kinga dama kema ki share naku idan baki ga dama ba ki barshi da datti" tana fad'in haka ta juya ta nufi gurin wanke-wanke da kallo Zainab ta bita tana d'an girgiza kai kafin ta saki labulen ta koma cikin d'akinta karasa kai surar da take yi sannan ta rufe al-qur'anin tayi addu'a tare da mi'kewa ta cire hijab d'in jikinta ta fita samun Bilki tayi a gurin tana wanke kwanukan su bata ce mata komai ba itama ta d'auki kujera ta had'a ruwan klin dana d'auraya ta fara wanke nasu ta gama ta d'auka takai kitchen sannan tazo ta saka ruwa ta wanke gurin ta share kofar tasu tas ta wanke ta tasaka tsumma ta goge tayis d'in daidai Umma ta fito ta kalleta cikin jin dad'i tace.
"Sannu Zainab Allah ya miki albarka" murmushi Zainab tai daidai ta wanke 'kafarta da hannunta tace "amin Umma nagode" kai Umma ta d'aga tana wucewa ta shiga kitchen domin ranar aikinta ne bin bayanta Zainab tai tana cewa "wanne aikin zan kama miki"? Doya Umma ta nuna mata tana cewa "ki d'auki wu'ka saiki fita waje ki fere mana ita yau da ita za'a karya jiya baban ku ya shigo da ita da dare" kallon doyar kitchen d'in tai da d'an yawanta tasan zatakai kusan dubu goma ko tafi maybe 'yar ribar daya samu ce yayo musu cefane saboda suji dad'i suma tunda taga d'aurin kayan miya kuma ga d'anyan kifi ma a gefe numfashi ta d'auko tana d'auko babbar roba da wu'ka Umma ta d'iba mata iya wacce zasuyi amfani da ita waje ta fita ta zauna akan kujera a kusa da kitchen ta soma aikin fere ta domin yau sai karfe d'aya zataje lecture harta gama tana shirin mi'kewa Umma ta sake mi'ko mata guda d'aya tace a dad'a saboda saura kofafin ma akai musu abinda ka bayar shine rabonka tana cikin gyaran wacce ta mi'ko mata Sameer ya shigo da sallama hangota dayai yasa ya taho inda take yana zuwa ya tsuguna a kusa da ita yana cewa.
"Yau kuma doya zamu ci kenan kece zaki dafa yau ba school ne"? Murmushi tai tana girgiza kai tace "a'a akwai amma ba yanzu zan tafi ba sai 'karfe d'aya".
"Ok Allah ya kaimu wannan doyar wanne kalar samfurin dafi za'ai mata ne"?.
"Nima ban sani ba saidai na tambayi Umma".
"A'a basai kin tambaye ta ba kawai ni ban cika son faten doya bane gara sakwara yanzu abinda za'ai tunda sai karfe d'aya kike da school bari kawai na siyo 'kwai kiyi min yamballs" ya fad'a yana mi'kewa ya fita daidai Asabe kuma ta shigo kofar tun daga nesa take zaro ido tana kallon Zainab harta karaso ganin abinda take yasa tace "tofa wannan wanne irin kalar munafirci ne dama jiya an shigo da kayan abinci amma shine ko a sanar dani wato ga bora ko? Humm zai dawo gidan ina nan ina jiransa za'ai bala'i saidai a raba mana girki dan bazai yuwu a ri'ka cuta ta ina kallo ba" ta fad'a tana juyawa ta shiga d'akinta Umma tana cikin kitchen tana jinta batai magana ba balle Zainab da ko rufeta zatai da duka bazata tanka mata ba saboda albarkacin son da Sameer yake mata ko Bilki baya yiwa kulawar da yake mata shiyasa bazata ta'ba iya furtawa Asabe komai ba sai alkhairi.
