta ji zai yi kira cikin kuka ta ce. "Dan Allah Daddy kar ka kira Yaya Hakeem ka bari zan fad'a maka ba ni da lafiya zazza'bi na ke yi"? Ta na rufe baki cikin fad'a Hajiya Fatima "aww zazza'bi zazza'bi ki ka ce shi ne ya ke damun ki wato Baby ba za ki fad'a ma na gaskiya ba ko"? Sosai ta ke kuka Amma taya za ta iya fad'a musu gaskiyar lamari su gane akan namiji ta mayar da kan ta haka, ganin ba daina kukan za ta yi ba ya sa Daddy mi'kewa ya na cewa "tashi mu je". "Ina za ku je Alhaji" 'kofar fita Daddy ya nufa ya na cewa "zan kai ta asibiti ne idan mu ta'ki fad'a mana tun da ba mu kai ba likita zai fad'i duk abin da ke damun na ta" jin abin da ya ce yasa Baby girgiza kai a susuce ta ce "Daddy please let me tell yo................. Tsawar da ya buga mata ya sa ta sake rud'ewa da gudu ta mi'ke tana 'kan'kame Hajiya Fatima cikin tsoro ta sake fashewa da kuka huci Daddy ya fitar ya na nuna ta da yatsa zai yi magana Hajiya Fatima ta yi masa nuni da ido alamar ya yi ha'kuri kar ya ce komai amma duk da haka sai da ya ce. "Ni za ta mayar 'karamin mutum har ina tambayar ta me ke damun ta tayi banza kin san........ "Alhaji please dan Allah shittttt" Hajiya Fatima ta fad'a ta na d'ago da Baby ta goge mata hawayen sannan ta ce "ki je ku tafi" kai Baby ta d'aga cikin tsoro ta kallo Daddy wanda ya ja tsaki ya na juyawa zai fita ya ce "ina jiran ki a mota" bin bayan sa ta yi su ka fita ta d'auka ko a mota zaiyi mata wata tambayar sai kuma ta ji ya share ta har ya kai ta wani private hospital aka duba ta iya dubawa akai mata binkicen tsaf sannan ya ke6e da doctor d'in ya fad'a masa komai mamaki kamar zai kashe Daddy haka ya 'kure Baby da kallo kamar ba zai daina kallon ta ba daga baya ya jinjina kai ya na yiwa Doctor godiya su ka fito su ka dawo gida. Kamar yadda takaici ya kama Daddy a hospital ita ma haka Hajiya Fatima ta ji bayan ya yi mata bayani kallon Baby wacce ta sunkuyar da kai ta yi tana cewa "tabd'ijan anya Baby kina da hankali akan saurayi ki ka d'orawa kan ki hawan jini waye shi a ina ya ke me ya ke da shi wanda ki ka nace a son shi har cuta ta shige ki"? Shiru Baby tai kan ta a 'kasa ta kasa d'agowa ta fuskance su saboda kunyar abinda ta aikata cikin fad'a Hajiya Fatima ta ce "wai ba magana nake miki ba waye shi ko ba ki jini ba"? Rawa muryar Baby ya ke da'kyar ta iya ce wa. "A.a.h.hospital d'in mu ya.ya.ke". "Humm a hospital d'in ku ko? Da kyau kin kyautawa kan ki ai shi ya na can lafiyar sa kalau hankalin sa kwance ke kuma ga ki kin kamu da jinya uban waya fad'a miki ana damuwa da wanda bai damu dakai ba ko tare ki ke da mutum ya nemi fita daga rayuwar ki ke kiyi gaggawar cire shi in da hali ma ki dad'a masa da kud'in mota uwar me zai baki shi wancan yaron me ki ka nema ki ka rasa da har za ki hallaka kan ki a banza shashashar yarinya kawai wannan ai ba ki san ciwon kan ki ba kuma bakya kishin kan ki da ki na son kan ki da arziki ba za ki fara son wanda ba ya son ki ba aikin banza aikin wofi ki ci gaba kar ki fasa son shi ki gani idan riba za ki samu ke idan ba tsabar gidahumanci ba ke fa mace amma ki ka kasa ri'ke martabar ki to ga Daddyn ki nan ki tambaye shi wuyar da yasha kafin na amince masa kuma