Share this page
tsaye suna gadin sa da sallama Aliyu ya je gurin amsa masa Daddy yayi yana nuna masa d'ayar kujerar dake gurin zama yayi shi kuma Daddy yayi wa securities d'in nuni su d'an basu guri za suyi magana matsawa su kai d'an nesa da su kafin su yi abin da za su yi kallon Aliyu Daddy yayi yana cewa "Aliyu dama tambayar ka nake so na yi magana ce akan aure shin ka shirya yi yanzu kana da wacce kake so"? Aliyu bai ta'ba kawowa a ransa wannan tambayar da Daddyn zai yi masa ba shiyasa ya d'ago yana kallon sa kai Daddy ya d'aga ya na cewa "eh kalle ni da kyau na ce akwai wacce kake so ko a'a idan baka da wacce kake so ni na samo maka" jin abinda Daddy ya ce daga 'karshe ya sa cikin fargaba Aliyu yace "a ina take Daddy"?. "Ba ruwan ka da inda ta ke da farko ka fad'a min wacce kake so ko babu"? shiru Aliyu ya yi zuciyar sa na harbawa addu'a kad'ai yake Allah yasa ba Amirah Daddy ya hango masa ba Allah yasa ba ita zai ce ba....................... "Aliyu". "Na'am Daddy". "Nace ka fad'a min in da yarinya take 'yar waye a wacce anguwa ta ke"? Numfashi da huci ya fitar lokaci guda yana d'an rufe ido ya bud'e tare da girgiza kai duk Daddy na hankalce da shi yace "uhum ina jin ka"? "Daddy a nan anguwar ta ke". "A nan anguwar ta wajen ina"?. "Gidan su Sameer 'kanwar sa ce". "K'annin nasa mata guda nawa ne"? "Su biyu ne Bilkisu da Zainab". "Ok na gane wacce daga ciki ka ke so"? "Zainab ce" baki Daddy ya bud'e yana kallon sa da mamaki ya ce "bayan neman ka da Momyn ku ta ce ina yi ta fad'a maka wani abu ne"? "A'a babu abin da ta fad'a min kawai cewa ta yi ka na nema na". "Ok shikenan dama dalilin kiran kenan tun da na ji a inda take ya wadatar tashi ka je" har ya mi'ke zai tafi ya sake tsayawa yace "amma Daddy ban fad'a mata ba". "Me ya sa zaman jiran me ka ke "?. "Lokaci na ke jira". "Oh! nan d'in baka fad'a mata ba idan kuma da wanda zata aura fa"? "Babu Daddy ai tasan da zama na saidai ba ta san ni bane kar ku shiga maganar har sai naje na same ta da kaina" murmushi Daddy yayi yana cewa "Ok yayi ba damuwa je ka" wucewa Aliyu yayi ya fita daga garden d'in sosai Daddy yayi mamakin jin abinda ya ke so ya tarar da shi a inda ya dace shi ke nan ba wata shan wahala ko aikin da na sani bai dad'e ba a garden d'in bayan sun gama maganar da Aliyu shi ma ya tashi ya shigo part d'in sa daidai Momy ta shigo ko bari ta zauna bai yi ba ya ce. "Ashe kin ji wai dama ita ce yake so da na tambaye shi ni da na ji ya kira sunan ta ma farko zargi na yi ko kece kika fad'a masa"? Dariya Momy tai tana 'karasowa ta zauna ta ce "wallahi a'a ban fad'a masa komai ba kawai da nace yaje kana neman sa shikenan humn gaskiya abun nan yayi mun dad'i sosai ba gamu ko Aliyu ba hatta a gurin su Elham nasan zata samu kar6uwa sosai suna yawan yabon halayen ta yanzu idan suka ji ita Aliyu zai aura farin cikin da zasu yi ba zai fad'u ba. "Haka ne amma saboda saka ido irin na mutane kawai zan kira mahaifin ta nan gidan mu yi magana ni da shi yafi sau'ki cikin sirri akan a taka zuwa gidan su" kai Momy ta d'aga ta na cewa "eh gaskiya hakan zaka yi nima bana so maganar ta fita da wuri saboda 'yan ba'kin ciki da ma'kiya ko mahassada ka san babu abin da ka yiwa mutum amma sai ka ga baya 'kaunar ya gan ka cikin walwala". "Gaskiya ne kin san abin da Aliyu ya ce? Wai shi bai fad'a mata ba lokaci ya ke jira". "Ka ji shi da wani shirme lokaci ya ke jira sannan ya fad'a mata idan wani ya riga shi fa, lalacewar agogo ba ya hana lokaci tafiya" Momy ta fad'a tana kallon Daddy wanda ya jinjina kai ya na cewa "ni ma dai abin da na gani kenan amma shi wai jiran lokaci ya ke ko wanne irin lokacin ya ke nufi"?. "Lokacin sa na shirme man ya ke nufi kaga idan da wanda zata aura shikenan ya tashi a tutar babu yanzu kawai abin da za'ai