Share this page
da sauri ta d'auka ganin Samiran ce ta biyo bayan kiran ta na d'auka ta ce "hello Samirah hasashen ki ya tabbata ashe da gaske ne neman auren ya ke yanzu na tambaye shi zai fita ya ce min eh". "Kan bala'i aure dai kuma yanzu ke ya za ki yi"?. "Akwai yadda zan yi man kinsan anguwar da yake neman auren har gida zan je na ci wa yarinyar dazai aura mutunci na yi mata barazanar kisa idan ta aurar min miji shikenan abun da na ke so haka kawai ba hannun sa ne ya cud'i bayan sa ba d'an albashin da ya ke d'auka mu na samu ya na isar mu ya taro aure haka kawai mu dawo zaman 'kaili 'kalula". "Gaskiya kam gara ki je da kan ki ta ga idon ki, ki nuna mata bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane" kai Sabirah ta jinjina ta na cewa "shikenan ga ni nan yanzu zan shirya na fito mu tafi shi ma ai ba makaranta ya tafi ba maybe akwai abin da za suyi na ga ya d'auki littafai har za mu dawo" ta na fad'in haka ta kashe kiran tare da shiga bedroom a gurguje ta d'auko hijab da kud'i ta fito da key ta rufe gidan sannan ta tari d'an Napep ya kai ta rijiyar lemo gidan su Samirah ita ma a lokacin ta shirya kawai fitowa ta yi su ka tafi domin ta san anguwar kuma da suka sauka su ka yi tambaya aka nuna musu gidan shiga su kai da Rasheedat su ka fara cin karo zata shiga 'kofar Hajiya caraf Sabirah ta ri'ke mata hannu tana cewa. "Ke tsaya ke ce Zainab"? Cike da mamaki Rasheedat ta girgiza kai ta na cewa "a'a ba ni ba ce wacce 'kofar ta 'karshe za ku shiga da alama ku ma ta kar6i kud'in d'inkin ku kuma ba ta yi mu ku ba ko"? Tsaki Sabirah ta ja ta na wucewa ta ce"dallacan ban guri uban d'inki zan kar6a na rasa wacce zan kawowa d'inki sai ita" dariya Samirah ta yi ta na cewa "ita abun da ya dame ta kenan amma ai ba gurin ta ki ka zo ba da zaki huce haushin ki a kan ta"?. "Eh ba gurin ta na zo ba amma tun ki ka gan ta a gidan ai watakil 'kanwar ta ce" ta fad'a ta na tura murfin kofar shiga lungun su Zainab ta ce "assalamu-alaikum"! Asabe da ya ke ranar girkin ta ce ba kowa a kofar duk su na d'akin ita kad'ai ce a waje ta na aiki d'agowa ta yi jin anyi sallama ga kuma ba'kuwar fuska da bata ta'ba gani ba ya sa ta ce "wa alaikum salaam ba'ki da ranar nan haka sai da muka kusa sau'ke tukunya mu da ko 'kwayar shinkafa ba ma dad'awa akan abun da mu ke dafawa🙊" ta6e baki Sabirah ta yi tana cewa "ke ce karayayyiya kuma mayunwaciya uwar me zan yi da abincin wannan gidan ko an ba ni aina zubar balle ma Allah ya sauwake" kai Asabe ta jinjina tana kallon ta tace "humm dama na san za'ai haka tun da ki ka fara magana na san cewa ke dangin Hauwa ce daga zuwan ki har zaki fara yi min rashin arziki". "Ke ki ka san wata Hauwa har ki ka damu Ina ruwa na da ita" hararar ta Asabe ta yi tana cewa "to dai kar ki kuskura ki zage ni" a masife Sabirah ta ce "idan na zage ki za ki dake ni ne". "To shikenan zage ni ki gani" bud'e baki Sabirah ta yi za ta yi magana Samira ta rufe mata bakin ta na girgiza kai ta ce "ba gurin ta mu ka zo ba gurin 'yar ta ne". "Wacece 'ya ta" Asabe ta tambaya cike da fargaba domin ta san Bilki ba ta gida tun safe ta tafi gidan da take wanke-wanke da shara ko dai wani abu ta yi aka kawo 'karar ta? Ji ta yi Samira ta ce " 'yar ki