Zainab tana zaune Sameer ya dawo da 'kwai masu yawa har saida ta zaro ido tana kallon sa tace "Yaya Sameer wannan ai yayi yawa ka rage ka mayar da wasu sai ka kar6o mai da kud'in" murmushi yayi yana shima yana kallonta yace "ai ba nawa bane ni kad'ai akwai naki a ciki gudu goma ne nawa sauran na cikin kiret d'in naki ne" da mamaki tace "nawa kuma aini basai ka siyo min ba".
"A'a nima ba nine na siya miki ba yanzu abinda za'ai ki d'ibi iya nawa nakin kuma saiki kai d'akinki ki aje kayanki idan kin tashi amfani dashi saiki d'auka" cikin rashin kwancyar hankali ta sake kallon 'kwan kafin ta d'ago ta kalli Sameer tana cewa "waye ya siya min 'kwai"? 'yar dariya Sameer yai yana cewa "ba ruwanki da wannan ke kam kawai kiyi abinda nace kafin Umman mu ta fito ta ganshi kinsan dai halinta idan ba so kike ta dugurguje su ba kowa ya rasa" jin abinda yace yasa Zainab ta mi'ke tana d'auka ta saka a cikin d'akinta amma data fito ba alamar Sameer d'in murhun gawayi ta d'auko ta d'ebi iya doyar da zatai masa yamballs d'in ta dafa ta da gishiri ta shiga kitchen ta fito da turmi ta d'ebo attaruhu albasa da maggi zama tai ta zuba doyar cikin turmin ta daka ta sannan ta d'auko roba mai fad'i ta zuba a ciki ta jajjaga attruhu da albasa ta zuba akan doyar ta kawo kori shima ta saka ta had'e ta gurin d'aya ta d'auko ta fara mulmulawa tana ajewa harta gama amma kuma bai kawo mai ba mi'kewa tai ta shiga d'aki ta d'auki wayarta ta kirashi yace sunje anguwa ne amma ta shiga d'akinsa akwai kud'i a cikin wani littafi ta d'auki yadda zata siyo man aje wayar tayi ta fito ta shiga d'akin nasa ta d'auko ta fito kenan Asabe ma ta fito daga nata d'akin ganin daga inda ta fito yasa ta zuba mata wani uban ihu tana cewa.
"Wayyo jama'ar gidan nan ku kawo min d'auki na kama 6arauniya🙊 ta shigar min d'akin d'ana zatai masa sata" da mamaki Zainab ta kalleta amma batai magana ba sai Asabe data aiko mata da wani irin kallo tana cewa "uban me kika shiga yi masa a d'aki"? Kamar Zainab zata shareta sai kuma tace "am cewa yayi nayi masa yamballs ya kawo min 'kwai amma bai kawo mai ba shine na kirashi a waya yace min yaje anguwa ne amma na duba d'akinsa cikin littafi na d'auki kud'in shine yasa na shiga na d'auko ba wani abu bane"? Kai Asabe ta jinjina tana cewa "ko ba yamballs ba? Kai amma Sameer ya ji kunya au nan d'in har yardar dayai miki takai ya fad'a miki gurin ajiyar kud'in sa gaskiya Sameer bansan wanne irin shashashan 'kauye bane ayi mutum ba nutsuwa tsabar rashin sirri wai 'yar kishiya ya d'auki yarda ya baiwa har tasan gurin ajiyar kud'in sa amma ni ban sani ba" tai maganar tana cizon yatsa tare da d'agowa ta kalli Zainab cikin takaici tace "uban me kika tsaya kina kallona da wadannan manyan idon naki wuce ki bani guri makira kenan a haka fuska fal da annuri amma zuciyar tana nan ba'ki 'kirim shiyasa ma kika rasa mijin aure zalunci fal ciki wazai auri masifa ya kai wa mahaifansa" tari da bai kama Zainab ba bataiwa Asabe ba sai wucewa datai ta koma gurin aikinta duk da taji d'aci kalaman Asaben amma ya zatai hijab d'inta ta d'auka da kanta ta fita siyan man.
Ayi ha'kuri yau typing d'in ba yawa ina uziri ne.
STORY WRITTEN ND EDITING
Yusrah Musa Abubakar.