ba wai dan ba na son sa sai domin mata an san mu da aji amma ke dai Baby kin ji kunya saboda wani namiji har ki ka damu da shi ciwo ya kama ki kai jama'a wannan asarancin har ina domin wannan kam asara ce ba komai ba"? Ta 'kasara maganar tana sakar mata harara ganin da Alhaji Abubakar yayi ran Hajiya Fatima ya 6aci sosai gashi ta saka ta a gaba da fad'a hakan ma zai sake haddasa mata wani ciwon shi ya sa ya ce "ya isa haka Fatima kiyi shiru na fahimta zan yi magana da ita daga baya wannan abun mu bar shi matsayin jarrabawa dan haka Baby kiyi 'ko'karin ciyewa karki bari shed'an yaci nasara a kanki aiki kuma daga yau na soke shi a wancan hospital d'in zan sa ayi miki transfer zuwa wani daban". Shiru Baby tai hankalinta a mugun tashe domin maganar gaskiya koda ace zata iya ha'kura da Shareef baza taso a cire ta daga hospital ayi mata canjin wani ba amma yanzu baza tayi jayayya ba zata yi ha'kuri zuwa d'an wani lokaci idan komai ya lafa ta samu Daddyn ta ro'ke shi ya barta taci gaba da aikinta acan indai ba haka ba gara ta ha'kura da aikin gabadaya akan ayi mata transfer ta koma wani gurin............... "Baby" ta ji ya kira sunan ta a hankali ta ce "na'am Daddy". "Kin ji hukuncin da na yanke ko"? Nan ma kai ta d'aga da'kyar ta ce "eh Daddy". "Ok yayi tashi ki je kuma ki kula sosai wajen shan maganin ki kin ji"? Kaita d'aga ta na mi'kewa a sanyaye ta shiga bedroom d'in ta Hajiya Fatima wacce ta had'e rai bayan wucewar Babyn ta ce "ni fa wallahi yarinyar nan ta bani takaici lokacin da ka ce doctor yace wai ciwon so ne ya haddasa mata hawan jini shi kad'ai ne namiji a duniya ga masoya nan da yawa sai kace wacce ta yi kwantai ko am fad'a mata mun gaji da ita ne har za ta fara neman kai namiji ya na mata yawo da hankali". Murmushi Alhaji Abubakar yayi yana kallon ta yace "baki ji ba aka ce soyayya gamon jini to jinin ta ne ya kaita inda zata sha wahala shiyasa ba don haka ba zai amince mata ko kad'an banga laifin sa ba domin ba'a so dole kamar yadda ita ta d'auka a ranta" da mamaki Hajiya Fatima ta ce. "Yanzu kenan da ace mutuwa ta yi ma za ka ce laifin ta ne"? Kai ya jinjina alamar confirm ya ce "kwarai ma kuwa to tsaya na tambaye ki laifin waye a cikin su shi ko ita na tabbata duk tsiya ya san tana son sa kuma ba zai bar ta tayi ta sonsa ba tare daya fad'a mata ba gaskiyar yana sonta ko baya sonta ba wai ke kin manta wace Baby ne akan naci"? Ajiyar zuciya Hajiya Fatima ta sau'ke tana cewa "idan na fahimta dai goyon bayan yaron da ko sanin sa ba kai ba ka ke yi akan 'yar da ka haifa haka ne"?. "No Hajiyan fassara ban goyi bayan sa ba kada ma kiyi wannan tunanin gaskiya ce nake fad'a a matsayin na uban dukkan su biyu ni d'an wani ma nawa ne kin gane"? Gyara zama ta yi tana cewa "shikenan" kawai shine abinda tace tana yin shiru daga haka kallon ta ya yi yana cewa. "Shikenan kin ji haushi kenan"?. "A'a ko d'aya". "Sai biyu"?. "Kamar ya"?. "Kamar yadda ki ka ji nace ba ko d'aya ki kace ba shiyasa nace miki sai zero tun da ko d'aya babu" 'yar dariya tayi tana kallon sa tace "kai wallahi Alhaji kana da barkwanci idan mutum ya zauna dakai ko mai 'kin son dariyar sa sai yayi". "Uhm gara na kasance me baiwa mata ta