Zainab" ta6e baki Asabe ta yi tana sauke ajiyar zuciya jin ba Bilki suke nufi ba cikin jin dad'i ta ce "a'a a'a Allah ya tsari gatari da saran shuka Zainab ba 'ya ta bace ni ban haife ta ba ga d'akin gyatumar ta nan ku shiga". "Ba shiga za mu yi ba kawai ki mana magana da ita". "Cafd'i ni ce zan yi muku maganar da ita ma kenan saboda tsabar samun gu akuya da tu'kin tuwo idan ku ba za ku yi mata magana da kan ku ba sai dai ku kwana a nan" ta na fad'in haka ta shige kitchen tsaki Samirah ta ja ta na cewa "ni fa na tsani harkar rainin wayo a rayuwa ta wannan matar ba mutunci ne da ita ba". "Bar ni da ita ina daidai da zamanin ta assalamu-alaikum wai ba kowa ne"? Sabirah ta dad'a fad'a ta na gyara tsaiwar ta fitowa Umma ta yi tana cewa "amin alaikum salaam su waye"? Jijjiga Sabirah da ke tsaye ta yi tana cewa "mu ne fito ki gan mu" da mamaki Umma take bin su da ido ba ta ta'ba ganin ko mutum d'aya ba a cikin su. "Sannun ku da zuwa daga ina"?. "Daga ko'ina ina 'yar ki Zainab take"? Da sabon mamaki Umma ta ce "lafiya dai ko"?. "Lafiya za ta kawo ni gurin Zainab ne har abada yanzu a duniya ina da wata ma'kiyiya sama da ita ne" d'aurewa Umma kai Sabirah ta yi shi ya sa ta kalle ta sosai ta na cewa "to me yayi zafi haka ko kun samu sa6ani da ita ne"? Tsaki Sabirah ta ja tana cewa "ni na ta'ba ganin ta ne ma da har zan samu sa6ani da ita ba dan yanzu da ta shigo rayuwa ta ba kawai ki fad'a min inda zan same ta" numfashi Umma ta sau'ke ta na cewa. "Ta je siyo kayan d'inki" ta na fad'in haka Zainab ta bud'o 'kofa da sallama ta na aje Ikram da ke hannun ta na 'ko'karin cire hijab Sabirah ta ce "ohhh yanzu na fahimta ko ba'a fad'a min ba ke ce Zainab tun da na ganki da nikaf ga hijabi har 'kasa haka ne"? Da mamaki Zainab ta kalle ta tana cewa "eh ni ce" zabura Sabirah ta yi tana cewa "au ke ce tsabar tsaurin ido ki ke ce min wai kece munafika dama kece annamimiyar da take son auren miji na? Hmm ai kuma kin yi kad'an wallahi kin yi tsararo ba ki kai ba tun wuri kafin lokaci ya 'kure miki ki je ki samu mijin aure domin Yaa Sayyidi yafi 'karfin ki babu 'yar iskan data isa na had'a kishi da ita idan tsautsayi ne ya ke kiran ki bismillah ki auri mijin nawa ni kuma na d'au alkawari sai na fard'e ki da wu'ka idan kunne ya ji jiki ya tsira idan kuma ki na ganin na yi 'karya ne dan Allah kar ki fasa ki aure sa zan nuna miki 'karshen ki" ta na fad'in haka ta juya fuuuu ta fice daga 'kofar Samirah ta bi bayan ta shiru Zainab ta yi cikin wani irin yanayi gabadaya ta rasa me ya ke mata dad'i ace ba dama saurayi ya fara neman ta sai an samu sa6ani Umma kam jin abinda Sabirah ta zo ta amayar a ya sa tace. "In dai dan Yaa Sayyidi ne ba shi kad'ai ne namiji ba insha Allahu Ubangiji zai kawo miki miji na gari ki na zaune tun da ta iya zuwa har gida tayi miki haka ina kuma da kin je gidan? Ba komai Allah ya rufa asiri" ta na fad'in haka ta juya d'aki Zainab ma jikin ta a mace da'kyar ta shiga na ta d'akin ta kwanta domin yadda jikin ta ya ke rawa ko ta hau kan keke ba za ta iya d'inkin ba dole sai ta samu nutsuwa. ZUCIYAR ALIYU CE ................PAGE 61 "A'a kai jama'a dad'i na da gobe saurin zuwa ayuririiiiiiiii wayyo dad'i zai kashe a gidan nan wato dai da alama fa Zainab