ZUCIYAR ALIYU CE.
@YUSRAHMS
PAGE 17
Asabe kam shiga d'akin Sameer tai tana bala'i tana bincike kamar tayi masa ajiya ganin kud'i kusan dubu ashirin a cikin littafin yasa ta d'ebe tareda d'aga katifarsa ko zata samu wani kud'in tabi duk ta birkice masa d'aki ta wargaza komai ganin iya wannan dubu ashirin d'in ne yasa ta fito daga d'akin batare data gyara masa komai ba ta shige nata d'akin ta bala'i da zage zage da habaici iri-iri an asirce miji da masifa d'an ma baza'a barta dashi ba shima ya juya mata baya.
Dawowar Zainab batasan maiya faru ba balle ta shiga ta gyara masa d'aki saida ta gama soyawa ta shiga zata aje masa taga komai a wargaje littafin an yaga wasu fefofin tasan aikin Asabe ne to amma yanzu babu kud'in da yake cikin littafin idan ta gyara d'akin Sameer ya dawo zaice itace ta d'auke idan ta barshi a haka zaice waye ya shiga masa d'aki bayan ita bata da mafita gara ta barshi a hargitsen idan ya shigo ya gani tayi masa bayani d'aukar yamballs d'in tayi ta mayar d'akinta lokacin sha biyu tayi ta dafa ruwa akan sauran garwashin datai suyar ta shiga band'aki tayi wanka ta fito ita ma Umma sannan ta gama sakwarar miyar ma ta sau'ke ta fitowa tayi ta kar6o kwanukan Asabe dana Bilki da Sameer sannan ta dawo ta raba ta sakawa kowa ta fitar dana Hajiya da yake yau Zainab bata shiga ba da safe sun gaisa ba shiyasa yanzu tace tunda tayi wanka ta fito takai mata itama tazo taci kafin karfe d'ayan tayi.
Saida ta shirya tsaf sannan ta d'auko hijab ta saka ta kar'ba ta tafi 6angaren Hajiya duk yaran gidan da 'yan mata suna nan sun cika kofarta kamar yadda suka saba dama ita kad'ai ce bata shiga saidai idan gaida ita zatai ko kuma wani uzuri saboda ayyuka sunyi mata yawa ba kamar sauran take ba zataje school zatai aikin gida ga d'inkunan mutane sannan tana koyarwa a islamiyya sufa sauran bai wuce daga school sai islamiyya ba kowace take aiki a cikinsu ba saboda sun d'auki rayuwar 'karya sun saka a gaba sun 'ki su tsaya iya matsayin da Allah ya ajesu.
Da sallama ta shiga a lokacin Haulat tana basu labari suna dariya sun cika d'akin da hayaniya ko sallamarta basu jiba sai ha'kura tayi ta shiga tsit kowa yai shiru duk suka zuba mata ido ba wanda ya sake tari zama Zainab tai tana cewa "ina yini Hajiya"? Kamar bazata amsa mata a da'kile tace "lafiya" daga haka bata sake cewa komai ba kuma ko kallon inda Zainab d'in take batai ba shiru itan ma Zainab d'in tayi ranta babu dad'i can tace "ga abinci inji Umma tace a kawo miki" ta fad'a zata mi'ke kenan taji muryar Hajiya tace "tsaya ki tafi da kwanon" tsayawa tai Hajiya dake kallon wani d'an yaro zai kai shekara sha biyu a cikin yaran da suke gurin tace "Khaleel jeka waje idan kaga almajiri ka kira shi" to yace yana mi'kewa ya fita jin abinda Hajiyan tace yasa ran Zainab ya sake 6aci saboda ta fahimci baza taci abincin bane tana tsaye har yaje ya kira almajiri Hajiya ta d'auki kular tace "mi'ka masa ya juye" kar'ba khaleel yayi ya mi'kawa d'an almajirin dake waje ya juye ya mi'ko masa yace Allah ya kar'ba dawowa d'akin khaleel yai yana mi'kawa Hajiya kular kaita girgiza tana nuna Zainab tace.