nishad'i idan ban saka ki dariya ba wa zan saka"? . "Babu fa ni d'in ce dai". "To kin gani yanzu tashi mu je ki had'a min ruwan wanka" "ok to" ta fad'a tana mi'kewa gaba ya wuce ta bi bayan sa su ka shiga part d'in sa. ZUCIYAR ALIYU CE @YUSRAH MUSA 08160983083 WhatsApp number. J.W.A PAGE.............67 Yau Zainab ba ta kwanta da wuri ba domin saida ta gama d'inkawa wasu 'yan mata biyu d'inkin su, su ka jira ta saka musu stone sannan su ka kar6a su ka tafi shi ya sa da ta yi wanka kawai ta domin idon ta har rufewa ya ke tsabar yadda barci ya cika su. Aliyu bai fad'awa kowa zai dawo gari ba ya yi saukar dare ya kira daga gida aka je airport aka d'auko shi lokacin duk 'yan gidan sun yi barci shi ya sa ya na shigowa bai nemi kowa sun gaisa ba sakamakon a mugun gajiye ya ke ga shi kuma dare ya riga ya ja sosai wanka ya yi ya kwanta shi ma. Duk da irin barcin da Zainab ta ji ya na damun ta da dare amma asuba na yi ta tashi ta yi alwala ta yi raka'atanil fajri ta yi 'yan addu'o'i sannan masalatai sun fara shiga sallah ta mi'ke ta bi masallacin kusa da su bayan an idar ta sake yin addu'a jin yadda idon ta yake zafi ta san barcin ne bai ishe ta ba shi ya sa ko sallayar ba ta nad'e ba hijab kad'ai ta cire ta koma ta kwana a take kuwa barci ya sake kwashe ta. 😃Dream works😃 Farkawar ta kenan ta d'ora idon ta akan fuskar Aliyu wanda ya ke barcin sa hankali kwance hannun sa ta kalla ganin yadda ya zagaye ta a jikin sa ya rungume d'an murmushi ta yi ta na shafa gashin girar sa tare da busa masa iska a hankali d'an motsawa ya yi amma maimakon ta ji ya sake ta sai ta ga ya sake sabon juyi ya na dad'a jan ta tare da cusa fuskar sa a gefen wuyan ta shiru ta yi ta zuba masa ido kamar me tunani can kuma ta juyar da hankalin ta kan agogo ta ga sha d'aya saura minti biyu rufe baki ta yi tare da yun'kurawa za ta tashi ya ri'ke ta, duk tunanin ta ko tashi ya yi sai taga idon sa a rufe har lokacin kama hannun nasa ta yi a hankali ta janye shi daga ri'kon da ya yi mata ta mi'ke ta na d'auke 'kafa saboda kar ta tashe shi ta shiga toilet murmushi Aliyu ya yi lokacin da ya ji ta rufe 'kofa dama ba barci ya ke ba tun lokacin da ta shafa gashin girar sa ya tashi kawai dai ya'ki bud'e idon ne kuma ya'ki nuna mata ya tashi d'in ta na fitowa ta sake kallon kan gadon ta ga ya sake salon sabuwar kwanciya ajiyar zuciya ta sau'ke ta na wucewa ta tafi gaban mirror ta d'auki 'karamin towel kenan za ta fara goge ruwan jikin ta, kawai ta gan shi tsaye a bayan ta da mamaki tace "Wai dama ba barci ka ke ba"? Gira ya d'auke ya na cewa "uhmm ta ya zan iya barci bayan kin tashi a kusa da ni ki dawo mu kwanta" ya fad'a ya na juyawa ya koma gadon ya kwanta ta cikin mirron ta kalle shi ta na cewa "na ga sha d'aya ta yi ne kuma ban je na gaida Momy ba". "Ok ki na nufin yanzun hakan wanka ki kai gurin Momy za ki je? Ai kuwa wannan wankan na ki bai wanku ba domin yanzu zan sake 6ata shi" tsayawa ta yi ta na aje towel d'in da ta gama goge jikin ta ce "da me kenan"? Ta tambaya tare da juyowa ta na kallon sa murmushi ta ga ya yi mata yana tashi daga kwancen da ya ke ya taho gaban mirror inda ta ke tsaye ya na 'karasowa ya ri'ke towel d'in ke d'aure a jikin ta ya ja zaro ido ta yi ganin ya na neman kissing d'in ta tace "A'a Aliyu kar k............................... Kai ya girgiza mata ya na janye hannunta da ta ri'ke na sa ba tare da ya yi magana ba ya matso ta jikin sa sosai ya manna ta ya na d'ago fuskar ta ya ri'ke lips d'in ta ya fara kissing d'in ta. 