ba za ta yi auren ba da gaske tun da gashi duk wanda ya fito sai an wargaje maganar wato ashe wannan matar Yaa Sayyidi ce ta zo har gida ta yi muku wankin babban bargo haka na ke so wallahi humm in dai zaman gida ne yanzu ta fara mu je zuwa bari na yi sauri na gama abinci na kai wa Hajiya daga nan sai na gulmata masa hehehehhhh" ta karasa maganar ta na fashewa da dariyar mugunta ba wanda ya fito balle su tanka mata kawai sun bar ta da fitowar rana da fad'uwar ta. Su na Napep Sabirah ta ke cewa "kai sai yanzu na ji dad'i da naje na kaddamar musu da zan bar abu a raina yayi ta damu na" dariya Samirah ta yi tana cewa "ai kin ban 'ko'kari ban ta'ba tunanin za ki iya fad'a irin haka ba sai da na gani". "Humm Samirah 'kyale ni kawai rai na ne ya 6aci da yawa babu wanda za'ai wa haka ya yi shiru balle ni Ina son Yaa Sayyidi sosai kamar rai na kuma yaushe zan bari wata ta shigo rayuwar mu na je ta raba mu shi ya sa tun abun baiyi nisa ba na yiwa tukar hanci" daidai me Napep ya tsaya su ka sau'ka Sabirah ta bashi kud'in sannan su ka shiga gidan. Yaa Sayyidi kam tun ya fita da safen sai bayan sallar magriba ya dawo a lokacin Samirah ta tafi bai zo ya same ta ba sai Sabirah da take ta faman cika ta na batsewa yasan akan maganar da su kai da safe ne shiyasa ma bai kula ta ba da yayi wanka ta kawo masa abinci ta d'auka zai tambaye ta fushin me take amma sai ta ga ya yi burus da ita cikin takaici ta ce. "Abban Nassar ashe dama waccan yarinyar ka ke so Zainab? Jin abun da ta ce ya sa ya fasa kai lomar abincin ya tsaya ya na cewa "ya akai ki ka sani"? Ta'be baki ta yi ta na kawar da kai ta ce "zancen duniya ba ya 6uya ai daka 6oye min ma an fad'a min wacce ita shi yasa na taka naje har gidan su nayi mata gargad'i" zaro ido Yaa Sayyidi ya yi ya na aje cokalin tare da d'aukar ruwa ya kur6a jin har lokacin abincin da ya ma'kale masa bai wuce ba ya ce. "Me ki ka fad'a mata"?. "Wannan kuma tsakanin mu ne". "Wai Sabirah ki na da hankali kuwa waye ya zuga ki kije gidan su Zainab kin yi hauka ne"?. "Idan haukan na yi ma kai ne sila ba kowa ba tun da hankali na ka aure ni kai ka ke son mayar dani me 'karamin ta6in kai kuma wallahi ka ji na rantse ba zan yi kaffara ba indai tsautsayi yasa ka aure ta sai na kashe ta" ta na rufe baki Yaa Sayyidi ya yi mata wani irin kallo ya na cewa "ai kuwa da ke ma sai an kashe ki" kafad'a ta d'age ta na cewa "ban damu da irin hukuncin da za'a yanke min ba in dai itan tabar duniyar hakan na ke so" ta na fad'in haka ta tashi ta bar gurin da kallo Yaa Sayyidi ya bi ta tare da yin shiru kamar me tunani daga baya ya mi'ke yana fita daga gidan ya tafi masallaci sai da akai sallar isha sannan ya dawo gida ya d'auki mashin d'in sa ya tafi anguwar Zainab a lokacin ta kunnawa Ikram kallo a wayar ta taji ana kiran ta ganin wanda yake kira yasa ta sa Ikram ta mi'ka mata wayar ta d'aga suka gaisa ya ce ta fito waje ya zo numfashi ta sau'ke tana ajewa Ikki wayar sannan ta d'auki hijab ta shiga d'akin Umma ta fad'a mata zata fita kallon ta Umma ta yi tana cewa. "Wannan Yaa Sayyidin ba shi ne wanda matar sa ta zo d'azu ba"?. "Eh shi ne" da mamaki Umma ta ce "amma kuma za ki je"? "Ai kuma Umma ba laifin sa ba ne maybe ma bai san matar tasa