"Ga asararriyar da zaka baiwa nan mi'ka mata kayan tsiyarta ki fad'awa uwarki daga yau karta kuskura ta sake kawo min girkinta bana so bazan ci ba domin niba mayunwaciya bace ina da 'ya'yan da zasu kawo min idan sun girka ba iya Abdullahi ne d'ana ba" jin abinda tace yasa Zainab d'an juyowa ta kalleta idonta ya fara tara ruwa cikin 6acin rai ta kar'bi kular a hannun khaleel ta fita daga d'akin.
Baki Haulat ta ta'be tana cewa "wallahi Hajiya Zainab d'in nan haushin da take bani kamar nasa bindiga na harbe ta kullum sai dare yayi kana son ka kwanta ka huta ita kuma sannan ne zata tsiri yin d'inki ta cika mana kunne da 'kara ba kofar mu d'aya ba amma tana mugun matsa min" karaf Bilki tace "to kema da kike wata kofar ta dame ki balle mu humm in Allah ya yarda saina lalata keken nan yadda ko masu gyara baza su iya gyara shi ba" dariya Rasheedat tai tana cewa "nikam ba ruwa na dajin wata 'kara ina can kofar mu Allah yasa bana ji balle gashi yanzu saurayi na ya turo mahaifansa nasan bikina bazai wuce nan da shekara d'aya ba Nima na shiga sahun su Aunty Arabiyyah" jin abinda tace yasa Hajiya cewa "kai kaiton abun da yafi karfinka wai suna ganin yarinyar nan dan masifa sun kasa sakata ta fidda miji 'kannin tama sai aure suke nikam nace Rafi'atu takai Zainab ne a haife"? Cikin gulma Bilki tace "Ina Aunty Rafi'atu zatai Zainab kusan shekara uku ne tsakanin su".
Takaici ne ya 'kara kama Hajiya tace "kiji fa kiji fa amma har yanzu tana jangwa6e a gida shekara ashirin da hud'u ba aure".
"Ai Hajiya indai kika biya Zainab da mahaifiyar ta ba aure take so tayi ba domin kwanan baya sabon murfin kofa suka baiwa Yaya Sameer kud'i ya siya aka kira wani mutum ya saka mata" Bilki tayi maganar tana dariya saboda ganin Hajiya ta zaro ido bayan 'karya tayi "kikace har murfin kofa aka saka mata"? Kaita d'aga tana cewa "kwarai Hajiya da idona naga wanda ya saka mata sai kallonsa take tana farfara masa ido dan yace yana sonta amma shi ko kallonta baiyi ba harya gama aikinsa ya tafi kyan d'an miciji ne da ita a haka ke kyace 'yar gidan gwamna kyau kamar balarabiya amma gashi wanda zaice yana sonta ma ta rasa".
"Ba'kin jini gareta mukam muna dasu kuma sai munyi aure mun barta a gidan nan tunda har gobe bata da tsayayye" Haulat ta fad'a tana cije baki cike da mugunta a masife Hajiya tace "ai Kuma wallahi bata isa ba ko ta'ki ko taso sai tayi aure tabar gidan nan indai bata tsayar da mijin aure ba ni zansa ayi mini cikiyar kowanne irin mutum aka samu dole ta aure shi kuma ba saki saidai idan mutuwa yayi" dariya suka she'ke da ita cikin zolaya Rasheedat tace "ko makaho ne"?.
"Ko kuturu ne saita aure shi" sabuwar dariya suka saki Zakiyyah na cewa "amma idan 6arawo ne fa Hajiya nan ya zaki"? Gyara zama Hajiya tai tana cewa "ko maye ne wallahi saita aure shi inyaso ya cinyeta a ranar da akai mata rakiya dan uwarta ni nagaji da wannan masifar jira nake a gama komai na auren Haulat nasa ai min cikiyar mai son 'yar sadaka ya kawo sadaki kawai a d'aura musu aure" shewa sukai suna cewa "sai dake Hajiyan mu Allah yaja zamanin ki" shiru Hajiya tai daga haka bata sake magana ba iya sune suka saka dabar gulmar Zainab d'in suna ta dariya.