🙊Hummm!!! kan babbar butar shayi🙉 wannan mafarki ya yi dad'i d'and'anon shi coiiii🙈. ME KU KE TUNANIN ZAI FARU IDAN ZAINAB TA FARKA DAGA WANNAN ZAZZA'KAN MAFARKIN NA TA?😁 MU JE ZUWA NEXT PAGE. 💓 ZUCIYAR ALIYU CE 💓 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION. J.W.A @YUSRAH MUSA PAGE 68 Wani irin tsalle Zainab dake kwance akan katifar ta, ta yi ta na cillar da bargon da ta rufu dashi tare da fasa wata firgitacciyar 'kara a gigice ta ce "wayyo Allah na shiga uku Aliyu me ye hakan wayyo Allah wayyo Umma ki taimaka min ya shigo min d'aki" gabadaya tabi ta firgice ko sanin cewa a cikin d'akinta ta ke ba ta yi ba sai had'e kai da gwiwa da ta yi ta na 'kan'kame jikin ta guri d'aya Umma ta na d'akin ta, ta jiwo 'karar ta da sauri shigo d'akin ta na cewa. "Zainab Zainab lafiya ihun me ki ke me ya faru"? Ganin ta tayi a takure a can jikin bango jikin ta sai kakkarwa ya ke "Zainab lafiya kuwa"? Umma ta sake tambayar ta tana 'karasawa ta d'ago da fuskar ta wacce ta ji'ke da hawaye da mamaki Umma ta ce. "Subanallahi wai me ya faru ne kukan me ki ke"? Kasa magana Zainab ta yi sai kai da take girgizawa hawaye sharr sharr ya na zuba mata ganin ba ta ce komai ba ya sa Umma ta ce "to ba ki fad'i me ya ke damun ki ba kuka maganin me zai yi miki na tambaye ki kin yi shiru"? Da'kyar ta na shashshe'ka ta ce. "Ba komai". "Ba komai kuma amma ki kai 'kara gashi na shigo na same ki kina kuka sai ki ce ba komai ki fad'a min me ya faru"? Sake girgiza kai ta yi ta na cewa "ba komai Umma mafarki na yi"? Baki Umma ta bud'e ta na kallon ta tace "mafarki kuma"?. Kai ta d'aga sabin hawaye masu zafi su na 'kara gangaro mata dafa ta Umma ta yi ta na cewa "wanne irin mafarki da har zai sa ki kuka"?. "Umma mafarki ne kawai abin da ya faru a mafarkin ne ya d'aga min hankali har na yi 'karar ban sani ba kuma sai da na farka na gane ba a gaske ba ne" kai Umma ta jinjina ta na "amma da alama kamar mummunan mafarki ki kai ko tun da na ga ki na kuka". "Eh Umma ba me kyau ba ne ki taya ni da addu'a Allah ya sa ya tsaya a iya mafarkin kar ya zama gaskiya domin ba na fatan hakan a rayuwa ta" kai Umma ta d'aga ta na cewa "shikenan ba komai Allah ya rufa asiri Ubangiji ya sa ba gaskiya ba ne" da sauri Zainab ta ce "Amin" tun da ta san addu'ar iyaye akan 'ya'yan su kar6a66iya ce juyawa Umma ta yi ta fita ta na cewa. "Allah ya kyauta kar ki saka mafarkin da ki kai a ran ki duk da ba gaske ba ne amma wata rana ya na zama gaskiyar" shiru Zainab ta yi ta zubawa guri d'aya ido bayan fitar Umma kawai abun ya fara dawo ma ta sabo gani ta ke kamar a gaske ne komai ya faru runtse ido ta yi ta na cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un mafarkin Aliyu kuma me ye had'i na da shi da har zan saka shi a rai na, na yi mafarkin sa kuma mafarkin nasa ma na rasa wanne kala zan yi sai na gan ni matsayin matar sa? Matar sa fa"?

Chapter 27 of 34