ta zo ba sai da ya koma gida". "To shikenan sai kin dawo Allah ya tsare". "Amin" ta ce ta na juyawa ta fita akan mashin d'in sa ta same shi a zaune sallama ta yi su ka sake gaisawa kafin ya kalle ta ya na cewa "wai d'azu da gaske mata ta tazo gidan nan"? Kai Zainab ta d'aga tana cewa "eh ta zo ashe ta fad'a maka kenan"?. "Ta fad'a min ai na d'auka da wasa take ashe da gasken dai tazo? Subanallah Allah ya rufa asiri shi ya sa da ta fad'a min na kasa nutsuwa dole sai na zo na baki ha'kuri dan Allah ki yi ha'kuri kin ji". "Ba komai a take na manta da abun ni ban ri'ke ta ba". "Yauwa masha Allah na ji dad'i sannan alfarma na ke nema kar wannan barazanar da ta zo tayi ya dame ki har tasa ki ji a ran ki cewa kin fasa aure na"?. "In sha Allahu hakan ba zai faru ba matar mutum kabarin sa idan akwai rabon aure tsakanin mu babu wani abu da zai hana" murmushi Yaa Sayyidi ya yi tare da shafa gemun sa ya ce "Alhamdulillah malama Zainab na ji dad'i sosai da ya kasance kin fahimce ni kuma na gode yanzu bari na koma gida dama dalilin zuwan nawa kenan" kai ta d'aga ta na cewa "shikenan ka gaida gida na gode sai da safe" ta fad'a ta na juyawa zuwa gida d'akin Umma ta fara shiga ta tarar da ita ta na karanta wani littafi na addini mai suna miftahul ibadat jin sallamar ta ya sa Umma ta d'ago ta na kallon ta tace. "Har ya tafi ne"?. "Eh ya tafi yanzu" jinjina kai Umma ta yi tana cewa "Allah ya kyauta Ubangiji ya 'kara rufa asiri ya za mu yi da rayuwar mu idan shi ne mijin na ki dole mu ha'kura ko ba ma so amma ni dai gaskiya Zainab lamarin yarinyar nan da tazo d'azu ya ban tsoro amma dai ba komai Allah ya tsare ki daga sharrin ta" jiki a sanyaye Zainab ta ce "Amin" kamar mara lafiya ta juya ta fita daga d'akin ba kuzari ko kad'an musamman yadda ta ga Umma ta damu akan abinda matar Yaa Sayyidin ta zo ta yi mata d'azun ta sani abun ya d'agawa Umman hankali kuma ya dame ta tun da har ta'ki ta manta, gaskiya ita kam indai Umma ba ta son auren nan gara ta ha'kura Allah zai kawo mata miji na gari duk daren dad'ewa duk mai ha'kuri ya na cin riba sannan indai har ka ro'ki Allah zai amsa maka idan ka tsaya a kofar sa zai kar6e ka idan ka nufe shi zai cika maka burin ka idan ka dogara da shi zai isar maka babu wani abu da ya ke faruwa ba tare da sanin sa ba shi ne sarki guda d'aya mai bud'awa gwanin jin 'kai mai tausasawa babu abin da ya 6uya gare shi dukkan fitar nishi da numfashi ya na sane ka dagora da shi ka ro'ke shi komai zai amsa maka ya biya maka bu'katun ka ya fitar da kai daga damuwa da ba'kin ciki shi ne Ubangiji abun nufi da bu'kata shi ne madogara shi ne mari'ka shi ne mafaka kuma shi ne matabbata daga gare shi mu ke sannan gare shi za mu koma, ya Ubangiji ka yi ma na rahma ka yalwata mu dukkan mu, mu bayi gare ka ne ya Allah ka gafartawa iyayen mu😭 Amin,,🤲. ❤️ZUCIYAR ALIYU CE❤️ JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION. J.W.A gidan kar6ar mutane hannu biyu da zaman lafiya. @YUSRAH DUTSE PAGE 62 Washe gari lahadi da ya ke a ranar Zainab za ta mayar da Ikram gida shi yasa bayan ta dawo daga islamiyyar wajen 'karfe biyu da rabi su ka je gurin wata me lallai a anguwar ta biya akaiwa Ikram su ka dawo gida ta iya kitso ta yi masa sannan ta