ZUCIYAR ALIYU CE
DEDICATED TO
😭MY LATE FATHER😭
)(MUSA ABUBAKAR GIMBA)(
Ina ro'kon Ubangiji ya garfarta maka Allah ya kai haske kabarin ka Allah ya yi maka rahma.
IBRAHIM MUSA ABUBAKAR
AISHAT MUSA ABUBAKAR
ABDULLAH MUSA ABUBAKAR
🤲Ubangiji Allah ya ji'kan ku da rahma Allah ya haskaka kaburburan ku Allah ya sa aljannah ta zamto makoma a gare ku.
@YUSRAH DUTSE
PAGE 18
Zainab kam data koma bata fad'awa Umma abinda Hajiya tayi ba saboda kar ranta ya 6aci kitchen ta wuce ta ajiye kular ta fito ta shiga d'akinta ta d'auki iya abinda zata d'auka taiwa Umma sallama zata tafi school "Amma Zainab baki ci abinci ba zaki tafi"? Umma ta fad'a tana kallon ta kai ta d'aga ta na cewa.
"Saina dawo zanci idan Yaya Sameer ya shigo ki fad'a masa yamballs d'insa yana d'aki na".
"Tom Allah ya tsare ubangiji ya dawo dake lafiya" Amin Zainab tace tana fita daga kofar tasu ta tsaya ta saka nikaf d'inta saboda bata ta'ba fita waje fuskarta a bud'e zai wahala mutum yace yasan yadda fuskarta yake saidai idan ya santa lokacin da take karama.
Sameer kam gidan su Amirah ya raka Aliyu ya gaisar da Maman ta sun dad'e acan amma har suka taho basu had'u da Amirah ba tana gidan kakanun ta bayan sun dawo Sameer yacewa Aliyu bari yaje gida ya d'auko musu yamballs saboda Aliyu yace yana so yaci irin girkin Zainab shiyasa ma ya'ki cin abinci a gidan su Amirah saboda kar yaji rashin dad'in sa
Baisan meya faru ba sai da dare ya shigo gidan a lokacin an kawo nefa yazo saka caji yana bud'e kofar d'akinsa ya shiga yaga yadda yake a hargitse wani irin jada baya yayi yana kallon komai da mamaki ya akai Zainab tayi masa haka meyasa ta 6ata masa d'aki yasan tana da nutsuwa anya hakan zai faru? Sakin labulen d'akin yayi yana juyawa ya koma kofar d'akin Zainab zaiyi magana ta fito kusan karo sukai d'an ja baya yayi yana cewa "Zainab meya faru ne"? Cikin rashin fahimta tace "Yaya Sameer wani abu ne"? Ta tambaya hankalinta a tashe domin ta manta abinda ya faru d'azu "eh wani abu ne zo muje ki gani" ya fad'a yana juyawa ganin ya nufi d'akinsa yasa zuciyarta harbawa wato bai shigo gidan yaga d'akin ba sai yanzu to ita me zatace masa ganin ya tsaya a kofar d'akin yana kallon ta yasa da'kyar ta iya d'aga 'kafarta taje gurin d'age mata labulen yayi yana cewa "meya faru d'azu da nace kizo ki d'auki kud'in da zaki siyo mai"? Ji tayi hankalinta ya sake tashi muryarta na d'an rawa tace.
"D'azu bayan kace min na shiga na d'auki kud'i a cikin littafin na d'auka na fito Umma Asabe ta shigo kofar ta ganni shine tace na shiga zanyi maka sata saboda naga baka nan nace Mata kaine kace na shiga na d'auko kud'i daga haka bata cemin komai ba na wuce na fita siyo man bansan abinda ya faru ba Yaya Sameer wallahi ba nice nayi maka haka da d'akin ba" tunda ta fara magana yake kallonta har takai karshe huci ya fitar mai zafi ransa a 6ace ya kalli littafin dake kasa da alama kud'in Asabe ta d'ebe kaiya jinjina yana cewa..