ka rabu da shi ka yi magana da iyayen ta kawai hakan ya fi". "Ni ma nafi yarda da hakan a raina domin a bari ya wuce ya na kawo rabon wani tsaya kawai na saka a kira min shi yanzun nan mu yi magana tun da ba dare ne ya yi ba" Daddy ya fad'a ya na mi'kewa ya fita daga parlon na sa wani security ya samu ya aika shi cikin sirri ya ce yaje yayi masa magana da baban Sameer yace yazo yana neman sa da yaje 'kofar gidan a lokacin da 'yan 'kananan yaran gidan a waje d'aya ya aika yace "ka je kace ana sallama da mahaifin su Sameer" "to" yace ya na tashi ya shiga gidan a lokacin Abba yana zaune yayi shimfid'a a kofar d'akin sa sakamakon yanayi na zafi Umma ta kawo masa abinci zai ci yaron ya shiga yace "Baba wani mutum yana neman ka a 'kofar gida" da mamaki Abba yace "wani mutum kuma baka san shi ba"? "Eh yace na kira ka". "To kace gani nan ina zuwa" to khaleel ya ce yana juyawa ya fita shiru Abba yayi yasan shi dai bai da ba'ko sannan ba zuwa gurin sa ake ba wa yake dashi aikin me yake da zai samu jama'a har su ri'ka biyo shi gida shi da ba ma'aikacin gwamnati b................... Ya na cikin tunani ya ji muryar Asabe ta ce "ka tashi ka je man kana ji ana neman ka in kaji kira an samu amma ban da kiran d'an sanda irin su Aminu" Asabe tai maganar tana kallon yadda yayi shiru har lokacin bai motsa ba taci gaba "kar kasa idan alkhairi aka kawo maka ma mutumin yayi zuciya ya tafi watakil sadakar kud'i ko kayan abinci ne ko kuma ma suturar sawa dan Allah ka tashi ka je watakil gobe da kaji za mu karya da safe idan kud'i aka kawo maka" kallon ta Abba yayi bayan ya mi'ke a damuwance yace. "Ke abin da ya ke ran ki kenan"? Kai Asabe ta d'aga ta na cewa "tabbas abin da ya ke rai na kenan kuma na fad'a wa ya'ki dad'i sai dai idan bai samu ba" bai tanka mata ba sai takalman sa da ya saka ya fita a can gefen gidan nasu ya hango mutumin a tsaye har tsoro abun ya bashi shi fa bai ta'ba ganin sa ba Allah ya sa ba makirci aka had'a masa ba balle ya gan shi da shiga irin ta masu aikin d'amara 'kasawa yayi ya na addu'a a ran sa yayi sallama amsa masa security d'in ya yi yana cewa "kai ne Abdullahi mahaifin Sameer"? Kai Abba ya d'aga gaban sa na fad'uwa musamman da ya ga mutumin da uniform gashi ya ambaci sunan Sameer Allah ya sa ba wani laifin Sameer d'in yayi aka kama shi ba ji yayi yace. "Ok dama Alhaji Ahmad ne ya aiko na kira masa kai" da alamar tambaya Abba yace "wanne Alhaji Ahmad d'in"? "Wannan nake fad'a na nan anguwar yana cikin gida shine ya aiko a kira ka magana za ku yi" da sabon mamaki Abba yace "ni kuma suna na ka ji ya ambata Abdullahi ko Habibu headmaster ko kuma Aminu d'an sanda wanne ya ce"?. "A'a Abdullahi mahaifin Sameer ya ce idan kai ne mu je"? Jiki a sanyaye Abba yace "shi ke nan nine mu je d'in Allah ya sa lafiya" ya fad'a suna wucewa sosai jikin sa ya d'au rawa ganin gidan suka shiga inda bai ta'ba zuwa ba shi da ba kowa ba abun tambayar ya akai Alhaji Ahmad ya san sunan sa kuma yasan shi ne mahaifin Sameer? Har cikin parlon Daddy ya kai shi sannan ya fita Abba jikin sa na rawa yake shirin zama a 'kasan carpet Daddy yace "a'a a'a haba bismilllah ga kujera ka zauna" ya fad'a yana nuna masa kujerar dake kusa da shi da'kyar ya zauna yana kallon table d'in dake gurin an cika su da kayan cinye-cinye gwanin sha'awa ga kaji nan yana gani kamar a banza numfashi ya sauke yana d'an girgiza kai. Fuskantar sa Daddy yayi yana mi'ka masa hannu yace "barka da dare malam Abdullahi" hannun Abba na ma'kyar'kyata ya mi'ka masa suka gaisa numfashi Daddy ya sauke yana cewa "nasan ka ji mamakin me yasa nake neman ka duk da ni ya kamata na taka naje inda ka ke to amma gudun maganganun mutane yasa na ce ka zo nan mu tattauna ya fi sirri sosai akan a gan ni acan kofar gidan dole kowa zai so sanin