yi mata wanka ta shirya ta dama ta fad'awa Sameer shi ne zai raka ta su mayar ta. Bayan ta shirya ita ma ta saka hijab da nikaf ta d'auki wata handbag d'in ta me d'an girma ta zubawa Ikram biscuits da chocolates sannan ta fito a lokacin Ikram ta na tsaye a gaban Umma wacce take zaune ta na tu'ka tuwon masara kallon ta yi bayan ta 'karasa gurin ta ri'ko hannun Ikkin ta na cewa. "Umma bari na je Yaya Sameer ya na chemist mun yi magana dashi shi ne zai raka ni na mayar da ita" kai Umma ta d'aga bayan ta gama tu'kin ta rufe tukunyar ta na cewa "to ba damuwa sai kun dawo Allah ya tsare" sai kuma ta kalli Ikram ta na murmushi ta ce "yar Abban ta yau sai kwanan gida ko ba za ki tsaya na gama tuwon ki ci ba"? Kai Ikram ta d'aga ta na ri'ke hijab d'in Zainab ta ce "gida zan tafi gurin Momy na". "Shikenan to ki gaida ita in ji wa zaki ce". "Cewa zan yi in ji Umman Aunty Mami" d'an murmushi Zainab ta yi tana kallon Ikki ta ce "wacece Aunty Mami kuma"? Nuna ta ta yi ta na cewa "ke ce Aunty Zainab zan cewa Momy na Umman Aunty Mami ta na gaida ita" dariya Umma ta yi tana "lallai Ikram ya yi kyau to ki gaida Yayan ki" to ta ce Zainab ta na ri'ke da hannun ta su ka fita daga 'kofar daidai Sameer ya shigo ya hango su. "A'a wai har kun shirya"?. "Eh tun d'azu dama gurin ka za mu fita ka kai mu ai". "Ok ai kuma ko wanka ban yi ba ya za'ai kenan"?. "Sai mu koma mu jira ka, ka yi" kai ya d'aga ya na cewa "shikenan mu je to" juyawa ta yi su ka koma Umma ta na d'aki ba ta san sun dawo ba sai da ta fito ganin takalmin da Zainab d'in ta saka a 'kofar d'akin ya sa ta ce "Zainab ki na ciki ne"?. "Eh ina ciki" da mamaki Umma ta ce"ya akai ku ka dawo bayan kun riga kun tafi kuma ko wani abu ku ka manta"?. "A'a Yaya Sameer mu ka dawo jira zai yi wanka". "Oh bai yi wanka kenan ya fita shikenan Ikram yau ma anan za ki sake kwana ba za ki ga Momyn ki ba" dariya Zainab ta yi ta na kallon Ikram wacce ta 6ata fuska ta na turo baki alamar za ta yi kuka cikin lallahi ta ce "yi shiru Ikki na da wasa Umma ta ke miki kar ki yi kuka yanzun nan za mu tafi gurin Momyn ki na mayar da ke kin ji"? Kai ta d'aga ta na goge ido alamar ya fara yi ma ta 'kai'kayin hawaye ta ce. "Mu tafi yanzu mu tafi gurin Momy na" ganin za ta d'aga ma ta hankali ya sa ta mi'ke ta na sakin nikaf d'in ta su ka fita waje daga d'akin har lokacin Sameer bai gama shiryarwa ba amma dai ya fito a wankan numfashi Zainab ta sau'ke ta na zuwa wajen 'kofar d'akin na sa ta ce. "Dan Allah Yaya Sameer ka yi sauri yarinyar nan za ta fara mun kuka" daga cikin d'aki ya ce "Subanallahi kuka kuma? Haba 'yar Abban ta gani nan yanzu zan fito mu tafi" Umma kam da take ta ayyukan ta ganin inda Ikram ta tafi ta tsaya a can wajen 'kofar shigowa lungun alamar ta matsu su tafi ya sa ta ce "Allah sarki Ikram anan za ta sake kwana ba mai a mashin d'in dawo ki zauna a nan idan na gama tuwo ki ci gobe sa mayar da ke" Umma na rufe baki ba zato su ka ji Ikram ta fasha kuka ta na zaman 'yan bori a gurin da sauri Zainab ta taho ta d'aga ta sai harharba 'kafa ta ke ta na ihu fitowa Sameer ya yi yana girgiza kai ya ce "kai gaskiya wannan yarinyar akwai caza kai wannan ai sai ta sakawa mutum ciwon kai ta na da rigima" dariya Umma ta yi