"Shikenan ba matsala jeki" jiki a sanyaye cikin rashin jin dad'i Zainab tace "bari na gyara maka d'akin" shiga yayi yana cewa "a'a karki damu zan gyara jeki" juyawa tai kamar mara lafiya ta koma d'aki shikam bai fito ba saida ya bincika ko'ina ganin babu alamar kud'in gashi har katifa a jingine take an d'agota ana neman kud'in ji yayi sabon 6acin rai yazo masa har wuya fita yayi ya shiga d'akin Asabe tana zaune ita da Bilki suna cin zazzafan tsire wanda yasha kayan had'i humm dama abinda yake zargi kenan kuma gashi tun ba'a je ko'ina ba ya tabbata tsaye yayi a kofar d'akin yana kallon ta yace.
"Umma ya akai kika shiga d'aki na kika wargaza min komai nawa"? Jin abinda yace yasa ta zafga masa wata uwar harara tana cewa "uban me zanyi a d'akinka wata uwar ka ajiye dama ni kad'ai ce a kofar da zakai min sharri ga 6arayi can kaje ka tambaye su ko saini saboda raini"? A damuwance Sameer yace "ni bana nufin haka dan girman Allah Umma kud'in da kika d'auka kawai zaki bani domin ba nawa bane" a she'ke Asabe tace "wanne kud'i"?.
"Dubu ashirin d'in da kika d'auka a cikin littafi" yana rufe baki ta mi'ke tsaye tana cewa "a cikin uban littafi da yaushe naje na d'auki kud'in ka a d'aki uban me zanyi dashi dama fatara nake"?.
"Umma dan Allah ki taimaka ki bani kud'in nan wallahi ba nawa bane kud'in amana ne" a masife Asabe tace "ai ko saidai amanar ta cinye ka amma ni ban d'auki kud'i ba uban waye yace maka na d'auka"? Shiru yayi bai bata amsa ba taci gaba "wato Zainab ce ko saboda d'azu na kamata tana shirin shiga d'akin tayi bincike taga na ganta shine reshe ya juye da mujiya 'yar gadon masharranta bari naje na ci ubanta ko Hauwa bata isa tai min sharri ba balle ita da aka haifeta a gaban idona" tare kofar Sameer yai fuskarta a mugun had'e yace "karki fita daga d'akin nan Umma indai gurin Zainab zakije ki 'kyale na ha'kura kud'i kuma zan biya" wani d'an iskan kallo tayi masa tana cewa "au saboda zanje naci mata mutunci shine ka hana ni amma da itace tazo zata ci min mutunci bazaka hanata ba saboda ka zama sakarai ko"? Har lokacin shiru Sameer yai bai bata amsa ba karshe ya juya ya koma d'akin sa yana barin gurin itama Asabe ta fita da sauri taje kofar d'akin Zainab tana cewa.
"Annamimiya fito min nan munafika wacce ta gaji ba'kin hali a gidan ubanki na shiga d'akin Sameer d'azu da yaushe na shigar masa d'aki fito ki fad'a min kona shigo d'akin nayi miki d'an banzan duka wallahi" ta karasa maganar tana d'aga murya sosai wanda yasa Umma fitowa da sauri Sameer ma yayo waje yana cewa.
"Wai Umma me kike yi haka ne wannan fa ba girman ki bane taya zaki zo kina aika mata da zagi alhali tana matsayin 'ya a gurin ki".