abinda ya kai ni ko"? Kai Abba ya d'aga ya na cewa. "Eh gaskiya ne haka ne". "Yauwa masha Allah dama dan Allah Malam Abdullahi alfarma na ke nema a wajen ka" baki Abba ya bud'e ya na cewa "alfarma a waje na ranka ya dad'e ni fa"? ya fad'a yana nuna kan sa da mamaki jinjina kai Daddy ya yi yana cewa "kwarai a wajen ka alfarma me daraja ma nake nema Kuma abu ne me muhimmanci Aliyu ne yake son yarinya d'aya daga cikin yaran ka" a susuce Abba yace "a cikin yara na wacece"?. "Am Zainab sunan ta'" cak numfashin Abba ya tsaya tsoro ya gama cika shi taya za'ai shi da ya ke talaka Aliyu zai ce ya na son Zainab wannan al'amarin abun jawo maganganun mutane ne idan su ka ji ba zai ta'ba hutawa ba "innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ya fad'a a fili ya na dafe kan sa da hannu biyu gumin firgici ya fara fito masa ya ji Daddy ya ce. "Malam Abdullahi na san za ka d'an ji mamaki amma ba abun mamaki bane wannan lamarin Ubangiji ne sannan 'yar ka ta cancanti a so ta fiye da tunanin me tunani domin dukiya da mulki ba su ne kwanciyar hankali ba mace ta gari wacce ta fito daga babban gida mai cike da tarbiyya irin na ku tabbas bazan 6oye maka ba, ba Aliyu ba ni ma ina son wannan yarinyar ta shigo cikin ahli na dan Allah da fatan zaka amince domin na ga kamar ba kayi na'am da maganar ba"? Shiru Abba yayi jikin sa yayi mugun sanyi Daddy yaci "ko dai akwai wanda za ka ba ta ne kayi mata miji"? A hankali ya girgiza kai ya na cewa "a'a ban yi mata ba amma gaskiya wannan abun da ka zo min dashi akwai tashin hankali da damuwa sosai a cikin sa". "Saboda me"?. "Yanzu da zarar wannan maganar ta fito kowa cewa zai yi ba haka kawai Aliyu ya gan ta yace yana son ta ba"?. "Kamar ya kenan ban gane ba"? "Za'a ga yadda na ke talaka ba komai ne dani ba kamar ku ace d'an da ya fito daga gidan nan ne yake son 'ya ta"? Kai Daddy ya girgiza ya na kallon Abba wanda ya cire hular kan sa tsabar zafin da ya d'auka ya ce "Malam Abdullahi mu fa daraja da kimar ka da ta 'yar ka mu ke dubawa ba talauci ba arziki da talauci duka na Allah ne kuma shine yake jarabtar bayin sa da su dan ya gwada imanin su akam me Ubangiji ya yi maka ni'ima ka ke son bijire masa ni dai na fad'a zan sake fad'a ina son wannan yarinyar ta shigo cikin ahli na saboda hankalin ta da nutsuwarta da kuma tarbiyyar ta dan Allah Malam Abdullahi kar ka ce a'a"? Nannauyan numfashi Abba ya sauke yana kad'a kai cikin rashin sanin abun yi yace "to shikenan Allah ya za6a mana abinda ya fi alkhairi idan matar sa ce Allah ya bashi ita babu komai amma yanzu zan je gida zamu tattauna da mahaifiyar ta". "Ok ba damuwa ina godiya sosai idan na ga kwana biyu baku gama yanke shawara ba saidai ka gan ni a 'kofar gidan da kai na naje ro'kon ka" Daddy ya karasa maganar yana murmushi shi ma Abban murmushin dole yayi cikin ya'ke ya ce "insha Allahu da zarar mun gama magana da ita zan sanar da kai". "Ok ba damuwa Malam Abdullahi bismilllah fa abinci ka shigo hankali na ya d'auke mu ta magana" girgiza kai Abba ya yi da fara'ar sa ya ce "a'a Alhaji alhamdulillah alhamdulillah na gode sosai zan tafi duk yadda mu kai da mahaifiyar ta in sha Allahu za ka ji" ya fad'a ya na mi'kewa shi ma Daddyn mi'kewa yayi ya sake bashi hannu suka gaisa sannan suka fita tare ya d'an taka masa zuwa bakin gate aka bud'ewa Abba ya fita shi kuma Daddy ya koma ciki.............. πŸ’“ZUCIYAR ALIYU CEπŸ’“ Mai son complete document d'insa yai min magana ta WhatsApp number zai same shi akan Naira d'ari bakwai complete har 'karshe. WhatsApp no. +234 8160983083 #700 Acc. 2410673902 Nm. Yusrah Musa Bnk. Zenith Bank Me kamar sarki 300 Minister Ashraf 300 Safreeyyah 400 Royalty 500 YUSRAH MUSA ABUBAKAR ✨ DUTSE JIGAWA STATE πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 34 of 34