ta na kallon yadda har lokacin ta'ki ta yi shiru sai faman jijjigen ta Zainab ke yi kamar wata jaririya ta ce. "Yau za mu huta sai dai ta je ta yi wa iyayen ta" kai ya jinjina yana cewa "sai mun dawo". "To Allah ya tsare Ikki ki gaida Abba da Momy ko"? Ta fad'a ta na kallon Ikram wacce ta yi shiru ta na kallon ta, fita sukai shi kuma ya d'auki mashin d'in na sa ya fita da shi zuwa 'kofar gida Zainab ta saka Ikram a tsakiya sannan ta hau bayan ta su ka tafi. Da yake dama Aunty Murjah ta san za su zo ita da Sameer su kawo Ikkin shi ya sa ta fad'awa Auwal shi kuma ya fad'awa Mukhtar zai zo su gaisa duk da Zainab ba ta sani ba sai da su ka je, su na zaune a parlor bayanta sun gaisa Zainab ta ce "to Aunty Murjah gashi na cika alkawari na dama kyan alkawari cikawa kamar yadda na d'auka na dawo miki da Ikki ki har gida" murmushi Aunty Murjah ta yi tana kallon ta tace "ai kuwa tun d'azu Mukhtar ya zo gidan nan saboda na fad'a masa yau zaki dawo da ita yace za ku yi magana suna ta jira ganin baki zo ba basu dad'e da fita ba shi da Sweet" da mamaki Sameer ya kalli Zainab wacce ta had'e rai ya na cewa. "Waye wani Mukhtar kuma" dariya Aunty Murjah ta yi ganin yadda Zainab ta ke dad'a cika ta ce "Mukhtar abokin Sweet ne ranar da mu ka je duba ta tare da shi ne dan dai ya na cikin mota ne a lokacin da ka je gurin na mu amma da za ka gan shi" kai Sameer ya jinjina ya na cewa. "Son Zainab d'in ya ke ko kuma yaya ban gane ba"?. "Eh man son ta yake sosai da gaske kusan shekara guda tun da ya gan ta tazo gidan nan da ace ta bashi fuska da yanzu an jima da yin bikin su domin tun a lokacin ya nuna min shi da gaske ya ke yi matsalar daga ita ne" ta'be baki Sameer ya yi yana cewa "ai kuwa ya had'a kan sa da wahala Zainab akwai wanda za ta aura ba rabon sa bace gara ki fad'a masa tun wuri ya nemi matar aure kafin lokacin ya 'kure masa" bud'e baki Aunty Murjah ta yi da mamaki ta zaro ido ta kalli Zainab wacce ta yi shiru kamar ba ita a gurin mai da hankalin ta kan Sameer ta yi ta na cewa. "Dan Allah Sameer da gaske ka ke kodan ka dakatar da Mukhtar ne"?. "A'a ba dan na dakatar da shi bane gaskiya na ke fad'a miki akwai wanda za ta aura" cikin matsuwa Aunty Murjah ta ce "to Masha Allah haka ake so ai waye wanda za ta aura dama kin tsayar da miji amma ba ki fad'a min ba da sai lokaci ya 'kure ko kuma ya"? Dad'a 6ata fuska Zainab ta yi tana juyawa musu baya ta'ki magana kai Sameer ya jinjina ya na cewa "ni za ki tambaya domin ni ne na san shi ba Zainab ba" dariya Aunty Murjah ta yi tana cewa. "Ah ah ban gane kai zan tambaya ba ita ba kenan ka fita sanin sa"?. "K'warai domin ita wacce ki ke tambayar ita ma ba ta san waye ba". "Ji Kayan tashin hankali ba ta san shi ba me akai kenan waye zaiyi irin wannan auren ka bar ta kawai ta auri Mukhtar d'in ya fi". "A'a an riga shi". "To in dai haka ne sai ka fad'i wanda ya riga shi mu ji waye"?. "Wani 6oyayyan masoyi ne ba yanzu za ki san shi ba sai ya bayyana" kai Aunty Murjah ta girgiza ta na cewa "kai dan Allah Sameer please ka barta ta auri Mukhtar ka ji" saurin girgiza mata kai shima ya yi yana cewa "a'a akwai wanda zata aura ki fad'a masa kar ma ya ji cewar ya na da rabo an riga shi" ha6a Aunty Murjah

Chapter 25 of 34