"Uban 'ya take a gurina wannan zan d'auka matsayin 'ya Allah ya suturu bu'kui inji kishiyar 'konanna wallahi Allah ya sauwake kai da Bilki dai dana haife ku na haife ku amma nikam ban haifi Zainab ba ga uwarta nan" ta karasa maganar cikin wula'kanci tana nuna Umma dake tsaye ta kasa magana kai Sameer ya girgiza yana cewa "da nasan abinda wannan tambayar zata jawo wallahi bazan tambayi kud'in nan ba gaskiya Umma ki gyara wannan ba rayuwa bace" yana fad'in haka ya juya ya koma d'aki da harara Asabe ta raka shi tana cewa "wannan ba rayuwa bace dan uwarka mutuwa ce mara mutunci har nice zan fad'i magana ka mayar min ina daidai dakai" juyawa 6angaren Zainab tai tana cewa "ke zo'kal'kalar banza mai had'a husuma masharranciya baki nasara ba saiki sauya tasha banza kawai" kan Umma ta koma tana nunata da yatsa tace "kema na dawo kanki kiwa 'yarki gargad'i karta kuskura ta sake min sharri idan kina bu'katar zaman lafiya a cikin gidan nan mtwwww" taja tsaki tana komawa d'aki.
Hawaye ne shar shar suke zuba a fuskar Zainab irin maganganun da Asabe ta fad'a mata suna mata ciwo bata son ace abu yana had'ata da ita amma ina ko bata takale taba ita kuma zata ta6o ta.................
Muryar Umma taji ta katse ta "Zainab ke d'in meya had'a ku nifa ban gane komai da take cewa ba a ina kika ganta ta d'auki kud'in"? Kaita girgiza tana goge hawayen fuskarta muryarta a hankali tace "d'azu ne da Yaya Sameer yace nayi masa yamballs ya kawo min 'kwai saiya manta ya tafi anguwa bai siyo farin man dazan soya masa ba shine na kirashi a waya na fad'a masa ni bansan ya tafi wani guri ba a lokacin ne yace na shiga d'akinsa na bud'e littafi akwai kud'i na d'auka na siyo na shiga na d'auko dubu d'aya Umma Asabe ta shigo ta ganni shine tace sata zanyi masa nace a'a kud'i yasa na d'auka zan siyo mai ne a lokacin ma ta zazzage ni daga haka nidai bansan komai ba hijab na d'auka na tafi na siyo man amma lokacin dana gama yamballs d'in na shiga d'akin zan aje masa naga an wargaje d'akin komai dabam shine na fasa aje yamballs d'in a d'akin nakai nawa d'akin na tafi makaranta yanzu kuma saiya kirani yake tambaya ya akai nace masa lafiya 'kalau nabar d'akin amma Umma Asabe ta shigo ta ganni daga haka bance masa komai ba bansan meya faru ba sai ji nayi tana zagina yanzu" numfashi Umma ta sauke tana girgiza kai tace.
"Allah ya rufa asiri koma d'aki ai shi Sameer d'in yana da hankali yasan bazaki ta'ba yi masa haka ba karma ki d'orawa kanki damuwa ki 'kyale" Umma tai maganar tana komawa d'aki itama Zainab d'in nata d'akin ta koma shikam Sameer saida gyara d'akinsa tas ya mayar da komai daidai sannan ya fita daga gidan.
Duk abinda akai Abban su Zainab bai sani ba daya dawo gida ma Umma bata nuna masa komai ba saboda bazai yuwu ya wuni yana fafutukar nema musu abinda zasu ci ba ya dawo gida dan ya huta kuma ta tada masa hankali ba amma me yana fara cin abinci kenan suna hira da Umma Zainab ta shigo ta gaida shi ta fita sai ganin Asabe sukai ta bamko muku kofa ta shigo ba sallama tana huci da mamaki Umma ta kalleta cike da fargabar Allah yasa ba abun d'azu zata fad'a ba karta taso masa da 6acin rai shi mutum mai sau'kin hali amma idan ka ta'bo shi zakaga tsantsan abinda ake kira da 6acin rai........
"Gaskiya na gaji da wannan na gaji da rashin adalcin da ake min a cikin gidan nan" sukaji ta fad'a da mamaki baba da baisan komai ba yace "akan me kike magana Asabe wanne irin rashin adalci akai miki kuma waye yayi miki"?.
"Waye kuwa banda kai tunda kaji na ambaci adalci a gurin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 34